Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce ''Eh baba'' Wani irin kallo Jalil ya sama irin na makaryaci na ajin farko,babu abin da bai sani ba a game da Hamid,yana sane da duk motsinsa,ya bari ranar da mahaifinsa ya gano da kansa sai ya bayyana abin da ya sani. Kafin Dauda Imamu ya ce wani abu carab Jalil ya caɓe da cewa...✍️ *BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050959771 [1/1, 1:11 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......* *_BAHAGON TUNANI_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_043_* ______________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* 'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇: _Gumbar matsi _Gumbar madara _Gumbar dabino _Sabulun warware sihiri 'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇 09130346510 ____________________________ Kafin Dauda Imamu ya ce wani abu carab Jalil ya caɓe da cewa ''Ka ji tsoron Allah,ka faɗa masa abin da kuke aikatawa Hamid'' ''Me kake son cewa Jalil?" Yana binsa da kallon rashin fahimtar inda maganarsa ta dosa. Jalil ya kawar da kansa daga kallon Hamid,ya ɗan yi shiru yana tunanin abin da zai faɗa. Can ya juyo da fuskarsa kan Dauda Imamu ya ce ''Abba ka raba Hamid da abokan da yake tare da su,wallahi ba aminan arziƙi ba ne. Za su ɓata mai rayuwa ta hanyar koya masa Yahoo da shaye-shaye....'' Sahura ta katse shi da murya mai cike da ƙaraji irin na wacce ta daɗe tana jin haushinsa,sai yau ta samu dama za ta sauke ɓacin ranta a kansa. ''To maƙaryaci ɗan maƙaryaciya! Saboda baka son asirinka ya tonu shi ne kake ƙalama yarona abin da kake yi duk dan ka goge laifinka? To wallahi ba zan lamunci hakan ba! Babu ruwanka da ɗana!" Dauda Imamu bai saurari hargowarta ba,sai ma kafe Hamid da idanunsa masu rikitarwa da sanya mara gaskiya fara gumi. Tun a daren jiya ya fahimci wani abu a game da ɗansa. Ya yi amfani da kalaman Jalil da abin da ya gani a tattare da shi jiya ya ɗaura su a mizani. Bayan ya nazarcesa na minti ɗaya ya ɗauke idanunsa daga kallonsa. Take ya sauke rinannunsa idanunsa da suka sauya saboda ƙunar rai a fuskar Sahura yana mata kallon irin na mara tunani da lissafi. ''Ban sako bakinki a maganar nan ba! Na fahimci duk abu indai na gaskiya ne zuciyarki na ƙyamatarsa! Mai sonka shi ke fada maka gaskiya don ka gyara. Yana son shi da shiriya shi ya sa ya bayyana abubuwan da yake a ɓoye don ya gyara!" Juyo da fuskarta wurin Jalil ta yi tana mishi kallon tsanar wanda ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. ''Bana son taimakon! Ya tsaya a matsayinsa! Ɗa dai ni na haifa shi ko? To abar mini kayana 'yan hassada sai dai su mutu,in shaa maka Allahu sai ya wuce tunanin mai tunani.'' Murmushi mai sauti Jalil ya yi yana mayar da hankalinsa ga wayarsa,tun da dai ya faɗa,ko wurin Ubangiji ya fita. Allah shi ne shaidarsa,baya ƙaunar mummunan hanyar da Hamid ya bi a yanzu,zai fi kowa farinciki ya ga yana kan turbar gaskiya. ''Har ni kike faɗa ma 'yan hassada sai dai su mutu?" ''Na faɗa! Sai me! Ka