Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dandamalin goshinta ta share,cikin murya mai tsananin sanyi da tsantsar karaya ta ce ''Na amince da duka sharuɗɗan ranki shi daɗe. In shaa maka Allahu ba za ki sameni da karya ɗaya daga cikinsu ba'' Murmushi mai ƙayatarwa Madam Ngozi ta yi sannan ta ce ''Good job! Ai ba just a baki za ki faɗa ba,dole ki saka hannu don tabbatar da abin da kika ce,domin idan kika kuskura kika yi gigin breaking just a single rule za ki sha mamakina,sannan zan dinga zuwa gidanki a bazata and karki manta duk abin da kike yi a gidan muna gani a cikin na'urarmu a nan, idan ma ƙarya ne za mu sani kuma za ki sha mamakinmu. Don haka ga pen ki saka hannu '' ta yi maganar tana miƙa mata biron tare da juyo da littafin zuwa gabanta. Hannunta na rawa ta amsa biron,sai dai ta kasa riƙe biron da kyau balle ta iya saka hannu. Ba islamiyya ta yi ba balle a kai ga boko. Babu abin da ta iya indai a kan harkar karatu ne. Madam Ngozi bata ce komai ba tana kallon ikon Allah,maganganu fal cikinta,kenan Sahura bata yi boko ba. ''Iletarate woman! Riƙe pen ɗin da kyau ki rubuta ko rubbish ne'' Jinjina mata kai Sahura ta yi tana riƙe biron da ƙarfi ta ɗan yi rubutu wanda ita kaɗai ta san shirmen da ta rubuta. (My Esteem fans ko kuna son na faɗa muku abin da Sahura ta rubuta ne😂) Amsar takardar ta yi sannan ta sake kiran Sergeant Mathew ya zo ya ɗauki littafin saita miƙe. ''Ina ƙara faɗa miki Sahura! Idan kika kuskura kika karya sharaɗi ɗaya i swear to Almighty God sai kin zauna a gaurd room na kwana goma sannan babu mai cetonki a duk barikin nan. Idan kina ganin ƙarya ne Please try to break one and see my true color. Muguwa!" Tana gama faɗin haka ta wuce wurin da sojojin suke kai mutane ɗakin laifi,'yan maganganu suka yi sannan ta bar ɓangaren baki ɗaya. Bayan tafiyan Madam Ngozi wasu mata biyu suka zo tafiya da ita. Kai tsaye suka kaita wani akurkin ɗaki sai dai babu datti a ciki suka sakata sannan suka kulle ɗakin. Abu goma da ashirin suka haɗe mata kai,a hankali tabi ɗan kurkukun ɗakin da kallo,wasu zafafan hawaye suka shiga rige-rigen sauka daga gurbin idanunta. Mutsu-mutsu Maryam ta fara yi a baya alamun farkawa take son yi. A hankali ta sauketa ta fara shayar da ita nono. Wani abu mai kauri da ɗaci ya tokare mata maƙoshi,zuciyarta na tafarfasa kamar talgen tuwo. Ta nuna kanta tana zubar hawaye ''Wai ni yau Sahurar gwaggwan bugaje aka saka cikin gaurd room silar yaran kishiyata! Ni Sahura! Kai ina! Wallahi da sake! Yanzu duk tarin uƙubar da na tanadar ma yaran kishiya sun tashi a banza!'' ta faɗa a fili tana share hawayen da suka kasa daina sauka daga kwarmin idanunta. Wata zuciyarta ta ce mata ta mayar da yaran kawai ta huta da bala'in Madam Ngozi,don ba barin za ta yi ba, ta tabbata duk abin da ta faɗa babu makawa za ta aikata,amma kuma wani ɓangaren na zuciyarta na raya mata gurɓatacciya kuɗuba a kan idan ta sake yaran Mairi suka koma wurin uwarsu shikenan Mairi ta yi gwaggwaɓar nasara