ganin jiri-jiri na shirin lulluɓe na mujiyarta. Zuciyarta cike da damuwa,jin wannan mummunan labarin da boka a Ataka ya sanar mata. Har ta fito kogon bata sani ba. Dusar ƙanƙarar tare da azababben sanyin wurin suka tabbatar mata da ta fito daga kogon. Cike da kasalar jiki da na ruhi ta fito daga yanki. Kasancewar akwai 'yan'uwan mahaifinta a ƙauyen Aouta, gida-gida ta bi suka gaisa sannan ta koma Bégajé. Kwananta biyar tana bin gidajen 'yan'uwanta ,a kwanata na shida ta dawo Sakkwato. Cikin dare ta dawo lokacin har Sahura ta yi bacci. Bata tayar da ita ba,ta ciro ƙaramar ƙwaryar da boka Ataka ya bata,ta yi mata kyakkyawan ɓoyo sannan ta bi lafiyar gado.
Washegari da safe, a bazata Sahura ta yi tozali da Gwaggwon Bugaje,cike da farinciki ta yi mata sannu da zuwa. Tsahara ta shigo kamar koyaushe ta ma Hamid wanka sannan ta taimaka ma Sahura ta yi wanka. Bayan ta saka kaya kunun kanwan da Tasallah ta aiko mata da shi ta sha. Cike ta zumuɗi ta tambayi mahaifiyarta ko an dace. Yalwataccen murmushi ta sakar mata,abin farincikin za ta sanar mata ban da na baƙin ciki da boka Ataka ya ce zai afkun mata. Ta yi imani kafin lokaci za ta samo mata wata maslaha tun da ba shi kaɗai ya iya sihiri ba. Akwai waɗanda suka fi shi...
''Gwaggwo kin yi shiru. Ko dai ba a dace ba ne?" Sahura ta faɗa a sanyaye.
''Ko kusa Uwata. An dace. Sai dai naki ba irin na sauran 'yan'uwanki ba ne. Boka Ataka ya ce za ki mallake kishiyarki yanzu amma mijinki sai nan da shekara huɗu, saboda mai riƙo da addini akwaii wuyar mallaka. Kin san mijinki ya fi Malam nutso a kogin ilimin addini.''
Shiru Sahura ta yi tana kallon mahaifiyarta,idanuwanta har sun fara tara ruwa. Wannan ai saci-faɗi ne, an sare kan maciji ba a birne kansa ba. Ita da take da burin mallakar Dauda Imamu me za ta yi da kishiyarta. Yoo ko ta mallaketa hakan ba zai hana fitowa fili ya nuna yafi ƙaunarta sama da ita ba. Cike da raunin murya Sahura ta ce
''Gwaggwo ta ya zan mallake kishiyata alhalin shi uban gayyan ban mallakesa ba. Ban rabu da bukar ba zan haifi habu, Soyayyar da yake nuna mata a fili ba zai bari ba,hakan na nufin ban rabu da ɓacin rai ba''
Sauke tagwayen ajiyar zuciya Gwaggwon Bugaje ta yi tare da gyara zama ta ce
''Wannan duk mai sauƙi ne Uwata. Cikin kaso ɗari saura hamsin,kin ga kuwa ai munci ƙarfin aiki. Sannan ba wai bazaki mallaki mijinta ba ne fa. Sai nan da shekara huɗu boka ya ce. Da guntun gatarinka ai yafi sari ka ba ni. Ki juyata son ranki,idan mijinki ya ce da ita zai je Kadunan ki hanata,sannan ki umurci ta ce lallai-lallai da ke zai yi tafiyar. Haba Uwata kamar ba mace ba. Ina kisisina da makircin da na sanki da shi tun kina budurwa? Ta ya saboda ɗan ƙaramin abu ki tayar da hankalinki''
''Haka ne kuma Gwaggwo. Sai yanzu na fahimci abin da kika haska mini. Yo ai Mairi ce za ta zama makamina. Ina matuƙar godiya Gwaggwo. Samun uwa kamarki a duniyar nan da matuƙar wahala. Cikin dubu da ƙyar za a iya samun biyu.''
