Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kira sunanta,cike da azama Tsahara ta ce ''Na'am mai babban ɗaki'' ''Sahura za ta dawo ɗakinki da wankan jego kafin na dawo. Ki tabbatar da kin kulan mini da diyata yadda ya kamata'' ''To mai babban ɗaki. Ko sauro ba zan bari ya cutar da ita da yaronta ba,kamar yadda za ki barta cikin ƙoshin lafiya haka za ki dawo ki sameta'' Murmushi mai sauti Gwaggwon Bugaje ta yi,domin ta yi amanna furucin Tsahara haka ne. ''Tasallah!" ''Na'am mai babban ɗaki '' Gyara zama Gwaggwon Bugaje ta yi sannan ta ce ''Idan na tafi kwana ɗaya ne rak! Kema za ki yi a turakar mijina. Daga kwanan kar ki kuskura ƙafarki ta taka turakar'' ''An gama mai babban ɗaki. Maganarki dutse yadda kika ce shi ne muradina.'' Gwaggwon Bugaje jinta take a sararin samaniya,babu wani shege a doron duniya sai ita. Yadda take juya kishiyoyinta da mijinta hakan na matuƙar faranta mata rai. Su bauta mata,haka 'ya'yansu da jikokinsu ma ba baya ba. Musamman yara mazan. Idan suka dawo daga ci-rani,ba sa tsayawa ko'ina sai ɗakin Gwaggwon Bugaje. Ita ce farkon buɗe jakarsu,ta ɗauki abin da ranta ya mata sannan su tafi. Daga sashenta ne suke wucewa na iyayensu daga nan kuma su wuce shiyyoyin (Gidajen) matansu, kasancewar dukkaninsu sun yi aure. Matan ma bata ƙyalesu ba. Ɗan lumfasawa ta yi sannan ta ce ''Kai kuma Malam na dawo gareka! Kar ka ga na barsu kwana ɗakinka ka ci amanata. Sannan kamar yadda kunnuwanka suka ji,kowacce sau ɗaya za ta kwana turakarka. Sauran kwanakin kai kaɗai za ka yi su. Fatan ka fahimta!'' ''To ranki ya daɗe. Yadda kika ce shi zan yi. '' Bata ce komai ba ta tashi tana miƙa tare da hamma. Ba rufe baki haka da wuce sashenta tana tafiya ɗaiɗai har ta isa sashen. A sashenta Sahura har ta kwanta saman ƙaramin gadon bacci ya fara janta. Motsin mutum ta ji sai ta yi saurin juyowa. Ganin Gwaggwonta ce,sai ta miƙe daga kwancen ta zauna. ''Gwaggwo ina ta jiranki,kin ƙi zuwa bacci har ya soma fizgata'' ta yi maganar tana murza idanunta tare da yin wata wakekiyan hamma kamar za ta haɗiyi ɗan tsako. Zama ta yi kusa da ita sannan ta ce ''Yi hakuri uwata. Ina can ina raba musu kwana ne kar su mini ba daidai ba. Amma ina ni ina barin uwata ita kaɗai. Ina so zuwa jibi na tafi Nijar wurin boka Ataka maganarki. Da zafi-zafi ake bugun ƙarfe. Kar muna nan mun saki baki ya wuce da makirar kishiyarki Kaduna. Kin ce za ki bani labarin abin da ake miki a gidanki. Kin ga idan na je wurin Boka Ataka zan san abin da ya dace na sanar masa'' Gyara zama Sahura ta yi tare da ba mahaifiyarta labarin abubuwan da suka faru a gidan. Sai da ta ƙara maggi da gishiri saboda labarin ya ƙara ɗanɗano. Tun daga kan tsantsar soyayya da kulawar da Dauda Imamu yake ba kishiyarta,da yawan jizgatan da yake yi, hanata shiga maƙota alhalin kishiyarta tana fita,bata bar komai ba. Tun daga kan biri har wutsiya sai da ta zayyane mata komai. Don ta ƙara tsuma ran mahaifiyarta ,sai ta fashe da matsanancin kuka tana faɗin '''Gwaggo ki taimake ni! Ina matuƙar cutuwa a gidan. Yaya