Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwando,ya rasa mai ya shiga kansa a lokacin. Har yanzu bai daina nadamar hakan ba. Gyara tsayuwa Dauda Imamu ya yi sannan ya ce ''Toh yanzu dai Mammann abin da ya faru ya riga da ya faru. Batun yara suna cikin ƙoshin lafiya,Hamida ce dai take kwance asibiti,kuma jikinta ya yi sauƙi sosai don da wuya yau ba su sallameta ba.'' Mamman bai ji daɗin amsar da Dauda Imamu ya ba shi ba,domin ba tambayar da ya yi masa ba kenan,amma sai ya share ko don mutumin da suke tare. ''Subhanallah! Allah ya bata lafiya da ɗaukakin musulmai. Daman na zo tafiya da yaran ne a gaskiya,tun da dai uwarsu na raye ban ga amfanin zamansu a barikin nan ba. Matarka tana wahalar da su da bauta don haka ba zamu lamunci hakan ba. Malam ya so zuwa da kansa amma tafiyar gaggawa ta same shi,shi ya sa ya aiko ni don na yi wa tufkar hanci. Yau zan koma da su Zamfara in shaa Allah! Domin ban zo da shirin kwana ba. '' ''Malam zan iya saka baki a maganarku'' Mahaifin Muhsin ya tambaya yana duban Mamman. ''Bismillah! Za ka iya'' cewar Mamman yana ɗan sakin fuska. Ɗan gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_030_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ Ɗan gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce ''Duk da maganar gida ce amma an zo wurin da zan iya tofa albarkacin bakina. Tabbas baka yi ƙarya ba matarsa tana cin zarafin yaran 'yar'uwarka. Domin ni ganau ne ba jiyau ba,amma kuma Allah ya saka musu tun da ba azzalumin bawansa ba ne,sai dai idan shi ya zalunci kansa. Jiya aka kaita ɗakin horo saboda kamatan da aka yi da cin zarafin yaran kishiyarta kuma an hukuntata sosai'' Waro ido Mamman ya yi cike da tsantsar mamaki,a ransa yana jera hamdala ga Ubangiji, cikin ruwan sanyi ya saka ma 'yar'uwarsa. Ɗan numfasawa mahaifin Muhsin ya yi sai ya ci gaba da cewa ''Yanzu haka riƙon Jalil ya dawo hannuna,domin abokin ɗana ne kuma na ji tausayinsa sosai a lokacin,kamar yadda na sanar ma Imam a wancan lokacin kai ma zan sanar maka. Na ɗauki alƙawarin cinsa,shansa,tufafinsa,makarantarsa da kuma neman aikinsa idan Mai Sama ya ara mini rayuwa. Don a gaskiya Jalil ya shiga raina sosai haka ma iyalina, yanzu haka da nake faɗa maka daga asibitin zan wuce da shi flat ɗina ya san komai a kaina saboda halin rayuwa. Sannan ƙarin daɗawa sauran yaran biyu an yi ma matarsa katangar ƙarfe a tsakaninsu,kuma ina da yaƙinin zuwa yanzu ta shiga taitayinta. Don akwai wata baiwar Allah da take ɗawainiya da su tsakaninta da Allah kuma za ta kula da su ɗari bisa ɗari. Don Wing commander na mu Madam Ngozi ta sanar mini uwarsu ta danƙa mata amanarsu kuma ta amsa da hannu bibbiyu. Yanzu dai Malam idan da hali babu takura a bar mana yaran. Duk hutu za su dinga zuwa wurinta in shaa Allah,sannan zan yi ƙoƙari idan na dawo daga tafiya na kai mata iyalina idan mijin matar ya barta sai muje tare da ita ta ganmu'' Tun lokacin da mahaifin Muhsin ya fara magana jikin Mamman ya yi sanyi,daman da faɗa ya zo barikin,idan Dauda Imamu ya hana shi yaran ya haɗasa da wani babban abokinsa soja da ke aiki a nan barikin. Sai dai daɗaɗan kalaman officer Kabir sun sacar masa da gwiwa. Haka kurum ya ji officer Kabir ya kwanta masa a rai kuma da alamu maganar da yake faɗa tun daga ƙasan zuciyarsa take fita. Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke,a gefe guda Dauda Imamu sai raba ido yake a tsakaninsu, zuciyarsa fes da ɗaukin gaggawar da mahaifin Muhsin ya kawo masa,don ya san halin Mamman sosai idan ransa ya ɓaci,tun da ya ce zai ɗauki yaran ba zai iya jayayya da shi ba,amma Ubangiji ya kawo masa ɗauki a lokacin da yake nema. Mahaifin Muhsin ya wankesa tsaf! A idon Mamman ko babu soso da sabulu. Ɗan gyara tsayuwa Mamman ya yi saboda ya fara gundura da tsayuwan ya ce ''To Alhamdulillah! Tun da haka abun ya kasance. Daman babbar damuwamu muzgunawar da matar Dauda take ma yaran,amma tun da karshe an yi maganinta Alhamdulillah. Na ji daɗin hakan sosai kuma zan sanar da Mairi abin da ka ce in shaa Allah. Na san ba za ta tayar da hankalinta ba tun da yanzu suna a hannu mai kyau ba kamar da ba. Sannan muna godiya sosai Allah ya saka da alkhairi ya ƙara ɗaukaka.Yanzu muje ni ma na ga jikin Hamidar don yau nake son komawa Zamfara in shaa Allah'' ''Ameen ya Hayyu ya Qayyum. Ai tun da kai ma kana nan sai mu je da kai ka ga iyalin nawa da wasu abubuwa da ya dace ka sani a kaina'' ya yi maganar yana buɗe murfin motar. Duka suka shiga sannan ya ja motar. A hanya suna tafiya suna hira har suka isa asibitin ya yi parking suka fito. A cikin ɗakin asibitin,mijin maman Jawaheer ne ya zo gaishe da Hamida, kasancewar bayan isha'i ya dawo garin ya samu pass na sati ɗaya,kanwar maman Jawaheer ta kwana da Hamida yayin da Yasir ya bi su momy ya kwana a can. Maman Jawaheer bata ɓoye masa komai a kan su Yasir ba,tun daga lokacin da ta gan su da safe sun je ɗiban ruwa har zuwa jiya. Babu abin da ta rage balle ƙari,har da ƙarin matsayin da Madam Ngozi ta ce za a mai.Da yake mijinta akwai tausayi, sosai ya jinjina al'amarin,sannan shi ma ya aminta da hakan ɗari bisa ɗari. Ko da ba su zauna a gidansa ba,ya bata damar zuwa ganin halin da suke ciki, idan da taimakon da za ta yi sai ta musu,shi ma idan ta kama ya taimaka,ƙofar aljihunsa a buɗe take. Hira suke a tsakaninsu lokacin da su Dauda Imamu suka shigo ɗakin da sallama. Cike da fara'ah suka amsa. Mijin maman Jawaheer ya miƙa hannu suka yi musabaha. Mamman ya ƙara jin daɗi ganin Hamida na kewaye da mutanen kirki,sai hakan ya ƙara faranta ransa sosai. Sun ɗan jima a ɗakin har Hamida ta farka ƙanwar maman Jawaheer ta taimaka mata ta yi brush sannan ta haɗa mata tea ta miƙa mata biredi bayan ta shafa masa butter. Mahaifin Muhsin da mijin maman Jawaheer sai hira suke alamun sun san juna,duk magana ɗaya mijin Mamman Jawaheer sai ya haɗa da kalmar oga kasancewar mahaifin Muhsin ya fi sa matsayi sosai. Mijin maman Jawaheer Flight Sergeant ne yayin da mahaifin Muhsin yake da matsayin flying officer. Sun ɗan jima daga bisani mahaifin Muhsin ya wuce da su gidansa. Haƙika Mamman da Dauda Imamu su samu tarba ta mutunci,domin momy ta cika gabansu da snack da drinks. Bayan sun gaisa ta koma ciki. Sun ci snacks ɗin sosai musamman Mamman da ya kwaso yunwa,bayan sun kammala ne mahaifin Muhsin ya faɗa musu komai a kansa da kuma matarsa,sannan ya ƙara tabbatar ma Mamman za su zo idan ya dawo daga Abuja. Daga nan suka miƙe ya rage musu hanya,shi Dauda Imamu ya wuce islamiyya,Mamman kuma ya nufi