Share this page
bacci ta tashi Adil ta yi mishi wanka ta shirya shi ta saka mishi rigar sanyi da hula dan yau garin dusar ƙanƙara ake yi ta soya mishi chip and egg ta haɗa mishi tea tsabar doki ita ta kasa cin komai tun da ta gama haɗa luggage ɗin su ta fito da su passage, Adil ya gama ko sallar Asuba ba a yi ba tace "dan kwanta a kujera kafin ayi sallah." sai kallon agogo take yi by now yakamata ace ya fito ya tafi masallaci ana kiran sallah ta koma ɗaki tayi sallar ta ƙarasa shiryawa ta fito ta saka Ãdil yayi sallah Abayar daya siya mata tsaraba ta saka dayake baƙa ce mai adon blue ta haska ta sosai tayi mata kyau, suna zaune sai gashi ya shigo daga masallaci yake ya kalle ta ya ɗauke kai, "good morning Papa I'm so excited." Ãdil ya faɗa, ya kalle shi yace "morning." "Barka da safiya." ya kalle ta ba tare daya amsa ba ya koma ɗaki, tayi masa kyau a ido ko kaɗan bai ɗauka rigar zatayi mata kyau haka ba wani haushin tafiyar yake ji dan haka ya share ta. "ko be ji ba oho mishi dan be amsa ba, kai wannan mutumin da bakin hali yake, wlh ni dai ya fito mu tafi kar mu yi latti Daddy yace jirgin safe ne." Sam ta kasa zama ta kai mari ta kai gwauro kamar tayi tsuntsuwa haka take ji, ta je ƙofar ɗakin zatayi knocking kenan ya fito da jibgegiyar rigar sanyi a hannun shi sai baza kamshi yake yi kamar wanda yayi wanka da turare, taja baya tana cewa "hmm dama kar mu bata lokaci ne." Be ce mata komai ba ya miƙa mata rigar sanyin ta karɓa ta saka "nagode." Ta faɗa, baiyi magana ba yadan matso kusa da ita ya gyara mata rigar yayi gaba kamar bashi ba, ta bishi da ido tana mamakin halin shi, ko duk wannan ƙuncin na meye oho masa? Suna fitowa compound ta tarar Mr charles ya zo Fahad yace ya ɗauko kaya a saka a mota, "good morning ma'am. "Morning." ta amsa aka saka kaya a boot, Fahad da Adil suna front ita tana baya Mr charles ya ja motar suka fita. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 3️⃣1️⃣ Suna sauka suka fito tare da Ãdil ta tsaya wajen ɗaukan luggage sun jira boxes ɗin su aka gangaro da su masu ɗaukan kaya suka ɗaukar mata suka fito harabar wajen parking motoci taga Uncle Ismah tare da abokin shi Abbas ta nufe shi da sauri tana dariya suka rungume juna. "Maamah you left me." murna ta saka ta manta da Adil "sorry" suka gaisa da Abbas Uncle Ismah ya riƙe hannun Ãdil yace "babu gaisuwa." yace ina kwana. "A'a sha biyu ta wuce ina yini dai." ku kadai kuka zo? Ta faɗa tana shan kunu, "ni na ce su zauna surprise zamu basu." Uncle Ismah ka yi kiba fah me Siyama take baka ne? Suka ƙaraso wajen mota Abbas Abokin Ismael police ne police Academy yayi wudil Asp ne shi ya zo da motar yan sanda mai siren, Uncle Ismah yace "ba kin ce da siren zaki shigo Kano ba? shi ne na kira Abbas." ta washe baki tayi mishi jinjina tace "indai da Uncle Ismah bani da matsala dole mu baza capacity." Abbas yana gaba Uncle Ismah suna bin shi a baya sai da suka zo kwanar Sultan road ya kunna siren har Kofar gidan Alhaji Muhammad Ali Bichi, kafin ma ayi horn Baba Idi ya buɗe gate, "ikon Allah ko yaya Sulaiman ne ya iso nake jin siren." Umma da ke aiki a kitchen ta faɗa tana leƙowa, suna ta aikin taron Umaima. "Ga Hajiyar ta sauka." suka ji muryarta da sauri Umma tayo waje "oyoyo oyoyo." ta tafi ta rungume ta, Baba suka firfito