ma..."
Kafin ta kai ƙarshen maganar Madam Ngozi ta sake ɗauke kumatunta na hagu da kafirin marin da ya fi na daman,take ta kwarma uban ihu tana faɗin
''Wayyo na shiga uku na lalace ni Sahura! Yasir aljana ka kawo mini har gida! Me na maka da zafi haka!"
Murmushin mugunta Madam Ngozi ta yi sannan ta ce
''Na mareki! In fact kaɗan na miki bastard!. Yau sai kin gane baki da wayo! Wicked woman! Kin ɗauko yaran kishiyarki kina musu mugunta. Yau za ki wuni a gaurd room. I will make sure an saisaitaki da kyau. Daga kansu ba za ki sake tunanin yi ma wani wicked look balle thinking of torturing him ba. Juliana and Co!" Ta kira. Cikin ƙanƙani lokaci wasu tiƙa-tiƙan mata har biyar suka shigo ɗakin,kana ganinsu kasan sun yi hannun riga da tausayi. Take cikin Sahura ya ɗura ruwa,yana ba da saukin ƙulululuuu! Tabbas idan ta bari waɗannan dakakkun matan suka damƙeta kashin ya bushe,ta gama yawo a doron duniya. Da sauri Sahura ta zube a ƙasa xjikinta na rawa ta riƙe ƙafar Madam Ngozi. Nan take ta fashe da matsanancin kuka mai nuni da tsantsar firgici da tsoro ta ce.....✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
*#Hatred*
*#Jealousy*
*#latesthausanovel*
*#hotlovestory*
*#Bahagontunani*
*#Theamazingpen*
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_027_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
Da sauri Sahura ta zube a ƙasa jikinta na rawa ta riƙe ƙafar Madam Ngozi. Nan take ta fashe da matsanancin kuka mai nuni da tsantsar firgici da tsoro ta ce
''Madam! Sorry Madam! Wallahi tallahi me no sake dukan yaran miji! Wallahi me kullum zan ba su food well well! Madam sorry me no sakewa!" Duk ta rikice ta fita hayyacinta a ɗan ƙanƙanin lokaci. Hankaɗeta da ƙarfi Madam Ngozi ta yi har tana bigewa da centre table. Take ta saki wata razananniyar ƙara tana riƙe goshinta,ihunta ya saka Maryam farkawa da kuka.
''Bata nono!" Madam Ngozi ta umurta tana zare mata idanu. Duk da azababben ciwon da kanta ya fara yi saboda bigewan da ta yi haka ta ɗauki Maryam ta fara shayar da ita,wani irin tsoron Madam Ngozi ya mamaye gangar jiki da ruhinta. Tabbas ba mutum bace. A bazata ta ji muryarta
''Ina miijinki?"
''Madam bai dawo gida ba" ta bata amsa a matuƙar sanyaye kamar ba ita ta gama ɗaga murya ɗazun ba.
''Wannan ne tambayar da na miki! Ina mijinki!" Ta faɗa da tsawace. A ruɗe Sahura ta ce
''Madam church! Mosque Madam!"
Banbaraƙwai Madam Ngozi ta ji maganar. Ƙara tamke fuska ta yi ta ce
''O'oooooh! Mijinki na zuwa church kenan?"
Sai a sannan Sahura ta ankara da katoɓarar da ta yi. Da sauri ta ce
''Sorry Madam. Yana masallaci! Jumma'a masallaci mosque"
Juyowa Madam Ngozi ta yi kansu Juliana ta ce
''Two of you should kindly go and call him now''
''Yes Ma!" Suka furta a tare suna sara mata da ƙamewa. Duban Yasir ta yi sannan ta sassauta muryarta ta ce
''Yasir ka kai su wurin Dad ɗinka a Mosque ku dawo yanzun nan"
Jinjina mata kai ya yi sannan suka tafi tare. Bayan fitarsu Madam Ngozi ta dubi Sahura da gumi ya gama wanke jikinta ta ce
''Ban taɓa ganin muguwar mata irinki ba! More than ciwo biyu a jikin yarinya ƙarama kuma duk ke ce source of it! Ki ci abinci da yaranki ki hanasu! Ki dinga ma yarinya ƙarama wanka da ruwan sanyi. Kasheta kike so ki yi? You wan kill herrrr?"
