Share this page
ka ba, ka yi hakuri nan da 7 days sai mu wuce." Da sauri yace "7days is far Dr." Ok 5days. Yace ba zai iya ba har zasu tashi wayar shi tayi ringing ya ɗaga sun daɗe suna magana ya kashe ya kalli Dr Huzaifa yace "ko dai addu'a ka yi min ta karɓu? ana buƙatar takardar shaidar mallakar mall ɗina a SAUDIA da takardar tax da nake biya duk shekara, hukumar SAUDIA tana buƙata su dole naje." Dole sai dai inya dawo sai su wuce zai yi Umrah ma ya godewa Allah sai ya dawo su wuce Nigeria kawai. Dr Huzaifa yace Masha Allah hakan yayi suka tafi wajen Ummi. Ya Rabb! Ya Rabb!! Ya Rabb!!! Ummi ta faɗa tunda aka yi mata bayanin abinda ke faruwa take ta kuka sai ta kalli hoton Umaima sai ta kalli Tahir "inna ha ibnatuk (she is your daughter)." Alhamdulillah hamdan kaseeran mubarakaan feek. Yaseer yake ta maimaitawa. Ummi ta daga hannu tana addu'a sai ta shafa ta shafawa Tahir ta shafawa Dr Huzaifa ta shafawa Yaseer, ta kalli hoton Umaimah ta fashe da kuka, Tahir dai zuciyar shi buɗewa take ya rasa a wanne yana yi yake Yaseer ya kira matar shi ya faɗa mata Khala ta karɓi wayar tana murna tayiwa Tahir murna suka ce daga nan Nijeriya zasu wuce har dare suna tare. Labarin ya bazu haka akayi ta kiransu a waya daga Lebanon ana muru murna. ***** Fahad sun sauka ana ta ruwa a Lagos airport suna zaune a waiting lounge ya kira Sa'ad yana daga wa yace "Guy har kun iso? Nima gani nan zuwa sako zan karɓa na taho ya Amal ma mun yi waya tana airport din jirgi ɗaya zamu hau." Fahad yace "ok." Suka yi sallama yana ajiye wayar Amal ta hange shi ta ƙaraso tana dariya tace "ɗazu Sa'ad yace min kana hanya." "yes". Yanzu kuka sauka? "yeah ya family? Fahad ya tambaye ta, kawai sai ta tsaya tana kallon shi, wai yau Dattijo ne yake tambayar ta ya family, ita idan tana mishi magana bata saka ran zai amsa, tace Alhamdulillah." ya kara kashe ta da mamaki yace "the waterfall started early this year?" Aunty Amal ta sake zare ido, wai Dattijo ne yake yi mata hira? tace "ai Lagos weather ɗin su daban take da arewa normally nan damina tana faɗuwa da wuri." suna haka Sa'ad ya nufo inda suke Amal ta miƙa mishi hannu suka gaisa. Guy ya hanya? ya dawo kusa da shi yace "fine." Adil ya farka daga baccin da yake, Sa'ad ya dauke shi, "Papi are we in Nigeria?" Adil ya tambayi Sa'ad, yace "yes Didi." Where is Maamah? Sa'ad yace "She's in kano? And where are we Papi? Lagos but mun kusa zuwa wajen Maamah. Adil yayi dariyar jin daɗi "I can't wait." Amal tace baka gaishe ni ba. yace "ina yini." Fahad yayi murmushin jin daɗin Adil yayi Hausa, "Ah lallai Umaimah ta yi kokari." Amal ta faɗa, Fahad yace sosai ma. Ita dai Amal mamaki ne ya cika ta kamar dai an canja Dattijo, ikon Allah suna zaune aka yi announcing zasu yi boarding suka tashi. ..........Su Daddy tun 2 suna jiran su Khadija a airport sai wajen 4 suka sauka duk a jigace suke sun yi zuru zuru dan Umaima a jirgi abunka da mai Yaron ciki sau biyu tana Amai amma daya ke ba laulayi take yi ba babu wanda ya gane ciki ne da ita, suna fitowa motocin su Baban sama da Daddy aka shisshiga Khadija kuwa gaba-daya a jikin Munnirah take haka aka sakata a Mota Umaimah na ganin Uncle Ismah ta rungume shi ta shiga motar shi aka nufi galadanci, gida ya cika damƙam da mutane ana jiran