suka rungume ta ɗaya bayan ɗaya ana ta murna. To mu shiga ciki Baba ya faɗa Abbas yayi musu sallama ya tafi, Uncle Isma ya ɗauki Adil dan har yayi bacci a mota daga airport zuwa gida, suna shiga palo Baba Rabi da Barira suka ta ho "lalle maraba da uwarɗakina, sannu da zuwa Aunty Umaima." yawwa, aka ruɗe da gaisuwa su Baba Idi da Tasiu ma suka Shigo Umaimah tace "lallai Tasiu kwana biyu bana samun ka baka hawa WhatsApp bana ganin alert fah." Ke kuwa ki bari ki huta mana. "waya ke wasa da dukiya Siyama." Bashi da lafiya Barira ta faɗa, "oh kece bakin shi? Yace Wallahi uwarɗakina bani da lafiya ne. "Allah ya sauwake." Ya tashi ya fita, tace "Siyama ba a haka dole a ɗan tuntuba, dukiya sai ana bibiya ko dai baki san zafin nema ba?" Ta faɗa tanawa Umma dariya, "Ina ta sani. Baba ya faɗa yana dariya, "Au daga zuwa kin fara ko? Daddy yace gaskiya ce kin iya neman ne? Daddy yace kin zo lafiya? Lafiya ƙalau Daddy. Mami ce ta shigo da basket a hannunta, "a'a wlh na ga zuwanki Mami, Siyama daga sannu da zuwa ko ruwa bata ba ni ba." "haka zaki ce tun Asuba nake tsaye a kafafu na." ta yi hugging Mami ta fara bude basket ɗin, Deborah ta biyo ta da wasu warmers ɗin a hannu "welcome maah." ta faɗa ta ajiye, Umma tace "to ki bari ki ɗan watsa ruwa mana kya ji daɗin jikin ki." Ko karyawa fah ban yi ba har wani jiri nake ji. Ta cika plate tana ci Baba yace "dan naki fah? A bashi idan ya tashi yaci abinci, a jirgi ma ya ci ni doki ya hana ni ci, Mami ina Amaryar ne da Amira? Sun fita rabon kati tun safe suka fita akwai ƙawayen ta da suka yi lawschool da yawa, da kawayen Amira basu san kin kusa sauka ba da baza su fita ba." Baba dai kallonta kawai yake yi daɗi ya ishe shi, Alhamdulillah ta yi kyau ta yi fresh hankalin su ya kwanta, Allah ya ƙara haɗa kawunan su "kai abincin gida duniya ne wlh, Siyama ina kajin? Ke kuwa duk ki saka a gaba kina ci wancan anjima ba sai ki ci ba. "naga ikon Allah wai don wa aka yi? Dan ke aka yi uwata Maryama ɗauko mata Daddy ya faɗa Umma ta miƙe tayi kitchen. UK Ya dafe kan shi ya mirgina daya ɓangaren daga kwance, tunda suka dawo daga airport yake kwance ya kasa fita aiki sai mail ya tura ba zai iya fita ba, baya jin daɗin mood ɗin shi ya canja kamar wanda ya tashi daga ciwo da kyar ya shiga toilet yayi wanka ya shirya ya fito falo sai yaga gidan yayi mishi faɗi ya shiga kitchen babu kowa Mrs Lawrence ta shigo kitchen din suka gaisa "where have you been? Ya tambaye ta, tace tana gyaran dakin Adil, ok ya faɗa ya haɗa coffee ya ɗauki bread ya dawo falo ya kunna TV ana wrestling yana kallo yana sipping coffee kaɗan kaɗan da ƙyar ya ci slice ɗaya na bread din sai daci ma yaji a bakin shi, ya kalli agogon hannun shi yasan sun isa tuni babu wanda ya kira ya ce mishi sun isa, ita yarinyar ma bata da hankalin neman shi tace sun sauka koda yake bata da number ɗin shi, toh bazata nema ba? Sai kawai ya ji ran shi ya ɓaci ya ɗauki wayar shi ya kira Sa'ad, "Hello Guy how far?" Fahad yace "fine." Sai kuma yayi shiru "ina jinka?" "where are you?" ya tambaye shi, "ina wajen aiki." sai yayi tunani kenan yana pothacourt baya kano, "wouldnt you attend the wedding? Sa'ad yace "zan je sai jibi idan naje zamu taho da Amira dan Alhamdulillah ta ji sauki." Fahad yayi tsaki ƙasa ƙasa shi ba wannan yake