Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN GORON SALLAH MUNAYI NUKU BARKA DA SALLAH DA FATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA MAIMAITA MANA AMIN. Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 VOLUME TWO *Try not to resist the changes that come your way. Instead let life live through you. And do not worry that your life is turning upside down. How do you know that the side you are used to isbetter than the one to come?* EPISODE 0️⃣1️⃣ Bayan likita yayi mata Allurai zazzaɓi ya sauka Sa'ad ya daɗe yana mata nasiha da rarrashi a ranta cewa take "abun da Uncle Aliyu be iya ba kenan lallami." ta yi shiru tana sauraren shi har ta yi bacci suka fita da Isma'il suka barta, sai can bayan sallar La'asar ta tashi ta yi sallah ta sha magani bayan ta ci abinci. Tanajin jikin ta yayi mata sauki tasa Sa'ad a gaba da rigimar saiya nuna mata hoton Farida, yana jinta yayi shiru kamar bazai yi magana ta sake cewa "ka ji." ya dawo da hankalin shi kan ta, "Na yi deleting pictures ɗin ta amma bari na duba." yayi searching Facebook account ɗin ta, ya nunawa Umaimah hoton Farida, ta kalleta ta ce "haka take da dargajejen baki?" Sa'ad yayi ta dariya kai Umaimah ba za ki kashe ni ba. ji kamar ba ita ce jiya ta tayar musu da hankali ba amma yanzu ta warware har tana tsokana, Dr ya shigo ya rubuta musu sallama, Sa'ad yace ta jirashi yayi settling bills ya fita daga ɗakin be daɗe da fita ba Umma ta shigo tare da Isma'il "Siyama sai yau kika zo? Umma ta ce ya kike so nayi har yanzu da mutane a gidan ga Amira ma ta kwanta ciwon kai tun jiya, taso mu je an sallame mu, muje gynea nake so ki gani." ba musu ta bi ta, already Umma sun yi magana da Ibrahim akan tanason Umaimah taga gynea Dr ya haɗa ta da wata abokiyar karatun shi, ta kira ta ta kwatanta masu office ɗin ta suka shiga, bayan tambayoyin da tayi wa Umaimah tace zata ba ta maganin da zata sha for 3months idan bata yi period ba zata dawo suka fito daga office ɗin, suna fitowa suka ga Sa'ad tare da Isma'il Umma ta bashi takardar magani ya karɓo a pharmacy suka wuce gida. Kwanan Tahir biyu a asibitin Mal Aminu Kano amma har yanzu an kasa gane kanshi, hankalin Ummi ba ƙara min tashi yayi ba kullum cikin kiran sunan Allah take, Dr Huzaifa ya samu likitan dake duba shi suka yi magana ya sake yi mishi bayanin zuciyar shi nagab da kumbura saboda tashin hankalin ɗaya shiga, maganar ba kaɗan ba ta tayar musu da hankali, babu ɓata lokaci Dr Huzaifa yayi magana da wani abokin sa likitan zuciya dake aiki a Saudiya nan da nan suka shirya tafiya da Tahir can, cikin kwana biyu komai na tafiyar ya kammala suka wuce da shi Saudiyya dan har yanzu baya cikin hayyacin shi. ***** After 2 months Lokaci ne na watan Azumin Ramadan da daukacin musululmin duniya su ke Azumtar wannan wata mai tarin falala da albarka, kullum Umma ke fama da Umaimah akan tashi sahur sai tace a bari sai ranar asabar babu makaranta, yau dai Umma ta gaji tace "wlh baki isa ba, Allah fah sai kin tashi." haba Siyama ki bari ranar Asabar babu makaranta sai na yi." Umma haushi ya ishe ta tace "wai ke baki da kishin zuci ne Umaimah? Amira kullum ba sai na tashe ta ba amma ke sai kowa ya ji mu? Ta zumboro baki "toh Siyama naga ni be hau kaina ba Allah na ma yi kokari ina laifi." wlh da laifi shekarar ki nawa? Shekenan zauna bari na kira Babangida." ba shiru ta mike ta shiga Toilet. Su Umaimah na class Principal ta yi excusing teacher da ke ciki ta shigo, "good morning mah. "morning