jikinta ya fashe. Kallon HAFIZA Dauda Imamu ya yi, lokaci ɗaya ya waro idanunsa,shi bai ma lura da ita ba a lokacin da ya shigo. Ransa a matuƙar ɓace ya kalli Hamid
''Me ta maka da za ka mata irin wannan dukan'' yana tsaresa da kaifafan idanunsa. Dukar da kansa Hamid ya yi don bai san amsar wannan tambayar ba. Ya dai san ya tsani yarinyar sai kuma ganin tana ma 'yar'uwarsa faɗa. Sahura ta bude baki za ta kare shi da ƙaryar da ta sa ba,Maryam ta rigata da furta
''Baba ba laifin HAFIZA ba ne,ni ce na yaga mata drawing books ɗinta,tana mun faɗa sai Hamid ya fara dukanta mama tana cewa ya ƙara mata. Ina ta roƙonsa shi da mama amma suka kyale ni'' ta kai ƙarshen maganar cike da yarinta. Kallonta yake ba ya ƙafta ido. Zai yi magana Aunty Saudah ta shi falon kamar an hakaɗota. Take Sahura ta zabura tana dafe ƙirji da hannu bibbiyu.
''Ni Sahura me zan gani!....✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*_Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️_*
07050959771
*_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_044_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
Take Sahura ta zabura tana dafe ƙirji da hannu bibbiyu.
''Ni Sahura me zan gani! Aunty Saudah! Hatsari kika yi?!'' Ta matso kusa da ita tana bin fuskarta da kallo. Babu wanda a cikin ɗakin hankalinsa bai ɗaga ba idan ka cire Dauda Imamu. Tun da ya mata kallo ɗaya bai kuma ba, hasalima matso da HAFIZA ya yi yana duba jikinta. Cikin shessheƙar kuka na wacce Ya jima tana rairawa ta furta
''Mama dukana ya yi! Ya ce mini na zo gidansa da farar ƙafa! Wai tun da ya aure ni ake yin nasara a kansa, duk cacar da zai shiga sai an cinyeshi! Mama har gidan da nake zaune ya saka a caca aka cinyeshi,shi ne cikin dare ina kwanshe ban san hau b ban san sauka ba ya kamani da duka yana ce mini mai ƙashin tsiya! Mama ba zan iya zama da shi ba! Ya daina sona da tarairayata, kullum cikin zagi da hantarata yake! Wai na haɗa kayana idan ya dawo zai saka ni a matsakin gida! Mama ki...''
Dauda Imamu ya katsets da murya mai cike da tsauri da hargowa
''Kin isa! Ai tun da kika ce sai shi to wallahi sai kin zauna da shi...''
A harzuƙe Sahura ta katse shi da cewa
''Wallahi ba zan yarda ba! Kalli yadda ya sauya fuskar ɗiyata ka ce sai ta koma..."
Nunata ya yi da yatsarsa manuniyya yana karkaɗe hannu tare da ƙanƙace ido ya furta
''Ki shiga hankalinki! Idan ba so kika na haɗa dake na koraku ba,ki fita a idona na rufe! Ni ba mutumin ban za ba ne! Ta koma ɗakinta tun da ba wani ya zaba mata shi ba! Tsuntsun da ya kira ruwa! Shi ruwa kan doka! Idan kika bari na dawo gidan nan na isketa za ki sha mamakina! Sai na nuna miki yadda ake jajjagen jaraba mai lasisi. Jalil mu je'' ya ɗauki hijab ya saka ma HAFIZA suka wuce. Suman tsaye Sahura ta yi tana bi kofar da suka bi da kallo. Abubuwa uku suka cure wuri guda suna farmakar zuciyarta: matsalar gidan Aunty Saudah,auranta da ke shirin tangarɗa ga babban da yafi kowanne kasa mallakarsa a wannan karon da ya fi kowani lokaci muhimmanci. Mutuwar Mairi bai amfaneta da komai sai ƙarin ƙunci da takaici.
