Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
share mata hawaye, burikan da suke kwance cikin zuciyarta da burtsosu. A ɓangaren Mairi daga ɗakin Sahura ta wuce ɗakinta,da kuka ta ƙarasa saman gadon. Wannan wace kalar musiba ce haka, a ce farad ɗaya zuciyarta ta kamu da tsoron kishiyarta,me ke shirin faruwa da ita ne. Me ya sa bakinta yake mata nauye idan za ta bujire ma Sahura ko ta faɗin akasin abin da take muradi. Me ya sa masarautar zuciyarta take gayyato tsoron Sahura cikin fadarta. Me hakan yake nufi! Hawaye masu ɗumin suka gangaro saman kuncinta. ''Ammu tuta kike?" Yasir ya faɗa da tsamin bakinsa. Jalil kuma gwaranci yake maata wanda ta kasa gane inda maganarsa ta dosa. Murmushi Mairi ta saki lokaci guda tana ɓoye damuwarta. Hannu Yasir ya sa ya goge hawayen fuskarta yana faɗin ''Ti daina tuta Ammu'' Rungumesu tsam ta yi a jikinta wasu sabbin hawayen na sake gangaro mata,har yanzu bata karaya ba,kokawa tare da zuciyarta a kan tsoron Sahura da ke son shigowa cikin duniyarta amma kamar tana ƙara rura wutar tsoranta ne a ciki. Suna a haka Sahura bankaɗe labulen ɗakin,ba tare da ta shigo ba ta ce ''Ki je ki kira mini 'yar ƙuda ya yanzu'' tana gama fadin haka ta sauke labulen Kafin Sahura ta sauke numfashi har Mairi ta sauke su Yasir daga jikinta ta miƙe, mayafinta ta lulluɓa sannan ta riko hannayen su Yasir ta fito,kai tsaye ta wuce gidan 'yar ƙuda. A ƙofar gida ta sameta ba tare da sun gaisa ba ta sanar mata saƙon Sahura ta juyo zuwa gidan. Cike da tsantsar mamaki 'yar ƙuda ta biyo bayanta ba tare da ta kulle gidan ba, kasancewar yaranta na gidan maƙota wasa. A kusan tare suka isa gidan. Dakatar da Mairi Sahura ta yi da tsawa. Da sauri 'yar ƙuda ta dafa ƙirjinta da matuƙar ƙarfi tana ware 'yan mitsi-mitsin idanunta waje tsabar mamaki. Wani irin girma kan Sahura yake. Cike da gadara Sahura ta ce ''yar ƙuda kin yi gyaran gidanki yau?'' Da sauri 'yar ƙuda ta ce ''A'a. Sai zuwa an jima da yamma'' Taɓe baki Sahura ta yi tana duban Mairi ''Mairi jeki gyata mata gidan. Duk abin da kika san ya dace ki yi,ki tabbatar da kin yi. Sannan kar ki daɗe'' ''Sahuraaaaaa!" 'yar ƙuda ta faɗa tana karkata kanta. Yau ta haɗu da wacce ta goge mata hadda,lallai ko a gidan giya akwai oga. Cike da gatsali Sahura ta ce '''Na'ammmm! Ko baki son gyaran ne na ce ta bari!" ''Wace ni 'yar ƙuda. Allah ya ba ni tsuntsu gasasshe daga sama taya zan ƙi ɗauka. Yau dai na tsinta dami na a kala'' Matsowa kusa da Sahura 'yar ƙuda ta yi,sai da ta tabbatar Mairi ta bar gidan da yaran sannan ta rage murya ''Maman Hamid! Na ɓace a kan hanya. Don Allah taimaka ki dawo da ni. Kaina ya yi gingirin ya huhin goro'' 'yar dariya Sahura ta yi tana zama saman kujerar tsakar gidan Hamid na hannunta ''Ya kika ga salo! Ba na sanar miki idan na je Sakkwato za ki ga canji ba. Sahura ce fa! Ɗiyar Gwaggwon Bugaje mai babban ɗaki'' Zama 'yar ƙuda ta yi a ƙasa kusa da Sahura kamar baiwa da uwar ɗakinta ta ce ''Sahura ki duba girman Allah ki ɗora ni a wannan lafiyyar hanyar'' Murmushi Sahura ta yi har fararen haƙoranta na bayyana. Ta yunƙura za ta bata amsa suka ji sallama,da sauri suka waiga hanyar ƙofar gidan. Lokaci guda zuciyar 'yar ƙuda ta tsinke, babu shiri bakinta ya furta...