Umaimah ta yi galala tana kallon su ta kashe wayar tana mitar amma Amira an yi yar iska wlh bari anjima sai ta goge ta.
*****
Delhi India
Sir Ganga Ram Hospital
Khadija ce ta fito su Baba sun mata waya suna asibitin ta fito, Umma tace bari ta ƙara kiranta, tana daga wa ta kwatanta musu inda take tsaye ba a fi minti 10 ba suka ƙaraso Khadija tana ganin su sai kuka ta tafi ta rungume Mami "ya isa, ya isa." ta rungume ta tana bubbuga bayanta, Baba yace "ko baki ji daɗin ganin mu ba? Umma kawai kallon ta take yi tayi fari ta rame ta gaishe da su tana share hawaye tana murmushi ta ƙaraso wajen Umma ta rungume ta, uwa mai daɗi ta lafe a jikinta Daddy yace "mu ƙarasa wajen Ahmad din, amma a wajen shi ki ke kwana ko?"
"ah ah ba a bari akwai nurse sai dai nazo da safe na tafi da daddare."
"to yayi Allah ya bashi lafiya." suka ranka ya dakin da yake, basu ji daɗin yadda sukaga jikin Ahmad ba suka yi mishi ya jiki Daddy yace idan likitan ya zo yana son ganin shi idan babu dama gara a canja mishi asibiti.
Su Daddy sun zo gidan Khadija za su sauke su Mami su wuce hotel Khadija tace "Dan Allah su tsaya su ci Abinci, "ah ah ma ci a hotel." Khadijah kamar tayi kuka Mami tace gaskiya ba zata ji daɗi ba suka Shigo Mami ta shiga kitchen ta ɗora musu Abinci sun taho mata da abubuwan buƙata.
Suna zaune bayan an gama cin abinci ana hirar jikin Ahmad Daddy ya duba wayar shi sai gani yayi Amarya added you, ikon Allah ya nunawa Baba, Umaima ce tayi creating whaapp group Baba ma ya duba uwata added you, kowa da sunan da yayi saving number ta, Baba ya nunawa Umma itama sai gani tayi Jika added you Mami kishiya added you, Khadijah lovely daughter added you, Khadija ta duba ta cewa su Daddy "ai kowa ta saka a group ɗin Uncle Ismah admin."
Su Baban sama Baban ABU da Baba Dr, Munnirah Amira Sa'ad har da su ya Surayya duk wanda take da number shi tayi adding banda Babangida da Fahad sai ta turo voice note.
Lafiya ƙalau gaisuwa tayi ta gaishe da iyayenta ta tsokani Siyama wai tayi kane kane a gida ita kaɗai wlh Baba aure zai yi Umma ta girgiza kai ana ta dariya sai kuma ga wai Vnote ɗin kawai ta fashe musu da kuka tana cewa "wlh mutumin nan ya ɗauke min Sasi."
A wayar Baba ne Umma tayi tsaki Daddy yayi dariya yace Khadijah ta duba Fahad yana group din? Ya bar glass ɗin shi a mota tace "ah ah babu shi."
"Khadija kira Hakimi tunda admin ne yayi adding ɗin shi tunda ƙarar shi ta kawo ba zata saka shi ba." Daddy be san bata da number shi ba ne, Umma tace "Allah a dena biye ta yaushe zata yi hankali." Khadija dai tayi shiru tana tunanin hali irin na Umaimah.
Ta ƙara turo wani Vnote ɗin "kun yi shiru?" Sa'ad ya turo emoji ɗin dariya Amira ta turo kuka, Isma'il yayi sallama ya gaishe da iyaye yace mata su je private.
Umma tace "za suyi gulma."
Fahad yana aiki a system ya ga kiran Daddy sai ya ga an yi adding din shi a group family lounge sunan group ɗin ya ɗan bi ta kara turo wani Vnote "wlh yayi ta cika yana batsewa yayi ta cin magani, ni wlh idan jini na ya hau shi ne." Subhanallahi Daddy yayi magana "ki yi hakuri, Dattijo ka fito ka yi mana bayani."
Yana jin me Daddy ya faɗa kawai ya fita daga group ɗin, Baban sama yayi sallama yace "wannan group yayi kyau idan wani abu ya taso za a iya tattaunawa anan a saukake Allah yayi miki Albarka." be yi maganar wata Sasi ba, Amin Baban sama Umaima ta turo.