bar mini yarona ya huta ya sarara mana!'' ''Yaushe kika koma mai zafi Sahura?'' yana tsareta da idanunsa masu fassara mamakinsa a fili. ''Dama can da zafina'' ''To shikenan! Bismillah! Zan baki mamaki daga ke har ɗan naki! Da alama baki gama fahimtar wa kike zaune da shi da tsayon shekaru ba har yanzu! Kai kuma'' ya faɗa yana kallonsa,da sauri Hamid ya share zufar data wanke goshinsa. Cikin sanyi murmushi mai cike da tsananin tsoro da rashin gaskiya ya furta ''Na'am baba'' ''Ka ci gaba da abin da kake! Kar ka fasa! Ni kuma zan shayar da kai giyar mamaki kai da uwarta da take mai ɗaure maka gindi. HAFIZA mu je'' ya mike yana riƙo hannunta,bai damu da mugun kallon da Sahura take aika mishi ba,abin da ya sani ba zai ɗauki iskanci ba,duk abin da ya san zai taɓa ƙimarsa da martabarsa yana ƙalubatar abun ko mene ne. Jalil ma ya miƙe ba tare da ya dubesu ba ya karkaɗe kafaɗunsa ya bi bayansu HAFIZA. Shiru ya mamaye ɗakin kowa da kalar abin da yake tattaunawa a cikin zuciyarsa. Ɗaki Hamid ya koma, Sahura ta bi bayansa da kallon irin na tausayi da jin ƙan uwa. Za ta ƙarfafa kanta da fuskantar mijinta,ba za ta yi sake yaranta su zama saniyar ware ba,kowani sharri idan ya ta so ya ƙare a kansu. Abin kari ta saka ta dawo falon ta zauna. Kadan ta ci ta ji ta ƙoshi. Mayar da kwanon ta yi ta koma ɗaki ta soma shirin tafiya asibiti. Bata ɗauki lokaci mai tsayo ta fito daga ɗakin. Sanye take cikin atamfa cote d' voire riga da zani ruwan chocolate da madara,ta saka hijabi ruwan madara. Ɗakin yara ta shiga, lokacin Gwaggwon Bugaje ta shirya suna ɗan taɓa hira da Ɗayyaba. Tare suka fito,Ɗayyaba ta rakasu har wajen flat ɗin sannan ta dawo falon kusa da Aunty Saudah ta zauna. Komai ya tafi daidai a ofishin principal din makarantarsu Hamida. Duk abin da ya dace Dauda Imamu ya biya ya bayar. Uniform da litattafan karatu aka miƙa mata cikin babbar leda mai tambarin makarantar. Malamin da zai kaita aji ya zo ya wuce da ita,kusan a tare suka fito da Dauda Imamu. Ɗari ya miƙa mata kuɗin break sannan suka yi sallama ya fice. Malamin na gaba tana biye da shi har suka iso ajin. Ganin malama a ajin ya umurci ta samu wuri ta zauna. Ya juya ba tare da ya shigo ajin ba. A hankali HAFIZA ta taka zuwa cikin ajin,idanun kowa ya bar allon zuwa kanta,bata damuwa da yadda ake binta da kallo ba ta ƙaraso ciki,ta ɗan rissina cike da girmamawa ta gaida Auntyn. Da murmushi mai fadi a fuskar Aunty ta amsa tana tambayar sunanta. A iya fatar bakinta ta furta _Aisha Dauda_ nuni ta mata da hannu alamar ta je ta zauna. Ilahirin 'yan ajin ta bi da kallo, idanuna na sauka a kan Raihana ta saki ɗan karamin murmushi tana wucewa bencinsu. Daga nan darasi ya ci gaba da gudana. Malamai biyu suka shigo kafin a yi break, duk wanda ya shigo sai ya tambaye sunanta. A ɓangaren guda, Nu'aymah ta cika ta yi fam da fushi,bata so zuwan HAFIZA ajin ba. Yadda maza da matan ajin suke yaba kyawun HAFIZA yana ƙona ranta,domin a da ita ce tauraruwar ajin,duk speech and prize giving day ita taƙe ɗaukar