dawowa. Washegari da safe ta yi wanka ta shirya,jakar kuɗinta ta dauka sannan ta zuri mayafi ta kulle gidan. Kai tsaye ta hau mashin a unguwsr ya kaita tasha daga can ta hau mota. Ta yi amfani da labarin da Dauda Imamu yake bata a kan yadda yake hawan mota daga Gusau zuwa Kaduna,da kuma yadda yake zuwa daga tasha zuwa barikin har yanayin gidan da suke ciki ya kwatanta mata sunan da ake kiransa. Sun jima suna tafiya a hanya. Motar da ta hau tana a matsala,tafiya kaɗan sai a tsaya a ɗauki lokaci wurin gyara sannan su ci gaba da lafiya. Sai kusan 5:40pm na yamma motarsu ta shiga garejin Kawo,da ta yi tambaya wani ya rakata inda ta bus ta sauka da Airforce base. A bakin gate din aka mata wasu tambayoyi sannan suka barta ta shiga. Daga nan ta samu lift bayan ta sanar masa inda za ta je ta hau gado. Cikin sa'a ya ajiyeta a daidai gidan Dauda Imamu. Ta yi masa godiya sannan ya ci gaba da tafiya. Ta kusa isa kofar flat din Sahura ta buɗe. Lokaci guda idanunsu ya sarƙafe...✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
https://chat.whatsapp.com/LrLN4jPxk3oD38jQSugHlV?mode=hqrc
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_023_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
Cikin sa'a ya ajiyeta a daidai flat na Dauda Imamu. Ta yi masa godiya sannan ta ci gaba da tafiya. Ta kusa isa kofar flat ɗin Sahura ta buɗe ƙofa. Lokaci guda idanuwansu ya sarƙafe. Take ƙirjin Sahura ya yi mugun bugawa. A daidai lokacin Dauda Imamu ya shanyo kwana. Ba tare da tsoro ko fargaba ba Sahura ta ƙarashe buɗe ƙofar ta fito. Ƙasa da sama ta kalli Mairi,yayin da Mairi ta tsaya cak tana ambaton sunan Allah a ranta. Rungume hannu Sahura ta yi sannan ta ce
''Maraba da gashasshe! In ji kura ta ga baƙin jaki! Ke a tunaninki kin zo ɗaukar yaranki ne?"
''Tabbas kuwa! Ƙafata ƙafarsu!"
Jinjina kai Sahura ta yi tana murmushin mugunta sannan ta ce
''Hmmmm! To kin yi kaɗan Mairi! Da ke da mijin naki da yaranki duka kuna a ƙarƙashin ikona ne! Idan kuma kina tantana yau zan nuna miki hakan"
Duban Dauda Imamu da ke bayan Mairi ta yi,ta cikashi da mayyan idanunta masu rikiɗa zuwa wani halitta a idanuwansa ta ce
''Dauda! Ina so ka kora Mairi ta bar barikin nan yanzu-yanzun nan'' kafin ta sauke numfashi,Dauda Imamu da ke bayan Mairi ya daka ma Mairi tsawa
''Uban me ya kawoki barikin nan! Kuma da izinin waye kika zo!" Ya furta a hasale. Narai-narai da idanu Mairi ta yi tana haɗiye abin da ya tokare mata maƙoshi. Cikin sassayen murya ta ce
''Baban Yasir ni ce fa! Mairinka! Don girman Allah ka saurareni! Ka ba ni yarana mu koma Gusau an dawo makaranta!"
''Mairi ki bar barikin nan ba na son ganinki,na tsaneki tsana mai tsanani. Yaranki kuma ba zan bayar ba tun da ni na haifesu!.''
Take ƙirjin Mairi ya yi matuƙar buguwa wanda sai da ta rike saitin zuciyarta saboda kalaman Dauda Imamu. Hawaye masu ɗumi suka shiga rige-rigen sauka daga idanunta. Wani irin zafi zuciyarta take mata wanda bata saba jin kalarsa ba. Ta yunƙura za ta ba shi amsa ta hangi yaranta dauke da bokitan ruwa har da Hamida suna tunkaro gidan duk sun jiƙe jikinsu ga sanyin yamma ya taso. A raunace ta kira sunansu
''Yasir! Jalil! Hamida!"
