Share this page
haɗa kaya don har ta saka ta a group ɗin su na yan diaspora (yan zaman ƙasar waje mutanen mu) sosai Umaima take tallata hajjarta abin mamaki da yawa sun nuna interest suna son kwatanta, suka yi magana da Ramla tace zata zo shi ne take ta aikin har Ãdil ya dawo daga makaranta, Mrs Lawrence ta yi mishi wanka ya zo yana saka ta surutu, Maamah kaza Maamah kaza kai Ãdil surutu ma idan yayi yawa babu daɗi ta lallaɓa shi ta kunna mishi cartoon ta samu ta kammala, bayan ta yi sallah tana duba message a WhatsApp Mrs Lawrence tace tayi baƙuwa ta fito suka haɗu da Ramla Umaima da murna ta tare ta, Ramla tace "sister sannu da ƙoƙari mutane suna ta son kayan nan." ta kawo mata drinks da snacks da ta yiwa Aadil na makaranta, Ramla tace "kai amma yayi daɗi naga ke mai kokari ce why not ki rinƙa yi a nan za ki yi ciniki sosai ko biki ko suna ko sallah muna gatherings sosai." Umaima tace "Dan Allah?" da murnar ta tace "me zai hana ni indai zan samu alheri bani da damuwa." Ramla tayi dariya, nan take faɗa mata sun daɗe a UK mijinta likitan ƙoda ne su mutanen katsina ne Umaimah ta dafe ciki, tace "Allah ya bar mu da kodarmu, ciwo maƙiyi ne." "Amin." Ramla ta faɗa tana dariya ta dauko mata kayayyakin tana dagawa tace "kinsan me? Za a yi Exbition a Leeds Town Hall in 3 days why not mu yi displaying kayan nan saboda za kifi samun customers and you will gain recognition, kinsan turawa suna son wannnan." ta ɗaga wata Kampala bubu, Umaimah tace "toh ko har abincin mu zan yi? "Kwarai kuwa display ake yi na abubuwa babu abunda ba a siya akwai wanda zan tambayar mana kuɗin stalls zan siya miki." Ta rungume ta, "nagode Aunty Ramla ina gullisuwa ma da alawar madara fah. "great meyasa ba ki yi posting ba? Ai kin ga babu wanda na sani sai ke da Allah ya hada mu." Umaima tace bari na shiga kitchen na yi Alawar madarar ma suka shiga tare, madarar da Mrs Lawrence ta siya na gida ta kwashe ta yi Alawar madara, da gullisuwa, sun gama sun dawo falo kenan Fahad ya shigo zai wuce ɗakin shi Ramla tace "barka da yamma." Yayi mata banza, "ni zaka mannawa hauka?" Umaima ta faɗa a ranta, ta kalli Ramla tace "kurma ne ai baya ji ba zai amsa ki ba." ya ɗan tsaya ya dakata da tafiyar sai kuma ya wuce ɗakin "lallai yarinyar nan wato shi ne kurma, abunta ya daina ba shi mamaki da gaske she needs medical attention.' Jikin Ramla yayi sanyi tace "Allah sarki, Allah mai halitta lalle mutum tara yake be cika goma ba." Umaima ta yi murmushi "bari na tafi tunda maigidan ya dawo, bari na debi wasu sai na fara dora miki." "toh shikenan." ta dauko leda ta zuba mata yafi rabi "wannnan sai mu tafi da shi can ɗin hakan yayi?" Ramla tace "eh." Ta kira uber, suka fito bakin gate tana kara mata godiya ta ce ta shirya ranar zata biyo ta dauke ta. Suna fita ya fito ya shiga kitchen yana ta dube duben madara zai sha tea babu, shi yayi dropping Mrs Lawrence tayi shopping, ga shi ta tafi har zai kira ta a waya ya fasa, ya dawo falo nan ya ga alawar madara da su gullisuwa oh shiriritar da ta yi kenan ya hade shi gaba ɗaya ya ɗauki key ya shiga mota ya fita, ita kuma suna sallama da Ramla ta dawo ciki. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE1️⃣8️⃣ Tana shigowa ta ga babu Alawar madarar ta, ta koma kitchen ta duba babu, "kai wannan mutumin yayi halin na shi, ni zai yi ta mannawa hauka shi wato duk yarda zai daƙile ni ya iya, kai innalillahi wa inna illahirrajiun." Wani abu ya tokare mata makoshi kamar zata yi kuka ta danne, indan madarar shi ne ai dan bata san gari ba ne shi ba a cin arzikin shi, kai subhanallah ta zauna ta ji kamar jiri zai ɗauke ta, ta tuna aiki ya sa ko abincin rana bata ci ba ta shiga kitchen ta ɗora musu coucous tayi sause suka ci tare da Ãdil ranta duka babu daɗi ƙarshe ma shi ta barwa ta dauko wayarta ta ga Hidaya ke kiran ta ta ɗaga. "wlh baki da kirki ba kya nema na." Hidaya tace "kusan kullum sai mun yi magana da Amira, amma ke daɗi aure." "ke bafa haka ba ne abubuwa ne sun yi min yawa kya hada ni da Amira? "To meye ita ma ai Amarya ce." "eh Amarya ce ni kuma CEO ce ina harkar arziki kina haɗa ni da cima zaune." Hidaya tayi dariya "Ke fa baki da kirki sai na faɗa mata." faɗa mata mana a gabanta ma na faɗa tana makarantar ne? Ni kwana biyu bamu yi magana ba tunda ta kular dani." "me tayi miki? cewar Hidaya, nan ta faɗa mata kiss ɗin da suka yi suka manta da ita a vedio call, Hidaya ta yi dariya tace "ke har yanzu babu cigaba kenan? "wlh akwai cigaba ina haɗa yan canji na ina ruwa na dashi." Allah ya yaye miki son kuɗi." "nuna min bolar su?" "ba dai kya kula da yayana." "da Allah tafi can yayan naki kurma da baya son mutane." Ke zaki gyara shi. Umaimah tace "nidan Allah mu bar maganar yaushe zaki gama ne? In 2 months time. "masha Allah ki ce mun kusa zuwa Nigeria Amaren bayan sallah kenan." Suna falo da Aadil tana koya mishi funwork, dan yanzu kwata kwata ita ke koya mishi komai na makarantar shi baya zuwa wajen Papan shi ya koya mishi kamar da, "yawwa we are done sai Hausa lesson Ina kwana -good morning Repeat after me." Aadil ya maimaita, Sannu da zuwa -you are welcome Zauna -seat Tashi-stand up sai tace "Ãdil HA." shima yace "ha." No I mean what does Ha means? ya kara cewa ha. "nooo open your mouth." ya gyaɗa Kai ya buɗa bakin shi. Sun daɗe suna yi suka dawo karatun Alkur'ani sun fara da suratul Fatiha kuma Alhamdulillah yana ƙoƙari sosai, Fahad ya dade yana sauraren su he was surprise yadda Ãdil yake kokari, shi wlh rashin lokaci ya hanashi koya masa, dan sun fara ya watsar, abun yayi mishi daɗi har yayi murmushi ya ƙaraso suka haɗa ido ya ɗauke kai, Ãdil na ganin shi yace "Papa sannu da zuwa." Fahad ya kalle shi, ya sake cewa "Papa ya aiki?" yace "fine." "No Papa you say Alhamdulillah." yace "Alhamdulillah it's time for bed let's go." ya ja hannun shi, da sauri Umaimah ta sha gaban shi tace "ina kaya na? Yayi mata banza zai wuce ɗaki tace "mutum ya jajirce yayi abu ka ɗauke fisabillahi, ka ɗauke Sasi, ka ɗauke keke, ka ɗauki waya gullisuwar ma bata tsira ba, wannan ba halin ƙwarai ba ne." ya juyo a fusace yayi kanta ta taka da gudu ta shige ɗaki ta saka key, ba shi kurma ba ne uban me zai ce mata ya girgiza Kai ya shige ɗaki ***** Kwana biyu na ji ki shiru da fatan ku na lfy uwata? Daddy ya faɗa, kamar tace be bata Sasi ba dai ta yi shiru, tace "lafiya ƙalau Daddy, kwana biyu ina busy ne." "me ake yi nasan ki da ƙoƙari." Tayi dariya "Daddy ku ci-gaba da yi min addu'a na kusa fasowa gari." Allah ki ce Alhaji nake? "wlh Daddy." ta faɗa, "Daddy bikin Hidaya fah ya kusa pls ina Son zuwa." Daddy ya ce kin faɗawa Dattijon? "Ah ah Daddy ba mu yi maganar ba tukunna." "toh shi ya kamata