ta daka mata tsawa tana faɗin
''Ni sa'ar uwarki ce da za ki kalla ki watsar kamar kin ga kashi!''
Cak Hamida ta tsaya tare da juyowa,cikin sanyin murya ta ce
''Allah ya huci zuciyarta wallahi ban lura da ke ba'' tana faɗin haka bata jira amsarta ba ta wuce ɗakinsu da sauri. A rayuwarta ta tsani Gwaggwon Bugaje ta zo gidan,saboda hanata rawar gaban hantsi take,ga yawan saka aiki kamar ta ga baiwa,duk da ga yara nan a gidan birjik amma ita ce 'yar aikinta da aikenta. Kwata-kwata ta tsani ta ga tana hutawa. Idan da ta san da zuwan Gwaggwon Bugaje da zamanta za ta yi a gidan maman Jawaheer abinta. Bayan ta cire kayan ta ajiye sai ta shiga bayi ta ɗauro alwala sannan ta kabbarta sallah. Tana idar da sallar ta ɗauki jakarta ta fara yin assignment ɗin da malamin Chemistry ya ba su,bayan kammala ta haye ɗan ƙaramin gadonta ta kwanta. Bacci ya fara ɗaukarta kenan Maryam ta shigo ɗakin da gudu tana faɗin
''Hamida Gwaggwon Bugaje na kiranki'' tana faɗa ta juya ta bar ɗakin. Tsaki mai tsayi Hamida ta ja,ta san aiki ne za ta sakata tun da ta mayar da ita jaka. Tsoron kar a sake zuwa kiranta sai ta yi hanzari fito falon. Kai tsaye Gwaggwon Bugaje ta aiketa da kuɗi da siyo mata maganin gaɓa-gaɓa,babu musu ta amsa ta sako hijabi ta fita. Fitarta ke da wuya Yasir ya dawo flat ɗin,laɓɓansa ɗauke da sallama, yaran suka amsa,ya ɗan russuna ya gaishe da Gwaggwon Bugaje sannan ta wuce ɗakinsu. Duk da a wulaƙance ta amsa hakan bai dameshi ba,halinta ne wanda yake tunanin a wurinta ne matar ubansu ta gado. Yasir ya girma sosai duk da bai kai Jalil ƙiba da tsayi ba amma gemu ya ƙawata fuskarsa,bai cika magana ba sai a inda ya so sannan bai shiga sabgar kowa a gidan idan ka cire 'yar'uwarsa Hamida,ko Hamid da suke kwana ɗaki ɗaya sai su yi wata magana bata haɗa su ba. A gajiye ya dawo gidan,yana ciro wayarsa ya ga missed call ɗin Ammunsa,take ya kira, bugu biyu aka ɗauka. A can HAFIZA ta ɗauki kiran
''Assalamu Alaikum Yaa Yasir''
''Wa'alaikum Sallam HAFIZA,ya kike? Ammuna bata kusa da wayar ne?" Ya tambaya.
''Bata da lafiya,ɗa zu har aman jini ta yi da yawa'' ta yi maganar tana ɗan duban Ammu da ke kwance tana bacci. Take hankalinsa ya tashi.
