Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ranar Sahura ta ajiye makaman yaƙinta a gefe,ko ɗaure fuskar da take musu ta daina,don ta ga alama za ta kwashi daɗi ita da yaranta ta hanyarsu,sannan hakan ba zai tabbatu ba sai idan ta ja su a jiki. lokaci bayan lokaci Jalil da Muhsin suna kawo ma su Yasir ice cream ko nama idan sun fita outing. Daidai gwargwado mahaifin Muhsin na ƙokari a kansu Yasir haka ma maman Jawaheer da mijinta. Da safe idan su Yasir suka ta fi boko ba su suke dawowa gidan sai yamma,a gidan maman Jawaheer suke cin abinci rana,kayan islamiyyarsu ma yana wurinta. Da yake yanzu ta ajiye aikin da take a wajen barikin sai ta nemi koyarwa da certificate ɗinta na diploma a primary school ɗin barikin. Cikin ikon Allah ta samu koyarwa a primary 4. Dauda Imamu kullum cikin yi musu godiya yake idan sun haɗu. Kwanci tashi babu wuya wurin Ubangiji lokacin kara ma su Officer Kabir matsayi ya yi. Officer Kabir aka ƙara masa matsayi zuwa Flying Lieutenant. A gefe guda mijin maman Jawaheer shi ma an ƙara masa matsayi zuwa Warrant officer da taimakon Madam Ngozi. Bayan ƙarin matsayin wanda lokacin azumi bai fi kwana goma ba Mahaifin Muhsin ya shirya musu tafiya zuwa Zamfara wurin Mairi kasancewar su Yasir sun samu hutun boko,yana so su yi hutunsu a can zuwa bayan sallah su dawo. A ɓangaren Sahura a ranar wata Laraba babu zato babu tsammani Madam Ngozi ta yi mata zuwan bazata,ta yi matuƙar tozara da ita,'yan wasu tambayoyi ta yi mata da kuma sake jaddada mata sharuɗɗan sannan ta bar gidan...✍️ ^^^^^^^^^^^^^ Mairi tun tana ƙirga kwanaki har ta koma ƙirga satitta zuwa watanni amma shiru bata ga keyar su Yasir da sojan ba. Hankalinta ya ƙara tashi,sau biyu tana zuwa Mada wurin Kawu a kan maganar,da yake bayan dawowar Kawu Rabi'u Mamman ya sanar masa komai sai ya ta fi a kan a gwara su gwadasu su gani. Gwiwa a saɓule take dawowa Gusau a duk zuwanta,bata san me ya sa sun kasa fahimtarta,sun kasa gane halin da take ciki,kullum cikin damuwa take duk da ta ɗan rage ba kamar da ba. Jamila ma tana goyan bayan 'yar'uwarta. Mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo,ita take jin zafin rashinsu a kusa da ita. Takanas ta kano ta je Mada ta nemi izini wurin mijin Jamila a kan za su Kaduna ɗauko yaranta kuma kwana daya ne rak za su yi. Fatan Allah ya tsare hanya ya yi musu,ya kuma kara musu kuɗin mota. Da rana suka dawo Gusau, duk abin da suke buƙata sun saka shi cikin jaka. Sun zauna suna hutawa HAFIZA na gefe tana zane suka tsinkayi muryar su Jalil kamar a mafarki,babu shiri HAFIZA ta saki pencil ɗin ta ruga da guda waje tana kiransu. A sukwane su Mairi suka fito wajen,mamaki kwance a fuskarsu,tsakar gidansu ta cika da baƙi har da waɗanda ba su san fuskokinsu ba. Momy ta yaranta,haka ma maman Jawaheer ta zo da yaranta. Da gudu su Jalil suka rungume Mairi,take ta rushe da kukan farinciki, sai ɗago su take tana sake duban su don tabbatar da ba mafarki take yi ba. Sake rungumesu ta yi tsam a jikinta kamar tana tsoron wani zai sacesu. Jamila ta yi musu iso zuwa falon. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa sannan suka shiga gaisawa. Momy ta dubi Mairi ta ce ''Ko ba a sanar mini ba wannan ita ce mahaifiyar hamma Jalil,wannan kuma ƙanwarta'' Murmushi Mairi da Jamila suka yi suna jinjina mata kai. Maman Jawaheer ce ta ce ''Maman Raihan kin samu wuri kin manta ta Dadyn Muhsin'' Waro ido momy ta yi tana faɗin ''Innalillahi! Wallahi shaf na manta. Daman tare da mijina muka zo'' ''Allah sarki! Jalil ku je ku shigo da shi'' cewar Mairi tana mikewa ta je ta saka hijabi haka ma Jamila. A Tare suka shigo bakinsa ɗauke da sallama. A one sitter ya zauna Jamila ta kawo mishi ruwa. Bayan sun gaisa sai shiru ya ratsa ɗakin. Can officer Kabir ya yi gyaran muryar,cike da natsuwa ya fara magana. ''To Alhamdulillah dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya ba mu ikon zuwa cikin ƙoshin lafiya. Sunana Kabir wannan ita ce mata Karima sai Maryam wadda mijin ya zama aminina sanadin yaraku. Kwanakin baya ɗan uwanku ya zo bariki ɗaukar su Hamida, lokacin ina tare da Imam. To dama Jalil ya dawo hannuna tun lokacin da na fahimci matar Imam tana muzguna masa,da yake ɗana Muhsin abokinsa ne kuma ajinsu ɗaya a boko da islamiyya. Tun kafin na san Jalil Muhsin yake faɗa mini wahalar da yake sha shi da 'yan'uwansa a hannun matar Imam. Ganin haka ya sa na roƙi Imam ya bar mini Jalil hannuna tun da yarona abokinsa ne,ni kuma zan kula da shi kamar ɗan cikina kuma Alhamdulillah ya danƙa mini amanarsa. Ina tunanin yadda zan kawo ma su Yasir ɗauki a kan izayar da take musu sai Ubangiji ya yi ikonshi a kanta,domin Ogata ta wurin aiki Madam Ngozi ta yi maganinta,wanda yanzu na san ta shiga taitayinta sannan ta bayar da gudummawa mai tsoka a lokacin da Hamida take gadon asibiti. Maryam ma ta yi matuƙar ƙoƙari a kansu wanda yanzu haka cikin ƙoƙarin take. Na so zuwa kwanakin baya kamar yadda na sanar ma ɗan uwanku amma sai na canja shawara a kan idan an ba su hutun boko sai su zo su yi hutunsu wurin mahaifiyarsu m,zuwa bayan sallah sai su koma. Ban san ra'ayinki a kan yaranki ba amma muna nemanmn wannan alfarmar,za mu yi iya ƙoƙarinmu a kansu sannan duk lokacin da suka samu hutu za su dinga zuwa har da yarana in shaa Allah. Amma ba za mu taruka miki ba, duk abin da kika ce ba za mu yi jayayya a kai ba'' Hawaye masu ɗumi Mairi ta share tana zuƙar majina,bata taɓa tunanin akwai irin waɗannan mutanen masu farar zuciya a doron duniya. A da ta fi son su dawo hannunta,amma kuma mutanen nan sun karyar mata da zuciya,sun taimaki yaranta a lokacin da suke tsananin neman taimako,ita kuwa wa ce ita ta watsa musu ƙasa a ido,tun daga Kaduna suka yi tattaki ƙwansu da kwarkwata zuwa wurinta. Bata taɓa riskar kanta a cikin farinciki kamar na yau ba,tabbas Ubangiji ya amsa addu'arta ta inda bata yi tsammani,ya kuma shigo da waɗannan mutanen don su taimaka mata. Sake goge hawayen ta yi cikin muryar kuka ta fara magana ''Ban san da me zan saka muku da irin wannan taimakon da kuka ma yarana ba. Kun yi mini