ki sanar mishi, shi ne mai bada izini ba mu da hurumi." ba haka ta so ba amma dai ta san lokacin idan yayi dole zata taho, ita kayayyakin sanar ta take son siyowa zuwan yana da matukar amfani suna sallama kiran Ramlah ya shigo suka gaisa take fada mata, komai ya ƙare ya kamata tayi wasu kafin gobe ga kuɗaɗen ta a wajenta daɗi ya mamaye zuciyar ta, tace mata "matsalar babu madara ba sanin gari na yi ba." Ramla tace "babu komai a kuɗin sai a siyo madarar mai delivery sai ya kawo." tayi godiya sosai ba yarda bata yi da ita ta ɗauki kuɗin ba tace a'a suka yi sallama. yanzu badan ɗan kurma ya kwashe mata ba ai da kaɗan zata ƙara amma babu komai shi ya ga duhu wlh dai ya sha kunya. Leeds Town Hall Ramla tana taya Umaimah yin prices na kayayyakin don sosai kayan da yawa ga su snacks da gullisuwa, Alawar madara da abinci mu na gargajiya abun mamaki nan da nan aka kwashe dogayen rigunan, mutanen mu sun raja'a a stall ɗin Umaima masu cin abincin gida wata mata daga ganinta Bahaushiya ce ta karɓi number Umaimah ta ce za su yi birthday party zata yi ordering snacks a wajen ta, an karɓi lambarts sosai, ta zama busy abun sha'awa har da turawa masu son dogayen riguna, ta siyar da kowacce akan 25pound ta ɗauko waya tayi lissafi 1 pounds akan 2000 yake a kuɗin mu na Nigeria kowacce ɗaya akan 50k kenan ta rufe baki tana murna daya ke event ɗin na dare ne sam bata san lokaci ya ja ba sai da ta kalli agogon hannunta, a ranta tace ai dai ta tambaye shi izini kafin ta fito duk da dai be ce mata komai ba, har a paper ta rubuta ta bawa Ãdil ya kai mishi ɗaki kuma yace ya kai, amma ko kallonta be yi ba, yana zaune Mrs Lawrence ta taya ta fito da kayayyaki ko tari be yi ba kai mutumin nan akwai mugun hali, Ramla ce ta katse mata tunanin ta rungume ta, tace "Sister Umaima it was a success." Umaima tace nagode Aunty Ramla ta miko mata kuɗaɗen hannunta ta ɗebi wasu ta miƙawa Ramla suka yi ta jayayya da ƙyar ta karɓa ta rage tace yayi yawa suka fito daga Hall ɗin sun sauke ta a gate ta shigo tana murna ran ta kamar takarda ta buɗe kofa a rufe, ta dawo ta window fitila a kunne tabbacin yana falon ta bubbuga ƙofar Fahad yana zaune yana aiki a system ya ji bugun ta, zai koya mata hankali ina ta sani gidan uban wa ta je? Salon wani abu ya faru da ita su Daddy su daga mishi hankali idan ta kwana a waje gobe ba zata ƙara ba, "Dan Allah ka buɗe min kofa wlh na gaji." sai gani tayi ya kashe fitila, tashi yayi kenan haushi ya kamata ta ɗauko bottle water ta sha ta dawo passage ta zauna ji wani likutin wulaƙanci, tana zaune tana gyangyaɗi marar ta ta cika da fitsari haushi ya ƙara kamata zai ga tsiya kuwa ta laluba jakar ta ta ɗauko kibiya, Babangida ma idan ya bata mata rai ramawa take ba wanda ya sani sai Uncle Ismah balle shi ta nufi motar shi ta sace mishi tayoyi ta dawo ta shinfiɗa mayafi ta kwanta, bata jima da kwanciya ba ya buɗe ƙofar ya ji abu ya tokare, yayi ta dukan kofar bata motsa ba sai ya ga ruwa kusa da ita ya yayyafa mata ta mike da sauri ta shige yana mamakin saurin tashi haka babu magagi, toilet ta fara shiga tayi fitsari ta dawo kitchen ta haɗa duk abunda zata buƙata ta yi sauri ta kammala dan gobe yinin daki zata yi ta shige ta saka mukulli. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Fallow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 1️⃣9️⃣ Ya idar da sallah ya fito yau be tsaya yin Azkar ba yana sauri ya fito ya shirya da brief case a hannun shi ya rataya jakar laptop ya fito ya tadda Ãdil Mrs Lawrence tana rarrashin shi ya ci abinci mashed potatoes da tea ne yaƙi ci yana ta rigima yana knocking ɗakin Umaimah yana kiran Maamah ta yi mishi lunch, bata buɗe ƙofa ba, yace "pls Didi be a good boy okay." ya faɗa yana sauri tea ɗin daya haɗa ma kurba biyu yayi ya ajiye meeting za su yi yau da GM kuma shi ne zai fara presentation ya fito ya shiga mota ya tayar ko motsi batayi ba, abun ya ba shi mamaki ya fito tyres ɗin sun yi flat fuskar shi har gumi ya tsartsafo saboda tashin hankali, ok shiyasa tana tashi ta shiga ciki da gudu? takaici ya kama shi ya duba abin buga iskar a boot din motar be gani ba, yayi mamaki toh yana ina? Ya duba time saura 10 mins a fara meeting haka yayi kiran uber ya tafi office, Allah ya so ya je 2 mins before time ya kira Mr charles ya je gida yayi fixing tyres sai San nan ya tuno abun iskar ma yana motar Mr charles. wannan yarinyar bata da hankali Sa'ad yace she is fine idan zai yi mata hukunci lahani zai yi mata Gm ya shigo aka fara meeting. Tana ɗaki ta yi wanka taci abinci ta fara dinki, dan ta gaji tayi da yawa saboda akwai demand sosai musamman dogayen riguna harma da gullisuwar akwai masu zuwa pick up tana bada timeline na lokacin karɓa kar Ɗan kurma yana gida bata son ciwon kai ko yaya ya kare da mota ta leƙa window mota bata wajen ta shiga kitchen ta fara Alawar madara ta gama ta ɗauki pictures tayi posting a status da group ɗin Yan diaspora da Ramla ta sakata ta rubuta yan Leeds azo a jiyar da rai abunda yake so, ta ƙara rubuta ku zo ku siya kar na koma Bichi, come and buy from me ga ta nan da Zafin ta pls send a dm. Ramla ta yi kiranta tana dariya "sister Umaima kina burge ni yakama ki buɗe banki anan." "to Aunty Ramla ke ce ido na. "eh ya kamata a buɗe bankin BARCLAYS." su na yin sallama Uncle Ismah ya kirata yace "wai lafiya kike roƙo a siya abun ki ko baki da kuɗi ne? Uncle Ismah ba fah roƙo ba ne neman customer ne, so nake mu samu kuɗi kasan harda share ɗinka a gullisuwar nan tare muka sha wahala."yayi dariya "wlh ki rage son kuɗi Umaimah kar Allah ya jarabce ki da kuɗi ya Fahad ɗin yana ganin abunda kike yi? "wani abu? kamar wacce ta yi sata wa ya ke zancen wannan ma, yawwa Uncle Ismah kace Siyama ta kira ni." "ke ki kira ta dai ba kuɗi gare ki ba." ta tsokane shi suka yi sallama, ta kunna TV har ta ɗauki remote wayarta ta yi kara masu karɓar order suka rinƙa zuwa ɗaya bayan ɗaya suna karɓa Umaima tana ta murna. Kai arziki yayi ta saita camera ta ɗauki hoton kuɗin ta tura group ɗin family lounge, ta tura Vnote "Baba shigowa ta kano sai da jiniya, Siyama yanzu na wuce iko da gani ganin ki Attajira na ke yanzu." har an fara turo mata message Ãdil ya shigo ta kashe data an yi mishi wanka ta saka shi a gaba tace "celebration zamu yi yau dole mu ji daɗi Didi." ta shirya ta kira uber ta yi searching googled map nearest eatery in Leeds ya bata options tasa Ãdil ya zaɓi Faversham suka tafi can Ãdil ya ɗauko kayan ciye ciye cake ne shawarma pizza, burger da yawa suka dawo gida suka baje suna ci Mrs Lawrence ma ta bata da yawa, Umaima ta ci shawarma ta lumshe ido tace "yau na Razana talauci ya rasa yadda zai yi dani sai dai ya koma