''Subhanallah me ke damunta"
''Ni ma ban sani ba amma Ammu Jamila ta ce za ta zo yau dubata''
''Ok. I think za mu zo goben don mun kammala exams ɗinmu yau. Ɗan bata wayar mu gaisa''
''Bacci take''
''Ok. An jima zan kira take care kin ji lil sis''
''In shaa Allah ''
Daga haka suka yanke kiran. Kicin ya nufa ya zubo abinci ya wuce ɗakinsu,yana ci yana duba takardunsa har ya kammala. Ya rataye jakarsa sannan ya mayar da kwanon ya fice. Su Gwaggwon Bugaje hira ta yi daɗi ta barbaje tana ba su labarin mulkin da take zubawa a gidan, sai dariya suke cike da nishaɗi. A kunnensu aka kira sallar Asr babu wanda a cikinsu ya yi tunanin miƙewa ya yi sallah. Hamida sai da ta je mamy market kafin ta samu chemist ta saye maganin. Bayan ta dawo ta miƙa mata za ta wuce ɗaki Sahura ta ce
''Zo ki ɗora girki. Shinkafa da miyar jajjage za ki mana''
''To'' ta faɗa tana nufar kicin jikinta na tsuma,a ranta tana jin babu daɗi,ga Aunty Saudah amma ba za ta sakata girki ba sai ita, ga shi tana son yin sallah amma haka ta haƙura ta ɗora girkin. Kunna risho ta yi ta ɗora ruwan dahuwar shinkafar sannan ta koma ɗaki ta yi sallah,bayan ta idar ta nufi kicin ɗin ta samu ruwan ya tausa ta wanke shinkafar ta zuba. Sai kai kawo take a kicin da wajen flat ɗin babu mai tayata. Idan da sabo ta saba,tun tana 'yar shekara sha huɗu Sahura ke bar mata girki,idan ta yi shirme ta sha faɗa ta kuma gyara mata,ahaka-ahaka har ta iya girkin. A cikin 'yan matan Sahura babu wanda ya iya girki,a cewar gidan hutu za su,girki ma ma'aikata za su dinga musu,shi ya sa bata mayar da hankali a kan su iya girki ba. Ta dai koya ma Hamida saboda ta dinga musu girki suna zaune kamar 'yan gayu.
*BAYAN ISHA'I*
Dukkaninsu suna zaune a falon sun mayar da hankulansu ga TVn idan ka cire Aunty Saudah da ta shagala tana chatting da Alhaji Shu'aibu shanawa,sai aika ma junansu suke da zafafan kalaman soyayya da tabbatar wa kansu da sun dace su zauna a ƙarkashin inuwa ɗaya. Hamida na ɗaki tana karatu da yake suna gab da fara rubuta jarabawan WAEC nan da 'yan watanni masu zuwa. Suna tsaka da kallo Dauda Imamu ya shigo flat ɗin,mamaki fal ransa ganin Gwaggwon Bugaje da autarta su yi kane-kane a saman kujerun ɗin suna kallo, Sahura bata sanar masa za su zo ba. Sannu da zuwa yaran suka masa, Sahura ko kallon inda yake bata yi ba balle ta mishi sannu da zuwa. Ɗan russunawa ya yi ya gaida Gwaggwon Bugaje,ta amsa masa cike da kulawa sannan ta juya ta ci gaba da kallonta. A kujerar da babu koma ya zauna a takure
''Maryam je ki kira Hamida ta zo ta zuba ma Babanku abinci'' Sahura ta faɗa ba tare da ta cire idanunta daga TVn ba.
''To'' ta faɗa taba miƙewa zuwa ɗakinsu. Ta sameta tana tsaka da calculations na calculus ta ce
''Hamida Mama ta ce ki zo ki zuba ma baba abinci yanzun nan''
''To'' ta faɗa sai Maryam ta fice tana 'yan waƙe-waƙen na boko. Ajiye littafin ta yi ta fito falon,ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da shi sannan ta wuce kicin ta haɗo masa abinci a tire da kawo ta ajiye a gabansa,sai ta sake komawa ta ɗauko jug ɗin ruwa da ƙaramin kofi ta kawo ta ajiye masa. Ta miƙe za ta koma ɗaki Jalil da Muhsin suka shigo falon da sallama a bakunansu. Har ƙasa suka gaida Dauda Imamu suka samu wuri suka zauna. Bayan ta gaishesu za ta koma ciki Jalil ya ce
''Dawo Hamida''
''To'' ta faɗa a sanyaye sannan ta dawo ta zauna a saman carpet tana fuskantarsu. Jalil ya dubi mahaifinshi ya ce
''Abba ɗazu HAFIZA ta kira ni take sanar mini Ammu bata da lafiya har aman jini take''
Rasssss! Ƙirjin Dauda Imamu ya buga,zuciyarsa tana wani irin zullo kamar za ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar yadda maganar ta dakeshi. Bai san me ke damunshi ba,a ce ko lambar matarsa bai da ita.
