faɗa mata gaskiya indai harkar abinci ce ko kwaɗayi. Tsam ta miƙe zuwa bayi ta wanko bakinta sannan ta fito falon, Nu'aymah na biye da ita tana kukan yunwa. Sauran yaran kuma suna falo sun kunna kallo.
''Aunty Saudah ɗan ɗauko Maryam a ɗaki ki zauna da ita kafin na gama muku abin karin''
''Mtssss! Haba mama muna kallonmu za ki zo ki isheni da aiki. Ni wallahi ba zan je ba!'' Aunty Saudah faɗa tana tsuke fuska.
''Yi haƙuri Auntyn yara. Abin kari zan haɗa muku. Ba zan daɗe ba zan amsheta'' ta yi maganar tana lallaɓata har ta miƙe zuwa ɗakin. Tana tafiya tana ƙuƙuni har ta je ɗakin ta ɗaukota.
Shayi ta fara ɗorawa,ya tafasa ta juye a flask,ta haɗa ma Nu'aymah nata ta yanka mata biredi sannan ta fasa ƙwai guba goma ta soya. Idan da da ne ƙwai huɗu zuwa biyar take soyawa,amma yanzu jinta take za ta iya soya duka kwai guda ashirin ta zauna lafiya.(Hmmmmm Sahurar gwaggwan bugaje a bi duniya dai a sannu😂. Ni da my Esteem fans muna baki shawara. Idan kuma kin ƙi ji to mu 'yan kallo ne,idan abin dariya ya sameki zamu dara 😂)
Tsaf ta kammala komai sannan ta fito da kayan karin falo,a daidai lokacin Dauda Imamu ya shigo gidan. Suna haɗa ido ƙirjinsa ya yi mugun bugawa. Kafin ya ari mayafin natsuwa sautin muryar da bai santa da ita ba ta antayo cikin na'urar sauraransa babu zato.
''Ka je ɗakin Hamid ka kwaso kayan fitsarinsa ka wanke yanzu!" Kafin ta sauke numfashi kamar wanda ake sarrafa shi da na'urar TV ya nufi ɗakin Hamid jikinsa na tsuma ya ɗauko kayan fitsarin zuwa harabar gidan,ya dawo ɗakin ya ɗauki bokita ya zuba ruwa sannan ya hau wankin kayan bil haƙƙi da gaskiya. Ɗaiɗaikun mutane na wucewa suna kallonsa cike da mamaki. Yau Babban Limamin masallacin Juma'a sunkutun guda ke dirzar kaya sai ka ce Gauro. Duk yadda ya so yaƙar zuciyarsa a kan bin umarnin Sahura ya gagara, jinsa yake idan bai gama wankin da ta saka shi a kan lokaci ba,zai iya mutuwa tsabar yadda zuciyarshi ke zafi tana azalzalansa. A ɓangaren Sahura murmushi yin nasara ta yi sannan ta zauna kusa da yaranta. Hamid da mamaki ya kusan nutsar da shi cikin ƙasa duk da ƙarancin shekarunsa ya dubi Sahura
''Mama kika saka Baba wankin kayan fitsarina? Kar fa ya dukan idan ya gama" ya yi maganar cike da tsoro wanda ke kwance mararan a fuskarsa. Murmushi Sahura ta yi tana zuba ma kowanne soyayyan ƙwan a ƙaramar roba ta ce
''Sha kuruminka Hamid babu abin da ya isa ya yi maka a yanzu. Saka ranta a sassanyen inuwa ka ji yarona'' Ba don ya gamsu da zantukanta ba ya ce ''To'' yana ɗaukar ƙwan.
''Kun dai wanke bakunanku da kuka tashi ko'' dukkaninsu suka furta ''Eh''
Bayi ta nufa ta cire ma Maryam nafkin ta tsaftaceta sannan ta fito falon ta soma karyawa. Suna tsaka da karyawan Dauda Imamu ya shigo ɗakin. Bata ko kallesa ta ce
''Zo ka karya''
Babu musu ya zauna ta hada masa abin karin sannan ta koma inda take ta ci gaba karyawa. Shi kuwa jinsa yake a takure. A haka ya kammala kari,duk yadda zuciyarsa ke son tambayar yaransa zuwa hadda kasancewar ɓangaren ba su je hutu ba ya kasa kamar an rufe masa baki. Haka ya haƙura da tambayar har suka kammala karin.
