bacci sai Hamid da ke kallo a TV shi kaɗai. Sannu da zuwa ya yi mishi sannan ya ruga uwarɗakan mahaifiyarsu ya tashe a kan Baba ya dawo. Hamma ta yi tana mika sannan ta fito falon. Zuwa yanzu Sahura ta zama 'yar lukuta,ta ajiye shirgegen tumbi,ɗuwawukanta sun ƙara cikowa da girma haka nonuwanta. Sannu da zuwa ta yi mishi tana zama kusa da shi lokaci guda.
''Hamid! Je ka kwanta dare ya yi. Madadin ka ɗauko litattafanka ka duba ko karatun Alkur'ani sai ka ɓige da kallon wannan shiriritar. Zuwa gobe zan ji sakamakon kowa a makaranta''
Mikewa Hamid ya yi yana zumɓuro baki yana ƙuƙƙuni ƙasa-ƙasa kar mahaifinshi ya ji ya wuce ɗakinshi. Shi kaɗai yake kwana a ɗakin wanda babu abin ɗakin ke yi sai zarnin fitsari,wai don ma Sahura na iya bakin ƙoƙarinta a kanshi. Ƙazami ne na ajin farko. Ga shi da magagin bacci,idan ya farka da magagin har ɗakinsu Aunty Saudah yake zuwa ya fito da gabansa ya tsulala musu fitsari,su yi ta rantsuwar ba su ba ne,da yake ta san halin kayanta kuma ta san yana magagin bacci sai ta share tare da tsaftace wurin. Ranar da iskancin ya kai shi tsula fitsari a bisa jikinsu Dauda Imamu da Sahura ya ci duba kamar babu gobe. Ran Sahura ya ɓaci har suka so samun saɓani don ita bata ga laifinshi ba tun da magagin bacci yake ba a zahiri ba ne.
Bayan ya wuce ɗaki sai Sahura ta dubeshi ta ce
''Na kawo mata abinci ne,ko wanka za ka fara yi?''
''Wanka'' ya faɗa a gajarce yana ɗora kansa a hannun kujeran ɗakin tare da lumshe ido. A matukar gajiye ya dawo garin,motarsu sau uku tana tsayawa a hanya daga karshe ma juye driban ya yi a Zaria. Kai tsaye Sahura ta nufi kicin wanda zuwa yanzu an sauya komai na ciki zuwa na zamani,don Dauda Imamu akwai ƙoƙarin kyautawa iyalinsa. Ta fito da kuloli biyu ta ajiye a saman centre table da ke tsakiyan ɗakin,ta koma ta dauko plate da jug na ruwa da karamin kofi ta ajiye. Bayan ruwan ya yi zafi ta katse rishon tare da juyewa a bokitin wanka ta kai masa bayi ta riska. Tana fitowa ta ce masa ta kai ruwan bayi,za ta wuce ɗaki ya ce ta dawo ta jira shi akwai maganar da yake son su yi. Take ƙirjinta ya buga da matuƙar ƙarfi. Ɗauko Maryamu ta yi sannan ta dawo falon tana shayar da ita. Sai da ya shirya tsaf sannan ya dawo falon ya ci abinci. Ya yi gyatsa tare da hamdala ya ce
''Daman batun komawarki Gusau ce ya taso ke da yaranki''
Dummmmmm! Ƙirjinta ya yi mugun bugawan da ya kusan tafiya da numfashinta. Miyau mai kauri ta haɗiye sannan ta ce
''Kuma yaya Mairi ta yarda da hakan. Na ga bata son zama bariki''
'yar dariya Dauda Imamu ya yi sannan ya ce
''Mairin da kika sani ban da ta yanzu. Sosai take farinciki da hakan,hasalima ita da kanta ta ce sai Yasir ya shiga sakandare sannan su dawo da zama nan. Tun waccan shekaran na so dawowanta amma sai ta ce na bari wannan shekarar. ''
Shiru Sahura ta yi kamar ruwa ya cinyeta,take zufa ta shiga kwaranyo mata duk da a watan decemba ne kuma lokacin sanyi . ' Kai anya Mairi ce da kanta ta faɗi hakan! Ko dai ƙayar da yanzu ya koya ne yake son yi mini don ya dawo da Mairi! Ta furta a ranta. Ta yi amanna ta rufe bakin Mairi a kan wannan zancen,sannan ta yi mata mummunan kashedi! Bai ci a ce mallakar har ta warware ba duba da mallakar da Gwaggwonta ta yi ma kishiyoyinta,har yanzu tana baza ikonta a gidan,kullum gaba-gaba take ba baya ba,ta ya sai ita. 'Yan'uwanta ma suna cin karansu babu babba a gidan mazajensu,sai abin da suka ce ake yi. Ta ya na ta zai kasance daban.