Da sauri ta girgiza kai tana share hawayen da suka kasa daina zuba tamkar idaniyar ruwa. A tsawace Madam Ngozi ta ce
''Baki da baki ne! Kina nodding!"
''A'a ina da shi Ranki shi daɗe kamar bishiyar dabino. Kin gani" ta yi maganar tana wage mata baki a ruɗe kamar ƙaramar yarinyar ta aka ce mata Haaa!. Sosai tsoranta ya yi nasarar dabaibaye lungu da saƙon zuciyarta,ga kwarjininta da ya cika idanunta. Tun da take,za ta iya cewa bata taɓa ganin mace mai girma kamar Madam Ngozi ba,ga tsawo,ga ƙiba,ga manyan idanunta masu ban tsoro da suka cikata. Kai za ta iya cewa ko namiji albarka, don girmanta ya wuce gaban kwatance. Sahura ta sha faɗa,don tsaf Madam Ngozi ta zageta ta kuma mata mumanan kashedi a kan su Yasir har su Juliana suka dawo. Da sallama Dauda Imamu ya shigo falon zuciyarsa a jagule da taraddudin me ke faruwa a gidan da har sojoji suka zo kiransa,don bai samu damar tambayar Yasir ba saboda sojojin. A sanyaye ya ƙaraso cikin falon. Sahura na ganinsa ta yi saurin ajiye Maryam tana matsowa kusa da shi, sake fashewa ta yi kuka ta ce
''Baban Hamid ka taimake ni. Haka kurum ban santa ba ta shigo ɗakina ba tare da na bata izini ba ta mareni, tana mini ƙazafin ina muzguna ma su Yasir! Kai shaida ne Baban Hamid nafi ƙaunar su Yasir sama da 'ya'yan cikina kuma...''
''Shut that your dirty mouth! Maƙaryaciya!" Madam Ngozi ta faɗa a hasale,da sauri Sahura ta rufe bakinta da hannu tana haɗiye sauran maganar. A fusace Madam Ngozi ta juyo wurin Dauda Imamu ta ce
''Kai ne mijin Sahura!''
''Eh'' ya furta a hankali domin jikinta ya gama mutuwa. I.D card Madam Ngozi ta ciro a aljihunta ta nuna masa tare da faɗin
''Sunana Ngozi Obi. Ni Wing commander ce. An ba ni umarnin tafiya da matarka saboda samunta da child abuse''
Tamkar an soki zuciyarshi da mashi,haka kalaman Madam Ngozi suka daki ƙofofin kunnuwansa har suka antaya ma'adanar sirrinsa. Lallai akwai cakwakiya a gabansa,yaransa ne take muzguna maa amma ai ita matarsa ce kuma uwar 'ya'yansa. Idan ya bari aka tafi da ita gaurd room mutuncinsa zai zube a barikin. Duban Madam Ngozi ya yi
''Madam sorry! Babu abin da take ma yaran! Ƙarya ake mata! Tana shayarwa sannan tana da yara har biyar. Madam idan kuka tafi da ita wa zai kula da yaran da jaririyar"
''Yawwa Baban Hamid faɗa mata gaskiya,sharri ake mini. Ina kula da yaran kishiyata tsakani da Allah'' ta faɗa tana jin sanyi a ranta,ko ba komai za ta kuɓuta.
Wani irin mugun kallo Madam Ngozi ta wurga ma Dauda Imamu da Sahuran a tare tana sakin tsaki.