Imamu ya fi ƙaunar Mairi sama da ni. Wallahi babu ranar da za ta zo ta faɗi ban kwashi kayan takaici ba. Har bagidajiya yake kirana'' Ɓacin rai mararan ya bayyana a fuskar Gwaggwon Bugaje,jin yadda ɗiyarta mafi soyuwa take wahala a gidan miji. Lallai kam! Dole ne a goben nan ta tafi Nijar. Tagwayen ajiyar zuciya Gwaggwon Bugaje ta sauke sannan ta ce ''Sha kurkuminki Uwata. Indai a kan mijinki ne da kishiyarki. To kin gama yin kuka har gaban abadan. Za su tabbatar da sun yi gangancin taɓa tsuliyar dodo. Domin karan batta da ni babu daɗi. Na fasa tafiyar jibi,gobe-goben nan zan tafi duk mai yiwuwa a yi. Ba za ki koma Zamfara ba sai da kambun ikonki a tafin hannunki,yadda za ki dinga juya su kamar yadda nake juya nawa da sauran 'yan'uwanki. Za ki koma ɗakin Tsahara da zama har na dawo. Na san gobe 'yan'uwanki za su zo duk da ba za su sameni ba. Kwantar da Hankalinta babu ke babu kuka a kan kishiya in dai ina numfashi a doron duniya. Yanzu ki kwanta ki barcinki,ni zan shirya kayan da ya dace na yi tafiyar da su sai na kwanta. Don asubanci zan yi.'' Kwanciya Sahura ta yi zuciyata fari ƙal tamkar farin wata. Ji take tamkar kaso mafi rinjaye na damuwarta ya gushe. Tana da yaƙinin uwarta tafi ta kowa a faɗin duniyar nan.Zuciyarta har ta fara hasko mata majigin yadda za ta ci karanta babu babbaka a gidan Yaya Imamu. Yadda za ta dinga bayar da umarni cike da iko da gadara kamar uwarta. Murmushi ta sakarwa kanta a karo na babu adadi tana lumshe idanu. Gwaggwon Bugaje kuma ta shirya kayan da za ta yi tafiyan da su da kuɗaden da za ta buƙata sannan ta kashe ƙwan fitila ta hau gado mai rumfa ta kwanta. *Wace ce Gwaggwon Bugaje* Asalin sunanta Maimuna, bafullatanar Bégajé da ke yankin Zinder na ƙasar Nijar. Tana da shekara sha biyar iyayenta suka dawo Illela da zama. Su biyu ne a ɗakinsu duka mata. Mahaifinsu yana da sha'awar noma sosai,sai dai ba su da ƙasar noma a can,dalilin haka ya yi hijira ya dawo Illela da zama da iyalansa,amma duk babban Sallah yana zuwa da iyalinsa Bégajé kasacewar alhalinsa da na matarsa duka a can suke. Iyayen Gwaggwon Bugaje ba su so auranta da Malam Kabiru ba,saboda ba mai arziƙi ba ne kamar na ƙanwarta. Da yake matar mutum kabarinsa,sai Ubangiji ya nufa aka yi auran ta zo a ta biyu. Sunan Gwaggwon Bugaje ya samo asali ne daga sunan garinsu na Nijar Bégajé,sai 'yan unguwa suka mayar da shi Bugaje. Wata tsahuwa a unguwarsu ta saka ma Maimuna Gwaggwon Bugaje kuma ya bita har gidan auranta. Haƙiƙa Gwaggwon Bugaje ta fuskanci kalubale da dama a gidan malam Kabiru,da yake irin makiran matan nan ne masu fuska biyu,bata bari daidai da rana ɗaya wani daga cikin gidan ya gano ainihin fuskarta ba. A hankali ta saye zukatan 'yan gidan. Wani faɗa da ta yi da Tsahara saboda yara Malam Kabiru ya saketa saki har biyu a lokaci guda ba tare da ya ji ba'asi ba. Hakan ya yi matuƙar gigita tunaninta,da sanya tsohuwar yunwar mallakar 'yan gidan da ke can cikin cikinta tasowa gadan-gadan. Yadda Tsahara ta yi silar Malam Kabiru ya saketa alhalin ita ke da