''Aman jini! Subhanallah? Me ke damunta?" Ya tambaya.
''Ni ma Abba ban sani ba,zuwa gobe ni da su Hamida za mu je Zamfara dubata''
''Shikenan ni ma zan bi ku goben mu je na ga jikin na...''
''Ba za ka je ba!" Sahura ta faɗa a tsawace tana tsayawa gabansu. Ta riƙe ƙugu tana kallonsu. A sanyaye Dauda Imamu ya ce
''Amma Ranki shi daɗe da kunnuwanki kika ji Jalil ya faɗa Mairi bata da lafiya,shekara ku san huɗu kenan rabona da Gusau,ko don rashin lafiyarta ka bari na je dubata. Ba ma waya balle na san halin da take ciki da HAFIZA''
''To na hana ba za ka ba! Ba kai kaɗai ba har su Hamida ba za su ba,makaranta za su je tun da suna kan karatu. Shi ƙwallon ɗan iskan sai ya je shi kaɗai amma ban da su. Bana son ka sake jayayya da ni a kan wannan maganar'' tana faɗin haka ta koma wurin zamanta ta zauna, Gwaggwon Bugaje da sauran 'yan ɗakin suka mayar da hankalinsu ga kallon. Muhsin ya kwankwaɗi shayin mamaki mara suga,lallai matar nan ta cika mara imani, Jalil kuwa cije laɓɓansa ya yi sannan ya miƙe ya tako har inda take,ido cikin ido ta ce
''Gobe zan tabbatar miki da ni Jalil Dauda Imamu ƙwallon ɗan iska ne na ajin farko. Za ki sha mamakina'' ya yi maganar yana sakar mata malalacin murmushi yana ɗaga mata gira ɗaya ya wuce ba tare da ya jira amsata ba. Ba Sahura kaɗai ba har ta su Gwaggwon Bugaje sai da suka tsorata da furucin Jalil,yaro ƙarami amma sai shegen tsaurin ido. Gaban Sahura bai bar faɗuwa ba har suka fice daga gidan,ta yi matuƙar tsorata da furucinsa kar dai dukanta zai yi tun da ba ta ido garesa ba. (Haba Sahuralliya 😂 fisabilillah mene ne na kawo tunanin Jalil zai dukeki😂 wato dai kin zama farar kura ga tsoro ga ban tsoro😂 ni da my Esteem fans muna biye don jin yadda za ta kaya a tsakaninku😂 mu dai 'yan team ɗin Jalil ne)
Komawa ɗaki Hamida ta yi tana fashewa da kuka,yanzu har rashin imanin matar ubanta ya kai ta hanata zuwa duba mahafiyarta. Wannan wace kalar kishiyar uwa ce mai tsananin son kanta da yaranta. Kasa ci gaba da rubutun ta yi ta kwanta,tunanin mahaifiyarta da ƙanwarta ya faɗo cikin zuciyarta. Fitarsu Jalil ke da wuya Yasir ya shigo falon,bayan ya gaishar da Abbansu ya wuce ɗaki,yana shiga ɗaki kiran Jalil ya shigo wayarsa ya ɗauka ,Jalil ya sanar masa ya shirya zuwa gobe za su Gusau duba Ammu sannan ya faɗa ma Hamida ita ma ta shirya tare za su je. Bayan kammala wayan Yasir ya nufi ɗakinsu Hamida ya faɗa mata ta haɗa kayanta gobe za su wuce Gusau, kuka take amma jin maganar ta yi saurin goge hawayenta sannan ta fara haɗa kayan sawarta fuskarta kwance da maɗaukakin murmushi tana jin daɗi za ta ga Ammunta da tilon ƙanwarta. Bayan Dauda Imamu ya kammala cin abincin ya wuce uwar ɗaka ya ɗauki babbar rigarsa da mayafi ya yi musu sallama ya wuce masallaci,ya gwammace ya kwana a masallaci da ya kwana tare da surikarsa. Sahura kasa zama falon ta sai kawai ta wuce uwar ɗaka ta kwanta,idanunta na kallon ceiling,maganar Jalil na mata amsa-kuwwa a masarrafar jinta,ta rasa dalilin da ya sa kwata-kwata Jalil ba ya shakkarta.