''Mama yunwa nake ji'' maganar Aunty Saudah kenan da ta farautota daga duniyar tunani. Sake bin fuskarta ta yi da kallo. Fuskar ta kumbura ga shatin yatsu da suka ƙawata kumatun gefe da gefe. Nan da nan tausayin 'yarta ya mamaye zuciyarta. Zuwa wurin malamints ya tashi,ba za juri ganin 'yarta tana azbtuwa a hannun wani banza da bai san zafin haihuwarta ba.
''Halima zuba mata abinci,bari na je block ɗinsu maman 'yar gayu na dawo yanzu,kai kuma ga kuɗi ka je a wanke goshinka'' ta miƙa masa dubu daya tajuya zuwa uwar ɗakanta. Kai zaune Aunty Saudah ta yi cikin kujerun ɗakin tana cije laɓenta na gefe da ƙarfi,ilahirin jikinta tsami yake mata. Aunty Saudah bata san daɗin aure ba tun da ta shiga gidan,a satin farko sun sha soyayya kamar babu gobe. Da tafiyar ta fara nisa komai ya sauya, daɗaɗan kalamansa suka koma masu zafi da tsauri,annurin fuskarsa ya yi ɓatan dabo musamman idan yana gidan. Hakan ya samo asali ne tun shiga caca da aka yi a Abuja ya saka babban gidan gonar ya faɗi warwar,ya kuma shiga wata cacar nan ma kamar mai bakin uwa aka ci shi. Duk faduwar da ya yi idan ya dawo gidan a kanta yake sauke fushinsa,magana ɗaya biyu sai ya kai duka. Wayar da ya siyan mata kafin su yi aure ya canja mata da mai botiri ya amshi wannan. Ana cewa aure yana gyara mace,amma ga Aunty Saudah lalacewa ta yi ta rame kamar mai ciwo. Kasa cin abinci ta yi duk da yunwar da take ji,ta zuba masa ido kamar mai nazartar wani abu a ciki abincin.
Gudu-gudu sauri-sauri Sahura ta isa block ɗinsu maman 'yar gayu. Ita kaɗai ta samu a ɗakin tana jin waƙar Ado Gwanja na Kujerar Uwar gida. Yanayin da Sahura ta shigo ɗakin ya sakata kashe kiɗin babu shiri.
''Maman Hamid lafiya" ta faɗa tana matsowa inda take.
''Ina lafiya fa Maman 'yar gayu! Aunty Saudah ta dawo gida, miji ya mata duka sannan ya ce zai komar da ita karamin gida.! Abin tashin hankalin Baban Hamid ya ce kar ya dawo gidan ya sameta'' ta fada tana share hawayen da suka gangaro mata.
''Toooo! Babbar magana! Yanzu ya za a yi! Ni na ma rasa abin faɗa"
''Zuwa gidan Malam Tsalha Mai yasin ya kamani gobe! Ba zan ɗauki rainin hankali ba! Duka fa maman 'yar gayu! Tun da na haifi Aunty Saudah ban taɓa buɗar baki na mata faɗa ba balle a kai ga duka! Lallashi ne ke shiga tsakanina da yarana! Haka kurum gabjejen ƙato ya hau ɗiyata da duka! Inaaaaa!"
''Mu je na rakaki goben! Dole mu ɗauki mataki babba! Ni ba na manta ba jiya na kira na sanar miki 'yar gayuna ta haihu,an samu ɗa namiji'' ta faɗa tana yin murmushi mai faɗi. Washe haƙora Sahura ta yi tana furta
''Ki ce mun samu zankaɗeɗan miji? Allah ya raya ya ɗayyaba. Gobe da safen idan na shirya zan biyo miki. Bari na je gida kafin baban Hamid ya dawo'' ta faɗa tana miƙewa. Sallama suka yi ta bar ɗakin. Shekara ɗaya kenan da auran 'yar gayu,a can garin iyayen Maman 'yar gayu ta samu miji bayan ta kammala secondary school aka sha biki.