Jin muryar mahaifiyarsu ya saka su saurin juyowa,suna haɗa ido kowanne ya saki bokitin hannunsa ya rugo zuwa wurinta. Rungumeta suka yi tare da fashewa da kuka,ita ma ta rushe da kuka mai sauti. Hamida sai faɗi take
"Ammuna ki tafi damu! Ammuna ki tafi damu! Ammuna abinci kaɗan ake bamu! Da safe a zuba mana ruwan sanyi a jiki,sai ta tura mu ɗibo ruwa! Ammuna za mu bi kiiiiii!" duk ta bi ta rikice
Sosai kuka ya ci ƙarfin Mairi jin kalaman Hamida, hankalinta ya ƙara tashi,ganin yadda Hamida ta koma,duka ilahirin jikinta ƙuraje. Yasir da Jalil duk sun rame musamman Jalil da yake da ɗan ƙiba duk ya bi ya ƙobare ya tsotse. Maman Jahaweer ta dawo daga aiki kenan ta za wuce block ɗinsu ta yi kaciɓis da abin al'ajabi. Tun ranar da ta zazzage Sahura bata sake bin hanyar ba sai yau. Kasa haƙuri ta yi ta ƙaraso inda Mairi take tsaye da su Jalil. Kallo ɗaya ta yi mata ta gane ita ce mahaifiyar su. Sahura na gefe da yaranta suna dariyar ƙeta yayin da Dauda Imamu ke tsaye ya cika ya tumbatsa,tsanarta na ƙara naso a cikin zuciyarsa. Kafin maman Jawaheer ta ƙaraso inda take ta ji muryar Sahura.
''Dauda wai me kake jira ne baka kori shegiya ta bar mana bariki ba!"
Da sauri maman Jawaheer ta dubi Sahura fuskarta kwance da maɗaukakin mamaki. Kafin ta samu furta wani abu idanunta suka yi arangama da Dauda Imamu ya tunkaro Mairi kamar wani zaki,jikinsa sai tsuma yake kamar ɗan mazari burinsa kawai ya aiwatar da umarnin Sahura. Yana zuwa inda suke ya shiga jan su Jalil,har ya yi nasarar janyesu,su kuma suna ihu suna kiran mamansu.
''Haba baban Yasir! Me ya sa idanunka suka makance ne a kan hanyar gaskiya alhalin kai malami...''
Tassss! Ya ɗauke Mairi ta zazzafan mari tare da tunkuɗata ta faɗi ƙasa. Da sauri maman Jawaheer ta nufota tare da taimaka mata ta miƙe. Su Hamida suka sake rungumeta suna kuka. Ita ma kukan take wanda ji take kamar ruhinta na barazanar barin gangar jikinta. A zuciye maman Jawaheer ta dubi Dauda Imamu da har yanzu yake huci
''Haba malam! Haba malam! Ta ya kana malami mai faɗin Allah ya ce Annabi yake a sameka da muzanta iyalinka a gaban jama'a. An ya ka ɗauki hanyar tsira kuwa!"
''Ke dakata! Ba da ke nake ba idan ba so kike na haɗa da ke ba!"
''To bisimillah Malam! Idan ka fasa ka raina Allan da ya halicceka! kai ƙaramin hauka kake yi to ni guguwa ce mai kwantar da ni sai Allan da ya halicce ni!" Ta yi maganar tana riƙe ƙugu.
Ganin mutane sun ɗan fara taruwa sai Sahura ta dubi Dauda Imamu ta ce
''Ɗauko yaran su dawo cikin gida. Ita kuma ka bar ta a nan ta shekara! Ke da yaranki sai gani sai hange daga nesa! Sannan ina jiran duk wanda za ki aiko ya zo ɗaukar miki su idan zai iya. Na faɗa miki ni Sahurar gwaggwan bugaje karan batta da ni babu daɗi! Ya kika ga salon! Bye! Bye! Sai watarana"
''Allah ba ya bacci Sahura! Sai ya yi hisabi a tsakaninmu! Yadda kika ƙuntata mini da yarana in shaa Allah ba za ki taɓa gamawa da duniya lafiya ba! Sai Allah ya fifita yarana sama da yaranki! Ban yafe ba! Kuma ba zan taɓa yafe miki baaaaa!...." Kuka ya hanata ƙarasa maganar da ta yi niyya. Sosai take kuka mai tsuma rai.