kambun macen da tafi duka 'yan makatanar kyau. Daga yadda 'yan aji suke koɗa HAFIZA ta tabbata wannan shekarar wanwar a ƙasa za ta yi. Abotar Raihana da HAFIZA ba ta yau ba ce, kasancewar lokacin hutu a kan zo da ita wurinsu a lokacin da Ammu ke raye,tun tana basar da ita idan suka zo hutu har ta sake da ita. Raihana akwai surutu da neman faɗa ba kamar HAFIZA da ta kasance mai sanyi hali da kawaici,ga uwa-uba zurfin ciki da ta gado wurin Ammunta. Yadda HAFIZA ke tunanin za ta sha wuya a ajin sai daga komai ya zo mata da sauki,duk abin da aka musu daidai gwargwado tana fahimta. Kowa a ajin yana son raɓarta don ya yi magana da ita,amma ta murtuke daga Raihana da ta kusa da ita take ma magana. Duk da ta san da wanzuwan Nu'aymah a ajin bata nuna ta santa ba kamar yadda ita ma bata nuna 'yar'uwataa ce ba. ^^^^^^^^^^^^^^^ *Da yamma* Bayan dawowarsu Gwaggwon Bugaje daga eye center ta hau shiri Ɗayyaba na tayata,asubanci take son yi zuwa Sakkwato. An wanke ido da kyau,sun haɗo mata magungunan ɗigawa a ido har kala uku da wasu kwayoyi. Sun bata baƙin gilishi mai tare hasken rana da ƙarfafa ido ɗayan da ya rage mata. Sahura ta shigo ɗakin ta zauna ana taɓa hiran da ita. Ɗayyaba na gama saka kayan a cikin jaka ta zugeta sai ta bar ɗakin zuwa falo inda yaran ke zauna.Tattaunawa mai muhimmanci ta shiga gudana tsakanin Gwaggwon Bugaje da Sahura. Ƙasa-ƙasa suke maganar duk da sun san Hamida da HAFIZA suna falon su ma. Sun tattauna a kan yanda za su nemi sabon boka mai aiki kamar yankan wuƙa irin na Boka Ataka. Raba kafa suka yi ta yanda kowa zai nema daga wurin shi har a dace. Sun jima suna tattaunawa har aka fara kiran sallar magrib. Shigowan HAFIZA ya tilasta su yin shiru tare da sauya hirar zuwa wata ta daban. Daga karshe suka bar ɗakin zuwa falo. Alla-alla Gwaggwon Bugaje take gari ya waye ta wuce Sakkwato fara neman wani bokan. Bata ga ta zama ba tun da har yanzu da sauran rina a kaba. Samun kwanciyar hankalinta shi ne ta ga Sahura na juya kowa na gidan kamar yadda take yi ita da sauran yaranta. Washegari da sassafe lokacin gari ya fara haske ta tafi tare da rakiyar Sahura, Ɗayyaba,Aunty Saudah da Amina,wajen barikin suka tsaya bayan sun ga shigewarta mota sannan suka dawo. A daren ranar Dauda Imamu ya kira Aunty Saudah gefansa Sahura zaune. Ya bayyana mata auranta da Alhaji Shu'aibu shanawa ba alkhairi ba ne. Da kansa ya yi bincike mai zurfi inda ya gano wasu muggan halaye nasa da yake a ɓoye. A binciken da ya yi,an tabbatar masa Alhaji Shu'aibu shanawa riƙaƙƙyen ɗan caca ne wanda ya shahara sosai a harkar. A wurinsa mace tamkar ledar pure water ne,ya aura a lokacin da ya so ya saketa a lokacin zuciyarsa ta so. Mutanen da ya tattauna da su sun ce ba su san adadin matan da ya aura ya saka ba,da ciki yake sakinsu. Daɗewar mace a gidansa shekara huɗu zuwa biyar idan mai hakuri ce da kawar da kai a duk motsinsa. Babban abin da ya muni shi ne saurin hannu,idan fushinsa ya tashi tsaf zai sauke a kan matarsa ko da kuwa tana da ciki ko ɗanyan