a hannunta ta wanke a cikin kofin. Shi dai Jalil kansa na saman cinyarta har bacci ya fara ɗaukarsa saboda daɗin wanka da ta yi masa. Ɗaukar kofin ta yi tare da zuba ruwan kaɗan a kunnansa tana murmushi. Firgigit ya tashi.
'' An Jalilina ne yaron mamanshi, yaro mai kyau''
Tana mishi wasa tare da juya kansa ta kuma zuba ruwa kaɗan a cikin kunnan,sai da ta tabbatar ya shiga cikin kunnan duk da ya firgita amma hakan bai dameta ba. Miƙar da shi tsaye ta yi tana jijjigasa,a tunaninta ruwan da ke cikin kunnansa ya shige ciki sosai. Da yake Jalil ya fara tafiya don yana wata na takwas ne da haihuwa. Ɗaukarsa ta yi tana cilla shi sama shi kuma yana dariya.
''Na tsani uwarka! Na tsani uwarka ɗan Jalil! Yaron mamanshi! Yaron mamanshi ɗan Jalil''
Tana ɗaga shi sama tana masa waƙa,shi kuwa sai dariya yake ɓaɓɓaka mata. Haka ta fito da shi daga bayin su na dariya tare kamar wani abu bai faru ba. Lokacin Mairi na kicin tana girki. Kai tsaye suka wuce ciki ta ɗauko man shafawa ta fara shafa masa,tsaf ta milke shi da mai, bayan ta kammala sai ta ɗan waiga ta ga babu mai shigowa kuma Yasir yana tare da Mamarsa a kicin da sauri ta lakaci man ta tura masa a duburarsa, sai da ta tabbatar man duka ya shige ciki. Hodar zafi ta barbaɗa masa a jiki kasancewar lokacin zafi ne ba a fara ruwa ba. Miƙewa ta yi tare da shi ta fita zuwa kicin
''Yaya Mairi ina kayan Jalil na saka masa?"
''Ki shiga ɗakina a drawer na farko kayansa suna a nan. Sai ki duba saman mirror na fito masa da tsumman ƙunzugu da zan yi masa nafkin.''
''To yaya Mairi bari na shiryasa sai na zo na amsheki''
'yar dariya Mairi ta yi
''Sahura kenan,ai aikin da kika yi haka ma ya wadatar, yi zamanki wallahi. Na gode sosai ''
''To bara na je na ɗauko''
Ta fito daga kicin ɗin zuwa ɗaki,bata tsaya a nan ba ta ƙarasa cikin uwar ɗakan Mairi. Tana shiga ta tsaya kalle-kalle tana taɓe baki. A ranta tana faɗin 'Aikin ɓur in ji tusa,kwanan nan zan yi kayan da suka fi naki'. sai da ta gama kalle ɗakin tsaf! Har tana 'yan dube-dubenta daga baya da nufi drawar da Mairi ta ce kayansa na ciki ta zaɓar masa.Bayan ta ciro sai ta ɗauki tsumman ƙunzugu da yake saman mirror ta fito. Shiryasa ta yi cikin riga da wando wanda ya yi matuƙar yi masa kyau sosai. Jalil kyakkyawa ne sosai,kamanninsa ɗaya da mahaifiyar har baƙin. Yasir kuma ya biyo mahaifinsa, fari ne sosai amma bai kai Jalil kyau ba. Don Jalil akwai manyan idanu da zara-zaran gashin ido kamar mace. Sosai Sahura ta tsura masa ido wani abu mai tsini yana cakar mata zuciya a kansa. Haka nan ta ji ta tsani yaron ba kamar Yasir ba. Ko don Yasir yana kama da ɗan uwanta ne shi ya sa. Muguntar ma bata ma Yasir ba sai shi. Miƙewa ta yi da shi suka fito waje, kicin ta nufa lokacin Mairi ta kammala haɗa shayi ta zuba a flask, yanzu ƙwai take soyawa.