su, sai da aka yi mishi wanka aka kira gwaggo da Khadijah su yi sallama za a kai shi makwancin shi, Munnirah ce ta riƙo Khadijah suka shiga ta durƙushe a gaban gawar gwaggo tana hawaye tana na yafe maka Ahmad Allah yasa ka je a sa'a Khadijah ta leƙa fuskar shi kamar ka kira shi ya amsa tayi mishi addu'a wani jiri jiri ne yake son daukanta aka dauke shi sai sannan ta fashe da kuka gwaggo ta rungumo ta Munnirah ta cire mata hijabi ganin numfashin ta yana sama da ƙasa, sai da aka yi La'asar aka yi mishi sallah yayi mutane sosai yaran shi su suka saka shi a kabari aka dawo ana karɓar gaisuwa har an kafa canopy cikin masu zuwa gaisuwar har da Alhaji Isah Daddy ya tura mishi text ɗin rasuwar. Allah ya jikan mu da iyayen mu gaba daya. Dare yayi su Umma zasu tafi gida an bar Munnirah ta zauna da Khadija sai an yi bakwai ta dawo gida Umaima ta biyo su Mami, gaba-dayan su suka dunguma zasu tafi Aliyu ma daga office nan ya wuto suna parking a motar su kafin Baba Idi ya rufe gate motar Malam Musa Direban Baba ta shigo da su Fahad, basu kawo da mutane a motar ba suka shiga ciki, Umaimah tace "wash wlh nagaji." Uncle Ismah ya mika mata ruwa "gashi ki kora mai sanyi." ta karɓa kenan ta kafa baki ta ji sallamar shi ta kware, "sannu." Daddy ya faɗa. A'a yanzu kuke tafe, Umma ta faɗa, da gudu Adil ya nufe ta ta buɗe mishi hannu, "Maamah I'm mad at you, you left me." yayi rau rau da ido zaiyi kuka tace "I'm sorry Didi." Aka fara da gaisawa Fahad kallon ta kawai yake yi sai ya ga ta ƙara haske ya kasa zama ya nade hannayen shi yana ƙare mata kallo straight kamar babu kowa a wajen sai ita, ji yake kamar yaje yayi hugging ɗin ta kozai samu sauƙin abinda yake ji a kanta. Zauna mana Dattijo. Baba ya faɗa, "duk ina kuka hadu yan UK da Lagos da pothacourt? ya Amal tace a airport muka hadu. Masha Allah. Ya muka ji da haƙuri? Umma tace "Alhamdulillah tana kallon Umaimah tace "ke meyasa kike haka? Baki gan su bane? ki tashi ki samar musu da abinci kinsan da zuwan su baki tanadi komai ba?" "Siyama naga dai tare muka shigo gidan dake dan Allah." ta turo baki gaba, kawai Fahad ya shagala da kallon ta yana dariyar sunan data kira Umma da shi, "kyale ta Uwata kema daga tafiya kike babu bako a cikin su, ke ma daga tafiya kika dawo." Mami tace "na saka Deborah ta ɗora girki bari a kawo musu." Sa'ad yace sai mun yi sallah tukun. Adil yana kan cinyarta yana mata rada a kunne tana dariya, daɗi ya ishi Baba, yace "me ake faɗa ne? Daddy yace "sirri ne na uwa da danta." Uncle Ismah yace ina ta Didi ma yaki Kulani." Aliyu ya kalli Umaimah fuskarshi a haɗe yace "ke tashi ki sama musu wani abu." ta tashi tana gunguni Fahad ya bita da kallo, Daddy yayi magana baiji ba sai da Sa'ad ya zungure shi, sannan ya shafa kai, Daddy yace "na ji daɗin zuwan ka Dattijo dama akwai contract da federal govt ta bani na tituna wannan Rasuwar ta saka ba zan je Abujan nan ba tunda field ɗinka ne ka yi supervising aikin zan zauna har ayi bakwai." Fahad kamar mutum mutumi haka yake kallon Daddy da kyar ya bude baƙi yace "ok Sir." wani abu ya tsaya mishi a makoshi. Shida yazo wajen matar shi a turashi wani aiki kuma. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣9️⃣ Tinda Umaimah ta ajiye masa abincin ta haye sama ya kasa ci sai juya abincin yake Baba har ya kula yace "ya dai Dattijo? yayi murmushi ya fara cin abincin. ina uwata? Daddy ya tambaya, Umma tace "tana ɗaki ita da Adil suna kallo, kamar mutane goma ne a ɗakin sun yi kaca kaca dashi." Isma'il ya ce "ai banbancin ta da Adil din kadan ne." "Au kai ma ka faɗa? toh bari na yi shiru tunda kai ka faɗa." Sa'ad ya faɗa yana kallon Uncle Ismah. Amal tace "Mami Yaya Surayya wai zasu zo Bakwai. "Allah ya kai mu." "yauwa sai su taho da Amira. Sa'ad ya fada, ana haka Ibrahim yayi sallama ya shigo aka gaisa Daddy ya ce "meyasa kake son tafiyar dare ne? ya shafa keya, yace "wlh Daddy aiki ne ya riƙe ni." Shikenan Allah ya cigaba da tsarewa. Adil ya sauko daga sama da gudu da waya a hannun shi ya bawa Umma ta karɓa Munnirah ce ta fada mata a haɗawa Khadija kaya ko Ismael ne ya kawo mata. Adil yana tsaye ta gama ta miƙa mishi wayar sai ya tafi wajen Fahad yace "Papa what are you eating? Sa'ad ya ja hannun shi ya fara bashi a baki ya ajiye wayar Fahad ya ɗauka hotonta ne a screen ɗin ya saka number shi yayi mata saving ya ajiye suka cigaba da hira hankalin shi yana wajanta, Ãdil ya koma wajen ta, Daddy yace "gobe in Allah ya kaimu sai ka wuce da wuri ko? Ya amsa da "ok sir." har ya mike Umma tace "ka hau sama mana tana ciki na san goben da kyar ma ta tashi kafin ka wuce." Wani dadi ya mamaye ran shi dama kaɗan yake jira, Amal tana gulmar shi a ranta ya mike kamar ba Fahad ba ya fara hawa steps muryar Ãdil ce ta fallasa ɗakin da suke ciki ya bude ya shiga. Adil ya danne ruwancikin ta yana counting 1,23 yes I won wai wrestling suke kallo a tv shi ne suma su ke yi duk sun watso da pillows ɗin kan gadon har sun saka kayan bacci, gajeriyar rigar bacci ta saka lilac iya gwuiwa sai daya kare musu kallo basu ma san ya shigo ba ya shagala da kallon su tana ta dariya "Didi dagani Allah ka sakar min nauyi." ya kara danne ta yana dariya suka hada ido dashi yana tsaye a jikin ƙofa ya harɗe hannayen shi a kirji, ta daga Adil da sauri ta tashi tana gyara wuyan rigarta, menene? Ta faɗa tana turo baki gaba, yayi wa Adil alamar ya zo da hannu ya ƙaraso wajen shi ko me ya rada mishi ya fita waje da gudu. Yana fita yayi maza ya saka key ya zare ya saka a aljihun shi kamar ya san me take son yi ya karasa ya kulle toilet ya zare key ɗin ya karasa wajenta tana tsaye ta juya masa baya, ta bayan ta ya rungumeta gaba ɗaya ya saka ta acikin jikin shi ya zagaye ta da hannayen shi yaɗan sunkuyo ya zuro kanshi ta wuyan ta yana leƙa fuskarta data sake haɗe wa, "ka sake ni kar Umma ta shigo." Ta faɗa tana kokarin ƙwace jikin ta, ya sake shigar da ita jikin shi yana sauke ajiyar zuciya, a hankali daidai setin kunnen ta yace "Zarahhhh Please ki tausaya min mana." Umaimah batasan ta ɗora hannunta akan kunnen taba da sauri ta sosa saboda yadda maganar ta sauka cikin kunnen ta saida tsikar jikinta ta tashi, take taji wani irin sanyi sanyi na shigar ta, hannun da take sosa kunnen yabi da firgitattun idanun shi da ganinta ya sake juya su Muahhhhhh!!!!.....ya manna mata kiss mai ƙara akan hannun yana shaƙar kanshin humarar dake tashi a wuyanta, da sauri ta matse hannun shi dake kan cikin ta tana sauke ajiyar zuciya a jejjere, wani irin yanayi take ji ajikin ta mai kama da kewa haka kawai taji tana son sake