son ji ba, ƙifadi irin na shi ya kasa tambayar Sa'ad number ta kawai yace it's okay. "ka kira baka ce komai ba? Don't mind kawai, ya ajiye wayar Sa'ad ya daɗe da waya a hannu "toh lafiya? Tunda dai be ce wani abu ba shike nan ya cigaba da aikin shi. Fahad ya rufe ido toh shi yaushe ma ya saba da zama da ita har da zai ji rashin jin dadi dan bata nan, zuciyar shi tana kimtsa mishi rashin jin daɗin ji daga garesu gangar jikin shi tana karyata hakan, kai dole ya cire wannan abun a ran shi kawai Adil ne ya ke missing yes Adil ne zuciyar shi ta kara bashi tabbacin hakan, ya tashi ya shiga ɗaki ya shirya a sport wears ya ɗauki key din mota gara ya tafi gym kawai. Kano Siyama Ina ta kiran number ɗin su taki shiga tun da muka zo har yanzu basu dawo ba? wanne irin rabon kati ne wannnan?" To ina zan sani? Umma na rufe baki Munnirah ta shigo da sallama "Mamin Rijiya Oyoyo." Umaima ta tafi ta taro ta, "oyoyo daughter." ta gaishe da Umma, Iman ce a bayan Munnirah da teddybear a hannunta "kin ganki masha Allah." ta rungumeta, Umaimah ta rufe ido tana dariya "zo Iman." Umma ta miƙa mata hannu, Umaima kawai take kallo sai rabewa take yi, ta daɗe tana kallon ta kamar bata gane ta ba sai can tace "Amama Amama." Umaimah tayi mata dariya ta ce "oyoyo my baby." sai kuma ta tafi ta zauna a cinyar ta Uncle Ismah ne suka fito tare da Adil yayi mishi wanka ganin Iman a cinyar Maamahn shi ya zo shima zai zauna suka fara ture ture Umaima tace to kowa ya tashi abun yara shike nan suka tashi suka fita compound suna wasa. Sai gab da magriba su Amira suka shigo ganin Umaima aka fara iface ifacen murna "yi mata a hankali ba ita kadai bace." baby bump ɗin Amira ya fito ta sake ta tayi hugging Hidaya tace "kaga Amaryar Hafiz sai wani glowing kike yi." Da daddare Umaimah na bawa Ãdil abinci Umma tace "Haka kike dirka mishi abinci kamar rikon kauye Umaimah? To Siyama ba gara ya ci ya ƙoshi ba, ba kya ganin yayi kumari da yaro sai cereal sai custard an mishi goyon turawa, ina mu ci muke ko Adil din Maamah?" ya ce "yes Maamah." Umma tace "Dan maaman uwa ta buɗe maka ciki maigida babu cefane." Ita Iman wasa take yi da abincin Umaima ta saka hannu tana bata a baki ganin Adil ya sa taki bin Mamin ta. "Siyama wlh kibar nan ki rage ta zan siya muku sport wears ke da Mami ku fara training kwa rage cholesterol." Baba ya shigo da sallama "me za a rage cholesterol? Baba baka ga timbin Siyama ba? "ya ilahi ya Allah ina ruwanki da tumbi na ne? Idan baki sa na yi magana ba ba kya jin daɗi." "rabu da ita uwata kullun cikin begen ki take yi da ƙyar ta dawo dai dai har rubutun dangana Tasiu ya rubuta mata." Umaima ta yi dariya "ashe haka ake so na? Rubutun dangana kamar wata yar yaye Baban Khadija? "To ba a yi ba ne? ki fada mana, Uwata har mafarkin ki fah ake yi." ya ce a kawo mana abinci ya fita. Umaima ta yi dariya, Umma ta sha kunu ta fita. Umaimah tayiwa Aadil da Iman wanka ta shirya su ta sakko ƙasa, Uncle Aliyu ke kallon BBC, su Daddy suna Dinning ta ƙarasa ta gaishe shi ya amsa ya ce "yaushe kika zo? meya kawo ki?" ta zumɓuro baki, ji baƙin hali "bikin Hidaya na zo." Bikin ne sai kin zo? Ta yi shiru, "ba dai matsala ko? sai ta saki ranta tace "babu komai." ya miƙawa Adil hannu zo mana wayar hannu ta tayi ƙara Hidaya ce tace ta same