Share this page
Tace da sauƙi, "toh Alhamdulillah ina sister khadija? Umaima tace yau tana gida itama bata jin daɗin. Sa'ad yace Subhanallah zan kira ta, Please take care of yourself zan kira ki zuwa gobe zamu yi magana and please tunda ba wanda ya ji zancen nan ina nemawa ɗan uwana Alfarmar kar ki faɗawa kowa please zamu gyara komai ba tare da sun sani ba Please, za dai muyi maganar." suka yi sallama ta harari wayar dama me zata ce idan aka ga ta koma Kano dole a nemi ba'asi iyakaci tace a neme shi yazo yayi bayani, Adil ya faɗo mata arai idan aka raba auren nan wlh sai ta karɓi Adil ya je ya karata da mugun halin shi, ta koma ta zauna a wasu kujeru da aka tanada domin zama bata daɗe da zama ba taga Dr Huzaifa ya nufo ta da file a hannun shi tayi kicin kicin da fuska ta sha kunu. "Assalam alaykum." yayi mata sallama ta kara hada rai da kyar ta amsa sallamar, yace "I forgot this." ya ɗaga mata file ɗin hannun shi ya zauna a kujerar dake kusa da ita har zata tashi yace "Please seat I'm sorry for disturbing you." ya fada ta kalle shi ta dauke kai ya nuna mata wajen da ta tashi "Please seat." sai taji ba za ta iya mishi gardama ba, "i won't take much of your time Please what is your name? Umaima kamar bazata amsa shi ba tace Fatima, "Fatima." ya maimaita sunan yace "Fatima you have a striking resemblance with someone I know, you two are like twins." "Da gaske ta?" faɗa with so much excitement, be fahimce me tace ba ya dai yi mata murmushi, tace "are you serious? "sure." ya faɗa, OK shiyasa yake ta kallon ta ke nan, "i will like to see the person didn't you her the person's picture." sai yayi wani tunani ya ce "I don't have her picture." ya tambaye ta Gwaggo wace ce a wajenta sai cewa tayi Mamanta ce he is confused, yace "Fatima where are you from?" yasan dai patient ɗin su is from Nigeria tace "I'm from Nigeria" How are you related to our patient? tace "he is my father." Ta fada a ranta mijin Amminta is like a father to her mana, ya ƙara shiga confusion yace "Fatima Please I need your number I want to introduce you to someone please." Umaimah bata da saurin sabo amma haka kawai taji tana son ganin me kama da ita ɗin nan, sau ɗaya aka faɗa mata an ga mai kama da ita a airport Amira ta gan shi, bari ta tambaya mace ce ko namiji ta tambaye shi yace mace ce sai jikinta yayi sanyi ta karanta mishi duka numbers din ta har na Nigeria tace amma wayar ta a kashe ta ke ya bata nashi ta rubuta a wayar Amminta zata yi saving a wayarta suka yi sallama yana tafiya yana waiwayo wa ya kalle ta, gaskiya wannan abun mamaki ne Mamanta is old enough to be her grandmother kuma basa kama Sam, Amma akwai wata da take kula da patient ɗin kwana biyu bata nan be san sunanta ba da a ce ita ce Khadijan Tahir tabbas zai ce Fatima yar shi ce amma Tahir be taɓa faɗa mishi sun rabu da ciki ba don kullum maganar shi rashin jin daɗin shi da suka rabu babu rabo a tsakanin su wajen Tahir za shi amma kawai sabida tunani sai tsintar kan shi yayi a dakin Ummi tana zaune Khaala tana bata tea gaban shi ya faɗi suka gaisa da Ummi yayi mata ya jiki ya nemi waje ya zauna Khala tace Abbu yana neman shi ya kalli Ummi ya ɗauke kai, yace zai kira shi, kaai dole yayi wani abu yayi musu sallama ya fita, zuciyar shi tace masa DNA is the only option. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣4️⃣ Dr huzaifa Yana office tunani ya mishi yawa shi yanzu wacce hanya zai yi amfani da ita yayi mata DNA test without her consent and is against his profession laifi ne babba amma dole haka zai yi risking duk abunda ya faru Allah ya kiyaye Tahir ba matsala zai samu abunda yake so sai dai shi ma ya damu ayi discharging ɗin shi dole ya kara rike shi, cewa zai yi akwai test ɗin da zai ƙara mishi running zai samu biyan buƙata, amma dole ayi tests infact is a most abunda zai bashi matsala na Fatima yaya zai samu abunda yake so without her consent dole yana needing blood samples, da saliva and her hair kafin ayi test ɗin wayar shi tayi kara Dr Vikram ne yace "meet me at no 122." ɗakin su Umaima da sauri ya ajiye wayar ya tafi yana shiga ya tarar da su a tsaye akan Ahmad an jona mishi machine din life support, Dr Vikram ya saka Huzaifa ya duba mishi wasu abubuwa yana rubutawa a file ɗin shi Gwaggo da yaran shi sai kuka suke yi Baban Ahmad yana bata baki Dr Vikram ya fita ya bar Dr Huzaifa yana ƙarasa shigar da information a file ɗin, Umaima tana toilet tana kakarin amai bata jin daɗi tunda ta tashi yau wani iri take jin ta har kamar jiri take ji ko lokacin da aka jona machine ɗin nan kan ta juyawa yake, ta wanke fuskar ta ta lallabo ta fito tana fitowa kamar abun sihiri ta yanke jiki zata faɗi Dr Huzaifa yayi sauri ya riƙo ta ai sai Gwaggo ta dena kuka tayi kanta tana cewa "na shiga uku me ya same ta?" Abban Ahmad ma ya rikice yayi kan Umaima yana tambayar Dr Huzaifa me ya faru, yace su kwantar da hankalin su babu komai yayi waya aka taho da gadon mara sa lafiya aka ɗora ta, "suma tayi." Dr Huzaifa ya faɗawa su Gwaggo Yanzu zata farfaɗo, a ran shi kuwa hamdala yake yi aikin shi zai zo da sauki Gwaggo ta tayar da hankalin ta Dr Huzaifa ya ce babu komai firgita ce kawai da stress nan da anjima zata warware, Gwaggo tace "kaai dole ta damu yau ma Khadija ita tace kar ta zo tana can tana zullumi yanzu ga yar ta a kwance bari ta kira su sutaho tunda ga abunda ya faru. Yaseer ne a wajen Tahir suna ta tattauna barnar da ya je ya tarar da yarda abubuwan suka kasance a Lebanon, jiya yazo don har Khala ta koma suna hirar Dr Huzaifa ya shigo suka gaisa yace akwai allurar da zai yi mishi Tahir yace shi fah ya warke Dr Huzaifa yace yayi haƙuri zata saka ya samu hutu da nutsuwar zuciya, ba yarda zai yi yaso ma yau ya je wajen Ummi duk da dai suna waya kuma Alhamdulillah ko a muryarta ya ji alamun sauki, ya kwanta Dr Huzaifa yayi mishi allurar ba a dauki minti 5 ba yayi bacci Dr huzaifa ya kalli Yaseer yace "Akeey muje office ɗina ka huta ba a son disturbance." Suka fito ya rufe mishi kofa zai yi kamar 15mins da fita ya dawo ya juyar da camerar ɗakin ya ɗauki blood sample ɗin Tahir, gashin kai da saliva sample da kan shi ya ɗauka ya fita ya koma ɗakin Umaima bacci take yi ba wani abu zai bata ba kawai stress ne sai shock idan ta farka daga bacci condition ɗinta zai yi stable ya juya CCTV din dakin yayi mata duk abunda zai yi mata tana bacci ya fito kenan Gwaggo da su Munnirah suka kawo kai. "kun gan shi Likitan me kirki." Gwaggo ta faɗa tana nuna Dr Huzaifa, "thank you soo much we really appreciate." Munnirah ta faɗa, Baba Dr ya miƙa mishi hannu suka gaisa dama wani aiki ya zo na sati ɗaya shiyasa ya taho da Munnirah ta debe wa Khadija kewa, "thank you Dr." Khadija ta faɗa da dasashiyar muryar ta "don't mind." ya fada yana Ƙare musu kallo Baba