shigewa jikin shi, a hankali ya juyo da ita yana ƙare wa idanun ta kallo data zuba masa su sai kuma ta lumshe su, kiss ya manna masu, "i miss you like crazy Babe." Surprisedly yaji ta rungume shi tana sauke ajiyar zuciya, wani daɗi yaji ya kama shi, tayi missing ɗin shi ke nan? Wow yayi wani cool smiling yana rubbing bayan ta softly. Haka kawai taji wani kuka ya zo mata wuya ta zame jikin ta a hankali zata juya masa baya dan bata so tayi kuka a gaban shi ya hanata juyawa ta hanyar riƙe hannayen ta ya zuba mata duka idanunsa yana observing yana yin ta, hawayen da take riƙe wa ne suka zubo muryarta na rawa tace "me ka zo ka cemin kuma? Ni meya haɗa ni dakai? Ba gidan ka kake so na bari ba kuma na bar maka to ina ruwan ka dani kuma?" Ta ƙarasa maganar tana murza ido kamar Baby, yadda tayi maganar ba ƙaramin melting heart ɗin Fahad tayi ba, har cikin zuciyar shi yake jin zafin zubar hawayen ta, calmly yayi kneeling a gaban ta yana riƙe da hannayen ta yana kallon cikin idon ta yace "Please Zahra I'm deeply sorry for my mistakes you hold a special place in my heart, and I will love to spend the rest of my life making it up to you, Before you left I had already terminated our contract please forgive me and consider a future together." Taji wani iri daya durƙusa mata amma data tuna kuɗi fa ya bata dansu rabu saita juyar da kanta taki magana, ya mike yana ƙoƙarin su haɗa ido ta ƙi juyo da fuskantar ta, yace "shikenan mun shirya ko, bari na faɗawa Daddy gobe zamu koma gidan mu ko?" Umaimah bata taɓa jin yayi magana mai tsayi da Hausa ba sai yau ta bude baki a tunzure tace "sai dai ka wuce kai ɗaya." dama wayo yayi mata tayi magana yayi amfani da damar ya hade bakin su ya fara bata zazzzafan French kiss dayake rigar jikinta silk ce ya zame ta yayi jifa da ita, ai Fahad nayin arba da asalin jikin ta kawai sai ya rikice ya manta inda suke tun tana protest har ta haƙura ta sakar masa jiki ya danganta ta da gado, wani irin nishi yake yi kamar wanda yayi gudu, Umaimah jikin ta ya saki itama fa tana enjoying sosai jikinta yayi missing ɗin shi, bata gane abun babba bane sai da ta tsince ta a ƙasan shi yayi mata rumfa da faffadan kirjin shi sarrafa ta kawai yake yi son ran shi, ta tuna inda suke tana kokarin tashi ya sakar mata nauyin shi, Fahad lokacin da ya jisa a jikin ta ya rasa inda zai saka kanshi ya rasa duniyar da yake ciki ya fara ƙara da surutai Umaima ta hade baƙin su kar a ji su, ya kara rikicewa kamar ta ƙara mishi kaimi wani daɗi da ya jishi har cikin kanshi baisan lokacin da ya zare bakin shi zai yi ihu ba ta toshe bakin shi da sauri tana shafa kanshi, abunka da mai karamin ciki abun yayi musu daɗi bama yashi zam zam ya sake jinta ya ƙara rungume ta kamar zai mayarta ciki yana shafa duk inda hannun shi ya kai jikinta, wata nustuwa na lulluɓe shi, bugun ƙofar dakin da Adil yake yi shi yasa shi miƙewa a hankali ya nemin kayan shi yasa. "Maamah open the door we are back." da sauri ta tashi jikinta duk yayi tsami ya ɗauke ta ya bude toilet ya sata sannan yazo ya bude kofar Adil ya shigo shi kuma ya fita da sauri yana addu'ar Allah yasa babu kowa a ƙasa, ta ƙofar kitchen yabi ya fice. Tana fitowa daga toilet kanta na digar ruwa jikinta da towel iya cinya Umma ta shigo dakin da kayan