gefe yana kallo na, ku yan yara gumi na nake ci." shi dai Ãdil kallonta kawai yake yi can yace "Maamah my birthday is on 4th." really we gonna celebrate Didi, ta kirga saura 3 days suka shiririce zasu gayyaci classmate dinnshi Ãdil yana ta murna shigowar shi kenan ta tuna ta sace mishi mota ta kwashi ledarta ta taka da gudu daki Ãdil ya saka dariya, yace mishi ya kira Mrs Lawrence ta gyara wajen ya kalli Kofar ɗakin ta ya girgiza Kai ya wuce Ãdil ya bi bayanshi "Papa my birthday is on 4th." yace yea I know we will celebrate it. "yeee thank you Papa." ya faɗa yayi hugging ɗin shi. Washegari ta yanka Cardboard a matsayin invitation card yau zai raba wa classmate din shi, har timeline an saka su 20 ne a class ɗin an bawa kowa tun fitar Fahad yau take aikin snacks ta bawa Mrs Lawrence siyan abubuwan da zata yi amfani da su harda drinks da zata yi ordering cake data yi converting to Naira tace yayi mata tsada da kanta tayi baking cake ta gama komai ta shirya ta saka wata blue-black gown ta saka kohl ta shafa lipgloss ta yi kyau sosai an shirya birthday boy sun gyara arrangement ɗin falon yara suka fara taruwa ta kunna waka a wayar ta oya shake body ta saka su a gaba suna rawa sai ta tuna da Friday party sun ci snacks an yi games hide and seek sun yi wasan balloons sun kawo wa Aadil gifts da yawa, amma an yi scattering falon an watsar da throw pillow gashi kujerun farare ne an shafa maiko da chocolate a jikin su, Fahad yana aiki ya tuno yau ne birthday ɗin Ãdil aiki ya rike shi bari dole ya gama ya ɗauke shi su fita ya san yanzu yana can yayi fushi yayi connecting CCTV sun hargitse anata rawa komai upside-down tana cikin su ta ɗauki wannan ta ajiye ta ɗauki wancan ran shi ya baci ya kashe ya dafe kan shi he is a private person baya son taro, meyasa ta tara mishi yara a gida? she is very annoying sai ta nuna bata da hankali ya ɗauki key ɗin motar shi ya fito, Umaima daya ke ta bada timeline babu ɓata lokaci aka fara zuwa ɗaukan yara, wasu ma anan suka jira lokacin ya cika sun fito tana yiwa iyayen yaran godiya "Maamah I'm soo happy thank you." Ãdil ya faɗa, "u are welcome Didi." ta saka musu wakar spyro joy is coming suka cigaba da rawa ba su ji shigowar shi ba sai jin kidan ya mutu sukayi da ƙarar faduwar abu tana juyawa taga wayarta ya kwankwatsa da ƙasa ta kalle shi jikinta har rawa yake yi ta ƙarasa ta ɗauki wayar, ta kalle shi ta bude baki tana rufewa ya kai sau uku ta rasa ma mai zata ce mishi tayi Alkawarin ba za ta sake yi mishi kuka ba amma bata san lokacin data durkushe a wajen tana gunjin kuka ba, ranshi a mugun ɓace yace "I warn you not to mess with me I don't want gatherings you have to learn the hard way." Yana gama faɗar haka ya shige ɗakin shi ya barta anan tana kuka abun yayi mata ciwo wlh sai ta rama. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 2️⃣0️⃣ Sorry Maamah, sorry Maamah. Ãdil ya matso kusa da ita yana share mata hawaye, ta kalli fuskar shi ya damu kamar zai yi kuka ta yi mishi murmushin yake tace "it's okay Didi go and watch cartoon." ya tashi ya shiga ɗakin shi jikin shi a sanyaye, Mrs Lawrence ta taho ta fara gyara falon. Da ƙyar ta mike tana jan ƙafa ta shiga ɗakinta ta saka key, duk abunda yake yi mata be taba ɓata mata rai irin wannan ba ya ɗauke Sasi ya ɗauke keke yanzu ya fasa waya, ta share hawaye