gaskiya,sai ta yi maganinta,sannan za ta nuna mata ɗan ƙaramin hakin da ka raina watarana shi yake tsole maka ido. Washe garin ranar ta ɗauki Sahura ta wuce da ita ta bar su Halima. Ran iyayen Gwaggwon Bugaje ya yi matuƙar ɓaci da sakin da Malam Kabiru ya yi mata. Mahaifiyar Gwaggwon Bugaje ta wuce da ita can Bégajé,sai kuma ta dawo Illela da Sahura bayan ta bar Gwaggwon Bugaje wurin Ƙawarta. Inda bayan tafiyar mahaifiyar Gwaggwon Bugaje da kwana biyu ƙawar mahaifiyarta ta kaita wurin wani hatsabiban Boka mai matuƙar hatsari a ƙarshen ƙauyen Aouta. Ba kowa yake iya tunkarar kogon da yake ciki ba saboda azababben sanyin da wurin ke tattare da shi. Nijar ƙasa ce mai ɗauke da ɗaiɗaikun bishiyoyi da tsirrai,a turance ana kiran irin wurin da _Sahara desert_ Sai dai a hamadar ƙauyen Aouta inda da za a ɗauki hanya zuwa kogon boka Ataka, dusar ƙanƙara ke sauka koyaushe tare da wani irin iska mai matukar sanyi kamar ba yankin sahara ba. Hakan ya samo asali ne sakamakon taƙadarin sihirin da boka Ataka ya yi wa yankin kogonsa. Mazaunan garin suna matuƙar tsoron yankin boka Ataka. Masu taurin zuciya ta son abin duniya kaɗai ke ƙundumbalar zuwa yankin. Zuciyar Gwaggonsa Bugaje a ƙeƙashe take shi ya sa da ƙawar mahaifiyarta ta sanar mata yadda wurin yake bata ji ko ɗar! A cikin zuciyarta ba. Burinta ɗaya MALLAKA kota halin ƙaƙa ne sai ta mallaki 'yan gidan bakiɗaya ba ma Malam Kabiru kaɗai ba,ya zama suna a ƙarƙashin ikonta. Ta zamanto mai riƙe da akala su kuma raƙuma,ko wuta ta umurci su je za su je da farinciki. Kamar yadda ƙawar mahaifiyarta ta sanar mata yadda yankin kogon boka Ataka yake haka idanuwanta suka yi tozali. Ba tare da tsoro a zukatansu ba suka shiga yankin har cikin kogon boka Ataka. Babu jira Gwaggwon Bugaje ta bijiro masa da ƙudirinta. Inda a nan ya yi mata kyakkyawan albishiri da burinta zai cika amma akwai wasu manyan ayyuka da za ta yi kafin cikar burin. Ba tare da jin irin ayyukan ba ta amince. Zai bata tukunyar tsafi wacce za ta kai maƙabartar garinsu ta birne, duk shekara dole ta zo maƙabartar kafin alfijir ya fito ta haƙa rami ta ciro tukunyar,ta wanke fuskarta sau uku sannan ta kira ATAKA sau goma sa'ilin nan ta mayar da tukunyar ciki ta birne. Sannan akwai sharaɗin kar ta bari wani ya ganta a lokacin tafiya zuwa maƙabartar da dawowanta. Ruwan tukunyar tsafin zai dawwama ba tare da ya bushe ba. Amma idan har ta kuskura ta bar wani ya ganta to ruwan ciki zai bushe sannan bala'i da musibu iri-iri za su sauka a kan da iyalanta har waɗanda ma ba su zo duniyar ba. Ba tare da wani tunani ba Gwaggwon Bugaje ta amince. Bai amshi wani abun hannunta ba ya umurci su tafi. Bayan sun dawo garin, washegari Gwaggwon Bugaje ta tattara kayanta ta dawo Illela. A nan Illela kwana biyu ta yi ta dawo Ƙofar kaɗe da Sahura. Babu wanda ya yi maraba da dawowarta har malam Kabiru, don cewa ya yi bai mayar sa ita ba don haka ta koma. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta kula shi da matan ba. Da daddare Gwaggwon Bugaje bata yi bacci ba har kunnuwanta suka fara jin kiran sallar farko. A hankali ta lallaɓa kamar ɓarauniya bayan ta yi ɓadda kama ta fita da tukunyar tsafin a hannunta. Lungu-lungun unguwar ta shiga bi har ya sadata da maƙabartar unguwarsu. Abinka da mai ƙeƙashasshiyar zuciya babu tsoro balle firgici a tattare da ita, burinta kawai ƙudirinta ya cika. Haka ta shiga maƙabartar zuwa wurin wata bishiya ta ajiye tukunyar tsafin a gefe guda ta ciro wuƙa daga ƙugunta ta fara haƙar ramin,da sauri-sauri take haƙar saboda ta kammala komai kafin alfijir ya keto. Bayan ta gama ta buɗe tukunyar ta wanke fuskarta da ruwan ciki sau uku kamar yadda boka Ataka ya shaɗanta mata sannan ta kira ATAKA sau goma,sai ta rufe tukunyar ta saka a ramin,ta rufe da ƙasa ta miƙe da sauri ta bar maƙabartar. Hanyar da ta biyo,a nan ta koma kafin alfijir ya keto. Tun daga ranar komai ya sauya. Zukatan 'yan gida suka cika da tsoron Gwaggwon Bugaje. Sakawa da hanawa ya dawo tafin hannunta sannan duk shekarar Allah sai Gwaggwon Bugaje ta je wannan maƙabartar ta ciro tukunyar tsafi ta yi yadda boka Ataka ya umurceta.Wannan kenan. *Cikin labari* Washegari da sassafe Gwaggwon Bugaje ta wuce ba tare da ta yi sallama da 'yan gidan ba. Tafiyar da ta ɗauketa tsahon awa takwas a mota dan ma dirban yana ɗan tsayawa a hanya masu azururruka suna saukewa. Cikin dare motarsu ta tsaya a Bégajé, da ƙyar Gwaggwon Bugaje ta samu abin hawa ya kaita gidan abokiyar wasanta. Da yake iyayen Gwaggwon Bugaje sun rasu duka a shekarun baya,mahaifinta ne ya fara rasuwa,ko shekara bai cika ba mahaifiyarta ta bi shi. Cike da mamaki yaron abokiyar wasanta ya buɗe mata ƙofa ta shigo. ''Maimuna ke ce cikin dare?" Abokiyar wasanta ta faɗa tana fitowa daga ɗakinta. ''Ni ce kuwa Sajida" ''To bisimillah ki shigo'' cewar Sajida tana shiga ciki. Babu musu Gwaggwon Bugaje ta shiga ciki. Bayan ta zauna sun gaisa sai Sajida ta miƙe zuwa wajen wata ƙwarya ta ɗauko ta ajiye gabanta ''Ga nonon Raƙumi nan ki sha sai ki kwanta,babu abinci gidan wallahi'' '' Haba! Babu damuwa wallahi wannan ma ya wadatar'' ta faɗa tana buɗe murfin kwaryar ta kafa baki ta fara sha,don yunwa ce sosai a cikinta. Kwanciya Sajida ta yi don bacci ne a idonta. Ta sha nonon sosai sai mayar da kwaryar wajen zamanta sannan ta hau ɗan ƙaramin gadon da babu yara samansa ta kwanta. Babu jimawa bacci ya ɗauketa. Washegari da safe bayan ta karya ta fita ba tare da ta sanarwa wa Sajida ainihin inda za ta je ba. Haka ma Sajida bata tambayeta,tunaninta ya fi karkata gidan 'yan'uwa za ta je ziyara. Bata sha wuya ba wurin gano hanyar da za ta sadata da yankin boka Ataka kasancewar yaranta biyu duka ta amso musu mallaka duk da ba irin nata ba ne. Ɗiyarta ta farko ce Halima wacce ta rasu a haihuwa kaɗai bata bari ta amsar mata ba,gani take hakan shirka ne babba kuma. Kamar a shekarun baya,dusan ƙanƙara ke sauka a yankin. Ba tare da tsoro ko firgici a zuciyarta ta fara tafiya cikin yankin,bata tsaya ko'ina ba sai a daidai ƙofar shiga kogon.. ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ A can gida Sahura kadai ce ta san da tafiyar Gwaggwon Bugaje. Da safe sai ga Tsahara ta shigo ɗakin kamar an jefota har ta so firgita Sahura. A tsawace Sahura ta ce ''Lafiya kika shigo haka kamar ana bin ki a baya!" ''Wurin mai babban ɗaki na zo. Daman tambayarta zan yi ko yau za ki koma ɗakina wankan jegon ko a bari goben'' Yatsina fuska Sahura ta yi sannan ta ce ''Yau dai gaskiya,sannan ba sai na koma ɗakinki ba. Nan ma ya wadatar.Ki samo mini abinci yunwa nake ji'' Ba tare da ta ce komai ba ta bar ɗakin, babu jimawa jikanta ya shigo ɗakin da ƙwarya a hannu. ''Miye ciki?" Ta yi tambayar tana watsa idanunta a allon fuskarsa. A tsorace yaron ya ce ''Fura ce Kaka Tsahara ta ce na kawo miki'' ''Ajiye'' kalmar data iya faɗa kenan,baƙin ciki ne ya mamaye zuciyarta. Da a gidan Dauda Imamu ne,biredi da shayi har da soyayyan ƙwai za ta karya. Amma a nan a rasa abin da za a bata sai fura. Dogon tsaki ta ja sannan ta kwantar da Hamid ta dawo saman 'yar kujera ta zauna. Furar ta ɗauka ta fara kurɓa a hankali kamar tana kurɓar maɗaci,sai faman yatsina fuska take. Bata jima ta fara shan furar ba Tsahara ta shigo ɗakin da bahon wanka,ta ajiya ta sake fita. Kasko mai ɗauke da rushi ta shigo da shi ta ajiye. Ɗaukan Hamid ta yi ta cire masa kaya,sai ta tsoma cikin ruwan a hankali. Lokaci guda ya tsandara wani uban ihu. Da sauri Sahura babu kunya ta ce ''Kar ki ƙona mini yaro! Baki san wahalar da na sha wurin haihuwarsa ba!'' ''Yi haƙuri" Tsahara ta faɗa cike da sanyin murya sai ta sake tsoma cikin ruwan a hankali. Wannan karon bai yi ihu ba sai dai ya dan razana kaɗan. A haka har ta gama masa wankan ta gasa masa cibiya ta shafa masa mai. Sahura ta fito masa da kayan sakawa ta amsa ta saka masa sannan ta kwantar da shi. Fitar da kayan wankan ta yi waje. Babu jimawa ta dawo tare da sanar wa Sahura ta kai ruwan zafi bayi. Bayan fitarta Sahura ta sauya kaya zuwa ɗaurin ƙirji ta yafa mayafi ta fito zuwa bayin. Da taimakon Tsahara ta yi wankan ta dawo ɗakin ta saka kaya. Bayan ta saka kayan ta sha kunun kanwan da Tasallah ta aiko maya da shi. Wuraren sha ɗaya sai ga yayarta ta iso ita da 'yarta. Wurin ɗaya ƙanwarta ta iso da yaranta biyu duk maza.nan da nan ɗakin ya ɗauki hayaniyar yara. A nan Sahura take sanar musu tafiyan da Gwaggwon Bugaje ta yi zuwa Nijar amso mata mallaka...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren Dauda Imamu sammako ya yi zuwa tasha,babu jimawa motarsu ta nosa hanya. Sai wurin goma na safe ya iso Gusau. Daga nan ya hau 'yar ƙumbula ya kai sa unguwarsu. Cike da farinciki Mairi ta tarbesa.Bai wani jima a gidan ba ya wuce kasuwa. Sabon yaro ya ƙaro a shago saboda ya taimaka ma Sadiƙu tun da zai yi tafiya kuma zai ɗan jima bai dawo ba. Ya daɗe a kasuwar har ya yi sallar azahar,don a can ya saye abincin rana ya ci. Bayan sallar azahar ya wuce islamiyarsu sallama da malam ciki,da yake ƙarfe biyu ake buɗe makarantar. Ya ɗan daɗe a makarantar ya dawo gida bayan ya yi sallar Asr. Lokacin har Mairi ta manta da ta gama girki,ta saka nasa a kula ta yi