Baba Dr daya ke mai barkwanci ne ya ce "ka fito ka bamu magen mu bama son turanci." Daddy yace "ai ya fita."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣5️⃣
Idon shi har rufewa yake yi saboda bala'i ya ƙyale ta ne dama ganin tun da yayi mata maganar cin abinci a falo tayi isolating kanta ya rabu da ita, Amma tunda ta saka Daddy yayi masa fada akan wata banzar mage zai ɗauki mataki, ya fito jin an fara kiran sallah akwai ƙaramin masallaci na wani Dan Afghanistan a kusa da su kusan sallar Asuba ma a nan yake ji, ko magrib idan ya dawo aiki, An idar da sallah ya daɗe yana Azkar kan shi ciwo yake yi dan daren jiya be yi bacci ba wayar shi tayi haske Sa'ad ne he needs to talk to him ya fito daga masallaci ya daga kiran, Sa'ad yace "Guy how far?"
"damn it I'm not fine." not fine toh? Sa'ad yace "me ya faru? ina daughter don't get you?" Ya faɗa, "Umaima"
ya ja tsaki "that stupid fool, and let me make it clear call her and warn her she should behave herself."
Fahad faɗa yake yi kamar Sa'ad ne Umaima, dariya Sa'ad yake yi ciki ciki ko ba komai zama da Umaimah bakin shi zai buɗe, yace ",ah ah fah ka bata magenta, and baka fahimce ta ba ne tana da daɗin zama."
Kit ya kashe wayar, yana shiga gidan direct ɗakinta yayi knocking da karfi, ta idar da sallah kenan da hijabi a jikinta ta fito suka haɗa ido, yace "follow me." ta biyo shi ya zauna ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya zata zauna a kujera ya harare ta yace "kneel down my friend, raise your hands, you have the audacity to report me to my parents."
Tirkashi ta faɗa a ranta "babu cigaba kenan kneel down a gida kneel down anan taɓ."
Yayi mata wata gigitacciyar tsawa ba ta san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana gunguni, "wlh dai Allah ya saka min to ni me nayi maka me Sasi ta yi maka." ta harare shi ta ƙasan ido ya ɗauke kai kamar be gani ba, hankalin shi yana kan waya yana scrolling abu data fahimci hankalin shi baya kanta da baya da baya ta rinƙa matsawa, Ãdil ya fito daga ɗaki ta yi mishi alamar yayi shiru da yatsa, tsiran daya rage tsakaninta da ɗaki kadan ne ta mike ta zura da gudu ta saka key, Ãdil ya kyalkyale da dariya, dariyar shi ce ta fargar da shi ya duba wajen wayam ta tashi yayi ƙwafa ya ja hannun Ãdil ɗakin shi yayi mishi wanka ya gama shirya shi Mrs Lawrence ta zo yau ta makara ya bar mata shi su ƙarasa shirin ya koma ɗaki.
Tunda ta gudo ɗaki suka yi waya da wizard ya bata number Ramla cousin ɗin shi dama yayi wa Ramlan bayanin Umaima, ta kira ta suka gaisa faram faram kamar sun daɗe da sanin juna tayi mata bayanin inda ta ke tace babu komai akwai yan Nigeria a area sosai ta faɗa mata tana ɗinki tace mata zata so ganin ayyukan ta, "baki da matsala yanzu kuwa zan turo."
"Okay ki bude instagram handle ki rinƙa posting sai ki saka location ni kuma zan miki reposting."
"kai amma nagode, na ji daɗi. "babu komai idan an kwana biyu zan zo mu gaisa." suka yi sallama, toh yanzu bari ta buɗe instagram account wanne suna zata saka? tayi creating account ta buɗe DRESSES BY UMAIMA tayi posting ayyukan da su kayi har kayan bikin su da aka ɗinka a DIJAH COLLECTION.
