Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ga ni na zo ba'' tana wasa da 'yan yatsunta. Hannunta ya kamo ya dora a saman ƙirjinsa yana fadin ''Na kuwa ganki. Yau zan baki kuɗi mai yawa amma za ki tayani matsa jikina. Ciwo ko'ina yake mini'' ''Tom'' ta faɗa tana duƙar da kanta ƙasa ''Kin ga idan kin gama sai na baki kuɗinki ki koma ko'' ''Tom'' Nan da nan ya tube kaya. Take Nu'aymah ta ji wani yarr a jikinta,hakan ya samo asali ne sakamakon shiga _Adolescence stage_ wato tashen balaga,domin ta fara ƙirgan dangi ma. Nuna mata yadda zama mishi ya yi. Babu musu ta shiga matsa masa jiki yana fitar da wani irin sauti...✍️ ^^^^^^^^^^^^^^ A falo suna tsaka da hira maman 'yar gayu da Nana suka shigo da sallama a bakunansu. ''Ni ba na manta na kira na fada miki sai an jima zamu ba'' Sahura ta faɗa tana matsa mata ta zauna. Hararar wasa maman 'yar gayu ta mata tana kai zaune ta ce ''To ai sai ki shirya yanzu'' ''Wa ce ni Sahura! Sai an jima dai maman 'yar gayu'' ''To shikenan! Bari na sha zamana zuwa an jiman sai mu je,babu abin da zan yi a gida. Ina za ki je Amina! Wannan kyau haka!" Ta yi maganar tana binta da kallo. Fuska Amina ta rufe tana murmushi. ''Baƙo za ta yi an jima'' Sahura ta furta tana bin Amina da kallo tana murmushi. ''Aaa'aaah! Ki ce siriki muka yi! Allah ya tabbatar da alkhairi mu sha biki'' ''Ameen'' duka 'yan ɗakin suka amsa. Shiru ya mamaye ɗakin. Hamid ya wuce ɗaki yana latsa taohuwar wayarsa. Daidai shigowan Yasir duk ya yi futu-futu da datti alamar daga wurin aiki yake. A tsai-tsaye ya gaida 'yan ɗakin ya wuce ciki. Tsuwwa wayar Sahura ta fara. Sunan wanda yake yawo a screen ɗin wayar ya saka saurin ɗagawa. A can Dauda Imamu ya ce ''Ki ce ma Hamida bakonta ya iso,ta shigo da shi'' ''To! To! Yanzun nan" ta katse kiran tana kallon Amina. ''Maza tashi ki je ki ɗauko shi a waje! Yau ne ranar amfanin karatun da na daɗe ina koya miki keda 'yan'uwanki'' ''Tom mama'' ta miƙe ta gyara zaman mayafinta sannan ta fita. Dubansu maman 'yar gayu Sahura ta yi ta ce ''Ku zo mu je ciki kafin ya wuce'' Tare suka mike, Sahura ta ja hannun maman 'yar gayu suka wuce ɗakinta. Ɗayyaba da Nana suke waje ɗakin yara. Sun tarar da Halima da Maryam suna bacci. A ɗakin Sahura. Fayyace ma maman 'yar gayu ta yi komai da matakin da ta ɗauka. Maman 'yar gayu ta yi na'am da canjin da Sahura ta yi. Naka ai shi ne naka. Sun fara hira kenan Amina ta shigo ɗakin tana kuka wiwi. A razane suka ɗago suna bin ta da kallo. Cike da tashin hankali Sahura ta nufo inda take tana faɗin ''Lafiya!" Cikin kuka Amina ta ce ''Mama ya ce baya sona! Shi Hamida yake so! Mama mai kuɗi ne sosai! Ki taimake ni Mama! Naa kamu da sonsa!...." Ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya fi na da. ''Kai amma an yi ɗan ƙwal uba! Bari ki gani" ta juya ta dauki hijabinta da ke saman gado ta saka ta fita. Maman 'yar gayu ta shiga rarrrashinta da ban baki har ta tsaigata kukan. A falo tun kafin Sahura ta karaso ciki ƙofofin hancinta suka tabbatar mata da wanzuwansa . Sassayen ƙamshi mara hayaniya yake tashi da falon. A hankali ta karaso bakinta ɗauke siririyar sallama. ''Wa Alaikumussalam'' yana juyowa. Yakub baƙi ne,ba zai yi ƙasa da shekara talatin da biyar ba. Kana ganinsa ka san kuɗin sun zauna masaa. Ɗan russunawa ya yi ya gaidata bayan ta zauna. Ya fahimci ita ce mahaifiyarsu. Cike da kulawa irin na sirikai