Share this page
die before death.”* EPISODE 0️⃣3️⃣ Leeds UK Bayan tafiyar su Daddy Fahad yaci gaba da renon ɗan sa da taimakon Nanyn sa Mrs Lawrence. Yau weekends babu aiki bai fito ba sai to 1pm a zaune yake a falo Aadil na tsaye a gaban shi da uniform a jikin shi, baice mishi komai ba sai zuba masa ido da yayi, "Papa are you mad at me? Ãdil ya faɗa yana kallon Fahad da yayi shiru yana kallon shi, "Please Papa I'm sorry." ya sake faɗa kamar zai yi kuka, lumsassun idanunshi ya buɗe akan Yaron da tausayin shi ya kama shi ganin duk yayi wani iri, ya ce "No I'm not, call Mrs Lawrence (Nanny). ya tafi kiranta be fi 5mins ba ya dawo tare da wata dattijuwar baturiya a kiyasi zata yi 50years sanye take da uniform black skirt da farar riga gashinta daure da band, tana da tsilli tsillin furfusa a kanta, "yes sir." ta faɗa, ta koma gefe tana jiran me zai ce saboda Mrs Lawrence ta daɗe tare da su sosai ta san halin shi, tun lokacin Aysha na laulayin cikin Ãdil suke tare da taimakon wata colleague ɗin shi a wajen aiki Mrs Susan ta yi mishi recommending wani company da su ke ba da ma'aikata, kawai zaka faɗi irin ma'aikacin da kake so ne, za su baka, babu ruwanka da payment ɗin mai aiki direct company zaka biya daga can company za su biya su, idan kana da ƙorafi company za ka yiwa a canja maka professional ne sosai ma'aikatan su . Ya kalle ta ya ɗauke kai kamar bazai yi magana ba can yace "I have noticed that my son hasn't been finishing his meals could we discuss some alternative meals?" "OK sir." ta ɗauki lunch box ɗin Aadil daya dawo da shi tana duba wa, mashed potatoes and mashed carrots ta yi mi shi for lunch na school, daya ke ya fara tunda yayi baki sosai, yanzu ya kusa 4 years yana da jikin girma zaka dauka yayi wuce haka, yana Blenheim primary school kusa suke da makarantar yana kindergarten. Taga be taɓa komai ba sai chocolates da juice, "I will try something different sir." Ba tare daya kalle taba yace "you can go." Ta kama hannu Ãdil "let's go and shower." babu rigima irinta yara ya bi ta. KANO Bata daɗe da shigowa ba ta hau sama suka yi clashing da Amira zata sauko kasa Umaimah tace "yawwa za ki rakani Birthday ɗin brother Sadiq Friend ɗina." kice Birthday ɗin saurayin ki." Amira ta faɗa, " oho whatever you want to say, say it ki shirya Mal Sadi ya kai mu." Mal Sadi shine sabon drivern da Daddy ya ɗauka musu saboda zuwa makaranta. "Ah ah ki je ke kaɗai gaskiya." Umaimah tace "oh wulaƙanci zaki yi min? "No Dr ne zai zo. "waye kuma Dr? Umaima tayi tambayar tana kallon Amira da ta lumshe ido tace "my heart mana." "oh soyayya manya" Amira da Hidaya suna level 3, Amira na Norhwest tana karanta Economics, Hidaya kuma tana karanta law a Unilag a Lagos tana zaune a gidan Aunty Amal, ita da Amira suna da 19years Hidaya ce mai almost 20years. Amira soyayya take yi da lecturer ɗin su Dr Musbahu Ɗan Iya shi take mutuwar so, Dr Musbahu irin masu kananan jikin nan ne yana da kunnuwa Masha Allah, ga shi siriri, idanuwan shi kanana a ciki amma a haka Amira take son kayan ta, Umaima ta yi ta tsokanar ta. "wlh dama ni ce a level 4 dinnan da tuni na shiga daga ciki." Amira ta faɗa tana wani kumshe ido, Umaima ta ce "lalle gaskiya wannan ya tafi da zuciyar ki." "wlh