''Hmmmm! Ban da lokacinki yanzu,domin na gaba ya yi gaba,na baya sai tsintar bola. Mugun bakinki sai dai ya tsaya a kan yaranki. Nawa yaran su za su taso sama da naki,ballagaza kawai! Dauda na ce ka ɗauko yaran mu koma cikin ɗakin kar ta tara mana jama'a mutincinmu ya zube!" Tana gama faɗin haka ta shige ciki da yaranta suna dariya. Kamar jira Dauda yake ta ba shi umarni. Babu jira ya cicciɓi Hamida ya shigar da ita ciki tana miƙa hannu tana kiran Ammunta,sai ya kora su Jalil suna ihu har suna shiga flat ɗin ya kullo ƙofar. Daɓas! Mairi ta zauna a ƙasa. Ta kasa gasgasta yau ita ce Dauda Imamu yake ma koran kare,yake mari,yake faɗin ya tsaneta tsana mai tsanani. Take ta rushe da wani sabon kukan tana faɗin
''Allah don Zatinki! Allah don Izzar mulkinka ka kawo mini ɗauki! Allah kai ne gatana! Allah ga yarana ka kare su daga sharrin kishiyarta!"
Sosai mutanen wurin suka tausaya mata,duk rashin imaninka idan ka dubi yadda take gurshiƙeken kuka sai ka tausaya mata. A hankali maman Jawaheer ta duƙa tana duban Mairi ta ce
''Ki yi haƙuri 'yar'uwa! Wallahi muna nan da ke sai Allah ya saka miki zaluncin da suka miki!''
''Yanzu shikenan ina ji ina gani ta rabani ta mijina da yarana! 'yar'uwa ki duba wannan lamarin fa! Zuciyata zafi take kamar za ta fasa ƙirjina ta fito'' ta yi maganar tana riƙe daidai saitin zuciyarta. Hawaye suka cika idanun maman Jawaheer. Tabbas matar nan abar tausayi ce,a ce kana ji kana gani an rabaka da yaranka da mijinka saboda mugunta da rashin imani. Share hawaye Mairi ta yi sannan ta ce
''Ko Sallah ban samu damar gabatarwa ba balle maganar sauke haƙƙin cikina. Allah ka kawo mini ɗauki''
''Kar ki da mu zo mu je ɗakina ki yi sallah. Amma ke 'yar wace jiha ce''
Da ƙyar Mairi ta miƙe
''Daga Gusau na zo!" Ta furta tana share hawayenta
''Ikon Allah! Kin sha tafiya mai tsayi gaskiya. Ki bari zuwa gobe ki koma tun da yanzu dare zai yi. Tafiyar dare ga mace babu daɗi''
''To ina zan kwanan! Tun da abin da na zo don shi ban samu ba miye amfanin kwanana a nan. Kina kallo suka kulle ƙofarsu''
''Kar ki damu! Sai ki kwana a ɗakina tun da mijina ba ya gari!"
''To na gode!'' iya abin da Mairi ta iya furtawa kenan ta fara karatun zuci. Haka suka ci gaba da tafiya har suka isa block C7 room 20. Bayan Mairi ta rama sallolin da ake binta sai Maman Jawaheer ta kawo mata snacks da lemu kafin ta gama girki. Bata ci wani abin a zo a gani ba. Kwata-kwata bakinta babu ɗanɗano. Zuciyarta kacokar tana wurin yaranta. Jikinsu kawai ta gani ta gasgata ba su samun kulawa. Tana zaunen aka kira sallar Isha'i, matsar da robar snacks ɗin ta yi ta kurkure baki sannan ta kabbarta sallah,a duk sujjada sai ta daɗe tana addu'a kafin take ɗagowa.Maman Jawaheer ta kammala girkin sannan ta shigo ɗakin,da yake kicin ba haɗe yake da ɗakin ba. Farar shinkafa ta dafa sannan ta yi cabbage sauce. Ta zubo abincin ta kawo ta ajiye mata.
''Baiwar Allah sannu da ƙoƙari ni ban tambayi ya sunanki ba sai ɗawainiya kike da ni!" Mairi ta furta a sanyayen tana jawo plate ɗin abincin. Murmushi maman Jawaheer ta yi tana zama kusa da ita da plate a gabanta.
''Allah sarki! Babu komai wallahi! Ai yi wa kai ne! Duk wanda ka taimaka baka san watarana taimakon da zai maka ba! Ni sunana Maryam amma an fi kirana da maman Jawaheer. Yarana biyu suna Kano hutun boko, cikin satin nan za su dawo tun da an koma makaranta''
''Maa shaa Allah ashe takwarata ce! Allah ya raya su''
''Ameen ya Hayyu ya Qayyum!"