''Yaya Mairi kamar Jalil na son mama fa,don tun ɗazu yake 'yan koke-koke"
''Oh Allah! Jalil ba dai tsotso ba wallahi''
Amsar shi ta yi ta zauna a saman turmin da ke cikin kicin ɗin ta ciro mama ta fara basa,ita kuma Sahura ta ci gaba da soya ƙwai da yake guda bakwai Mairi ta fasa. Tana tsaka da suyar suka tsinkayi sallamar Dauda Imamu cikin gidan. Da gudu Yasir ya je wurin mahaifinsa yana masa oyoyo. Ɗan kallon Dauda Imamu Sahura ta yi tana murmushi tana ganin yadda idanunsa suke nuna tsantsar ƙaunar Yasir. Juyawa ta yi ta ci gaba da aikinta a ranta tana fatan wata rana ita ma za ta haifa masa kyawawan 'ya'ya kamarta.
''Barka da safiya Baban Yasir ''
Mairi ta faɗa tana masa murmushin da yafi ƙauna akodayaushe. Martanin murmushin ya mayar mata tare da amsa mata cike da kulawa ya kafeta da idanunsa. Sahura dai na kallon ikon Allah,a gabanta mijinta yake wa wata banza kallo irin na ƙauna. Wani abu mai tsini da kaifi ta ji ya soki ƙahon zuciyarta tamkar mashi. Ganin bai ma lura da ita ba hankalinsa na kan matar so ya sa ta gaida shi cike da girmamawa har da ɗan russunawa. Cike da kulawa ya amsa mata tare da tambayar ya baƙunta. Ta amsa tana duƙar da kanta. Ba haka ta so ba, ba haka take fata ba,burinta bai wuce ta ga ya mata wannan kallon ƙaunar da yake jifan Mairi da shi tare da murmushin nan me kwantar da zuciya,amma ba komai akwai lokaci. Wucewa Dauda Imamu ya yi zuwa ɗaki da ledoji a hannunsa, Mairi ta bisa tana masa magana ƙasa-ƙasa shi kuma yana 'yar dariya haɗe da girgiza kai. Rungume hannu Sahura ta yi tana bin inda suka bi da kallo. Wato don ba a ɗauketa a bakin komai ba shi ya sa maganar ma Mairi a hankula take yi duk don kar ta ji. Cije laɓɓanta ta yi da ƙarfi tare da runtse idanu tana tuno yadda Dauda Imamu ke 'yar dariya. Sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta yi tana girgiza kai. An ya za ta iya jure mijinta yana ma kishiyarta kallon ƙauna a gabanta kuwa? An ya za ta iya amfani da kuɗubar mahaifiyar akan rintse idanu daga kallon abin da suke yi kuwa? An ya za ta iya zamowa kurma daga sauraran batutuwansu kuwa? An ya? An ya? Tambayoyi ne bila adadin suke rangaji a cikin zuciyarta. Ƙauri hancinta ya jiyo mata,da sauri ta juya wurin suyan tare da zare ido tana rage ƙarfin rishon. Kwan har ya fara ƙonewa,cikin sauri ta cire ƙwan tare da goge kaskon da tsumma ta sake ɗorawa. Har ta gama bata sake yin wani tunanin ba. A can falo Mairi ta ba shi labarin abubuwan da Sahura ta yi a gidan.
''Haka ake so, Allah ya ci gaba da haɗe kanku,nasan in dai wurin aiki ne ba za ki taɓa samun matsala da Sahura ba don akwai aiki sosai. Tun da nake zuwa wurin Kawu ban ganinta zaune, kullum cikin aiki take'''
Kafin Mairi ta ce wani abu Sahura ta shigo ɗakin bayan ta yi sallama. Kuma ta yi abin da Dauda Imamu ya ce akanta. Sai dai ta fiske duk da ranta ya yi matuƙar sosuwa,to wai me suka mayar da ita ne? *JAKA* lallai da Sahurar gwaggwan bugaje suke.