Sosai kalaman Sahura suka faranta ran Gwaggwon Bugaje . Babu abin da a duniya yake sakata farinciki irin ta ga yaranta suna annashuwa.
''Idan kin ta shi komawa Zamfara zan ɗauko miki ƙwaryar,sai na faɗa miki yadda boka ya ce ki yi amfani da ruwan ciki da ƙwaryar bakiɗaya''
''To gwaggwo.''
Wani sabon shafin hira suka buɗe. Cike da shauƙi suke hirar har da dariya, Hamid na kwance a saman gafon runfa ya yi bacci...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Tudun Wada premier road, Gusau. Zamfara state Nijeriya*
A ɓangaren su Mairi cikin satin Dauda Imamu ya yi tafiya zuwa Kaduna. Sai da ya tabbatar ya bar musu komai da suke buƙata sannan ya bar gidan. Kafin ya tafi ya kai Yasir islamiyyar da yake koyarwa,daga baya idan ya ƙara wayau sai a saka shi boko. Da sassafe take kai shi makarantar zuwa goma idan an tashe su sai ta ɗaukoshi daga can ta wuce islamiyarsu ta matan aure da shi,zuwa sha biyu su dawo gida. Yau ta kama Alhamis ranar hutu, Mairi na zaune tare da yaranta a tsakar gida,tana duba arba'una hadith wanda aka koya musu jiya. Yasir da Jalil sun duƙufa wasa da mota. Kwatsam suka jiyo sallamar 'yar ƙuda tare da yaranta. Ba ita ba,ba yaran ba kamar an tsamo su daga kwata, da alamu kayan ya jima a jikinsu musamman yaran. Hancinsu kamar hancin kare tsabar yadda majina ke yoyo. Cike da fara'a ta iso inda Mairi take zaune da yaranta. Samun wuri ta zauna tare da faɗin
''Bisimillahi Allah! Ina kwana Maman Yasir''
''Lafiya lau 'yar ƙuda,ya yara''
''Lafiya lau suke wallahi'' ta amsa tana rarrraba ido a tsakar gidan ko za ta ga gilmawan Sahura. Don kwana biyu ta rabu da jin ɗuriyarta. Mairi bata sake bin takanta ba,littafin da ke hannunta ta ci gaba da dubawa. Ganin idan ba ita ta fara mata magana ba ko za su kwana a haka bazata ce mai ka ci shara bakinka ba. Domin Mairi ba mai yawan surutu bace da hayaniya,shi ya sa ta su bata zo ɗaya ba tun a farko. Gyara zama 'yar ƙuda ta yi sannan ta ce
''Ni kuwa Maman Yasiri. Ina kishiyarki ta je ne. Na rabu ta sakata a ido''
Murmushi Mairi ta yi,zuciyarta na raya mata gulma ce ta kawota ba komai ba. Shi ya sa mijinta ya yi matuƙar birgeta da ya hanasu shiga biki ko suna. Ta ga amfanin hakan yanzu, ƙarya ne a yi biki ko suna a unguwar gagarumin faɗa bai kaure a gidan ba, idan aka bi salsala gulma da tsaigumi ne suka janyo hakan. Ajiye littafin ta yi gefe sannan ta dubi 'yar ƙuda ta ce
''Maman Hamid na Sakkwato wankan jego''
Waro ido waje 'yar ƙuda ta yi tsabar mamakin da ya dirar mata
''Wankan jego Sakkwato!" Ta maimaita.
''Eh 'yar ƙuda. Faɗi ki ƙara'' cewar Mairi.
Taɓe baki 'yar ƙuda ta yi sai ta ce
''Biri ya yi kama da mutum. Wato sai da ta gama haɗa miki kitimurmuya a unguwa,matan unguwa sun ɗauka sannan ta tsare ta bar garin.Eh Lallai Sahura ta iya barikanci. Kin san Allah babu gidan da bata je a unguwar nan ta faɗi aibunki ba. Har gidana sai da ta zo ta ce mini wai mijinku ba...''
