Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba,zaman lafiya da kwanciyar hankali su yi maka hijira' . Sauke ajiyar zuciya ya yi yana ambaton sunan Allah a ransa...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^^ *Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya* Zaune suke a falon suna musaffar Al'qur'ani mai girma. Idan Yasir ya sauke aya ɗaya,sai Jalil ya ɗauki ta kusa ta ita,yayin da yana kai ƙarshe Mairi za ta ɗauka amma ita tana duba Al'qur'ani saboda bata da hadda,Hamida ma da kai take kawowa kasancewar daga suratul Nasi suka fara. Da HAFIZA na nan da har da ita za a yi musaffar. Sosai suke karatun cike da natsuwa da ƙwarewa. Makarantar da suke zuwa hadda ba su da wasa,suna da tsauri sosai,daɗin daɗawa sun yi dacen uwa wacce take tsaye a kan tarbiyyarsu da karatunsu. Bata wasa da karatunsu musamman na islamiyya da Hadda,kullum cikin musaffar Al'qur'ani suke. Har ya fara bin jikinsu. Sun fara musaffar bayan sun dawo daga islamiyya wuraren ƙarfe 10:15am na safe,bayan sun cire kayan islamiyya suka fara karatun. Sai wuraren 12:01pm na rana suka tsaya da karatun,zuwa lokacin sun yi izu ɗaya a musaffar. Mairi ta wuce kicin ɗaura girkin rana. Yasir ya ɗauki littafinsa ya fara rubutu, Jalil ma haka,duk surar da suka hadda sai sun rubuta sun kai malamarsu ta yi marking. Hamida kitso ta fara ma babynta. Lokacin sallah ya yi su Yasir suka wuce masallaci, Mairi da Hamida suka yi sallah a darduma ɗaya. Lokacin da suka dawo abinci ya nuna,da yake taliya ta dafa musu,zuwa dare take da marmarin cin tuwo don sun kwana biyu rabonsu da tuwon. Kamar koyaushe sun fito da tabarma sun shimfiɗa. Yasir da Jalil suna ci a faranti ɗaya. Mairi da Hamida suna ci a kwano ɗaya. Cike da natsuwa suke cin abincin ''Assalamu Alaikum '' Dauda Imamu ya shigo gidan da sallama,sai dai suna haɗa ido da Mairi wani irin tsanarta ya mamaye zuciyarsa lokaci guda. ''Wa Alaikum Salam '' dukkaninsu suka amsa cike da fara'ah musamman Mairi,da take ɗaukin ganin mijinta. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ƙaraso cikin gidan,bai tsaya a ko'ina ba sai a falo, yana cika yana batsewa. Wani haushinta yake ji ba tare da ya san dalili ba. Gefe guda zuciyarsa na ƙara jaddada masa maƙasudin zuwansa garin. Mamaki ya cika zuciyar Mairi ganinsa a ɗaure. 'yar ledar da yake zuwa da ita na tsaraba yau ya shigo hannu rabbana. Cire hannunta ta yi daga abincin ta nufi ɗakin,ta iske kalle-kalle yake yana yatsina fuska kamar wani baƙo. Suna haɗa ido ya ɗaure fuska,wani irin muni ya ga ta yi masa. ''Ki je ki haɗo mini kayansu Yasir zan wuce da su Kaduna'' Dummmmmmm! Zuciyarta ta buga da matuƙar ƙarfi. Tsabar yadda maganarsa ta shigeta sai da ta dafe saitin zuciyarta. A raunace ta ƙaraso cikin falon za ta zauna kusa da shiga ya miƙe yana faɗin ''Malama ni karki matso kusa da ni! Ki je ki yi abin da na sakaki'' ''Baban Yasir! Kai ne kuwa! Kodai an sauya mini kai ne! A'ah! Ba kai bane! Baka taɓa shigowa gidan nan a irin wannan yanayin ba tun