class have your seat, Fatima Tahir Al-arabey, Aminu Bello and Sadiq Mukhtar." "yes mah" suka miƙe, tace "see me after school." suka amsa ta fita, Umaimah ta ce wa Sadiq me muka yi? Yace mata ya zan sani "ni wlh ba abunda na yi, ina na ga kuzarin neman magana inata kaina." Umaimah ta fada tana kwanciya akan desk. Ana tashi Suka je wajen Principal ta bawa kowa letter su kai wa iyayen su, suka karɓa suka fito, "wlh sai na buɗe tab wa zai kai letter gida a lulluɓe, idan laifi muka yi fah, yanzu haka ma kora ce." genius ya faɗa, "kora kuma saboda an tsane mu." cewar Sadiq, tuni Umaimah ta nemi kasan bishiya ta buɗe ta karanta me takardar ta kunsa. Dear parent/Guardian I am writing to bring to your attention the exceptional academic abilities of your child Fatima Tahir as her principal I had the pleasure of obseving her outstanding performance in her studies, and I strongly believe she possess the intellectual capacity to excel in senior secondary certificate Examination ssce even at ss2 level,I would appreciate it if you responce to this recommendation by Tomorrow as this will enable us to make the necessary arrangements Fatima's examination registration. Thank you for your attention to this matter and I look forward to hear from you. Best regards Mrs magashi Principal. Umaima ta daka tsalen murna Sadiq suka rufu a kanta, suka karanta suma su ka buɗe tasu, exactly abunda aka rubutawa wa Umaimah a ka rubuta musu, sai murna suke yi, "ki zo Mal Musa yazo." Amira data ƙaraso wajen ta faɗa, suna shiga mota Umaimah ta miƙa mata letter ta karanta tace da gaske? Da farin ciki Umaimah ta ce "ga zahiri kin ga ni." "congratulations sis." Amira ta faɗa tana rungume ta. Sosai su ke yin karatu da Isma'il saboda rubuta ssce da zata yi, ta mayar da hankali, ita murna take yi zata shiga jami'a sun gama karatu tace Uncle Ismah azumi nawa za a yi 29 ko 30? "Ina zan sani Umaima." ya bata amsa, data gama karatu take sharbewa a falo bata kara morowa sai dai Amira Baba Rabi da Umma ke yin abincin buɗa baki, idan aka gama kuma ta fi kowa ci. Bayan sallar isha'i har Umaimah ta kwanta ta ji ana kunce mata kai, ta kai hannu ta ji Umma ce "menene Siyama? Umma tace "haba Umaima ke ko zafi ba kya ji kalabar nan satin ta nawa ba na son kazanta." "ni wlh ba ƙazama bace. toh faɗawa wani ba ni ba." tana ta mutsu mutsu da kai haka Umma ta kwance kalabar, tace "tashi mu je a wanke kan, wlh dan Baban Khadija yace a ƙyale ki amma da ba wanda zai barki shiga wata jami'a yanzu." ta mike ta shiga Toilet, ta yi minti 5 da shiga sannan Umaimah ta bi ta haka dai aka wanke kan tana ta danne hannun Umma, suka fito idon ta yayi jawur. Washegari tun safe take ta shige da fice a ɗakin Ismael Umma dai bata kula ta ba ko me suke kullawa ta fada a ranta, anan dai ta hau sama ta bar su tunda akwai sauran lokacin fara aikin buɗa baki, bata daɗe da hawa sama ba suka fita ita da Isma'il sai da aka kira sallah suka dawo. Yau jajiberin sallah Umma tace da Amira ta wanke kanta Ramma me kitso yau zata zo ta musu kitso ita da Umaimah, da yake duk ƙaramar sallah sai Umma ta yi rabon abincin sallah da yamma suke tafiya Bichi duk gidan har Baba Rabi ita ma tayi Sallah a gida, sallar layya ce suke tafiya ana gobe sallah, Umaima ta shigo palour da Ghana must go, tace "ga ɗinkin na gama." Umma ta buɗe jakar tana kallon kayan, Umaima mai abun tsiya dana kirki yanzu ta ƙware sosai a ɗin ki, duk ranar Asabar da Lahadi DIJAH COLLECTION take zuwa, kusan ita ce ke