''Ka ɗaura ruwan wankan yara,idan ya yi zafi ka sirka kama Aunty Saudah da su Nu'aymah wanka ka shiryasu sannan ka kaima Hamid ruwan wankansa ba yi shi ma ya yi,sai ka fito masa da kayan sakawa,sannan ka gyara ɗaki da wankin bayi. Ni zan koma ɗaki na kwanta zuwa an jima ni da Maryam sai mu yi wankan. Idan ka gama komai za ka iya tafiya. Ka ji ni ko!"
''Eh! Eh! Sahur..."
''Daga rana irin ta yau karka sake kirana da Sahura. Sunan da za ka dinga kirani da shi _Ranki shi ɗade_ ''
Da sauri ya furta ''To ranki shi daɗe''
Taɓe baki ta yi sannan ta wuce ɗaki hannunta ɗauke da Maryam suka kwanta. Babu jimawa bacci a sake ɗaukarsu. Bawan Allah haka ya yi ta tiƙar aikin yana gumi abinka da ba a saba ba. Ya yi musu wanka ya shiryasu. Ya soma aikin gidan,Halima da Amina suka tayashi duk da ba wani abin a zo a gani suka iya ba,amma tausayin mahaifinsu ya cika zuciyarsu. Hamid da Aunty Saudah ko a kwalar rigarsu hasalima kallo suka ci gaba da yi. Nu'aymah kuma ta tasa sauran ƙwan da aka rage gaba tana ci...✍️
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_019_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
.........Taɓe baki ta yi sannan ta wuce ɗaki hannunta riƙe da Maryam suka kwanta. Babu jimawa bacci ya sake ɗaukarsu. Bawan Allah haka ya yi ta tiƙar aikin yana gumi abinka da ba a saba ba. Ya yi musu wanka ya shiryasu. Ya soma aikin gidan,Halima da Amina suka tayashi duk da ba wani abin a zo a gani suka iya ba,amma tausayin mahaifinsu ya cika zuciyarsu. Hamid da Aunty Saudah ko a kwalar rigarsu hasalima kallo suka ci gaba da yi. Nu'aymah kuma ta saka sauran ƙwan da ya rage gaba tana ci. Ba shi ya kammala aikin ba sai wurin 9:35am na safe. Gudu-gudu ya yi wanka ya shirya zuwa makarantarsu.
Sai kusan 11:05am ta farka,a nan ma aljanar abincin ce Nu'aymah ta tasheta da kukan yunwa. Miƙa ta yi tana hamma a lokaci guda
''Abinci zan ci! Ki ba ni abinci! Ni ni ni ki ba ni abinci'' Nu'aymah ta yi ta faman bubbuga gadon tana mitar ta bata abinci. Sauka ta yi daga gadon ta nufi kicin. Take ta saki murmushi ganin ko'ina fes a gyare. Ruwan wankansu ta fara ɗaurawa ita da Maryam. Sauran biredin da ya rage ta miƙama Nu'aymah...✍️
^^^^^^^^^^^^^
*Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya*
A ɓangarensu Mairi, sun sha hira sosai da 'yar ƙanwanta,daman ba kwana za ta yi ba,sun zo gidan wata 'yar'uwan mijinsu ce,ganin suna kusa sai ta ce bari ta zo su gaisa da 'yar'uwarta. Ta miƙe za ta tafi HAFIZA ta ce bata san zancen ba. Ita sai an tafi da ita. Abu wasa-wasa ya koma gaske. Kuka ta saki tana bubbuga ƙafa sai Ammu Jamila ta tafi da ita. Abin da ba su sani kishin wannan yarinyar da Jamila ta zo da ita ne,shi ya sa ta ce tare za su je. Jamila ta dubi Mairi
''Haɗo mini kayanta mu tafi tun da suna hutu''
''Haddar fa?" Mairi ta tambaya.
''Yoo wannan ai mai sauƙi ne yaya,sai na dinga mata ƙari da musaffan Al'qur'ani. Ban zan iya da darun HAFIZA ba,tun da ta kafe kin san halin kayanki''
''Ammu Jamila wallahi saboda kin zo da yarinyar nan ne. Tun ɗazu take harararta''. Hamida ta faɗa tana dariya. Dukkaninsu suka dubi HAFIZA,cunno mitsitsin bakinta ta yi tana juya fuskarta gefe.
