Share this page
faru wallahil azim ba laifi na ba ne duka har da sharrin mace. har Baba zai dakatar da shi sai ya ƙyale shi ya faɗa da bakin shi saboda Khadija ta ji da kunnenta daga gareshi, ya fadi irin makircin da Zaliha ta mishi. "Allah ne kadai ya san irin cutar da ta yi min iyakar abunda kunne na ya ji kenan na sake ta." Baba ya tari numfashin sa da cewa "ta zo nan duk ta faɗi abunda ya faru." wani sanyi ya a ji a ran shi, okay shiyasa aka yi musu kyakkyawar tarba. Kuka Umaimah ta ke yi harda shassheka tunda Baba ya fara magana Khadijah ta kame ta juya fuskar ta bangaren Baba ta kafe shi da ido gata dai a zaune tana sauraran su amma kamar an yi formatting kwakwalwarta. "wannan shi ne abunda ya faru kuma tazo neman gafarar Khadija bata tarar da ita ba tana wajen makokin maigidan ta. "Zazzzzaliha Hayateey." Khadija ta ƙwalla da karfi sai yaraf ta faɗa kan cinyar Munnirah, ai kafin kowa ya kula sai ganin Tahir aka yi a gabanta kamar walkiya zai taɓa ta a gigice kuma sai ya mayar da hannun shi. "Subhanallah." gaba daya matan suka rufu a kanta duk sun firgice "Yaya Khadija." Amira tana kuka tana girgiza ta, Ummi ta rike Umaima ta hana ta tashi ku gafara Baba Dr ya ɗauke ta Ibrahim ya rufa mishi baya Dr Huzaifa yace "can I join you pls?" Baba Dr yayi mishi alamar ya biyo su, ɗakin Ismael suka shiga ta ita kowa yayi jigum jigum. In sha Allahu babu wani abu Khadija ta sha jarrabawa cewar Daddy Subhanallah Baba isah ya faɗa, Tahir ya kasa hakuri ya yi ɗakin Ismael yana tsaye daga waje Ibrahim ya fito da sauri yace ya shiga mana, Daddy ya tambayi Ibrahim me ake ciki yace Allura zai siyo. Yaseer ya je wajen Umaima ya mika mata hannu Ummi tace your Uncle ta rungume shi tana kuka Umaimah ta bawa kowa tausayi, wannan kukan da take yi har ran shi yake jin shi kamar ana keta zuciyar shi da reza, Baban ABU ne da Baban sama su ke magana a hankali a tsakanin su, Ibrahim ya shigo da sauri ya shiga ɗakin. An yi mata allura bata kai minti biyar ba tayi bacci,Tahir gaban shi faɗuwa yake yi idon shi kamar gauta shi dai da za a bar shi da yayi jinyar ta wata zuciyar tace ai ba muharramarka bace. Baba Dr yayi musu alama su fito aka ja mata kofa. .......Likita yaya jikin nata? Daddy ya tashi ya nufi Baba Dr yana tambayar shi, yace "shock ne sannan ciwonta yana son motsawa amma in sha Allah idan ta farka zata samu mutsuwa kuma dole zata sha magani ko na 3months ne." ajiyar zuciya Umma ta sauke kowa sai hamdala yake yi Amira tace Alhamdulillah. Adil ne da Iman suka Shigo da gudu suna ta dariya "Maamah I will carry my sister along when we are going." ya faɗa yana neman Umaima dayake mutane da yawa har ya je wajenta, ya bata fuska yana share mata hawaye yace "why are you crying?" Yaya Surayya ta ja su suka hau sama. Daddy yace Alhamdulillah kowa ya nutsu yace dama meeting mu ke yi kuma zuwan ka yayi dai dai.. Fahad da ke zaune kanshi a ƙasa har yanzu gabanshi ya faɗi tun dazu ya kasa ɗago wa ya kalli kowa, shi kanshi kunayar kanshi yake ji, da girman shi da shekarun shi ace yayi wannan abu ai da kunya, amma yaji wata murya kamar ya san me ita. Daddy yayi musu bayanin komai in brief abunda ya hada su, "shi ne dalilin dana ce maka muna da meeting." Yayi maganar yana kallon Baba Isah. Tahir yayi shiru yana jinjina dattako irin na su ɗan shi fah yake yiwa hukunci, Tahir yayi shiru shi me zai ce, Baba Isah yace "ba za a yi haka ba." Dr Huzaifa ya tambayi me yake