Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
asuba idan ta cire Yaa Hamida da Yaa Yasir. Da safe ma idan suka tashi ba wanda take gani ya yi sallah. Ƙaramarsu ce wani lokacin takan ganta tana burbura sallarta. Dogon numfashi ta ja ta sauke a lokaci guda,wardrobe dinta ta bude ta cire brush da toothpaste ɗinta wanda Yaa Yasir ya siyan mata,gidan kowa da kwandon wankan da brush ɗinsa. Matsa toothpaste ɗin ta yi a saman brush ɗin sai ta miƙe. Hamida na fito daga bayin ta shiga,tsarki ta yi sannan ta wanke bakin ta ɗauro alwala ta fito. Ta iske Hamida na sallame da sallah,dogon hijabinta na islamiyyarsu ta Gusau ta saka,ta duba jakarta islamiyyarta da ke rataye a kusa da ɗan ƙaramin gadonta. Hisnul muslim ta cire ta ajiye a gefan daddumar,sai ta mayar da jakarta inda take. Kabbarta sallah ta yi,cike da natsuwa ta gabatar da raka'atul fijr ta sallame,ta sake mikewa ta kabbara sallar asuba. Bayan ta idar ta yi lazumi sannan ta ɗauki Hisnul muslim dinta wanda Ammuna ta bata shi kyauta ta fara karantawa,a nutse ta kammala azkhar ɗinta sannan ta fara muja'iar haddarta har safiya ta yi. ''God! What the fucking hell is this! Mutum yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ana damunshi da karatu! For what!. Abin da ba za mu dauka ba kenan a gidan nan!" Aunty Saudah ta faɗa a hasale tana zuwa inda HAFIZA take saman dadumar. Bata tanka mata ba kuma bata daina karatun ba, ran Aunty Saudah ya sake ɓaci ganin ta yi buris da ita. ''Ke dan uwarki ba da ke nake ba...!" ''A'a fa! Wannan ne kuma abin da ba zan ɗauka ba! Karki sake tsomo uwarmu a cikin zancenki! HAFIZAN da ta miki laifin ki tsaya a kanta amma ban da uwarmu'' abin da Hamida ta faɗa kenan tana ajiye kayan da take linkewa a gefe. Sheƙeƙe Aunty Saudah ta tsaya tana kallonta,haka ma su Amina da ke shirin makaranta cak suka tsaya suna mata kallon mamaki. Yaushe Hamida ta yi baki da har za ta mayar da magana. Ita da ko autarsu Maryam ta saka aiki babu musu take yinsa,amma yau take mayar ma babban yayarsu magana cikin ido. ''Eh lallai Hamida! Wuyanki ya isa yanka! When did your dirty mouth start to throw back words on me! Ni sa'arki ce'' Aunty Saudah ta furta rai a ɓace. Taɓe baki Hamida ta yi bata amsa mata ba,linke kayan ta ci gaba da yi abinta. HAFIZA ma karatunta take sosai ba tare da ta ji tsoron tsayen da Aunty Saudah ta yi a kanta ba. Kallon mamaki Aunty Saudah take bin Hamida. ''Aunty Saudah ki kyaleta! Don ta ga Auntynta ta duki mama ne shi ya sa ta yi baki yanzu! ga Baba ya dawo ji da su'' cewar Amina tana shigewa bayin wanka. ''Fine! Wannan ya zama kashedin karshe da zan miki! Idan kika sake shiga gonata i will teach a great lesson!" Tana fada tana nunata da ɗan yatsa. ''Na dai faɗa karki sake tsomo uwarmu da ke kwance cikin kabari a maganarki idan har kin son zaman lafiya a gidan nan'' Tsaki Aunty Saudah ta ja tana yin ƙwafa ta koma saman gado. Wayarta ta ɗauka ta shiga Whatsapp duba saƙonnin da aka turo