kai shinkafa loka guda? ''
Ɗan ɓata fuska Sahura ta yi don ba haka ta so ji daga bakinta ba.
''Yaya Mairi yi haƙuri kin san na saba da girkin gandu, na za ci girkin har dare ne ba sai an kuma yin wani ba irin na gidanmu.''
'yar dariya Mairi ta yi ''A'a! mene ne na ba ni haƙuri kamar kin mini laifi. Ba komai wallahi. Baban Yasir bai cika son abinci mai sanyi ba musamman da daddare. Shi ya sa nake girki biyu a rana. Karin safe sai girkin dare da yake baya wuni gida sai yamma yake shigowa.''
''Ai shikenan zan kiyaye na gaba''
Daga haka suka ci gaba da aikin a tare har abinci ya kammala wanda a lokacin an kusa kiran sallar azahar. Cikin kuloli Mairi ta zuba abincin tare da kai su cikin falo ta bar Sahura a kicin. Plate ɗaya na shinkafa ta take sannan ta koma cikin falon. Bata tarar da Dauda Imamu ba sai Mairi tana shayar da Jalil. Zama ta yi har aka kira sallah sannan ta fita ɗauro alwala. Bata iske Mairi a falon ba ta wuce ɗakinta buga sallarta ta 'yar faki ba yawa sai lada. Koda ta idar bata fito ba ta yi kwanciyarta tun da cikinta ya dau lodi.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidan Dauda Imamu inda Sahura bata bar koda taku ɗaya wanda za a gane halayyarta ba. Cike da salo irin na hawainiya take komanta, sannan bata daina yi musu laɓe ba.A ɓangaren zamantakewarta da Dauda Imamu ba laifi yana kyautata mata daidai gwargwado. Bata ganin kyautatawan idan ta haɗa da yadda yake nuna tsantsar kulawa ga Mairi da yaranta,sai ta raina kanta,ƙiyayyar da ta ji akan ya sake linkuwa. Jalil kuma tun daga ranar ya fara mata ƙyuiya, baya yadda da ita kwata-kwata.A cikin satin ta samu damar zuwa gidan 'yar ƙuda,inda ta samu sabbin darussa waɗanda tamkar muggan makamai ne da za ta yi amfani da su wurin kai abokiyar zamanta ƙasa warwas!. Da zarar Mairi ta tafi makaranta sai ta kulle gidan ta nufi gidan 'yar ƙuda a can suke kafa majalisa su yi ta ƙulla makirci kala-kala ga abokan zamansu. Burinsu ɗaya,tafiyarsu ɗaya sannan BAHAGON TUNANINSU iri ɗaya ne a kan abokan zamansu. Sun zama tamkar ɗan juma da ɗan jummai. 'yar ƙuda irin makiran matan nan ne masu tsananin kishi, ba su da lokacin kula da yaransu balle mazajensu sai zafin kishi da mitar magana,wanda dalilin haka ne ya sabbaba wa mijinta ƙaro mata kishiya duk da ba a gida ɗaya suke ba amma bata tsira daga sharrinta ba. Abu mafi muni daga cin halayyar 'yar ƙuda shi ne kyakkyawan ƙawancen da ta ƙulla da ƙazanta tare da rashin iya girki. Bambancinta da Sahura abu biyu ne: ita Sahura ta iya girki sannan tana da tsafta sosai. Mugun hali ne dai ya zo irin ɗaya.