✍️ _jama'a ba mu fara komai ba a wannan zazzafan wasan,ban tunanin ko sharan fage mun yi🥰. Ku gyara zama don ganin yadda wasan zai kaya,domin baku da tsoro balle fargaba tun da kuna da gangariyar mai ɗauko muku rahoto. Ni ce dai NARRNARHH BUKAR, lady with the Amazing pen✍️. Ku biyo ni don samun damar kwankwaɗar madarar karatu mara garwaye. Let's goooooo!_ ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_Narrnarhh Bukar_* _(Lady with the Amazing pen ✍️)_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_009_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ ........Murmushi Sahura ta yi har fararen haƙoranta na bayyana. Ta yunƙura za ta bata amsa suka ji sallama, kowannansu ya waiga hanyar ƙofar gidan. Lokaci guda zuciyar 'yar ƙuda ta tsinke, babu shiri bakinta ya furta ''Jamilaaa! Ke ce da rana tsaka'' Wacce aka kira da Jamila na yi mata kallon tsaf, fara ce sosai kamar ka tsaga fatarta jini ya fito, sannan suna matuƙar kama da Mairi kwabo da kwabo,bambanci kawai launin fata ne. Jamila ƙanwa ce ga Mairi,shekararta ɗaya kenan da aure,a wurin yayan mahaifiyarsu suka taso kasancewar tun suna yara iyayensu suka rasu sannan su kadai suka haifa, Mairi ce babba sai Jamila daga su iyayensu ba su sake haihuwa ba har lokacin da ƙasa ta rufe idanuwansu. Halin Jamila ya sha bambam da na Mairi,domin ita Mairi tana da sanyin hali,hakuri da kawaici ga uwa-uba zurfin ciki. Jamila sha yanzu magani yanzu ce, matsifaffiya ce ta bugawa a jarida,ga baki ga ƙarfi,kuna fara cacan baki za ta kai naushi. Sanin halin yayarta ya sa take shige mata faɗa, duk girman mutum za ta tsaya tsaf ta zage shi kamar zogale,shi ya sa ake shakkarta duk da bata shiga sabgar kowa,amma idan ka shiga nata ba za ku wanyewa lafiya ba. 'yar ƙuda ta san wace ce Jamila, don bazata manta ranar da ta nakaɗa mata na jaki lokacin Mairi na amarya, ita kuma 'yar kuda na ji da tashen iskanci,ganin Mairi bata kulata sai liyafa ta ci gaba har gida take zuwa sakar mata maganganu. Rana ɗaya da ta zo yada maganar da ta saba sai ta haɗu da Jamila kafin ta yi aure,ashe ita a baki ne kawai,domin Jamila ta dameta ta shanye a masifa da ruwan bala'i. Gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta,ta daku ta kuma kirɓu hannun Jamila tamkar dakan sakwaran gardawa. Tun daga ranar take tsoron Jamila. Wata uwar harar Jamila ta watsa musu tana ƙarasowa cikin gidan. ''Ya dai! Na ga kun zo gidan yayata lafiya!" Tun da idanuwan Sahura suka yi arangama da Jamila zuciyarta ta yi matukar bugawa. Take wata guguwar tsanarta ta yi