''Wai me ya taka ne da zai faɗa mini na jira gobe?" Ta tambayi kanta. Ganin za ta jayo ma kanta ciwo ta ajiye tunanin a gefe ta gyara kwanciyarta. Hamid sai kusan sha biyun dare ya dawo gidan idanunsa jajur,bai iske kowa a falon ba, kulle kofar ya yi sannan ya nufi ɗaki ya kwanta yana layi...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^
*Tudun Wada premier road Gusau jihar Zamfara Nijeriya*
Jamila sai bayan magrib ta shigo gidan, lokacin Mairi na saman darduma tana lazumi, HAFIZA kuma tana saman kujera tana tilawar Al'qur'ani da ka. Da sallama a bakinta ta shigo ɗakin, HAFIZA na kai ƙarshen aya ta amsa mata fuskarta ɗauke da murmushi.
''Ya jikin Ammunki?" Jamila ta tambaya tana ƙarasowa falon
'' Da Sauƙi Ammu''
Hijabi ta cire sannan ta fita ɗauro alwala,ko da ta dawo Mairi ta kammala lazumi. Kabbarta sallah ta yi. HAFIZA ta je kicin ta zubo musu abinci a tire ɗaya ta ajiye,ta sake komawa ta ɗibo ruwa ta ajiye a tsakiyar falon. Bayan Jamila ta kammala sallah ta yi lazumi sai ta zauna kusa da Mairi. Kallon tsanaki ta yi mata,take tausayinta ya ƙara tabbatuwa a cikin zuciyarta. Tabbas ko ba a faɗa ba yayarta bata da lafiya,duba da yadda ta yi rama,idanuwanta sun ƙara fitowa,ta ƙara baƙi ba kamar kwanankin baya da ta zo gidan ba. Kamo hannunwata ta yi tana kallon ta ce
''Yaya me ke damunki haka! Kin ga yadda kika koma kuwa?"
Ɗan murmushi Mairi ta yi tana matsa hannunta cikin na Jamilan ta ce
''Me kika gani! Ni fa babu abin da ke damuna! Shirmen HAFIZA ne kawai, ta kiraku don ta ɗaga muku hankali,amma ni lafiyata lau''
''Kayyah! Na san abin da za ki faɗa kenan yaya! Yanzu dai mu ci abinci tukunna''
Babu musu suka sauko daga saman kujerar, kowa ya ɗauki cokali suka fara ci bakinsu ɗauke da bismillah. Lokaci bayan lokaci Jamila tana duban yayarta har suka kammala cin abinci sai HAFIZA ta tattara kayan ta kai kicin. Koda HAFIZA ta dawo falon bata samesu ba,sai kawai ta ɗauki Al'qur'ani mai girma ta fara tilawa.
''Yaya idan kin ɓoye wa kowa damuwarki,ni bai dace ki kasa faɗa mini ba, a ce kina rashin lafiya har na tsawon watanni babu wanda kika kira kika faɗama wa,ke baki yi tunanin zuwa asibiti a dubaki ba. Kuma kin dage ke lafiyarki lau. Me ya sa kike wasa da lafiyarki?''
''Ko na sanar miki baki da maganin damuwa ta Jamila'' ta yi maganar cikin sigar kuka.