jego. Bayyana musu iya wannan halayyar ya yi sannan ya ɗora da cewa,idan tana da wani ta faɗa amma ba Alhaji Shu'aibu shanawa ba. Kuka Aunty Saudah take tun fara maganarsa har da ya kai ƙarshe. Soyayyar Alhaji Shu'aibu shanawa ta gama mamaye lungu da saƙon zuciyarta ta yadda idanuwanta suka makance a kan begensa. Sun kai ruwa rana sosai da Sahura a kan sharri ake masa, maganganu marasa dadi ta yi ta sakar masa. Bai damu da zantukanta domin ya dade da sakata a jerin mahaukata 'yan ajin farko. Ya tabbatar mata maganarsa ɗaya ce ba zai aura ma Aunty Saudah Alhaji Shu'aibu shanawa ba. A daren Sahura da Aunty Saudah ba su yi bacci kirki ba kowa da abin da yake kissamawa a cikin zuciyarshi. Aunty Saudah ta ci kuka sosai, yayin da Sahura ta shiga saƙa da warwarar yadda za ta ɓullo ma al'amari,ba zai yiwu tana kallon tsuntsu daga sama gasasshe ya fado a gabanta a hanata taunarsa ba. Kwanciya ta gyara tana sakar wa kanta murmushin nasara wanda ita kadai ta san abin da za ta yi. A ɗayan washegarin ranar Dauda Imamu yana masallaci Kawu Kabiru ya kira shi,inda a nan ya roki ya bar yarinya ta auri wanda take so,ta ci alfarmarsa a matsayinsa na Kawunsa. Bayan sun kammala wayar Dauda Imamu ya ƙissima a ransa Sahura ce da wannan shirin,wato saboda ta san baya jayayya da Kawunsa sai ta haɗasa da shi. Da daddare ya dawo ya kira Aunty Saudah ya umurci ta faɗa ma saurayin nata ya turo,amma ta sani daga ita har uwar kar su kawo masa ƙorafi a auran,ya tsame hannuwansa a ciki. Sosai suka yi na'am da maganarsa. Kamar jira Alhaji Shu'aibu shanawa yake,Aunty Saudah na sanar masa an ce ya turo washegari ya turo da magabatansa da suke neman masa aure a duk lokacin da hakan ta taso,yana jiƙasu da ƙoramarsa shi ya sa ba sa jin ƙyashin zuwa nema masa aure. A masallaci suka sameshi,ba tare da jira ko ɓata lokaci ba ya yanke sadaki a kan Naira dubu hamsin, kasancewar da kuɗi mai yawa suka zo,nan take suka miƙa masa dubu ɗari har da kuɗin na gani ina so. Sannan suka ɗora da cewar angon ya ce baya buƙatar komai daga wurinsu na kayan ɗaki,ya buƙaci idan so samu ne a saka ranar auran bayan karamar sallah da sati biyu ma'ana nan da wata biyar kenan. Shiru ya yi yana binsu da kallo har wanda ke maganar ya ɗige aya,daga ƙarshe ya ce zai yi shawara duk abin da ake ciki za su ji in shaa Allah. Cikin mutanta juna suka yi sallama. Bayan fitarsu ya kira kawunsa ya fada masa abin da wakilan angon suka ce,ya yi na'am na watannin da suka ɗauka,ya kuma yi farinciki da ɗawainiyar kayan ɗakin da angon zai ɗauke,rai ba don ya so ba suka yi sallama. A daren ya sanar musu tattaunawar da suka yi da kuɗin sadakin,ya ce idan an ɗaura aure zai danƙa mata a hannunta. Farincikin da Sahura da Aunty Saudah suka shiga a daren misaltawa ɓata farar baki ne, musamman kayan ɗakin da angon ya ce zai yi.