''Ko bacci kike yi ne Sahura?"
''A'a baban Hamid,gajiya ce ta lulluɓe ni. Uhm! Yaushe ne za su dawo nan ɗin''
Gyara zama ya yi sannan ya ce...✍️
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_015_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
Gyara zama ya yi sannan ya ce
''Na ce ta bari bayan kun dawo daga yawon arba'in sai su dawo''
''To shikenan'' ta faɗa tana mikewa lokaci guda,a zuciye ta bar falon. Ɗagowa ya yi yana bin ta da kallo har ta shige ɗakin. Taɓe bakinsa ya yi yana furta ''Hmmm'' a fili,domin bai yi zaton irin furucin da za ta yi ba kenan. Wato dai ta nuna rashin jin daɗinta a zahiri. In ban da halin mata,baiwar Allah ta yi haƙuri sama da shekaru goma,bata taɓa takowa Kaduna ba amma don an ce ki koma can ita ta dawo nan kike ɓata fuska. Wace mace ce za ta iya yin haƙuri kamar yadda Mairi ta yi. Tsaki ya ja sannan ya wuce ɗakin. Duk da gajiyar da ke lulluɓe da shi,haka ya daure ya ɗauko Al'qur'ani mai tsarki ya fara karantawa. Dauda Imamu ya fara manyanta,ɗawainiyar gida da buga-bugar yau da kullum sun saka shi gaba. Biyan kuɗin makaranta da kuɗin lafiyarsu kaɗai sun ishe shi riga da wando. Sauƙinsa ma a nan bariki kuɗin da yake biya daidai yake da wanda soja ke biya wa yaransa,ba kamar farar hula ba _Civil servant_ A can Gusau ma ya samu sauƙin kuɗin makarantarsu,inda yake biya ma mutane uku, HAFIZA a matsayin _scholarship_ take. Karatun Alkur'ani yake cikin natsuwa da kwanciyar hankali,yayin da Sahura ke aikawa bayansa harara tamkar idanunwata za su firfito,hawaye ba su bar sauka daga kwarmin idanunta ba. Domin tun lokacin da ta dawo ɗakin ta kwantar da Maryam ita ma ta kwanta take sharɓar kuka,shigowarsa ɗakin sai ta rage sautin kukan. Duk da wani ɓangare na zuciyarta na kwantar mata da hankali,domin zuwanta Sakkwato yawon arba'in zai matuƙar yin tasiri. Duk mai yiwuwa za ta yi, koda kuwa za ta tafi tsirara ne wallahi sai ta mallake Dauda Imamu ta yadda duk abin da ta kindaya masa ba zai musa mata ba. Zama bariki kuwa yanzu ta fara,bata ga uban da ya isa ya hanata ba. Jan majina ta yi tana gyara kwaciyarta tare da share hawayenta. Sake hararar bayan Dauda Imamu ta yi tana ƙwafa tare da juya kwanciyarta. Bata san lokacin da ya kammala karantun Alqur'ani ba ya kwanta. Cikin dare ta farka fitsari ta yi tozali da shi ya kai goshinsa ƙasa yana sujjada,ta jima tana jira ta ga ya ɗago daga sujjadar amma bai ɗago ba,da ta gaji ta miƙe zuwa ban ɗaki tana karatun zuci,ta yi amanna wannan ibadar da yake ne ya sa boka Ataka kasa yin galaba a kansa. Wannan karon sai sun yi nasara a kansa,idan ta kama su canja boka ne za su yi,burinta kawai ta ga ya dawo tafin hannunta,tana juya shi kama waina a tanda,ba shi kaɗai ba har ta da makirar matarshi da yaransa kamar yadda Gwaggwonta da sauran 'yan'uwanta suke yi. Bayan ta fito ta tarar da ya ɗaga kafta-kaftan hannayensa sama bakinsa na motsi. Yatsina fuska ta yi ta koma bacci zuciyarta fal alwashin mallakar Dauda Imamu a wannan karon.
Washegari da safe suna karyawa Dauda Imamu ya dubi yaransa
''Hamid na nawa kazo a makaranta?"