kula da abubuwan shagon. "Ah ah haba Umaima ya zaki ɗin kawa Baba Rabi doguwar riga, zani fah na ce ki yi mata." Umma ta faɗa tana sake duba ɗinkin, "wai Siyama wa yake saka zani yanzu, toh basu yi ba kenan?" Baba Rabi da sauri tace "ah ah sun yi uwar ɗakina Allah yayi miki Albarka kin fito dani." Sallamar Ramma me kitso ce ta katse su Umma tace "sai ki zauna a fara yi miki." Umma ta juya wajen Ramma suka gaisa. Babu musu Umaimah ta zauna, Umma na barin wajen ta cewa Ramma "dan Allah yimin kalba kuda shida kan Siyama ta dawo." Ramma ta kalli tsayin gashin tace "oh kiyi hakuri ayi miki me kyau kinga sallah ce." "Kawai ni kimin yadda nace." Da Ƙyar ta yarda tayi mata guda goma shima tanayi tana irgawa. Ana gama mata ta tashi ta kwalawa Amira kira ta zo ayi mata nata. Dare ne sosai lokacin karfe 3:30 na dare Umaimah sai juye juye take yi ta kasa bacci ita kadai ce a ɗakin marar ta ke mata ciwo ta tashi ta kwanta haka tayi ta yi kawai sai ta nufi ɗakin Baba tana turawa ta ji ƙofar ta buɗe, Baba yana kiyamullaili ta shigo, Umma yau ta gaji bata kwanta da wuri ba ta soya kajin sallah tana zuwa ta haye gado bata fi minti 5 da kwanciya ba bacci ya kwashe ta, kusa da Umma taje ta kwanta Umma na juyi ta ji mutum a jikinta, "inna lillahi, subhanallahi." Umma ta fada da ƙarfi ta tsorata, Baba da yayi sallama ya kunna fitila sai ganin fuskar Umaimah ta yi ta na bacci hankalin ta kwance, Baba yayi ta dariya Umma ta sake kulewa ta fita daga ɗakin, can goshin Asuba Baba ya fita Masallaci, ya tashi Umma. Umaimah ta farka da ciwon mara ta shiga cikin Toilet ɗin Baba sai ganin jini ta yi ta kurma ihu, Umma da ke falo kamar ta yi mata banza sai kuma ta kasa haƙuri ta zo, tana ganin abunda ya faru sai ta fashe da kuka tana faɗin "shi kenan girma ya zo miki babu hankali. **** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two *Most of the problems of the world stem from linguistic mistakes and simple misunderstandings. Don’t ever take words at face value. When you step into the zone of love, language as we know it becomesobsolete. That which cannot be put into words can only be grasped through silence.* EPISODE 0️⃣2️⃣ Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, cikin ikon Allah su Umaimah suka zana neco da waec, kafin result ɗin su ya fito ta fara zuwa catering school, sosai take ganewa su Uncle Ismah nashan practical a gida Umma nayin ƙorafin tana mata ɓarnatar gas Baba zaice ta kyale ta. Result ɗin su ya fito taje ta duba yayi ƙyau sosai, haka jamb ɗin tama tayi ƙyau, makarantar su suka basu schoolaship duka su ukun saboda ƙoƙarin su ba ƙaramin ƙara fito da darajar maganar yayi ba. Umaimah BUK tayi applying cikin ikon Allah suka bata course ɗin da take so wato computer science. Ta fara zuwa makaranta cikin sa'a sosai take ganewa tare suke tafiya da Uncle Isma yana level 3 tana level 1, duk rawan kan Umaimah bata da wasu ƙawaye, dan yawan ci course mate ɗin ta duk sun girme ta, Abokin ta Aminu ne komai tare suke yi tinda course ɗin su ɗaya, wannan yasa suke mata kallon mai girman kai wasu kuma suce dan taga tana da kyau ne, sosai suka saka mata ido, wasu Click ɗin ƴan mata da suka yi yin duniya Umaimah ta shigo cikin su taƙi suka sakata a gaba babu dama tazo wucewa ta inda suke sai sun faɗa mata magana, haka zakiji suna cewa "baza mu tabbatar da ƙaryar kyau da girman kai ba sai an kafe result." Sai kuma su kwashe da dariya suna nuna ta. Bata taɓa nuna tasan sunayi ba, wanda hakan ke sake ƙular