Mami an sauko mai make up, ana ta yi musu kwalliya kafin ayiwa Amarya."
Wani lace suka yi ashobe light purple sai suka saka silver head yayi musu kyau sosai. Umaima ta shigo dakin tace "yau nima rana ɗaya ayi min make up ɗin nan." Amira tace "dama ke ce ba kya so kiyi zai miki kyau."
"bari a gama mata sai ayi min." ta samu waje ta zauna ta fara kallon pictures ɗin jiya na kamu Sa'ad ya turo mata hotunan sun yi kyau barin wanda suka ɗauka su ukun nan tana kallo tana murmushi kiran Uncle Ismah ya shigo ta ɗaga "uba na na kaina."
Luncheon
A amnef event centre ne yan uwa da abokan arziki sun hallara Hidaya white gown ta saka Angon ya saka farar shadda sun yi kyau sosai suna mota, kawayen Amarya a tsautsaye suna jira a basu damar shigo da Amarya Adil da Iman an musu kwalliya za su rako Amarya da Ango su Umaima kowa sai yace ta yi kyau don bata yin make up sosai kwalliyar tayi mata kyau sai da Baba yace ayi musu hoto kafin su fito wai kamar India, ya Amal ce ta bawa ƙawayen damar shigo da Amarya da Ango Dj ya saka wakar ogechi da abokan Ango dayake tashin Lagos ne akwai Yarabawa sun yi ashoben su da hula irin ta Yoroba demon's sun shigo da rawa Umaima da Amira ne a ƙarshe aka zazzauna Mc ya fara gabatar da best man ya fito ya bada brief history, best friend din Amarya Maimoon ta fito ta bayar da speech ɗin ta aka yi tafi mc ya gabatar da games tsakanin couple aka yi refreshment kawayen Amarya suka fito rawa, Umaima ma ta yi wa Amarya liƙi wani abokin Ango ya fara mata liki ta fito ta bar wajen, yau ma sun dauki pictures sosai a haka taro ya watse sai gobe kuma za a kai Amarya gidanta Abuja.
Sun dawo daga luncheon ana zazzaune a falo Umaima tace "Siyama wannan ma Isiyaka ne yayi? bafa a biya kuɗin ɗinki ba. Uncle Ismah yace "nawa ne." "A'a ba kai zaka biya ba." Sa'ad yace "babu komai sai na biya." Ibrahim ne yace "wlh ki rage son kuɗi."
Haba Uncle Ibrahim Siyama kuɗi gare ta, ta karɓa a wajen Baba ta karɓa a wajen yan banki." Aliyu ya galla mata harara ta ɗauke kai, Umma tace "zan koma wajen Musbahu wannnan bita da kulli." Ai kuwa Isiyaka ya fi Musbahu iya ɗinki. Umma ta matso kusa da ita tayi magana a hankali "ni yaya ne har na fara tunani ko ciki ne dake? Umaimah ta kama baki "Siyama sirrin ma'aurata kike son ji ko? toh bani da komai." Umma na jin haka ta bar wajen kar ta tara mata mutane, Daddy yace "Sa'ad miƙo min remote ɗin nan." ya tashi ya miƙa mishi kenan wayar shi tayi ƙara yana ƙoƙarin Ciro ta a Aljihu har ta katse ya duba 15 missed calls Fahad ne, gaban shi ya faɗi ya fara ƙoƙarin kiran shi ya ji lafiya, tana fara ringing ya ɗauka "guy how far?" Muryarsa a tsaye yaji yace "what the he'll, why are you irresponsible?" kan Sa'ad ya kulle "wai me ta faru?
Bai bashi amsa ba ya sake cewa "aren't you ashamed of your self? You snaped a mannerless picture trying to touch her boobs, are you for real?why? are you mad? answer me." ya faɗa da ƙarfi.
Sai da Sa'ad ya shiga tunani kafin ya gane abunda yake nufi ai kuwa ya rinƙa dariya har da kwanciya a kujera, jin yana mishi dariya ya saka ya kashe wayar gumi ya tsartsafo mishi ranshi yayi mugun bacci, gidan yayi mishi ƙunci ya fito strolling a estate shi kan shi he is confused an ya kuwa ko dai ya fara son yarinyar nan ne? No how? hakkin Allah yake karewa ai ba dai dai bane zuciyar shi taƙi Aminta saboda ƙifadi irin nashi.