karamci,kun kawo ma yarana ɗauki a lokacin da suke tsananin buƙatar hakan,ta ya ni Maryam zan butulce muku. Tabbas Allah ne ya turoku cikin rayuwata! Na gode! Na gode! Allah ya saka muku da alkhairi ya albarkaci zuri'arku. Na aminta da zamansu Jalil a wurinku,tun sa ga HAFIZA wurina. Allah ya tayaku riƙo. Ina kara godiya!" ''Mun gode sosai da taimakon da kuka yi ma yaranmu. Wallahi yanzu muka gama shiri zuwa gobe mu je Kaduna ɗauko su. Zuwanku ya sacar mana da gwiwa. Tun da duk hutu za su dinga zuwa hakan ma ya yi. Daga kallon jikinsu zuwa tufafinsu na tabbatar da suna samun kyakkyawar kulawa. Muna kara godiya'' cewar Jamila. Wani irin sanyi Officer Kabir ya ji a ransa,tun a hanya yake tunanin ko mahafiyar Jalil za ta aminta ko A'a,sun yi mugun sabo da shi musamman Raihan. Idan taƙi aminta tabbas ya san Raihan za ta shiga cikin wani hali. Cike da jin daɗi officer Kabir ya ce ''Mu ke da godiya. In shaa Allah za mu riƙe amanar da hannu bibbiyu.'' ''Muna godiya sosai takwarata'' cewar maman Jawaheer. ''Idan kika ce ba za ki bar mana Jalil ba ai sai mu haɗo da Raihan ki haɗasu ki riƙe. Don bata da yaya sai Hamma Jalil'' cewar momy tana dariya. Dariyar su ma suka yi. Mairi kuma da ɗan murmusa. Sallama officer Kabir ya yi musu sai momy ta bi bayan shi. Jamila ta fita ɗaura girki. Mairi da maman Jawaheer suka fara hirar yaushe gamo,momy ta dawo suka ci gaba da hirar,tsarabar da suka zo da ita ta miƙa mata. Sai bata labarin iskancin da Sahura take,da kuma wahalar da sha hannun Madam Ngozi. Babu abin da Mairi take sai murmushi zuciyarta fes,yanzu bata da wata damuwa sai ta Dauda Imamu. Shi ma tana rokon Allah ya dawo mata da shi cikin hayyacinsa. Bayan da ɗora girkin ta dawo falon aka ci gaba da hirar tare da ita. A ɓangare guda yaran sun haɗe suna surutu,manyan suna gefe yayin da ƙananun suke wuri ɗaya. Hamida da Jawaheer suna hirar boko. Raihan da take sa'ar HAFIZA ta zauna kusa da iya,sai dai kwata-kwata bata samu fuskar yi mata magana ba,don HAFIZA akwai tsare gida idan bata so magana ba,sai da Jalil ya yi mata magana sannan ta ɗan sake jiki da ita har suka fara hirar karatu,labari da ya yi daɗi zai HAFIZA ta fi Raihan zaƙewa,har da shiga uwarɗaka tana ɗauko mata result ɗinta na wannan karon tare da drawing books ɗinta. Mahaifin Muhsin ya nemi wani hotel ya kama ɗaki na kwana ɗaya tun da gobe za su koma,daga hotel ɗin ya shiga zaga garin.Cikin ƙanƙanin lokaci Mairi ta yi sabo da su momy,haka ma Jamila,sallah ce take tashin haka yaran. Bayan sallar Isha'i officer Kabir ya dawo gidan,a tsakar gida aka shimfiɗa masa tabarma momy ta fito masa da abinci,ƙatuwar leda ya miƙa mata ta shiga da shi ciki ta mika ma Mairi sannan ta dawo wajen. Tana tayashi hira har ya kammala cin abinci suka ɗan taɓa hirar sannan ya yi sallama da su,Mairi ta yi mishi godiya da abin arziƙi momy ta rakashi ya wuce hotel. Bayan ta dawo falon Jamila ta kakkasa tsiren da officer Kabir ya kawo a 'yan kwanuka ta miƙama kowa,suna ci suna hira. Sai wurin goma na dare suka kwanta. Washegari