a kanta. Ita kuma ba haka take so ba,a kullum bata da wani tunani sai na ganin ta baƙanta ranta,ta cusa mata baƙincikin da har ta mutu tabon na nan a ranta,hakan kuma ba zai tabbatu ba sai idan yaran suna hannunta,duk da an shata mata babban layi a kansu amma suna hannunta kuma tabbas tana da yaƙinin Mairi tana nan cikin ƙunci da baƙin ciki mai girma na rashinsu ga Dauda Imamu da take juyawa tamkar waina a tanda. Dole ta nemi shawarar maman 'yar gayu ta ji ta bakinta. Lokaci guda kuma ta saki kuka mai sauti tuno da sanwar da ta ɗaura a risho,ta san da wuya hankalin Dauda Imamu ya je wurin kicin ɗin. Yanzu haka yaranta za su dawo da yunwa su samu bata gidan? Ya Nu'aymah za ta kasance idan bata ci abinci ba? Wa zai kular mata da yara kafin ta dawo? Yanzu haka za su wuni basu ci abinci ba har sai lokacin da aka fito da ita. Hannu ɗayan da bata riƙe Maryam ba ta ɗaura a kai tana kwarma uban ihu tare da kururuwa tamkar wacce aka aiko ma saƙon mutuwar Gwaggwon Bugaje. Sosai take kukan kamar ranta zai fita tana faɗin ''Wayyo ni Sahura na mutu na lalace! Shikenan yau yarana za su wuni da yunwa! Gwaggo! Gwaggo ki taimake niiiiii! Yiiiiiiii! '' Ihunta ya farkar da Maryam da ta koma bacci,take ta saki matsanancin kuka saboda firgitar da ta yi. Sahura na jijjigata tana kukan,ba komai ya ɗaga mata hankali ba sai yaranta,bata tunanin Dauda Imamu zai dawo gidan ya duba ko sun dawo balle ya yi tunanin nemo musu abinci ko kuma gyara sanwar da ta ɗaura a saman risho. Haka ta ci gaba da kuka tamkar ƙaramar yarinyar goye...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren mahaifin Muhsin yana komawa gida ya ɗauko Momy suka taho asibitin,har da sauran break fast da suka rage ta taho da shi. A gurguje suka gaisa da maman Jawaheer sannan ta musu sallama ta bar asibitin domin hankalinta ya koma gida kar su Jawaheer su dawo bata nan,Mahaifin Muhsin ya wuce cikin gari aka bar momy da Yasir da ke shan farfesun kayan ciki da kakkauran shayi cikin natsuwa wanda momy ta kawo, lokaci bayan lokaci tana jansa da hira,tun yana takurewa har ya saki jikinsa da ita. Dauda Imamu na komawa masallaci tafiyar gaggawa ta taso mishi zuwa barikin da ke cikin Jaji wurin limamin masallacin juma'ar can.Kasancewar shi ne babba sai haƙƙin zuwa barikin ya rataya a wuyanshi. Da tunanin Sahura da Hamida da kuma su Aunty Saudah idan suka dawo daga makaranta babu abinci ya tsallake zuwa Jaji,ko samun damar zuwa flat ɗinsu bai yi ba. Lokacin dawowa makaranta ya yi,su Hamid cike da farinciki suka saho gidan,sai dai ga mamakinsu suka tarar da gidan babu kowa. Nu'aymah kuma sai jera hamma take tana shafa ɗan cikinta. Hankalinsu su Hamid ya ƙara tashi domin tun da suke da mahaifyarsu a duk inda take idan lokacin dawowarsu ya yi za ta dawo ta ɗora musu girki. Kicin Aunty Saudah ta nufa sai dai bata iske abinci ba,hasalima tukunyar da take saman rishon take ƙauri alamun abin ciki ya ƙone. Da sauri ta ɗauki tsumma ta sauke tukunyar tare da kashe rishon. Dawowa