faruwa Tahir yayi mishi bayani. budar bakin Dr Huzaifa cikin turanci sai cewa yayi "they are having marital issues, they should work towards resolving it especially considering Fatima's pregnancy." Fahad baisan lokacin daya mike ba kamar wanda wutar lantarki ta ja, "Zarahhhh." ya faɗa yana kallon inda take zaune, kowa da mamaki a fuskar shi yake kallon ta. "Ɗana." Tahir ya kira Fahad, suka haɗa ido da sauri Tahir ya riƙo hannunshi ya rungume shi, kowa sai mamaki yake Baba yace "ku yi mana bayani." Umaima ta sauke kanta daga cinyar Ummi, ko dai Abba ne? farin ciki ya cika Tahir ya buɗe musu hannu duka su biyun ya rungume su yana hawaye yace "ƴaƴana sun samu misunderstanding, aure ya gaji haka, yarana ba za ku yi mistake ɗin dana yi ba da yardar Allah." Ikon Allah ku zauna. Baban sama ya faɗa "me yake faruwa?" Tahir yace Isma'il ɗana ne Ranar wata jama'a a Haram.........ya basu labarin yadda suka haɗu da yarda su ke gaisawa a waya yake jin muryar Khadija a tare da Umaimah, da a kwanakin da suka yi magana da Fahad yace yayi musu addu'a sun samu matsala, kuma yayi addu'a sosai da kiran daya yiwa Umaimah duka ya faɗawa su Daddy ya ɗora da cewa "ina nemawa ɗana Afuwa ayi haƙuri." Allahu Akbar Baban ABU ya faɗa "shikenan ayi musu afuwa. Daddy yace "shikenan akayi musu fada sosai. Umma sai kallon Umaimah take yi tana mamakin Umaima da ciki, Mami ta haɗa kan matan ayi musu girki Amira ta kalli Tahir tace "wlh shi na gani a airport mai kama da Umaimah." Tahir ya kalle ta tabbas yace "Ummina Masha Allah." da mamaki Baba yace kin san shi? Tahir yace "zuwana na farko neman Hayateey muka hadu a airport, kafin na dawo na biyu." Aliyu da shi ya tsiri tafiyar yayi mamakin ikon Allah, Ibrahim yace "ai mun haɗu ranar ɗaurin auren yaya Khadija. yace "zuwa na biyu kenan." Sa'ad ya zunguri Fahad yana mishi dariya, Fahad bai kula shiba aka sallami matan suka tafi part ɗin Mami, Umaima ta rike hannun Ummi su tafi ɗakinta, Baba Isah ya fuskanci su Daddy yace "yanzu Khadija tana iddah haramun ne a furta wani abu daya danganci neman aure ko wani abu makamancin haka, amma dai ayi mana Alfarmar su rinka gaisawa ko a waya ne yana jin lafiyarta. Daddy yace babu komai in sha Allahu, adai kiyaye hakkin Allah. Daddy ya fada,Tahir ya sunkuyar da kai yana murmushi anan aka yi kiran sallar Azahar suka nufi masallaci. Aliyu da bashi da sakewa har sun saba da Yaseer Dr Huzaifa shi da Ibrahim suna ta tattaunawa akan field din su har yake fada mishi ya samu scholarship na karo karatu a US. Fahad surukin shi Tahir ke tsokanar shi ya kawo kuɗin addu'ar da yayi mishi a Harami ana ta raha. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 5️⃣5️⃣ Farka warta kenan wajen karfe 6 na yamma Munnirah ta shigo ɗakin ta duba ta, a ka'ida zata farka tun 4. Tana ganin ta tashi tace "my sis kin tashi? Khadijah ta buɗe idonta da yayi mata nauyi ta tashi ta zauna. "sannu my sis bari na kira Baban Iman yace idan kin tashi na kira shi." ta fita bata daɗe ba ta dawo tare da Baba Dr "yaya kike jin jikin naki? akwai inda yake miki ciwo ne? Ta Nuna kirjinta yace babu komai zai daina, bari a kawo miki magani. ya kalli Munnirah yace "make sure she eats something, kar ta wahalar da kanta she should rest pls." In sha Allah. ta faɗa, Baba Dr ya fita. Tunda aka ce ta farka Tahir ya kasa sukuni su Baba Isah sun tafi shi ya kasa tafiya yana jiran ta farka, yana tare da Baba Dr yana ƙara wayar mishi