''Dakata 'yar ƙuda! Bana buƙatar wannan maganar! Jeki kawai na gode da ziyarar. Allah ya ba da lada!'' Mairi ta faɗa a hasale,tare da ɗaukar littafinta ta ci gaba da dubawa. Wani irin mugun kallo 'yar ƙuda ta watsa mata ba tare da ta sani ba,a ranta tana faɗin 'Banziya! Wawiya!Wacca bata waye ba! Shi ya sa Sahura take birgeni' a zahiri kuma ta miƙe tare da faɗin
''To ai shikenan! Ni dai Allah ya ga zuciyata. Bana son a cutar da ke saboda zumuncin da ke tsakaninmu. Amma tun da kin ce kar na sake miki maganar, to bakina alaikum. Ni kin ga tafiyata'' ta ja hannun yaranta fuuuu! Kamar za ta tashi sama ta bar gidan. A fili Mairi ta furta
''A sauka lafiya. Haka kurum muna zaman lafiya za ki shigo don ki wargaza zamantakewarmu,to ta Allah ba taki ba. In shaa Allah kamar yadda nake zaune ƙalau da Sahura, haka zai ɗore har tsufanmu in da rai da lafiya. Mtsss'' ta ci gaba da duba littafinta. Da ta gaji da zaman wajen ta nannaɗe tabarmar suka koma ciki. Mairi mace ce mai matukar haƙuri da ladabi,shi ya sa Dauda Imamu yake alfahari da samunta a matsayin uwar yaransa. Duk inda ya ajiyeta nan take tsayawa,ba faɗa balle jayayya. Tun auransu zuwa yanzu wani saɓani mai girma bai taɓa gittawa a tsakaninsu ba. Ba Mairi ba Dauda Imamu ba,kowannansu daidai gwargwado yana kyautata wa ɗan'uwansa. Babu inda take zuwa idan ta dawo daga makaranta,cefane ma kawo mata ake daga kasuwa. Duk abin da take buƙata na rayuwar yau da kullum akwai shi a gidan. A makaranta bata yarda ta bankaɗa sirrinta kamar yadda wasu matan suke ba. Suna bayyana abubuwan da mazajensu suke musu na alkhairi,a tunaninsu sun fi kowace mace sa'ar miji,a baɗini ba su san hanya suke buɗe wa maƙiya damar yin gwaggwaɓar nasara a kansu ba. Mairi ta ci gaba da ba yaranta kula da ita kanta, daga makaranta sai gida,a gida bata ba wata 'yar unguwa fuskar shigo mata gida har ta kawo gulmar wata ba. Wannan kenan...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Garkar Bala fari mai fata,Ƙofar kaɗe. Sakkwato. Nijeriya*
A ɓangaren Sahura wankan jego take sosai,wanka irin na mutan da Gwaggwon Bugaje ta koma yi ma, maganin sanyi ya zama tamkar ruwan shanta. Ga kulawa ta musamman da take bata da Hamid. Cikin ƙankanin lokaci Sahura ta murje,ta ƙara ƙiba,haskenta ya sake bayyana kamar ka latsa fatarta jini ya fito. Hamid ya ƙara girma ka ce ɗan wata shida ne. 'Yan'uwanta na kawo mata ziyara da sake bata sabon darasin zama da kishiya wanda bata san da shi ba,ga wanda Gwaggwon Bugaje take bata na musamman. Ta ƙara samun ilimin kisisina,makirci,bita da ƙulli waɗanda za su taimaka mata samun gindin wurin mijin,tun da bazata samu damar mallakar Dauda Imamu yanzu ba. Tafiya ta yi tafiya,tun ana ƙirga kwanakin da suka rage Sahura ta kammala wankan jego har ranar ta zo. Galleliyar atampa super Gwaggwon ta sa a ɗinka mata ta saka. Gidajen 'yan'uwa da abokan arziki ta je yawan arba'in. Daga karshe da yada zango a gidan innarta,da yake mai kuɗi take aura,sai da ta shafe kwanar biyar can yana narkar daɗii sannan ta dawo gidan ta fara shirin komawa Zamfara. A daren ranar da za ta koma Gwaggwon Bugaje ta ɗauko ƙwaryar da boka Ataka ta miƙa mata tare da cewa
''Ki kula sosai Uwata da ƙwaryar nan har ku isa Zamfara. A tsakiyar dare za ki wanke fuskarki da duka ruwan da ke cikin ƙwaryar nan,sannan ki kira Ataka sau goma. Washegari da kuma ki dafa abinci sai ki zuba abincin da za ki bata a kwaryar,daga bisani sai ki mayar cikin kwanon da za ki bata. Idan ta ci abinci shikenan kuma,sai abin da kika ce za ta yi. Fatan kin fahimta''
''Na fahimta sosai da bayananki,zan yi yadda kika ce.''