A can gida,Aunty Saudah na zaune ta kafa uban tagumi tana tunani kunnuwanta suka tsinkayo mata sallamar mahaifinta. Kamar wacce aka tsikara da tsinin allura,zurum ta miƙe tana rarraba ido. Suna tozali ya ɗaure fuska yana ƙarasowa cikin falon a bayansa HAFIZA hannunta riƙe da ledar magani. Idanunsa a kanta ya furta
''Me na faɗa miki?"
Muryar mai cike da rawa Aunty Saudah ta ce
''Ka....kaaa yi haƙuri babaaaa!" Sai kuma ta rushe da kuka. Ko kaɗan bai ji ɗigon tausayinta a cikin ƙoƙon ransa ba,abin da ya hangan mata kenan amma ta rufe idanunta ita mai soyayya. Kallo mai cike da kashedi ya mata
''Kafin na ƙirga u...''
Sahura da shigowanta kenan falon ta katse shi da murya mai cike da damuwa
''Ka yi hakuri Baban ta zauna ko na sati ɗaya ne?"
''Da wa kuma a ina?!'' ya juyo yana ware idanunsa a kanta.
''Da kai kuma a gidanka mana baban Hamid"
Murmushi ya yi, murmushin da ba na farinciki ba sai na tarin takaici da dana sanin auranta tuun a farkon fari.
''HAFIZA je ki ɗaki ki canja kaya ki sha magani. Ke kuma ina zuwa'' ya fada yana wucewa uwar ɗaka,fin minti ɗaya ya fito da ƙatuwar dorinar da yake hukunta ɗalibai marasa ji musamman maza. Kanta ya yo gadan-gadan, zabura ta yi ta ruga wurin mahaifiyarta tana ci gaba da kuka. Bayanta ta koma tana sharɓar kuka kamar ƙaramar yarinya. Kakkareta Sahura ta yi da hannayenta tana faɗin
''Haba Yaya Imamu me kake shirin yi?"
''Wallahi idan baki matsa daga wurin ba sai na haɗa dake"
''Wasa kake wallahi! Ina matsayin ma...''
Ta ji Tsuuu! A hannunta,take ta kwarma ihu tana fadin
''Wayyo Allahna! Da gaske baban Hamid kake dukana za ka yi''
Ba tare da ya bata amsa ba ya sake ɗaga bulalar da iya ƙarfinsa, kafin da sauka a kan Aunty Saudah ta matsa sai ta samu Sahura a allon bayanta. Take ta banƙare kamar banƙararriyar kaza,raɗaɗi da zugi suka mamaye illahirin allon bayanta. Sake ɗaga bulalar ya zai kai ma Aunty Saudah bugu da ke ɓoye a bayanta ya sake sauka akanta.
''Na shiga uku ni Sahurar Gwaggwon Bugaje! Wannan jaraba har ina!"
Ba tare da ya ce komai ba ya saita bulalar ya zubama Aunty Saudah,nan take ta saki gigitacciyar ƙara tana ambaton
''Wayyo Allah mama bayana''
''Kki yi takanki Aunty Saudah aljanun yaya Imamu sun tashi'' ta faɗa tana barin wurin a sukwane. Ganin da gaske mahaifinta yake,ɗaukar mayafinta ta yi ta saka takalmi ta ruga waje a sittin. Tsaki mai tsayi ya ja yana yin ƙwafa. Halima da Nu'aymah da ke leƙensu suka ruga ɗakinsu da gudu. Mayar da bulalar ya yi mazauninta sai ya ɗauki littafin ba tare da ya kalli Sahura da ta barbaje a gado ta saki fanka ya wucewarsa. A ransa yana fadin 'Gobe ki ƙara shiga sabgata ki gani' Ko a mafarki bata yi tunanin baban Hamid zai iya ɗaga hannu ya dake ba balle da bulala. Tana kwancen ta lalubi wayarta ta kira Gwaggwon Bugaje,a bugun farko ta ɗaga. Shessheƙar kukan da ta ji Gwaggwon Bugaje tana yi ya sakata saurin tashi daga kwancen. Hankali a matukar tashe ta ce
''Gwaggwo lafiya? Mutuwa aka yi!"