''Har kin kammala Sahura? Ina shirin ta shi na sameki Jalil yaƙi bari na''
Murmushi Sahura ta yi ta faɗin
''Ba komai Yaya Mairi,kin san namiji da tsotso''
''Haka ne kuma''
Mairi ta ce tana miƙa wa Dauda Imamu yaron ta fita zuwa kicin ɗauko kofofin da plate ɗin da za a saka kwan. Bayan ta dawo sai ta zuzzuba wa kowa a plate ta miƙa masa tare da haɗa masa tea. Bredi kuma kowa ya ɗiba da hannunsa,ga mamakin kowa wanda Sahura ta ɗiba ya fi rabi. Babban bredi ne mai tsada ga saurin ginsarwa. Yasir tun a kicin ya ƙoshi,tea kawai ya sha don bai cika son bredi ba. A nutse suke karyawa tare da hira jefi-jefi wanda sukan saka Sahura a ciki har suka gama. Sahura ta kwashe kayan ta nufi kicin da su ta wanke. Mairi kuma ta tsaftace ɗakin. Koda Sahura ta dawo Mairi ta kammala goge inda tea ya zuba. Bayan kowa ya natsu sai Dauda Imamu ya yi gyaran murya tare da fara magana.
''To Alhamdulillah. Godiya ta tabbata ga Allah Sarkin Sammai da Ƙassai,wanda ya ba mu lafiya tare da ni'imar Musulunci. Akodayaushe bawa dole ya kasance mai tawakkali da yin kyakkyawan zato ga Ubangijinsa. Mairi"
Ɗan ɗagowa ta yi ta dube sa ba tare da komai ba.
''Ga 'yar'uwarki nan Sahura,ina so ki riƙeta da gaskiya da amana. Idan ta yi ba daidai ba a matsayinki na babba ki gyara mata cikin hikima irin naki. Ban da shakka balle kokwanto a kanki"
''In shaa Allah za ka sameni cikin masu riƙon amana da gaskiya. Allah ya taya ni riƙo''
Da Ameen suka amsa. Sai ya juya wurin Sahura da ke rarraba ido a tsakaninsu.
''Sahura ga yayarki nan Mairi,na san halinta,na san abin da za ta aikata da wanda ba za ta aikata ba. Don haka bana son faɗa. Ki zauna tsakaninki da Allah da ita. Ban da gulma da tsaigumi da 'yan layi. Don sa'anarsu kenan faɗa da junansu. Babu ruwanki. Ga 'yar'uwarki idan kina da wata shawarar da kike so ki yi to da ita ya dace ki yi ba 'yan layi ba. Bana so ki yi ƙawance da kowa a layin nan,ban ƙi zuwa barka ko rasuwa idan ta kama amma ban da suna. Daɗin daɗawa ba na aureki ba ne don bana son matata. Ina ƙaunarta ƙauna mai tsanani. ''
Miyau mai ɗaci Sahura ta haɗiye muƙut! Cike da takaici ta ce
''To Allah ya haɗa kawunanmu gabakiɗaya ''
Da ''Ameen'' suka furta
''To sai abu na ƙarshe,Mairi ya kwanan kike so ya kasance''
''To Baban Yasir ni dai a nawa shawarar,bayan ka yi kwana uku a ɗakinta yanda ake wa bazawara sai ka koma yin kwana bibbiyu a ɗakin kowacenmu''
''Maa shaa Allah hakan ya yi daidai ɗari bisa ɗari. Allah ya haɗa kawunanku, ya kawar da sharrin shaidan da mutanan gari a tsakaninmu bakiɗaya''
''Ameen '' suka amsa. Miƙewa Sahura ta yi ta nufa ɗaki, ranta a matuƙar jagule yake. Ƙiri-ƙiri ana nuna mata son kai. Wannan wace kalar rayuwa ce,tun kan aje ko'ina ta fara karaya. Anya kuwa! Ta tambayi kanta. Ganin tana niyyar caja ƙwaƙwalwarta sai kawai ta bar tunanin ta yi kwanciyarta.