mata. Kwata-kwata bata da walwala, maganar Hamida ta kwashe rabin farincikinta da ta farka da shi yau. HAFIZA na kammala muraji'arta ta ɗauki Hisnul muslim dinta ta mayar cikin jaka,ta ɗauke daddumar ta ajiye a saman wardrobe ɗinta. Kakkaɓe gadon ta yi ta gyara. A can Falon, Ɗayyaba, Gwaggwon Bugaje da Sahura suke zaune a falon suna jajanta abin da ya faru da ita. Ɗayyaba ta shiga ruɗu a safiyar yau da ta fito ɗora abin kari kamar koyaushe. Ba su yi maganar da Sahura ba a kan zuwan Gwaggwon Bugaje ba,sai dai ta gantaa kamar a mafarki idonta ɗaya a rufe da bangeji tana bacci. Take zuciyarta ta halba tana ƙarasowa inda take tana sake duba fuskar Gwaggwonta. Sunanta da ta ambata ya farkar da Gwaggwon Bugaje daga bacci mai daɗin da take,daidai Sahura ta fito daga ɗakinsu Amina tashinsu shirin makaranta. Zama Sahura ta yi kusa da Gwaggwon Bugaje haka ma Ɗayyaba suna kallon fuskarta. Babu abin da ta rage na daga abin da ya faru da ita a hamadar boka Ataka,sun jimanta sosai musamman Ɗayyaba da abin da taɓa zuciyarta sosai. A raunace ta wuce kicin ɗora abin kari kar yaran su makara. Ɗan muskutawa Sahura ta yi tana sake duban fuskar Gwaggwon Bugaje ''Gwaggwo da wuri da mu je asibitin kar mu tarar da layi'' ''To! Asibitin akwai tsada?" Ta tambaya. ''Eh. Da tsada gaskiya. Cikin kuɗin da nake ajiyewa na hidimar bikin Aunty Saudah idan ya ta so zan ciri wani abu a yi miki maganin! Lafiya ta fi komai'' Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana jinjina tausayi irin na ɗiyarta. ''Karki damu Uwata! Mene ne amfanin su Bashiru da Hayatu. Yanzu nan zan ɗaga waya na kirasu. Ki adana kuɗinki da kyau saboda fita kunya'' ''To Gwaggwo'' Sahura ta furta tana jin sanyi a ranta. Miƙa ma Sahura wayar ta yi don ta kira mata su. Sahura bayan ta amsa ta nemo lambar Hayatu,har ta tsinke bai ɗauki kiran ba,ba tare da gajiya ba ta sake kiransa a nan ba bai ɗaga ba,sai da ta jera kira kusan shida babu wanda ya ɗauka sai ta haƙura. Lambar Bashiru ta kira,wayar ta shi ma a kashe take. Fuskarta ɗauke da damuwa ta kalli Gwaggwon Bugaje ta ce ''Gwaggwo babu wanda na samu a layin,ɗaya bata shiga,ɗayan kiran bai ɗauka ba'' ''Too! Yanzu ya za mu yi kenan? Gaskiya bana son ki taɓa kuɗin ajiyar biki'' ''Bari na kira Baban Hamid na ji ko zai taimaka mana da wani abu,jiya na yi yana waya da wani soja yana masa godiyar ya ga abun alkhairi,sai dai bai faɗa mini abin ya samu ba'' ta faɗa tana ɗaukar wayarta daga hannun kujera. ''Allah ya sa a dace'' ''Ameen Gwaggwo'' ta faɗa tana kara wayar a kunnunta. A bugu biyu ya ɗauki kiran yana mata sallama. ''Wa Alaikumussalam! Barkha safiya'' A can Dauda Imamu ya ce ''Barkha dai'' Tattaro da natsuwarta ta yi tana gyara zama ta ce ''Daman Gwaggwo ce nake son na kai asibiti idan mun karya,shi ne na ce zan samu wani abu a hannunta na haɗa da nawa'' A can Dauda Imamu ya yi ɗan jim,har ta cire rai da amsarsa ta ji ya ce ''A gaskiya kuɗin da ke hannunta na amfanin yau