naso a cikin zuciyarta ba tare da ta san dalili ba,tsanar da take mata ya linka wanda take wa Mairi. Lokaci guda malolon baƙin ciki ya yi mata karan tsaya a daidai tantani-maƙwallatonta, ya ƙi shiga ya ƙi fita. Kafin 'yar ƙuda ta bata amsa Sahura ta yi wuff ta caɓe da cewa ''Ke zan cewa lafiya malama,kin wani shigo gidan mijina kina nuna isa'' Mamaki sosai ya lulluɓe Jamila sai dai bata nuna a fuska ba,a ranta tana faɗin 'Dauda Imamu ya ƙara aure? Kishiya ya ƙaro ma yayata ikon Allah?' a zahiri kuma ta saki ƙasaitaccen murmushi,a hankali ta ƙaraso har inda Sahura take zaune da 'yar ƙuda. Yatsina fuska Jamila ta yi ''Dole na nuna isa a gidan nan kuwa,domin gidan yayata ne,ki iya bakinki don bana barin ko ta kwana,ta kusa da ke ta ba ki labari'' tana fadin haka ta wuce cikin falon tana ambaton sunan yayarta da Yasir. Sahura ta yunkura za ta mike 'yar ƙuda ta yi sauri dafata tare da girgiza mata kai ''A'a Maman Hamid. Jamila ba kamar Mairi bace. Kaɗan daga cikin aikinta da miki dukan tsiya duk da ɗanyantakan jegonki. Ki ja tazugen bakinki har sai ta bar gidan nan idan kina son zaman lafiya. '' Furucin 'yar ƙuda ya zama tamkar garwashi ne da ke shirin ƙone zuciyarta murmus.Zuciyarta sai tafasa take kamar talgen tuwo. Ji take tamkar ta fizgo Jamila ta hau ruwan cikinta ta yi ta kai ma fuskarta naushi. ''Ta ya Ubangiji ya tsaga mini baki ki hanani magana. Na ce miki tsoronta nake ji ne,ita ɗin wa! Ita ɗin banza! Me aka yi aka yi ta! Ta isa ta..." ''Da wa kike!" Jamila ta faɗa tana ƙarasowa wurin a hasale, tsaf! Kunnuwanta sun ji komai. Sahura ta yunƙura za ta bata amsa a zuciye sai suka ji sallamar Mairi. Turus Mairi ta tsaya tana duban ƙanwarta. ''Ko ba ki yi murna da ganina ba ne na koma inda na fito" cewar Jamila tana ɗaukar Jalil. Murmushi Mairi ta saki tana faɗin ''Wace ni Maryam! Saukan yaushe?" Ta tambaya suna shigewa ɗakin lokaci guda. Sun ma manta da wa su halittu a wurin. Yadda Mairi ta yi burus da Sahura,sai hakan ya kara rine zuciyarta ta koma baƙa ƙirin. A ranta ta furta 'Akwai sauran rina a kaba kenan,amma mu je zuwa akwai ranar ƙin dillanci,ranar da awakan Sarki suka ɓata,za ku sha mamakina ke da shegiyar ƙanwar taki'' ''Ni dai kin ga tafiya Maman Hamid don zuwan Jamila ba alkhairi ba ne a gareni. Shaiɗaniya ce wallahi. Sai an jima'' cewar 'yar kuɗa tana miƙewa tare da barin gidan ba tare da ta tsaya jin ta bakin Sahura ba. Sahura ba ta ma san 'yar ƙuda ta bar gidan ba,tsabar kogon tunanin da ta faɗa mai zurfin gaske. Tunani kala-kala suke kai-kawo a zuciyarta. Tashi ta yi ta shige ciki. A tunaninta za ta gansu a falon,amma sai kuma akasin tsammani muryoyinsu ta ji a ɗakin Mairi,hakan ya bata tabbacin hirarsu suke cikin raha. Wucewa ɗakinta ta yi ta kwantar da Hamid ita ma ta bi lafiyar gadon.Duka farincikin da ta samu a yau ya rikiɗa zuwa baƙin ciki. Dole ta koya ma Jamila hankali,ta kuma gane