Daga haka ba su sake magana ba suka ci gaba da cin abinci,babu laifi Mairi ta ɗan ci abincin ba kamar snacks ɗin ba. Bayan sun kammala cin abinci maman Jawaheer ta tattara plates ɗin ta kai kicin ta kulle sannan ta dawo ɗakin ta zauna.
''Maman Yasir ki yi haƙuri da yadda Ubangiji ya jarabceki,in shaa Allah za ki ji daɗi nan gaba ke da yaranki. Kar ki manta Allah ba ya yafe laifin wani a kan wani daidai da ƙwayar zarra. Ki sha kuruminki wallahi sai Ubangiji ya yi ikonsa a kanta''
Tun san da maman Jawaheer ta fara magana hadari ya fara haɗuwa a idanunta,cikin ƙanƙanin lokaci hadarin ya fara zubar da ruwan hawaye. Jan majina Mairi ta yi tana share hawayen da suka fara zubo mata sannan ta dubi maman Jawaheer
''Maman Jawaheer baki san yadda zuciyata take zafi ba ne. Tun lokacin da Baban Yasir ya zo Gusau ya ɗaukesu ban sake samun lafiyayyen bacci ba har zuwa yau,kullum cikin zullumin a wani hali suke ciki. Zuwana yau na ƙara karaya duba da yadda suka koma kamar almajirai masu kamun yunwa. Hamida duk jikinta ƙujare ne kamar ƙazzuwa. Ta ya maman Jawaheer hankalina zai kwanta. Na san wannan ita ce ƙaddarata kullum idan na kai goshina ƙasa ina addu'ar Allah ya ba ni ikon cin wannan jarabawar. Amma da ciwo a zuci. Akwai raɗaɗi! Baki ji yadda nake ji ba ne"
Sauke ajiyar zuciya Maman Jawaheer ta yi sannan ta ce
''Babu komai akwai Allah. Ki kwantar da hankalinki in shaa Allah za ki yi farinciki nan gaba. In Allah ya yarda zan saka ido a kansu sosai tun da makarantarsu ɗaya da yarana,duk abin da ya dace na yi a kansu zan yi. Sannan zan san yadda zan yi ma Hamida maganin ƙurajen. Ki kwantar da hankalinki. Allah ba zai taɓa wulaƙantaki ba tun da kika dogara da shi. Sai ki ga cikin ruwan sanyi Allah ya tsiratar da yaranki daga kaidinta ba tare da kin yi wani yunƙuri ba. Ki ci gaba da addu'a domin Ubangiji yana amsa addu'ar wanda aka zalunta tata-izan da gaggawa ba tare da shamaki ba.''
Share hawayenta ta yi,sai a sannan hankalinta ya ɗan kwanta.
''Na gode maman Jawaheer! Allah ya saka miki da mafificin alkhairi ya bar zumunci. Bari na kwanta gobe sammako zan yi ''
''Ana tare. Ga wuri bismillah'' ta yi maganar tana nuna mana gadon. Babu musu ta kwanta,sai dai ta jima bacci bai ɗauketa ba,sai can cikin dare baccin ya ɗauketa. Washegari da sassafe Mairi ta wuce bayan ta karya kumallo. Maman Jawaheer ta rakata sannan ta dawo. Tunanin Mairi ya fi karkata ta wuce Mada madadin Gusau. Don har yanzu bata haƙura ba,sai inda ƙarfinta ya ƙare...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^
A ɓangaren su Sahura da safe bayan su Yasir sun kammala cika mata bokitai da ruwa sun zauna tare da su Hamid suna karyawa sai Sahura ta fito daga uwar ɗaka tana bambami ita kaɗai. Tana zuwa falon ta kamo Jalil lokacin ya kai biredi bakinsa kenan. Yatsunta biyar ta sauke a kuncinsa na dama tana zare masa ido tare jijjjigasa.
''Ba ni kuɗin da ka ɗauka a jakata! ɓawaron banza wanda ya gaji sata iyaye da kakanni.!''
''Wallahi ban ɗauki kudinki ba!" Ya furta a sanyaye yana zubar hawaye.