da na aureka shekara sama da goma sha uku. Kullum da fara'a kake shigowa gidan nan. Me ya shiga kanta kake mini irin wannan furucin. Na zo nan zauna kusa da kai ka mike kamar ka ga kashi!..." ''Kashi na gani Maryam! Ke kashi ce a wurina! Ki tashi ki haɗo mini kayansu! Idan kuma ba za ki yi ba ni zan yi da kaina,don Ranki shi daɗe Sahura ta ce a yau take so mu dawo tare!" Cike da mamaki ta ce ''Sahura! Sahura! Sahura ce ta koma ranki shi daɗe! Yanzu Baban Yasir Sahura ce za ta aikoka ka zo don ka kai mata yarana wurinta! To wallahi tallahi ban yarda ba! Sai dai idan tare za mu je Kadunan! '' Tamkar tana ƙara rura gwarwashin da ke ci a cikin zuciyarsa. Wani irin ɗaci maganarta yake masa,ji yake kamar bai taɓa jin munanan kalamai irin waɗannan ba. Sunan Sahura da ta ambata tamkar ta ƙara ƙarfafa masa bin umarninta ne,wani irin tsuma ya ji jikinsa na yi tsabar yadda zuciyarsa take azalzarsa a kan bin umarnin Sahura. Idanunsa sun kaɗa zuwa ja. Wani irin mummunan kallon da ya yi mata ya saka ƙirjinta bugawa ''Kar ki kuskara ki sake kiran Sahura gatse kamar wata sa'arki! _RANKI SHI DAƊE_ ake kiranta! Sannan cika umarninta a wurina tamkar ibada ne. A yau ba sai gobe zan za mu wuce Kaduna. Ba ki isa ki hanani cika umarninta ba! '' '''Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil! Allahuma Ajurni Fi Musibati War Zuƙni Khairan Minha! Baban Yasir lafiyanka kuwa! An ya kana cikin hayyacinka kake irin waɗannan zantuka kamar wanda aka shanye!" Wani dogon tsaki ya ja ya wuce uwar ɗaka fuuuu! Kamar zai tashi sama. Kayansu Yasir ya shiga zubawa a ƙatuwar ghana-must-go. Yana tsaka da haɗa kayan ta shigo,da saura taje inda yake tana jan ghana-must-go ɗin da faɗin ''Baban Yasir don Allah ka saurareni! '' Fizgar jakar ya yi ya ci gaba da haɗa kayan ciki bil haƙƙi da gaskiya kamar wani zautacce. Ganin da gaske Dauda Imamu yake,sai ta rushe da kuka tabbas ba a hayyacinsa yake ba,domin ba za ta manta yanayin da ta shiga a lokacin da Sahura take gab da zuwa bariki ba,tabbas irin yanayin da Dauda Imamu yake ciki haka ta ji. Kenan ta mallakesa,sai abin da ta ce shi zai yi. ''Innalillahi wa inna ilaihi raji'un'' ta furta a ranta. Durƙushewa a ƙasa ta yi tana haɗa hannunta bibbiyu ''Baban Yasir na roƙeka da girma Allah! Kar ka kai yarana inda za su halaka! Ka tausaya mini ka bar mini yarana!'' Ta zuƙi majina sannan ta ci gaba cewa ''Baban Yasir ni ce fa Maryam! Mairinka! Don Allah ka saurare ni! Wallahi Sahura cu...'' ''Dakata!!!!" Ya furta a tsawace yana katse mata sauran maganarta wanda hakan ya sabbaba maata saurin miƙewa daga duƙen. Ya shiga nunata da yatsansa manuniya na dama hannunsa na kakkarwa ''Wallahi! Idan kika sake kiran sunan Sahura ba ranki shi daɗe ba sai na baƙanta miki rai! Sannan baki isa ki hanani cika umarninta baaaaaa!" Yana gama fadin hakan ya ja zip ɗin jakar ya saɓata a kafaɗa kamar wanda zai je ci-rani ya fito. Da sauro ta biyo bayansa tana kuka kamar ranta zai fita. Ta tabbata azabtar da yaranta take son yi