A can Gwaggwon Bugaje ta ja majina mai kauri ta ce
''Idan mutuwa ce wannan da sauƙi a kan tashin hankalin da muke ciki ni da yan'uwanki!"
Ƙirji Sahura ta dafa tana furta
''Ni 'yasu meke faruwa daku Gwaggwo?!''
Sai da Gwaggwon Bugaje ta sharce majina sannan ta ce
''Cikin shege Naja'atu (autar Abida yayar Sahura ta biyu )ta yi, Abida bata sani ba har ya bayyana. Unguwa kowa ya san da cikin. Abin ban takaicin wai mai gadin makarantar bokonsu ya ɗirka mata. Ni Maimunatu ina zani da kayan kunyaaaaa!" Ta sake rushe da kuka mai sauti har da shessheƙa. Tashin hankalin da Sahura ta shiga baya fassaruwa,wannan abin kunyar har ina.
''Gwaggwo ina tunani da hankali yaya Abida ya shiga ta aikata wannan abin kunyar? Yanzu shikenan Naja'atu ta kawo mana abin kunya har gida. Ta rasa wanda za ta buɗe wa ƙofa sai mai gadi! Amma an yi 'yar ƙwal uba! Zan kira Yaya Abida anjima na jajanta" Ta katse kiran. Wayar Aunty Saudah ta kira bugu biyu da ɗauka. Ba tare da sun gaisa ba Sahura ta ce
''Kin wuce gida ne?"
A can Aunty Saudah ta ce
''Eh mama!"
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,abu mai kauri da ɗaci kamar maɗi yana tokare mata wuya. A hankali ta furta
''Ki kwantatr sa hankalinki! Indai ina raye babu ke babu yin kuka a gidan miji. Gobe zan je wurin malamina. Duk abin da ake ciki zan kira na sanar miki''
''To mama na gode''
Katse wayar Sahura ta yi sakamakon kukan da ya taso mata saboda tausayin babban 'yarta.
Kwata-kwata Sahura bata da walwala har dare. Su Ɗayyaba da sauran yaran suke kai kawo abinsu. Ta shige ƙuryar ɗakin tana karatun zuci. HAFIZA bata fito falon ba tana ɗaki. Duba sabbin kayan zanen da Yaa Jalil ya siyo mata take fuskarta ɗauke da murmushi. Ainihin kayan zane na artist for beginners ya yi tattaki zuwa centra market ya hado mata su. A ƙarkashin gadonta ta ajiye su.
^^^^^^^^^^^
*Ƙarfe 10:12pm na dare*
A wannan lokacin Sahura da Dauda Imamu suna kwance a gado,ba su yi bacci ba, kowanne yana karanta wasikar jaki a ransa. Sun daɗe a haka Dauda Imamu ya katse shirun da cewa
''Jiya da yau abubuwan akwairai suka ta shigowa cikin rayuwata silar yarana''
Murmushi kwance a fuskarta ta ɗan kalli inda yake kwance ta ce
''Haka nake fata kullum a kodayaushe. Wasu abin alkhairai muka samu Yaya Imamu?"
A hankali ya tashi daga kwancen ya jingina da gadon,idanunsa a ɗan rufe ya furta
''Na farkon abin da ya saka ni farinciki,ɗazu bayan na idar da sallah ina tare da Jalil lokacin aka kirani daga makarantar haddarsu HAFIZA. An tsayar da ita a matsayin wacce za ta wakilci Nijeriya a gasa Alqur'ani ta mata ta Duniya da za a yi a ƙasar Jordon nan da watanni takwas masu zuwa in shaa ALLAH. Ya faɗa mini ita ce mace ta farko mai karancin shekaru da za ta wakilci Nijeriya a gasar.Ashe tun lokacin da ta shiga makarantar ake tafiya da ita musabaƙa a cikin Kaduna amma bata taɓa faɗa mini ba saboda mislitanci irin nata! Malamin ya ce daga hukumar masu tashe Hafizai suka tsayar da ita bayan tantancetan da suka yi,zuwa gobe zan je tare da ita makarantar daga can za mu wuce ofishin hukumar da ke Rigacikun za su karɓi bayanai daga wurina. Kai Alhamdulillah tabbas HAFIZA ta daban ce!"