ruwa ba sa'an kwando ba ne. Dogon tsaki ta ja tana juyi a saman gadon. A cikin ɗakin Mairi,a nutse Jamila ke cin taliyar da Mairi ta kawo mata. Ta ci sosai sannan ta ajiye plate ɗin gefe ta sha ruwa. Kallon tsanaki ta yi wa Mairi sannan ta ce ''Yaya ashe Dauda aure ya ƙara?" Murmushi Mairi ta yi sannan ta ce ''Eh Jamila 'yar'uwarsa ce. Jiya ta dawo wanka daga Sakkwato" Taɓe baki Jamila ta yi tana 'yar gyatsa tare da shafa shamulallan cikinta ta ce ''A gaskiya kishiyarki bata mini ba. Da ba dan kin zo cikin lokaci ɗazu ba,lafiyyayen mari na so sauke mata don na ga alamun kanta na turiri.'' Waro manyan idanunta Mairi ta yi waje tana riƙe haɓa,sai kuma ta ce ''Rufa mini asiri Jamila. Muna zaman lafiya da baiwar Allah ki tayar mana da ƙayar baya.'' ''hhhhhhhh!. Ai na ga kamar kanta na rawa ne,kin ga kuwa gwara na tayata tsayar da shi wuri guda. Hmmm. Wato dai namiji namiji ne,duk inda yake halinsa na nan a cikin jininsa. Yanzu fisabilillahi me kika gaza wa Dauda,wani irin kyakkyawan kulawa ne baki ba shi, saboda tsabar munafinci ya rasa wacce zai auro sai 'yar'uwarsa don su haɗe miki kai.'' Hannu Mairi ta sa a bakinta tana mata alamar ta yi shiru kishiyarta na ji, Dogon tsaki Jamila ta ja ''Sai aka yi me idan ta ji! Tsoranta nake! Daudan ma karan kansa ba tsoransa nake ji ba. Ke kankat! A gabansa ma zan iya amayar da abin da ke zuciyata. Haka kurum! Allah ya sa dai ba mugunta take miki ba,tun da ke ba mai hayaniya bace...'' ''Ki rufa mini asiri don girman Allah Jamila! Kwana nawa za ki yi a nan'' A gatsale Jamila ta ce ''Huɗu!" Waro idanu waje Mairi ta sake yi,zamanta a gidan tare da Sahura matsala ce babba. Yadda take nuna tsantsar tsana ga Sahura ba za su wanye lafiya ba,ɗabi'arta ce idan ta tsani mutum ya shiga uku kenan, duk hanyar da za ta bi don ta takalesa faɗa sai ta bi,sai sun goge raini sannan hankalinta ke kwanciya. ''Ki yi wa darajar ma'aikin Allah Muhammadul Rasulullahi (S.A.W) ki koma gobe. Zaman ku tare a gidan nan ba ƙaramin matsala ba ne. Na san halinki idan kika tsani mutum ya shiga uku'' ''Ni fa ban tsaneta ba amma raini ne bana so. Idan ta kawo mini abin da zuciyata ba za ta ɗaukaza mu kwashi 'yan kallo. Bassss!" Shiru Mairi ta yi tana kallon 'yar'uwarta, Jamila ko a jikinta hasalima wasa ta koma yi da su Yasir suna dariya. Suna zaunan suka ji kiran sallah a masallacin kusa da gidan. Tsam! Jamila ta miƙe ta bar ɗakin,alwala ta yi ta dawo falo inda Mairi ta ajiye dadduma da sallaya ta saka sannan ta kabbarta sallah. Fitowa Mairi ta yi zuwa waje ɗauro alwala,zuciyarta sai nauyi take mata,ji take kamar kar da ɗauro alwalan ta yi sallar a haka. Da ƙarfi da yaji ta yi nasarar yakice mummunan tunanin ta soma alwala. Bayan ta kammala za ta shigo falon ta ci karo da Sahura. Dummmmmmmm! Zuciyarta ta buga da matuƙar ƙarfi. Da sauri ta dafe saitin zuciyarta tana duƙar da kanta lokaci guda tare da azamar shiga falon. Murmushin mugunta Sahura ta yi,zuciyarta na ammana tsoranta ne cunkushe cikin ranta. 