shi ya sa ta nemi ya kai mata su. Har tsakar gida suka fito Mairi na roƙon kar ya tafi da yaranta. Sosai su Yasir suka saki baki suna kallon iyayensu,abin da ba su taɓa gani ba a duniyarsu. Tsawa ya daka musu yana faɗin ''Ku tashi muje!" A ruɗe dukkaninsu suka miƙe,kowanne jikinsa na rawa kamar an jona musu kiɗan disko. Musamman Hamida ta ji labari,ta fi su tsurewa. Da sauri Mairi ta riƙe jakar cikin kuka ta ce ''Baban Yasir ka tausaya mini! Ka bar mini yarana don girman Allah!'' Wani irin jan jakar ya yi har sai da goshin Mairi ya bige da windon ɗakinsu kasancewar tana kusa da windon. Take wurin ya fashe jini ya fara zuba. Da sauri Jalil ya ruga wurin Mahaifiyarsa yana kuka tare da ambaton sunanta,haka ma Yasir. Hamida kam fashewa da matsanancin kuka ta yi don tana matuƙar tsoron jini. Allah ya sa HAFIZA bata gidan don da tafi kowa ruɗewa a cikin gidan tana ihun jini. Sosai jinin yake zuba amma Dauda Imamu ko kaɗan bai ji tausayinta ba. Hasalima wani irin haushinta yake ji kamar ya fizgota ya dinga bugu. Burinsa bai wuce ya ga ya gurfanar da su Yasir gaban Sahura hankalinsa ya kwantaba ,zuciyarsa ta samu natsuwa. Duk da yaninyan da take ciki haka yaje da ya ajiye jakar a waje ya dawo gidan. Ya ja hannayansu ya fitar da su daga gidan duk da ihun da suke musamman Jalil don ya fi su shakuwa sosai da Mahaifiyarsa. Duk da halin ciwon sda take ji haka ta miƙe ta bi bayansu tana kukan ya dawo mata da yaranta. Kan ka ce me unguwa ta cika da matan layi. Kowa ya shiga ruɗu da tashin hankali,abin da ba su taɓa gani ba a kan su Mairi,har kwatancen su ake in dai zaman lafiya ne da tarbiyyar yara. Kowacce haƙuri take ba Dauda Imamu da zuciya ɗaya amma kamar suna ƙara tunzura shi. Haka ya tasa ƙeyar yaran suka bar unguwar. Jalil ya ci duka hannunsa, don ya fi su kafewa a kan ba zai je ba. Yana da taurin kai da na zuciya sosai ba kamar Yasir da yake da sanyin hali ba. Tana ji tana gani Dauda Imamu ya rabata da yaranta a lokacin da suke buƙatarta,ita ma take buƙatarsu. Wasu daga cikin matan suka taimaka aka kaita chemist wanke ciwon. Abin takaicin duk mazan unguwa suna wurin nema balle wani ya kwaɓa masa ko da da fin ƙarfi ne a hanashi tafiya da su...✍️ ^^^^^^^^^^^^ *Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya* A ɓangaren Sahura bayan fitar Dauda Imamu ta goya Maryam sannan ta koma ɗaki ta yafa mayafi ta fito. Ta riƙe hannun Nu'aymah sannan ta dubi su Hamid ''Ku ci gaba da kallo yanzu zan je na dawo" ''Ok'' suka furta a tare suna mayar da hankalinsu a TVn. Fitowa suka yi daga gidan suna tafiya. Block C ta nufa inda Maman 'yar gayu take,duk inda ta wuce maza da mata suna gaisheta. Ta yo kwana kenan da hadu da oga Sabo,wanda suke shiri sosai. ''Matar Malam sai ina haka" ya tambaya cike da fara'ah. Sihiraccen murmushi ta sakar masa har haƙoranta na bayyana ta ce ''block C zani wurin maman 'yar gayu.'' ''To dawo lafiya. Ungo Nu'aymah '' ya yi maganar yana ciro naira ɗari ya miƙa mata. Wuff! Nu'aymah ta karɓe kuɗin tana ta