''Uhmmm! Ya yi kyau! Sai kuma wani abun alkhairin ne ya kara samunka?" Tana tashi daga kwancen ta ɗan fuskanceta,fuskarta babu yabo babu fallasa. Ba tare da damuwa da amsar da ta ba shi ba ya ɗora da faɗin
''Sai na biyun. Bayan na kammala waya da malamin na yi masa godiya,sai Jalil yake sanar mini gobe in shaa Allah za su wuce makarantar sojoji ta NDA shi da ɗan uwansa Muhsin. Ashe tuntuni Officer Kabir yake ta kai kawo yana nema musu NDA bai faɗa mini ba,shi ma Jalil ya yi gum da bakinsa ya bari ya mini bazata ta yadda zan yi farinciki sosai. Wallahi kamar ya shiga cikin ƙoƙon raina,na shiga farinciki irin wanda ban taɓa riskar kaina a ciki,ga shi farincikin ya haɗe da na gasar da HAFIZA za ta je ta duniya a ƙasar Jordan. Kai Alhamdulillah!''
Tun da ya fara magana ta kafeshi da manyan idanunta. Bata taɓa shiga cikin ƙunci da bakinciki kamar a yanzu ba. Me yake nufi da waɗannan labaran da yake bata masu kama da tatsiniyoyi. Kenan maganar Mairi da take cewa yaranta za su ɗaukaka a kan nata yaran maganarta ta tabbata 'Kai Ina wallahi da sake' ta furta a ranta. A zahiri ta ce
''Amman shi ne ko ka kara Hamid a nema masa makarantar sojojin. Da yake Jalil ɗan so ne ai gashi an samarsa masa! '' ta kai ƙarshen maganar da yin ƙwafa.
''Ikon Allah! Sai aka ce miki ni da kaina na samar masa! Ko kin manta wanda yake rikonsa ne! Yau fa na san da tafiyarsa! Daman na san abin da za ki faɗa kenan! Na gani dai duka yaranki ne idan da kara amma! Ke ce farkon da za su duba a matsayin uwa tun da mahaifiyarsu bata raye!"
Fuska ta yatsina alamar Allah ya tsare ɗin nan. Can kuma ta ce
''Wai su kenan abin alkhairan da ka samu ko da wasu?"
Girgiza mata kai ya yi yana faɗin
''Sai kuma na auran 'yan matanki guda biyu?"
Ɗan ware ido ta yi a kan fuskarsa
'' 'Yan matana! Amina da Halima? A ina suka samu miji?"
A kaikace ya kalleta sannan ya juyar da fuskarsa yana faɗin
''Amina dai da Hamida! Wancan satin wani daga cikin ɗalibai masu girmamani ya zo neman auran Amina. Ya kammala Islamic Education a ABU Zaria. Yanzu haka yana koyarwa a Kulliyatul Banaat. Sunansa Haruna. Yana da kirki da sanin ya kamata,ɗan kawo ne. Ita Hamida jiya bayan sallar juma'a wani daga cikin sojojin da nake mutunci da su ya ce yana son haɗa zuri'arsa da tawa. Babban soja ne mai muƙamin Air commodore,sunansa Yakub, star ɗaya garesa sannan yana da mata da yara uku. Ya suffanta mini ɗaya daga cikin yarana. A nan na fahimci Hamida yake nufi tun da anbaci Fara mai manyan idanu da ƙiba...''