falon ta yi tana yin kicin-kicin da fuska. Hamid da ke lallashin Nu'aymah ya ce ''Mama ta bar abinci kuwa?" Girgiza masa kai ta yi, nan da nan fuskarsa ta sauya. ''Aunty Saudah ke da su Amina kuje gidan ƙawayen mama ku ga ko tana nan. Ni zan je masallaci na amshi kuɗi hannun baba mu saye wani abu mu ci. Babu musu suka fita shi ma haka aka bar Halima da Nu'aymah a gida. Sosai Nu'aymah take kuka ita ina mamarta ta bata abinci yunwa take ji. Hamida ya je masallaci bai ga Dauda Imamu ba sai ya wuce islamiyya,a nan ba mai ganshi ba sai ya dawo flat ɗin. Su Aunty sun gama gantalinsu gidajen ƙawayen Sahura ba su ganta ba. Maman 'yar gayu ma ɗakinta a kulle yake alamun bata nan. Haka suka dawo gidan a galabaice. Hankalinsu ya tashi,kuka suka shiga rerawa kowanne da kalar sautin muryarsa suna kiran baba da mama. Nu'aymah ta fi kowannensu galabaita,a ɗan ƙaramin tunaninsu iyayensu su gudu sun bar su. Babu wanda a cikin ya yi tunanin zuwa kicin ɗin ko akwai garin kwaki su sha,abinka da 'ya'yan gata komai yi musu ake,ba su san wata aba wai wahala ba. ^^^^^^^^^^^^^^ Kai tsaye mahaifin Muhsin ya wuce makaranta ya ɗauko su Jalil bayan ya dawo daga cikin gari ya wuce da su asibiti. Sai da ya tsaya restaurant ya saye musu abinci aka saka a robobi masu murfi,ya haɗa da drinks sannan ya nufo barikin. A asibitin suka ci abincin har da shi, Hamida ma ta ciabincin sosai,domin zuwa yanzu ta ji sauƙi,ƙurajen sun fara mucewa, tarin da take yawan yi ta daina sakamakon kyakkyawar kulawar da take samu daga wurin ma'aikatan asibitin da maman Jawaheer. Suna ci suna hira har maman Jawaheer ta dawo tare da yaranta biyu mace da namiji,sai ƙanwarta budurwa da suka zo tare domin bata kammala girki ba suka iso. Tamkar Family ɗaya haka suka shiga hira, yayin da mahaifin Muhsin ya fita. Bayan fitarsa wata nurse ta zo duba Hamida,ganin ta samu sauƙi sosai sai nurse ɗin ta ce zuwa gobe za su sallameta. Wannan kenan...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Ƙarfe 5:40pm na yamma* A daidai wannan lokacin aka fito da Sahura daga akurkin ɗakin, domin da gangan sojojin suka ƙara mata lokaci don ta sake ladabtuwa. Ko ba a faɗa ba Sahura ta ladabtu kuma ta shiga taitayinta, idanunta sun ƙara manya saboda kukan da ta sha. Kafin ta tafi sai da suka sake jaddada mata sharuɗɗan sannan ta wuce. A hankali ta goya Maryam sannan ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki. Ta shanyo kwanar flat ɗinsu kenan ta haɗu da...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_029_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ A hankali ta goya Maryam sannan ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki. Ta shanyo kwanar flat ɗinsu kenan ta haɗu da maman 'yar gayu ita da yaranta,alamun daga unguwa suka dawo,duba da yadda suka cancaɗi ado suna walwali. Maman 'yar gayu na haɗa ido da Sahura zuciyarta ta halba, kamar an sauya mata kamanni. Fuskarta ta yi ɗan jaja,idanunta sun ƙara girma kuma sun sirka kamar ta yi dambe