da safe bayan sun karya officer Kabir ya zo suka tafi inda aka bar Yasir,Jalil,Hamida,Raihan da Muhsin. Yaran maman Jawaheer gobe za su Kano hutu shi ya sa ba za su tsaya hutu nan ba. Cikin daɗin rai suka yi sallama tare da addu'ar Allah ya tsare hanya. Washegari Jamila ta koma gida. Walwalar HAFIZA ta dawo sakamakon zuwansu Jalil,sun yi azumi cikin farinciki da annashuwa tare da shagulgulan sallah da ziyarar 'yan'uwa a Mada. A ɓangaren Sahura bata san da tafiyansu Yasir ba,ko da ta gano sun je hutu Zamafara bata damu,ita dai fata take karsu daɗe saboda kayan daɗin da take ci ita da yaran ta dalilinsu. Bayan an dawo hutu abokin officer Kabir ya je Gusau ya ɗaukosu Yasir ta haɗa su da tsaraba. Rayuwa ta ci gaba da tafiya inda duk hutu Yaran suke zuwa Gusau tare da tsaraba niƙi-niƙi ciki har da tufafi, zuwa yanzu hankalin Mairi a kwance yake,bata da damuwar komai sai na rashin tozali da madubin rayuwarta, shi ma tana fatan zai dawo gareta ko ba daɗe ko ba jima. Har Kaduna Sadiƙu ya zo wurin Dauda Imamu,ya sanar masa da ci gaban da kullum suke samu a shagon,Dauda Imamu ya yi farinciki sosai da yadda ya riƙe amanar shagon da iyalansa,bayan sun ɗan zanta daga bisani ya dawo Gusau a ranar.A ɓangaren Sahura ta mayar da hankali wurin tsuma 'yan matan,bata damu da karatunsu ba musamman islamiyya, ta dora burin duniya a kan su idan sun girma. Tun ana ƙirga watanni suka rikiɗa zuwa shekara,daga shekara ɗaya ya linku zuwa shekaru masu ɗumbin yawa. Zuwa yanzu HAFIZA na da shekara sha uku a duniya,kuma ta haddace Alqur'ani tana maimaici a karo na uku,a boko tana Jss2. Ta taso cikin kyakkyawar kulawa,ga ta natsuwa da rashin son magana amma kuma bata ɗaukar raina,sam bata shiga sabgar kowa haka bata son a shiga sabgar. Tafi son ta yi rayuwarta ita kaɗai,a ɓangaren zanenta kullum gaba-gaba yake,ta ƙara ƙwarewa ba kamar lokacin da take yarinya ba. A waɗannan shekarun masu tarin yawa sau biyar Dauda Imamu ya yi kundumbalar zuwa Gusau,ko kwana bai yi yake dawowa saboda kamar ana ƙara masa tsanar Mairin,idan ya je HAFIZA yake ja a jiki su yi hira sannan ya bata kuɗi ya dawo Kaduna,magana bata taɓa haɗa su a waɗannan zuwan ba balle kuma kwanciyar aure. Idan ya koma Mairi ta shige uwar ɗaki ta ci kukanta ta more. Da Sahura ta gane yana zuwa Zamfara sai ta masa mummunan kashedi,tun daga lokacin bai ƙara zuwa ba wanda kusan shekara huɗu kenan da faruwar hakan. A ɓangaren Jamila har yanzu Allah bai bata haihuwa ba,abin mamakin duk asibitin da suka je magana ɗaya ce lafiyarta ƙalau sannan ƙwayoyin haihuwarta suna nan lafiyaba,lokaci ne dai Allah bai kawo ba,tun tana damuwar har ta fawwala ma Allah komai. A ɓangaren su Yasir sun girma sosai,don Yasir da Jalil sun fara gemu,Hamida kuma maƙerin budurci ya fara ƙerata. Yasir yana a Kaduna state University level 4 yana karantar Civil Engineering shekararsa 23, Jalil yana da shekara 21 yanzu,yana son applying NDA shi da Muhsin next year,suna zuwa computer training a wajen barikin shi da Muhsin. Hamida kuma tana cikin