''Kin sanar mini kinga ban miki maganin matsalarki ba? Idan ta fi ƙarfina ai bata fi karfin Ubangiji ba"
''Haka ne. Shekara huɗu rabon da na saka Baban Yasir a idanuna Jamila. Shin wannan ba abin damuwa ba ne? Babu ranar da za ta zo ta faɗi ban ji ciwon rashin Baban Yasir ba. Kullum cikin raɗaɗin rashinsa nake? Sahura ta cuceni! Ta bar mini tabon da kullum cikin fama shi nake! Ta raba soyayyar da ta gino a turbar gaskiya! Silarta 'ya'yana suka yi nesa da ni! Don ma Ubangiji ya haɗa ni da mutanen arziƙi sun riƙe mini su tamkar ni na riƙe su! Sai Allah ya saka mini! Ba zan taɓa yafe mata hae in mutuuuuu!" Take ta rushe da gurshiƙeƙen kuka mai sauti,Allah kaɗai ya san karatun kurma,babu wanda ya san yadda take ji a cikin zuciyarta,tabbas kowa da na shi ƙadaddar,ita ta ta ƙadaddar rashin jigonta ne. Idan ta tuno da rayuwar baya da suka yi cikin so da ƙaunar juna sai kawai ta ji saukar hawaye. Rungumeta Jamila ta yi tana kuka,ranta na mata zafi da halin da tilon 'yar'uwarta take ciki. Sun jima suna rungume sai tari mai ƙarfi da zurfi ya sarkafe Mairi,yi take babu ƙaƙƙautawa,babban tashin hankalin aman da ta fara mai ɗauke da jini guda-guda. Idan hankalin Jamila ya yi dubu ya kai ƙarshen tashi,rasa ma abin da ya dace ta yi sai kawai ta ƙwallama HAFIZA kira,kamar jira take ta shigo ɗakin a sukwane. Cikin ruɗu HAFIZA ta ce
'' Innalillahi Wa inna ilahi raji'un! Wayyo Allah! Ammu Jamila mu kaita asibiti"
Sai a sannan ta yi tunanin asibiti ya dace su kaita. To amma babbar matsalar ina za su samu abin hawan da zai ɗaukesu kai tsaye daga gida zuwa asibitin,tsakaninsu da titi akwai ɗan tazara. Kuka Jamila ta fashe da shi tana faɗin
'' HAFIZA ina za mu samu abin hawa cikin daran nan! ''
Bata amsa mata ba ta ruga da gudu waje,ita kuma ta dinga shafa bayan Mairi tana mata sannu. Raɗaɗi sosai Mairi take ji a ƙirjinta wanda misaltawa ɓata fatar baki ne, ga wata iriyar masassara da ta saukar mata cikin ƙanƙanin lokaci. Ɗakin ya fara juya mata tana ganin Jamila bibbiyu, a hankali ta nemi ganinta ta rasa,jikinta ya saki. Razananniyar ƙara Jamila ta saki tana jijjigata daidai nan HAFIZA ta shigo gidan da wasu makotansu mata biyu da namiji ɗaya,ta taimakon matan aka saka Mairi mota,suka shiga ciki motar aka tafi da ita asibiti. Kai tsaye mai motar ya wuce da su Yariman Bakura specialist hospital. Nan da nan likitoci biyu da nurses suka duƙufa a kanta har ta farfaɗo daga sumar. Sun yi mata kwaje-kwaje sannan aka aka baya gafo. Maƙocinshi ya yi ta kai kawo a asibitin har aka samu ɗaki. Ya dawo daga wurin aiki zai shigar da motarsa gida HAFIZA ta tsayar da shi tana kuka ta sanar masa rashin lafiyar Ammunta. Babu bata lokaci ya kira matarsa sannan Hafiza ta shiga gidan da Ammun suke shiri da matar ta sanar mata,shi ya sa cikin ƙanƙanin lokaci suka zo. A ɗaki mai gado biyu aka kwantar da ita HAFIZA, Jamila da matar maƙocinsu suka shigo cikin ɗakin bayan nurses sun saka mata drip na jini. Sai a sannan Jamila ta tuna bata dauko wayarta balle ta kira su Yasir da mijinta ta sanar musu halin da ake ciki. Da maƙotan za su koma Jamila ta bisu don ko gidan ba su kulle ba ta ɗauko jakarta da wayoyinsu da duk abin da suke buƙata ta kulle gidan sai mutumin ya sake mayar da ita asibitin. Lokacin agogon na hararar ƙarfe 9:30pm na dare. Duk wanda ya dace ta kira ta sanar masa ta yi...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^
*Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya*
*Washegari*
*Ƙarfe 6:30am na safe*
A daidai wannan lokacin Jalil ya ƙwanƙwasa ƙofar flat ɗinsu,Muhsin na gefansa ya goya jakar baya. Sahura da kanta ta zo da buɗe ƙofar, da sauri ta matsa suka shigo falon
''Lafiya za ka zo mana gida da assusuba! Kai me ya sa baka da hankali ne!"