Aliyu ne yake kallon Sa'ad daya ke ta dariya sai da Daddy yayi mishi magana ya hana shi jin labarai sannan ya tashi ya fita compound, ya kira Amira ta same shi a waje tana zuwa da yake wajen babu mutane ya daga ta yana juyi sai da ta ce "zan yi Amai ka ajiye ni." sannan ya tsaya, "you know what?"
"sai ka faɗa."
"Dattijo sai yayi dariya ya faɗa tarkon daughter." nan ya faɗa mata abinda ya faru, "Alhamdulillah wannan nasara ce tunda Umaima ta shiga rayuwar shi na kula tun kwanaki daya dauke mata keke bakin shi ya fara buɗewa, wlh I'm soo happy we need to celebrate this baby." ya kashe mata ido.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 3️⃣4️⃣
Ranar Juma'a kafin masallaci aka kawo motocin kai Amarya da wuri a ka tafi saboda a dawo da wuri yawanci na jiki jiki ne suka yi rakiyar tun da ba a Kano ba ne Baba yace waɗanda basu je ba su yi hak'uri sa je wani lokacin, mota biyar aka yi ɓangaren su Daddy yan Bichi mota 2 ɓangaren Mami mota biyu, sai su Umaima mota ɗaya da wasu daga cikin ƙawayen ta guda 2.
An kai ta gidan ta a Maitama Ghana street, yan uwan mijin sun yi musu tarba sosai aka yi sallah aka ci abinci basu daɗe ba aka fito tunda ba kwana za a yi ba Hidaya idon ta ya tara ruwa kamar zata yi kuka Umaima tace "ba wani nan ina miki karatu kina wata dariya." ta yi maganar a hankali, "faɗa min babu mai ji kila ma an dace ko?" Hidaya ta harare ta tace "me kike nufi?
'Da abun da ya faru daga ganin idon ki wlh kun saba da mijin ki." ta ɗaka mata duka.
Ya Amal ce ta shigo tace da Hidaya kin gani waɗannan kayan anan muka saka miki idan kina nema duk abunda baki gane ba ki kirani. kamar zata yi kuka tace "wai dan Allah ba za ku kwana ba?
"rufa mana asiri ba maganar kwana.
Wash wlh ni dai gaskiya dana sani ban zo ba jikina duk ciwo yake yi. cewar Amira, "a fito fah har an fara shiga mota kar mu yi tafiyar dare." ya Hindu ta shiga ta faɗa aka mimmike ƙawayen ta su Maimoon suka yi mata sallama sai a mota Umaima take tunani data tsokani Hidaya ashe fah ba a dace ba kenan tunda tana period, sai an sake wahala kenan mtsw ta yi tsaki. "lafiya? Amira ta tambaya, babu komai ta fada ta cigaba da tunani sun isa dab da magrib sun sha gajiya aka yi sallah, yan Bichi sai gobe Asabar za su wuce, "ku zo ku ci abinci ko Barira ta kai muku sama." sannun ku suka amsawa Umma, masu sallah na yi masu cin abinci na yi, Amira ta yi baje baje ta kwanta a ƙasan carpet tana mayar da numfashi Umaima ta kalle ta tace ta tashi ta ci abinci "wlh na gaji ne."
Tana kwancen har ta fara bacci, ita ma a gajiyen ta ke bari tayi wanka, dama ita indai tana period bata kyashin wanka da yawa, ta fito daga wanka Amira har ta farka tana zaune "kin ci abinci?' ta turo mata warmers, tace "wlh shawarma na ke son ci.' "toh Maman baby bari na idar da sallah sai a nemo miki." tana idarwa ta saka hijab ta ɗauki jaka ta sauko ƙasa, "ke kuma ina zuwa? Uncle Ismah ya tambaya, tace "Maman baby ce zata ci shawarma" waye haka ? "Amira mana." ta fada, Baba yace "shi ne zaki fita kusan goma? Toh Baba ita babyn ke so ai. "Eh lallai yau ga taɓara ina gani." Umma ta faɗa, Baba yace Hakim ya je ya siyo.