wankanta ta ci kwalliya ta fito tsakar gidan ta shimfiɗa tabarma ta zauna a samanta. Yasir da Jalil suna gefe guda suna wasa. ''Assalamu Alaikum'' Dauda Imamu ya yi sallamar yana ƙarasowa cikin gidan. ''Wa'alaikum salam Baban Yasir '' Mairi ta amsa cike da fara'ah. Da gudu Yasir da Jalil suke rige-rigen yi masa oyoyo,har abin ya so ba shi dariya, yadda Jalil yake gudu kamar zai fadi yanason rigan Yasir zuwa wurinsa. Cike da so da tsantsar ƙauna mara gauraye ya ɗaukesu lokaci guda duk da akwai leda a hannunsa amma haka ya ɗauke su yana dariya. Bai ajiye su a ko'ina ba sai a saman tabarmar kusa da inda Mairi take zaune,shi ma ya zauna yana daukan Jalil ya ɗorasa saman cinyarsa. Tsam! Mairi ta mike zuwa ɗaki ta ɗauko kula da kofin babba na ruwa da ƙarami guda ta ɗaura a saman babban tiren silver ta fito.Dafa-dukar Shinkafar ta fara zuba mishi daga bisani ta tsiyaya ruwa a karamin kofi ta koma gefe. Ajiye Jalil ya yi sai ya natsu ya fara ba ma cikinsa haƙƙinsa babu ƙaƙƙautawa,har sai da ya tabbatar babu wurin wata ajiyar sannan ya sha ruwa ya yi hamdala. Hira suka fara,inda a nan ta tambayesa ya ya baro su Hamid da 'yan gida. Sanar mata ya yi cikin ƙoshin lafiya ya baro su. Sosai suke hirar cike da shauƙi da annanshuwa. Su Yasir na gefe guda suna wasansu...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ A can hamadar Aouta,bayan Gwaggwon Bugaje ta tsaya a daidai ramin kogon,sai ta tattara duka natsuwarta zuwa wuri ɗaya ta saka ƙafar ta dama kamar koyaushe ta shiga ciki. Iska mai sanyi na tsirran wurin ke kaɗawa,bangon kogon akwai zanen rubutu da halittu mutane da dabbobi, sannan akwai duhu sosai cikin kogon,a hankali take tafiyar har ta iso inda wuta ke ci a cikin tukunya ta zauna. ''Boka Ataka na zo'' ta faɗa bayan ta zauna a ƙasa,ga ƙasar wurin na ɗauke da damshin ruwa da sanyi mai tsuma jiki. Kamar walƙiya sai ga shi ya bayyana a kusa da tukunyar wutan. Wani irin haske mai ƙarfi ya garwaye kogon lokaci guda.Da Wata iriyar muryar mai cike da ƙaraji da amon gaske ya fara magana....✍️ ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_Narrnarhh Bukar_* _(Lady with the Amazing pen ✍️)_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_007_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ ''Boka Ataka na zo'' ta faɗa bayan ta zauna a ƙasa,ga kasar wurin ɗauke da damshin ruwa da a sanyi mai tsuma jiki. Kamar walƙiya sai ga shi ya bayyana a kusa da tukunyar wutan. Wani irin haske mai ƙarfi ya karaɗe kogon lokaci guda. Da wata iriyar murya mai cike da ƙaraji da amon gaske ya fara magana ''Ataka mun sani! Ataka mun gani! Ataka faɗi buƙatarki'' duk jimla guda sai ya ambaci kalmar Ataka,wanda shi kaɗai ya san ma'anarta da kuma dalilin da ya sa yake amfani da ita. Gyara zama Gwaggwon Bugaje ta yi tana dubansa da kyau. Boka Ataka baƙi ne sosai kamar baƙin zunubi, jikinsa ɗauke da zane-zanen baƙi. Fuskarsa ɗiɗɗinke take kamar an ɗinke ƙwarya. Gashinsa murmurɗe irin na dada. Yana da taɓaɓɓan hanci da fala-falan kunnuwa. A takaice boka Ataka bai da