'Hmmmm. Ba a yi komai a wasan ba Mairi,ko taka ledar ma ba mu yi ba. Mu je dai zuwa yarinya.' ta furta a ranta tare bar gidan zuwa gidan 'yar ƙuda. Mamaki ne ya kusan nutsar da Jamila a saman sallayar,tabbas idanunta ba ƙarya suka yi mata ba,yayarta tsoron kishiyarta take. To me hakan yake nufi? Ta fi kowa sanin wace ce yayarta wurin zurfin ciki da nuna komai ba komai ba,koda kuwa hakan zai cutar da ita. Abin haushin duk tambayar duniya idan aka yi mata a kan abin da ke damunta ba za ta sanar ba. Tsotsa leɓanta na ƙasa ta yi tana tashi daga saman daddumar Mairi ta amsa sallayar ta saka tare da kabbarta sallah. Baƙon yanayin da ta tsinci kanta a lokacin da take shirin ɗaura alwala ya sake kawo mata ziyara. Wani irin zafi zuciyarta take mata ,gaɓoɓinta kamar ana kwankwatsa su. Da ƙyar da siɗin goshi ta kammala sallar. Wannan karon ma Jamila na hankalce ta ita. Don ba daidai ta yi sallar ba.Sai da ta sallame sallar Jamila da buɗi baki ta ce ''Yaya baki da lafiya ne?" Jinjina mata kai ta yi,zuwa yanzu abin da take ji a jikinta ya ƙara girmama. Da sauri ta cire sallayar ta wuce ɗakinta. Kallon tausayi Jamila ta bi 'yar'uwarta da shi,ko bata furta ba,akwai ɓoyayyen abin da ke damunta. Abin mamaki Mairi na isa ɗakin ta ji yanayin ya ɗauki kamar ɗaukewar ruwan sama,zafin da zuciyarta take mata yanzu babu. Me ke shirin faruwa da ita ne yau? ''Yaya'' Jamila ta furta da sanyin murya na ƙarasowa cikin ɗakin tare da su Yasir. Ɗan ɗagowa Mairi ta yi ba tare da ta ce komai ba. Kusa da ita Jamila ta zauna idanunta a kanta ''Yaya me ke damunki? Ɗazu na ga tsoron da kika ji lokacin da kika haɗu da kishiyarki a falo. Ko tana miki mugun abu ne yaya?" Da sauri Mairi ta furta ''A'a Jamila. Ko kusa kar ki zargi baiwar Allah,babu abin da take mini wallahi'' ta karashe maganar zuciyarta na tabbatar mata hakan da ta faɗa shi ne daidai,domin bata manta mummunan kashedin da Sahura ta yi mata ɗazu ba. Kallonta Jamila take bata ko ƙyafta ido. Kwata-kwata bata gamsu da furucinta ba, akwai wani abun da take ɓoye mata wanda yake cutar da ita. ''Tun da kin ce haka,shikenan! Amma kar ki yi wasa da addu'a yaya,tun muna gida bi ki ciki mayar da hankali a kan sallar dare ba. Kar ki manta yanzu kina da kishiya sannan baki san me take ƙudurtawa a ranta ba. Ki yawaita sallar dare tare da Istigfari. Kin ga sallar dare kamar wani turke ne wa bayin Allah a kan bin Allah. _Manzon Allah (S.A.W) ya ce:Na horeku da sallar dare domin al'adar salihan bayi ce kafinku,kuma kusanci ce zuwa ga Ubangijinku,sannan tana kankare zunubbai,tana hana saɓon Allah_ kar ki yi wasa da sallar dare don Allah yaya. Ki naimi tsari daga sharrin kishiyarki don zuciyata bata kwanciya da ita. Ki ja yaranki a jiki sannan su ma ki din ga tofe su da addu'a. Kin ji Yaya'' Jamila