an naushesu tsabar yadda suka kumburo. Suna haɗuwa Mama 'yar gayu ta ce ''Maman Hamid! Me ya sameki haka? Faɗa kika yi ne aka tumurmushe fuskarki? Kin ga kuwa yadda kika sauya kuwa?" Murmushin gefan baki Sahura ta yi tana share hawayen da suka gangaro mata ta ce ''Ko ɗaya maman 'yar gayu. Hankalina yanzu yana kansu Nu'aymah na san har yanzu ba su ci abinci ba. Idan na natsu za mu yi magana'' ''Muje gidan naki yanzu sai 'yar gayu ta tayaki girkin,hankalina ba zai kwanta ba idan ban ji abin da ke damunki ba" ''To'' kawai ta ce sannan suka ci gaba da tafiya. A dakalin gidan Sahura ta iske su Hamid sun yi jugum-jugum kamar marayu, ko uniform ɗinsu ba su cire ba, Nu'aymah na kwance a saman cinyar Aunty Saudah tana kuka. Lokaci guda tausayin yaranta suka sake mamaye zuciyarta,ko ba a faɗa mata ba ta san ba su abinci ba. Wasu hawaye masu ɗumi ta share zuciyarta ta tuƙuƙi. Su Halima na ganin mamarsu suka kira sunanta da iya ƙarfinsu,da gudu suka yo kanta tare da faɗawa jikinta suna sakin wani sabon kukan. Cak! Ta ɗauki Nu'aymah da ke ambaton ta bata abinci cikinta zai gudu,yunwa take ji. _(Allah sarkin daɗi wai in ji ɓarawon takanɗa! Haba Nu'aymar Sahuralliya me aka yi da maza 😂 just yunwar wuni guda kina faɗin cikinki zai gudu. Allah ya ba su Yasir haƙuri da Gyatumarki ta dinga azabtar da su da yunwa😭. Wallahi akwai kishiyoyin da suke da irin halin Sahura a wannan duniyar. Allah ka tsarkake zukatanmu. Ka ba mu ikon aikata alkhairi ka kuma tsare mu daga aikata sharri duk ƙanƙantarsa)_ Idanun maman 'yar gayu sun cika da ruwan hawaye ganin yadda su Hamid suke kuka ita ma Sahuran na zubar hawaye,duk da bata ma san taƙameman abin da ke faruwa ba,ƙarasawa cikin flat ɗin suka yi. Sahura na shiga cikin falon ta zauna saman kujerar jagwab kamar kayan wanki duk da goyon da ke bayanta,ita ma karan kanta yunwarce ke ƙwaƙular hanjin cikinta, bata taɓa kaiwa yamma bata ci abincin rana ba,ko lokacin watan ramadan idan ta ji azumin na wujijjigarta bayi take shiga ta kulle ta ci ta ƙoshi sannan ta fito. Maman 'yar gayu da kanta ta shiga kicin ta ɗora girki,ganin akwai jajjagyen kayan miya ga kuma taliya a gefe har guda biyu sai kawai ta ɗora jollof ɗin taliya na manja. Bata fito a kicin ɗin ba sai da ta kammala girkin tsaf. Tire guda ta zuba ma su Hamid ta cika shi sosai,ta zuba ma Sahura a plate. Kiran Hamid ta yi ya shigo ya ɗauka sai ta fitar ma Sahura da nata. Koda ta fito ta iske su Hamid har sun fara kai hannu cikin tiren duk da turirin da abincin ke yi. Hannu na rawa Sahura ta amsa abincin tana kwanshe goyon Maryam,Maman 'yar gayu ta amsheta sannan Sahura ta ja zip ɗin rigarta ƙasa don abincin ya shiga ciikinta da kyau. Haka ta fara cin abincin hannu baka hannu ƙwarya duk da ƙonewan da hannunta yake yi. Sosai tausayinsu ya kewaye lungu da saƙon zuciyar maman 'yar gayu,ta matsu ta ji me ke faruwa da babbar aminiyarta. Tsaf suka cinye tafiya suka suɗe tiren kamar an wanke ka ce masu kamun yunwa ne. (😂 Wa ya faɗa muku