su a bangaren Mami. ****** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 3️⃣2️⃣ Washegari Umaima ta sauko ƙasa ta gaishe da su Daddy, Baba ya kalleta yace "kiyi ƙoƙari kafin ki tafi ki je Bichi Dada tana jajenki, ta ji kin zo." Daddy zani tinda nazo ɗan hutawa nake yi sai mun gama hidimar biki, su Siyama ina suka tafi ne da safe haka? Kasuwa suka tafi kina bacci har da su Adil su Ibrahim sun fita da su Amira. Ni kadai aka bari kenan? "mu ba mutane bane? cewar Baba, kya ce ke kaɗai." tayi dariya tace "ku ne mutane kuwa Baba " tana rufe baki sai gasu sun shigo, kasuwar Ƴankaba suka je siyan cefanen biki gobe Laraba za a fara kamu jibi ayi launcheon ranar Alhamis, juma'a za a tafi da wuri kafin masallaci Abuja za a kai ta dan ranar za a juyo. "Siyama kin gan ki kuwa sai tsiyaya kike yi kin haɗa gumi, wlh kitse yayi miki yawa." Umma bata kula ta ba ta kira Barira da Baba Rabi su kwaso kaya a boot ta amsa da toh ta fita, Mami ta wanke yalo cike a bowl ta ajiye a gaban su Daddy "yawwa Mami irin wannan za ku rinƙa ci yan China suna cin shi sosai yana ƙara lafiya. Daddy yace "yawwa Uwata wacce irin Amarya zaki nemo mana? Tace "Daddy yar shawalwala." a fusace Umma ta jefe ta da throw pillow "sai dai ayi miki kishiya ba a nan ba wlh." "Siyama duk shekarun nan ke kadai kin yi sharafinki ina laifi? Ato faɗa mata dai Uwata cewar Baba "Nidai a bar batun wasa zamu fara execise." "yawwa Mami kin nemi maslaha, Amma Siyama sai mun danganta ga kishiya yar shawalwala." Umma ta rasa me zata yi mata ta huce tace "wlh kin yi wa tsarabar ki haka zamu yi dake? Su Baba na dariya Amira ta shigo tace ita suka zo ɗauka sun yi parking a waje ne za su kunshi da gyaran gashi, "yawwa tunda kun zo ku fita dan Allah a sauka lafiya. "Sai mun dawo." suka fita. UK Yau kwanan su biyar da tafiya kullum lissafi yake yi ya kikkira Daddy sun gaisa sau wajen uku suna magana da Adil a wayar Daddy, ita ce dai kawai tunda ta tafi be ƙara ji daga gareta ba, in banda ita yarinya ce ai ta kira ta ce sun sauka lafiya tunda dai shi ya bada izinin tafiyar koda yake shi ina ruwan shi da ita? Kai da rabuwa ma za ku yi wata zuciyar ta tuna mishi, haka ne fah ashe ma rabuwa zamu yi, yes rabuwa zamuyi meye na damuwa? He miss Adil. Ya tashi daga falon ya shiga ɗakin Adil komai neat kamar da mutum a dakin yasan aikin Mrs Lawrence ne ya zauna a bakin gadon still dai ya ji zuciyar shi tana commanding din shi ya leƙa dakin Umaimah, to ya shiga yayi me? Ko dai ita ma kana missing din ta? No ya za a yi yayi missing dinta yaushe ma ta shigo rayuwar shi, kamar sarrrafa shi ake yi ya mike ya nufi ƙofar ta ya ya tsaya kamar me tsoron wani abu ya murda ƙofar dakin ta buɗe, towel a kan kujera kan dressing mirror ta bude lotion da hair cream a bude ya rufe mata ya ɗauke towel ɗin ya shanya a toilet fararen panties kusan shida a shanye ya ƙura musu ido ya fito ya dawo ɗakin har yanzu da kamshin humrarta a ɗakin, haka kawai ya ji yana son yiwa ɗakin shara ya ɗauko vacuum cleaner ya share ɗakin tas ya nade centre carpet din yayi mopping ya zo yaye bedsheets din ya ga bra dinta a kan gadon ya haɗa ta da bedsheets ɗin mai colours ɗin flowers kan shi har ya fara juyawa ya nade ya saka a laundry basket be canja mata wani ba tunda babu kowa a ɗakin yayi goge goge