(Kwaɗayi mabuɗin wahala ne Sahura😂 amma bari na yi shiru,mu je dai zuwa🚶) A satin Sahura ta fara tsuma Aunty Saudah da kayan mata,ta kuma aika Sakkwato a haɗo mata kayan mata lamba one. Takanas ta kano Sahura ta je bikon maman 'yar gayu,ta bata haƙurin abin da ya faru tare da sanar mata abin alkhairin ya sa samesu. Maman 'yar gayu ta yi farinciki sosai, ajiye tsoron ta yi a gefe ta shiga harkar bikin ka'in da na'in. A ɓangaren HAFIZA a satin Jalil ya kaita makarantar Abdullahi bn Mas'ud da ke cikin kawo,makarantar na da ɓangarori da dama, akwai ɓangaren hadda, islamiyya,karatun matan aure da boko. Na ɓangaren hadda ya sakata. Kasancewar tun a Gusau ta kammala hardarta kuma tana muraji'ah daidai gwargwado,sai bata samu tankarɗa a jan da aka mata ba,ja ukun duk da haye. Ganin ƙwazonta da kaifin basirarta,duk da ƙarancin shekarunta,babban aji aka sakata wanda kusan sun girmeta nesa ba kusa ba. An yankan mata shafukan da za ta dinga kawowa a ranakun da akwai makaranta. Jirjicewa da ƙwazo suna taka muhimmiyar rawa a dukkan al'amurra. HAFIZA ta dake,ta jajirce,ta mayar da hankalinta sosai ga karatun bokon da islamiyya. Da daddare mahaifinta na mata ja wanda hakan yana matuƙar taimaka mata da fahimtar kurakuranta. Yaa Hamida ta mayar da hankali ga jabawar waec da ke tunkararsu. A wurin Amina babu yabo babu fallasa. Hankalinta da sauran 'yan'uwanta ya fi karkata ga gagarumin bikin da ke tunkarosu. Bayan wata biyu da zuwan HAFIZA barikin Ammu Jamila ta yi musu zuwan bazata,ta zo musu da tsarabobi masu yawa,kawu Rabi'u ma ya bata tsaraba ta kaima jikokinsa. Ta ji daɗin ganinsu cikin kwanciyar hankali da natsuwar jiki. Hakan ya faranta ranta sosai. Wani abu bai haɗata da Sahura ba,domin tun da ta diro gidan bakin Sahura ya tsuke,Maman 'yar ta janye ƙafa,kwana uku ta yi ta koma Mada bayan ya ziyarci Maman Jawaheer da Momy. Tabbas duk abin da Ubangiji ya tsare ya tsaru kenan har gaban abada. Duk ƙwaƙwar Sahura da Uwarta na ganin sun yi nasara a kan Dauda Imamu da yaran Mairi abin ya ci tura. A 'yan watannin Gwaggwon Bugaje ta je wurin bokaye da malamai sama da biyar,maganar ɗaya ce ba za su iya ba. Wani tagadarin malamin tsubbun da Gwaggwon Bugaje ta je wurinsa,kai tsaye ya ce _Kun yi sake hasken da shugaban matsafa ya sharɗanta kar a raba kuka raɓa,ba za ku taɓa yin nasara a kansu ba,idan kuka matsa da yawa zaku hallaka,ki koma gidan don babu wani mahalukin boka ko malami a doron duniya da zai iya yin nasara a kansu_ Kalaman malamin nan sun yi matuƙar tayar da hankalinta Gwaggwon Bugaje. Ba don rai ya so ba ta watsar da makaman yaƙinta. A ɓangaren Sahura haka zancen yake. Lungu-lungu kusufa-kusufa ta bi wurin bokaye da malamai amma maganar ɗaya ce ba za ta taɓa yin nasara a kansu ba. Wani kogo da Sahura ta shiga a dajin birnin Gwari da kyar ta sha ita da Maman 'yar gayu,da yake kusan duk zuwa tare suke tafiya. Dole ƙanwar naƙi suka saduda. Sai dai sun samu gangariyan malamin da zai dinga ma yaransu aiki don samun farin jini da mallakar samari idan hakan ta taso. Kwanci tashi babu wuya wurin mai duka,tun ana ƙirga saura watanni biki ya komai satittika,zuwa yanzu da ya rage sauran sati ɗaya. Ba a bariki HAFIZA da sauran yayyayen suka yi sallah