A gefe guda Dauda Imamu yana koyarwansa da sayar da hatsinsa. Wani abu da ke ci mishi tuwo a kwarya shi ne ƙarancin addinin da Sahura ke fama da shi. Ya yi matuƙar mamaki a daren da ya kwana ɗakinta,inda ya yi mata 'yan wasu tambayoyi waɗanda suka shafi addininta, sai ya ji ɗif! Tamkar an ɗauke ruwan sama,ta kasa ba shi amsa sai inda-inda take. Ganin 'yan tambayoyin addini ma ta kasa amsawa,sai ya tambayeta yadda ake addu'ar saduwa da iyali da wankan janaban. Tirƙashi! Yau ake yinta wai tsohuwa ta ga ranar mutuwarta. Tamkar ruwa ya cinyeta haka ta yi shiru tare da duƙar da kanta saboda kunya. Ya kwankwanɗi madarar mamakin da bai taɓa kwankwaɗa ba, a ce 'yar gidan kawunsa ta kasa amsa tambayoyi masu sauƙi da suka shafi addininta. Ɗiyar malami mai tsanani a kan mayar da hankali wurin karatu. Ta ya hakan ta faru? Ganin babu mai ba shi amsa,sai kawai ya koya mata yadda ake wankan tsarki da sauran abubuwan da suka shafi ma'aurata.Daga bisani suka canja channel. Washegari ya samu Mairi a kan ta fara koyar da ita abubuwa mahimmai da suka jiɓanci addini kafin ya sakata islamiya,don wannan abin kunya ne mai girma gare shi,a ce matarsa ko farillan alwala bata sani ba. Bayan fitar Dauda Imamu Mairi ta tuntuɓi Sahura maganar koyarwan. Shafa ma idanunta toka ta yi tana mazurai a kan ba wani Dauda Imamu ya ce ta koya mata karatu, karya take. Abinka da mai sanyin hali fita daga har karta ta yi,sannankoda Dauda Imamu ya dawo bata sanar masa abin da ya faru ba gudun cece-kuce.
Cikin ikon Allah a cikin wata biyu da zuwan Sahura gidan ta samu juna biyu, ta yi murna sosai wanda misaltawa ɓata lokaci ne. Da yake tun da ta zo gidan bata ga baƙonta ba ga kuma ɗan massasara da ke yawan kawo mata ziyara musamman da yamma, sai Dauda Imamu ya kai ta asibiti inda a nan aka tabbatar masa da juna biyu gareta na sati uku. Ya yi murna da samuwar cikin haka Mairi lokacin da ya sanar mata. Sahura ta ci gaba da renon cikinta inda take samun kula sosai musamman wurin Mairi,duk fitar da za ta yi sai ta dawo mata da kayan maƙulashe wanda ta san masu ciki na so. Dauda Imamu ma wani lokacin yana kawo mata. A gefe guɗa ƙawancenta da 'yar ƙuda sai ƙara ƙarfi yake. Haƙiƙa Sahura ta yi nasarar saye zukatan Mairi da Dauda Imamu da kyawawan halayyarta da take nuna musu. Ga hakuri da kawaici, duk abin da za su yi idan bai shafeta ba bata saka musu baki koda kuwa a ranta tana son hakan. Duk da cikin da ke jikinta bata fasa aikin gidan ba,Mairi ta kwaɓe ta a kan ta bari amma ina neman gindin zama take da iya ƙarfinta,haka Mairi ta hakura sai dai suna komai a tare kamar yaya da ƙanwa.
Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangijin halittu, cikin Sahura ya shiga watan haihuwarsa, da yake tana zuwa asibiti awo duk da ba kowa yake zuwa a unguwar ba amma Dauda Imamu ya kafe tare da tirjewa a kan zuwanta asibitin duba tafiyarta da ɗan da ke cikin. A ɓangaren Mairi kuma ta yaye Jalil amma har yanzu babu ciki,hakan ma take so ,a cewarta gwara ta huta. A ranar wata asabar Sahura ta tashi da matsanancin ciwon baya,Allah ya ƙaddara shigowan Dauda Imamu kenan ya ga halin da take ciki, bai yi wata-wata ba ya fita da kiran mai 'yar ƙumbula, cikin ƙanƙanin suka wuce da ita asibiti, ta daɗe tana naƙuda daga bisani Allah ya sauketa lafiya,ta haifo zankaɗedan Jariri mai dogon hanci irin nata. Da yake Mairi ta taho da kayan haihuwa,ana haifar yaron wata malamar asibiti ta fito daga ɗakin ta amsa kayan. Da kusan mintuna ashirin aka fito da jaririn cikin kayan sanyi masu kyau. Mairi da ke ƙofar ɗakin ta yi saurin amsarshi cike da murna. Kallon ƙauna take yi masa murmushi kwance a fuskarta,sai ta miƙa ma Dauda Imamu inda a nan ya yi masa kuɗuba da kiran sallah. Ya tauna dabino ya ɗiba kadan ya lakata masa a baki da ruwan zam-zam. Unguzoma ta sanar musu sun yi mata allurar bacci zuwa nan da awa ɗaya zata farka. Ɗakin da aka kwantar da ita ta yi musu jagora kasancewar a ɗakin haihuwa akwai ƙofar da ake fita da masu haihuwa zuwa ɗakunan hutu. Sun sameta tana bacci. Barin Yasir Mairi ta yi hannun Dauda Imamu, sai ta goya Jalil ta bar asibitin zuwa giɗa haɗo ma Sahura abin da za ta ci,Babur ta hau ya kaita har unguwarsu cikin ƙanƙanin lokaci. Ruwan zafi ta dafa sai ta juye a flask sannan ta hado da madara da biredin da suka rage ta nufo asibtin,har ta kulle gidan za ta tari mai babur 'yar ƙuda ta fito daga gidanta,a tsaitsaya Mairi ta sanar mata da haihuwar sannan ta hau babur ya wuce da ita fatanta kar Sahura ta farka babu wani abu mai ruwa da zai warware mata 'yan hanji. 'yar ƙuda komawa gidan ta yi ta sauya shiga. Tsaftattun kaya ta saka sai ta kai yaranta biyu gidan maƙotanta sannan ta nufi asibitin. Mairi bata cika mintuna goma da zama ba Sahura ta farka,sai faman ɗaura na mujiyarta take a allon fuskokinsi. Jaririn Dauda Imamu ya mika mata
''Ya jikin naki?" Ya tambaya bayan ta amshi yaron
A hankali da furta ''Da sauƙi''
Miƙo mata kofin shayi Mairi ta yi tana mata sannu.
''Assalamu Alaikum'' 'yar ƙuda ta yi sallamar tana shigowa ciki,ta cancaɗa ado kamar mai zuwa biki. Har yaranta sun laƙanceta, bata kwalliya ko saka sutura mai kyau sai idan za ta unguwa. Kujerar da ke kusa da gadon ta zauna tana mata sannu. A hankali Sahura ta ɗaga mata kai. Yaron na tsotson nono ita kuma tana kurɓar shayin a hankali kamar an yi mata dole. Malaman asibiti biyu suka shigo suna tambayar ya jikin nata ko akwai inda yake mata ciwo. Sanar musu ta yi bata jin ciwon komai sai cikin kaɗan da ƙasanta. Jin komai lafiya lau ɗaya daga cikin malaman ta dubi Dauda Imamu tare da sanar masa za su iya komawa gida amma kafin nan ga wasu sunan magani da ta rubuta za ta din ga sha ya siya. Mikewa ya yi ya bar ɗakin zuwa kemis da ke wajen asibiti,koda ya dawo har Sahura ta kammala shan shayin sun haɗa kayansu. Sake fitawa ya yi ya nemi 'yar ƙumbula,sai suka dawo gida
'yan barka suka shiga zuwa ganin jariri da yake yanzu Sahura tana shiga gidaje. A washegari Dauda Imamu ya yi tafiya zuwa Sakkwato faɗin haihuwa. Kwanansa biyu daga bisani ya dawo tare da ƙanwarta Sahura autarsu da ƙanwar mahaifiyarta, lokacin saura kwana huɗu suna. Danƙareran rago ya siyo mata,a ranar suna jaririn ya ci sunan HAMID DAUDA ƊAHIRU IMAMU. 'yan layi sun yi kara sosai don babu masaka tsinke a gidan. Washegari aka soye rago,Inna Rahane ta kasa ragon kowa ya ɗauki nashi, ɗayan washegarin su kuma suka koma Sakkwato. Sun bar Mairi ta yi wa Sahura wankan jego tun da ta iya. Da safe bayan sun kammala karyawa ya yi gyaran murya don akwai maganar da ke guntse cikin bakinsa ta farinciki yana so ya furza musu su ma.