'' HAFIZA! har kin san kishi. Ni Jamilatu na ga abin mamaki yau,daman saboda Ruƙayya kike son bi na. Haba in ce! Ni na yi mamakin kukan da kike sai kin bi ni tun da ba yau na saba zuwa gidan ba,rakiya ce kawai tsakaninmu. Allah ya baki miji ke kaɗai HAFIZATA,ki huta da kishi'' ta ƙarashe maganar tana shafa kumatunta da suke jiƙe da ruwan hawaye.
''Ammu Jamila ni ma za ki da ni?" Hamida ta tambaya.
''Kina gida yarinya. Daman na san kin faɗi hakan ne don kar aje da HAFIZA '' cewar Jalil yana hararanta. Yasir kuma murmusawa ya yi yana girgiza kai.
''Ita ma don saboda kukan da take ne ya sa zan je da ita. Ki bari ni da kaina zan zo na ɗaukoku ku yi mini sati. Kin ji Hamida?" Gyaɗa kai Hamida ta yi,fuskarta ta sauya saboda ba haka ta so ji daga bakin Ammu Jamila ba. Babu jimawa Mairi ta fito da 'yar jakar HAFIZA ta ajiye a ƙasa
''A sauka lafiya''
''Ammuna ina drawing book ɗina. Kin manta da shi. Ya Jalil, Ya Yasir baku ba ni naku drawing book ɗin...''
''Sai aka ce miki shekara za ki yi a can HAFIZA'' Jamila ta katseta,sai ta dubi Mairi ta ƙara da cewa
''Ɗauko mata guda ɗaya da pencil. Ku da kayanku ke bisa ka. A kowani lokaci za ku iya komawa Kaduna''
Ɗan jim kaɗan ta dawo da drawing book ɗin. Suka tattara suka wuce. Hamida na ganin fitarsu ta saki kuka wai ita ma za ta bi su. Ban za kowanne ya yi da ita har ta ƙaraci kukanta ta yi shuri. Lokacin zuwa haddarsu ya yi suka shirya...✍️
^^^^^^^^^^^^^
*Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya*
A ɓangaren Sahura, Maryam ta fara ma wankan ta kwantar da ita,sai ta wuce bayi ta yi nata. A gurguje ta shirya saboda Nu'aymah da ta sake dawowa ɗakin ta cinye biredin tana kukan yunwa. Kicin ta koma tare da ɗora sanwan rana. Macaroni biyu ta dafa musu. Ta aiki Hamid ya kaima Mahafinsu na shi, kasancewar ta rana takan aika mishi da abinci. Suna tsaka da ci aka ƙwanƙwasa ƙofarsu.
''Waye?" Ta tambaya a zaunan.
''Maman 'yar gayu ce''
''A'aaaaah mutanen birnin Ikko ne! Bari a zo a buɗe miki'' ta faɗa tana duban Aunty Saudah ta ce
''Je ki buɗe ma Maman 'yar gayu ƙofa''
''Ni kullum kullum ake sakawa aiki a gidan nan saboda ba a sona. Ga su Amina ba za a saka su ba sai ni. Ni Allah na gaji, daga wannan ba zan ƙara zuwa aikenki ba''
''Yi haƙuri ki je tana jira.''