^^^^^^^^^^^
Wasa-wasa Dauda Imamu gobe zai koma ɗakin Mairi bayan sauke haƙƙin Sahura na kwana uku a matsayinta na bazawara. Cikin dare Dauda Imamu ya farka shi da Sahura sakamakon kukan da Jalil yake yi, na yau yafi na kullum don da iya ƙarfinsa yake. A hankali ya miƙe ya fita zuwa ɗakin Mairi. Da harara Sahura ta bi bayansa don bai san ta farka ba. Ya yi lallashin duniya amma Jalil yaƙi shiru,ga shi yaƙi amsar nonon. A daran dai ba su rintsa ba sai gabanin kiran sallar farko ya samu bacci. Sai a sannan Dauda Imamu ya koma ɗakin Sahura. Ta ji dawowarsa don ba bacci take ba idanunta ne dai a ɗan rufe. Takaici gami da ƙunar zuciya suka taru suka yi mata dirar mikiya. Ta tsani kukan yara musamman wannan yaron wanda yake hanata bacci cikin natsuwa ita da mijinta. Tana jin ya shimfida dadduma ya juya mata baya ta galla ma bayansa wata uwar harara kamar idanunta za su zazzago. Ɗan kwanakin nan da ta yi da shi,abin da ta lura shi ne mai yawan ibada ne sosai. Ita kuma ta tsani hakan don bata manta kalaman mahaifiyarta ba _'Sahura kin ga mai yawan addu'a da sallar dare wuyar mallakuwa yake. Da ƙyar na iya mallakar babanku don har sai da na kusan tafiya tsindir kafin na yi nasara. Ban sha wahala ba wurin asirce su Tsahara ba, ina fatan mijinki ba ya cikin masu sallar dare don ina jiye mana wahalar da za mu sha'_ Sake galla wa bayansa harara ta yi sannan ta juya wurin kwanciyarta. Bayan sallar asuba Sahura ta koma ɗaki da yake sun raba aikin gidan tun da har yanzu tana cikin amarci. Bata jima da kwanciya ba ta ji sallamar Dauda Imamu falo,tana a kwance ta ji ya wuce ɗakin Mairi yana tambayar ko su tafi asibiti ne. Ba dai ta ji me Mairi ta ce. Sake gyara kwanciyarta ta yi abinta. Bacci ya kasa ziyartarta saboda kukan Jalil. Bayan wasu 'yan mintuna gari har ya fara haske Dauda Imamu ya leƙo ɗakin tare da kiran Sahura. Kamar mai baccin gaske a hankali ta amsa tana miƙewa tare da murza idanu.
''Mun wuce asibiti don kukan yaron nan ba na lafiya ba ne''
''Yaya ba za ku bari safiya da ƙara yi ba, cikin duhun asuba za ku?"
''Gwara muje yanzu, asibitin mu ba irin naku ba ne na Sakkwato kodayaushe akwai malaman asibiti. Mu mun wuce''
Yana gama faɗin haka ya saki labulan. Taɓe baki ta yi sannan ta miƙe ta fito, lokacin Mairi tana goya Jalil wanda har yanzu kukan yake kamar ƙara ingiza shi ake.
''Yaya Mairi ina kwana. Jalil ashe kuka ya yi ta yi miki cikin dare"
''Wallahi kuwa,tun daran shekaran jiya ya fara yi mini kukan amma na daren yau yafi tsananta don ko rintsawa ban iya yi ba''
''Wayyo! Allah ya ba shi Lafiya. A dawo lafiya ''
''Ameen. Yawwa na ce ga Yasir nan na bar shi yana bacci, don Allah idan ya farka ki yi masa wanka kafin mu dawo in shaa Allah ''
''To. Allah ya tsare''
Ameen ta furta tana barin ɗakin. Dauda Imamu yana waje yana jiranta. Da yake yana da babur sai ta hau suka tafi. Bayan fitar Mairi Sahura ta saki dogon tsaki
''Aikin ɓur in ji tusa. Kwa yi kwa gama Sahura ce dai wacce bata barin ko ta kwana,da sannu zan yi maganinku. Allah ya sa idan kun je likitocin su ce ba su san abin da za su yi mishi ba. Shikenan sai ya zama bebe hankali kwance. Mtss!"