Borno gabas take,yunwa ai ba sa'ar ubansu ba ce😂 ko ya kuka ce my Esteem fans. Wallah ina jinku Kamar jinin da ke wayo a jikina my Esteem fans. I love you lodi lodi muahhhh😘😘😘🥰🥰🥰) Bayan sun kammala ci suka shiga gasar gyatsa,idan wannan ya saki gyatsa sai ɗayan ya saki,zuwa lokacin an fito daga sallar magrib. Har yanzu Dauda Imamu bai shigo gidan ba,ita Sahura har ta manta da batun Dauda Imamu,da yaranta take. Bayan Sahura ta natsu yaran sun sauya kayansu saai suka zauna kallo,ɗan matsowa ta yi kusa da maman 'yar gayu. Tamkar mai faɗin rahoto a gidan redio, tiryan-tiryan ta shiga labarta mata abin da ya faru,,komai ta sanar mata. Tana kai ƙarshen maganar ta rushe da kuka tana faɗin ''Maman 'yar gayu yau na gama ganin tozarci a idon duniya. Ni Sahurar gwaggwan bugaje za a kai gaurd room da garƙame tamkar wacce ta saci tagullar sarki. Duka a kan yaran tsinanniyar kishiyarta! Kalli shatin hannun basamudiyar sojan a kuncina'' ta yi maganar tana jujjuya ma maman 'yar gayu kumatunta,sai a sannan maman 'yar gayu ta ga tambarin yatsun hagu da dama sun yi ja abinka da farar mace. Tsoron,tashin hankali da mamaki suka cika zuciyar maman 'yar gayu. Lallai Sahura yau ta yi gamo da gamonta. Wata nauyayyar ajiyar zuciya mai ƙarfi maman 'yar gayu ta sauke jin lamarin ya girmi tsohonta. ''To yanzu ke wani mataki kika ɗauka. Za ki mayar da yaran ko za ki zuba musu ido ne tun da dai yanzu an yi miki karan tsaye a kansu?" Share hawayenta ta yi zuciyarta na tabbatar mata hukuncin da ta yanke shi ne daidai. ''Haba dai! Ai wallahi sun zo kenan babu komawa! Ai maman 'yar gayu abin da baki sani ba idan na mayar da su shikenan Mairi ta yi galaba a kaina,ga mari ga tsinke jaka duk a lokaci guda sannan na mayar da su sai ka ce BADAKKARIYA! Zaman su a nan shi ne babban makamina da zan ci gaba da yin nasara a kanta. Na san yanzu haka tana cikin baƙin cikin rashinsu,balle lalacewar da ta ga sun yi,na san zuciyarta na cunkushe da tsantsar damuwa. A Da na so ki ba ni shawara amma yanzu kan na samar wa kaina mafita'' Jinjina kai maman 'yar gayu ta yi,a fili ta nuna farincikinta da matakin da ta ɗauka,a baɗini kuwa bata ji daɗin haka ba, mene ne amfanin barinsu a gidanta tun da bata da iko a kansu, gwara ta mayar da su hannun uwarsu sai ta ci gaba da juya mijin. Gyara zaman mayafinta ta yi sannan ta ce ''Tun da dai yanzu baki da iko a kansu,idan ki bi tawa shawarar ki mayar da hankali a kan yaranki sosai,duk da na sanki gwanace wurin kula da yara,musamman matan don yaranki za su yi kyau da matan manya wallahi'' Wani sanyi Sahura ta ji a ranta wanda rabon da ta ji irinsa tun safe,juyawa ta yi ta kalli 'yan matanta zuciyarta na tabbatar mata da sun fi dacewa da masu ƙumbar susa musamman Nu'aymarta. Juyowa ta yi fuskarta kwance da maɗaukakin murmushi ta ce ''Tabbas kin kawo shawara mai tsada,kuma in shaa maka Allahu zan mayar da hankali sosai a kansu. Kin san Allah yanzu yaran Mairi ba su raina,koda sun dawo gidan nan babu ruwana da su, hankalina