Ita ta manta da wani Fahad tana buɗe ƙofa sai ganin shi tayi a dinning da sauri ta rufe Kofar "Me yake yi har yanzu be fita ba ita wlh yunwa take ji." shi kuwa Fahad yau ba zai je office ba yana rage wasu ayyuka a system ya ga fitowar ta zai maganin ta ya lura tana son Abinci, ta ƙara buɗe ƙofar a hankali da sadaf sadaf ta wuce kamar barauniya tana shiga kitchen ya mike ya shiga ɗakinta ya cire mukullin ɗakin har zai fita ya kula da wayar ta a kan gado ya koma ya ɗauka.
Umaima tana suyar wainar flour tana sauri ta gama ta koma ɗaki, duk abunda ta bata Mrs Lawrence tana gyarawa, ta gama ta fito hankali kwance ta shige ɗaki ya bi bayanta ta ajiye ta shiga toilet kenan ya ɗauke plate ɗin wainar da tea mai kauri ya fito ya saka key ya kulle ta ya zare mukullin, tana fitowa waina tace ɗauke ni "ah ah to ina ta kai ta? ko tana kitchen kai haba ta dauka fah ta tafi ta murda ƙofar ta ji a rufe, "waye ya rufe ni? ta rinƙa buga ƙofar yana ji yadda jiya ya kasa bacci sai ya ɓata mata rai, zai ga wayar kai ƙara, bugu take yi "wlh ka dauki hakki nasan kana ji." sai ta buga da ƙarfi "wlh sai Allah ya bi min hakki na." sai ta fara hawaye, "kuma Allah kaci min sai ka yi Amai da gudawar ta."
Shi dariya ma ta bashi kamar zai yi dariya ya maze can ya ji ta yi shiru ta jingina da ƙofa in ba zalinci ba yanzu kusan 11 ita bata jimirin yunwa ta yunƙura, ghana must go ta buɗe wanda aka yi mata cin cin da kilishi ita tafi gane abinci sosai shiyasa bata ko kalle shi ba ashe zai yi mata amfani tana ci tana hawaye, "mugu ɗan masara."
Ta ware murya yadda zai ji tace "Allah ya saka min mugu kawai."
Taci cin cin sosai ta dauko dambun nama taci ta bude fridge ɗin ɗakin kamar ta sani jiya ta ɗebo ruwa a store ashe zai yi mata amfani, da ya ji shiru ya kira Mrs Lawrence yace ta bata lunch idan ta gama ta buɗe window ta ajiye mata.
"ok sir."
Ta faɗa ta cigaba da abinda take yi ya shiga ɗaki.
Haka ta yi shiru a ɗakin sai dai idan lokacin sallah yayi ta tashi tayi sallar tayi kuka ta goge hawaye wato muguntar shi kenan horon yunwa, duk zaluncin Babangida ba ya horon yunwa hasali ma sai ya tabbatar ka ci ka ƙoshi yake maka hukunci, amma shi ya ƙulle ta kamar a kurkuku an aiko mata da wani munafukin potato porriage a yar cointainer sai kace iman ce zata ci zai ga tsiya tunda haka zai yi wlh babu wanda zata ƙara kai wa ƙarar shi da kanta zata ɗauki mataki mtsw aikin banza.
Kwanciya yayi a ɗaki sai da ya daidaici lokacin tashin Ãdil a makaranta yayi ya shirya ya fito ya cewa Mrs Lawrence idan ta yi dinner ta ƙara miƙa mata ta window zai ɗauki Ãdil a School idan ta gama ta tafi yayi ficewar shi daga gidan ya biya ya ɗauki Ãdil a makaranta suka shig gari, sau tari a weekends yana kai shi eatery su yi yawo ya dawo dashi gida, yau dan kar ya koma gidan yace wajen Umaimah za shi kawai ya zarce dashi eatery ya siya mishi abinci, "Papa I want takeaway for Maamah." ya kalle shi yace bashi da kuɗi, Ãdil ya buɗe baki irin na mamaki zai dame shi da tambaya yace yayi mishi shiru, daga nan ya kai shi park ɗin wasan yara ya karɓi pass ya ajiye shi, Ãdil yana ta murna sosai ya saba da zuwa wajen shi kuma akwai supervision na aiki da zai je.