Dr yace "meyasa me ta? Yace stress ne kawai sai shock din ganin machine ta samu panic attack amma tana tashi zata warware Baba Dr yayi mishi godiya ya fita, yana tunanin duk da Tahir auren kuruciya suka yi da Khadija tabbas wadannan biyun za su iya haifar Fatima ya tafi lab ya kira miss Jane ya bata yace "is DNA test pls treat it with urgency and I need accurate result pls." ya fito yana tunani jiya da kyar ya rintsa ya kasa zama waje ɗaya ya hau fourth floor ya kalli Ummi ya dawo down floor ya kalli Umaima ya so ɗaukan hoton Ummi toh Yaseer yana nan, kamar tasu ta ɓaci kawai abunda ya bambanta su Fatima akwai ƙuruciya kuma she is chubby, Ummi kuma fuskar ta ta manyan ta sannan ta rame sosai, acikin yaran Ummi Tahir yafi kama da ita sosai saboda haka Fatima ma suna kama da Tahir sosai, kai shi abun ya daure mishi kai Allah ya kai mu gobe test din zai fito anjima dole zai koma he needs to confirm something tace Ahmad patient din su shi ne Babanta and Tahir yayi aure a Nigeria anya dayar da suka Shigo ba ita ce Maman Fatima ba kuwa? shi sai yanzu ya tuno yarda Tahir yake fasalta mishi Khadijan shi kusan haka dayar take a lokacin daya kwanta accident a Lebanon kusan komai na labarin Khadija ya sani ya haddace labarin ta tsab a kwakwalwar shi anya Khadija bata haihu ba? Something is fishy gaskiya Allah ya kaimu gobe. ***** UK Dr ya ƙara rubuta mishi wasu drugs ɗin ya fito ya nufi pharmacy ya siya yaushe rabon shi da shan maganin ma har anti depressant ɗin daya ke sha wlh ya manta, ya shiga mota ya dawo gida Mrs Lawrence ce kadai a gidan Adil yana makaranta ya buɗe ɗakinta ya shiga har yanzu yana ƙamshin humrarta, tinda ta tafi ya mayar da dakinta wajen zaman shi, jiya da kyar ya lallaɓa Adil yayi ta mishi rigimar neman ta, kan shi ya Sara yunwa yake ji ya kira Mrs Lawrence ta dafa mishi spaghetti tace stew ɗin ta ƙare ya dafe kai, ashe don be samu irin abincin daya ke so bane shi yasa baya cin abinci sosai, dan yanzu sosai su ke ci da Adil, har mamakin cin abincin Adil yake yi, jiya daya daga shi sosai ya ƙara nauyi. "should I make something for you?" Mrs Lawrence ta faɗa, yace ta bari ba lalle tayi mishi yarda yake so ba yace ta soya mishi meapie ko samosa tace shi ne na ƙarshe data soyawa Adil ya tafi dashi makaranta, a ranshi yace yau akwai rigima kenan, yana zaune wayar shi tayi ringing Sa'ad ne suka gaisa yace mishi next steps ɗin dama so yake su yi magana da Umaimah in sha Allahu komai zai yi dai dai, ya kira bata da lafiya ne amma sun fara magana wajen gobe zai kira ta, jin bata da lafiya Fahad yaji hankalin shi ya tashi "what is wrong with her?" ya tambaya da sauri, "ban tambaye ta ba." "but you should have ask her mana." Sa'ad yayi dariya ana gabas yana yamma, calmly yaji Fahad na cewa, "yeah she is annoying yet so sweet, but I miss her and I always pray for her please Ad I need your assistance help me talk to her please." tausayin shi ya kara kama Sa'ad yace mishi zan kira gobe in sha Allahu, but before then call Khadija ka yi mata ya mai jiki." Haka ne fah shi wlh kwata kwata he is not thinking straight, Sa'ad yace "and wayar khadijan ma tana hannu ta." Zan kira. ya faɗa da excitement, "Ad ina tunanin kawai zamu taho Nigeria na rigata zuwa ina tsoron abunda ta faɗa a letter tace zata yi min sharri." Fahad ya ƙara bashi tausayi, ya bashi dariya duk a lokaci daya, yau shi ne da