tace wlh sai ya ji abinda ta ji ba wanda zata kai wa ƙarar shi ta kalli wayar ta danna button ɗin gaba-daya screen ɗin a fashe ya ke ta mutu ya jawo mata asara yanzu dole ta siyi waya, ta san za a yi ta neman ta gobe aji shiru dan akwai masu karɓar order, ga matar da tayi mata zancen birthday ɗin danta ta ƙara kiran ta har ta tura mata charges ɗin ta, amma babu komai idan baya son mutane ita sana'ar ta ta mutane ce Azzalumin kawai kamar tsinto shi aka yi kamar ba ɗan Daddy ba, kamar an mintsine ta ta tashi ta fita ta buɗe ƙofar ɗakin shi taji a rufe ta yi knocking "kana ji na wlh ka ɓata min rai sai Allah ya bi min hakkina." ta buga da ƙarfi "ka yi shiru wlh zan yi Ashar kuma yadda ka ɓata min rai kaima ba za kayi farin ciki ba." taji shiru ta haƙura ta koma dakinta. Washegari da safe Ãdil ya kalle shi yace "Papa I'm not happy with you, you always scold Maamah and you damaged her phone." Aadil ya tsare shi da ido an shirya shi za shi makaranta, ya kalli yaron ya ɗauke kai, dama tun be kai 2years ba yayi understanding he is very observant yaro ne mai wayo da basira dole wani shirmen na ta ya rinka ɗauke kai kafin tasa yaron shi ya tsane shi, calmly yace "I will ignore her and distance myself for my own emotional wellbeing." horn ɗin da aka yi shi ya saka ya bar maganar Mrs Lawrence ta fita dashi. A ranshi yace "in sha Allahu ba zan ƙara kula rashin hankalin ta ba, ta yaya ma aka zo nan? Har ta raina shi haka." ya tashi ya fara gyaran ɗakin ya canja bedsheets ya fara arranging komai da idon shi ya kai wajen har kan mirror da turarukan shi suke kai ya koma toilet nan ma sai da ya tabbatar yayi mishi yadda yake so sannan ya shiga wanka, ya fito ya shirya ya kalli falon an gyara amma Sam be yi mishi ba ya ɗauki wayar shi yayi online shopping ya zabi wasu kujeru milk colour da carpets komai na falon sai da yayi ordering sabo ya biya da card ɗin shi za a yi mishi delivery, yana zaune aka kawo ya kira charity shop su zo su kwashe tsofaffin, aka shirya falon komai yayi to his own taste, Mrs Lawrence ta sake gyara ko'ina komai aka saka shi a muhallin shi. Umaimah na ɗaki a kwance kamar mara lafiya tun safe a kwance ta ke tana dai jin maganganun mutane a Falo ana ta turanci, ta shiga toilet tayi wanka ta saka wata atampa turquoise blue tayi mata kyau sosai tana gama shiryawa ta fito sabida bacin ran jiya ko yunwa ma bata ji, ta fito ta ga an canja komai, hmmm oh sabida ita aka canja ke nan wato ta ɓata mishi waje, ta shiga kitchen tea kawai ta haɗa ta koma ɗaki tana zaune aka yi mata knocking Mrs Lawrence tace tana da visitor ta fito Aunty Ramla ce ta rungume ta "me ya samu wayar ki tun jiya?" "wlh faɗowa ta yi ta lalace." Ramla tace "nayi tunanin haka sorry for that an yi ta min magana you need another phone." ta faɗa, ta fito da wata cute phone a jaka tace "ga wata ki yi amfani da ita babu abunda ta yi Abban su Suhaila ya canja min wata saina ajiye ta, idan kuma sabuwa kike so sai mu je ARGOS ki zaɓa." "kai Aunty Ramla wannan kauna bata yi yawa ba?" Umaimah ta faɗa tana rungume ta, "wlh tun jiya nake jin babu daɗi na samu yaya a UK thank you." Ramta tayi murmushi "kar ki damu." ta cire sim ɗin ta a tsohuwar wayar ta fara kokarin settings wayar iPhone ce mai kyau. ***** Vedio call su ke yi da Amira, tace "wai Amira wannan ki bar

Chapter 8 of 27