💫 UMAIMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣6️⃣
Zaman ne ya ishe ta, ta dauko ghana must go ta bubbuɗe su ta fitar da turaren wuta da humra ta jera akan dressing mirror, gyaran dole ta ke yi boxes ɗin ta duba ta fitar da kayan sawarta ta jera a wardrobe ta haɗe boxes ɗin waje ɗaya, ta shiga gyaran ɗakin dole, ita matsalar ta she is not organised sam bata da tsari kaya duk inda ta zubar shikenan, bata saka kaya masu datti sai dai tayi ta tarawa, ta gama gyaran har wankin toilet ta yi, yamma lis ta ji an buɗe window Mrs Lawrence ce ta ƙara ajiye wani abu a bowl ta ce mata ta tafi, haɗin salad ne an yanka kwai manya tayi mishi dahuwar su ɗanye ɗanye an saka curryflour a ciki bata san lokacin da hawaye ya ziraro mata ba wannan ne abincin daren? Lallai ya so kashe ta amma babu komai, kamar wacce aka mintsina ta fara dube dube tayi gyaran ɗakin ta gama, sam ta manta da wayar ta yanzu haka ma an yi following ɗin ta sosai a instagram, ta duba bata ga wayar ba "kar dai ya dauke mata waya? daurewa ta yi bata yi kuka ba, babu komai "in sha Allahu indai akan zaluncin ka ne bazanyi kuka ba."
Ta kalli haɗin salad "waye zai ci wannan kawai babu mahadi? Sai kace wata zomo, idan ba iskanci ba wannan ne zai rike ta?"
Ta tashi ta shiga toilet ta dauro Alwala tayi sallar magrib, shirun yayi mata yawa ta kunna TV tunda ta zo bata ko damu da kallo ba ita dama can tafi gane su yi hirar su da Uncle Ismah, tuna shi da tayi kamar ta yi kuka ta daure ta kunna tv ta kai Aljaxeera aka nuna yaƙin Gaza, yara ƙanana anyi bombing gidajen su wasu an sauko su abun babu daɗin kallo duk jini a jikin su (Allah ya ba su kariya ya dafa musu,ya basu rinjaye). Boms taga an ciro a karkashin ƙasa jini ta ko'ina nan ta lalace tana kallo tana kuka "kai Allah ya isan su, shegu Azzaaluman banza idan ta ga wani tashin hankalin sai ta rufe ido.
Fahad ya shigo gidan Ãdil yayi bacci a hannun shi ya kai shi ɗaki ya dawo falo ya haɗa tea ya ji kamar magana ya ɗauka ma ta yi bacci, sai ya ji kuka kuma shi mamakin ta yake yi kodai bata da lafiyar kwakwalwa ne aka haɗa shi da wahala ya ɗan matsa jikin ƙofar sai ya ji TV na yi, "shegu Azzalumai, Allah ya wulaƙanta ku." ya ji ta faɗa, is she alright? Sai yaji ta yi ihu "matsa, matsa." ta faɗa tana rufe ido "boms ya tashi da wasu."
Ya girgiza kai ya nufi kitchen ya ɗauko ruwa, ya dawo dakin shi yayi dialing number Sa'ad yayi mishi 2 missed calls be ɗauka ba ya rabu da shi, wlh tsoro ta bashi kar ya je ta samu matsala a kwakwalwa mutum mai hankali ba zai yi ta magana shi kaɗai ba kamar mad person (mahaukaci ) ya ɗauki key a bedside ya buɗe ɗakin tana zaune taji an buɗe ƙofar ɗakin ta tashi ta buɗe ƙofar har ya bar wajen "Azzalumi." ta faɗa da sauri ta shiga kitchen neman abunda zata ci.
Fahad ya fito wanka ya fesa turarukan shi ya tayar da sallah yayi shafa'i da wuri ya buɗe Qur'ani yayi tilawa ya daɗe yana yi ya rufe ya ɗauki ruwa ya sha maganin shi ya buɗe system ya fara aiki kiran Sa'ad ya shigo wayar shi ya share shi sai da yayi mishi 3missed calls sannnan ya daga, "sorry I missed your calls I'm busy doing bedroom acrobatics."
"what was that?" Fahad ya tambaya, "I mean I'm busy in the other room enjoying myself." wani tsaki Fahad ya ja "you are not serious."