da kai akan ciwon nata don ya damu da yanayin da ya ganta ɗazu, su Yaseer da Dr Huzaifa ma sun koma hotel. BABA Dr yace sallah zata yi sai ku je ka duba jikin nata ko? ya gyaɗa Kai, surukin shi ne amma tun can da ma baya wani jin Nauyin shi. Tayi wanka ta fito daga toilet Munnirah ta kawo mata abinci tace ki daure ki ci sai ki sha magani. Ummi da Umaimah suka Shigo tare Munnirah ta bata wajen zama ta kalli Khadija tace "Ash shifah ya bint." Khadija ta kara gyara lullubin kanta, kamar tana ƙoƙarin rufe fuskar ta ta sunkuyar da kai, "Ammina dan Allah kalli kakata ki kalle ni wallahi kamar mu daya Ummi ta kalli Umaima, ɗan zaman da suka yi da Ummi na hours ta fahimci neman fassara take tayi mata bayani da turanci Ummi ta yi dariya, tace wa Khadija ɗago fuskar ki yata, yaya jikin ki?" ta faɗa da larabci, da ƙyar Khadija ta mayar mata. wani katon madubi Umaimah ta dauko ta kafa musu ita da Ummi, "Mamin Rijiya dan Allah dauke mu a hoto." Munnirah tace waya ta na bar ta a ɗakin Hakimi bani wayar ki. ta miƙa mata, cikin dabara Khadija ta ɗago tana kallon su hukumullah wannan shi Bahaushe yake cewa kamar an tsaga kara, Munnirah ta yi musu wajen kala 6 duka sun yi kyau sosai rashin sakewar Khadija yasa Ummu tace wa Umaimah su barta ta ci abinci ta huta suka fice daga dakin. Tahir yana zaune yana jiran Baba Dr, Allah Allah yake yace yaje wajen Khadija notification ya shigo wayar shi ya duba ikon Allah Umaima ce ta turo mishi hoto ita da Ummi, ya daɗe yana kallon hoton Baba Dr yace masa bari Hakimi ya raka shi ya ganta, yaji kamar an saka shi a Aljanna, Baba Dr ya kira Ismael be fi 5mins ba ya shigo suka hau sama Bayan fitar su Ummi Khadija tace "My sis da gaske Zaliha haka ta faɗa? kuma ta aika ta da gaske?" Munnirah tace "oh ba na son kina tayar da hankalin ki Dr yace kar ki yi tunani da yawa." hawaye ya ziraro mata tace "Ashe my sis mutum sai ya cuci wanda ya Amince masa? Ashe soyayya tana zama kiyayya? Ashe kyautatawa tana zama hassada?" "Dan girman Allah Khadija ya isa haka ki bar zuciyar ki ta huta." Ta yaya zan bar zuciya ta ta huta? ta raba ni da mijina uba da yarsa da Ahalinta me nayi miki Zaliha." sai ta fashe da kuka dai dai lokacin kuma Tahir yayi sallama ya shigo, Munnirah tana ganin shi tayi dariya ta bashi kujera. yace "ke ce haka kika yi ƙiba?" ta harare shi tace "ka jika kai da haka ka ke? Bari na baku waje dama kuka take yi." Ta mike ta fita hankalin shi a kanta zuciyar shi sai buga wa take, hawayen da take fitarwa, kamar digon dalma a ran shi haka yake jinsu yace "Hayateey." Kanta a kasa bata amsa ba ya sake cewa Hayateey pls dago kanki, ta rame sosai abun ya sosa mishi rai "Khadija." ya ƙara kiran suna ta da ƙyar ta ɗago fuskar ta wasu kibiyoyin kaunar ta yaji suna sukar shi yayi istigfari yace "ya karin hak'uri?" zuciyar shi ta tsinke yayi matukar kokari kar yayi mata kallon da ya wuce na shari'a, wani irin sanyi jikinta ya ɗauka kamar wacce aka kwararawa ruwan kankara ta rasa a wanne yanayi ta ke dakin yayi tsit ya nisa yace "Hayateey ina mai baki hak'uri duk abubuwan da suka faru babu amfanin maimaici ina miki godiyar Fatima, Alhamdulillah na yiwa Allah godiya, Allah ya haɗa ni da ita tun kafin nazo." ta kalle shi yace "eh nan yayi mata bayanin komai ya ƙara da cewa "Zaliha ta cutar damu har pills take baki ba ki taɓa faɗa min ba ga shi Allah yayi ikon shi har zamu zama kakanni." da sauri ta dago ido yace "Yes Fatima