Murmushi Gwaggwon Bugaje ta sakar mata tare da miƙewa da ɗauke wata 'yar ƙaramar jaka ta buɗe cikinta. Hannu ta sa da ciro kayan da ke ciki. Ƙullin magani kala-kala,gumba,turare mai ɗauke da wasu itace ciki,sai zuma da wasu tarkacen kayan mata. Ɗaya bayan ɗaya take mata bayanin yadda za ta yi amfani da su lokacin da mijin na ɗakinta da wanda idan baya ɗankinta za ta yi amfani da su. Jinjina mata kai ya yi alamar ta fahimta tana murmushin jin daɗi. A ranta tana faɗin wace uwa za ta ma 'yarta gata irin wannan. Galoli biyu ta ɗauke na tsumi da tabaje ta miƙa mata. Ta sanar mata yadda za ta yi amfani da su idan ta koma. Daga nan ta tayata shirya kayan a ƙatuwar ghana-must-go ta zage zip ɗin. Duk abubuwan da ta sani nata ta haɗe wuri guda saboda halin mantuwa sannan ta bi lafiyar gado,ranta fes! Kamar an yi mata bushara da gidan aljanna. Zuciyarta cike take da ƙudirin gallaza wa Mairi da yaranta. Kamar yadda mahaifiyarta take juya kishiyoyinta haka take fatan ta yi ma Mairi har ma nata ya fi na uwarta. Da wannan BAHAGON TUNANIN bacci ya lallaɓo ya sureta zuwa wata duniyar ba tare da ta farga ba...✍️
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_Narrnarhh Bukar_*
_(Lady with the Amazing pen ✍️)_
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_008_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
.......Zuciyarta cike take da ƙudirin gallaza wa Mairi da yaranta. Kamar yadda mahaifiyarta take juya kishiyoyinta haka take fatan ta yi wa Mairi har ma nata ya fi na uwarta. Da wannan BAHAGON TUNANIN bacci ya lallaɓo a hankali ya sureta zuwa wata duniyar ba tare da ta farga ba. Washegari da safe bayan ta yi wanka ta karya ta fara shiri. Mazan gidan suka taimaka da kayan zuwa waje, daman tun jiya Gwaggwon Bugaje ta daidaita da mai 'yar ƙumbula, kayan aka saka a ciki. Duka 'yan gidan suka fito har waje yi mata sallama ciki har da mahaifinta. A hankali ta hau 'yar ƙumbular zuciyarta fal tsoron kar ƙwaryar da ke cikin jakarta ta girgiza har ruwan su zube duk da a rufe take ruf!. A gabansu 'yar ƙumbular ta wuce sannan suka koma gida. Kai tsaye ya kaita tasha ta hau motar Gusau. Ta ɗan jima a motar saboda babu fashinjoji sosai,ɗaya bayan ɗaya fasinjojin ke zuwa har ta cika suka nosa hanya. Tafiya ta yi nisa,Hamid da ke baya ya fara mata kuka. A hankali ta ajiye jakar a gefanta,da yake ta ci sa'a akwai wani ɗan lungu a gefanta. Ta kwance goyon ta ciro Hamid,sai ta fara shayar da shi har ya yi bacci. Sun jima suna tafiya daga bisani suka sauka a Gusau. Drop na 'yar ƙumbula ta samu suka yi ciniki ya kaiya har gidan, lokacin ana kiran sallar azabar. Bayan ta sauka ta miƙa masa kuɗin tare da roƙonsa arziƙin ya shigar mata da kayan ciki bata da wanda zai taimaka ga kuma goyon. Babu musi ya sauko tare da tayata shigar da kayan cikin gidan. Mairi da ke alwala ta miƙe cike da farin ciki ta ce