"ko you are not serious ba, guy calm down and understand your wife wlh you will thank me later."
mtsw yayi tsaki "hold on pls I want sincere answer did she have any mental issue? "who?' Sa'ad ya tambaya, "that small clown." Sa'ad yayi dariya sosai yace "bata da komai lafiyar ta ƙalau." I don't think so, it's okay." ya kashe wayar, Sa'ad dariya ya ke yi Amira ta tambaye shi meya faru ya faɗa mata abinda Fahad yace, tace "wlh da za su fuskanci juna Umaimah is very sweet rabu da ita da hargitsi tana da tausayi ita ta ɗauko Tasiu, ita ta dauko Barira, tana da son yara, idan a girki ne kuwa bata da kasala, kuma duk son kuɗinta abunta be rufe mata ido ba Allah, tana sana'a sai ta kashe mana kuɗinta, bata da rowa sai dai ban ce ina so ba zata ja min rai dai amma zata bani I pray they understand each other."
Tun safe Ãdil yazo yana mata knocking ta buɗe mishi tace yayi sallah yace "No."
"What." uban shi faɗin rai ya iya da kafidiri amma ba za a koya mishi sallah ba ita Siyama tun bata kai shi ba ta fara koya mata sallah, tayi mishi Alwala ta nuna mishi yadda zai yi sallah, yana gamawa ta yi mishi wanka suka fito ta soya musu Dankali suka ci dayake weekends ne Mrs Lawrence bata zuwa da wuri tace wa Ãdil.
"I want you to check my phone in Papa's room but it should be a secret ok." ya gyaɗa mata kai.
Fahad ya gama duk abunda zai yi aka kira shi daga office yana sauri ya fita, ya manta be rufe kofar ba Ãdil har ya shiga ɗakin ya jawo drawer sai ga Fahad ya dawo yayi mantuwa, "what are you doing here." akwai motar shi a drawer ya ɗaga ta, "my car Papa."
"ok." ya wuce toilet, Ãdil ya buɗe drawer ƙasa sai ya ga wayar daya ke motar tana da girma sai ya ɗauki wayar ya ɗora motar akai Fahad ya fito yayi mishi kallon tsarguwa, Ãdil yace "nothing I promise." suka fito tare ya ƙulle ɗakin ya fita.
"yes" ya nunawa Umaimah tace "good job." ta karɓa wayar har ta mutu babu charge ta saka a charging ta kunna kamar jira ake ta kunna Sa'ad ya kira ta mai delivery zai kawo mata keke yanzu tana ta murna, ta duba posting ɗin ta mutane da dama sun yi following ɗin ta Mrs Lawrence tace tana da saƙo ta fita ta karɓa ta yi signing yinin ranar wunin haɗa keken ta tayi keken wuta ne mai kyau, tana ta murna ta fito da materials da Atamfofi zata fara ɗinka ready to wear, tayi dogayen riguna bubus.
Ya dawo a mugun gajiye wanka kawai yayi don ya riga ya yi sallah zuuuu zuuuu zuuuuu ya rinƙa jin sound shi baya son ƙara ko kaɗan shiyasa ya karɓe motar Ãdil ya saka a drawer, ya ja blanket still be daina jiba, ya sauko ya saka silifas ya fita zuuuu zuuuu zuuuuu......yaji inda sound ɗin yake fitowa ya murɗa ɗakin ya shiga ya ganta a kan keke kaya jibge a ƙasa tayi yanka duk pieces ɗin kyalle a ƙasa.
"and what was that? Ta yi kamar bata ji shi ba ya ƙara hasala, yace "I'm talking to you my friend." "toh ni me zan ce maka?"
"Get up." tayi mishi banza "I said get up." Ta wani tura baki gaba tace "ni idan dare yayi bana jin turanci." ta faɗa tana tsattsare shi da ido, babu tsoro wlh duk abunda zai faru sai dai ya faru.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣7️⃣
Ya kalle ta ran shi ya ƙara ɓaci, ya saka hannu ya yarfar da hannun ta a kan keken ya laluba ƙasa ya kwance shi, ta dafe hannun shi "ina zaka kai min keke na?" Ya ɗaga hannun shi da sauri ta rufe fuska ya ɗauke keken zai fita "ina zaka kai min?" ta biyo shi a baya tana sake riƙe hannun shi ya juyo a fusace cikin tsawa yace "don't try me if not you will regret it."