hanyar komawa gida bayan mahaifin Muhsin ya tanƙa masa matsabbai ya ƙara na mota. Sai yamma aka sallami Hamida,babu laifi sauƙi ya samu sosai don har surutu take idan ta kama ita da 'yan'uwanta,da yake bayan su Yasir sun dawo daga boko ya zo da su asibitin har da momy. Suna nan har aka sallameta. Mahaifin Muhsin ya tuƙosu zuwa block ɗin maman Jawaheer, a nan za ta zauna idan jikin nata ya ƙara samun sauƙi sai ta koma flat ɗinsu. ^^^^^^^^^^^^^^ A ɓangaren Sahura bata san wainar da ake toyawa ba,ta ƙara jan yaranta a jiki sosai. Ta ɗaukar wa kanta alƙawarin daina shiga sabgar su Yasir, duk abun da za su yi ba za ta kalla ba balle ta tanka,yaranta su ne komanta,farincikinsu shi ne burinta,baƙincikinsu shi ne damuwarta. Tana da tarin burika a kan yaranta musamman matan. Fatanta idan sun girma su zama abin kwatance a barikin saboda farin jinin samarinsu da kuma kyawunsu,babu laifi yaranta akwai kyau abinka da jinin buzaye da fulani,dukkaninsu farare ne kamar ka tsaga fatarsu jini ya fito. ^^^^^^^^^^^ *Hayin bijini Mada jihar Zamfara Nijeriya* Sai cikin dare Mamman ya iso Mada,kai tsaye ya wuce gidansa,ya bari zuwa gobe da safe sai ya sanar masu Mairi komai. A ɓangaren Mairi kuwa ta yi matuƙar ƙosawa Mamman ya dawo ta ji halin da yaranta suke ciki ko kuma ya taho da su,kaso mafi rinjaye na tunaninta ya fi karkata a kan dawowa da su zai yi,ta sansa da zafi da kuma faɗa a kan gaskiya,ko Sahurar daidai yake da ita. Idan Allah ya sa yaranta suka dawo hannunta burinta ya cika,dole ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tsananin murna. A ɓangaren Jamila ma hakan take don ta ma fita ƙosawa Mamman ya dawo. Bini-binii sai ka ji ta ce ''Ohhhh! Mamman ana can. Allah ya sa ya dawo da su Hamida,ƙila ma yanzu haka suna hanya'' Ganin dare ya yi har zuwa lokacin ba su ga ɗan aiken da zai zo kiransu ba suka haƙura,sai dai zukatansu ba su bar tunani ba. WASHE GARI Wuraren ƙarfe 9:30am na safe yaron Mamman ya zo gidan Jamila kiransu, jiki na tsuma suka saka hijabi,Jamila ta riƙe hannun HAFIZA suka taho gidan. Da yake Mamman a gidan mahaifinsa ya zauna tare da iyalinsa,matansa biyu ne,yana da yara shida. A hanya Mairi da faɗi take ''Allah ya sa ina zuwa na ga su Jalil'' Jamila kuma ta amsa da Ameen. Bakinsu bai daina motsi ba har suka iso gidan Kawunsu. A zaure suka tarar da shi zaune a saman tabarmar kaba yana jin rediyo hankalinsa kwance fuskarsa cike da annuri. Tun da Mairi ta shigo zauren fuskarta ta sauya haka ma Jamila, a tunanin kowannansu za su tarar da su Yasir,sai dai suka ga wayam! Cike da girmamawa suka gaishe shi. Bayan ya kashe rediyo sai ya gyara zamansa sannan ya fara magana ''Na san tunaninku ya fi karkata akan ɗauko su Yasir zan yi,duk da ni ma hakan take a wurina. Sai dai kuma ta sauya zani domin na je da zafi kamar garwashi na dawo da sanyi kamar ƙanƙara'' ''Yaya Mamman ban fahimci zancenka ba" cewar Mairi fuskarta shimfiɗe da tsantsar damuwa. Ɗan Murmusawa Mamman ya yi sannan ya ce ''To dai abin da zukatanku sukwe raya muku a kansu Yasir ba haka ba ne'' Babu shiri Mairi ta ɗago da manyan idanunta fuskarta kwance da maɗaukakin mamaki. ''Ni fa da idanuna na ga yadda suka sauya,sun rame,sun ƙobare kamar masu kamun yunwa,duk wanda ya gan su zai shaida