Yau Lahadi duk an watse sai yan gida har su Amira sun koma kayan tsarabar ta Umma ta dauko mata tana daga wa tace "Siyama wannan Riyal 1000 fah, canjin mu ya lalace kowanne riyal daya 470." ta dauko waya tayi calculating 470,000 "haba Siyama ashe kina da ƙarfi, ni Sweetheart ɗina ya siya min Abaya tafi wannan, kuma ma dai ina da su da kuɗin kika bani" ta daga wata Ash colour itama Riyals masu yawa, Umma kawai ta tsaya tana kallon ta, "amma dai ke ba a miki abun arziki na ƙulle kuɗina na yi miki abun kirki ki gwale ni?" ta ɗaga kayan Adil jalabiya da turare na Fahad ne, tace "a'a mungode musamman na dana ma nafi murnar su." ta mayar da kayan cikin jaka ta cewa Umma "nagode Siyama amma wlh kuɗina zan karɓa kin ga na shiga kasuwa account ɗina yayi low." Allah ya raba ki da son kuɗi kamar ki yi sata wlh ki canja hali. "toh Siyama wannan Almabazzaranci ne a lefe an saka min da wannan kayan Allah gara ki ƙara min jari." Umma takaici yasa tace "bani da kuɗin baki jari."
To shikenan Nagode.
Aliyu ne ya shigo yace wa Umma ta zo su gaisa da Shamsu Abokin shi, Umma ta miƙe ta fita Umaimah ta rufa musu baya ta sauka, su Isma'il da Adil suna cin Abinci Umma suka gaisa da abokin Aliyu ya ajiyewa umma rafar 1000, yana fita Umaimah tace "Siyama mu raba." Ta harare ta, "shikenan bari nima na kasa hajata." ta hau sama ta sauko da leda a hannunta. Ina zaki da kaya?
Tace "Siyama tsaya ki kalli ikon Allah." Aliyu yana shigowa tace Uncle Babangida ga Abayas ka Siyawa Aunty." ya kalle ta "waye Aunty? Ta fara bude ledar tana fitowa da su, "Auntyn mu mana ko a lefe sai a saka su." Ismael yayi dariya yace "wlh ke yar rainin hankali ce to aure kika fara nema mi shi? Sai da Isma'il ya faɗi haka ma ya fahimce ta, yace "ke yaushe muka fara wasa ni da ke?
Umma ta ce rabu da ita ba a yi mata gwaninta. ta mayar mishi yadda suka yi."
Aranshi yake musu dariya amma ko babu komai tana ƙoƙarin nema, single handedly ta biyawa iyayen su Umara ya jinjina mata, ya ga ƙoƙarin ta atleast she needs encouragement and support "bani account number ɗinki." Ya faɗa yana danna wayar shi, da sauri ta karanta mishi ya turo mata kuɗi masu nauyi ta kalla ta kara dubawa, "Allah ya biyaka ya baka mata ta gani ta faɗa." Wacce irin addua ce wannan, ta gari dai."
To Siyama ta gari mu sha biki. ya sha kunu be amsa ba "Uncle Ismah kalli ta nuna mishi.
"Sai ki bamu salala." cewar Umma, "ta tattare kayanta ta hau sama tana cewa gobe in sha Allahu sai kasuwa.
UK
A lissafin shi dai da suka yi magana da Mami tace ranar Juma'a za a kai Hidaya, toh sai su fara shirin tahowa zaman me kuma su ke yi? Duk da ɗazu sun yi magana da Daddy amma be ji yace sun fara shirin tahowa ba, toh me ye nashi ma idan sun ga dama su yi wata, anya kuwa su yi wata? Inaah dan yanzu kwata kwata sai yayi isha'i yake dawowa yau weekends ne kusan yini yayi a gym be dade da shigowa gidan ba, ko lokacin da ya shigo ma magriba ta kusa ganin ma shi kaɗai ne babu wani aiki yace Mrs Lawrence ta yi zamanta yau kar ta zo ya bata off, kafin ya fito ya gyara ko'ina ɗakin shi ma sanitation yayi mishi na musamman duk don yayi keeping kan shi busy ya tashi ya haɗa coffee ya dawo ya zauna a Dinning ya bude system ya fara aiki wayar shi tayi blinking alamar text ya shigo Sa'ad ne yayi mishi text kamar haka.