''Kai Malam! Ko me zaka faɗa sai na tafi da ita ta yi wuni guda a can. Har kana da bakin faɗar babu abin da take ma yaran! Ni witness ce domin da hannuna na ɗauki small girl ɗin zuwa asibiti. Kar ka kawo wani stupid excuses saboda ba zan ɗauka ba. Commanding officer ya ba ni dama,and dole sai ta je gaurd room na wuni ɗaya. Saboda breast feeding ne ya sa punishment ɗinta ya ragu. Ba shawararka muke nema ba. She must serve punishment for her stupid act on innocent child. Juliana come with her to the guard room''
Tana gama faɗin haka ta kama hannun Yasir suka fita,ta yarda da maganar maman Jawaheer da ta ce asiri ta masa,ta ya matarka tana muzguna ma yara cikinka kake kareta,alhalin har 'yarka aka kwantar a gadon asibiti silar muguntarta. Da sauri Dauda Imamu ya biyo bayanta har waje yana roƙon ta,sai dai tamkar da dutse yake. Bata saurareshi ba sai ma ƙara sauri take saboda yau take son zuwa Abuja amma sai ta biya asibiti ta ga jikin Hamida tukunna. Rantsatstsiyar motarta ta hau suka bar wurin. A kan idanunsa aka saka Sahura a mota Maryam na goye . Da yake ba da Khaki suka zo gidan ba,shi ya sa babu wanda ya yi tunanin an zo kamata ne. Ita kanta Sahura da aka fito da ita bata yi iface-iface ba saboda bata son mutuncinta ya zube a barikin,yadda ake gaisheta maza da matan sojoji da kunya su ga an kamata. Janyo hijabin ta yi ya rufe fuskarta har ta shiga motan. Zuciyarta fal tsoro da firgici. Tana jin labarin gaurd room a bakunan mutane yau wai ita ce za ta shigeshi silar yaran kishiya,amma kuwa kishiya bata mata rana ba. Shaye hawayenta ta yi tana gyara zamanta a cikin motar. Duk wanda ya ga Sahura a lokacin zai tabbatar da a tsorace take,idanunta sun yi ja sun kumbura,abinka da farar mace fuskarta ta koma kamar ƙosai saboda jan da ta yi.
Ko minti biyar bai cika da wucewarsu Sahura motar mahaifin Muhsin ta tsaya a kusa da Dauda Imamu. Kafin Officer Kabir ya gama fitowa daga motar Dauda Imamu ya yi saurin zuwa inda yake a ruɗe.
''Officer ka taimake ni! An tafi kulle matata!"
''Matarka Imam! Subhanallahi! Garin ya ya! Yaushe aka kulleta?"
''Yanzu suka wuce da ita guard room,saboda muguntar da take ma yaran uwar gidana, duk da yarana ne amma ita ɗin matata ce kuma uwar yarana har biyar,ga shi tana shayarwa. Wallahi ina tsoron mutuncina kar ya zube a idon mutanen barikin nan.''