''Ƙarya kake dan uwarka! Waye a gidan nan yake sata idan ba kai ba! Na shiga ɗaki na buɗe jaka zan ɗauki ɗari biyu na rasa! Wallahi yau sai na yi maka dukan mutuwa! Shege ɗan tsinanniya!'' tana fadin haka ta sake shi tare da shiga kicin tana dube-dube. Bakin Dauda Imamu ɗauke da magana amma babu damar furtawa,ya san babu wanda zai ɗaukar mata kuɗi a jaka sai ɗanta Hamid domin shi da kansa ya kamashi hannu dumu-dumu. Ɗauke idanunsa ya yi daga kan Jalil da ke kuka zuciyarshi na ƙuna, yaran ɗakin kowa ya yi tsuru-tsuru musamman Hamid da ya san shi ya buɗe jakarta ya ɗauki kuɗin. Sosai Jalil ke kuka saboda bai san mene ne sata ba balle ya yi. Yana tsaka da kukan Sahura ta fito daga kicin hannunta riƙe da muciya. Jalil na ganin ta tunkaro shi ya ruga da gudu ya bar flat ɗin gabaɗaya ko takalmi bai tsaya sakawa ba. Cike da takaicin ya bar gidan ta juyo kansu Yasir
''Ku tashi ku je makarantar a haka! 'yan iska ɗan uwanku ya ja muku! Ba za ku karya ba! 'ya'yan ya ku bayi masu ƙarshin tsiya kawai!" Ta faɗa cike da tsawa. Kafin ta kai karshen maganar sun sunkuci jakukunansu suka yi waje. Yasir ko quarter na biredin bai yi ba,ga jiya taƙi ba su abincin dare wai uwarsu ta ja musu. Hamida kam kuka ta saki lokacin da suka fito domin fara shan shayinta kenan Sahura ta kaɗo su. Tun jiya take fama da ciwon ciki. Haka Yasir ya riƙo hannun Hamida suka wuce makarantar. Daman ba kuɗin break ake ba su ba balle su saka rai. Yaranta nairi goma take ba kowanne har da Nu'aymah da take nursery.
^^^^^^^^^^^^^^^^^
Tafiya motar take a hankali. Mushin sanye da kayan makaranta yana zaune a kujerar gaba,mahaifinsa ke tukin motar yau kasancewar ya samu pass na sati biyu. Flying officer ne mahaifinshi,suna zaune a G.R.A da ke cikin barikin sojojin inda manyan sojoji ke zaune da iyalansu. Suna tsaka da tafiya,Mushin ya hangi Jalil zaune a ƙarƙashin bishiyar mangwaro yana kuka,sai waige-waige yake kamar yana neman wani abu. Ajinsu ɗaya da Jalil,tun ranar da Jalil ya fara zuwa jininsu ya haɗu. A gida bai da magana sai na Jalil kishiyar mamanshi bata sonshi,iyayen Muhsin ba su ɗauki maganar shi da muhimmanci ba duba da ƙarancin shekarunsa.
''Dad! Dad! Ga Jalil can yana kuka da uniform ɗin makaranta!" Ya yi maganar yana nuni da hannunsa. Ɗan kallon wurin mahaifin Muhsin ya yi sannan ya samu wuri ya yi parking suka fito. Da sauri Muhsin ya ruga wurin Jalil yana kiran sunansa. Jalil da ke sharɓar kuka yana waige-waige ko zai ga Ammunsa ya juyo jin muryar abokinsa Muhsin da ke ba shi abinci lokacin breaktime. Tahowa ya yi yana share hawayensa har suka haɗu, mahaifin Muhsin na biye da shi.
''Jalil me ya sa kake kuka? Ina jakar makarantarka? Ina takalminka?" Muhsin ya jero masa tambayoyo cike da tausayi. Share hawayensa ya sake yi sannan ya ce
''Baaba Sahura(sunan da suke kiranta)ce ta ce na ɗaukar mata kuɗi alhalin Hamid ne ya ɗauka. Jiya ma taƙi bamu abinci da daddare saboda Ammuna ta zo tafiya da mu. Yau ma ina cikin cin abinci ta kamani da duka''
Muhsin ya yunkura zai yi magana suka ji muryar Dad.
''Subhanallah! Mahaifiyarka ta rasu ne? '' Mahaifin Muhsin ya tambaya yana ƙarasowa inda suke,da yake ya ji duk abin da Jalil ya faɗa
''A'ah! Jiya ta zo ɗaukarmu Baaba Sahura ta hana Abbanmu barinta ta ɗaukemu. Har marin Ammuna Abba ya yi tare da tunkuɗeta ta faɗi. Ya koramu falo ya kulle ƙofar ya bar Ammuna a ƙasa tana kuka'' cewar Jalil cikin shessheƙar kuka. Sosai tausayin Jalil ya dabaibaye zuciyar mahaifin Muhsin.