ta amsa tana sakin fuska. (Ho Sahuralliya😂 an san kan duniya. Mu je zuwa mu ji mai za ta ce🔥) Shiru ne ya mamaye ɗakin bayan sun gaisa,kowa na tattaunawa da zuciyarsa. Fin sakan goma Sahura ta katse shirun da cewa ''Sai na ji Amina na faɗin ka ce Hamida kake so?" ''Eh mama!" Ya faɗa babu ko kunya irin na sirikai. Danne fushinta ta yi ta ce ''Allah sarki! Da kai da kayana duk mallakar wuya ne. Duk ɗaya suke a wurina! Hamida na mata miji! Imamu ya manta ne ya ce ka zo wurinta! Amina ce daidai da kai. Tana da tarbiyya da natsuwa ga kamun kai'' ta kai ƙarshen maganar tana tsare shi da manyan idanunta. Shiru Yakub ya yi yana sauraronta kafin ya motsa bakinsa ya furta ''Shikenan daman Hamida ce nake so amma tun da kin ce an yi mata miji na haƙura! Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi '' ya miƙe ba tare ta jira amsarta ba ya ficewarsa. Tamkar mutum mutumin da aka sassaƙa,haka Sahura ta zauna tana bin kofar da kallo. Can kuma ta saki tsaki ta miƙe ''Wallahi na rantse da izu tamanin sai Amina ta aureka! Mu zuba mu gani shege kan fasa ɗan halak sai yanka! Kuma Hamidar ba za ka aureta ba! Ɗan gidan abun kwari kawai! Mtssssss!" Fuuu ta wuce ɗakin. Tana isa ta ɗauki jakarta da ke rataye a bango ta dubi maman 'yar gayu ta ce ''Ta so mu je maman 'yar gayu! Idan ban je wurin Malam Tsalha mai yasin ba haɗiyar zuciya zan yi na mutu!" Ta faɗa tana yin gaba,maman 'yar gayu ta biyota ta bar Amina a saman gadon tana shessheƙar kuka. A hanya Sahura ta faɗa mata yadda suka yi da Yakub suna tafiya suna tsine masa har suka iso bakin titi. Sahura ta dubi agogo ta ga ƙarfe 10:30am. Mayar da wayar ta yi cikin jaka. Wata empty Keke napep suka shiga,tsabar yadda Sahura ke son zuwa wurin Malam Tsalha Mai yasin,drop ta ɗauka suka tafi. Duk tafiyar da Sahura take cike da sauri take yinta. Burinta ta ganta a gaban Malam Tsalh Mai yasin ko zuciyarta za ta yi sanyi. Drop ta sake ɗauka bayan sun Tsallaka titi har Rafin guza. Daga can suka gangara har inda ake hawan kwale-kwale suka hau ya tsallaka da su hayin gogi. Mashin daya suka yi goyo har cikin hayin kogin. Da yake duka 'yan mashinan sun san Malam Tsalha mai yasin,cikin ƙanƙanin lokaci ya kai su. Matan da suka gani a layi ya tayar da hankalin Sahura. Manyan mata har aa maza masu hannu da shuni sun faka rantsattsun motocinsu. A hankali Sahura ta tsaya a layin bayan ta tambayi ta ƙarshen. Sannu a hankali layin ke tafiya har aka zo kanta. Ta shiga tare da maman 'yar gayu. Turare mai hawa kai ya doki hancinsu. Saman tabarma suka yada zango. A hankali na bi ɗakin da kallo, normal ɗaki ne da aka rubuce bangon ɗaki da tawada. Ɗakin bai da hargitsin kaya. Mutumin na ma kallo irin na ƙurilla. Baƙi ne sosai mai matsakaicin jiki, idanunsa sun fa farin kwalli tamkar tsohon bazawari. Shigar manya ya yi shakwara da janfa da rawani a kansa. A gabansa ƙasa ce baƙa da jajayen wuri. A hankali Malam Tsalha Mai yasin ya furta ''Me ke tafe da ku!" Zama Sahura ta gyara da kyau tana fuskantarsa ta fara magana ''Malam matsoli gareni masu tarin yawa! Ina son kowacd matsala ka mini maganinta!" ''Ina saurare'' ya furta yana tsareta da jajayen idanunsa. Natsuwa Sahura ta yi ta fara magana ''Ina so ka hana yarinyar kishiyata zuwa gasar Alqur'ani da za ta je a ƙasar waje! Sannan yayanta Jalil ya tafi makarantar sojoji ta NDA,idan so samu ne ka haukatar da shi ko kuma ka saka shi ya yi abin da za a koresa daga makarantar. Akwai yarinyata Saudatu da ke azabtuwa a hannun mijinta,ina son ka bata mallakar ta yadda za ta dinga juya mijinta a tafin hannunta. Sai na karshe Ɗiyata ta biyu Amina,ina son ka sama Yakub soja soyayyarta ta yadda nan da nan zai aminta a ɗaura musu aure. Waɗannan su ne bukatuna'' Kai ya jinjina yana ɗaukar wurin duka ya watsa a saman ƙasar. Ya sake ɗauka ya watsa a saman ƙasar. Sau huɗu yana yi sannan ya ɗago. Ilahirin...