shekara ta 17 tana SS3 ita da Amina. A waɗannan shekarun Officer Kabir ya samu ƙarin matsayi zuwa Wing commander,haka ma mijin maman Jawaheer ya samu ƙarin matsayi zuwa Air Warrant officer. Madam Ngozi yanzu tana matsayi mai girma wato Air Commodore,amma saura shekara biyar ta yi retire,duk da bata cika zuwa barikin Kaduna ba,ta wakilta wani daga cikin sojoji suna ziyartar Sahura lokacin zuwa lokaci. A ɓangaren Sahura kuwa ta ƙara zama cikakkiyar uwa,inda yanzu Hamid dinta yake cikin shekara da 19 ya kammala secondary amma yaƙi shiga babbar makaranta,bai da aiki sai biyema yaran yare marasa jin magana,Dauda Imamu yana jin zafin hakan a ransa amma babu yadda ya iya, furfura ta fara ƙawata gashinsa sakamakon ɗawainiyar iyali. Aunty Saudah na cikin shekara ta 18 ita ma ta kammala secondary,ta zama budurwa son kowa ƙin wanda ya rasa,domin Sahura bata wasa da gyaran ciki da wajensu. Amina na cikin shekara ta 17 ajinsu ɗaya da Hamida,Halima kuma tana cikin shekara ta 15 tana SS 1, Nu'aymah kuma tana a shekara ta 13 ,JS 2 take. Autarsu Maryam mai shekara ta goma tana a primary 4. A cikin yaran Sahura Nu'aymah ce uwar rashin jinsu,ga shi Allah ya ɗarsa ma Sahura ƙaunarta fiye da sauran yaran, tana da mugum kwaɗayi da ɗanbanzan roƙo. Mazan ajinsu har sun santa a kan roƙo. Ta fi duka yaran ɗakin kyau shi ya sa Sahura take alfahari da ita. Ƙawancen Sahura da maman 'yar gayu yana nan daram hasalima ƙara aminta da juna suka yi,'ya'yan maman 'yar gayu biyu suna Adamawa wurin iyayenta,ƙaramar ce take hannunta wacce take sa'ar Nu'aymah. Yanzu da su Yasir suka girma Sahura ta ƙara jansu a jiki,kayan Hamida tare da su Amina ake kashesu,haka idan Jalil ya kawo musu kayan ƙwalam tare suke cinyewa,wani lokacin idan Sahura na jin mugunta sai ta ɗan sammata kaɗan ta cinye sauran,da yake Yasir bai cika zama ba sai dai idan bai da lectures. Da Jalil ya gano abin da suke,rana ɗaya ya goge mata hadda don bai raga mata ko da farcen susa ne,Hamid ya ta so zai buge shi Jalil ya mishi dukan tsiya,Jalil ƙarƙƙarfa ne sosai ga tsawo sannan da 'yar ƙiba. Tun daga ranar Sahura ta ƙara tsanar Jalil wanda basa ga maciji,shi kuma tuno da irin azabar da suka sha hannunta wani lokacin yake ƙin rage mata. ^^^^^^^^^^^^ *BAYAN SHEKARU MASU TARIN YAWA* Aunty Saudah ta samu wani Alhaji mai kuɗi sosai a wajen barikin ana kiransa da Alhaji Shu'aibu Shanawa,yana da gidaje da kantuna. Sosai yake kashe ma Aunty Saudah kuɗi kamar ɓarnar iska. Har babbar waya srceen touch ya siyan mata. Shekararsu biyu kenan da haɗuwa. Jiya da ya jo yake sanar mata yana son ya turo iyayensa a yi maganar aure. Bayan ya tafi Aunty Saudah ta sanar ma mamanta. Washegari Dauda Imamu na zaune,Jalil na gefe da wayarsa yana chatting Sahura ta dubi Dauda Imamu ta ce ''Ni ba na manta ba. Aunty Saudah jiya take sanar mini Alhaji Shu'aibu shanawa yana son ya turo iyayensa a yi maganar aure'' Shiru Dauda Imamu ya yi yana nazari,ya fi son ya fara bincike a kansa kafin ya ba shi damar turo iyayensa. ''Me zai hana a fara