gode. Sosai Sahura ta ji daɗi har sun yi sallama za ta tafi sai ta dawo ta dubesa ''Ni kuwa kamar ka taɓa sanar mini matarka na garinku ko oga Sabo" da sauri jinjina mata kai ''Ƙwarai kuwa! '' ''Allah sarki! To me zai hana idan na girka abinci a dinga kawo maka tun da matarka bata nan! Wallahi na tausaya maka lokacin da ka sanar mini baku tare da matar! A ce kullum cikin siyan abinci ai babu daɗi!" Waro ido Oga Sabo ya yi ''Matar malam! An ya malam zai barki ki ringa girki da ni! Kar ki damu na saba cin na waje! Gaki da yara kar ɗawainiyar ta yi miki yawa'' 'yar dariya Sahura ta yi tana gyara goyon ''Haba oga Sabo babu ruwansu! Ai shi bawan Allah ne ga tausayi! Har ɗakinka zan dinga aiko maka da abincin! '' Nan da nan oga Sabo ya washe baki. Duk taba ta rine laɓɓansa. ''Amma kuwa na ji daɗi sosai. Bari ki ga" ya yi maganar yana saka hannu cikin aljihunsa. Sahuru kuwa idanunta ƙyar! A aljihun tana murmusawa. Ɗari biyar guda huɗu ya miƙa mata sabbabu ''A'ah oga Sabo kuɗi da yawa haka! To Na gode" Ta yi maganar tana amsar kuɗin zuciyar cike da farinciki. ''Haba matar malam! Ni ke da godiya ai! Babban taimako kika mini! In shaa Allah zan dinga baki kuɗi akai-akai malam na samun sauƙi siyan kayan abinci '' ''To shikenan. Yaushe kake son a dinga kawo maka abincin?" ''Da rana ma ya wadatar! Da daddare ina bakin gate gadi,zan iya siya a waje daman na rana ne yake wuyar samu har saina fitar barikin ko naje Mamy market,na su kuma akwai tsada gashi babu daɗi'' ''In shaa maka Allahu zan dinga aiko yarona yana kawo maka,a wannan block ɗin kake ko'' ''A'ah. Block D room 6 nake'' ''To shikenan! Zuwa gobe zan aiko yarona ya kawo maka'' Daga haka suka yi sallama,sai dai ba haka oga Sabo ya so ba,ya so a ce matan za ta aiko yana rage zafinsa da su yana ba su kuɗi musamman wannan ƙaramar da ya ga alamu ta gado uwarta a son kuɗi. Oga Sabo yana fama da matsananciyar sha'awa kasancewar matarsa na garinsu,iyayensa sun ce sai dai ya dinga zuwa hutu gidan,amma ba su yarda ya taho da ita ba. Tsoron kar idan ta zo ya ɗauke ƙafarsa daga garesu kasancewar shi kaɗai ne suka mallaka a duniya. Saboda rashin mace a tattare da shi ya ɗauki munanan ɗabi'u. Da daddare yakan rage zafinsa da karuwai idan ya samu. Wani lokacin kuma shi yake biya ma kansa bukata. Babu abin da bai sha a kayan shaye-shaye,fari ne amma taba ta rine laɓɓansa da duddugensa. Cike da farinciki Sahura ta ƙasara block C. A waje ta sameta da yaran. Sosai maman 'yar gayu ta yi farincikin ganinta. Tare suka shiga ciki,bayan sun zauna 'yar gayu ta kawousu zoɓo sun sha sai yaran suka fito waje wasa. Sahura ta dubi Maman 'yar gayu ta ce ''Daman in neman abokiyar shawara ta tattauna damuwa da farincikina a barikin nan, wallahi tun lokacin da kika tafi birnin Ikko na rasa abokiyar shawara'' Ɗan murmushi maman 'yar gayu ta yi sai ta ce ''Kar ki damu maman Hamid! Ki ɗauke ni a matsayin 'yar'uwa kuma aminiya! Sirrin a rufe yake da yardar Allah'' Murmushi Sahura ta yi ''Na gode maman 'yar