✍️ *_SHIN AMINA ZA TA SAMU SOYAYYAR YAKUBU SOJA HAR TA AURESHI KUWA?🔥_* *_ SHIN MALAM TSALHA SAI HANA HAFIZA ZUWA GASAR ALQUR'ANI?🔥_* *_SHIN ME KE SHIRIN FARUWA DA NU'AYMAH A TANTIN NAN🔥_* *_SHIN SAHURA ZA TA YI NASARAR HAUKATAR DA JALIL🔥_* *_SHIN AUNTY SAUDAH ZA TA MALLAKI ALHAJI SHU'AIBU SHANAWA?🔥_* *_AKWAI GAGARUMIN AL'AMARIN DA ZAI FARU DA DAUDA IMAMU WANDA ZAI ZAMA FARINCIKI GA SU HAFIZA,YAYIN DA ZAI TARWATSA ZUCIYOYIN SU GWAGGWON BUGAJE, SAHURA HAR DA MA YARANTA. WAI SHIN MENENE WANNAN AL'AMARIN?🔥_* *_SU WAYE MAZAJEN ZA SAHURA ZA TA YI KITIMURMURA TA HANA AURAN HAFIZA DA SU. ME YA SA TAKE TSORON HAFIZA ZA TA FI YARANTA JIN DAƊIN GIDAN MIJI?🔥_* *_HAFIZA ZA TA AURE NAMIJI ƊAYA TAMKAR DUBU DA YA WUCE MAZAJEN 'YAN'UWANTA. WANE NE WANNAN MIJIN? A INA YAKE? TA YA ZA A YI AURANSHI ALHALIN SAHURA TA YI KANE-KANE?🔥_* *_HAFIZA ZA TA YI AURE A BAHAGON GIDA MAI CHAKWAKIYA MASU MATUƘAR YAWA,SILAR ZUWANTA GIDAN SIRRIKAN DA KE ƁOYE SAMA DA SHEKARA ASHIRIN DA BIYAR ZA SU BAYYANA. WAI SHIN WANI IRIN SIRRIKA NE HAKA?🔥_* *_AKWAI MUTANEN DA SUKA LINKA SAHURA A MUGUNTA DA SON ZUCIYA A GIDAN DA HAFIZA ZA TA YI AURE. SU WAYE WAƊANNAN MUTANEN🔥_* *TAMMAT BI HAMDULILLAH AZZA WA JALLA* _Duka-duka a nan na kawo ƙarshen Book 1 na ƙyataccen littafina mai suna BAHAGON TUNANI. Mu hadu a paid book Littafin kuɗi ne a kan ₦700 ta OPAY 7050959771 Aisha Abubakar. Shaidar biya ta 07050959771. MUTANEN NIJAR 96069955 My Nita Sajida 500CF. Shaidar biya ta wannan lambar +227 93 81 16 18 *KI TSAYA KI KARANTA KAFIN KI TURO MINI KUƊINKI DON GIRMAN ALLAH* _Ki tabbatar da kuɗin da za ki turo mini kin saka remark ko description. Ki saka LOAN/GIFT saboda kar Gwamnati ta cire wani abu a cikin kuɗi da sunan HARAJI/TAX. Please ki kula sosai ki tabbatar ki saka LOAN/GIFT a wurin remark ko description. Na gode! Na gode. Don Allah kar a ki turo da USSD saboda bsbu remark._ *_My Esteem fans ta hanyar siyan littafina ne zan tabbatar da ƙaunar da kuke mini. A YI SUPPORTING TALENT ƊINA TARE DA ƘARFAFA MINI GWIWA TA HANYA SIYA💯. Allah ya saka muku da mafificin akhairi🥰_* ___________________________ *_TALLA! TALLA! TALLA!_* Wai! Wai! Wai! Wanga musulmin daɗi har ina😋. Jama'a kuna da labarin TOP CROWN YOGHURT kuwa?. Hmmmm idan ana sallah ba a magana,domin TOP CROWN YOGHURT ɗaya ne tamkar dubu daya amsa sunansa wurin kauri tamkar kindirmo, garɗinsa da daɗinsa kuwa ba a ba yaro mai ƙyuiya. Daɗin daɗawa yana ɗauke da sinadaran da jiki ke buƙata irinsu protein, vitamins da dai sauransu. Sannan suna da rassa a duka faɗin Nijeriya,ko'ina kike za su je gareki cikin aminci. 'Yar'uwa karki bari daɗi ya wuceki,maza hanzarta tuntubar shahararren kamfanin TOP CROWN YOGHURT ta lambobinsu kamar haka: 08036099452 09130346510 ________________________ *_Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️_* 07050950771 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 33 of 33