Rassss! Ƙirjinsa ya buga da matukar ƙarfi don wannan karon bai kwaso abin kirki ba,wancan karon ya zo na sha bakwai cikin su ashirin da biyu, wannan karon madadin ya ƙara ƙasa sai gaba ya kuma yi.
''Da kai fa nake!" Ya yi maganar cike da tsawa.
''Haba Baban Hamid! ka kwantar da hankalinka mana,zai faɗa maka. Ƙara rikita shi kake idan kana tsawar'' Sahura ta faɗa tana tamke fuska,don a rayuwarta ta tsane ta ga ana ma yaranta tsawa ko faɗa. Babu ɗan da ta taɓa masa tsawa balle duka a cikinsu,iya karta ta lallaɓasu har su yi abin da ta so.
''Ke baki ji shirun da ya yi mini ba. Wasa nake mishi da zai mini shiru''
''Na ashirin da ɗaya na zoooo'' ya ƙarashe maganar cike da tsoro.
''Cikin ku nawa?"
''Mu ashirin da biy....'' Paaaap! Dauda Imamu kai ma bakinsa bugu yana faɗin
''Wato shiriritar taka ƙara gaba take ko! Last term ka zo na sha bakwai,madadin ka dawo baya sai ƙara gaba kake yi. Cikin ku ashirin da biyu ka zo na ashirin da ɗaya,to mene ne marabar dambe a faɗa! Babu abin da ka saka a gaba sai kallace-kallacen banza ko, kuna dawowa daga Sakkwato za ku koma Gusau da zama na dindindin. Ko TV ba zan saka muku ba! Ke Sauda'' ya kira sunanta.
''Na'am baba'' ta furta da sauri jikinta na tsuma tsabar tsoron da ya ɗarsu a zuciyarta.
''Na nawa kika zo?"
''Ummm! Ummm! Daman a aji malaminmu baya sona! Kuma! kuma sai ya...''
''Tambayar da na yi miki kenan?"
Da sauri da girgiza kai tana sosa ƙeyarta.Miyau ta haɗiye tana satar kallon mahaifiyarta ko za ta kawo mata ɗauki,amma sai aka yi rashin sa'a ba ita take kallo ba. Gwara Hamid sau dubu a kanta,don kullum ita ke cin na ƙarshe a ajinsu
''Baba na karshe na zo wallahi tallahi Baba ba laifina ba ne...''
''Rufe mini baki ja'irar banza! Kamar an yi miki baki kullum ta ƙarshe. Idan ba laifinki ba ne! To laifin uban waye! Ni zan zauna miki a ajin?"
Girigiza kanta ta yi tana matsar ƙwalla. Juyawa ya yi yana duban Amina da Halima.
''Ku kuma fa!”
''Baba na goma na zo cikin mu talatin'' Amina ta faɗa cike da murna,ko ba komai ta san tafi yayyanta ƙoƙari.
''Ni kuma na bakwai cikin mu talatin da huɗu'' cewar Halima tana murmushi. Sai a sannan Dauda Imamu ya saki fuska,ya ɗan ji daɗi a ranshi.
''Uhmmm! Yanzu na ji batu! Kun yi ƙoƙari amma ku sake dagewa nan gaba,yadda next term za ku zo daga na ɗaya zuwa na huɗu sai na yi muku kyauta mai tsoka kamar sauran 'yan'uwanku na Gusau. Ko yanzu ma bata ɓaci ba,idan kun dawo daga islamiyya zan baku kyauta.''
''Mun gode Baba'' Halima ta faɗa cike da farinciki tana ma Aunty Saudah gwalo. Harara ta wurga mata tana yin ƙwafa.
''Ke kuma fa! Nu'aymah!. Na ji na 'yan'uwanki''
Kafin Nu'aymah ta amsa Sahura ta caɓe da cewa
''Ai kasan a nursery take yanzu,ba a rubuta musu sakamako"
''Na sani amma ai ana ba duk wadda ta zo daga na ɗaya zuwa da huɗu certificate na karramawa. Wannan karon ma HAFIZA an bata da ta zo ta ɗaya''
Tsuke fuska Sahura ta yi jin ya ambaci sunan da ta fi tsana a duniyar nan. Ba komai ya sabbaba mata wannan tsanar ba sai yawon yabon da yake mata tare da fifita a kan yaranta. (Haba Sahuralliya 😂 'yar mitsitsiyar yarinya sa'ar Nu'aymarki kike ma wannan tsanar😂 a huce haka. Ko ya kuka ce my Esteem fans 🥰💯)
''Hmmm! Wa ya sani ƙila ita HAFIZAR ba ƙoƙarinta ba ne. Ka san dai ana cuwa-cuwa don a ce yaro na da ƙoƙari ko.''