''Maraba lale marhabin da zuwa Maman Hamid"
Murmushin yaƙe Sahura ta yi sannan ta ce
''Barkha da gida''
Da sauri Mairi ta kammala alwalar ta matso tare da tayata shiga da kayan falo. Za ta amshi jakar hannunta da sauri Sahura da girgiza mata kai da faɗin
''Haba kar ki damu wallahi. Ai kin yi ƙoƙari. Je ki yi sallarki kar lokaci ya wuce''
Murmushi Mairi ta yi sannan ta ce
''To bari na ƙarasa miki da sauran kayan cikin ɗakinki''
''Na kuwa gode Maman Yasir''
Ɗaya bayan ɗaya ta ɗauki kayan zuwan ɗakin Sahura ta ajiye. Ta koma kicin ta zubo mata abinci a plate da ruwa ta kawo mata ɗakin sannan ta wuce ɗakinta ta kabbarta sallah. Yasir da Jalil na saman gado suna shaƙar baccinsu. Bayan ta ciro ƙwaryar daga jakarta ta yi mata mugun ɓoyo sannan ta kwance goyon Hamid ta kwantar da shi saman gadon. Ba tare da tunanin Sallah ba ta ɗauki abinci ta fara ci. Tass ta cinye abincin ta sha ruwa. Gefe ta ajiiye plate ɗin tana yatsina fuska,jinta take ba wata shegiya kamar ta. Tun kan ta aiwatar da aikin boka har ta fara cika tana batsewa ita kaɗai. Abinka da mai gajiya bata jima ta kwanciya ba bacci ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta farka daga bacci ba sai kusan bayan Asr,shi ɗin ma Mairi ce ta zo ta tasheta saboda lokacin sallah ya wuce kuma babu kyau bacci bayan sallar Asr. A fuska bata nuna mata ta ji haushi ba,amma a ƙarshen zuciyarta tsinuwa da zagin ƙare dagin ne ta yi mata. Bayan Mairi ta fita ta ja uban tsaki tana harar ƙofar kamar ita ta yi mata laifin. Alla-alla take dare ya yi ta fara aiwatar da ƙudirinta. Da daddare a falo dukkaninsu suka ci abinci, daga nan kowa ya wuce ɗakinsa bacci. Hamid da ya tsiri kukan dare ya fara sana'arsa,da ƙyar ta samu ya kwanta,Mairi sai da ta shigo ta ji ko lafiya.
Kwance take amma idanuwanta biyu ta kafesu a agogon bangon da ke kallonta,ta ƙosa ƙarfe ɗaya na dare ya yi ta tashi. Sannu a hankali lokaci ya cika. A hankali ta mike ta nufi inda ta ɓoye ƙwaryar ta ɗauro. Murfin da aka rufe ƙwaryar da shi ta buɗe, bayanin da Gwaggwon Bugaje ta yi mata yana kai-kawo a kwanyar kanta. A hankali ta karkata kwaryar ta zuba ruwan wanda baki ne ga ɗoyin gaske,haka ta daure ta zuba a hannunta ta wanke fuskar,sai da ta tabbatar ta karar da ruwan kamar yadda mhaifiyarta ta ce sannan ta ambaci Ataka sau goma. Sake ɓoya kwaryar ta yi ta gyara wurin da ruwan ya ɗan zuba sannan kwanta. Murmushi ta sakarwa kanta tana lumshe ido lokaci guda. Tana gab da cim ma burinta,duk da ba duka burin za ta cim ma ba,amma ta san ta taka babban matsayi a hanyar ta cimma ƙudirinta gabakiɗaya. Gyara kwanciyarta ta yi tana fuskantar Hamid. A hankali ta fara lumshe ido tana buɗesu daga bisani ta rufe su ruf!.