Ta sake buga uban tsaki sannan ta koma ɗaki ta yi kwanciyarta.
^^^^^^^^^^^
*Yariman Bakura specialist hospital*
A can asibiti su Mairi ba su ga likita ba sai nurses da yake da sassafe suka je. Sai wurin bakwai na safe yake zuwa. 'yan dube-dube aka masa wanda suke da tabbacin ba jikinsa ke masa ciwo. Dole sai likita ya zo don aikin ya fi ƙarfinsu ga shi har yanzu Jalil kuka yake. Sun yi zaman kusan awa ɗaya da rabi daga bisani suka shiga ofishin likita. Umurtar Mairi ya yi da ta ɗora Jalil a saman gadon duba marasa lafiya.bayan ta ɗora shi sai ya shiga dubasa, idanunsa, kansa da kunnansa. A nan ya ga lemar ruwa a kunnan. Hannunsa da ke cikin hand glove ya sa ƙaramin yatsar ciki ya taɓo ruwa. Cike da mamaki yake kallon hannunsa. Da yake likitan ya karanci abin da ya shafi kai har maƙogaro. Hance,kunne, baki da dai sauransu.
''Zo ki ɗauke shi " ya faɗa yana komawa mazauninsa. Bayan ta ɗauke shi ta dawo ta zauna tana miƙa wa Dauda Imamu Jalil.
''Ya aka yi kike barin ruwa yana shiga kunnan yaron?"
Ya jefo mata tambayar lokaci guda yana kallonta. Mamaki ne ya cikata ita kuwa hauka take da za ta bari ruwa ya shiga kunnan yaronta. Bayan ta gama musu wanka har hura kunnuwansu take don ta tabbatar da ruwa bai shiga ba.
''Dakta wallahi koda wasa ba na yarda ruwa ya shiga kunnuwansu, idan ma na kammala musu wanka har hure kunnuwansu nake don tabbatar da ruwa bai shiga ciki ba''
''To dai ɗanki ruwa ne a cikin kunnensa,shi ya haifar masa da yawan kukan da kuka ji yana yi tun da bai da bakin magana. Dole sai mun yi mi shi wankin kunne mun tsatso ruwan kar ya taɓa masa dodon kunne''
''To Dakta duk yadda ka ce shi ne daidai'' Dauda Imamu ya faɗa a sanyaye.
Miƙewa likitan ya yi ya ce ta biyo shi da yaron. Babu musu ta bi shi,yana gaba tana biye tamkar raƙumi da akala har suka shiga wani babban ɗaki da akwai na'urori da dama sosai. Nurses biyu suka shigo da yake don su taimaka masa. Amsar Jalil ɗaya daga cikin nurses ɗin ta yi tare da ce ma Mairi ta koma waje. Nan ma ba bata musa ba ta fito. Sun ɗauki tsawan lokaci a cikin ɗakin daga bisani suka fito da Jalil . Amsarsa ta yi idansa biyu amma kuma ya daina kukan sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Sai ta bi bayansa zuwa ofis. Dauda Imamu da ke wajen ofis ɗin zaune ya miƙe da sauri yana tambayar har an kammala aikin. Jinjina masa kai ta yi sannan suka shiga ciki a tare.