idan aka daura min ɗan Iya da gudu zan kwance na kama gabana na yakice shi mutum ga muni ga gajerta ke wai kunnuwan shi basa firgita ki? kana kallon fuskar shi kunne kake fara gani." Amira ta sha kunu "bana son wulaƙanci.? "ku kuma me kuke yi kun tare hanya, ku matsa ku ba ni waje." Umma ta faɗa suka matsa, "kin dawo? ta kalli Umaimah "eh yanzu na dawo, fita zan ƙara yi." Tayi maganar tana kallon agogon hannunta, "sai ina kuma?" Umma ta tambaya, "hmmm hmm Sadiq ne zai yi Birthday shine zanje." Amira ta kalle ta da sauri, "toh wa kika tambaya? "Siyama ba gashi na fada miki ba. yanzu karfe nawa? Umma ta faɗa, tace karfe biyar. "toh ki tabbatar magriba ta yi miki a gida." "toh Siyama yadda kika ce haka za a yi Maman Babangida." ta wuce ɗaki ta shirya ta gama dube dubenta a sif ɗin ta ta fito ta shiga ɗakin Amira tun da Khadija ta yi aure suka raba ɗaki Amira ta koma dakin Khadijah, ta buɗe wardrobe ta ɗauko wani skirt high waist Ash colour da wata riga long sleeve white colour, ta nemi siririn mayafi light Ash ta yi rolling da jaka baka a hannunta, kayan sun mata kyau sosai, shape ɗin ta ya kara fitowa da hasken fatarta sosai kamar ta da Ummi ta sake fitowa kamar kwabo da kwabo, don Tahir sosai yake kama da Ummi, amma Umaimah da yake mace ce sai kamar ta da Ummi tafi fitowa sosai, kawai banbancin su da Ummi shekaru. Amira na ganin ta tace "ke kuwa haka zaki fita babu ɗan makeup? kut kayana kika saka wlh baki isa ba." Umma tace "ko watsa ruwa ba ki yi ba kin fito daga rana." Kai Siyama na yi wanka fah da safe kuma sauri nake." "wlh koma ki cire min kayana." Amira ta sake faɗa tana tare hanya. Umma tace "Dan Allah ƙyale ta ta je, yanzu idan kuka fara sai kun yi faɗa kema fa kina ɗaukar nata." "wai tsaka tsami." Amira ta faɗa a hankali don tayi wajen shoe rack tana neman takalmin da zai dace da event ɗin, duk rashin son gayunta ta wajen iya dressing Umaimah ba daga baya ba, intayi dressing kina mace sai kin kalle ta kin ƙara kallo gata mayyar turare kusan kuɗin ta anan yake ƙare wa, har ta yi ƙofa zata fita ta dawo ta cewa Umma "Siyama idan Tasiu ya shigo ki faɗa mishi za mu yi lissafi ya jirani komai dare." (Tasiu Almajirin da ta sa Baba ya dauka )shi yake mata handling cinikin kayan sanarta yanzu. Tinda Isma'il bai fiya zama ba da yake ya samu aiki a Company MTN tin daga service suka riƙe shi. Ta kalli agogon hannunta 8:30 don ma ta yi sallar magrib ɗazu amma gaskia lokaci ya ja, "meye kike ta duba time?" Sadiq ya faɗa, "sam ban san lokaci yayi haka ba gaskia tafiya zan yi kai." "smart ki ɗan ƙara jira mana." genius ya faɗa, "pictures kawai za a ɗauka sai mu tafi." Huzaifa yayan Sadiq sosai yake nuna interest akan Umaimah har mamansu sun kulla zumunci da Umma suna ziyartar juna yana ta kama ƙafa a wajen Ismael don ya fahimci na hannu damanta ne kusan Huzaifa ɗan gida ne don idan ya zo har ciki yake shiga ya gaishe da Umma, tun Umma bata ga ne ba har ta fahimci san Umaimah yake, ta dai yi shiru bata ce komai ba tukun har sai yayi magana, tana dai yi wa Umaimah tsiya. Umaima yar abi yarima ce a sha kida kwata kwata bata wani jin wani abu makamancin soyayya idan suna tare da Huzaifa kamar Uncle ismah haka ta ke ganin shi. "Assalamu alaikum. wani