Bai tanka mata ba ya nufi ɗakin Yasir ya kira shi sai ya wuce ɗakinsu Hamida ya tayar da ita,a tare suka fito. Sahura ta yi tsaye ta kalmashe hannayenta tana son ta ga gudun ruwanshi. Gwaggwon Bugaje da Ɗayyaba suka fito jin motsi,tsaitsaye suka yi suna kallon ikon Allah.
''Yau zan gani ni da kai wa yake da iko a kansu'' ta yi maganar tana ɗaukar wayarta a saman centre table ta kira Dauda Imamu,a bugun farko ya ɗaga kiran. Kai tsaye ta ce maza ya zo gidan sannan ta katse kiran. Kallon ƙasƙanci ta ma Jalil sannan ta ce
''Yau zan tabbatar maka da karan batta da ni babu daɗi''
Malalacin murmushi Jalil ya yi sannan ya ce
'' Then mu zuba mu gani ni da ke waye zai faɗi ƙasa warwas!''
''lallai Jalil wuyanka ys isa yanka! Wallahi zan saka ubanka ya tsine ma...''
''And so what idan ya tsine mini! A tunaninki ko tsinuwa sau dubu zai mini za ta kamani ne! Hhhhh! Kin yi sake marayan zaki ya girma! Karan bana shi ke maganin zoman bana! Ba...✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
*_Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️_*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_035_*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
''And so what idan ya tsine mini! A tunaninki ko tsinuwa sau dubu zai mini za ta kamani ne! Hhhhh! Kin yi sake marayan zaki ya girma! Karan bana shi ke maganin zoman bana! Ba Yasir ba ne da kika mallake yake bin umarninki jikinshi na rawa ko Hamida ba! Na san komai! Duk abin da kike ƙullawa ke da uwarki ina sane da su! Babu abin da kika isa ki yi da yardar Allah wallahi"
''Assalamu Alaikum'' Dauda Imamu ya yi sallama yana shigowa ɗakin,Sahura bata iya amsa sallamar ba saboda mutuwar tsayen da ta yi tana kallon Jalil bakinta sake tsabar mamakinsa. Bata taɓa tunanin Jalil haka yake ba,ido cikin ido yake faɗa mata baƙar magana babu tsoro balle firgici. Muryar Gwaggwon Bugaje ce ta farautota daga duniyar tunani.
''Dauda! Yanzu tarbiyyar daka ba yaranka kenan! Suna zagin matarka kamar sa'anninsu!''
Dauda Imamu da bai fahimci inda maganarta ta dosa ba ya ce
''Gwaggo ban fahimceki ba,me ke faruwa ne? Wa ya yi zagin a cikinsu?"
''Jalil mana mai ido kamar na mujiya! ''
Juyowa Dauda Imamu ya yi wurin Jalil ya ce
''Jalil da gaske zaginta ka yi...''
''Ƙarya zan yi mishi Dauda!''cewar Gwaggwon Bugaje tana katse maganarsa.
''A'a Gwaggo mamaki ne ya saka ni faɗin haka.''
Wani irin zafi zuciyar Jalil take yana kallon Gwaggwon Bugaje cike da tsana. Yasir da Hamida rataye da jakukkunansu suna jiran umarni. Sauran yaran gidan ma sun fito idan ka cire Nu'aymah sun tsatstsaya suna kallon ikon Allah. Hamid ne kaɗai bai fito ba yana can yana sharɓar baccin asarar da ya saba duk safe. Sake juyowa Dauda Imamu ya yi yana fuskantar Jalil fuskarsa a ɗaure ya ce
''Jalil rashin kunyarka har ta kai ga zagi matata!'' ya yi maganar yana nuna kansa.