zan mayar gurin 'yan matana na ci gaba da tsumasu da kayan mata" ''Da kyau animiya! ni ma dai idan kin tashi aika saƙon kayan matan,ki mini magana zan bayar da nawa kuɗin a haɗo da ni don na fara tsumasu,kayan mata su ne a gaba a inganta gidan aure'' ''Maganarki dutse, idan Dauda Imamu ya tashi zuwa Sakkwato zan yi miki magana,Gwaggota sai ta haɗo mana kayan'' ''To shikenan bari na wuce gida kar dare ya yi mana,Allah ya kiyaye na gaba'' Ta yi maganar tana miƙewa, yaranta da ke kallo suka miƙe ,ta yi ma Sahura sallama sannan suka wuce. Da ƙyar Sahura ta iya miƙewa ta je kicin ta jona ruwan wanka a heater,sai ta dawo falon. Hirar da suka yi ta maman 'yar gayu ta shiga dawo mata,tabbas yanzu ne ya dace ta mayar da hankalinta a kan yaranta musamman 'yan mata,don tana da yaƙinin masu kuɗi za su aura idan sun girma. Lokaci guda ta sakarwa kanta kasaitaccen murmushi. Har ta fara hasaso yadda masu manyan motoci za su jeru a ƙofar flat ɗinsu sun zo hira wurin yaranta. Kamar wasa ta tsunduma kogin tunanin 'yan matan,babu irin hasashen sa bata yi ba. Ta ce Nu'aymah za ta auri yaron sarki,Aunty Saudah ta auri ɗan shugaban ƙasa,Amina ta auri yaron shugaban sojojin Nijeriya. Halima da auro babban likitan ƙasa da ƙasa sai autarta ta auro yaron babban ɗan kasuwa mai kamfanoni bila adadin a cikin gida da wajen Nijeriya. Hamid kuma ya zama major genaral. Kai idan wannan tunanin ya tabbata ta gama hannun riga da talauci. Murmushi ne kwance a fuskarta tana tunanin,can ta miƙe zuwa kicin ta juye ruwan wanka ta nufi bayi,bayan ta yi wanka ta amshi Maryam daga hannun Amina ta yi mata wanka ta shiryata sannan ta fito ta zauna tare da yaran. Sai a sannan tunanin Dauda Imamu ya faɗo ranka,ko yana ina har yanzu bai dawo gidan ba oho. Sai kusan goman dare Dauda Imamu ya dawo gidan a matuƙar gajiye,ga mamakinsa sai ya tarar da yaran duka suna falon suna kallo idan ka cire Nu'aymah. Kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa,idan da da ne ta nuni sun firgita ko kuma su ruga daƙinsu da gudu saboda sun san ya hana kai goma ana kallo,tun da suka yi masa sannu da zuwa suka ci gaba da kallonsu ba tare da shakkar komai ba. Abu mai ɗaci ya tsaya masa a maƙoshi,bai tsaya a falon ba ya wuce uwar ɗaka inda ya samu har Sahura na minsharin bacci. Komawa falon ya yi ya kulle ƙofa sannan ya dawo ya kwanta,daman tumbinsa a cike yake ga kuma gajiyar da ta nannaɗe gaɓɓan jikinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci bacci mai daɗi ya yi awon gaba da shi...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ *Hayin bijini Mada jihar Zamfara Nijeriya* A ɓangaren Mairi da 'yar uwarta hankalinsu ba a kwance yake ba,sun yi matuƙar ƙosawa gobe ta yi Mamman ya je Bariki ya ji halin da su Jalil suke ciki. Suna raya daren da nafilfili, sun yarda da Allah shi ke yin komai sannan shi yake da iko a kan kowa,duk raka'ah ɗaya suna daɗewa a sujjada,Mairi wani lokaci. har kuka take tana addu'ar Allah ya kare mata yaranta daga sharrin kishiyarta. HAFIZA kuwa ta sake zama miskila ta ƙarshe,kaɗaicin 'yan'uwanta ya saka ta zama shiru a koyaushe,halayyarta takan tsoratar da Mairi da Jamila,sai ta wuni bata ce uffan ba,tana nan tana zane-zanenta wanda ta mayar da shi kamar ibada,bata kula yaran gidan kwata-kwata, koyaushe za ka sameta da littafi kuma tana tilawar Al'qur'ani mai girma. Wannan kenan...