*Salam let's put this behind us Umaimah is like a daughter to me and the picture is harmless can we move on?*
Jiya be ji daɗin bacci ba ya karanta ya kara he overeacted wai what is wrong with him Ad doesn't deserve this ya daga wayar ya kira shi suka yi magana komai ya wuce, kamar zai yi masa maganar dawowar su sai kuma yace "it's okay thankyou." suka ajiye wayar ya sake duba status din Sa'ad ya ga ya cire hotinan yana scrolling ya zo kan status ɗin little sis (Hidaya ) ta doddara hotunan kawayen ta a ƙasa ta saka thanks for coming, sai nasu da Hafiz, ya zo kan wani hoto Umaima ce da Amira tare da Amarya da Ango da Abokan angon, wani abokin Hafiz ya tsaya a kusa da Umaimah directly idon shi a kan ta yake ita kuma tana kallon camera, tayi kyau sosai she looks different sabida make up ɗin yayi mata mugun kyau, wani abu ya tokare mishi makogwaro har wani daci daci yake ji a maƙoshin shi jikin shi har bari yake yi ya danna wa Hidaya kira
Hidaya ta gaji jikinta duk babu dadi tun bayan sallar Asuba ta koma ta kwanta Hafiz ya fita be tashe ta ba tasan tausaya mata yayi is not Easy an sha hidima gajiya duk jiki sai da ta tashi ta ga text din shi ya je su yi sallama da friends din shi da suka sauka a hotel da yawa Lagos zasu koma, tun tana wanka ta ji wayar ta na kara ta fito wayar a bedside ta dauko Yaya Dattijo sunan da ta yi saving kenan sai da gabanta ya faɗi ba don kar ta yi ƙarya ba sai tace anya suna waya, ita ce dai take mishi ta Whatsapp ta tambaye shi Adil, ko ya aiki shi ma sai yayi a week kafin ya buɗe yace mata fine shikena.
Ta ɗaga da sallama be amsa ba sai jin muryar shi ta yi cikin daga murya "you are very stupid, are you Mad?remove those pictures on your status, who does that?"
"Yaya bangane ba?" gaba-daya ta rikice muryarta na rawa, wlh iya gaskiyarta kenan.
"I said remove her pictures."
"wlh Yaya bangane ba." kawai kar ya wahalar da kan shi ya ga tana son ɓata mishi lokaci yace "my wife pictures I said remove it or else you regret it."
Ya kashe wayar yana huci ya dafe kai oh God cewa yayi his wife sai abun yayi mishi nauyi a baki wife ɗin da rabuwa za su yi ya kashe System din ya tattara kayan shi ya shiga ɗaki.
Kano
Yauwa Isiyaka komai yayi yanzu mannuquine zamu karo sai a rinƙa saka ɗinkin masu kyau ana display mutane su na kallo, akwai buƙatar a karo keke ma gobe zan shiga Sabon gari nayi order Abekuta Kampala daga lagos ina tunanin baku wasu ku gwada dogayen ruguna dan a can suna tafiya.
"toh Hajiya sai mu gwada."
Salisu saka min wannan a mota ya karɓi kayan ya fita, wayarta ta yi ringing ta ɗauka da sauri "Amarya me ye labari?" kukan Hidaya ne ya saka hankalin ta ya tashi, "menene?" Hidaya muryar ta na rawa ta faɗawa Umaima yadda suka yi da Fahad da zagin da tasha suman zaune Umaimah ta yi "his wife kuma? Ko ya manta da deal din su ne?"