ta ƙarashe maganar a sanyaye. Sosai zantukan Jamila suka yi matukar tasiri a zuciyarta. Sai dai wani ɓangare na zuciyarta na shirin rinjaye tasirin da kalaman Jamila suka mata. A sanyaye ta furta ''Zan dinga yi in shaa Allah. Sannan ki tayani da addu'a'' ''Na ɗaukar mini alƙawarin tayaki da addu'a,Allah ya yi miki katangar ƙarfe tsakaninki da kishiyarki tare da duk wani masherancin da ke bibiyarki ta ƙarƙashin ƙasa.'' Wani sanyi zuciyar Mairi ta yi,tare da ƙara ƙaunar tilon 'yar'uwarta ta. Wani shafin hira suka buɗe wanda ya jiɓanci danginsu,cikin raha da annashuwa suke hirar...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren Sahura bayan ta bar gidan ta nufi gidan 'yar ƙuda. A zaune ta isketa ta saka hannu cikin zani tana susar gabanta kamar za ta zauce. '' 'yar ƙuda lafiyanki kuwa kike susar gabanki kamar wacce ta yi tsarki da ruwan karara?'' ta yi maganar tana zama a ɗaya daga cikin kujerun ɗakin tana fuskantar ta. 'yar ƙuda da ke susa tana jin daɗi da zafi lokaci guda ta ce ''Hmmmm. Wasu ƙuraje ne ƙananu suka fesu mini masu ɗan banzan ƙaiƙayi a gabana,jiya sai da muka samu saɓani da babansu. Saboda rashin imani da tsabar iskanci bai ga azaban susan da nake yi idan ƙaiƙayin ya taso mini ba,don rainin hankali ya dubi tsabar idona ya ce wwai ina warin gaba,sannan a bushe ni ke,har da cewa kwata-kwata ban da ni'ima. Fisabilillahi ya mini adalci,haka ake. Ita kishiyar tawa haka yake mata? '' Murmushi Sahura ta yi ganin yadda 'yar ƙuda ta hasala. ''Ba komai ya haifar miki da waɗannan ƙurajen ƙaiƙayin ba sai sanyi da rashin kula da jiki. Sanyi na matuƙar tasiri sosai a jikin ɗan'adam musamman mace. Idan ya zamana baki kula da kanki yadda ya dace,nan da nan sanyi zai miki shigar farad ɗaya, ya dauke miki ni'ima, idan kuna mu'amalar aure keda mijinki ki dinga jin zafi,ga uwa-uba warin gaban da zai haifar miki da shi'' Waro mitsi-mitsin idanunta 'yar ƙuda waje ta yi tana faɗin ''Au Allah! Daman sanyi ne ya yi mini wannan illar a gaba? Maman Hamid wane maganin zan saye na riƙa sha don girman Allah'' Murmushi Sahura ta saki tana kwanto Hamid daga bayan ta fara shayar da shi sannan ta ce ''Eh to akwai wani haɗi na musamman da gwaggota take mana, yana kashe cututtukan sanyi a jiki,yana tsaftace mahaifa da gaba ga uwa-uba yana ƙara wa mace kuzari da lafiyyayen sha'awa. Nan da nan ni'imarki za ta dawo'' Cike da zumuɗi 'yar ƙuda ta ce ''Maman Hamid sai ƙara tsumani kike wallahi,sanar mini inda zan samu kayan haɗin,ko daga nan zuwa birnin Legas ne zan je'' 'yar dariya Sahura ta yi tana canja Hamid zuwa ɗayen ɓangaren ''Ba a kai can ba 'yar ƙuda. A cikin kasuwar garin nan akwai, ma za ki samu citta,kirfa,kanunfari,daddoya(Basil) da tafarnuwa ki tafasa su sannan ki tace. Ki matsa lemun tsami ki zuba zuma ki juya. Ki sha kofi ɗaya safe da yamma zuwa mako ɗaya. Za ki sha mamaki 'yar ƙuda. Amma fa za ki ƙulla