A can kuma gidan Sahura ta sha baccinta sosai har Yasir ya ta shi yana kuka ganin bai ga mamarsa ba. Kukansa ne ma ya tayar da ita. Tsaki ta ja tare da yin miƙa ba salati. 'yan aikace-aikacen gida ta shiga yi sannan ta yi wa Yasir wanka ta shirya sa. Sai bayan da ta yi wanka sannan ta girka musu ruwan shayi. Daman akwai sauran bredi da jiya suka karya da shi. Bini-bini sai ta buga tsaki. Da zaman ɗakin ya isheta sai ta shiga ɗakin Mairi ta ɗauko tabarma ta shimfida a waje ta yi zamanta. Yasir na falo yana wasansa da mota. Bata daɗe da zama ba ta ji sallama wata mata wacce ba za ta haura shekaru ashirin da biyar a duniya. Babu yabo ba fallasa ta amsa mata sallamar
''Maman Yasir na ciki?" Matar ta tambaya
''A'a bata nan''
Juyawa ta yi har za ta fita sai ta dawo tana duban Sahura ta ce
''Ammm baiwar Allah amma ke 'yar'uwarta ce hala''
''Kishiyarta ce'' Ta faɗa a gadarance tana kallon ƙwayar idanunta. Waro idanu waje matar ta yi tana sakin baki.
''Don Allah da gaske kike ke kishiyarta ce?"
'yar dariya Sahura ta yi
''Ƙwarai kuwa ki faɗa ki ƙara, mijinmu ɗaya Dauda Imamu. Kwana na huɗu kenan da zuwa ni 'yar kawunsa ce, kwana shida kenan da auranmu''
Wata bazawarar dariya matar ta shiga ƙyaƙyatawa kamar wata zautatta har da ƙwalla. Galala Sahura ta tsaya tana kallonta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tare da rangaɗa guɗa
''Ayyiririiiii! Daɗi kasheni ni 'yar ƙuda...✍️''
_____________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
______________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_Narrnarhh Bukar_*
_(Lady with the Amazing pen✍️)_
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_003_*
Wata bazawarar dariya matar ta shiga ƙyaƙyatawa kamar wata zautatta har tana ƙwalla. Galala Sahura ta tsaya tana kallonta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tare da rangaɗa guɗa
''Ayyiririiiii! Daɗi kasheni ni 'yar ƙuda! Na kuwa ji daɗi da Baban Yasir ya ƙara aure,ta ji yadda zuciyata ta soyu lokacin da ni ma aka ƙaro mini kishiya. Ai daman na faɗa sai Allah ya saka mini''
''Ban gane inda zancenki ya dosa ba baiwar Allah ''Sahura ta faɗa tana matsowa kusa da ita. Ɗan taɓe baki 'yar ƙuda ta yi sannan ta ce
''A lokacin da aka danƙaro mini kishiya ƙafarta bata tako zuwa gidana taya ni alhini balle dannar ƙirji. Da muka haɗu a gidan barka ta yi mursisi abinta. Ai Allah ba azzalumin bawa ba ne. Yanzu ga kishiya nan an ƙaro mata galleliya sabuwa fil a leda,ta ji yadda zuciyata ta ji''
Riƙe baki Sahura ta yi da faɗin ''Au Allah! Haka daman take! A fuska kamar ta annabi ashe mugun hali gareta! To gwara da kika sanar mini kin ga na ci maganin zama da 'yar ƙwal uba''
Washe baki 'yar ƙuda ta yi jin furucin Sahura,da alamu dai za a yi tafiyar da ita.
''Kar ki damu ƙawata mun zama ɗaya yanzu, zan sanar miki waɗansu sirrika da za su taimaka miki wajen zama da ita. Idan kin samu lokaci ki zo mu tattauna tun da tana zuwa makaranta, Baban Yasir ma haka. Gidana na kallon gidanku''
''Kar ki damu in shaa maka Allahu za ki ganni kuwa,yooo ni da nake neman hanya ruwa a jallo na samu a ɓagas 'yar uwa! Za ki ganni wallahi!. Sun tafi kai shegen ɗanta na goye mai idanu kamar na mujiya asibiti,ya addabemu da kuka.''