ba su samun kyakkyawar kulawa. Yanzu kuma ka zo da zance na dabam wanda kwata-kwata na kasa fahimtar inda ya dosa'' cewar Mairi. ''Nii ma gaskiya Yaya Mamman ƙwaƙwalta na kasa fahimtar zancenka'' Jamila ta faɗa ita ma fuskarta ɗauke da damuwa. Wannan karon ma murmushim ya kuma saki sannan ya ce ''Maganar gaskiya Allah ya yi ikonsa a kan Sahura,domin da gamu da gamonta,shekaran jiya aka kai da ɗakin horo na barikin a kansu Yasir'' ''Allah Yaya Mamman!'' cewar Mairi tana ɗan waro manyan idanunta tsabar mamaki. Mamman bai yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar musu duk abin da mahaifin Muhsin ya faɗa mishi. Madadin Mairi ta yi farinciki sai baƙinciki mararan ya bayyana a fuskarta. Tsabar takaici shiru ta yi sai Jamila ce ta ce ''Kai kuma Yaya Mamman ka yarda da shi,haka kurum baka san mutum ba,baka san halinsa ba za ka aminta ya riƙe yaran 'yar'uwarka. Mu dai wallahi ba mu yarda ba. Ai duk irin kulawar da su Yasir za su samu koma bayan na Yaya Mairi ce. Uwa ce kaɗai za ta iya shanye komai na ɗanta,domin soyyayarsa da jinin jikinta yake . Duk irin kulawar da su Yasir za su samu hannun mutumin ba zai kai kwantan-kwantan na Yaya Mairi ba. To ai an yi ba yi ba kenan'' ''Karki manta Jamila,labarin zuciya a tambayi fuska, da gaske sojan yake son riƙe Jalil hasalima ya ce yana nan zuwa da duka yaran wurin Mairi ya kuma sake neman alfarmarta. Sannan idan an samu mutanan banza ba a rasa na kirki ba. Kin taɓa jin an rasa nono a Ruga?. Mu gwada shi na wata biyu mu gani,ni da kaina zan je na gani da ido,idan ya karya alƙawari ai sai a ɗaukosu. Amma ba mu jaraba shi ba,bai da ce mu yi saurin yanke hukunci ba.'' ''Eh kuma maganarka haka take,shikenan mu zuba ido mu gani zuwa wata biyun. Hakan ya miki Yaya'' Cewar Jamila tana duban Mairi. Jinjina mata kai kawai ta yi,amma ba abin da ke cikin zuciyarta kenan ba,ita dai yaranta su dawo hannunta,ta fi gane hakan. Sun ɗan taɓa hira wanda kusan da Jamila yake daga bisani suke shiga ciki gaida matan gidan,ba su daɗe ba suka wuce gida. A ranar Mairi ta tattara komanta ta dawo Gusau. Duk da kaso mafi rinjaye na damuwarta ya kau amma har yanzu da sauran ɓirɓishinsa. HAFIZA ta koma boko da islamiyya. Duk safiyar Allah sai an yi daru da ita a kan zuwa boko,ita da su Yaa Jalil za ta je makarantar bata son rakiyarta,da kyar take shawo kanta ta yarda,wani lokacin Mairi har hawaye take idan HAFIZA ta ce da su Jalil za ta makaranta,a ranta tana faɗin ba za ta iya bayar da yaranta har uku riƙo ba alhalin tana raye kuma daidai gwargwado tana da halin riƙesu tun da Sadiƙu ba yashar da ita ya yi ba,kullum cikin aiko da cefane yake wani lokacin idan kasuwa ta buɗe har da kaji ko nama da kuɗi. Mairi bata wasa da sallar dare wanda yanzu ya bi jikinta,kullum cikin kai kukanta take ga Ubangiji yi mata sakayya a kan zalincin da Sahura ta yi mata,don bata ga laifin mijinta ba tun ita ma shekarun baya ta tsinci kanka a kwatankwacin yanayin da yake ciki a yanzu,Allah ne ya tarfa ma garinta nono asirin bai jima a jikinta ba. Ta kasa ta tsare tana jiran zuwan sojan da Mamman ya ce zai zo da yaranta...