'' A'a Abba ban zageta ba! Kawai don na zo kiransu Yasir saboda sammako nake so mu yi zuwa Gusau shi ne ta ce ba za su ba. Jiya Ammu Jamila ta kira ni cikin dare suna asibiti Ammu na cikin mawuyacin hali. Mene ne haɗinta da Ammuna da za ta hanasu zuwa''
''To na ce ba za su je ba! Makaranta za su!'' cewar Sahura wadda sai yanzu ta yi magana.
''Baki isa ki hanasu zuwa ba wallahi'' cewar Jalil yana buɗe mata manyan idanunsa.
''Jalil ka hakura ka je kai kaɗai mana tun da ta ce makaranta za su je'' cewar Dauda Imamu don kwata-kwata baya son ɓacin ranta. Ƙunci Jalil ya ji a cikin ransa yana bin Abbansu da kallo,matar nan ta gama cutar su, yanzu ƙiri-ƙiri ta katange Abbansu zuwa wurin Ammunsu sannan kuma yanzu tana niyyar hana su zuwa wurin Ammunsu dubata. Me take so da su ne,wani irin son zuciya ne da ita haka, kanta da 'ya'yanta ta sani su kuma ko oho,wata shari'ar sai a lahira don ba za su taɓa yafe zaluncin da ta musu tun suna yara har zuwa girmansu ba.
''Ka ji dai da kunnuwanka ubanka ya ce ba sai sun je ba tun da baka jin maganata. Idan kuma ka yi jayayya zan saka shi ya tsine maka!'' ta yi maganar cike da izza da iko.
Shiru ɗakin ya yi kowa na jiran abin da Jalil zai ce. Hamida sai hawaye take jin da wuya ta je ganin Ammunta,fuskar Yasir bata nuna yanayinsa ba,ya dai ɗan dukar da kansa ƙasa. Dauda Imamu ya tsaya yana jiran umarnin Sahura,shi dai burinsa kar ran Sahura ya ɓaci,yayin da su Gwaggwon Bugaje ransu fes suna jiran ganin yadda wasan zata kaya. Buɗar bakin Jalil ya ce
''Muhsin''
Mushin da ke gefansa yana bin 'yan ɗakin da kallo ya amsa ''Na'am ɗan'uwa''
''Kira Madam Ngozi yanzu ka ba ni wayar!"
''Ok" ya faɗa yana ciro wayarsa. Tsuru-tsuru Sahura ta yi ƙirijin na duka,sunan madam Ngozi da ya ambata kaɗai ya birkita mata lissafi balle kuma ta ganta a zahiri. Babu shiri Sahura ta ce
''Hamida! Yasir ku ta fi Allah ya tsare hanya! Shege ya san abin da ya taka shi ya sa yake gaggasa mini magana son ransa''
Munafikin murmushi Jalil ya yi sannan ya miƙa ma Muhsin wayarsa,daman plan suka haɗa mata,idan taƙi yarda da tafiyan su Yasir sai su yi kiran ƙarya a waya. Tabbas haƙarsu ta cimma ruwa,tun kan su yi kiran har ta tsorata. Lallai madam Ngozi ce babban makaminsa, cewar Jalil a ransa suna tafiya, zuwa lokacin har rana ta ɓullo. Keke napep ɗaya suka hau su hudun zuwa bakin gate ɗin barikin. Officer Kabir ya turo ma Jalil dubu ashirin a account saboda tafiyar,tun jiya da yamma ya sanar masa a waya rashin lafiyar Ammunsa kasancewar baya garin, momy kuma ta ba su dubu goma su ƙara da yake tare da Muhsin za a yi tafiyar.
A falon Gwaggwon Bugaje ta harari Sahura tana faɗin
''Yanzu saboda an kira kirista soja kike saurin tsorata,sai ka ce baki haihu ba! Kin manta halin ɗan yau ne! Ƙila ma karya suke ba itan za su kira ba. Kawai don sun fahimci nan ne makasarki''
''Kuma fa maganarki tana kan hanya! Ƙila ƙarya suke don Jalil ya san ina matuƙar tsoron Madam Ngozi. Shegen ɗuniya! Za ka iya tafiya Baban Hamid daman a kan Jalil ne na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 33