Ina daga gefe nace ko ba wife ko🤓
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 3️⃣5️⃣
Tuni Umaimah tayi wankan tsarki ta fara ibadah kawai harkokinta ta ke yi kullum tana hanyar kasuwa da store ɗin da suke bada kaya, sam ta ma manta da wani Fahad kawai kudaden ta take kamawa, Umma ta yi mata zancen komawa ta ce sai yayi magana tukun shike nan bata sake mata maganar ba, ita fah wlh ta fi jin daɗin zaman nan koda yake kamar yau ne zata dawo, dan har ta je wani shago a farm centre tana son kamawa ta ƙara expanding Business dinta, to amma su Isyaka ba za su iya ba dole sai ta samu ma'aikata zata bari kawai pending lokacin da ta dawo kawai tayi kamar yau ne ai, mtws ta yi tsaki wannnan wahala haka za a yi tayi wlh ba don tana son haihuwa ba itama da ta haƙura kawai.
"Maamah I want to ease my self." Adil ya faɗa, tace "zo na cire maka wandon. ya ƙaraso ta cire mishi suka shiga toilet tare, "Maamah call Papa pls I miss him." ta kalle shi tace "ka je Daddy ya kira maka shi." "Grandpa isn't around." To kaje wajen Mami.
Kawai sai ya fara mata kananan kuka shi saita kira masa Papa, "kayi min shiru wlh kar raina ya ɓaci dana sani ma ni kaɗai na taho ku karata da kurman uban ka."
"Papa! Papa!! Ya ƙara volume yana kuka, Uncle Ismah ne ya shigo dakin yace "menene? zo nan." ya ja hannun shi, "kyale shi rigima ce kawai ba wani abu ba, come and lay down." ta gyara mishi cinyarta ya zo ya kwanta, "Uncle Ismah I want to talk to Papa." Shi ne kake kuka? Bari na kirawo maka shi goge hawayen ka.
UK
Yana aiki ya kasa concentrating sosai mistake yake tayi don ya turawa Mrs Susan ta kara dawo mishi da shi be yi ba, me ke damun shi? ba a taɓa dawo mishi da aiki ba ya kara concentrating da kyar ya kammala aikin sai wajen yamma don har an tashi ya jawo calender ya duba, wannnan yarinyar is careless yayi ticking in 2 days time zata fara ovulating ita ta kawo condition amma ya fi ta mayar da hankali, su Daddy sun zuba musu ido to so ake yi yayi magana ko me? Ya jawo wayar shi ya fara dialing number Sa'ad tana fara ringing ya dauka "guy ya kake? Ya aiki?"
"fine." ya amsa sai yayi shiru, "ina jinka?" Sa'ad ya faɗa, da kyar yace "give me that girl's number." Sa'ad ya kawar da wayar yayi dariya, sarai ya fahimci Umaimah yake nufi yace "which girl? Haushi ya kama Fahad sai ya ji Sa'ad yace ko Hidaya yayi tsaki ya kashe wayar shi, suna ajiye wayar yayi mishi text din number Hidaya da sauri ya bude ganin number Hidaya ran shi ya ƙara ɓaci, shi Ad zai yiwa wulakanci? uban me zai yi da number Hidaya, idan ba Ad ba babu wanda zai tambaya number ta gudun zargi ya haƙura duk lokacin da suka so sa dawo, wata zuciyar tace masa kar lokacin ovulation ya wuce ya dafe kai, dole ya kira Daddy.
Yana shiga gida ya gama duk abinda zai yi yana zaune a daki ya dauko wani littafi yana karantawa (Tresure Island by Robert Loius Stevenson - a timeless pirate adventure) shi yayi keeping din shi busy yana jin dadin karatun wayar shi tayi ringing Ismael junior kamar yadda yayi saving sunan Uncle Ismah, yayi picking vedio call ne shi be cika son vedio call ba ya dai daga sai ganin fuskar Adil yayi yana dariya shi ma murmushi yayi "Papa I miss you, Papa when are we coming home? kawai kallon kumatun shi yake yi "how are you Didi?
I'm fine Papa and you? "I'm Didi."