''Zo mu shiga mota ka kai ni block ɗinku'' ya yi maganar yana nufar motarsa. Biyo bayansa suka yi hannunsu maƙale. Wannan karon Jalil ne ya zauna a gaban motar suka ci gaba da tafiya. Yana nuna masa hanyar da zai bi har suka iso ƙofar flat ɗinsu. Tare suka fito Jalil ya fara yin gaba. Lokacin Sahura ta buɗe ƙofar za ta block ɗinsu maman 'yar gayu. Tana ganinsa ta murtuke fuska
''Dan kutumar ubanka me ka dawo yi! Tsinanne dangin tsinannu! Ai daman na san za ka dawo ɗan gidan abun kwari! Oleh ɓarawo! Idan na riƙeka sai na kusa kasheka! Maii...''
''Malama ina mijinki!'' cewar mahaifin Muhsin a ɗaure don kunnuwansa ba za su iyar ɗaukar waɗannan muggan alkaba'in ba. Sai a sannan Sahura ta lura da su.
''Yana ciki" ta furta da sanyin murya
''Yi masa magana don Allah'' ya furta kafin ta sauke numfashi don wata tsanarta yake ji,a rayuwarsa ya tsana ya ga ana cin zarafin yara. Babu musu ta juya zuwa falon ta kira Dauda Imamu zuciyarta na saƙe-saƙe, a tare suka fito. Dauda Imamu na haɗa ido da mahaifin Muhsin ya washe baki tare da ƙarasowa wurinsa da sauri yana miƙa hannu. Gaisuwa ta mutuntawa suka yi sannan mahaifin Muhsin ya dubi Jalil sai ya juyo ya ce...✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_024_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
Babu musu ta juya zuwa falon ta kira Dauda Imamu zuciyarta na saƙe-saƙe, a tare suka fito. Dauda Imamu na haɗa ido da mahaifin Muhsin ya washe baki tare da ƙarasowa wurinsa da sauri yana miƙa hannu. Gaisuwa ta mutuntawa suka yi sannan mahaifin Muhsin ya ɗan dubi Jalil sai ya juyo ya ce
''Wannan ɗanka ne Imam?"
Da sauri Dauda Imamu ya furta ''Eh officer Kabir''
Gyara tsayuwa mahaifin Muhsin ya yi sai ya ɗan kalli Jalil sannan ya sake duban Dauda Imamu
''Imam zan iya neman alfarma a wurinka?"
''Haba officer! Faɗi alfarmarka ni kuma in shaa Allahu indai bata fi karfina ba zan yi maka''
Murmushi mahaifin Muhsin ya yi sannan ya ce
''Ina son yaranka Jalil ya dawo wurina da zama idan babu damuwa. Ni kuma in shaa Allah zan rikesa kamar ɗan da na haifa. Na yi alƙawarin zan ɗauki nauyin cinsa,shansa,lafiyarsa, tufafinsa da karatunsa tun daga primary har babban makaranta sannan zan samar masa da aikin yi da yardar Allah idan da rai da lafiya. Wallahi Kallo ɗaya na yi ma Jalil na ji ya kwanta mini a rai.''
Da matuƙar ƙarfi ƙirjin Sahura ya yi mugun bugawa, jikake Daram! Dam! Dadam! wani irin hajijiya ta ji yana niyyar kai ta ƙasa amma ta dake. Furucinsa bai tsaya a haka ba ya rikiɗa zuwa bingida yana harbin ko'ina na zuciyarta. Yau ake yinta wai tsohuwa ta ga ranar mutuwarta. Take baƙinciki da hassada suka mamaye zuciyarta,don daga kallon tufafin sojan ta san babba ne kuma da alamu yana da ƙumbar susa. Murmushi Dauda Imamu ya yi,sosai ya cika da farinciki mara misaltuwa.
''Na yarda kuma na amince officer. Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci. Ban san yadda zan kwatanta irin farincikin da nake ciki ba. Na gode! na gode!"
''Babu damuwa zaman taren kenan. Yarona bai da magana sai na Jalil kasancewar ajinsu ɗaya a boko. Ammm! Ina jakar makarantarsa da takalmin bokonsa?''
''Suna ciki bari na ɗauko har da kayan sawarsa'' cewar Dauda Imamu cike da zumuɗi. Da sauri mahaifin Muhsin ya ce
''Ban da kayanshi Imam,idan ya dawo daga makaranta zan dauke shi zuwa plazar da ake mana ɗinki a gwada shi daga nan sai na ƙaro masa da 'yan kanti. Yanzu dai takalminsa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 33