ne,domin ina son na kai HAFIZA boko kar a yi mata nisa a karatu. Ba Kawu Kabir yana nan ba,ta kira ta ji ko za ta samu kuɗi a hannunsa. Na san ma za ta samun in shaa Allah '' ''To'' ta faɗa tana katse kiran. Malolon baƙin ciki ta haɗiye tana bin wayar da kallo. Dauda Imamu ya gama raina mata hankali,yanzu saboda 'yar iskar yarinyar nan ne zai ƙi taimaka mata ta kai uwarta asibiti. An ya za ta iya ci gaba da shan ruwan takaici daga wurinsa a kan HAFIZA kuwa! Yaushe kambun ikonta zai dawo hannunta? Dole ta miƙe don zama bai ganta ba!.... ''Uwata lafiya na ga kina bin wayarki da kallo? Ko bai da kuɗi ne?" Ta faɗa tana katse mata tunani. ''Ko ɗaya Gwaggwo! Dole na miƙe tsaya na samar wa kaina mafita! Baban Hamid bai taɓa ɓata mini rai irin na yau ba'' Sahura ta yi maganar tana share ƙwallar takaici. ''Me ya ce miki Uwata?'' ta faɗa tana kallon Sahura. ''Ni Baban Hamid zai ma cin fuska! Na kawo mishi ƙoƙon barana amma ya watsar saboda shegiyar yarinyar mai zubin aljanun ruwa!" ''Ni fa ban fahimci inda zancenki ya dosa ba?" Gwaggwon Bugaje ta ce tana ɗan gyara zamanta. ''Gwaggwo cewa ya yi yana da kuɗin amma na amfanin yau ne zai kai HAFIZA makarantar boko kar a mata nisa a karatu! Don Allah ki ji wannan banzar maganar!" Taɓe baki Gwaggwon Bugaje ta yi zuciyarta na mata suya tamkar gyaɗa marau. ''Da sake kam! Na ga alama zaman wannan zabiyar yarinyar a cikinku ba alkhairi ba ne! Bari na samu sauƙi sosai,zan nemi wani bokan mu ji ko za a dace. Ƙarfen ƙafa za ta zamo muku daga ke har yaranki. Tun kan a je ko'ina ya fara nuna baki da daraja a wurin shi! Da sake kam!....'' Faɗa sosai Gwaggwon Bugaje take kamar ta ari baki,Sahura na tayata. Ran Gwaggwon Bugaje ya yi matuƙar sosuwa,miƙa ma Sahura wayar ta sake yido ta kira mata mijinta wato mahaifin Sahura. Amsar wayar ta yi ta kira shi, a bugun karfo ya ɗauki kiran. Ba tare dogon magana ba ta ce ya san yanda zai yi ya turo mata dubu hamsin kafin azahar,bata jira amsar ba ta katse kiran. Babu wanda ya san abin da ya faru da Gwaggwon Bugaje har shi mijin nata bata damu da ko bashi ne ya ɗauka ba burinta ya turo. Ta ajiye wayar a gefenta kenan za ta yi magana HAFIZA ta fito daga ɗakinsu za ta je kitchen ɗaukar tsintsiya. Kamar kurayen da suka ga abin farautarsu, kallon tsana suke binta da shi. A tsawace Gwaggwon Bugaje ta ce...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050959771 [1/1, 1:11 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_042_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ Kamar kurayen da suka ga abin farautarsu, kallon tsana suke binta da shi. A tsawace Gwaggwon Bugaje ta ce ''Dan gemun ubanki da gashin hammatar uwarki kafin ta rasu ki zo nan!'' Dummmmm! Ƙirjin HAFIZA ya buga da ƙarfi,tun da ta zo duniya bata taɓa jin irin zagin nan ba sai a bakin tsohuwar nan,abin da yafi raunata zuciyarta,Ammunta da ta zaga tana kwance cikin ƙabarinta. Take ta runtse ido hawaye na gangarowa saman kuncinta. ''Ba dake nake ba annamimiya!" Gwaggwon Bugaje ta sake faɗa a tsawace,zabura HAFIZA ta yi tana ƙarasowa inda suke da sauri. A gabansu ta tsaya idanunta na kallon ƙasa. Kallonta suke cike da tsana musamman Gwaggwon Bugaje da take ganin ita ce silar tsiyayewan idonta ɗaya. ''Me kika taka dan gashin hammatar ubanki! Na ce me kika taka da kika zamar mana ƙarfen ƙafa ni da ɗiyarta!