ya wanke toilet, wata zuciyar tace meyasa kake mata aiki? Saboda bana son datti kuma nan gida na ne I have every right to do so. wata zuciyar ta bashi amsa har zai fita idon shi ya kai kan bedside wani cute frame ne hoton ta ne tayi murmushi, tayi parking gashinta da ribbon farkon wayar uncle Ismah da zai shiga BUK Aliyu ya bashi ita aka fara dauka a wayar, ya kurawa hoton ido na wani lokaci ya mayar da shi ya ajiye sai kuma ya koma ya dauko ya fito daga dakin, gidan shiru Mrs Lawrence ta tafi gida, kai boredom zai kashe shi. Kano Yau kamu anyi decorating gidan sosai yayi kyau setting din wajen ya ƙayatar musamman wajen da Amarya zata zauna dayake kamu ne decoration din gargajiya aka yi an jere akwatinan karfe a gefe da kumbo, an yi adon kore, an yi kwalliya ta musamman a wajen da Amarya zata zauna abinci ma an yi na gargajiya da snacks gida ya dauki harama yan Bichi sun zo, yaya Surayya ce kawai bata zo ba ta raka maigidan ta Paris sai ya Amal da su ya Hindu da Munnirah ne suke zirga zirga dan jiya suka dawo daga Abuja. Dj ya saki wakar share hawayen ki amarya share hawayen ki, yara suna rawa friends ɗinta suna tare da ita a bangaren Mami a sama Umaima ta shigo dakin tace "ya kamata a fito wajen ya cika ance dangin Ango sun iso." babbar ƙawar Hidaya Maimoon tayi wa Hidaya rada a kunne suka yi dariya, "me ake cewa? Umaima ta faɗa "yarinya naga alama kan ki rawa yake yi ni bari na faɗa miki kinsan bani da mugunta irin ta Amira." Amiran tayi dariya ta girgiza Kai "wlh za ki ji maza yarinya. Hidaya da ake karasawa make up ta harari Umaimah, "Au harara ta kike yi ilimi ne kyauta ko dai har kin fahimci komai ban yarda da ke ba? ta tsare ta da ido, friends din suka hau shewa ana dariya Aunty Amal tace "lallai duniya ta yi muku dadi to ku fito waje ya cika." Iman da Adil da su Laila da Hanif yaran Aunty Amal suka bita a baya wai ta ba su kudin liki, suka fito kawayen Hidaya Kampala suka yi marron colour suka yi dinkin borno style, Amira da Umaima wani material suka yi blue black ya yi musu kyau suka fito aka Zazzau na Mc Jakadiya ta fara gabatar da abunda ya kamata an bude taro da addu'a, dangin ango suka zo kamu aka bukaci kawayen Amarya su fito su yi rawa masu daukan hotuna suka zo ana dauke dauken hotona Sa'ad da su Ibrahim da uncle Aliyu suka zo suka dauki hoto da Hidaya, "Papi snap us with Maamah." Ãdil ya faɗa, "bari na dauke ku da wayata." Sa'ad ya faɗa ya dauke su, Uncle Ismah dauke mu. Sa'ad ya bashi wayar Adil a tsakiya Sa'ad ya saƙala hannun shi a kafaɗar Umaima suka yi dariya hoton yayi kyau sosai Amira ta zo wajen "sweet mu dauka." mai hoto ya rinƙa daukar su, Abokan ango suka zo tare da Ango suka dauka da Amarya. "Maamah I want to eat this." ya nuna Awara, ku zo mu je ku ci abinci ta ja zugar yara, ƙawayen Amarya suna rawa an saka musu wakar Amarya ta Ali isa jita suna rawa abokan Ango ana musu liki a haka kamu ya tashi. Dan Allah Siyama yi min tausa an dade ba a yinmin tausa ba wlh na gaji zaman gidan ƙunshi. Ni Allah ya kiyashe ni da yi miki tausa. Amira tace dani zance kimin tausar ma wallahi bakiji baya na ba." Hidaya ta ce "ba kin biyewa ya Sa'ad kina rawa ba." Umaimah tace "har na ji na wartsake kwanta Maman baby sai nayi miki indai zaki ji daɗi." Zan ji daɗi wlh. ta wani