gayu! Ban da wata damuwa yanzu. Don yanzu malam yana a tafin hannuna ne! Sai abin da na ce shi zai yi" Waro ido maman 'yar gayu ta yi ta ce ''Maman Hamid kar dai ki ce mini kin mallake shi" ''Yooo ni ta wasa ce! Hauka nake ya yi mini sakiyar da babu ruwa! Ai zuwana wankan arba'in ɗin nan na yi mai gayya mai aiki, duk da mamata ce ta yi'' Dariya maman 'yar gayu ta yi har da tafawa ta ce ''Shikenan abin ki ɗanainas kunama a wando! Ki ci karanki babu babba! Ni da yake ban da wata matsala da shi gaskiya,daidai gwargwado yana kyautata mana. Har kuɗi yanzu yake ba ni ko ban tambaye shi ba. Kin ga kuwa ba saina mallakesa ba'' ''A'ah! Naki ai no case in ji turawa! Nawa zuma ne sai da wuta. Yau din nan na saka shi ɗauko yaran kishiyata,don na gaji da aikin gida'' Guɗa maman 'yar gayu ta yi tana faɗin ''Ka ji manya!. Hakan kuwa da kika yi shi ne daidai'' ''Ke da kika san komai. Daman na zo mu gaisa ne bari na koma gida zan ɗora girkin rana'' ta yi maganar tana miƙewa. Maman 'yar gayu ta saka hijabi ta rakota har gaban block ɗinsu sannan ta koma...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ *Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya* A ɓangaren Dauda Imamu ta ƙarfin tuwo ya hau da su 'yar ƙumbula sannan suka wuce tasha, ya kuma tsawatar musu a kan idan ba su yi masa shiru ba zai musu ɗan banzan duka. Nan da nan kowannansu ya haɗiye kukan sai dai ajiyar zuciyar har suka iso tashar. Sun tarar da motar Kaduna babu kowa haka suna shiga tare da zaman jira. Dauda Imamu ya bi ya ƙosa motar da cika su fara tafiya. Jinsa yake kamar ya rikiɗa zuwa tsuntsu yaransa su hau bayan ya kai su wurin Sahura ko hankalinsa zai kwanta. Lokaci guda ya yi zuru-zuru ya rame, zuciyarsa tana faɗa masa abin da ya yi ma Mairi shi ne daidai,tsantsar tsanarta ne ke ɗawainiya da shi,a gefe guda cika umarnin Sahura zuciyarsa ke fata. Daya bayan ɗaya suka cika motar,daga bisani direba ya shiga suka ɗauki hanya. Wuya ta yi wuya fifita da tsinken tsire,sosai su Jalil suka jigatu da zaman motar,don goyan-goyo suka yi. Dauda Imamu ya ɗauki Jalil sai Yasir ya sauki Hamida. Haka motar ta yi ta sharara gudi a titi...✍️ A ɓangaren Mairi bayan an wanke mata ciwon an saka bandage sannan aka bata magunguna ta dawo gida,matan ne suka biya kuɗin,don kwata-kwata ba a hayyacinta take ba. Kai tsaye ta wuce uwar ɗaka ta saka hijabi tare da ɗaukarkuɗi da akwati ta fito. Babu wanda ya dace ya ji damuwarta sama da Jamila,wurinta kaɗai ta je da samu kwanciyar hankali. Tun da ta zo duniya bata taɓa riskar kanta cikin tashin hankali makamancin na yau ba. Tana ji tana gani an rabata da yaranta har uku silar kishiya. Wacce ta yi amanna muzguna musu za ta dinga yi. Ita kuwa auran Dauda Imamu bai yi mata rana ba. Ya aura ala-ƙaƙai,ta shigo ta tarwatsa farincikin da suka gina ita da mijinta sama da shekaru goma. Tana tafe tana kuka bata damu da yadda ake kallonta ba. Burinta ta yi tozali da Jamila da HAFIZA ko za ta samu sassauci a cikin ranta. Kai tsaye ta hau motar