Washe gari da safe bayan sun karya sai Sahura ta dubi Mairi ta ce
''Maman Yasir bari yau na rage miki aiki na ɗora girki''
'yar dariya Mari ta yi sannan ta ce
''Haba Maman Hamid. Duka-duka yaushe kika dawo da za ki ɗora girki ga ɗanyan goyo. Kar ki damu wallahi,ki bari sai nan da sati biyu haka sai ki fara girkin. Ƙila ma lokacin Baban Yasir ya dawo''
Murmushin yaƙe ta yi a ranta tana faɗin 'Kutumar ubancan kayyasa! Ai yau babu fashi sai na girka abinci a gidan nan kinci kamar yadda Gwaggwona ta sanar mini. Lallai ma' a zahiri ta ce
''Babu damuwa Wallahi. Na kwana biyu ban shiga kicin ba ne,sai nake ji na wata iri. Kin san a can gidan babu abin da nake daga ci sai shayarwa da bacci. Tun da nake gidan ban leka kicin ba. Yau dai ina da sha'awar shiga kicin, karki hanani Maman Yasir''
Wannan karon dariya sosai Mairi ta yi har hakan ya so ɓata ran Sahura,amma ta ɗaure ba tare da ta bari ta ga canji a fuskarta ba. Cikin dariyar Mairi ta ce
''To Maman Hamid. Na ga alamar tsohon tsiminki na aiki ne ya taso gadan-gadan. Tun da ke da kanki kike bukatar shiga kicin ɗin ban da matsala. Daman kwana biyu na yi kewar daddaɗan abincinki.''
Murmushin yaƙe Sahura ta sake saki domin tagane inda maganarta ta dosa. Watau dai ta mayar da ita jaka wacce bata gajiya da aiki. Har da iya ce mata tsuminta ne ya motsa. Lallai kuwa za ta ga tsumi. Yadda take daukarta jaka ita za ta koma jakar. Da Sahurar gwaggwan bugaje take zancen. A zahiri ta ce
''Kamar kuwa kin shiga ƙokon raina Maman Yasir. Bari ki gani da wuri zan girka abincin na huta'' ta yi maganar tana miƙewa lokaci guda ta fita. Kai tsaye ta wuce kicin ɗin ta ɗaura sanwar rana. Jollof na taliya ta girka,sai da ta fakaici idanun Mairi ta ɗauko kwaryar ta taho da ita kicin ɗin. Da ta kammala abincin sai ta zuba wanda za ta Mairi a ƙwaryar sannan ta juye a plate ɗin. Cike da taka-tsantsan take aikin,tana 'yan waige-waige kar Mairi ta shigo ba tare da ta ankara ba. Tsaf ta kammala komai lokacin a masallatai ana sallar, ta kai kular falo ta dawo ta kai mata plate ɗin abinci da cokali lokacin tana Sallah,sai ta dawo kicin ta ɗauki sauran abinci. Koda ta shiga falon ta tarar tana cin abincinta hankali kwance. Wani munafikin murmushi ta sakar wa kanta zuciyarta fari ƙal. Ɗakinta ta koma ta ɓoye ƙwaryar sannan ta ɗauki plate ɗin abincin ta soma ci cike da farinciki da annashuwa. Don ta tabbatar da aikin ya fara cin Mairi, tana a cikin ɗakin ta ƙwalla mata kira
''Mairiiii!" Kafin ta sauke numfashi Mairi ta amsa tana shigo ɗakin da gudu jikinta na tsuma. Tana zuwa ta zugunna tare da faɗin
''Gani Maman Hamid ''
Ƙasaitaccen murmushi Sahura ta sakar wa kanta tana jinjina kai lokaci guda. Mairi kanta a ƙasa, zuciyarta na halbawa,wani irin tsoron Sahura take ji a hankali yana bin jini da ɓargonta ba tare da tasan dalili ba.