Da sauri Sahura ta katseshi da faɗin
''Ko dai Amina yake nufi! Suffar da ka ambata ai Amina ke da su''
Kallon mamaki ya bita da shi
''Kin dai fadi ra'ayinki ne amma Hamida ce keda irin suffarsa da ya ambata. Don na sake tabbatarwa na ambaci Hamida ya ce ita yake nufi''
''Yau ne na san wane ne nake zaune da shi! Baban Hamid! Kamar da yarana saniyar ware ko! A gabana kake fifita yaran Mairi a kan nawa! ''
''Haba Sahura! Daidai da rana ɗaya ban taɓa tunanin fifita yaran Mairi sama da naki ba idan za ki yi mini adalci. ''
''Ba ga shi nan ba! Ƙiri-ƙiri za ka kai Hamida gidan hutu. Ɗiyata ga malamin islamiyya. Ba komai''
Shi dariya ma maganar Sahura ta ba shi. Sai kawai ya ce
''Ni dai zuwa gobe ki sanar ma Hamida ta shirya zai zo su gaisa,ba zan samu ganinta ba. Daga sallar asuba ba zan dawo gidan ba,tun ɗazu na sanar ma HAFIZA idan ta shirya ta sameni a makaranta mu wuce.''
''To'' ta faɗa tana kwanciya ta juya masa baya, kwanciyar ya yi yana lumshe ido. Bacci ya ƙaurace idonta. Saƙa take tana warwarewa,dole ta ɗaga tafita wurin malam Tsalha Mai yasin zuwa yamma lilis lokacin sojan ya zo sai Maman 'yar gayu ta rakata. Duk yanda za ta yi Amina ce za ta auri sojan,daga jin muƙaminsa ta san yana da ƙumbar susa. Ba za ta bari Hamida ta ganshi ba balle su daidaita. Lallai akwai tarin matsalolin da za ta kaima Malam Tsalha Mai yasin. Ko za ta tafi tsarara sai ta hana HAFIZA zuwa gasar. Jalil kuma ta san muguntar da za ta ce a mishi. Kwanciya ta gyara tana sakarwa kanta murmushin. Babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.
^^^^^^^^^^^
*Washegari*
*Ƙarfe 8:10am na safe*
A wannan lokacin Sahura ta aiki Hamida central market ta mata siyayyen yadikan hijabai daga can sai ta wuce Kasuwar bacci a ɗinkasu. Da gangan ta aiketa saboda har sojan ya zo ya tafi bata gidan,har da kuɗin abinci ta bata kar ta ji yunwa idan ta daɗe. Kudin Hamida ta amsa ta koma ɗaki ta shirya sannan ta wuce,Sahura har da mata Allah ya tsare hanya. Tun da wuri HAFIZA ta wuce makarantarsu Abbanta daga daga can suka wuce . Sosai Sahura ta natsu tana duban Amina da ke kwance a saman doguwar kujerar ɗakin
''Tashi ki yi maza ki shirya. Kina da baƙo! Babban soja ne mai muƙami,sunansa Yakubu,jiya babanku ya ce wurin Hamida zai zo,shiyasa na aiketa da wuri don ku gana. Na san za ta jima a can,har ya tafi ba zai ganta ba. Ni natsu sosai ki nuna masa ƙauna ta haƙiƙi,kisisinar da nake koya muku lokacin amfaninta ta zo. Kayanki na kasan akwati za ki saka kin ji 'yar albarka''
''Too mama yanzun nan kuwa" ta mike da tsananin farinciki da ke bayyane a saman fuskarta. Jinjina Ɗayyaba ta mata tana faɗin
''Wannan shi ne daidai yaya Sahura! Gwara da kika kora shegiya!"
Murmushin Sahura ya faɗada har hakoranta na bayyana. Za ta yi magana Hamid da tun daga sallar asuba bai dawo gidan ba ya shigo da ihu yana furta
''Na yi waya!" yana ɗaga ledar da ke dauke da kwalin waya. Waro ido Sahura ta yi saboda tsantsar murna
''Da gaske ɗana!"
''Wallahi kuwa. Ɗazu bayan sallar asuba abokina ya kira ni. Ina zuwa block dinsu ya mika mini'' yana fada yana zama kusa da ita.