Mada. Babu jimawa motar ta ɗaga,rushewa ta yi ta kuka tuno da yaranta da yadda suke kuka suna kiranta, mutanan cikin motar suka ti tambayar ko lafiya. Girgiza musu kai kawai ta iya yi ta ci gaba da kukanta har suka iso Mada. Mai mashin ta tara ya kai ta umguwarsu Jamila. Tana sauka ta mika masa kuɗin,yana kiran za to ta amsa canji amma ina hankalinka kwata-kwata ba a jikinta yake ba. Ko sallama bata yi ba ta shiga cikin gidan. Jamila da kishiyarta suna zaune suna hira kamar 'yan'uwa yayin da yaran suke gefe suna wasa, ita kuma HAFIZA tana zaune kusa da Jamila tana zane suka tsinkayi shigowar Mairi gidan, tana zuwa ta durƙushe a gabansu tana sake rushewa da gurshiƙeƙen kuka. Da sauri kowannansu ya miƙe. Jamila a ruɗe ta bugi ƙirji tana faɗin...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *#Hatred* *#Jealousy* *#latesthausanovel* *#hotlovestory* *#Bahagontunani* *#Theamazingpen* *Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️* 07050959771 [12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_021_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ Jamila da kishiyarta suna zaune suna hira kamar 'yan'uwa yayin da yaran suke gefe suna wasa, ita kuma HAFIZA tana zaune kusa da Jamila tana zane suka tsinkayi shigowar Mairi gidan, tana zuwa ta durƙushe a gabansu ta sake rushewa da gurshiƙeƙen kuka. Da sauri kowannansu ya miƙe. Jamila a ruɗe ta bugi ƙirji tana faɗin ''Me zan gani ni Jamila! Yaya lafiya! Me ke faruwa ne? Ko rasuwa aka yi?" Ta jero mata tambayoyi idanunta a kanta Mairi ta kasa magana,ta riƙe saitin zuciyarta tana kuka kamar ranta zai fita,zuciyarta ƙara zafi take. Da sauri kishiyar Jamila ta shiga ɗaki ta ɗebo mata ruwan randa mai sanyi ta bata. Amsar ruwan ta yi ta kafa kai ta shanye,take ta shiga sauke ajiyar zuciya. Suna haɗa ido da HAFIZA wani sabon kuka ya taso mata. Jawo HAFIZA ta yi ta rungume tana ƙara sautin kukan, HAFIZA ma da bata san a kan me take kukan ta shiga rerawa. Jamila da kishiyarta gabansu sai faɗuwa yake, musamman Jamila da take tunanin ko dai an yi rasuwa ne. ''Yaya ki sanar mana me ke faruwa! Wallahi kukanki ƙara tayar mini da hankali yake '' Mairi cikin kuka ta zuƙi majina, sannan ta fara magana wanda shessheƙar kukan ya hana su ji abin da take faɗa da kyau. ''Ya!...ya!...yaranaaaaa!" Ta furta cikin kuka. Da sauri Jamila ta zauna a ƙasa daɓas! Hankali a tashe ta ce ''Yaya me ya samesu! Ba jiya na barosu lami lafiya ba!" Girgiza mata kai ta yi tana sake rungume HAFIZA tsam a cikinta kamar tana tsoron wani zai ƙwaceta. ''Maman yara hutu Yaya take buƙata yanzu,idan hankalinta ya kwanta,kukan ya ragu sai ta sanar mana abin da faruwa" cewar kishiyata. Cire HAFIZA suka yi daga rungumar da ta yi mata sannan suka taimaka mata ta miƙe,don wani jiri-jiri take ji yana niyyar kaita ƙasa,ga azababben ciwon da kanta yake yi. Sai a sannan Jamila ta ga ciwon da Mairi ta ji an rufe da bandage amma akwai ɗan shedar jini-jini. Bayan sun kai ta ɗakin ta zauna a saman kujera,sai ta sake