matashi ya faɗa yana zama a kujerar da ke kusa da ita ba zai wuce sa'an Huzaifa ba, zai sake yi mata magana Sadiq ya riga shi da cewa "Ya Hisham Inlaw ɗin muce fah." "oh ko ita ce Umaiman? ta yi murmushi kawai bata ce masa komai ba, ta miƙe ta cewa Sadiq "ka faɗa mishi kawai na wuce." "Please ki tsaya bari na faɗa mishi." Huzaifa na tare da friends din shi ana ta daukan pictures, komai a nutse ake yi colleagues din shi na office a Aminu kano International Airport ya ke aiki, music ɗin ma kaɗan kaɗan yake tashi babu hayaniya sai ka shigo Hall din kake jin music ɗin, abu ne na matured mutane babu hargitsi. Ba a dauki lokaci ba sai ga shi da photographer ya matso aka dauke su yayi excusing kan shi yace bari ya kai ta gida ya dawo, Hisham yace "no ai daka bari mun kai ta ni da su Sadiq." "No No." Huzaifa ya faɗa, Umaimah ta miƙe suka fita. Aliyu nayin parking wata Mercedes Black colour ta shigo ya ɗan tsaya ya gani ko wajen Baba aka zo dan kafin ya dawo sun yi waya da shi ya fita Aski baya gida, kawai sai gani yayi Umaimah ta fito daga gaban mota saurayin ya fito da kan shi yace mata thanks for your time, take care tana waving ɗin shi ya fita. Tana tsaye a wajen Aliyu ya fito kamar wuta ta ja shi sai kawai Umaima ganin shi ta yi a gabanta "daga ina kike? "hmmm hmmm. ta fara kame kame "waye wannan? Tace "yayan Sadiq ne. "waye Sadiq? "Friend ɗina. Ita wlh ta ga motar shi a wajen amma bata dauka yana ciki ba, Huzaifa ya sha dawo da ita gida idan ta je wajen Sadiq bata ɗauki hakan a laifi ba ne. "Follow me." ta ji ya faɗa ya koma motar shi ya buɗe ya shiga, ta tsaya tana kallon shi yace "will u get in my Friend? Umaimah jiki na rawa ta buɗe baya zata shiga, ya daka mata tsawa "waye direban ki? Ta dawo gaba ta zauna a zuciye ya ja motar da gudu kamar zai tashi sama, ta kifa kanta a cinya yana ta gudu sai ta ji motar ta tsaya, "bani jakar ki. ya faɗa da tsawa, ta miƙa mishi, yace "get out of my car." ta daga ido ta kalli inda su ke Tahir Guest Palace, "fita ki ba ni waje ba bariki kike so ba, toh gashi nan na kawo ki fitar min a mota." ta fito jiki na rawa ya jaa motar shi ya barta a wajen wasu hawayen baƙin ciki suka zubo mata. oh shiyasa ya karɓe jakarta ke nan kar ta kira kowa ga shi bata da kuɗi ya karɓe jakar gashi 10 ta kusa akwai dokar masu adaidaita kar su wuce 10 a waje, ta tsayar da kusan masu mashin uku kowa sai yace ya tashi parking zai yi haka ta yi ta tafiya tana hutawa motoci su ka rinka tsayawa suna mata magana bata kula su ba. Amma Babangida ba haka ake nusar da mutum ba. Daddy ya faɗa yana kallon shi, "ba a gyaran kuskure da kuskure." Umma ta karɓi zancen da cewa "na san yaron, wlh yaron kirki ne mahaifiyar shi har nan tasha zuwa, ita dai ƙyale ta da danyan kai amma banda irin wannan zargin." Umma ta faɗa a fusace, wayar Baba ta yi ƙara ya daga ya saka ta a speaker muryar Ismael ce, yace "Baba gani a Tahir ɗin bata nan. "Tashi mu je neman ta Muhammadu." Daddy ya faɗa yana miƙewa, Aliyu ranshi ya sake ɓaci, ai ya san babu inda zata shiyasa tun farko be kai ƙararta ba, dama so yayi ta taho a ƙasa duk sun sangarta yarinya kamar ita kadai ce jika, so suke ta gagare su. Sallamar Umaima ce ta katse mishi tunani ta shigo kafarta tayi busu