is pregnant." murmushin da bata shirya masa ba tayi, da sauri ya mike kamar yaje ya rungume ta babu hali ya juya mata baya yace "zamu wuce Lebanon jibi zan dawo mu yi sallama kafin jibin dan Allah a rinƙa daga waya ta, yaumak sa'id (have a good day)." ya fita ta daɗe tana kallon kofar hawaye ya ziraro mata alokaci daya kuma tana murmushi ta share hawayenta. ........Tahir ne Fahad ya rako shi zai ajiye shi a hotel din da suka sauka Ummi zata zauna anan Umaima ta hana ta komawa gidan Baba Isah, Fahad ya buɗe mishi gaban mota har ya tashi motar Umaima ta fito da sauri suka tsaya tace "Abbi ba a nan zaka kwana ba? A'a kwana gidan surukai. toh ina ka sauka? A Hotel ya faɗa "nima zan bika." Yace "a'a ya zaki bini hotel zo mu je dai ki rakani ina son ganin ku dama." ta buɗe bayan motar ta shiga tace Abbi yanzu ka na Saudiyya, daɗi ya cika shi yace ina Saudia Ibnati. To tare da Ummi za ku koma? Eh Lebanon zamu wuce tare da ita. Tace Abbi ka bar min Ummi mu tafi da ita. Ɗan zaman da suka yi ya fahimci character ce dan ɗazu tana ta tsokanar kakaninta ita bata jin Hausa sai jagwalgwala dan larabcin da ta iya take yi aka yi ta dariya. "dama ba ni da dan zaman ɗaki kawai sai ka ba ni Ummi mu koma. Yana murmushin maganar ta yace Ibnati mufa? "shekara nawa kuna tare Abbi? Kar ki damu zamu kawo muku ziyara. Fahad dai yana jin su har aka iso Tahir ya fito ya bude bayan motar Umaima ta fito Fahad ya zagayo Tahir ya haɗa hannayen su yace "ku zama sirrin juna ku zauna lafiya kun kusa zama iyaye duk abunda ya faru a tsakanin ku banda third party kun ji Allah yayi muku albarka." ya rungume su yayi musu sallama yana tafiya Fahad ya rungumeta yayi ajiyar zuciya yace "thankyou Zarah we are pregnant." ya shafa mararta "kin bani wahala." ta harare shi tace "wlh ka godewa Allah da sai dai ka koma kai kadai." Yace na sani my love na gane kure na ya riƙe kunenshi ba zan kara ba Maamah. ta yi murmushi ya bude mata kofa ta shiga suka tafi Suna isowa gida yayi kalar tausayi da fuska yace "Pls I'm Hungry ki taimaka min da wani abu pls." Ni wlh gida zan shiga sai dai ka shigo kaci. Wallahi kunyar Umma nake ji da Mami suna nan. toh meyasa? Ta tambaye shi, yace "ki kawo min nan pls zan fada miki meyasa." ta ƙura mishi ido sai ta ji ba zata iya mishi musu ba tace "toh ina zuwa." Ta nufi cikin gida babu kowa a falo ta shiga kitchen Amira ta tarar tana hada tray tace "ke kuma ina zaki kai wannan abincin? Sweet ne wlh ya taso ni yunwa yake ji congratulations once more har kina da ciki kika ki faɗa min. Kuma sai nayi ta shelar nayi ciki. Amira tace "oh haka ne? Shikenan yi hakuri Maman baby kin san rasuwar nan da aka yi shi yasa. Kya ji dashi bazan fada miki edd dina ba. Dan Allah yaushe ne? Oho miki. ta dauki tray ta fita sharp sharp ta yi mishi jellop ɗin spaghetti da dried fish ta hada mishi coffee da sauran peppersoup ta yi mishi warming ta fito ta nufi chalet din su ta yi knocking shiru ta kara knocking ya fito da towel a daure a kugun shi ya bude mata kofa ta juyar da kai taki haɗa ido da shi ta ajiye kenan ta ji ya rufe kofar ya zare key. Tace "haka muka yi da kai? Ta yi rau rau da ido wai mun shirya ne? Ni fah ba wani sonka nake yi ba. kamar zai yi dariya yace na sani, kuma ni son ki nake yi. Haba? Ta fada, ni da baka taba ce min I love you ba irin na masoya. yayi dariya yace yanzu zan fara fada miki ai ban makara ba ko? Ka kusa makara ta fada "pls serve me kinsan