jawo HAFIZA ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciya. Ta saka hannu ɗaya ta fyace majina,sannan ta ƙara matsa HAFIZA a jikinta. Jamila da kishiyarta sai kallon ikon Allah suke. Kowanne a cikinsu ya ƙagu ya ji abin da ke faruwa da ita. Sai can ta ɗan ɗago idanunta waɗanda zuwa yanzu sun ƙara girma abinka da mai manyan idanu,cike da rauni haɗi da dasararriyar murya mai nuni da ta ci kuka ta fara ba su labari ''Muna tsaka da cin abinci Baban Yasir ya shiga gidan. Fuskarsa babu fara'ah kwata-kwata sai hakan ya tayar da hankalina na bisa falon. Tun kafin na iso gare shi ya ce, na tattaro kayan su Yasir za su bi shi Kaduna. Sai hakan ya ba ni mamaki ganin bai ambaci har da ni ba. Da na sake tambaya saii yake sanar miki wai Sahura ce ta umurci ya dawo da yaran wurinta. A ambaton sunan nata har da ranki shi daɗe ya faɗa. Mun kai ruwa rana da shi amma saina fuskanci ba ya cikin hayyacinsa duba da yadda yake sakar mini maganganun masu zafi da jaddada bin umarnin Sahura kamar addininsa ne. Wallahi har tsakar gida na fito ina roƙon ya bar mini yarana amma kamar ina ƙara zuga shi. Na riƙe jakar da ya saka kayan su Jalil sai ya fizge wanda hakan ya sabbaba na bige goshina a windon ɗaki. Jamila tun da na zo duniya ban taɓa shiga damuwa irin ta yau ba. Har waje na fito babu mayafi ina roƙon shi ya bar mini yara amma kamar ina ƙara tunzurashi. Jamila ina ji ina kallo ya wuce da su Yasir suna kuka suna kiran sunana. Jamila me na tsare wa Sahura! Me na mata take son ganin baya na! Ta tsaya a kan Baban Yasir mana! Me zai saka ta saka yarana cikin shirmenta! Idan saboda zuwa bariki ne ta yi hakan! Ni wallahi na yafe har gaban abada! Ta dawo mini da yarana don ban san wace kalar tarbiyya za ta ba su a can ba! '' ''Innalillahi wa inna ilahi raji'un! Lallai Sahura ta cika mara imani da tausayi! Yanzu dan tsabar iskanci da rainin hankali za ta aiko Dauda ya ɗauki yara ya kai mata!.'' Jamila ta faɗa tana tsotar leɓanta na ƙasa saboda takaici. Jinta take kamar ta zama mikiya ta dira gaban Sahura ta fara yagalgalan naman jikinta. ''Kai amma wannan kishiyar taki bata da imani! Allah ka tsarkake mana zukatanmu! Yanzu saboda tsabar mugunta ta rabaki da mijinki sannan ta zagayo ta rabaki da yaranki! Wallahi ba za ta taɓa ganin daidai ba ita da zuri'arta. '' cewar kishiyar Jamila da ta cika da mamakin Sahura. Ita dai har ga Allah ba haka halinta yake ba,bata da wannan mugun hali a kan kishiyarta. Ita da kishiyarta sai alkhairi. Wani tunani Jamila ta yi,sai ta dubi Mairi ta ce ''Yaya yanzu ki kwantar da hankali! In shaa Allahu babu abin da zai samu su Jalil! Allah na tare da su a duk inda suke! Babban abin da suke bukata a wurinki ita ce addu'a! Ki dage da sallar dare da sadaka in shaa Allah babu abin da zai samesu sai alkhairi! Sannan mijinki ma yana buƙatar addu'arki,domin yana tsaka mai wuya. Duk wanda ya ji labarin nan zai sheda aikin asiri ne,shi ya sa hankalinsa ya koma kanta! Kar ki manta yaya,Allah ba ya

Chapter 15 of 33