''Akwai magana mai muhimmanci da nake so na sanar muku. Daman wani abun alkhairi kuma cigaba ya same ni a wancan satin,ganin ana hada-hadar suna ya sa na bari sai bayan suna sai na sanar muku da abin farin ciki''
Hamdala kowannansu ya yi,sai Dauda Imamu ya ɗan numfasa sannan ya ɗora
''An aiƙo mini saƙo daga Kaduna a kan...✍️
_____________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
______________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_Narrnarhh Bukar_*
_(Lady with the Amazing pen ✍️)_
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_004_*
Da safe bayan sun kammala karyawa ya yi gyaran murya don akwai maganar da ke guntse a bakinsa ta farinciki yana so ya furza musu su ma.
''Alhamdulillah taro ya tashi lafiya. Daman akwai wani abun alkhairi da ya same ni wancan satin,ganin ana hada-hadar suna ya sa na bari sai bayan suna sai na sanar muku da abin farin cikin''
Hamdala kowannansu ya yi,sai Dauda Imamu ya ce
''An aiƙo mini saƙo daga Kaduna a kan ana roƙon na zo na koyar tare da limancin jumma'a a sabon masallacin da ke cikin barikin sojojin sama na cikin jihar Kaduna. Ba a daɗe da gama ginin islamiyyar da masallacin ba. Ta hanyar abokina wanda muka kammala sakandare tare sakon ya iso gare ni''
''Alhamdulillahi khasiran! Wannan kuwa abin farinciki ne sosai a garemu. Allah ya ci gaba da buɗa maka hanyoyin samun dubban nasarori.'' Mairi ta faɗa cike da murna. Da ''Ameen'' suka amsa.
''Na yi murna sosai da wannan abin farincikin. Hamid ya buɗe hanyar samun nasarori garemu...''
''Auzubillah! Sahura! Kin san girman saɓon da kika yi yanzu kuwa!" Dauda Imamu ya faɗa yana katse mata sauran furucin da bata ƙarasa faɗi ba. To ita me furucinta ya yi da za a haɗa shi da saɓo. Narai-narai da idanu ta yi tana duban Dauda Imamu ta ce
''Yaya Imamu me furucina ya yi? ''
''Au ba ma ki san saɓo kika yi ba yanzun ! Ta ya za ki ce sanadin Hamid hanyar nasara ta buɗe. Wa ya ce miki saboda wani ne Ubangiji ke ikonsa a kan bayi. Ana saura kwana huɗu ki haihu saƙon ya iso gare ni. Sai da na bincika sahihancin saƙon da kusan kwana uku kika haihu. Yanzu a nan ina alaƙar haihuwar Hamid da wannan saƙon? Ki dinga auna magana kafin ki furta?"
''To Yaya Imamu zan kiyaye. In shaa maka Allahu..''