✍️ ^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* BAYAN KWANA BIYU Jikin Hamida sai dai mu ce Alhamdulillah,ta warke fes babu kurajen sai tabo. Da kuɗin da Madam Ngozi ta ba ma Maman Jawaheer ta yi amfani da shi ta je Tudun Wada Kasuwar Bacci ta siyo ƙananun katifu 12 inches da gadajen ƙarfe biyu su ma 12 inches da yake Yasir ya faɗa mata a ƙasa suke kwana shi da Hamida. Drop ta ɗauka har barikin ya sauketa a flat ɗin Sahura. Driver ya taimaka aka sauke kayan sai ta sallameshi. Barin kayan ta yi a gurguje ta je block ɗinsu ta kira ƙanwarta da su Yasir. Da taimakon ƙanwarta ta matsar da kayan kusa da ƙofar flat ɗin sai ta ƙwanƙwasa. A cikin Sahura ta ce ''Waye?" 'Mu ne '' iya abin da maman Jawaheer ta ce kenan. Babu jimawa Hamid ya zo ya buɗe. Da sallama a bisa laɓɓanta ta shiga ciki. Ta tarar da su a zaune suna kallon TV. Barin kallon Sahura ta yi ta juyo ta ga wace baƙuwa ta yi. Sai dai tana haɗa ido da maman Jawaheer annurin fuskarta ya yi ɓatan dabo. Cike da tsantsar takaici da kuma mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta ce...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_031_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ Cike da tsantsar takaici da kuma mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta ta ce ''Mara zuciya bai yi a rayuwa ba,shisshigi da katsadanla sun zama tufafin da kike yawo da su. Ni yanzu ban da lokacin ɓata da irinki,domin na gaba ya yi gaba. Mtsss!" Murmushi maman Jawaheer ta yi sannan ta ce ''Kya dai ji da shi,an ji maza an saduda'' Banza Sahura ta yi da ita,gyara zama ta' yi ta ci gaba da kallonta. Juyawa maman Jawaheer ta yi kiran Hamida ta nuna mata ɗakinsu a shigo da gadajen. Zuciyar Hamida cike da tsoron Sahura ta shigo falon,kallo ɗaya Sahura ta yi mata ta watsar ta ci gaba da kallonta. Ɗakinsu ta fara kaita sannan ta nuna mata ɗakinsu Yasir. Fita maman Jawaheer ta kuma yi,katifun suka fara shigawa da su sai daga baya suka shigo da gadajen. Suka saka a kowanni ɗaki kasancewar ɗakin da girma sosai,ƙanwarta ta shimfiɗa zannuwan gadon masu kyau da ɗaukar hankali a gadajen. Bayan sun kammala suka fito falon sai maman Jawaheer ta dubi Sahura duk da ta san ba amsa mata za ta yi ba ta ce ''Ga gadajen su Hamida mun kawo,ba don yaranki aka kawo ba,idan kina da zuciya a jiki ki hana yaranki hawa gadajen,idan kuma zuciyar karnuka gareki bismillah'' tana gama faɗin haka ta ja hannun Hamida suka bar flat ɗin. Sahura ta daɗe tana bin ƙofar da suka bi da kallo. Lallai ma matar nan ta raina mata hankali,ta zo har cikin gidanta tana gaggasa mata magana saboda ta ga yanzu bata da iko da su,idan bata yi wasa ba za ta saisaita tunanin. Cije laɓɓanta na ƙasa ta yi da ƙarfi tana yin ƙwafa sannan ta ci gaba da kallon duk da ba fahimtar komai take ba. Hamida da Yasir ba su dawo gidan ba sai a washegari da yamma bayan an tashi daga islamiyya. Sai da suka fara biyawa gidan maman Jawaheer suka canza kaya zuwa na gida sannan suka rataya jakar makarantar boko suka taho. Ƙirjin kowannansu na bugawa suka shiga flat ɗin. Lokacin Dauda Imamu na zaune a falon yana duba wasu takardun islamiyya. Gefe guda Sahura da yaranta suna ɗan taɓa hira kasancewar babu wutar lantarki. Da sallama a bisa laɓɓansu suka shigo falon, Dauda Imamu ya amsa cike da kulawa. Su Hamid kuma suka bi su da kallo kamar sun ga TV,Sahura ko kallon inda suke bata yi ba. Kai