busu. UK Papa do you think I look neat and tidy today? are you not proud of me? Ãdil ya faɗa yana kallon Papan shi, ya ɗaga ido ya kalle shi "I'm proud of you, but not happy with your eating habit." Fuskar shi kamar zai yi kuka yace "I'm sorry Papa." Its okay is bed time." Yes Papa. Ãdil ya mike suka shiga toilet ɗin shi da kan shi yayi mishi wanka yayi mishi brush ya daura mishi Alwala suka fito ya shafa mishi lotion kayan wankan shi da lotion ɗin shi na yara kaya ne guda kamar masu buɗe kanti, ya saka mishi nighties yace "pray. Aadil ya haɗa hannun yace "Bismikallahumma amootu wa ahyana." suka karanta falaq da nasi tare, ya ja mishi blanket, "good night Papa." "gud night Didi." haka yake kiran shi. kafin Ãdil ya kai haka wayo, idan Aysha ta tambaye shi sunan shi sai yace Didi lokacin bakin be iya fadin Ãdil ba sai take ce mishi Didi. yayi kissing goshin shi ya kashe switch ɗin ɗakin ya rufe mishi ƙofa, har ya zauna zai fara aiki ya kara tashi ya duba switch ɗin ɗakin Aadil ko ya kashe yayi haka ya kai sau uku tukunna ya buɗe system ɗin shi ya fara aiki, yana aikin tunanin Aysha ya ratso mishi, ta yi haƙuri da shi ta so shi, ya dafe kan shi Aysha ta yi enduring behaviour ɗin shi sun yi kusan shekera babu abunda ya shiga tsakanin su tun tana kunya har ta kasa haƙuri ta faɗawa Sa'ad, lokacin da Sa'ad yayi masa magana sai da suka yi fada sosai suka yi kaca kaca dan kula tan da yake yi data kai kararshi ya dauke mata wuta, sai ce mata yayi she is free to go, Sa'ad beyi fushi ba ya rinƙa turo mishi text na shi ba jahili ba ne yaji tsoron Allah da ayoyi da hadisi tare da tsoratarwar zaluncin da yake yi mata. Ranar da ya karɓi budurcinta jinin ma kadan ne amma saboda tashin hankali gidan ya bari ya nemo nurse ta kula da ita daga lokacin sun fi 3months wani abu be sake shiga tsakanin su ba, daga baya kuma sai cikin Aadil ko bayan ta haifi Aadil sai su yi 3-4 months ba abunda ya shiga tsakanin su, dama ita take kai kanta idan ta gaji haka zatayi ta riƙon shi, da ya biya mata bukata zai ce I need space. Babu wani romance buƙatar ta kawai yake biya a irin wannan lokacin ita ke kidan ta tayi rawar ta, harta mutu shi besan wani daɗin sex ba dan bashi da nutsuwar zuciyar dazai fahimci haka, zai iya rantsewa tinda yake da Aysha bai taɓa kissing ɗin ta ba, haka bai taɓa bata dama tayi masa ba, basu taɓa kwana daki ɗaya ba, kuma bata damuwa, Aysha ta rasu da second babyn su acikinta ya shafa fuskar shi hawaye tausayin ta ya zubo mishi "I hurt her." ya faɗa yana rintse ido. ***** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 *We live today and tomorrow we died. what's the meaning of life?* Volume two EPISODE 0️⃣4️⃣ UK Nanny din Aadil ta fito bakin gate ganin lokacin tashin shi yayi ta na fitowa School bus ta ajiye shi aka bata log book ta yi ticking shaidar sun ajiye shi a gida suka tafi Aadil yace "good afternoon Mrs Lawrence." afternoon sweet heart. "is my Papa around? Ya tambaya, No sweetheart Papa is at work place now. "oh No Papa come home soon. suka shiga gidan quietly ya cire shoes ɗin shi yayi arranging ɗin su a shoe rack, ya wuce ɗakin shi ya ajiye jakar shi a bag holder ya shiga Toilet ya cire uniform ɗin shi ya saka a laundry basket, "I'm ready