''Wace magana na ji kuna tattaunawa ke da mijina ana gobe zan tafi Sakkwato?" Sahura ta tambaya fuskarta ɗaure tana tsareta da manyan idanunta. Da matuƙar ƙarfi zuciyar Mairi ta halba tana rintse idonta, furucinta tamkar mashi ne mai matukar tsini da ke caccakar zuciyarta tare da silasta bakinta bayar da amsar da bata shirya ba. Kokawa take da zuciyarta, tana son ta ƙarfi da yaji ta kice tsoron Sahura da ke shirin yi wa zuciyarta ɗaurin gwarmai amma hakan ya faskara.
''Da ke nake!" Sahura ta furta a tsawace tana zare mata ido. Su Yasir da shigowansu kenan sai da suka firgita. Da sauri Jalil ya rungume mamanta yana shigar da kanta cikin jikinta tsabar firgicin da ya saukar masa tamkar dirar mikiya. Wasu zafafan hawaye suka shiga rige-rigen sauka daga gurbin idanunta,ta rasa wace kalar musiba ce take shirin afkowa rayuwarta. Cike da sanyin murya ta ce
'' Mun tattauna ne a kan idan ya dawo daga Kaduna lokacin kin dawo wankan jego,zan je Mada wurin 'yar'uwata da sauran dangina na yi musu sallama,daga bisani sai ya wuce da ni Kaduna,ke kuma ya saka ki a...''
''A Islamiyyar garunku! Hhhhhhhhhh! Wato ke 'yar daɗi miji za ki bi shi Kaduna ku bar ni a Gusau ina tsotar tsamiya! Buɗe kunnuwanki!"
Da sauri Mairi ta yakice ɗankwalin kanta hannuwanta na rawa ta riƙe su. Yasir da Jalil sun taruke jikinta saboda yanayin da ba su ganinta a ciki ba.Murmushin mugunta Sahura ta saki sannan ta ce
''Daga yau har zuwa ranar da mijina zai dawo gidan nan ke za ki dinga aikin gida da renon ɗana. Kin ji ni ko! ''
Da sauro Mairi ta ce
''Eh Maman Hamid''
Gyara zama Sahura ta yi tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ta ce
''Sai magana ta biyu, idan mijina ya ce zai tafi da ke Kaduna kar ki amince. Ki ce masa kina son ya je da ni can. Sannan idan na tafi can kar watarana ya zo ya ce zai ɗaukeki ni na dawo ki amince. Kar ki kuskura ki yarda ko da kuwa za yi fushi da ke. Idan kuka kika tsallake maganata,ha ha ha za ki ɗanɗani kuɗarki. Ahir ɗinki na ji kin faɗa wa wani halin da kike ciki,daga ƙarshe na dakatar da ke zuwa islamiyya,koda kuwaun tafi Kaduna,ban amince ki je islamiyya ba,sannan idan sahibin zuciyata Yaya Imamu ya tambayi rashin zuwanki makaranta ki ce masa haka kike da ra'ayi yanzu.Kin ji niiiiiiiiiiii!"
''Na ji ki maman Hamid. Ban zan taɓa tsallake maganarki ba.''
''Gyara ɗankwalin sannan za ki iya tafiya''
Da sauri Mairi ta mayar da ɗankwalin tare da miƙe ta rike hannuwan su Yasir ta ja su a sauri suka bar ɗakin. Mairi na fita Sahura ta sheke da dariya har da tafawa tana faɗin
''Ho ni Sahurar gwaggwan bugaje 'yar ƙunan baƙin wake! Duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha! Kaɗan kika ga ni daga cikin nau'in baƙin cikin da na tanadarwa rayuwarki ke da 'ya'yanki. Sai na zama silar mutuwa Mairi. Kina gab da haɗiyar zuciya ki mutu da zarar na mallake Yaya Imamu. Zan shayar da ke da 'ya'yanta gubar mamakin da baku taɓa sha ba! ''
Kwanciya ta yi ta matso da Hamid ta ciro nono ta fara shayar da shi. Guguwar farinciki na sake mamaye farfajiyar zuciyarta. Tun da ta zo duniya bata taɓa tsintar kanta cikin farinciki kwatankwacin wannan ba. Ta yi dacen uwa mai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 33