bincikar halinsa tukunna,idan mun ga yana da halin ƙwarai sai ya turo'' ya faɗa yana ɗan dubanta. Wani irin mugun kallo ta wurga ma Dauda Imamu, kafin ta ce wani abu Jalil da ke gefe ya rigata cewar ''Ai Abba kar ka yi wahalar binciken Alhaji Shu'aibu shanawa,domin ba mutumin kirki ba ne,sana'ar....'' *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_032_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ Wani irin mugun kallo ta wurga ma Dauda Imamu, kafin ta ce wani abu Jalil da ke gefe ya rigata faɗin ''Ai Abba Alhaji Shu'aibu shanawa ba mutumin kirki ba ne,sana'ar caca yake wallahi, abokina Tahir ɗan uwansa ne,ko motar da yake hawa yanzu a caca ya..." ''Rufe mini baki! Na tsomo bakinka ne! Idan abin da ya fi uban caca yake bai dameni ba balle ma ƙarya kake saboda ka ga 'yata za ta samu gidan hutu kake mata hassada da baƙinciki'' ''Allah ya tsareni da cutar hassada. Well tun da kina kare saurayin ɗiyarki saboda ya buɗe bakin aljihunshi yana muku aman kuɗi ni babu ruwana. Garin son kuɗinki za...'' ''Jalil!" Dauda Imamu ya kira sunansa cike da tsawa. ''Na'am Abba'' ya amsa a sanyaye. ''Yanzu a gabana kake faɗa mata irin waɗannan maganganun? Idan Mairi ce haka za ka faɗa mata'' Miƙewa ya yi irin ko a jikinsa ɗin nan yana ma Sahura kallon tsana a ransa ya furta 'Allah ya kiyaye wannan muguwar matar ta zama uwata' duban Dauda Imamu ya yi sannan ya ce ''Abba gaskiya na faɗa,ka bincika da kanta za ka sha mamakin mutumin, a fuska kamar na Allah. '' Galala Dauda Imamu ya yi yana kallon Jalil,yaushe ya yi baki har haka. ''Ka riƙe gaskiyarka munafikin banza munafikin yofi!'' ''Oho dai! Ko me za ki faɗa na jima da saninsa. A rubuce yake a cikin ƙwaƙwalwata. Kwaɗayi mubuɗin wahala ne! Na faɗa na ƙara faɗa ehehhh!'' yana kai ƙarshen maganar ya yi hanyar waje. Duk kiran da Dauda Imamu yake masa bai amsa ba har ta fita ya hau mashin ɗinsa ya ƙara gaba. Da ƙarfi Sahura ta cije laɓɓanta na ƙasa tana bin hanyar da Jalil ya bi da kallo,ta rasa me ya sa yaran nan yake da tsaurin ido,shi ko shakkar gasa mata magana ba ya yi,duk maganar da ta fito daga bakinsa ko mummuna ce hankalinsa kwance ya furta mata kamar sa'arsa. ''Don girman Allah ki yi haƙuri Ranki shi daɗe. Zan hukuntasa,in shaa Allah ba zai sake gigin faɗa miki baƙar magana ba'' Yatsine fuska Sahura ta yi tana taɓe baki ta ce ''Da ya fi maka,don da kai da shi zan haɗa na ɓata muku rai'' ''In shaa Allah ba za a kai ga haka ba. Zan bincika da kaina don neman aure yana buƙatar bincike kar mu kai 'yarmu inda za ta sha wahala'' ''Na san Jalil ƙarya yake amma ka bincika,ko caca yake ba dumuwata ba ce tun da babbar sana'a ce,kuma babu laifi ana samun matsabbai a cikinta. Idan ya tabbata cacar ma yake sai na haɗa shi da Hamid ya ɗora shi a kan hanya mu ma mu dangwali arziƙi'' ''Ranki shi daɗe caca haramun ne fa! Laifi ne mai girman gaske'' Hararsa ta yi sannan ta ce ''A zamanin annabawa ba,amma ban da yanzu, ko kwanakin baya na ji wani mashahuran babban malamin Musulunci na ƙasa da ƙasa ya halarta