''Kai amma kuwa na ji daɗi. Allah ya tsunduma yaron nan a gidan aljanna''
Cike da jin daɗi ya ciro kwalin wayar ya hadata a gabansu ya kunna sannan ya miƙa mata. Hannunta na rawa ta amsa wayar,daga gani tasan mai tsada ce. Ta duddubata sosai ta miƙa ma Ɗayyaba. Ita ma ta yi murna sosai da wayar. Samsung Galaxy S20 ultra ce wayar,'yan Yahoo sun fi amfani da irinta saboda ƙarfin network ɗinta. Sahura ta yi addu'a sosai. Sake jaddada mata yake ''Mama kar ki bari baba ya san sana'ar da nake,haushi zai ji ya hanani saboda su Jalil ba su iya ba. Kwanan nan zan yi ƙudi na siya miki babban wayar da zinari''
''Har da zinari ɗana!'' tana ware idanunta a kansa tsabar mamaki. Jinjina mata kai ya yi. Nu'aymah da ke bayan kujera tana tsaye ta saka hijab hannunta riƙe da littafi ta ce
''Mama zan je na kaima kawata littafinta da na ara''
''To Nu'aymah a dawo lafiya''
''Ameen'' ta yi gaba abinta. Ɗaki ya kai wayar sannan ya dawo aka ci gaba da hirar tare da dashi. Fada musu maƙuden kuɗaden da ake samu a harkar yahoo yake,su kuma sai washe baki suke kamar gonar audiga, musamman uwar gayya Sahura da take ganin watan jin daɗinta yana gab da kamawa. Babu jimawa Amina ta fito sanye cikin riga da skirt ɗammanmu sai tashin ƙamshi take,har da yafa gyale a saman ɗankwalinta da ya ji daurin zamani wanda ake yayi. Ta yi matukar kyau sosai. Kowa sai yaba kyawunta yake har ta kai ga zama aka ci gaba da hirar tare da ita.
^^^^^^^^^^
Madadin Nu'aymah ta bi hanyar gidan ƙanwarta da tace za ta kai mata littafi,hanyar da zai sada ta da tantuna na sojoji ta nufa wanda yake a karshen blocks din barikin. Unguwar shiru babu motsi da hayaniyar komai da na sautin kukan tsintsaye. Tun da ta je unguwar bata haɗu da mutum daya ba. Ta iso kusa da tantunan ta hadu da wani soja wanda ba zai wuce shekara ashirin da huɗu mai matsakaicin kyau ya yi tsaye yana kallon hanyar da take bi . Suna hada ido ya sakar mata sassanyen murmushi alamar sun san juna. Tana isowa inda yake ya riko hannunta suka ci gaba da tafiya har zuwa wani tanti da ke ƙarshe. Ciki suka shiga ya zuge zip ɗin tantin ya saka kwaɗo. Juyowa ya yi yana sakar mata murmushi. Musa sunansa dan jihar Sakkwato. Sahura na matukar shiri da shi. Idan ta haɗu dashi sai ta ce ɗan garinmu ya kaza ya kaza. Ya san gidansu don Dauda Imamu ma ya sanshi sosai. Yana yawan ba Nu'aymah da Maryam kuɗi idan ya gansu a hanya. Har ta kai musamman Nu'aymah take zuwa inda suke gadi idan an tashi boko ta roƙesa kuɗi. Ganin Nu'aymah na da mugun kwaɗayi ya sa ya yi amfani da wannan damar. Ya ce mata idan tana son kuɗi mai yawa ta zo inda yake a ƙarshen blocks ranar lahadi da safe ta amsa. Ya yi mata kashedin karta faɗa wa koya. Cike da murna ta ce masa to. Da yake a ranar Alhamis suka haɗu,sai ta yi ta alla-alla lahadi ta zo ta je wurinsa. Musa ya fadi lahadi ne saboda a ranar sojoji Christian suna zuwa church. Musulmai kuwa dukkaninsu suna wajen aiki. Matsowa ya yi kusa da ita yana faɗin
''Nu'aymah sarauniyar cika alƙawari! Na za ci ba za ki zo ba''
Da murmushi a fuskarta tana kallon ƙasa ta ce
''Ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 33