kyakkyawar fuska irin ta mutane. Bayan ta gyaran zamanta ta ce ''Boka Ataka yarinyata mai suna Sahura ke da matsala a gidan mijinta. Kwata-kwata bata jin daɗin gidan. Ga uwa-uba mijin ya fi son kishiyar a kanta. Kamar yadda ka taimake ni da sauran yarana,ina so ka sake taimakona a wannan karon,domin ina jin Sahura sosai a raina. Ka bata mallaka'' Siririyar dariyar irin ta yara ya shiga ƙyaƙyatawa yana dubanta,sai can ya gimtse tare da ɗaure fuska. A bazata ta ji ya fara magana cikin muryar nan ta sa mai amo kamar ana dukan garwa. ''Ataka gidan yarinyarki akwai matsala! Ataka kishiyar kadai za ta iya mallakewa a yanzu! Ataka mijinta na da wuyar mallaka! Ataka saboda yana riƙe da addininsa!" Zaro ido Gwaggwon Bugaje ta yi waje jin uban gayyar ba zai mallaku ba,an yi ba a yi ba kenan, ai gwara mijin ya mallaku a kan a mallake kishiyar. Cike da damuwa Gwaggwon Bugaje ta ce ''Yanzu boka Ataka babu yadda za a yi a mallake mijinta?" Siriyar dariyar ya yi,wannan karon bai jima ba ya tsagaita sannan ya ce ''Ataka akwai wuya! Ataka amma zamu taka zuwa shekara huɗu mu gani ko zamu samu dama! Ataka ba sai kin dawo ba! Ataka ita da kanta za ta ga ya fara bin maganarta! Ataka daga nan ta mallake shi! Ataka amma mallakarsa bazata jima a jikinsa ba! Ataka kin amince?!" Da sauri Gwaggwon Bugaje ta ce ''Eh Boka Ataka na yarda na amince" Siriyar dariyar ya kuma yi,wannan karo ya jima yana siriyar dariyar daga bisani ya tsagaita tare da ɗaga hannunsa na hagu sama. 'yan surkulle ya yi wanda kamar walƙiya wata 'yar ƙaramar ƙwaryar ta bayyana a tafin hannunsa. Ƙarama ce sosai ƙwaryar baƙa da kwalliyar ratsin fari da ja kaɗan. Ɓacewa ƙwaryar ta yi,sai ta bayyana a gaban Gwaggwon Bugaje. A hankali ta ɗora idanunta saman ƙwaryar. Kunnuwanta suka tsinkayi Boka Ataka na faɗin ''Ataka ki kai mata! Ataka ta tabbata sai ta je gidan za ta yi amfani da ƙwaryar! Ataka idan ta koma gidan! Ataka a tsakiyar dare za ta wanke fuskarta da duka ruwan sai ta kira Ataka sau goma! Ataka washegari ta dafa abinci ta ɗiba da ƙwaryar ta juye a kwanon kishiyar! Ataka idan ta ci abinci shikenan za ta mallaketa! Ataka ta bar mallakar miji a hannumu! Ataka nan da shekara huɗu za mu mallake shi! Ataka amma mallakarsa bazata daɗe ba ɗuii! Ataka na sallameki! Ataka akwai sharaɗi!" Cike da jin daɗi Gwaggwon Bugaje ta ce ''Ina sauraronka boka Ataka'' Siriyar dariyar ya kuma yi wannan karon bai jima ba ya tsagaita sannan ya ce ''Ataka za ta samu matsala nan gaba! Ataka allon tsafina bai hasko mini inda matsalar take ba! Ataka kishiyarta za ta haifi haske mai yaye duhu! Ataka ban san me hasken yake nufi ba! Ataka allon tsafina ya nuna mini ɗiyarki za ta ji dadi na ɗan wani lokaci!Ataka amma ba zai dawwama ba! Ataka 'yarki za ta sha wuya a ƙarshe! Ataka hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh!" Ya ƙarashe maganar da sakin Siriyar dariya. Lokaci guda hasken mai ƙarfi ya ɗauke sai na wutar tukunyar kaɗai. ''Ataka na sallameki'' daga haka ya ɓace.A hankali Gwaggwon Bugaje ta miƙe tana

Chapter 5 of 33