yaushe rabon naci abincin ki mai daɗi? ta bude baki "yaushe ka fara ci? Ya fada mata tare suka ci komai data yiwa Adil, and you are a great chef tayi murmushin jin dadi ta zuba mishi yace zauna mu ci. ta zauna suka cinye tas ya shiga toilet ya fito yace ɗazu kin tambaye ni meyasa nake jin kunyar su Umma? Ta daga kai ya rada mata a kunne kin ga dole na ji kunya ya rike hannunta yace "my hope is that our bond will be streghthen by mutual love and understanging allowing us to overcome any obstacle that may come our way I love you Zarahhhh." Ya dauke ta yayi kan gado da ita yayi switching light, the feeling was mutual and they take great pleasure in spending time together, sosai Umaima ta bashi hadin kai ta kai shi wonderland sai bayan komai ya kammala ta fara kukan shagwaɓa, ita sai dai ya raka ta cikingida ba zata kwana ba ya kunshe dariyar shi ya dauke ta yayi toilet da ita. suna fitowa ya bata pyjamas din shi da suka yi mata oversixed ta saka. yana idar da sallah ya ganta gaban dressing mirror tana shinshina perfumes din shi yayi murmushi yace "ki fesa mana it won't bite you." ta juyo ta harare shi tace "bakar magana zaka fada min, me kake nufi?Ya kama kunnen shi babu abunda nake nufi your highness. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 5️⃣6️⃣ Daddy ne ya kira shi, yake faɗa mishi Umaima zata bi Babanta Lebanon tayi 2 weeks, yana durƙushe a gaban Daddy maganar ta zo mishi a bazata. "jiya muka yanke hukuncin ya kamata ta je wajen yan uwanta muna ganin kaima mai bata iznin zuwan ne duba da yarda abubuwa suka faru shiyasa muka yanke hakan." Fahad yayi shiru gaskiya shi ya so su koma tare amma yaya zai yi, "baka ce komai ba?" "ok sir, Allah ya kai su lfy yaushe zasu tafi?' Gobe da safe. Daddy ya faɗa, ya ƙara jaddada yin hakuri kuma shi ne jagora su zauna lafiya. yayi wa Daddy sallama ya fita. Bata ko fada mishi ba ya nufi part din Baba yayi sallama Umaima da Ummi suna palon ta kwanta a cinyar Ummi, tana kwance mata kalaba. "sai yanzu ka tashi?" ta faɗa daga kwancen, "yanzu ka shigo? Umma da fitowar ta kenan daga kitchen ta faɗa, Ummi tayi mishi murmushi ya gaishe su, Ummi tayi mishi alama ya zo "tace my grandson." ya durƙusa a gabanta ta yi mishi kiss a goshi, "barakallah fikum." ya kalli Umaima sai lumshe ido take yi tace "ina kwana yayi mata banza." tun Asuba ta gudo ya ki amsawa. Umma tace a kawo maka abinci? Sai ya ji bashi da appetite yace sai anjima. ta mirgina kai a cinyar Ummi tace "Siyama kin ga yarda ake abin arziki abinda ke baki iya ba ina daga kwance ana min tsifah a hankali kamar yar baby don Allah yaushe rabon na kwanta a cinyar ki? "ALLAH YA tsare ni wlh baki da tausayi itama daga ta." Umma ta dake ta da throw pillow, haba Siyama me yasa ke yar hana ruwa gudu ce? "eh na hana ɗin." Fahad yayi dariya yace "Umma haka tace miki?" "hmmm wannan ai ciwon kai ce nasan hakuri kawai kake." Umaima ta zumɓura baki, Baba ne ya sauko daga sama Ummi har tayi mata parking gashin yana ta kyalli sun gaisa da Ummi. Fahad ya durkusa ya gaishe shi. "yauwa Baba back to business komai dai yanzu ya lafa gobe zamu wuce Lebanon." sai ta kalli Fahad ya harare ta, tayi dariya ta fuskanci Baba "kaga sallar layya ta kusa kuma ka ga dai Ragunan nan sun girma sosai guda nawa zaka siya? Uwata ni da zan miki lissafi. "na me kuma? Suna haka Daddy ya shigo suka gaisa da Ummi, yace "Muhammadu in dai ka gama sai mu wuce ko?" Baba ya kalli agogo