A fili officer Kabir ya tausaya wa Dauda Imamu amma a baɗini farinciki ne fal ransa,gwamma da aka tafi da ita,ko ba komai za ta koyi darasi. Nan gaba ba za ta yi gigin kallon banza ga yaran ba balle kuma ta yi musu mugunta. Ɗan gyara tsayuwa ya yi yana duban Dauda Imamu da ya gama rikicewa ya ce
''Kwantar da hankalinka Imam,babu abin da za su ma matarka balle ma tana shayarwa. A dokar soja ba a wulaƙanta mace balle mai goyo. Kawai dai za su ja mata kunne ne a kan yaran saboda ta kiyaye nan gaba. ''
''Amma Officer Kabir yanzu har sai yamma za su sako mini mata ga yara har huɗu a gida. Da wanne zan ji,da yaran ko da masallacin da islamiyyar. Ga shi Hamida na asibiti an kwantar da ita jiya''
''Subhanallah ƙanwar Jalil ce? Me ke damunta''
''Hmmm, in ji mai ciwon haƙori. Kawai dai a yi sha'ani. Wai an ce saboda matata ce aka kwantar da Hamida asibiti, amma ni yanzu babban damuwa shi ne ka taimakeni matata ta fito don girman Allah '' ya yi maganar yana roƙonsa da hannu biyu. Ajiyar zuciya officer Kabir ya sauke,a gaskiya ba ya tunanin zai iya taimaka masa don fito da muguwar matarsa. Bai ƙi ta shekara a can ba. Gwara ɗiyar zai iya yin ruwa ya yi tsaki a kan ta samu lafiya ban da shaiɗaniyar matarsa. Ɗan dubansa ya yi sannan ya ce
''Yanzu hau muje na ga jikin yarinyar idan ya so daga baya sai muje can gaurd room ɗin. Allah ya sa su yarda. Daman na zo n kai ka gidana ne ga ka iyalina''
''To to mu je Officer'' ya faɗa yana yin gaba kamar shi zai tuƙa motar tsabar yadda yake a rikice. Murmushi officer Kabir ya yi yana girgiza kai sannan ya biyo bayansa. Kai tsaye ya wuce asibiti. Children ward suka nufa ɗakin da aka kwantatr da Hamida. Sun tarar da Madam Ngozi a ciki. Officer Kabir na haɗa ido da ita ya yi saurin ƙamewa tare da sara mata. Ogarsa ce a wurin aiki,mijinta ma uban gidansa ne kuma yana kyautata masa sosai. Da ɗan murmushi a fuskarta ta ce
''Kabir how family? So you know this man and his family?"
Jinjina mata kai ya yi yana faɗa mata inda ya san su ,har silar dawowan Jalil hannunta. Ganin Madam Ngozi a wurin sai Dauda Imamu ya shiga roƙonta kamar zai yi kuka. Ko kallon inda yake bata yi ba balle ta tausaya masa,ita haushi ma yake bata,yadda ya bi ya rikice a kan shaiɗaniyar matarsa. Maman Jawaheer na zaune tana kallon ikon Allah,bata san an tafi da Sahura gaurd room ba sai yanzu da Dauda Imamu yake faɗa,domin Madam Ngozi bata sanar mata ba. Ta dai tambayi ya jikin Hamidan sannan ta tambayi matsayin mijinta a wurin aiki,don tana son saka sunanshi a cikin waɗanda za a ƙarama matsayi nan da wata biyu masu zuwa. Sannan Madam Ngozi ta tambayi ko za ta dinga saka ido a kan su Yasir tunda mahaifiyarsu bata nan kuma ta ga yadda kishiyar uwarsu take cutar da su,sai kuwa ta yi sara a kan gaɓa domin ɗari bisa ɗari maman Jawaheer ta yarda sannan ta sanar mata ai ta yi ma mahaifiyarsu alƙawarin kula da su,kuma ta san mijinta zai yarda shi ma domin yana da tausayi sosai,saboda haka za ta ɗaukesu kamar yaranta. Sosai Madam Ngozi ta yi farinciki da kuma alƙawarin taimaka mata da duk abin da take buƙata. Har ga Allah Yasir da Hamid sun shiga ran madam Ngozi sosai ta yadda misaltawa ɓata lokaci ne.