for shower, I'm ready for shower." Ya faɗa yana cilla ƙafa, "I'm coming Didi." Nanny din shi ta amsa. Fahad ya kalli time yana wajen aiki yasan yanzu ya dawo gida already yayi connecting CCTV a gidan ya jona da laptop ɗin shi, he is very intentional akan Ãdil a duniya bayan iyayen shi babu abun da yake mugun so kamar Ãdil baya wasa da sha'anin shi, tar tar hoton shi ya fito a system ana mishi wanka, yace da Nanny when is Papa coming back home? he will be here soon sweetheart, I can't wait ya fada yana dariya, Fahad yayi murmushi ya cigaba da kallon su har aka shirya shi, "come and have lunch." ya bita ta ɗora shi a Dinning. Berries ne aka yanka into small pieces, sai cooked and mashed green beans da yogurt a glass cup ya cacakala yace "I'm okay. No add a little. ya ɓata fuska, haka dai ya ƙara one spoon ya shanye yogurt ɗin ya tashi. ****** Baba Rabi na soya gullisuwa, Barira na yanka alawar madara Umaima ta shigo kitchen din Sasi na bin ta a baya "yauwa Baba Rabi kin karasa? eh uwar ɗakina saura kadan a gama. "Aunty Umaima ina kwana. Barira ta gaisheta, "lfy ƙalau Barira ki shirya an jima Malam Sadi idan zai ajiye ni makaranta sai na fara kai ki makarantar kafin na wuce." "kai madallah uwar ɗakina" Baba Rabi ta faɗa, an gode, "na gode Aunty Umaima." Barira jikar Baba Rabi ce mahaifiyar ta ta rasu a hannun matar uba take, zaman nasu babu daɗi shine baba Rabi take bawa Umma labari Umaimah naji tace a taho da ita. Baba yace Baba Rabi taje ta ɗakko ta, yanzu ma ita ce tayi enrolling ɗin ta a makaranta. Shigowar Umma ce ta katse su, ta kalli Umaimah ta ce in ye baki isa ba wlh, Barira kin gama aikin da na sa ki? Yanzu zan yi idan na karasa wannan." "Ba shakka na wa aikin aka bari ake yin na Umaimah ay shikenan. Baba Rabi tace ayi haƙuri Hajiya yanzu zamu kammala. Umma tace "rabu da Umaimah ita ta je ta yi min aikin. "Toh Siyama na ga ni na ɗauko Barira. eh lallai ke kika ɗauko ta sai yadda kika tsara haka za a yi. Umaimah ta kama haba "wacce ni Fatima Tahir jikar Maryama. ta faɗa tana dariya. "Barira kirawo Tasiu mu yi lissafi sai ki shirya mu tafi." toh Aunty. tana rufe bakinta Munnirah ta yi sallama ta shigo da Iman a hannunta, Munnirah Allah ya amince ta haifi yar ta mace ta ci sunan Dada, faɗin irin murnar da aka yi bata baki ne, Dada kullum maganarta Allah ya sa kana da rabon haihuwa likita,Tasiu Umaimah ta saka a gaba kamar wasa tunda Almajiri ne, tace masa wai ba kwa bada lakanin haihuwa ne? Yace malam yana rubutun haihuwa amma yana Funtua, tin daga nan duk sati ake aiko da rubutu Umaima ce mai karbowa a Tasha ta kaiwa Munnirah har gida, Baba Dr yayi ta dariya idan ta kawo yace ke da wannan yar ta ki sai a hankali yayi ta musu dariya, don shirme ya dauki abun nasu, ita kuwa Munnirah idan Umaima ta kawo rubutun haka take sha duk da bata san rubutu na ƙarshen da ta kawo mata tace wannan wai sai kun keɓe zaki sha, Munnirah tace "ah ah Babbar magana kawai a bani lambar malam idan da wani abu yayi min bayani." cikin ikon Allah sai ga ciki a jikin Munnirah, Umaima ranar da aka haifi Iman tace Baba Dr yayi alƙawarin babyn ta ce da ƙyar Daddy ya kashe maganar ta dawo sai dai a saka sunanta ya ce ita ya saka Amma sunan Dada ne yayi mata wayo shi