''Ba in shaa maka Allahu ake cewa ba, in shaa Allah ake faɗa''
''To''. Sahura ta faɗa a sanyaye zuciyarta na ƙuna saboda tozarcin da ya yi mata gaban kishiyarta. Ya rasa inda zai jizgata sai gaban kishiyarta 'Akwai ranar ƙin dillanci. Mu je zuwa! Za ku sha mamakina ne! Da Sahurar gwaggwan bugaje kuke taɗin' ta faɗa a ranta. Zama Dauda Imamu ya gyara sai ya ci gaba da cewa
'' Gobe zan yi tafiya zuwa Sakkwato sanar da su Inna da Kawu maganar aikin, idan na dawo zan tafi Kaduna. Zan je na ga komai da idanuna, idan komai na wurin ya kwanta mini ciki har da tsarinsu,to a tafiya ta biyu zan ɗauki ɗaya daga cikinku mu je can, daga baya ta dawo sai 'yar'uwarta ita ma ta je. Sadiƙu zai riƙa aiko da kuɗin cefane. Sannan idan kuna da buƙatar wani abu ku sanar mishi. Kamar yadda kuke zamanku lafiya don Allah kar don bana nan ku sauya hali. Ban da shiga maƙwabta da zuwa suna na sake jaddadawa. Musamman ga ke Sahura da har yanzu baki gama sanin kan unguwar ba'' ya ƙarashe maganar yana dubanta. Jinjina masa kai ta yi a ranta tana faɗin 'Sai dai kar a kuma, shiga maƙwabta na nawa. Da sahurar gwaggwan bugaje kake zancen'
Fita Dauda Imamu ya yi daga gidan zuwa kantinsa da ke kasuwa. Mairi ta wuce ɗakinta ko mintuna goma bai cika ba ta fito sanye cikin hijabi mai zip a baya. Ta goya Jalil ta riƙo hannun Yasir.
"Maman Hamid zan je gaishe da 'yar'ajinmu. An kwantar da ita a asibitin Yariman Bakura. Ban samu zuwa tare da 'yan'aji ba saboda ranar sunan Hamid ne. "
"A dawo lafiya! Ki yi mata sannu da jiki" Sahura da faɗa tana ciro wa Hamid nono. "To" Mairi ta ce sannan ta nufi hanyar waje. Watar uwar harara Sahura ta bi bayanta da shi tana taɓe baki. Sai da ta tabbatar ta bar gidan sannan ta ja tsaki mai tsayi tana faɗin
"Kallonku kawai nake yi! Duk cin fuskar da kuke mini sai na yi muku wanda ya fi shi! Shiga maƙota yanzu na saka ƙafa. Haka kurum! A hanaka shiga jama'a saboda munafunci. To ba zan yarda ba!''
Mayar da nonon ta yi cikin riga sannan ta wuce ɗaki ta goya Hamid sai ta zuri mayafi ta fito tana bambami ita kaɗai. Kulle ƙofar falon ta yi sannan ta fito ta kulle ƙofar waje. Sai ta wuce gidan 'yar ƙuda. Ta tarar da gidan kaca-kaca. Kayan wanki a gefe guda wasu an tsumasu cikin ruwa,wasu kuma an matse su amma suna ajiye, ga baho cike da kayan wanke-wanke ƙuda sai cin kasuwarsu suke ciki hankali kwance. Ga sumumun warin da ke tasowa daga kwatar da ke tsakiyar gidan. Toshe hanci Sahura ta yi tana tsallake kwatan sai ta shige ɗakin 'yar ƙuda,a ranta tana mamakin ƙazantar 'yar ƙuda. Ita dai bata taso gidansu ta ga ana ƙazanta ba. Gwaggwon Bugaje mahaifiyarta ƙarshe ce a tsafta, duk sati sai ta yi kwalemar ɗakinta haka sauran matan ubanta dukkaninsu suna da tsafta daidai gwargwado. Da zancen zucinta ta shige cikin ɗakin laɓɓanta ɗauke da sallama.
''Salamu alekun''
''Wa'alaikum salam. Maman Hamid! ke da kike jego me ya fito da ke?'' 'yar ƙuda ta furta cike da mamaki tana dubanta.
Zama Sahura ta yi a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin tana sake jin ƙyanƙyamin ɗakin ba tare da ta bata amsa ba. 'yan matan Kaduna sai bidirinsu suke a saman kujerun.
''Ina na ga ta zama 'yar ƙuda! Dole na zo na tsaigunta miki da dumu-duminsa'' Sahura ta faɗa bakinta kamar gonar audiga tana ciro Hamid da ke ɗan mutsu-mutsu a baya. 'yar ƙuda da jin haka ta tashi daga saman kujerar da take ta dawo kusa da kujerarta.