Officer Kabir ya saka baki a kan a ɗan sassauta mata hukunci, madadin a kulleta har yamma,a rage zuwa ƙarfe uku na rana haka,sai duk kashedin da ya dace a mata a kan yaran sai a mata. Madam Ngozi ta yi na'am da shawararsa sai dai Dauda Imamu bai so hakan ba,kawai a fito da matarsa ba wai a rage hukuncin ba. Rai bai so ba haka ya haƙura domin da babu gwara babu daɗi. A nan Madam Ngozi ta natsu ta sanar ma Dauda Imamu maganarsu su Yasir da kuma amincewarsa a kan zuwan maman Jawaheer gidansa ko kuma yaran su dinga zuwa gidanta a duk lokacin da hakan ta taso don kula da su. Da farko ya so ƙin amincewa tsoron Sahura kar ta kawo cikas,sai dai Madam Ngozi ta fahimtar da shi amfanin hakan tunda mahaifiyarsu bata nan. Officer Kabir ma ya saka baki don shawarar Madam Ngozi tana kan layi,shi ya sake fahimtar da shi daga baya Dauda Imamu ya aminta da hakan. Sun ɗan jima suna tattaunawa har Hamida ta farka maman Jawaheer ta bata abinci sannan suka miƙe. Maman Jawaheer ta dubi Dauda Imamu ta ce
''Malam idan da hali za ka iya tsayawa da Hamida na je gida girka abinci saboda yau nake saka ran dawowar yarana daga Kano''
Ɗan jimmm! Dauda Imamu ya yi kowa na kallonshi don jin amsarsa amma ya yi gum da bakinsa. Buɗar bakin Officer Kabir ya ce
''Idan babu damuwa bari naje gida yanzu na ɗauko matata ta zauna da ita sai ki tafi ''
''Yawwa hakan ya yi officer Kabir ina godiya sosai'' cewar Dauda Imamu yana murmushi. Murmushi Officer Kabir ya yi don ya fahimci hankalinsa kacokar yana ga kilakin matarsa. Kuɗi mai yawa madam Ngozi ta ajiye ma maman Jawaheer ta rubuta bayanan mijinta sannan ta yi musu sallama har ta tafi sai ta dawo ta amsa lambar ɗakin maman Jawaheer sai ta wuce. Kai tsaye Officer Kabir ya wuce gida ɗauko momy. Madam Ngozi ta wuce bangaren masu laifi,Dauda Imamu ya so bin ta amma ta ƙi,haka ya hakura ya koma masallaci. madam Ngozi na isa ta yi parking sannan ta fito zuwa ciki. A zaune ta samu Sahura ta kafa uban tagumi tamkar wacce aka aikoma saƙon mutuwa(Ni kuma na ce saƙon mutuwar Gwaggwon Bugaje ta wulla barzagu😂). Cikin ƙanƙanin lokaci ta faɗa,fuskarta ta yi fayau kamar mara lafiya. Suna haɗa ido ƙirjin Sahura ya yi mugun mugawa har tana razana kamar ta ga mala'ikan mutuwa. Da sauri Juliana da sauran waɗanda suke tare suka taho wurinta suna sara mata tare da ƙamewa. A daƙile ta ce su taho da ita, tana faɗin haka ta ƙarasa ciki inda ake rubuta sunan masu laifi a file. Taso ƙeyar Sahura suka yi har ɗakin. Wani daga cikin sojojin wurin ya tambayi ya sunanta. Cikin kuka ta ce
''Sahura Kabiru''
Ya rubuta sunan sannan ya tambayi wasu bayanan,duk ta sanar mata ya rubuta. Juyowa mutumin ya yi wurin Madam Ngozi,cike da girmamawa ya ce
''Ma is your turn''
''Ok'' ta faɗa tana tashi daga kujeran zuwa inda Sahura ke zaune tebiri a tsakiya. Ko kusa Sahura bata yi gigin haɗa ido da Madam Ngozi ba. Kusancinsu ya ƙara sabbaba bugun zuciyarta hauhawa. Bayan madam Ngozi ta zauna ta ce
''ke ɗago ki kalle ni and don't waste my precious time i have alot to do''
A hankali Sahura ta ɗago da fuskarta sai dai idanunta basu kallon Madam Ngozi. Murmushi mugunta Madam Ngozi ta yi sannan ta ce
''Za ki zauna a gaurd room na tsawon awa biyar zuwa shida instead of complete day for the sake of your husband and children. Sannan akwai sharuɗɗa da za mu saka miki a kan yaran,za ki saka hannu because idan kika yi gigin karya sharaɗi ɗaya za ki zauna a gaurd room na tsawon kwana biyu sannan a wurin da yafi ƙazanta za mu ajiyeki''
Babu shiri Sahura ta ware manyan idanunta tare da saukesu a kan fuskar Madam Ngozi. Hankalinta idan ya kai duba ya tashi,shikenan burinta na azabtar da yaran Mairi ya tashi a banza. Suna tana so ta ce bata da iko a kan su Yasir yanzu,gaskiya kam da sake. Buga tebiri Madam Ngozi ta yi da ƙarfi sai amon sautin ya farauto Sahura daga kogin tunanin da ta yi nutso a ciki. Tsawa ta daka ma Sahura tana faɗin
''Are you stupid! Ina magana kina min shiru! Sergeant Mathew!'' ta kira. Wanda ta kira sunansa ya amsa yana ƙarasowa wurinta.