''Karatun da kullum take a gida ita kaɗai shi ma cuwa-cuwar ce idan kin ce sakamakon cuwa-cuwa ne?" Ya yi tambayar yana tsareta da ido domin ya harbo inda maganarta ta dosa. Cike da borin kunya ta ce
''Kar ka fassara ni Baban Hamid. Ai gaskiya na faɗa, daga ƙinta sai faɗawa halaka. Kun ga ku yi sauri ku kammala kari kar lokaci ya ƙure. Yau za mu fara shirin tafiya zuwa Sakkwato. Sauƙinta ma yau za a baku hutu'' ta kai ƙarshen maganar tana miƙewa,sam! Ta tsani maganar HAFIZAR nan,idan da ya san yadda zuciyarta ke tafasa tana turiri tare da fitar da baƙin hayaƙi da bai yawaita yin maganarta a nan ba,amma ba komai akwai lokaci. Har ta shige ɗakin bai bar kallonta ba,tun ba yau ba ya fahimci Sahura da manufarta a kansa, duk abubuwan da take a barikin yana sane da su. Kawai ya bari akwai lokaci tun da idan ta dawo daga Sakkwato za ta koma Gusau da zama na dindindin. Dole ya saka mata takunkumi domin har yanzu bata bar ɗabi'arta na yawon gidaje da tara matan sojoji a gida ba, musamman idan ya tafi Gusau. Har su Hamid suka kammala karyawa Sahura bata fito ba. Mikewa ya yi shi ma zuwa makarantar.
Duk abubuwan da ta san za su buƙata a Sakkwato ta ajiyesu a gefe,babbar ghana-must-go ta saka kayan ciki ta zuge zip . Ta fitar da kayan da za su saka gobe a gefe. Su Aunty Saudah na dawowa daga islamiyya ta tsefe musu kai ta wanke,sannan ta kai su gidan kitso. Ta ba Hamid kuɗi ya yi aski. Cikin dare ta yi musu lalle ja suka kwanta da shi.
*Ƙarfe 8:30am na safe*
A daidai wannan lokaci suka iso tashar kawo inda za su hau motar Sakkwato. Kuɗi mai yawa ya miƙa mata tare da addu'ar Allah ya saukesu lafiya ya dawo gida...✍️
^^^^^^^^^^^^^^
*Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya*
"HAFIZA! Wai ba na hanaki taɓa mini drawing book ba!" Cewar Hamida wacce yanzu take cikin shekara ta takwas, ta ɗaure fuska tana zuba ma HAFIZA manyan idanunta kamar za su fito . HAFIZA wacce take cikin shekara ta biyar ta cunno bakinta tana ci gaba da zanenta kamar ba da ita take maganar ba. Sosai basarwar HAFIZA ya sake ƙular da Hamida.
''Wai ba da ke nake ba! '' kamar da dutse take,nan ma taƙi tanka mata kuma bata bar zanenta tana murmushi ba. A duk duniya abin da ta fi ƙauna shi ne zane,sai ta wuni tun safe har dare tana abu ɗaya,abinci da sallah kaɗai ke tayar da ita. Ko muryar ƙawayenta ta ji sun zo su yi wasa,da sauri take rantamawa a na kare zuwa uwar ɗakansu ta ɓoye,idan suka gaji da jira su wuce,gobe ma ba za su fasa zuwa ba. Domin HAFIZA akwai farin jinin mutane ba yara kaɗai ba. Sai dai ita sam bata sakewa da su, idan kana son jin dariyarta da surutunta to sai a wurin mutane huɗu;Abbanta,Ammunta,Ammu Jamila sai Yaa Jalil. Ko Yaa Yasir da Adda Hamida bata sake musu har su yi labari. Idan tana waje tamkar kurma take komawa,ga shi bata da sabo da mutane. Haddar Alqur'ani,karatun boko da zanenta kaɗai take ba muhimmancin a rayuwarta.
Ganin idan za ta shekara a nan HAFIZA ba za ta ce uffan ba,sai kawai ta fizge drawing book ɗin tana huci. Miƙewa HAFIZA ta yi tana riƙe mitsitsin ƙugunta tare da sauke manya-manyan idanunta da ke zagaye da zara-zaran gashin ido a kan Hamida tana tsuke ɗan mitsilin bakinta.