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana zare mata ido dayanta. (My Esteem fans kun ji ƙarfin halin Gwaggwon Bugaje mai ido ɗaya😂 duk ta bi ta rikita HAFIZARMU fisabilillah! Da alama har yanzu bata saduda ba😂 amma duniya ce! Za ta koya mata babban darasi. Mu je Maha!🚶🚶🚶😂) Sosai kalaman Gwaggwon Bugaje suka daki zuciyar HAFIZA duk da ƙarancin shekarunta,ita kuwa me ta tare musu,mene ne haɗin biri da gada,me suke nufi da ita ne! Ba su ba ba yaran ba,duk wanda ya ɗebo kashi a kanta yake saukewa bata ji bata gani ba. ''Wai ba dai take ba yar ƙalbu uba! Mayya mai zubin aljanun ruwa'' Bakin HAFIZA na rawa ta ɗan ɗago ta dubesu,zuciyarta ta karanto addu'ar neman tsari daga garesu ta ce ''Ku yi haƙuri...'' daga haka ta rushe da matsanancin kuka. Ba wai tsoronsu take ji ba,ba wai bata da bakin ramawa ba ne,sai dai ba haka Ammunta ta bata tarbiyya ba. A kullum cikin ce mata take _Komi babba zai fada miki,duk rashin daɗinsa da dacewarsa ki ba shi hakuri ko da kuwa ke kike da gaskiya. Ba a samun yaron kirki da mayar da magana ga wanda ya girme shi ko ya haife shi,ki zama mai haƙuri akodayaushe, kin ga mai hakuri HAFIZATA,shi kaɗai ne a faɗin duniyar nan yake iya dafa dutse ya sha romansa hankali kwance,komai aka miki kar ki rama HAFIZA,ki bar wa Allah sakayya ki ga yadda Ubangiji zai yi ikonsa. Allah ya miki albarka ke da 'yan'uwanki Autata_ wannan ce nahisar da Mairi ta mata ana sauran sati uku ta bar duniya. Magana mara daɗi Gwaggwon Bugaje da Sahura suka shiga antaya mata babu kaƙƙautawa,Mairi kuwa ta sha zagi a wurinsu duk don su baƙanta ranta,kamar kuwa sun sani,ranta ya sosu da kalamansu a kan Ammunta. Ana haka Dauda Imamu ya shigo falon da sallama a bakinsa. Kamar haɗin baki kowannansu ya yi gum da bakinsa, kasancewar kujerar da suke zaune tana fuskantar kofar, HAFIZA ta juya ma ƙofar baya. Sahura bata yi tunanin dawowarsa yanzu ba,don sai tara ta gitta yake dawowa gidan. Dukkaninsu sun sha jinin jikinsu. Cike da barikanci Sahura ta miƙe zuwa wurin HAFIZA tana sauya yanayinta zuwa na damuwa ''Ayya HAFIZATA kin ga gababanki nan ya zo a daidai sai ya kai ki asibiti a dubaki?" ''Subhanallah bata jin daɗi ne? '' ya yi maganar yana ƙarasowa inda suke. Dubanta ya yi hankalinsa a tashe ya ce ''HAFIZATA baki da lafiya ne?" Shiru HAFIZA ta yi tana kallon su Sahura, Gwaggwon Bugaje sai ƙyafta mata ido take alama ta ce ''Eh'' Tuno da zagin da suka ma Ammunta da ita karan kanta ta ce ''Abba lafiyata lau! Na fito zan je kicin na ɗauki tsitsiya suka tsareni. Kaka sai ce mini take me na taka da zan zamo musu ƙarfen