yace "basu karaso ba bari mu dan basu lokaci." Tahir ne dasu Yaseer, Dr Huzaifa da Baba Isah za su je Bichi wajen Hakimi da har Ummi Daddy yace a bar ta ba sai an wahalar da ita ba. "Lissafin me zamu yi ne baba? Baba ya bude baki su Tahir suka Shigo aka gaggaisa Umaima ta je ta rungume shi ta gaida Baba Isah Fahad ya matso ya mika mata hijabin ta ta karɓa ta saka. "Baba wai lissafi me?" To uwata haka ake kiwon tunda kuka siyi abinci sau daya shikenan kuka bar ni da aiki ai kuwa ina da share ." Lalalala Baba kar mu yi haka da kai. Toh a kira manager mana. Uncle Ismah yana wajen aiki. Ai zai dawo cewar baba, gasu can na miki kiwo mai kyau zamu samu alkhairi ni bani da Buri ma 10% ma kika bani yayi ladan ciyarwa." A'a Baba ka fadi nawa ka kashe gara na biya, kamar fah hadin gwuiwa muka yi ni bana hada dukiya ta da kowa." Tahir dariya yake ya tambaya ta yi mishi bayani, "yauwa Abbi guda nawa kake so? "haka ake yi? Umma ta fada, "eh haka ake yi Siyama idan baku siya ba wa zai siya? Daddy nawa kake so?" "Toh nawa aka yi musu kudi? "tunda kai ne kowanne ɗaya ka bani 200k." Yayi dariya yace "toh a bani account number." Yanzu kuwa. ta tura mishi, Baba ka motsa, "ni babu wata motsawa da zan yi ni da na ciyar miki da su. Gaskiya Baba bama haka da kai. Fahad yace "Baba sai mu biya." "ƙyale ni da ita ta saka ni wahala kullum sai na shiga na basu ruwa bata kira tana jin yaya su ke." Baba Uncle Ismah yana kula dasu. Haka kika ce shi kenan. Daddy yace "wai Muhammadu nawa ka kashe ne?" Kuɗi masu yawa. Baba Isah yayi dariya yace "wlh haka kakanta yake da jajircewar nema ba 'a kasa ta dauka ba, haka Tahir yake shima." Dr Huzaifa ne yake neman bayani Tahir yayi mishi bayani yake ta dariya, "Abbi guda nawa kake so gidan surukai fah zaka bawa nawa za a dibar maka? "diba kamar wasu kaji." Daddy ya faɗa, "sun shigo." ta faɗa ta kalli Daddy tana murna 1m Daddy Allah ya kara arziki. Tahir yace ta kirga nawa ne zai siye." A'a Daddy ni zan siya na yi Rabo." dama ya kan yi haka duk shekara cewar Fahad, Daddy sai ganin alert din 1m yayi Fahad ya mayar mishi da kudin shi. Daddy yace su tashi idan suka biyewa Umaima zasu yi rana tace itama zata Bichin Fahad yace ta zo su fara yin gaba. ........ washegari da Azahar jirgin su ya tashi sun wuce Lebanon Tahir, Umaima Ummi da Yaseer. Dr Huzaifa ne zai koma wajen aiki shi ta Lagos ya tashi, su kuma ta Abuja. Fahad ne a daki duk sai ya ji Kanon ta fita a ran shi tunda yayi mata rakiya airport, ya roke ta ta dawo bayan 1 week idan ba haka ba zata gan shi a Lebanon shi yanzu Adil yake tsoron rigimar shi don ma suna gidan Munnirah ya bi Iman sosai sun shaƙu da Iman ko dan shi kadai ne acan, ya kira Sa'ad suka gaisa yace "Guy yaushe zaku koma ne? "zan koma dai ni kadai ne zan tafi." Me yasa? ya tambaya, yace "sun wuce Lebanon ɗazu, I'm worried about Adil reaction if he finds out she is not around I don't know what to do." ya faɗa murya a karye. Kawai ka bar shi anan ta ina zata dawo? idan ta Kano ne sai su wuce tare." yayi wani tunani yace "haka za a yi where is your wife my regards to her." zata ji. suka yi sallama Sa'ad yana mamakin maganar Fahad don sun yi gulmar shi da yaya Surayya ranar da zasu koma har airport yayi musu rakiya babu kunya a gaban shi ya riƙo hannun Umaimah. Aadil ya shigo da gudu "Papa where is Maamah? Iman na biye da shi a baya yace "Adil pls I want to rest I'm having headache." Ok

Chapter 23 of 27