caca,har ma yake bayar da shawarar ya kamata kowa ya tsunduma sana'ar caca saboda alkhairi ce babba a musulunci'' Shiru Dauda Imamu ya yi yana jinta,tsoro yake ya ƙaryatata ta haushi da masifa,don wannan maganarta ta bata da maraba da ƙanzon kurege. ''Wannan haka yake. Bari na je masallaci muna da meeting da sojoji'' ''Toh'' ta faɗa tana ɗaukar 'yar ƙaramar wayarta Itel ta faralatsawa. Ɗaukar hularsa ya yi ya bar flat ɗin. Bayan fitarsa babu jimawa Aunty Saudah ta shigo falon hannunta ɗauke da babbar leda alamar daga unguwa take,sun dawo daga shopping tare da saurayinta Alhaji Shu'aibu shanawa. Fara ce sosai ga dogon hanci,tana da tsayi don ta ɗan fi Sahura, dirarriyar mace ce mai tashen balaga,sanye take cikin Egyptian abaya ruwan ƙwai,ta ɗan yafa gyalen abayar har ana ganin gashin kanta wanda ya sha gyara. Tana zuwa ta zube a saman kujerar tana faɗin. ''Washhh Allahna! Mama na gaji wallahi'' Ɗan murmushi Sahura ta yi tana bin ledar da kallo,sai ta ɗago ta ce ''Wace gajiya Aunty Saudah. Keda kike cikin luntsattsiyar mota mai A.C a ciki'' ''Mama kenan, ina nufin yawon da muka sha cikin shoprite ɗin nake nufi, da na gaji na ce mu bar kayan sai next time '' 'yar harar wasa Sahura ta yi mata ''Kai amma kin kwafsa! Wa ya ce miki ana nuna gajiya a irin wannan harkar arziƙin,ai idan ni ce ke jidar kaya zan yi babu ƙaƙƙautawa,haka kurum na samu tsuntsu daga sama gasasshe zan yi wasa da cinsa. Yanzu dai me kika siyo mana don miyauna har ya fara tsinkewa. Allah ya sa kin haɗo da wannan gasasshiyar kazar mai ɗawafi da dankalin masu jajayen kunne!" 'yar dariya Aunty Saudah ta yi sannan ta ce ''Ai mama har da ice cream na haɗo mana,abayas kuda biyar ne 'yan dubai sai takalma uku da gyale biyu muka siya,ina da kayan make up shi ya sa ban haɗo da su ba. Mama ko yau da zan sauka ya sake faɗa mini shi yana son ya turo iyayensa.'' ''Ki ce masa ya turo babu matsala'' ''Ok Mommata'' Jawo ledar Sahura ta yi zuwa gabanta,ta saka hannu ta ciro wata farar leda babba, lokaci guda wani daddaɗan ƙamshi ya ziyarci ƙofofin hancinta,take ta lumshe manyan idanunta miyonta na ƙara tsinkewa. Buɗe ledar ta yi ta yagi damɓasheshiyar cinyar kaza ta kai bakinta. Haɗaɗɗiyar wayarta Aunty Saudah ta ɗauka ta fara chatting da ƙawayen da suka kammala secondary school a group. Cike da annashuwa take latsa wayar,gefe guda Sahura na ma kaza karan tsaye tamkar mayunwaciyar zakayya. Tana tsaka da ci wayarta ta fara ringing,cikin sauri ta ɗauka ganin sunan GWAGGOTA ɓaro-ɓaro a screen ɗin wayar. Cike da hanzari ta ɗaga ''Gwaggota har kin iso?" A can Gwaggwon Bugaje ta ce ''E, ni da Auta '' ''To bari Aunty Saudah ta zo ta ɗaukoku'' sai ta katse kiran,kallon Aunty Saudah ta yi ta ce ''Don Allah ki je ki ɗauko su a gate'' ''Ummmmm! Mama! Yanzu fa na dawo daga shoprite! fisabilillah sai kuma na ƙara fita! Ni wallahi i'm tired and exhausted!'' ta faɗa a shagwaɓe kamar karamar yarinya. ''Yi haƙuri,su Amina na makaranta balle su je ɗauko su. Ke kaɗai ce a gidan,ki taimaka Don Allah

Chapter 23 of 33