''Yawwa aminiya tsaigunta mini! Ji nake kamar na antaya cikin zuciyarki na karanto da kaina! Hala a kan Maman Jalil ne?" 'yar ƙuda ta tambaya tana amsar Hamid daga hannunta. 'yar dariya Sahura ta yi bayan ta miƙa mata shi ta ce
''Ko kusa 'yar ƙuda. Baban Hamid ne ya samu aikin koyarwa a barikin sojojin sama da ke cikin jihar Kaduna''
''Da gaske Aminiya?!" 'Yar ƙuda ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi.
''Wallahi kuwa. Yau ɗin nan yake sanar mana ni da 'yar iyayi"
''Kai amma na tayaki murna. Da ke zai je hala. Garin 'yan boko kuma wayayyu ƙila ma ki koyi turanci a can''
''Ban san takamaiman da wacce zai je ba. Amma na yi imani da mai sama Mairi ba za ta taɓa taka ƙafarta zuwa Kaduna ba,in dai ina numfashi a doron duniya.'' Sahura ta faɗa cike da fariya. Dariya 'yar ƙuda ta yi tare da faɗin
''Wannan rantsuwa haka maman Hamid. Kar Imamu ya ce ta ita zai je fa"
Harara Sahura ta wurga mata tare da cije gefan leɓanta na ƙasa kaɗan. Tsabar bala'i miƙewa ta yi ta shiga jujjuya yatsanta manuniya na hagun tana faɗin
''Wallahi! Wallahi! Wallahi! Rantsuwar musulmi uku ce ko? Idan na bar Mairi ta je Kaduna tsinuwar Allah ta tabbata a kaina. Kin san Allah! Hah! Hah! Haaaa! Da alama baki gama sanin halina ba! Ba dai zan yi yawon arba'in ba. To magana ta ƙare kuma za ki ce na sanar miki''
''Sai da ke 'yar ƙunan baƙin wake. Duk da ban gama sanin halinki ba amma idanunki kaɗai sun shaida za ki iya komai a kan cikar burinki.''
Amsar Hamid Sahura ta yi sai ta koma mazauninta,a nan 'yar ƙuda take sanar mata faɗan da suka yi ita da ƙanwar kishiyarta a kan kwanan miji. Har gida 'yar ƙuda ta yi ma kishiyarta takakka ta so mata zagin soso da sabulu amma ta haɗu daa daidai da ita. Da yake lokacin ƙanwar kishiyarta na nan kuma masifaffiya ce har ma ta zarceta a faɗa. Sai ta tsoma baki tana tare ma 'yar'uwarta, nan faɗa ya kaure a tsakaninsu har maƙotan kishiyar suka zo bayar da haƙuri. Da yake mijin driban mota ne mai tafiya zuwa garuruwa. A ranar da ya dace ya kwana gidan 'yar ƙuda ya manta ya kwana gidan kishiyar,sai hakan ya ƙona mata rai duk da ya rama mata kwanan kuma ya bata haƙuri amma sai da ta yi mata takakka,sai dai ta haɗu da daidai ta ita,domin ƙanwar bata rage mata koda kuwa farcen susa ba ne. Da ƙarshe ita ya ba rashin gaskiya sai hakan ya ƙara ƙona mata zuciya. Sahura da jin wannan labari ta shiga zuga 'yar ƙuda a kan kar ta kuskura ta yarda da wannan iskanci, ba wani ya manta,da sananshi ya yi hakan saboda ya ga kishiyar ta fi ta tsafta da iya kwalliya. Cikin hikima Sahura ta yi maganar, hannunka mai sanda take mata a kan rashin tsaftarta saboda ta gyara. Kamar Sahura ta sani 'yar ƙuda ta ce mata haka ne,don ƙanwar kishiyarta sai da ta goranta mata a kan ƙazama ce wai taya miji ba zai manta ɗakinta ba. Nan Sahura ta rikiɗa zuwa mallamar tsafta tana ba wa 'yar ƙuda darussa a kan tsaftar jiki da na muhalli. Kamar da gaske haka 'yar ƙuda ta shiga jinjina kai tamkar ƙadangaruwa. Bayan sun gama tattaunawar sai Sahura ta yi azamar barin gidan kar kishiyarta ta dawo ta tarar bata nan.