doguwar magana da hausa haka, yace 'shikenan kayi shirin tahowa sai na biyo ka muje." "thankyou Ad I really appreciate." suna ajiye wayar Adil ya shigo da uniform a jikin shi "Papa I'm Hungry." Ya Allah save me ya faɗa a ran shi yace ya je Mrs Lawrence ta bashi abinci, before then ya zo su yi wanka ya shirya shi ya wanke toilet ya gama ya koma ɗakin yayi mishi tas ya canja bedsheets din ɗakin Umaima dan daga yau har su tafi Nigeria zai dawo kwana dakinta koya rage kewarta dake addabar zuciyar shi, dama frame picture dinta kullum da shi yake kwana. Har ya zauna ya tashi ya koma ya fara wanke hannu ya dawo ya zauna ya kara komawa yayi haka ba adadi sannan ya fito Ãdil ya shigo da bowl ɗin cin cin a hannun shi da juice a tray ya tambaye shi waya bashi, yace "Maamah made it for me before she left, will you try it Papa is nice." ya ja hannun shi suka fito Dinning ya wuce kitchen ya dauko glass cup ya dawo suka ci cin cin ɗin tare, "Papa when are we leaving? Ya tsare shi da ido bari ma ya fara processing tafiyar, ya dade yana neman jirgin da zai kai su Nigeria abun haushi be samu ba sai nan da kwana uku Sam be ji dadi ba kamar yayi tsuntsuwa haka yake ji kwana uku yayi nisa, wani kunci ya mamaye zuciyar shi lokacin sallah yayi ya tashi ya fita masallaci. **** 💫 UMAYMAH💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣5️⃣ Gida ne mai dakuna birjik wata mata kakkaura ta yi sallama ta shigo ana jin muryrta mutanen gidan suka fara firfitowa dan bata da kirki da ɗan koren ta a bayanta Mudan kana kallon idon shi kasan babu mutunci a tare dashi, duk lokacin da tazo karɓar kuɗin haya suna tare da shi, Hajiya Asibi kenan ita wata shida shida take karɓar kudin haya babu afuwa Babu daga kafa, "sannu da zuwa Hajiya." matan gidan suka rinƙa fitowa suna kawo gaisuwa Murja ta ƙaraso da kujera yar tsugunne tace "zauna Hajiya." Ba shi ya kawo ni ba ku hado kuɗin ku larai ta durƙusa a gabanta tace "wlh maigidan ya je Rani aikin lambu Jos wlh ya dade be yi mana aike ba dan Allah Hajiya ayi hakuri." ta lailayo Ashar tace"da ke muka hada kuɗi muka gina gidan kenan, Mudan watso musu kayan su waje." To Hajiya ya shiga dakin ya fara fito da katifa, tace b"a'a dakata Mudan, Hajiya akwai wasu kudi a wajena na Adashi amma 15000 basu cika ba ayi min lamuni dan Allah zan cika." Yanzu naji zance, na baki kwana 2 ki nemo min kuɗina duk inda suke." haka aka rinka bata kudu Mudan yana kirgawa yana zubawa acikin wata jaka, gidan ba wani mai kyau bane dakuna ne a jere dama da hagu ga wata katuwar kwata a tsakiyar gidan gefe uban shara dakuna sun yi ashirin amma bandaki 2 ne daya na tsugunno, daya na wanka ,Hajiya Asibi mamallakiyar gidan daya ke a unguwar Birget kwanar Takari yawancin yan zaman SAUDIA idan aka kamo su nan suke zama. "Wannan ɗakin ba mutum ciki ne? Akwai Hajiya tana ciki bata da lafiya. wata ta faɗa acikin matan, "shiga ka karbo min kuɗi na." Mudan ya bankade labulen dakin "Dalla malama fito ki bamu kudi." Mama da yau kwanan ta 2 a kwance babu lafiya da kyar ta fito ta durkusa agaban Hajiya Asibi tace "ayi min hak'uri yata ta tafi karbo Albashi yanzu tana hanya." tayi mata kallon uku saura kwata tace "me yasa matsiyata ne ku? kullum sai kun ba ni ciwon kai Mudan watso musu kayan su." dama ba wani abun kirki ba ne a dakin yar yalolowar katifa ce sai Ghana must go da yan kwanokan abinci ko leda babu sai