ba. Hamida da Amina sun kammala jarabawar waec dinsu ana sauran kwana biyu azumi,shi ya sa tafiyar tama Hamida dadi sosai. Dauda Imamu ya tsawatar a kan babu shagalin da za ta yi q bikin,ganin rawar kanta da Sahura take a kan bikin. Rai ba don ya so ba ta haƙura. Ana sauran sauran kwana uku biki 'yan'uwanta suka zo. Yaya Abida wacce take ta biyu a ɗakin tare da autarta mace sa'ar Halima, Huwaila wacce take bi mata ita da 'yarta mai yara biyu. Ƙanwar Gwaggwon Bugaje da 'yarta ɗaya da Gwaggwon Bugaje. Bata gayyaci kishiyoyinta ba,amma ta karɓi gudunmuwarsu har da yaran masu tsoka.(Gwaggwon Bugaje mai ido ɗaya kina wuta ina binki da fetur🔥😂😂😂💃💃 Mu je zuwa akwai shagali💃) A washegarin zuwan su Gwaggwon Bugaje dangin Alhaji Shu'aibu shanawa suka kawo akwati guda biyar da babban jaka ɗaya,kaya iya kaya,masu kyau da tsada. Sahura sai washe baki take ɗiyarta ta yi goshi, ƙawayenta da waɗanda suke shiri duk ta aika sun zo sun ga akwatuna.Inna Salame ta zo bikin,sai dai tana tare da su Hamida ganin an waresu a gidan. Da HAFIZA ta ji kanta ba zai ɗauka ba,sai ta tattare kayanta ta yi gudun hijira zuwa gidansu Raihana. Dauda Imamu bai so hakan ba amma ba bu yadda ya iya. Rana bata ƙarya! Sai dai uwar ɗiya ta ji kunya! Ranar da ake jira Ubangiji ya kawota cikin ƙoshin lafiya. A babban masallacin juma'a aka ɗaura auran,bikin ya tara manya kuma gogaggun 'yan caca waɗanda suka yi shura a fadin Nijeriya. Kawu Kabiru ya samu halartar ɗaurin auran,Sadiƙu ma ya zo amma ana daure auran ya wuce. A mazan Dauda Imamu Jalil ne bai samu zuwa ba sakamakon yana shirye-shiryen tafiya NDA shi da Muhsin,bai riga da ya sanarwa mahaifinsa ba,ya bari idan koma ya kankama sai ya faɗa mas. Taro ya yi taro,Sahura akwai jama'a ciki da wajen bariki,kowa nata ne,har mazan sojoji waɗanda take shiri da su sun mata kara. Zan iya cewa bikin Aunty Saudah ya yi zarra a duk bukukuwan da ake yi a barikin. Sai bayan isha'i aka wuce da Aunty Saudah gidan miji. Rantsatstsun motoci masu numfashi ɗaiɗai har biyar aka ajiye. 'Yan'uwa da abokan arziki suka rakata. Sahura ta yi kuka sosai a lokacin da za su rabu da Aunty Saudah,amma abin mamakin idanun Aunty Saudah ƙamar tamkar ƙafarriyar rijiya. A unguwar lema da ke cikin garin Mando aka ajiyeta. Babban gida ne mai kyau da tsari, zan iya cewa ya fi duka sauran gidajen unguwar kyau da daukar ido. Ko'ina na gidan Maa shaa Allah. Kowa sai addu'a yake Allah ya sa gidan zamanta ne,babu kunya take amsawa da Amin tana murmushi. Kwayen amarya sun kwana, washegari aka yi budar kai kowa ya kama gabanta. Su Gwaggwon Bugaje sun so kai Aunty Saudah gidan iyayensa amma ya ce ba a garin suke ba,dole suka haƙura. A dayan washegarin kowa ya yi hanyar garinsa. Rayuwa ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata. Hutun makaranta ya ƙare aka koma boko. Zuwa yanzu HAFIZA da Nu'aymah suna Jss 3. Maryam ta shiga Jss 1 inda Halima take SS2. A farkon satin da suka koma makaranta dasari bi fara ɗaukar zafi ba,sai a sati na biyun lokacin duka