Buɗe kofar ta yi ta dawo ta zauna cin abincin. Ita da yaranta suka shigo ɗakin. Zuwa yanzu yaranta uku ne. Zaynab babbar 'yarta da take kiranta da 'yar gayu,sai Fa'iza sa'ar Amina da ƙaramarsu Firdausi tana kiranta da Nana sa'ar Nu'aymah. Cike da farinciki ta tarbesu. Sun jima ba su ga juna ba, kasancewar mijin maman 'yar gayu ya zo ya ɗauke zuwa birnin Ikko inda yake aiki. Wani daga cikin abokansa da ke aiki a nan barikin sojojin ya tsaigunta masa sharholiyar da Maman 'yar gayu take da manyan sojoji. Sosai ransa ya yi matuƙar ɓaci. Ya yi amfani da pass ɗin da aka ba shi na sati biyu ya zo ya ɗauketa. Da farko ta so yi masa gardama sai ya nuna mata ɓacin ransa sannan ta bi shi,madadin ya wuce da ita barikin sai ya kai ta garinsu, ya kuma sanar da 'yan'uwansu abin da take idan ba ya garin kasancewar auran zumunci aka musu. Maman 'yar gayu ta yi matuƙar mamakin ta ina ya san tana wannan harƙallar. Ta so yin gardama a kan ƙazafi yake mata har da yi masa sharrin ba ya ciyar da su yadda ya kamata. Lokaci guda ya goge mata hadda ta hanyar lissafo manyan sojojin da suke sharholiyar tare a gaban iyayensu. Take bakinta ya rufe tsabar mamaki. Kafin mijinta ya kai ƙarshe mahaifinta da yayanta suka hau ta da duka babu ji babu gani,ihu take tana neman ɗauki. Cike da azama Mahaifin Mijinta ya shiga tsakaninsu,sai dai kafin ya yi nasarar cetonta ta daku iya dakuwa a hannunsu. Mijin na gefe ya ƙi motsawa balle ya ceceta. Ta sha faɗa sosai,iyayenta mata suna yi,mazan ma haka,duk ta ji ta muzanta a idonsu. Daga faɗa suka koma yi mata nasiha mai tsuma rai, sosai ta magantu ta kuma shiga taitayinta. Satinsu guda suka koma birnin Ikko. Maman 'yar gayu ta yi sanyi sosai,domin wa'azin da iyayenta suka mata ya yi matuƙar tasari a kanta sai dai mugun halinta da rashin saka ido a kan yara yana nan daram, ku san halinsu ya zo ɗaya da Sahura a kan yara. A can ta haifi su Fa'iza, an yi posting din mijinta nan ya sa suka tattaro suka dawo,sai dai kafin su dawo yayanta ya yi mata wa'azi sosai a kan zina da illolinta. Daman tuni ta watsar da ɗabi'ar duba da yadda ta ji labarin wata ta mutu ana zina da ita. Sai tsoran Allah ya kamata.
Zama wuri ɗaya suka yi suna duban junansu da murmushi
''Maman 'yar gayu ashe rai kan ga rai! Sai dai na ji wai mijinki ya zo ya ɗaukeki babu ko sallama''
Murmushin yaƙe ta yi,
''Wallahi kuwa! Na so zuwa amma ya hanani! A washegarin ranar da ya zo muka wuce garinmu daga can kuma muka wuce birnin Ikko''
''Allah sarki! Wurin mama favour naje take sanar mini kin koma barikin sojoji na birin Ikko. Ki ce yanzu yaranki uku'' ta yi maganar tana duban yaran
''Eh Maman Hamid! Fa'iza da Firdausi amma ina kiranta da Nana''
''Ga su Tubarkallah. Bari na sako muku abinci''
'' Da kin barshi a ƙoshe muke...''
''Momy ni zanci'' cewar Nana tana katseta
''I know it must be you chop chop!'' cewar 'yar gayu tana hararta,a duk cikin yaranta ita ta fita zakka,akwai hankali da natsuwa.
''Mama ki ƙara a nan mu ci a tare!" Cewar Nu'aymah tana miƙo robarta.
''Yau kam za a yi ruwan sama da ƙanƙara. '' cewar Sahura tana amsar kwanon ta nufi kicin. Babu jimawa ta dawo falon da abinci da ruwa. Ta ajiye ma su Nu'aymah robar suka fara ci a tare. Maman 'yar gayu ta sha ruwa suka ci gaba da hirar yaushe gamo. Sun sha labarai kala-kala,kowa na bayar da labarin abubuwan da suka faru da shi a waɗannan shekarun. Sai kusan yamma suka koma block dinsu. Sahura ta miƙe zuwa kicin ta ɗaura girkin dare.
A ɓangaren Dauda Imamu tsoro da fargaba ne suka hanashi dawowa gidan da rana . Daga asubar yau zuwa yanzu zuciyarshi ta gama sallama wa Sahura,duk yadda ya so yakice tsoranta ta karfi da yaji hakan ya faskara. Sai bayan isha'i ya yi kundumbalar dawowa gidan. Da sallama a bisa laɓɓansa ya shigo ɗakin. Takunsa biyu ya tsaya,ƙirjinsa na dukan uku-uku.
''Ba za ka ƙaraso ciki ba ne,ka tsaya tana tsattsare ni ido!" Sahura ta furta a tsawace. Kafin ta ɗige aya ya shigo da sauri cikin falo ya zauna a saman kujerar.
''Sahura fisabilillah mai ya shigeki ne kika son muzantani da ɗaga mini mur...''
''Dakata Dauda! Kasan abin da bakinka zai furta!"