''Adda Hamida ki ba ni! Ai Abba ya ce idan an yi hutu kowa zai dinga ba ni drawing book dinsa ina zanena a ciki'' ta faɗa cikin zazzakar muryarta da take ma mutane rowa idan sun ce ta yi musu magana.
''To ba zan bayar ba malama" Hamida ta faɗa tana saka drawing book ɗin a jaka. A zuciye HAFIZA ta wuce ɗaki. Tun daga nesa Mairi take murmushi don yadda HAFIZA ta tsuke fuska tana tunkarota ya tabbatar mata sun sayar da halin da 'yar'uwarta.
''Lu'u-lu'uta wa ya ɓata miki ke ne ya karɓa hukunci yanzun nan"
'''Ammuna Adda Hamida ce! Ba Abba ya ce idan an bayar da hutu su dinga ba ni drawing book dinsu ba?"
Jinjina mata kai Mairi ta yi
''Haka ne lu'ulu'uta.''
''Ammuna har na fara zane gidan da idan na girma za mu koma ciki ta fizge. ''
'' La la laaah! Ai kuwa bata isa ba,dole ta kawo ki kammala zana mana gidan da za mu koma.''
Sai a sannan HAFIZA ta saki fuska,hayewa saman cinyarta ta yi tana dubanta da murmushi
''Ammuna bayan gidan ma,zan zana asibitina da zan riƙa mutu allura idan na girma. Ai Ammuna baki kukan allura ko?"
'yar dariya Mairi ta yi jin shirmen HAFIZA sai ka ce ita ba kukan allurar take ba.
''Bana yi HAFIZA''
Dariya HAFIZA ta yi har ƙananun haƙora ta na bayyana. Sallamar yayyinta ne ya katse mata dariyar. Da sauri ta sauka daga cinyar Mairi ta ruga tana musu oyoyo. Tare suka ƙaraso cikin ɗakin hannun kowanne ɗauke da leda.
''Kayan cefanan ne haka da yawa yau'' Mairi ta yi maganar tana amsar ledar. Budewa ta yi tana ganin abubuwan ciki.
''Har da kaza! Yau za mu ci daɗi! Sadiƙu na ƙoƙarin kyautata mana! Kun saye ashanar da na ce kuwa?''
''Eh Ammuna" Jalil ya bata amsa. Kasancewar hantsi ya fara dubar ludayi,mikewa ta yi da ledojin zuwa kicin. Hamida da ke ɗaki ta fito,suna haɗa ido da HAFIZA ta galla mata harara.
''Yaa Jalil ka amsar mini drawing book ɗin Adda Hamida.'' cewar HAFIZA. Juyawa Jalil ya yi yana duban Hamida fuska a ɗaure duk don kar ta kawo masa wargi
''Bata drawing book ɗin! Ba Abba ya ce idan an bamu hutu mu dinga bata ba?"
Zumɓuro baki Hamida ta yi tana ƙuƙƙuni.
''Ba da ke nake ba!" Ya furta a tsawace. Da sauri ta koma ɗakin ta ɗawo drawing book ɗinn ta wurga mata. Yasir da ke gefensu bai tbai saka bakinsa ba,don bai cika magana sosai ba. Kusan halinsu ya zo ɗaya da HAFIZA, bambancin shi idan ya samu wuri yana zuba kamar kurna, har cikin abokansa yana surutu ba kamar HAFIZA ba. Kwata-kwata ta tsani shiga mutane,tafi son ta killace kanta duk da karancin shekarunta,a turance ana kiran masu kalar wannan halayyar da _Introvert_ Cike da farinciki HAFIZA ta ɗauki drawing book din ta koma ɗakinsu.
Zuwa yanzu Yasir na da shekara sha uku kuma yana Jss2,a islamiyya yana aji huɗu. Jalil kuma na primary five wanda yanzu shekararsa sha ɗaya,a islamiyya yana aji uku. Hamida na primary three sai a islamiyya tana aji ɗaya,inda HAFIZA ke nursery two,a islamiyya ajinsu ɗaya da Hamida. Sun ta so cikin kyakkyawar tarbiyya da kulawa daga mahaifyarsu Mairi,duk da yanzu Dauda Imamu ya saka musu TV,amma ba su cika kunnawa ba sai azumi idan ana tsafsir. Tarbiyya irin ta addinin islama Mairi ta shimfiɗawa yaranta. Suna daga cikin yaran da ake buga misali indai tarbiyya ne da natsuwa tare da girmama manya. Yasir da Jalil suna izo goma a hadda,yayinda Hamida da HAFIZA suke gogayya da juna wurin hadda,dukkaninsu suna izu biyu. Wannan ahalin sun zamo tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya ne,kansu a haɗe yake. Duk rashin jituwar Hamida da HAFIZA a gida ne,takan tare mata HAFIZA faɗa duk da bata cika tsokana ba,idan faɗan yafi karkinta Yasir ko Jalil su shiga ciki...