''Bring me the oath book''
''Ok Ma'' ya faɗa yana sara mata tare da ƙamewa. Babu jimawa ya zo da ƙaton littafi da biro. Amsa ta yi sannan ya koma mazauninsa. 'yan rubuce-rubuce ta yi sannan ta ɗago ta ce....✍️
*BAHAGON TUNANI paid book ne a kan ₦700. Book 1 free ne amma book 2 and 3 zai zo a matsayin paid. Za ki iya biya ta 7050959771 OPAY AISHA ABUBAKAR. Shaidar biya ta wannan lambar 07050959771*
___________________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka:
08036099452
09130346510
________________________
_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_
07050959771
[12/25/2025, 1:00 PM] narrnarhh Bukar (Amazing pen): *_The Amazing Pen_ ✍️.......*
*_BAHAGON TUNANI_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_028_*
______________________
*_TALLA! TALLA! TALLA!_*
'Yar'uwa wai shin kina da labarin UWARGIDAN RAN GIDA daga TASKAR UMMU BANAT!💃. Karkaɗe kunnuwanki domin ta zo da sahihan kayan mata masu inganci sosai,suna matse mace ta koma tamkar budurwa sabuwa fil a leda ga uwa-uba ƙara ni'ima,'yar'uwa za ki ji ki tamkar kankana uwar ruwa💯. Kayan mata ne da mallakarsu sai mace mai capacity,domin an yi su ne daga itatuwa masu matukar muhimmanci ga jikin ɗan'adam musamman ɗiya mace. Kaɗan daga cikin kayan UMMU BANAT 👇:
_Gumbar matsi
_Gumbar madara
_Gumbar dabino
_Sabulun warware sihiri
'Yar'uwa idan kin shirya gigita oga da saka shi zuwa wata duniyar da tunaninsa bai je ba,to ga dama ta samu. Maza ki hanzarta tuntubar UMMU BANAT ta lambar wayarta👇
09130346510
____________________________
Amsa ta yi sannan ya koma mazauninsa. 'yan rubuce-rubuce ta yi sai ta ɗago ta ce
''Sharaɗin farko shi ne: Babu ke babu hana yaran kishiyarki abinci tun da ba your Papa ne ya kawo ba!"
Jinjina mata kai Sahura ta yi kamar wata ƙadangaruwa. Hararta Madam Ngozi ta yi tana faɗin
"You don't have mouth ne kina nodding!"
''Ina da shi ranki shi daɗe. In shaa maka Allah su Yasir abinci har sai sun tureshi,ba zan sake wasa da cikinsu ba'' ta yi maganar cike da muryar tabbatarwa.