guga tana jerawa a wardrobe kan gadon a yamutse, bedsheets din ya cukwukuye ta kalli gadon suka hada ido da Umma sai cewa tayi "ni wlh Siyama babu abunda aka yi." kawai sai ta fashe mata da kuka Umma bata kalle ta ba ta fita daga ɗakin tana girgiza kai, tace "Allah dai ya kawo miki hankali." Abun ya kara bata mata rai wlh ya cuce ta, kuka take yi bil hakki, ta ji haushin kanta ita ya aka yi ma ta biye masa haka ta faru, sai da tayi mai isarta ta tashi ta shirya ta saka kayan bacci ta gyara gadon anan ta ga agogon shi ya manta ta saka mishi a handbag dinta ta dauko Adil da yayi bacci a ƙasa ta mayar da shi kan gado. .............Kafin Tahir ya taho ya kira Shahir mai yi mishi hidima yace masa yana hanya, yana sauka direct bayan ya huta a gida ya tafi ya sauke Umara zuciyar shi fes da farin ciki mara misaltuwa ya daɗe ya na addu'a yayi wa Khadija da Fatima da Ummin shi Yaseer da Dr Huzaifa, yayi murmushi ya godewa Allah in sha Allah Khadijah tashi ce ya dade yana addu'a ya dawo gida yayi wanka ya huta yana farin ciki ya dauko wayar shi bari ya kira Ismael (Fahad ) yace zai zo musu amma yanzu ba zai samu zuwa ba sai ya dawo daga Nijeriya, ya kira layikan shi na UK basa tafiya ya kira na Nigeria tana ringing amma ba a daga ba, ya kara gwada kiran Khadijah har yanzu wayar ta a kashe, ya Rabb Allah yasa ta kunna tun jiya baya samun isasshen bacci tunda abun ya faru kullum a cikin tunani ya ke kamar almara. **** Indai yana kano ɗakin Aliyu ya saba sauka duk da suna da chalet a part din Daddy amma anan ya sauka boxes din shi yana dakin ya shiga toilet yayi wanka yanajin wani farin ciki na mamaye zuciyar shi he feels good. Amma ya fahimci zata ɓata mishi lokaci be so zuwa Abujar nan ba amma so yake yana dawowa su wuce, yayi murmushi zuciyar shi sakayau yake jinta, idan zata ɓata mishi lokaci Baba zai samu da maganar ayi mishi faɗa, he is ready ya bada haƙuri kawai awuce wajen, amma shi tsoron shi Daddy yaji maganar dan yasan ba za su kwashe ta dadi ba tun yana toilet ya ji ringing ɗin wayar shi, ya fito ya canja bedsheets yayi sallar isha da shafa'i da witiri yayi addu'ar Allah ya dora shi a kanta ya lura bata sauko daga fushin ba ya jawo wayar shi Muhammad Fadoul (Tahir) ne ya kira shi ya danna mishi kira back ya dauka. "dana." Suka gaisa yace na maka Alkawarin zuwa UK uzuri ya taso min ashe baka UK ma kana Nigeria? "Eh I'm in Nigeria I will be in Abuja tomorrow." Masha Allah nima next week zan zo Kano zamu haɗu insha Allah." Fahad yace "am." sai kuma yayi shiru yana tunani, Tahir yace "fadi mana ɗana feel free to talk to me." "pls ina so kayi min addu'a a harami we had misunderstanding with my wife pls pray for me." Fahad ya faɗa Muryar shi a sanyaye, "in sha Allahu zan maka addu'a la waqu illah min ind Allah (no harm shall befall except from Allah), barak Allahu fikuma (may Allah bless you both), send me her number I will like to call her." Fahad sosai ya ji daɗi yayi mishi godiya suka ajiye wayar ya tura mishi number Umaima. Sa'ad ya shigo ɗakin da sallama yana kallon shi "Guy me ya faru ne naga sai murmushi ka ke yi? Fahad ya kalle sa yace "Yes I am in love with my wife." ya faɗa unexpected, da ƙarfi Sa'ad yace "Allahu Akbar gaskiya daughter ta yi kokari yau kai ne kake magana haka? Me