dalibai sun dawo aka fara karatu babu kama hannun yaro. ^^^^^^^^^^^^^ Yau ta kama asaba ranar hutu. Sahura ta aiki Amina,Ɗayyaba da Hamida kasuwa siyo kayan cefane. Nu'aymah da Halima suna ɗaki suna bacci. Maryam ta fito da drawing books na HAFIZA tana yayyagawa saboda mugunta,daman suna tsole mata idanu,tayi-tayi ta ga ta iya drawing amma ta kasa,hakan ya kona rantsa da sake jin haushin HAFIZA duk da kasancewarta kamarsu kuma autar gidan. Tun da safe HAFIZA ta wuce hadda sai sha biyu suke tashi. Sosai Maryam ta mayar da hankali tana lahanta drawing books din. Kamar a mafarki ta ji siriyar muryar HAFIZA mai cike da tsauri da fushi. ''Na akeki taɓa mini drawing books ɗina me? Me yakai hannunki kansu'' tana matsowa inda take fuskar a tsuke babu digon annuri. Nan da nan Maryam ta miƙe tana zare ido alamun bata da gaskiya, bin drawing books ɗin da ta yaga da kallo ta yi. ''Ba da ke nake ba!'' tana ɗaga sautin muryarta duk ba ba a tsawace ta yi maganar ba. Kamar a mafarki HAFIZA ta ji an kwashe fuskar da lafiyayyun maruka hagu da dama. Saurin ɗago kanta ta yi tana binshi da kallo,idanuwanta sun ciko da ƙwalla. Maryam da ba ita aka mara ba sai ta da rike kumatunta da hannu biyu tsabar amon marin ''Dan ubanki me ta miki kike mata tsawa! Baki san ina ciki da ke ba!'' furucin da Hamid ya yi yana binta da kallon tsana. A bayansa Sahura ta ce ''Da kyau ɗana,koya mata hankali dan uwarta gobe ba za ta yi gigin yi ma auta kallon banza bare faɗa.'' Hamid bai ba HAFIZA damar magana ba, tamkar wanda aka aiko haka ya zari wsyar charger daga sucket ɗin falon ya shiga dukan HAFIZA ta ko'ina na jikinta,kuka take sosai tana kama ko'ina na jikin. Ihu Maryam ta shiga ƙwallawa ana tsalle, faɗi take ba laifinta ba ne,ita keda laifi amma ina,Hamid da Uwarta da ke koyan bayansa sun yi nisan da ba su jin furucinta. Kashe Mashin ɗin Jalil kenan ya yi sautin kukan HAFIZA da ihun Maryam tana faɗin ba ita ba ce. Hankalinsa a mutukar tashe ya bangaje kofar ya shigo. Take zuciyarsa ta halba ganin aika-aikar da Hamid ya ma HAFIZA a jiki abinka da farar mace. Kukan kura ya yi ya cacumi wuyansa,kansa ya gwara da bango,jikake ƙum! Take goshin ya tsage jini ya fallattsa,dukansa yake da iya karfin da Ubangiji ya basa. Ganin mummunan dukan da Jalil yake ma Hamid,Sahura bata san lokacin da ta gwarma uban ihu tana fadin ''Na shiga uku na lalace! Zai kashe mini ɗa'' ihunta ya farkar da su Halima da ke bacci,a sukwane suka fito ɗakin,daidai Dauda Imamu na shigowa falon ya zo ɗaukar wani littafi da ya manta zai ma matan sojoji karatu. Ransa a ɓace ya ƙaraso cikin ɗakin,da ƙyar ya raba Hamid a hannun Jalil. Ɗaukesa da lafiyyayen mari ya yi yana faɗin ''Baka da hankali ne! Kashe ɗan uwanka kake son ka yi!'' ''Abba kalli jikin HAFIZA! Kalla mugun dukan da ya mata! Ita ba ƙanwarsa bace! Me ta masa data cancanci irin wannan dukan a hannunsa!" Ya nuna HAFIZA da ke rakuɓe a ƙasan kujera tana shessheƙar kuka,farar rigar makaranta duk ta yi layin-layin jini alamar fatar

Chapter 31 of 33