ƙawance mai ƙarfi da fitsari.'' Babban yatsa 'yar ƙuda ta shiga jinjina mata bakin nan kamar gonar auduga ta ce ''Ai kuwa na gode sosai Maman Hamid zan yi yadda kika ce.'' Murmushi Sahura ta yi ''Kar ki damu wallahi.Daman na zo ne ki ba ni labarin shaiɗaniyar ƙanwar kishiyata. Kallo ɗaya na yi mata na ji na tsaneta'' 'yar ƙuda sai da ta ɗan soshe gabanta kaɗan sannan ta ce '' Ba zan ce ga ainihin wace ce ita ba amma idan kina neman 'yar tasha kika samu Jamila to ki shafa fatiha. Idan kin bi ta tawa Maman Hamid,kar ki nuna ikon da kike ma Maman Yasir a gaban Jamila,don za ku kwashi 'yan kallo ne daga ƙarshe a gane kin mallaketa ne. Ki bari idan ta koma garinsu sai ki ba za ikonki son rai,ni ma a dinga turota tana mini aiki'' ta kai karshe da sheƙewa da dariya. Dariyar Sahura ta yi sannan ta ce...✍️ ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_010_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ ...Dariya Sahura ta yi sannan ta ce ''Zan kuwa bi shawararki, idan ta san wata ai bata san wata ba. Kin ga bari na koma kar a kuma irin na wancen karo. Ya diro garin nan ban sani ba'' ta yi maganar tana mikewa tare da goya Hamid ta bar gidan. Kamar yadda Sahura ta ɗauki shawarar 'yar ƙuda na janye ƙudirinta a kan Mairi har sai Jamila ta bar gidan hakan ta faru. Kwanaki huɗun da Jamila ta yi a gidan, Sahura bata nuna wani iko a kan Mairi ba,hasalima sabgar gabanta take tana jan Mairi a jiki saboda tsabar iya ƙwarewa a makirci. Jamila dai kallonta take kwata-kwata bata yarda da ita ba,jira take ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ta sammaceta,sannan kwana huɗun da ta yi a gidan kullum sai ta tashi Mairi sallar dare. Jamila mace ce mai riƙo da addini,a fuskarta kaɗai za ka fahimci hakan,wawakeken tabon sallah ne raɗau a goshinta,sai ya ƙara fito da kyawunta ziryan. A rana ta huɗu Jamila ta koma Mada. Ko awa biyu ba a yi da tafiyan ta ba Dauda Imamu ya yi musu saukan bazata. Cike da farinciki suka tarbe shi tare da shirya masa kirki na musamman a tare kamar ƙawaye a kicin,nan kuwa Sahura sake jaddada mata maganar tafiyan take. Da daddare bayan sun kammala cin abinci ya ba kowa tsarabarsa sannan ya yi gyaran murya ''To Alhamdulillah na je na ga wuri,kuma ya yi mini ɗari bisa ɗari. Don haka Sahura zan sakaki islamiyya sai na tafi da Mairi,zan dinga zuwa wurinki a duk wata uku zuwa shekara ɗaya sai Mairi ta dawo ke kuma Sahura na tafi da ke'' ''Malam ina da magana'' Mairi ta ce cike da sanyin murya. ''Ina saurare'' ya faɗa yana dubanta da murmushi. Miyau mai kauri ta haɗiye tana satar kallon Sahura da ta tsareta da manyan idanunta sannan ta ce ''Idan so samu ne ka tafi da Sahura Kadunan,wani zuwan sai ka tafi da ni'' ''Mene ne dalilin yin hakan'' ya faɗa a ɗaure yana dubanta. Ɗan muskutawa ta yi tana gyara kwanciyar Jalil a saman cinyarta ta ce ''Saboda makarantarmu,mun

Chapter 7 of 33