tsaye suka wuce ɗaki suka ajiye jakar makarantarsu sannan suka dawo falon,kusa da mahaifinsu suka zauna, lokaci bayan lokaci yana tambayarsu a kan karatunsu,cike da natsuwa suke ba shi amsa. Lokacin sallar magrib ya yi Hamid da Yasir suka bi Dauda Imamu masallaci. Hamida kuma ta wuce ɗakinsu ta ɗauro alwala a bayi ta ciro hijabinta a jaka ta kabbarta sallah. Bayan ta idar ta dawo falon,su Aunty Saudah babu wanda ya yi sallah a cikinsu,Sahura kam ba a maganarta ko karatun sallar bata iya balle ta koyama yaran. Gwara-gwaransu Hamid kasancewar yana bin Dauda Imamu masallaci. Lokacin Sahura ta kammala abinci,ta kira kowanne ya ɗauka,Hamida har ta cire rai ta ji ta kira sunanta. Da sauri ta je ta ɗauko ta dawo falon. Su Yasir ma sun dawo, Sahura ta ce su je su ɗauko abincinsu. Yasir karan kansa ya kwankwaɗi madarar mamaki. Sun natsu suna cin abinci aka kawo wutar nepa. Da sauri Hamid ya kunna TV, dukkaninsu suka mayar da hankulansu ga TVn har suka kammala cin abincin. Suna tsaka da kallo aka ƙwanƙwasa ƙofarsu. Sahura ta dubi Yasir ta ce ''Yasir ɗan je ka buɗe ƙofar ka ga wane ne'' ta yi maganar cike da sanyin murya. Ba komai ya sabbaba mata yin sanyin nan sai don bata manta tsauraran sharuɗɗan da madam Ngozi ta gindaya mata ba a kansu Yasir. Yasir na buɗe ƙofa ya yi tozali da su Jalil cikin kyakkyawar shiga sai ƙamshi suke,hanya ya matsa musu suka shigo,ko kallon Sahura Jalil bai yi ba balle kalmar gaisuwa ta ratsa a tsakaninsu. Ita da yaranta idanunsu kyar a kansu,ga ƙamshin turarensu da ya cika ɗakin. Turaren officer Kabir suka fesa shi da Muhsin. Baƙar leda ya miƙa ma Yasir yana faɗin ''Ga shi in ji Dadinmu(Mahaifin Muhsin) ya ce ku ci ku kaɗai,sauri muke ana jiranmu a mota'' yana miƙa masa suka bar falon Jalil ya turo musu ƙofar. Ƙiƙam Yasir ya tsaya yana kallon ƙatuwar baƙar ledar hannunsa. ''Yarona Yasir me aka kawo muku haka na ji yana tashin ƙamshi'' ta yi maganar tana washe baki kamar gonar audiga,ta tabbata kayan daɗi ne aka kawo musu,eh lallai dole ta sauko ita da yaranta su ma su kurɓi romon demokradiyyar officer Kabir. A sanyaye Yasir ya ce '' Ban san me aka kawo ba'' ''Zo mu gani na tayaka dubawa'' Babu musu ya kai mata,da sauri ta amsa ta saka hannu ta ciro lemon 5alive guda biyu masu raɓa,sai takarda duƙunƙune duk jikinta maiƙo. Nan da nan miyon Sahura ya tsinke,da sauri ta cire takardar ta ɗora a saman cinyarta. Zumbur Nu'aymah ta mike daga zaune tana faɗin ''Mama zan ci'' ''Kar ki damu yayyanki ba su da rowa. Za ku sammana ladar ganin ido ko?" Da sauri Yasir da Hamida suka jinjina mata kai. Takardar ta buɗe, lokaci guda ta ware manyan idanunta ganin gasasshen nama da uban yawa ya ji kayan lambu ga ƙullin yaji a gefe. ''Hamid ɗauko tire'' Da gudu Hamid ya nufi kicin ya ɗauko tire ya miƙa mata,gabaɗaya ta juye naman, zuwa lokacin Nu'aymah ta ci kusan yanka biyar. Raba naman ta yi gida uku,ta kwashe ma su Yasir kashi ɗaya a takardar sai ta sake haɗa sauran kashin ta rarraba musu. Ta aiki Aunty Saudah kicin da ɗauko kofuffuka,cikin hanzari ta nufi kicin ta ɗauko guda bakwai. Buɗe gorukan 5alive ɗin ta yi ta zuba ma kowa,daidai ta zuba 5alive ɗin a kofukan sai ka ce don su aka kawo. Kowanne ya ɗauka suka ci gaba da kallo. Tun daga

Chapter 22 of 33