ƙafa. Abba sai zagin Ammuna suke tana kwance cikin ƙabari...'' kuka mai sauti ta saki wanda yafi na farkon,don kalamansu sun yi matuƙar ƙuntata ran HAFIZA. Ran Dauda Imamu ya yi matukar ɓaci da abin da HAFIZA ta faɗa, musamman zagin da ta ce sun yi ma matarsa abar ƙaunarsa. Kafin ya ce wani abu zurum! Sahura ta ce ''Kai amma an yi maƙaryaciyar yarinya! Yaushe Gwaggwo ta zagi Mairi! Ce nake ke da kanki ki zo wurinmu kina faɗa mana da zazzaɓi kika kwana'' Cikin kuka HAFIZA ta ce ''Ni ban ce muku ba! Lafiyata lau" Murmushin takaici Dauda Imamu ya yi yana binsu da kallon mamaki. ''Na san za ku aikata abin da ya fi wannan ma!...'' ''Kai Dauda! Ka ji tsoron Allah wace riba zan samu idan na ƙuntata ma marainiyar Allah!" Dariya maganarta ta ba shi da takaici a lokaci ɗaya. ''Riba kuwa mai tsoka Gwaggwo! Tun ba yau ba na fahimce ki da Sahura kun tsanar da kuke maHAFIZA. Idan kin manta bari na tuna miki,a lokacin da kuke asibiti wani irin suna ne baki kira HAFIZA ba san da na je tare da ita,har ce mata kika yi zabiya! Ko kin zaci na manta ne!'' Girgiza kai Gwaggwon Bugaje ta shiga yi tana matsar ƙwallar ƙarya. ''Ka ba ni mamaki Dauda! Ina matsayin matar kawunka kuma sirikarka kake faɗan wannan muggan kalaman masu susan rai! Amma babu komai ba laifinka ba ne! Laifina ne da na zo gidanka!" ''Ke dai kika juya maganar zuwa wata sigar da ta ƙona miki rai!" Ya fada yana goge ma HAFIZA hawayen da suka wanke fuskarta. Duka yaran gidan sun fito falon suna kallon abin da ke faruwa,Ɗayyaba da ke kicin ita ma ta leƙo tana kallonsu. Sosai ranta ya sosu da abin da mijin yayarta ya ma mahaifiyarta,take tsanar HAFIZA ta sake linkuwa a cikin zuciyarta. Tabbas sai ta koya mata hankali. Yaran ma ransu ya yi mugun ɓaci da abin da HAFIZA ta saka babansu ya ma mamansu da kakarsu. Ƙowanne ya ƙullacceta a rai idan ka cire Maryam, Hamida ji take kamar an tsomata cikin aljanna,yau dai Abbanta ya rama mata cin kashin da Gwaggwon Bugaje take mata a duk zuwanta gidan. Jalil da zuwansa kenan ya riski fadan da ake,daɗi sosai ya ji a ransa,dole yau ya kira Ammu Jamila ya fada mata daddaɗan labari,Abbansu dai ya dawo cikin hayyacinsa. Cike da ɓacin rai Sahura ta dubi Dauda Imamu ta ce ''A gaskiya ka ba ni mamaki baban Hamid! Ban yi zaton....'' kasa karasa maganar ta yi saboda mummunan kallon da ya wurga mata mai haɗe da kashedin ta ja bakinta,aikuwa gum ta yi. Bai ce komai ba ya ja hannun HAFIZA, ya zo wucewa ya kalli yaran,ai kafin ya ce wani abu kowanne ya kama gabansa,zuwa yanzu mugun shakkarsa suke. Waɗanda suka shirya suka fito karyawa,sauran suka koma ɗaki. Daman Halima da Maryam ce ba su gama saka kaya ba. Aunty Saudah ma ta fito falon. Zaunar da ita ya yi a saman gadon, shi ma ya zauna kusa da ita. Ta dukar da kanta ƙasa tana ajiyar zuciya akai-akai. ''Uwata!" Ya kira sunanta da murya mai tsananin taushi. ''Na'am Abba'' Ajiyar zuciya ya sauki mai ƙarfi,mai damu da wanzuwansu Halima a ɗakin ba ya fara magana ''Ki yi haƙuri kin yi HAFIZA. Duk abin da aka miki wanda kika ji ranki ba zai ɗauka ba ki sanar mini. Kin ji'' ''Tom Abba in shaa Allah '' Murmushi ya yi ya ɗan shafa kanta ya ce ''Yanzu ki je ki yi wanka ki shirya,an jima zan kai ki bokonsa Nu'aymah'' ''To Abba'' ta faɗa cike da murna wanda ya kasa ɓoyuwa a kyakkyawar fuskarta. Murmushi ya yi ya miƙe tare da barin ɗakin zuwa ɗakinsu. A falo bayan fitar Dauda Imamu Gwaggwon Bugaje ta rushe da kuka ita ta fasa zuwa asibitin yau za ta koma Sakkwato. Sahura,Ɗayyaba da yaran suka shiga lallashinta. Jalil ya yi kane-kane a one sitter yana latsa wayarsa, lokaci bayan lokaci yana kallonsu yana murmushi. Daɗi sosai yake ji a ranta,tun kan aje ko'ina Ubangiji ya fara saka musu zalincin da aka musu. Hamida mayar ta hankalinta ta yi ta kammala shan kunun za ta wuce Jalil ya ciro ɗari biyu ya bata kuɗin break,ta masa godiya ta bar flat ɗin. Yasir bai san wainar da ake toyawa a gidan ba,daga sallar asuba ya wuce wurin aikinsa na pop da yake yi tare da abokansa a wajen barikin,da kayansa a jaka ya tafi masallacin shi ya sa bai dawo gidan ba. Duk kuɗin da ya samu yana tara su a account ɗinsa saboda makaranta,yana rage ma haifinsa ɗawainiya musamman na kuɗin mota tun da ba shi kaɗai ba ne a gidan. Ɗa ƙyar suka shawo kanta har ta tsagaita kukan, amma ta ce zuwa gobe za ta goma Sakkwato tun da gori ake mata. (A ji tsoron Allah Gwaggwon Bugaje 😂 yaushe aka miki gorin gida 😂) Lallaɓata Sahura ta yi ta wuce ɗakinsu Aunty Saudah ta yi wanka,ta sirka mata ruwan wanka ta kai mata bayi lokacin HAFIZA ta fi daga wanka sannan ta dawo falon ta zauna,sai a sannan su Amina suka samu damar kammala karin. Sahura ta basu kuɗin kashewa suka bar flat ɗin. Ya rage daga Jalil,Sahura, Ɗayyaba da Aunty Saudah a falon. Bini-bini Sahura na aikama Jalil muguwar harara,yana hankalce da ita sai dai ya yi murmushi. Duk wannan dambarwar da ake a gidan Hamid bai sani ba,yana cikin ɗaki yana baccin asarar da ya saba. Ɗaki Ɗayyaba ta wuce ganin Dauda Imamu ya fito. Kusa da Sahura ya zauna. Sahura ta dubi Aunty Saudah ta ce ''Aunty Saudah je ki haɗo ma babanku abin kari'' ''Ciwon hannu kike da ba za ki je ki haɗa mini da kanki ba?" Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. ''A'a!'' ta faɗa tana miƙewa da sauri ta wuce kicin. Bayan tafiyanta Jalil ya rissina ya gaida shi,cike da kulawa ya amsa. A gabansa ta ajiye sannan ta samu wuri ta zauna. A nutse ya fara cin abincin bayan ya yi bismillah. A can ɗakin yara koda Gwaggwon Bugaje ta shiga ta iske HAFIZA na wanka,ruwan da Hamida ta rage mata ta yi amfani da shi. Sai da ta jira ta fito sannan Sahura ta shiga da ruwan bayi sai Gwaggwon Bugaje ta shiga. Ko kallon inda HAFIZA take bata yi ba,dole idan ta koma gida su sake sabon shiri na musamman,bata ƙi HAFIZA ta halaka ba idan har ɗiyarta Sahura ta za ɗaukaka a gidan,ya zaman tana baza iko kamar da. Fitowar Gwaggwon Bugaje daidai da shigowar Ɗayyaba,sai da ta