Uncle Ismah is very nice he call you for me with his phone. Fahad ya jinjina mishi hannu great "where is Uncle Ismah? His downstairs Papa, papa did you miss me? ya ce "sure Didi." suna magana shima dadi yake ji, ta shiga wanka ta fito kenan da towel da kadan ya wuce mazaunan ta kawai Adil ya miƙa mata wayar "Papa wants to talk to you." ya sauka ƙasa da gudu za su fita da Uncle Ismah.
Fahad ya ƙura mata ido yana ƙare mata kallo, shi gani yayi ta yi fresh babu ƙarya ta yi kyau, ya kafe kirjin ta da ido ta kalli inda yake kallo ta yi maza tace "ina yini." ta dauki hijab ta saka "hmmm ya yaja doguwar ajiyar zuciya, muryar sa very low yace "fine, when are you coming back?" kawai ya ji baƙin shi ya faɗa ba tare da ya shirya ba, ta kalle shi ta juyar da kai "sai mun gama hutawa." ta faɗa "your ovulation is in 2days time I hope u are aware?" ta turo baki "ni wlh ma kamar na fasa kawai."
"No No don't start that you and I agree on that we are fully committed don't forget is an AGREEMENT." Yayi maganar da sauri, Ta harare shi ta murguɗa baki kawai ta kashe wayar.
Ya Allah wannan yarinyar zata kashe shi, yayi ta kira ta ajiye wayar kawai ta cigaba da shiryawa tana mita haka kawai ta jawo wa kanta wlh Amira ce duk ta ingiza ta koda yake itama tana so ta haihu tana jin wayar tana ringing ta yi banza sai da ya kira sau biyar taki daga wa, sauri take ta shirya su Sadiq ne za su zo shi da Aminu genius.
****
Wacce irin wahala ce wannan tun ɗazu idan ya tuno yadda ta murguɗa mishi baki sai ya ji jikin shi ya saki, to me wannan ya ke nufi? Can sai ya saki murmushi shi kaɗai, ta bashi haushi ta kashe mishi waya amma ya ji daɗi da suka yi magana me yasa tuntuni be kira Uncle Ismah nata ba ya haɗa su, sai kawai yayi dialing number Daddy suka gaisa yayi shiru Daddy yace ina jinka "Ãdil has been absent from school for quite some time when should I exepect them?" Daddy yace "na yi tunanin haka ka siya musu ticket wajen jibi sai su taho ga Baban ku ku gaisa." Daddy ya miƙa wa bana wayar.
Washegari
Umma ce ta sauko ƙasa Munnirah tana zaune suna hira da Isma'il, Iman da Adil suna ta wasa da kayan wasan da Uncle Ismah ya siyo mishi jiya da suka fita shopping Umma suka gaisa da Munnirah "zuwan kenan ko kin dade? A'a Umma ban fi minti 30 ba, Hakimi yace zai kira ki nace ya barki ki sauko ai ina nan yini zan yi."
Umma tace "toh shikenan dama ina neman ki." ta kalli Ismael tace ina Umaima ne?
"Ta fita shago."
Haka dai ta barbaza kaya a ɗaki kuma gobe fah za su wuce na yita mata magana ta rabu dani na san sai ta manta wani abu kin ga shirgin yar ki kuwa? Munnirah ta yi dariya tace "ya ta yar albarka kenan neman fah da gaske ake yi." Naga alama, Umma ta kalli Ismael tace "Ubana ɗan bamu wuri zan yi magana da ƴata." ya miƙe "nima fita zan yi ita ta zaunar dani." Adil suka ce zasu bi shi yace su sa takalman su suna murna suka fita.
Umma ta gyara zama tace "yawwa kayan gyara ne aka siya musu tare da Amarya kinsan yar ku sai a hankali daga tambayarta ko ciki gareta tana ciwon mara ashe period ne sai ce min tayi ina son sanin sirrin ma'aurata ko yaushe ma tayi auren? Gasu can bari na ɗauko miki ki bata da kanki kar sunana ya fito." Munnirah na dariya tace "shikenan Umma yau din ma ita ta fito dani na karbo mata wasu daga Maiduguri sai a haɗa mata." yawwa Allah dai yayi miki Albarka.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 27