Tabarma, Mama kuka take yi ga zazzabi a jikinta ya gama watso kayan ke nan Zaliha tayi sallama ta shigo "yawwa Magajiya zo ki biya kudin." ranta babu daɗi ta kirga kudin su ta basu, dama su kadai suka rage suna karɓa suka fita Zaliha ta mayar da kayansu ɗaki tana hawaye, dama kudin aikin shara ne da gwamnati ta dauke so 20000 haka ta mika musu, tasan haƙƙin Khadija ne ke binsu, da Gold dinta na nan wacce ta dauka matsayin Aminiya bata cuce ta ba da gida zata siya dashi. **** Dr Huzaifa har ya shiga office tunani ya dame shi yana gama ganin patient ya tafi wajen Tahir ya samu ya farka yana zaune yana kallon Aljaxeera. "sannu jiki yayi sauki." Tahir yace "Alhamdulillah da sai dai ka zo ka tarar na tafi wajen Ummi kun barni ni kaɗai" "Yi hakuri na kusa discharging din ka." Dr Huzaifa ya nisa yana son yi mishi tambaya yana tsoron kar ya motsa mishi zuciya amma indai abunda yake tunanin haka ne ace Fatima yar shi ce dole ya shiga wani yanayi, "me kake tunani haka? Tahir ya tambaye shi, "Hmmm babu komai." ya ɗauke kai daga kallon shi ya kira sunan shi Tahir ya amsa yana mai da hankalin shi kanshi. "ni kuwa bayan rabuwar ku da Khadija kun kara haduwa kuwa? Ya dade yana kallon Dr Huzaifa kamar ba zai amsa shi ba sai kuma yace "tun ranar da muka rabu ban sake ganin Khadijah ba har ta kwanta a asibiti Uncle ɗinta ya roke ni na haƙura mu koma na ki I won't forgive myself I hurt Hayateey." idon shi yayi ja. "ni na manta yarda ka fasalta min ita ko kana da hoton ta?" Dr Huzaifa ya faɗa yana binshi da kallo. "Hmm hoton ta yana SAUDIA fasalta Khadijah shi yafi komai sauki." tiryan tiryan ya fasalta mishi ita "sai dai shekarun da yawa maybe ta canja yanxu she is around 38 -39 she a grown and matured woman now." yawwa abunda yake son ji kenan waɗannan da ya gani ɗazu baza su wuce wannnan shekarun ba, "naso kun haihu tare." Dr Huzaifa ya faɗa dan ya ga reaction dinnshi, yayi shiru kamar me karanta wani abu yace "I wish same for myself dana fi kowa farinciki a duniya." Koda Dr Huzaifa ya baro ɗakin Tahir wajen Umaima ya wuce yana shiga ta farka Munnirah ce tana zaune tana jan carbi Khadija suna wajen Ahmad itama tana son ganin jikin na shi, ba kowa ne a wajen Umaima kar ta farka ta bukaci wani abu shi yasa ta zauna da ita, "a'a kin farka ?" Munnirah ta faɗa suka gaisa da Dr Huzaifa ya kalli Umaima yayi murmushi "my patient how are you feeling, is there any problem? Ta girgiza Kai ya kalli Munnirah yace a hada mata tea, ta taimaka mata tayi brush ta hada mata tea Munnirah tace bari taje wajen Khadija ta dawo tunda Dr yana nan ya zauna kan kujera yace mata "Please I want a honest answer Fatima that woman is she your biological mother? Sai da tayi tunani ta tuna oh ashe ce mishi tayi Gwaggo Mamanta ce "why do you ask?" "Because you don't look alike." ta yi dariya tace "she is my mum mother inlaw." toh mahaifiyar mijin Mamanta kenan amsar shi ta fara fitowa, "and who is your mother Fatima?" ta kalle shi tambayar ta fara yawa, yace "don't mind me, naga ba kwa kama ne shiyasa, Ita wannan dana faɗa miki kamar twins ke da ita." sai tayi murmushi "ok I got you." be ƙara magana ba gudun zargi sai tace "Mamanta ita ce mijin ta bashi da lafiya." Correct yayi ajiyar zuciya yaso tambayar ta ina mahaifinta yayi shiru dama tunda tace patient din su shi ne mahaifinta kamar be yarda ba yayi shiru ya samu amsar daya ke son ji ya