lumshe ido tana wani langwai ɗan ta samu lagon Umaima akan cikin nan duk abunda tace tana so haka ta ke yi mata, ko ta saka ayi mata Sa'ad kuwa cewa yake ta biya shi wlh har kiranta ya ke yi a waya ya yi mata godiya sai dai ta yi dariya tace babynta ne. Ta dage tana mata tausa har ta yi bacci ta fito daga dakin ta bar Hidaya suna waya da Hafiz, ta shiga dakin Umma su ya Amal ne a ciki tace "ina Siyama? naji da mutum a toilet." suka ce ba ita ba ce ya "Hindu ce." yaya Anisa ta fada, ta sauko kasa yan Bichi ne a falon suna kallon kwana Casain, bangaren Mami yan uwanta ne yan Maiduguri, Munnirah ta kira Umaima suka shiga dakin kasa matar Baban sama da matar Baban ABU Aunty maimuna da Aunty Bilkisu suna tare da Munnirah suna packaging sovenier da za a raba gobe, Umma tace "gani neman me kike min? Tausa zaki yi min.' "a'a goya ki zan yi." aka yi musu dariya, tace hamma shikenan tunda baza ki yi ba idan Baba yayi Amarya ta yi min mu kwana lafiya." ta fita daga dakin "Allah ya baki sa'a. Umma ta bi bayanta da harara. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 3️⃣3️⃣ UK Ya dawo daga aiki a gajiye gidan shiru dan Mrs Lawrence ta tafi haka dai yake rayuwa duk babu dadi ya shiga dakin shi ya kunna AC ya shiga toilet ya fito da ruwa a jikin shi ya shirya ya ɗauki wayoyin shi ya dawo falo ya kunna TV ya haɗa tea yana kallon CNN Mrs Susan ta kira shi suka yi magana, wayar na hannun shi ya ga Ad yayi updating status ɗin shi ya fara kallon pictures jijiyar kan shi ta mike har sai da ya tashi tsaye hoton da suka ɗauka ne da Umaimah su uku suna dariya, ya kalli hoton material ɗin yayi mata kyau, amma shi ba kyan ya gani ba, bata da hankali ne ga background ɗin picture ɗin akwai maza me yasa Sa'ad yake ƙoƙarin taɓa boobs ɗin ta? this is bullshit, damn it, yayi wurgi da wayar a kan kujera kamar an tsikare shi ya ɗauki wayar ya fara kiran Sa'ad sai da ya yi mishi 6missed calls abunda baya yi, iyaka ci ya kira sau 2 Sa'ad be daga ba yayi cilli da wayar yana mayar da lumfashi to me yasa ma abun zai dame shi? Hakkin Allah yake karewa ko menene dai za a kira ta da matar shi duk da rabuwa za su yi. ***** Umaima ce take kwance tunda safe ciwon mara take yi ta sha magani amma dai har yanzu marar ta tana ciwo Adil ne ya shigo ya zauna kusa da ita yace "sorry Maamah." ta gyaɗa kai, "kirawo min Siyama." Yaa fita yana "Siyama Maamah is calling you." Umma tana tare da Baba, ya tsokani Adil be iya Hausa ba "zo ka karɓa." ya bashi Ayaba, ya karɓa Baba yace "baka ce komai ba." yana nufin be yi godiya ba Adil da ba Hausa ce ta ishe shi ba yace "komai " aka yi dariya Umma ta tashi ta je wajen Umaima, "ya marar sannu, ga magani Ibrahim ya rubuta an siyo miki a pharmacy." ta tashi ta sha maganin ta kwanta, ina su Hidayan? sun tafi Bichi da Angon zai gaishe da Hakimi. Sun karɓo mana ɗinkin? Eh sun karɓo kayan yana ɗaki na. ta lumshe ido bacci ya dauke ta. Tun da ta tashi daga bacci ta shiga toilet ta ga period ɗin ta ya zo shike nan ciwon ya ɗauke aka fara shirin tafiya luncheon Amira ce ta shigo ɗakin da sallama "ga dinkin ki na karɓo mana." ta daga kai "amma yayi kyau sosai ku fara shiryawa fah kun san Daddy baya son African time in dai event centre za a je kar mu yi dare friends din Hidaya suna part ɗin

Chapter 13 of 27