dasu, dan burinsu ta kulasu su zageta. Karatu ya fara nisa dan gaf suke da fara exams ɗin First semester sosai Umaimah ta sake dage wa da karatu. Ginin Daddy daya bari a hannun Baba tini ya kammala, gida yayi kyau an zuba komai na buƙata katangar data raba tsakani aka rushe gidan saiya zama guda ɗaya kowa da ginin shi amma gate ɗin shigo da parking space ɗin duka ɗaya ne. Su Daddy nagaf da dawowa gida gaba ɗaya dan ya kusa yin retire. Sometimes Sa'ad yana zuwa musu hutu, Hidaya na Lagos wajen Aunty Amal suna SS3 yanzu Ita da Amira. After four years abubuwa da yawa sun faru a cikin shekarun nan, Daddy yayi retire ya dawo Kano da zama Yau Litinin tin 7am ta fita daga gida Mal Musa ne ya kaita makaranta dan Isma'il bashi da lecture safe. Ƙarfe shida na yamma ta shigo gidan a gajiye, tana shigowa ta jibge a falo gaba ɗaya tayi yaushi, wata yinwa ke cinta yau bata samu damar zuwa cafeteria ba saboda lectures ɗin babu interval Sallah ma sai squeezing time suka rinƙa yi suna fita. Baba Rabi na tsokanar ta da ƴan Boko ta kawo mata ruwan sanyi da abinci, anan falon ta baje tana gama cin abincin Umma ta sakko daga sama ta ganta tayi ɗai-ɗai akan carpet ga plate da cup a gefan ta, tace "a'a yaushe kika shigo? Ban daɗe da tashi bafa, yanzu nake cewa Rabi bari na kira ki shirun yayi yawa." Umma tayi maganar tana zama a kan kujera, Umaimah ta ɗaga gajiyayyun ida nunta tace "Siyama wallahi na gaji da rage min hanyar nan da ake yi kullum haba dan Allah ya kamata a bani mota kona rage wahala, Allah yau harda jiran Malam Musa yasa na sake gajiya tinfa five muka fito amma dubi sai yanzu six nake gida. Umma ta girgiza kai "babu ruwa na wallahi wannan ba zance na bane kindai san halin Babangida inya kafe akan abu sai wani ikon Allah ya sakko." "Tsakani da Allah Siyama haka ma zaki ce? Shi ke nan ni wajen Daddy zan koma da zama wallahi sai ya yi wa wasu ikon bani ba." Tana gama faɗar haka tadau jakar ta fuuuuuuu..... tahau sama. Umma ta bita da kallon mamaki, "to ni ina ruwa na da zaki ga lefi na." Umaimah bata juyo ba. Bata daɗe da hawa sama ba Baba ya shigo gidan tin daga bakin falo Umma take jin salatin shi da sauri ya ƙaraso cikin falon yana cewa "na'am na'am, innalillahi wa inna ilaihirraju'un! Subhanallahi!! Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar!!! Allah ya gafarta mata yayi mata rahama." Umma najin haka ta miƙe tsaye jikin ta har rawa yake jira kawai take Baba ya gama wayar ya faɗa mata wanda ya mutu gabanta sai faɗuwa yake. "To sai ayi hakan in sha Allahu, na'am na'am sai nayi musa maganar muji in zasu duk saimu tafi gaba ɗaya, kai wannan Yaro Allah ya basa hakuri, to shima Sa'adun zashi ke nan?" Ya ɗan yi shiru yana sauraren abinda ake faɗa a cikin wayar, "Eh ya kamata Allah ya basa hakuri ita kuma Allah ya gafarta mata." Sukayi sallama yana sauke wayar Kafin Umma tayi magana, yace "Azumi kinji matar Dattijo ce Allah yayi mata rasuwa ɗazu wajen haihuwa." Baba ya faɗa yana zama akan kujera, Umma ta rafka salati tini idanta ya tara ruwa, sunan Allah kaiwa take kira. "Allahu Akbar kabiran wani cikin gare ta ke nan? Baiwar Allah yarinya mai kirki Allah ya jikanta yayi mata rahama, Allah sarki Ãdil uwa ta tafi." Baba yace "toya za'ayi haka Allah ya tsara, bata haihun bama ta mutu wai dama cikin bai isa haihuwa ba nakudar ta taso ana ƙoƙarin shiga da ita theater ta rasu." "ikon Allah ke nan." Umma ta faɗa da jimami, Baba yace "kinga muje ki bani Passport ɗina munyi magana da Daddyn su, yace yau