Cike da rawar jiki ya ce ''To! To! Na tsuke bakina ranki shi daɗe''
''Da yafi maka. Abincinka na kicin kaje ka ɗauko ina shayar da Maryam''
Zumbur ya miƙe kamar wanda aka tsikara da tsinin allura ya nufi kicin ɗin,tiren gabaɗaya ya ɗauko ya fito. Su Aunty Saudah sun kwanta, Hamid ne dai yake falon yana kallo. Idan da da ne yana ganinsa zai ce ya tashi ya kwanta, amma yau bakinsa alaikum yana tsoron ya yi magana cibi ya zama ƙari. Bai wani ci abincin kirki ba saboda jinsa yake duk a takure. Wani irin kwarjini Sahura ta yi masa ta yadda misaltawa ɓata lokaci ne. Tsam! Ya miƙe saɗaf-saɗaf zai bar falon ya ji muryarta
''Wa ka bar ma tiren ya ɗauke maka!''
Da sauri ya dawo falon tare da ɗaukan tiren ya kai kicin. Zai wuce uwar ɗaka ta sake dawo da shi falon. A hankali ya dawo ya zauna kamar wanda ƙwai ya shafe masa a ciki. Kwantar da Maryam ta yi a gefanta sannan ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta dubesa. Suna haɗa ya yi sauran duƙar da kansa yana addu'ar da duk ta zo bakinsa.
''Ina so gobe da safe kaje Gusau ka ɗauko yaranka duka su dawo nan da zama kuma na dindindin''
Da sauri ya ɗago yana dubanta
''Eh ka ji me na ce,kuma a goben za ku dawo tare. Na sallameka za ka iya tafiya''
Miƙewa ya yi,bakinsa ɗauke da magana amma kamar an rufe masa baki ya gaza furtawa,hasalima haɗiye maganarsa ya yi da suka haɗa ido. Da sauri ya shige uwar ɗakan har yana bigewa da bango. Tintsirewa da dariya ta yi ganin ya bige goshinsa tsabar hankalinsa ba a wurin yake ba. Daɗi sosai ya cika zuciyarta,wai yau itace Dauda Imamu yake mutuwar jin tsoranta. Boka Ataka ya gama mata komai a duniya. Sosai ta zurfafa kogin tunani. BAHAGON TUNANI ne ya cika ƙwaƙwalwarta,tana hasaso yadda za ta wahalar da yaran kishiyarta. Haka shi ma Dauda Imamu ya azabtu a hannunta. Sannan ta zama uwar mata da mazan bariki,daman Dauda Imamu ne ke taka mata burki. Shi ya sa a baya take zumunci a ɓoye da sojojin amma yanzu kuwa sai gani sai hange,tun da kullum matar malam sama matar malam ƙasa suke kiranta,za ta shige su sosai ta yadda za ta tatse aljihunsu tun da matan wasun su ba a barikin suke ba. Ya zamana suna bata kuɗi tana musu girki. Ta jima sosai a falon tana tunani,yayin da Hamid ke kallonsa hankali kwance. Har ta gaji da zaman ta ɗauki Maryam suka wuce ɗaki Hamid bai tashi ba. Tana isa uwar ɗakan ta ji muryar Dauda Imamu na karatun Alqur'ani. Sosai ranta ya yi mugun ɓaci,da sauri ta dawo falon ta zauna tana tuƙuƙin baƙinci. Lallai kuwa dole ta taka masa birki a kan karatun Alqur'ani a gidanta,domin ba za ta lamunci hakan ba.(Oh! Ni Narrnarhh Bukar! Lallai Sahura kin yi nisa. Ni da Esteem fans ɗina muka ce "To sannu sara mai baƙar takashi! Al'qur'anin ma kina son hanashi karantawa! Tab! Kin kuwa zunguro sama da kara, domin irinku babu inda kuke zuwa a duniya.'' Allah ya tare mana imaninmu!)
Kwantar da Maryam ta yi a one sitter sannan ta koma three sitter ta kwanta,don wani irin bacci ne mai daɗin gaske yake fizgarta. Har ta fara bacci sai kuma ta farka tana duban agogon falon. Ƙarfe 12:01am na dare yake haskowa. Duban Hamid ta yii da hankalinsa kacokar ke allon TVn ta ce
''Je ka duba mini ɗakinmu ko Babanku ya gama karatun?"