^^^^^^^^^^^^
*Garkar Bala fari mai fata Ƙofar kaɗe jihar Sakkwato Nijeriya*
A ɓangaren su Sahura, sai wurin biyar na yamma suka isa gidan. Dukkaninsu sun jigatu da zaman mota musamman Nu'aymah da bata saba hawan mota ba. Gwaggwon Bugaje sai nan-nan take da su,ji take kamar ta tsaga ƙirjinta ta sakasu zabar murna da shauƙi. Nan da nan da aika sashen kishiyoyin aka kawo musu tuwan dawa da miyar kuka har da manshanu. Nu'aymah sai yatsina fuska take tana faɗin
''Mama mene ne wannan kamar amala?"
Da yake Sahura tana da ƙawa bayarabiya,takan kawo mata amala da miyar ewedu har da ganda,silarta ta san amala. Girgiza mata kai ta yi
''Tuwan dawa ne wannan ba amala ba. Ki ci da daɗi''
''A'ah! Wallahi bazanci ba! Ni taliya nake so!"
Waro ido Sahura ta yi ''Yi haƙuri ki ci Nu'aymah tarh, yarinyar mamanta,gobe ki ci taliyar kin ji''
Rushewa da kuka Nu'aymah ta yi jin ba za ta samu taliya ba. Nu'aymah sangartacciyar yarinya ce da sam bata san babu ba, duk abin da ta ce tana so shi Sahura take mata. A duk cikin yaranta ba mai bakin kwaɗayi irin Nu'aymah duk da ita ce ƙaramarsu amma tafi su cajama Sahura kai musamman idan ta nemi abu ta rasa. Dauda Imamu ya yi faɗa har ya gaji, kullum cikin ce mata yake ta daina shagwaɓata domin gaba ake gudu idan ta taso da irin wannan halayyar kasancewarta mace,abun ba zai yi kyau ba. Ga ta da roko har na fitar hankali,duk wadda ta zo gidan Sahura da abu tana ci sai Nu'aymah ta roƙa a ba,ko kuma ta saka kuka,ko a hannun yaro ƙarami yake sai ta nemi ta danne shi ta amsa. Ko a jikin Sahura,ita a ganinta yarinta ne idan ta girma za ta daina.
Sahura ta yi lallashin duniya amma taƙi shuru, Gwaggwan bugaje na shigowa ɗakin ta iske dramar. Zama ta yi tare da jawo Nu'aymah a jiki
''Kishiyata kukan me kike?"
Cikin shessheƙar kuka Nu'aymah ta ce
''Mmmama ce na ce zan ccci ttttaliya ta hananiiiiii! yiiiiiiiiii! Yiiiiiiiiii!" Sai ta rushe da sabon kuka.
''Ina Kishiyata! dole ki ci taliya tun da kina so yanzun nan,yi shiru kin ji. Za ki ci taliya ko?"
Jinjina mata kai Nu'aymah ta yi tana tsagaita kukan. Duban Hamid Gwaggwon Bugaje ta yi tare da faɗin
''Jeka sashen Tasallah ka kira mini ita''
''Ok madam Bugajet jet, amma har da ni za a ci taliyar '' ya yi maganar cike da shaƙiyanci yana barin ɗakin. Sahura tun da ta samu Gwaggwan bugaje na lallaɓa Nu'aymah ta natsu ta fara cin tuwan,ta jima bata ci tuwon dawa ba. Sosai take kwasar loma,a gefe guda Maryam na tsotso. A tare suka dawo da Hamid. Kallon ƙasƙanci Gwaggwan bugaje ta yi mata tana yatsina fuska ta ce...✍️
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_016_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
Kallon ƙasƙanci Gwaggwan bugaje ta wurga mata tana yatsina fuska kamar ta ga kashi, sai can ta taɓe baki tana hura hanci. Tasallah kanta a ƙasa jikinta na tsuma kamar ta ji kiɗi disko
''Jikata na son cin taliya...''
''Har da nama'' Nu'aymah ta faɗa tana katseta. Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi sannan ta ce
''Kin ji da kunnuwanki ta ce har da nama, don haka cikin kuɗinki ki aika a siyo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 33