zai dawo daga tafiyar da yayi gobe zamu wuce wajen Dattijo nida shi da Sa'ad in sha Allahu dama visa nake ji samuwar ta zai yi wahala to kuma sai yace min yayi magana da Mijin Amal yace za'a samu, zan yi magana da Uncle ɗin ta naji inda me zuwa ta bangaren su duk saimu tafi tare Allah dai ya gafarta mata." Umma ta amsa da "Aamin." Yana karɓar Passport ɗin ya sake fita, Umma na kokarin shiga wajen Mami sai gata ta shigo nan suka haɗu suka yiwa juna gaisuwa. Lokacin da ƴan gidan suka ji mutuwar abun ba ƙaramin taɓa su yayi ba, Umaimah sai addu'a take mata jikin kowa yayi sanyi. Washegari da sassafe Aliyu yakai Baba da Daddy Malam Aminu Kano anan suka haɗu da abokin Baba Uncle ɗin Aysha suka sake yi masa gaisuwa suka wuce Lagos, suna sauka a Lagos suka samu Sa'ad yana jiran su komai nasu ya zama ready babu wani ɓata lokaci suka bi Qatar airway suka wuce UK. Dada har gidan su Aisha tazo musu gaisuwa, Hakimi da mutanen shima sunzo, Umma da Mami acan suke wuni, Munnirah ma da ita ake zaman makokin A'isha, su Baba Dr duka sunzo sun yi wa iyayen ta gaisuwa Khadijah bata samu zuwa ba dan ta raka Mijin ta ganin likitan shi a Germany sai gaisuwa tayi musu ta waya. Bayan kwashe tsawan awanni suna tafiya suka sauka a birnin London, taxi suka samu Sa'ad ya basa kwatancen gidan Fahad ya kaisu har ƙofar gida. Fahad na ganin Sa'ad ya rungume shi. Gaba daya yayi wani iri kamar ba shiba jikin sa duk ya saki, kana ganin sa kasan ƙarfin hali kawai yake yi dan ba ƙaramin dukan sa mutuwar tayi ba. Bayan kwana uku da rasuwar A'isha su Baba suka yanke hukuncin zasu tafi da Ãdil (ɗan su na fari) wanda gaba ɗaya ba zai fi shekara uku ba, dan ma Yaron lafiyayye ne yana gudun sa ko ina, A'isha renon ƴan gayu tayi masa, tinda ta haifeshi Nanin shi ke kula da shi yafi sabawa da ita akan Maman shi sai Papan shi da indai yana gida to suna tare, zuwan su Mami nema yake ɗan zuwa wajen ta ita ma yana ganin Fahad zai koma wajen shi, ko lokacin da Aisha na raye yana wahala ka ganshi a wajen ta komai Nanin shi ke masa da Papan shi dan haka sosai yafi sabawa da shi akan ta. Fahad jinsu kawai yake yi amma bayajin duk duniya akwai wanda zai iya bawa riƙon Ãdil. Anata magana baice komai ba, Baba yace "Dattijo bakace komai ba?" Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan a hankali yace "Baba zan riƙe sa da kaina." Daddy da Uncle ɗin Aisha suka buɗe baki zasuyi magana Baba ya hana, yace "to hakan yayi, Sa'ad kuje yaɗan huta ko Allah yayi muku albarka ita kuma Allah yaji kanta." Suna fita Baba ya cewa su Daddy suyi hakuri subar masa ɗan sa shima baya goyan bayan a raba shi da ɗan yanzu ciwon sai yayi masa yawa kuma an riga an yaye shi yana cin abinci sannan ga Nanin shi. Saida aka kai ruwa rana tsakanin Daddy da Baba Sannan suka haƙura akan za su bar masa shi a hannun shi, Uncle ɗin Aisha saboda tsabar kara baice komai ba sai addu'ar Allah ya raya sa da yayi. Randa suka cika kwana bakwai a UK suka baro Fahad da ɗan shi Ãdil bayan sun sake yi masa nasiha dajan kunnen ya kula da shi. ****** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN https://wa.me/+2348039352724 VOLUME TWO *It is never too late to ask yourself, Am I ready to change the life I am living? Am I ready to change within?’ “Even if a single day in your life is the same as the day before, itsurely is a pity. At every moment and with each new breath, one should be renewed and renewed again. There is only one way to be born into anew life to

Chapter 1 of 27