"ni ba na jin turanci da daddare, Allah ka bani keke na." ta faɗa da sangarta, ya kama hannunta ya matse ta saki ƙara ya yarfar da hannun ya shige ɗakin shi ya saka key kasan wardrobe ya saka keken ya dawo ya zauna a bakin gado ya dafe kai, wannan wacce masifa ce? da farko tana shakkar shi amma yanzu ya fuskanci rashin kunya ta ke son mishi, sai ya ji bugun ƙofa "ka ba ni keke na baƙin ciki kake min zan yi kuɗi, in sha Allahu sai na ci da kai, sai ka ci albarkaci na wlh." sai ta ƙara bugu "Allah ka na ji na ka rasa wa zaka yi wa hassada sai matarka, kana jina idan ma wani abu kake so sai na biya ka meye aciki?" Ta kara bugawa da ƙarfin gaske, ya tashi ya shiga toilet ya watsa ruwa bayan ya fito ya kalli agogo after 1am ya ji shiru ya ɗauka ta tafi sai ya ji tace "wlh Hassada dai babu kyau Uncle Sa'ad ya siya min ka ɗauke Allah zan fa yi Allah ya isa tsab zata bi ka, ni ina ruwana da kai neman na kaina na ke yi." har ta tafi ta dawo yaji footsteps ɗin ta ta ƙara bugawa "Mahassadi kawai."
Ya ji shiru ta tafi sai kawai abun ya ba shi dariya sosai yake dariya "wai matar shi zai yiwa hassada? Zata ci dashi. she is damn funny wai matarshi so she consider herself as his wife, wai ta yaya ma ta yi communicating da Sa'ad? ya jawo drawer wayam babu waya, "Ãdil." ya faɗa, bari gobe ya kira Sa'ad ɗin yayi switching light ya kwanta
Saboda ɓacin rai ta daɗe a zaune bacci ya kauracewa idanunta hawaye ya taru kamar zata yi kuka ta mayar "wlh ba zan kara kuka akan ka ba." sai da ta tattara kayan da ta ɗinka tana ta zancen zuci gobe zata kira Sa'ad ta faɗa mishi ya kwace keken wannan kurman ba zai manna mata hauka ba sai wajen 3 ta kwanta, daya ke a gajiye take tana kwanciya bacci ya dauke ta da ƙyar ta tashi sallar Asuba tana idarwa ta ƙara bingirewa ta koma bacci sai wajen 11 ta farka shi ma yunwa ce ta tashe ta, ta yi wanka ta fito falo gidan tsit babu motsin kowa ko Ãdil bata ji kwarabniyar shirya shi ba ta shiga kitchen ta yi toasting bread ta leƙa window babu motar shi, ba Mrs Lawrence ko bata zo ba? Amma ko'ina a gyare tana wannnan tunanin ta ji an buɗe ƙofa Mrs Lawrence ce ta shigo daga shopping take na kayan amfanin gida, su ka gaisa ta gama cin abinci kira ya shigo wayarta da sauri ta daga Sa'ad ne suka gaisa "me ya haɗa ki da sweetheart ɗin naki ya kira yana ta faɗa kin hana shi bacci."
"waye sweetheart? Wlh ku kamar ba twice ba sam opposite ɗin ka ne shi." Sa'ad ya yi dariya yace "with time zai canja kin fara canja shi ma."
"Ni kuma ta yaya?"
"da ai baya magana daughter."
"Hmmm yanzu ma baya." yi ta tari numfashin shi, "Akwai improvement sosai yau yayi kusan 15min yana min complain a kan ki all thanks to you ba zan ɓoye miki ba naji daɗi is part of his therapy." Umaimah saita zama confused tace "wani abu ke damun shi?"
"Eh yana da OCD."
"haba no wonder shiyasa tsabtar shi ta yi yawa, Ashe lalura ce dashi." Sa'ad yace "karki damu za a kawo miki wani keken, amma Please promise me sai baya gida zaki yi ɗinki." tayi ihun murna tace "daga Uncle Ismah sai kai thank you." suka ajiye wayar.
Yau Ramla ta yi mata Alkawarin zuwa wajenta tun safe bayan fitar Fahad take ƙoƙarin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 27