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* Cikin dare Sahura ta ji amon muryar Dauda Imamu a falo yana karatun Alqur'ani. Tsaki ta ja mai tsayi tana sake ƙudundunewa cikin bargo,ita ta rasa wannan jarabar,mutum kullum cikin karatun Alqur'ani ko gajiya ba ya yi. Da safe da ta tashi bata iskeshi ba,sai ta yi ma yaran wanka ta ɗora abin kari gudu-gudu sauri-sauri ta kammala saboda kar su yi latti. Bayan sun ci ta ba su kuɗin break suka wuce makaranta. Miƙewa ta yi ta gyara gidan sannan ta koma bacci ita da Maryam. Yau da wuri Dauda Imamu ya dawo gidan. Ganin bata falon sai farinciki ya cika ransa. Kai tsaye ya nufi kicin ya ɗauko abin karinsa ya karya,ya ɗora ruwan wanka a risho ya yi zafi ya juye sannan ya wuce bayi wanka. Duk bidirin da yake a gidan Sahura bata san yana yi ba,domin bacci sosai take sharɓa ita da 'yarta,gajiyar zaman akurkin ɗakin bai gama sakinta ba. Bayan ya sanya kaya ya fito. Zuwa lokacin ƙarfe 12:12am na rana har ta yi. Ya fito kenan ya haɗu da mahaifin Muhsin ya fito daga motarsa zai nufo flat ɗinsu. Cike da mutuntuwa suka gaisa. ''Daman na zo mu je da kai wurin iyalina,don zuwa gobe nake son zuwa Abuja amsar takardar transfer. Wannan karon jihata ta Kaduna suka ajiyeni'' ya faɗa cike da murna. ''Alhamdulillah haka ake so. Allah ya ci gaba da tsare mana ku. Da na so zuwa ganin jikin Hamida ne'' ''To muje tare daga can ba sai mu wuce gidan nawa ba'' ''Eh hakan kuwa ya yi. To muje'' Har Dauda Imamu zai shiga mota kenan ya ga an sauke Mamman a mota. Cak! Ya tsaya daga shiga motar. Mahaifin Muhsin ya fito yana kallon inda Dauda Imamu ya mayar tamkar TV. Bayan an sauke Mamman ya ƙaraso inda motar mahaifin Muhsin take da yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Hannu ya miƙa suka da Mahaifin Muhsin sai ya juyo ya gaisa da Dauda Imamu wanda mamaki ya ƙawata fuskarsa. ''Na san ka yi mamakin ganina ko Dauda'' Ɗan murmushi Dauda Imamu ya yi sannan ya ce ''Sosai kuwa Mamman! Rayuwa ta yi tsada,na jima sosai idanuna ba su yi tozali da kai ba. Ya iyalin,ya ka baro su'' ''Duka suna nan lafiya Alhamdulillah.'' ''Officer Kabir ga yayan uwar gidana ku gaisa'' cewar Dauda Imamu yana nuna Mamman. Sake gaisawa suka yi sannan Mamman ya ce ''Daman Malam ne ya aiko ni wurinka a kan batun yaran Mairi. Yana so na zo na gani da idanuna. Shin da gaske ne ka muzanta iyalinka a gaban mutane ko dai Mairin ta faɗa ne dai saboda tana son ka bata yaranta?'' Ɗif! Dauda Imamu ya yi saboda an kai gaɓar da bakinsa ba zai iya furta komai ba. Bayan faruwar al'amarin ya yi nadamar abin da ya aikata mata yafi cikin

Chapter 21 of 33