Tsaki Madam Ngozi ta yi sai ta ce
''Eh! Mayar da ni wawuya like you mana! You think say your sweet mouth ɗinki zai saka ni yarda! So buɗe kunnenki da kyau. Yanzu haka na saka sojoji sun sassaka na'ura a ko'ina a cikin flat ɗinku, idan kika hanasu abinci ko kika dukesu za mu gani a nan''
Babu shiri Sahura ta ware manyan idanunta a fuskar Madam Ngozi,don tamkar ta karanci zuciyarta ne,ta dai faɗa ne amma sam bata tunanin za ta iya ciyar da yaran kishiyarta kamar 'ya'yanta, haka kurum su fi nata ƙiba da kyawun kallo. Ganin yadda Sahura ta ware idanunta a ɗan tsorace ya tabbatar ma Madam Ngozi ƙarya take,kawai ta dai faɗa ne. Ɗan Murmusawa Madam Ngozi ta yi sannan ta ce
''Kina tantama ne ko?"
''A'a ranki shi daɗe wace ni ''
Taɓe baki Madam Ngozi ta yi sai ta ce
''Bari na karanto miki sharuɗɗan complete sai ki amsa lokaci ɗaya don i have alot to do now. Sharaɗi na biyu: ko da wasa kar ki sake amfani da ruwan sanyi wurin yi musu wanka,sannan dole yaran su dinga kwana a wuri mai ɗumi because likita ya ce yarinyar tana da _pneumonia_ don haka ita da brother ɗinta must sleep in a warm place,sannan karki manta idan ma baki cika waɗannan sharuɗɗan ba ko shekara hamsin za a yi as far as kina cikin gidan za mu gani kuma za mu hukuntaki. Sai sharaɗi na gaba: babu ke babu saka su aikin da yafi ƙarfinsu,sannan ban da faɗa balle kuma dukansu,idan muka sameki da ɗaya daga cikin waɗannan za ki fuskanci serious punishment,domin har da duka za mu miki idan ta kama. Sai the last but not the least: buɗe kunnenki da kyau saboda wannan yana daga cikin manyan sharuɗɗan, dole ki yarda momy Jawaheer ta dinga zuwa flat ɗinku a duk lokacin da hakan ya samu don kula ta yaran, because ba za mu bar miki yara kina threatening ɗinsu badly ba. Don haka dole ki yarda momy Jawaheer ta dinga shigo gidanki at her own comvinient time,and yaran su ma za su dinga zuwa gidanta direct babu shamaki. Kin yarda!"
Jar uba! In ji kanawa. Yau ake yinta wai ita Sahurar gwaggwan bugaje ake ginyawa Waɗannan muggan sharuɗɗan da ko a mafarki bata tunanin za ta iya aiwatar da su balle a zahiri. Sharaɗin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zuwan maman Jawaheer gidanta. Matar da ta sakata cikin jerin maƙiyanta a bariki shi ne ake son ta barta zuwa gidanta don kula da yaran kishiyarta. Kutumar dumadu,za ta iya amincewa da duka sharuɗɗan amma ban da na zuwa maman Jawaheer gidanta,domin ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Kamar Madam Ngozi ta fahimci tunanin da take yi,a ɗan tsawace ta fara magana ganin bata da niyyar amsa mata.
''Duk abin da kike faɗa a ranki koma mene ne i don't care. Dole ki yarda da sharuɗɗan complete idan ba haka ba. Na rantse da Yesu almasihu sai kin kwana goma a gaurd ɗin nan,ba zan damu da kina breastfeeding ba,ko kuma kina da yara sannan a ɗaki mai duhu da mosquitoes za mu ajiyeki mu amshe yarinyar. Idan kina ganin it's a lie kar ki yarda da sharuɗɗan ki gani ko ba zan yi abin da na ce ba!"
Tun da Madam Ngozi ta fara zayyano danƙara-danƙarar uƙubar da za ta mata idan taƙi amcewa jikinta ya yi mugun sanyi. Ta yarda sojar nan da gaske take za ta aikata abin da ta faɗa. Dole ta sallama idan tana son lulluɓa wa kanta kwanciyar hankali da natsuwar zuci. Gumin da ya tsattsago a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 33