aikama HAFIZA mummunan kallon sannan ta samu wuri ta zauna. Hira suka shiga yi kamar ba su san da wanzuwanta a ɗakin ba. Ko a jikin HAFIZA, alla-alla take ta kammala shiri ta fito ta sami Abbanta, ɗauki take za ta shiga sabuwar makaranta sabuwar rayuwa. A falo bayan Dauda Imamu ya kammala karya kumallo Aunty Saudah ta kai kayan kicin ta dawo. Zamanta keda wuya Dauda Imamu ya jefo mata tambaya. ''Saudah kika ce iyayen saurayinki suna son turowa ko?" ''Eh Baba'' ta faɗa da sanyin murya ''Kafin su turo,yau idan na fita zan yi bincike da kaina in shaa Allah '' ''To Abba'' ta furta tana jin sanyi a ranta,ta ƙosa ta auri Alhaji Shu'aibu shanawa,don kullum cikin kashe ruhinta da kalaman soyayya yake,tare da alƙawarin tarin farinciki da jin daɗi a rayuwar auransu. ''Ni ban ga amfanin binciken nan ba baban Hamid! Mutumin yana da kirki sosai da ibada ga girmama na gaba da shi,idan ya ganni har durkusawa yake ya gaida ni'' Sahura ta fada cike da tabbatarwa. Ɗan murmushi Dauda Imamu ya yi ''Sai kuma aka ce miki duk da kyawawan halayansa da ke bayyane ba za a binciki yadda yake mu'amala da mutane ba? Ba kwanakin baya mun yi maganar ba duk da na manta abubuwan da kika ce mini. Kin ga shi aure ba abun wasa ba ne,rayuwa ce ta dindindin da za a gina,dole ayi bincike me kyau tukunna'' ''A yi bincike lafiya'' ta faɗa a iya fatar bakinta,ta yi amanna duk sukan da zai kawo ba za tta amince ba,haka kurum tana kallon idan hutu da jin dadi yake ya mata buƙulu,bata manta kwanakin baya da yake cikin ƙasƙashin ikonta,yana kawo mata suka da nuna baya goyon bayan auran balle yanzu da yake jin kansa mai jan wuya ne,ko sama za su je su dawo tana nan a kan bakanta babu gudu babu ja da ya baya. Dauda Imamu ya buɗe baki da niyyar bata amsa Hamida ya fito daga ɗaki, bakinsa duk miyon bacci alamar yanzu ya tashi daga bacci. Yana haɗa ido da mahaifinsa hantar cikinta ta yi mugun kaɗawa,wannan shi ake kira da Ali ya ga Ali,domin bai manta abin da mahaifinsa ya ce jiya ba. Ya juya zai koma ɗaki ya ji muryarsa mai cike da gargaɗi ''Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya za ka sha mamakina'' Cak Hamid ya tsaya gabansa na faɗuwa,babu shiri ya t ƙaraso cikin falon daidai da fitowan HAFIZA sanye cikin kayan makarantarta na can,ta rataya ƙatuwar jakarta. Hankali Dauda Imamu sai ya rabu gida biyu,nuni ya mata da hannu alamar ta zo ta zauna sannan ya juya wurin Hamid fuskarsa matuƙar ɗaure tamkar bai san wata aba ita dariya ba. Madadin HAFIZA ta zauna,sai kawai ta ajiye jakarta ta nufi kicin ta haɗo abin kari ta dawo falon. Har ta dawo Dauda Imamu bai daina yi ma Hamid kallon ƙurilla yana nazartarsa ba. Ganin alamomin shaye-shaye sun fara bayyana a jikinsa sai ya ce ''Saboda kai raina ni,daga ganina za ka juya ko?" Da sauri Hamid ya girgiza kansa yana faɗin ''A'a baba brush me zan je ɗaukowa'' ''Mayar da ni brush mana! Ka ce mini jiya a gidan abokinsa ka kai dare ko?" Da sauri Hamid ya

Chapter 30 of 33