kenan aka samu lafiya. "Amama". Iman ta faɗa tana miƙo mata hannu, Umaima ta ɗauke ta, tace "ba ki da kunya Maamah za ki ce min dan wlh wahalar da na sha a kan ki sai Allah." Amama ta ƙara faɗa "Na'am my baby." Yanzu ku ke tafe? Umma barka da safiya. Baba Rabi ma suka gaisa. Mamin Rijiya na gama project ɗina yau zan je na yi submitting shikenan sai ki bar min Iman. Munnirah tace ni bani da matsala da wannan ke da Babanta. Ta gama duk abunda zata yi a makaranta tana jiran Malam Sadi ya zo ɗaukan ta wayarta tayi ƙara ta dauko ta a jaka Huzaifa taga sunan yana yawo a screen ta ɗaga kiran "lafiya Alhamdulillah." ta faɗa, yaushe? Ta tambaya sai ta kalli agogon hannunta ta kalli time toh shikenan "i will be there. ok thank you." ta faɗa ta yi hanging call ɗin, ta kira Malam Sadi ya bata hakuri yace yana hanya ya haɗu da hold up ne a hanya, ta yi jiran kusan 30mins kafin ya ƙaraso, "Ayi haƙuri Hajiya sam ban san zan ɓata lokaci wajen shan mai ba dana bari sai na kai ki gida tukunna." "babu komai Malam Sadi jigilar ka ma tazo ƙarshe yau na kammala project na yi submitting yanzu sai jiran bautar ƙasa. kai masha Allah, Allah ya sa albarka yasa an gama a sa'a. "Amin." ta amsa tace "yawwa Gusto restaurant zamu je na nan lodge road. toh Hajiya ya karkata kan motar. Aliyu ne yayi baƙi daga regional office ya kawo su gusto su yi lunch, wajen parking motoci ya ga motar Malam Sadi yayi mamakin me ya zo yi nan ya leƙa babu mutum a ciki suna shiga ciki tare da baƙin shi Mr Balogon da Mr Taiwo suka zauna suna kalle kalle wajen ya yi musu kyau, yayi excusing ɗin kan shi "let me make order." har ya faɗi abinda za a kawo musu juyawar da zai yi yayi kyakkyawan gani Umaima ce a zaune Huzaifa ya tashi daga seat ɗin shi riƙe da wani box a hannun shi ya durƙusa a gabanta tana wani murmushi kawai Aliyu ya tsaya yana kallon ikon Allah, Huxaifa ya buɗe box ya Ciro gold ring yana durkushe a gaban ta yace "will you marry me please?" har ta miƙo hannunta ta yi ido huɗu da Aliyu ta kame tana kallon shi, Huzaifa ya kalli direction ɗin da take kallo suka hada ido da Aliyu, yayi kamar babu abinda ya faru ya koma wajen baƙin shi, jikin Umaimah ya hau rawa kamar mazari bata kara ko minti ɗaya ba ta yi hanyar waje da sauri tana zuwa Malam Sadi ya buɗe mota zai mayar da sallaya ta afka ciki, Huzaifa ya biyo ta da sauri ga box din ring a hannun shi "tsaya mana." yana faɗa yana binta, bata saurare shiba tace "mu je Malam Sadi." a kidime ya ja motar ganin yadda ta ke rawar jiki kuma ga wani ya biyo ta Malam Sadi sai ya tsorata ko wani abu ne ya faru ya figi motar da gudu aka bar Huzaifa da zoben sa a hannu. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two *Don’t let life get you down. Not everyone will appreciate what you do for them. Don’t be discouraged as there are many ungrateful people out there. You just have to figure out who’s worth your efforts & who’s merely using you. Focus your energy on those who matter.* *Mufti menk* EPISODE 0️⃣5️⃣ Da sauri ta shigo gidan ta haye sama ta yi sa'a babu kowa a ƙasan ta wuce daki ta shiga Toilet ta dauro Alwala dan karfe 2 :30 har ta wuce tana idar da sallah ta ɗauki waya ta kira Uncle Ismah duk da ta san yana wajen aiki,

Chapter 2 of 27