Ciro wayar shi a Aljihu, yace "let's snap picture Fatima I will send it to your twins and ask her to send hers too." da murna Umaima ta gyara rolling din veil ɗinta suka yi selfie da Dr Huzaifa, ya dauke ta ita kaɗai tayi murmushi hoton yayi kyau sosai yayi mata sallama ya fita. Leeds UK Yana kwance yana duba instagram page ɗinta yana dariyar adverts din gullisuwa da ta yi posting azo a jiyar da rai abunda yake so, oh wannan abun da ya zubar mata, wani vedio kuma ta fito a vedion tana nuna snacks din da tayi a kitchen "Umaimah food at your sevice book now we are just a DM away." Sai kallon adverts yake yi ya girgiza kai waya koya mata son kudi? Sai pictures din dogayen riguna da tayi posting da yawa hankalin shi ya yi kan wani vedio da suka yi da Adil sun saka matching outfit gown ce ta atampa, ta dinkawa Adil shirt ta rike hannun shi suna fashion parade sun yi kala kala wajen biyar different outfit har sai da yayi murmushi haƙoran shi suka fito tana son Adil, kafin ta shigo rayuwarsu yayi fama da shi akan cin abinci amma yanzu cikin shi ya bude sosai ko dai dama don basu samu irin wanda suke so ba ne? Amma ko da can shi ba mai cin abinci ba ne kuma tayi kokari akan makarantar Adil tunda ya lura suna karatu ya bar mata suke yi, the best part ma karatun addini tayi kokari sosai he will forever grateful to her duka vedios ɗin sai daya gani har wanda ta turawa su Baba ta zama Hajiya tana kirga kuɗi da siren zata shigo kano yayi murmushi a hankali yace "silly girl." rabon daya ji nishaɗi tin tana nan vedios ɗin sun kare he needs more sai yayi tunani akwai cctv a ɗakin da sauri ya dauko System ɗin shi yayi connecting yayi rewinding vedios sosai yana kallo har inda ya kulle ta a ɗaki duk sunayen data kirashi dasu ya ji "mai bakin hali, kurma Azzalumi, mugu ɗan masara." yayi dariya harda hawaye da ciye ciyen da suke yi da Adil kaf sai daya kalla, ya tuna ɗakinta daa shi ne na Aadil har toilet yayi connecting CCTV saboda yayi monitoring Mrs Lawrence idan baya gida ya koma toilet, toh me kake son gani? Ya tambayi kanshi, yana kallo yana kare fuskar shi sai ya buɗe ya kalla ai nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi, jikin shi ya fara rawa kamar mai zazzaɓi da sauri ya kashe system ɗin yana sauke ajiyar zuciya, yayi danasanin kallon ta haka, ya shiga toilet ya rinƙa kwarawa kan shi ruwan sanyi. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣6️⃣ Safiya ce sosai irin baccin bayan Asuba din nan Gwaggo bacci ya kwashe ta Munnirah kuma tana dakin da Umaima take duk da ta warware tun jiya Dr Huzaifa yace ta bari yau ayi discharging ɗin ta Khadija ta jingina da kujera da qur'ani a hannunta tana karantawa sai taga kafafun shi sun motsa tana daga zaune ta yi maza ta miƙe ta kura mushi ido a hankali hannun shi ya motsa tana kallon hannun sai ya fara ƙoƙarin bude ido ya bude idon shi ta kalle shi suka hada ido da hanzari zata danna kararrawar kiran Dr ya rike hannunta ya kura mata ido baya numfashi sai da oxygen yayi amfani da dayan hannun shi ya zare oxygen ɗin tana kallon shi murna cika ta tace "sannu Dear." Sai kuma tayi sujada shukr yana kallonta ta dade a sujada sannan ta mike da murna ta tashi Gwaggo firgigit Gwaggo ta miƙe ta yi kan shi, tace Alhamdulillah sannu Ahmadu. ya kifta mata ido alamar amsawa, ta lalubi wayarta tace "bari na kira Abbanku. daɗi ya ishe

Chapter 18 of 27