Ta fito daga gidan kenan idanunta suka yi arangama da Dauda Imamu tsaye a barandar gidan ya sarƙafe hannunsa yana kallon ƙasa kamar mai nazari. Miyau mai kauri ta haɗiye muƙut! Sannan ta ci gaba da tafiya kamar wacce take tsoron ƙwai ya fashe mata a ciki. Tana isowa wurin ta yi ƙarfin halin cewa
''Sannu da zuwa yaya Imamu. Daman 'yar ƙuda ce ta ari...''
''Ban tambayeki ba! Buɗe mini ƙofa!" Ya faɗa yana katse mata hanzari a tsawace.
Mukullin tasa ta buɗe ƙofar ƙirjinta na dukan uku-uku. Bai kulata ba ya shiga ciki,jiki a sanyaye ta bi bayansa,yau dai dubunta ta cika. Ko awa ɗaya ba a yi da faɗa mata a kan shiga maƙota ba amma ta shige. Suna isa falon ya jiyo idanunsa duk sun kaɗa saboda ɓacin rai ya ce
''Wani kashedi na yi miki ɗazu?" Ya tambaya yana kallon ƙwayar idonta. Da sauri Sahura ta yi ƙasa da idanunta sabon firgici da tsoro suna sake lulluɓeta.
''Da ke nake!" Ya furta a matuƙar tsawace wanda hakan ya sabbaba mata firgici ita da Hamid da ke goye. Ta yunƙura za ta ba shi amsa Mairi ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama. Amsawa Dauda Imamu ya yi a ɗaure,Sahura kuma ta duƙar da
kanta tana jin zafi a zuciyarta. Tambaya Dauda Imamu ya sake yi mata. Cike da inda-inda Sahura ta fara magana tana jijjiga goyonta
''Daman Daman Yaya Imamu ka ce ne Mu daina shiga gidan gidan maƙota. Kuma ni wallahi tallahi na rantse maka da Allah kaya na...''
''Rufe mini baki! Ke har kin yi taurin kan da zan kafa doka ki ƙetare! Kina wankan jego amma kin iya fita gulma!Na maimata yau da safe a kan bana son kuna shiga gidan maƙota amma kika yi biris da zantukana,kika yi tafiyarki! Saboda kin raina ni! Babu abin da ke cikin ƙwaƙwalwarki sai yawon bin gidajen maƙota gulma da tsaigumi. To wannan ya zamanto na farko kuma na ƙarshe idan har kina son zama da ni a gidan nan lafiya! Kar ki kuskura ƙarfarki ta sake taka gidan wata idan ba barka ko rasuwa aka yi ba! Idan kuma kin ce ba haka ba, to zan fito miki da aihinin launina. Haka kika ga Mairi tana yi ne. Na ga alamar zaman gidan ne kika gaji da shi,da zarar na dawo daga Kaduna zan saka ki islamiya.'' Daga haka ya wuce ɗakin Mairi ya bar Sahura tsaye ƙiƙan tana zubar hawaye. Mairi tun da ta yi sallamar ta ga yanayin yadda ya amsa mata bata sake cewa komai ba ta ja hannun Yasir suka shiga ciki ta shimfiɗar da Jalil da ke bacci. Koda Dauda Imamu ya shigo ciki wani littafi ya ɗauka ya bar gidan ba tare da ya dubi Sahura da ke tsaye wuri guda ba. Takaicin duniya ya gama lulluɓeta, a kan abin da bai taka kara ya karya ba yake mata sababi a kunnuwan kishiyarta. Tun da ta zo gidan bata taɓa jin ya yi mummunar furuci ga Mairi ba sai ita,duk wani kashi idan ya tashi ita yake yaɓama wa. Matar so bata laifi sai ita. A gaskiya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 33