daughter ta yi maka ne?" Fahad ya shafa kai ya tuno da moment din su na ɗazu, sai murmushi yake yi kamar hauka sabon kamu. "this is serious." Sa'ad ya faɗa suka hada ido suka tintsire da dariya. Da sassafe ya gama shirin tafiya Abuja su Daddy ne kadai a falo ya gaishe su Umma data fito daga kitchen suka gaisa zai wuce ta ce ka tsaya ka karya yace jirgin sassafe ne zai wuce kawai tace to ka shiga ku yi sallama ta tashi. kamar yace a'a ya kalli su Daddy hankalin su baya kan shi ya hau sama da sauri ya buɗe dakin tana kan sallaya a kwance ga dukkan alama bacci kwashe ta yayi bata shirya ba, ya sunkuya yayi kissing lips dinta kamshin turaren shi ne ya tashe ta a zabur ta tashi "wai meye haka?" "na zo muyi sallama zan tafi " ta harare shi da idanunta da sukayi laushi saboda baccin da tayi"oh my God Zarahhhh I like it." wani haushi ya kara kama ta, so yake ya mayar da ita mahaukaciya ta tuno yarda suka yi da Umma jiya ta sake haɗa rai tace "wlh ka fita kaga jiya Siyama ta gane." "me ta gane? Ya kura mata ido, ta turo baki "ni wlh ka bani divorce paper ɗina dama ba sona kake yi ba." I will never do that Zarah not in my dreams. ya fara matsowa "wlh zan maka ihu inka taɓa ni." "go ahead pls Daddy sai yace nayi zama na." ta juya zata shige toilet step ɗaya tayi ya kamo ta ya fara bata zazzzafan kisses ya lalube duk inda yake so a jikin ta, wayar shi ta yi ƙara ya cika ta yana sauke ajiyar zuciya, ya kalle ta yace "take care of yourself for me please Daddy ya aike ni Abuja." ya ajiye mata ATM card ɗin shi "if you need something."ya juya ya fita. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 5️⃣0️⃣ Yana fita ta dauki ATM card din ta ajiye tasan yarda zata yi dashi Sa'ad zata bawa tace yace a bashi ita ma Allah ya rufa mata asiri me zatayi da kuɗin shi, haushin kanta take ji meya sa ta biye masa? Ya mayarda ita bata san kanta ba duk lokacin daya yi niyya ya zo yayi mata san ranshi, wayar ta ce tayi ringing ta dauko number SAUDIA ce bata daga ba ta fara tunanin waye aka sake kira ta daga. "Assalamu alaikum Fatima yata". Tahir ya faɗa a sanyaye, ok ta gane mutumin, "wa alaikumussalam Abbi." suka gaisa Tahir gaban shi ya fadi muryar Khadija yake ji duk lokacin da yayi waya da ita, jikin shi a sanyaye yace "yata dan Allah ina nemawa Isma'il (Fahad) afuwa kiyi haƙuri kome yayi miki shi aure ɗan hakuri ne." Umaimah a ranta tace lallai mutumin nan wato karar ta yakai? Ita bata faɗawa kowa ba shi ne zai ɓata mata suna a wajen mutumin da take ganin mutumcin shi, amma zata bashi mamaki. "kina ji na?" Ya faɗa da muryar lallashi, "eh Abbi." "Yawwa Ummina zaman aure ibada ne kin ji yarinyar kirki kiyi hakuri." Bakin ta a tunzure tace "Abbi shi ne fah bashi da gaskiya." "Ni ba neman mai gaskiya nake yi ba haƙuri kawai nake baki." network ya yanke tana ta kokarin kiran shi taƙi shiga, wlh ita saita faɗa mishi komai, gani ake wani mutumin kirki ne shi, tana jin Nauyin mutumin nan ya haɗa ta dashi Allah ne kadai ya san me ya faɗa mishi, Allah ya dawo dashi lafiya, wallahi ba zata bi shi ba dole ya tonawa kan shi asiri tunda abin nashi haka ne, bari ayi uku ta faɗawa Uncle Ismah ya faɗa mata waye mai laifi a cikin su. Haka ta yi ta gwada sake kiran shi network yaki bata hadin kai

Chapter 20 of 27