Taɓe baki 'yar ƙuda ta yi tana huro buɗaɗdun hancinta
''Kaɗan kika gani in dai Jalil ne. Kin ga! na yi tafiyata kar su iskemu tare su zargi wani abu. Bakinki alaikum idan kina son ƙawancanmu ya ɓulle'' ta yi maganar tana nufar waje. Sahura bata yi ƙasa a gwiwa ba ta rakata har ƙofar gidan tana mata godiya da alƙawarin kawo mata ziyara idan ta samu lokaci. Bayan ta dawo cikin gidan farin ciki mara misaltuwa ya kewaye lungu da saƙon zuciyarta. A hankali ta zauna a saman tabarma tana sakar wa kanta murmushi akai-akai,da alamu dai ta zo da sa'a gidan Yaya Dauda Imamu, hancinta sun fara jiyo mata ƙamshin nasara. Ta jima tana tattaunawa da zuciyarta,da ta gaji da zaman ta koma cikin falon, har ta zauna sai kuma wata zuciyar ta umurci ta je ɗakin Mairi sake ganin ƙwaƙwaf. Zumbur ta miƙe har Yasir da ke wasa da mota ya ɗan dubeta sai kuma ya cigaba da wasansa yana gwarancinsa shi kaɗai. Tsaf ta natsu tana kallon yadda ɗakin ya tsaru ya yi kyau wanda ko a sakkwato mai irin kayan sai 'yar attajiri. Gadon katako ne fari 6by7 wanda sai 'yar wane da wance. Ga saitin samiru a bango ɗaya rairas. Cije laɓɓanta ta yi da ƙarfi wani abu mai kauri ya tsaya mata a daidai wuyanta.
''Yanzu duka waɗannan kayan Yaya Dauda Imamu ne ya yi ma 'yar ƙwal uban nan! To wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa. Ni ma dole a gwangwaje ɗakina da irin waɗannan koma su fi waɗannan,domin sawun giwa ya take na raƙumi. Hhhhhh! Cab! '' Ita kaɗai take maganar tana ƙara kallon ɗaki. Ta jima a ɗakin tana dube-dube wai ko za ta ga inda ta ɓoye asiri a wani wuri,don ita bata yadda da son da Dauda Imamu yake wa Mairi na gaskiya ba ne. Haka ta haƙura ta bar ɗakin kar su dawo su sameta ciki. Falo ta dawo abinta. Ganin har 10:30 na safe ya yi amma har yanzu ba su dawo ba. Ta nufi kicin don ɗora sanwa, a gidansu ana gama karin safe ake ɗora na rana kasancewar suna da yawa a gidan. Inda aka ajiye kayan abinci a cikin kicin ta nufa, ganin akwai komai baja-baja ta kunna risho tare da ɗora babbar tukunya mai cin loka guda na shinkafa. Tumaturin da ke wurin ta kwashi kusan rabi da tarugu da albasa sai ta fito da turmin waje ta fara daka. Lokaci bayan lokaci tana duba tukunyar a kicin. Yasir da ya gaji da wasan ya fito waje ya zauna saman tabarma. Ta yi nisa a girkin ƙofofin kunnuwanta suka tsinkayi sallamar Mairi da Dauda Imamu. Da gudu Yasir ya je garesu yana murna.
''Sannunku da zuwa'' Sahura ta faɗa tana miƙa hannu za ta ɗauki Jalil. Noƙewa ya yi jikin mahaifiyarshi yana shirin sakin wani sabon kuka.
''Ai tun da ya fara wannan kuka yake ƙyuiya har malaman asibiti bai bar su ba''
Murmushin da bai kai ciki ta yi tana satar kallon Dauda Imamu da ya shagala wasa da Yasir.
''Girki kika ɗaura ashe'' Mairi ta tambaya.
''Eh yaya Mairi,ai na ji shiru-shiru ba ku dawo ba,ga hantsi ya fara duban ludayi shi ya sa''
Murmushi Mairi ta yi tare da miƙa wa Dauda Imamu shi,abin mamaki da fara'ah ya mika hannunsa. Suka shige ciki,sai ta nufi kicin ɗin. Mamaki sosai ya cikata ganin aika-aikar da Sahura ta yi da kayan abinci. Duban Sahura ta yi
''Sahura ai kin cika abincin,ina za mu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 33