''Ok! '' ya miƙe da gudu ya nufi uwar ɗakan. Babu jimawa ya dawo ya ce mata ya kwanta. Tsam ta miƙe tana lumshe ido ta dauki Maryam ta wuce uwarɗakan. Hamid kuma ya ci gaba da kallonsa,wanda sai wurin ɗayan dare ya kashe kallon ya wuce ɗaki ya kwanta.
Dauda Imamu bai samu damar sallah dare ba,amma kiran sallar farko ya farka,ya tashi ya ɗauro alwala sannan ya shimfiɗa dadduma,zai kabbarta sallah ya ji muryar Sahura.
''Ka koma falo da daddumarka kar ka hanamu bacci ni da ɗiyata, sannan ka rage sautin karatunka shi ma yana damuna. daga yau a falo za ka dinga sallar darenka da karatun Alqur'ani''
''To ranki shi daɗe'' ya furta yana ɗaukar daddumar ya fito falo. Sosai ransa ya sosu da furucinta amma ya ya iya. Gefe guda Sahura murmushi ta saki tana cire nonon daga bakin Maryam tana gyara kwanciyarta. A kunnuwanata aka kira sallar farko,ta san zai iya tashi ya ce zai yi Sallah,shi ya sa taƙi komawa baccin. Bayan ya kammala sallar ya nufi ɗakin Hamid ya tayar da shi sannan ya wuce Masallaci .
Sai wurin 8:12am na safe Dauda Imamu ya dawo gidan. Zuciyarsa sai dawo masa da maganar Sahura take a kan ɗauko yaransa,tamkar zuciyarsa ta muhawara da Sahura. Ya so sai wurin 10:00am ya dawo amma kwata-kwata ya kasa samun sukuni. Dole ya dawo gidan bayan ya sanar ma Malam Tsalha a kan zai yi tafiya amma yau zai dawo. Fatan Allah ya tsare hanya ya yi masa sannan ya dawo gidan. Koda da ya shigo ya samu gidan a gyare yaran ma ta yi musu wanka har ma sun karya. Nu'aymah ce dai har yanzu bata gama karin ba. Da sallama a bisa laɓɓansa ya shigo ɗakin. Yaran ne kaɗai suka amsa sallamarsa amma Sahura ko kallon inda yake bata yi ba. Zama ya yi a ɗaya daga cikin kujerun ya rakuɓe wuri guda kamar mai roƙon gafara. Babu zato ya ji muryar Sahura
''Sai yanzu ka ga damar dawowa gidan bayan kasan na ce yau nake so yaranka su dawo gidan nan!''
Take 'yan hanjinsa suka kaɗa, muryar da ta yi amfani da ita wurin yin furucin ya ɗarsa masa tsoro a cikin zuciyarsa. A ruɗe ya ce
''Zan je yanzun nan!"
''Da yafi maka! Kuma a yau nake son ku dawo ba sai gobe ba!"
''To ranki shi daɗe''
Miƙewa ya yi zuwa uwar ɗaka,a gaggauce ya yi wanka ya fito ya sauya kaya,ko samun damar shafa mai bai yi ba balle kuma maganar kari ya fice daga gidan....✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_020_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
Miƙewa ya yi zuwa uwar ɗaka,a gaggauce ya yi wanka ya fito ya sauya kaya,ko samun damar shafa mai bai yi ba balle kuma maganar kari ya fice daga gidan. Kai tsaye ya nufi tashar kawo inda zai hau motar Zamfara. Ya tsaye inda ake tuyar ƙosai,ya saye kunu da ƙosai ya sha sannan ya wuce inda ake loading Zamfara,Gusau. Daman mutum ɗaya ake jira,yana hawa motar ta ɗaga. Damuwa,ƙunci da fargaba suka mamaye duniyarsu,ya rasa inda zai tsoma ransa ya jii daɗi. So yake ya hana kansa bin umarnin Sahura amma hakan ya gagara. Bai san me zai ce wa Mairi idan ya isa Gusau ba. Kwata-kwata ya kasa samun sukunin rai da gangar jiki,gabaɗaya tunaninsa ya fi karkata a kan bin umarnin Sahura. Idanuwansa sai hasko masa fuskar Sahura yake a lokacin da take ba shi umarnin,yayin da zuciyarsa take azalzarsa a kan cika umarninta. Ya rasa me ke damunsa,da wani ido zai kalli Mairi. Wata zuciyar na sanar masa 'Umarnin Sahura tamkar ba shi ne,da zarar kunnuwanka sun saurara,dole ne ka aiwatar,idan kuma ba haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 33