da sauri tun ɗazu take son ɗaukar shi yana hannun ɗan kurman Baban shi ta hakura ta basar, ta miƙa mishi hannu ya maƙe kafaɗa, tayi murmushi sai kuma taja hancinsa ta raɗa mishi wani abu a kunne ya miƙa mata hannu yana mata murmushi back, ta ɗauke shi suka fita a falon, Baba Dr yace "uwata sarkin yara." Mami murmushin fuskarta yaƙi gushewa ita wannan zaɓi yayi mata addu'a ta ke yi Allah yasa uban gayyar kar ya ba su matsala ta kalle shi ya hakimce yana latsa waya hankalin shi gaba-daya yana kan wayar, su Baban sama na magana a tsakanin su har Umaimah ta dawo riƙe da hannun Ãdil Baban sama yayi gyaran murya ya ɗora da cewa
"Abunda yasa muka tara ku a yau shine muna son haɗa kan ku cikin ƙanƙanin lokaci ayi a gama ba tare da wani kai ka wo ba, muna son kulla alkhairi ne wanda gaba za ku yi farin ciki da hakan in sha Allahu, a taƙaice dai mun yake hukuncin haɗa ku aure da ƴan uwanku." da sauri Fahad ya ɗago kan shi ya kafe Baban sama da ido dan shi maganar jinta yayi wani iri har cikin kansa, Amira ma gabanta ya faɗi duk da dai zancen ba a kai ƙarshe ba amma ta tsorata.
"Dattijo Allah ya jikan Aisha mun riga mun yanke magana mu Iyayen ku zama haka babu daɗi dole kuna buƙatar iyali, dan haka kai mun zaɓa maka yar'uwarka Fatima."
"WHAT."
ya faɗa da karfi jikin shi har rawa yake yi, Baban sama ya ɗaga mishi hannu dole yayi shiru, ya kalli Sa'ad da yayi mutuwar zaune, yace "kai kuma an baka lokaci baka yi wani yunƙuri ba dan haka mun yanke zamu haɗa ka aure da yar uwarka mai sunan Dada." sai a sannnan Umaima ta gane wato Fatiman da aka fara faɗa ita ake nufi kenan? Kai tsaye ta kalli Baban sama tace "wai Baban sama ni Fatiman?" yayi murmushi yana kallon yadda ta riƙe Ãdil yace "eh mana uwata ga shi nan har kin samu baby kyauta abinki."
Umaimah ta ɗanyi shiru kamar mai tunani sai kuma ta saki wani murmushi har fararen haƙoran ta masu kyau na bayyana, tace "Dan Allah an bani shi?" Su Daddy suka kwashe da dariyar jin daɗi ganin yadda tayi maganar tana sake kallon Ãdil, wato ita ba auran nema a gaban taba a'a ɗan da akace an bata ne ya dame ta, Umaimah ke nan ita indai sabga da yara to zero tension take zama, Amira ta sunkuyar da kai tana hawaye babu wanda take tunowa sai Masoyin ta ɗan Iya, Umma hankalinta ya kwanta da furucin Umaimah dan da farko har taji tsoro ganin tayi shiru, amma ta fuskanci Amira bata so, Sa'ad jikin shi yayi sanyi be dai ce komai ba, falon yayi tsit, wani gumi ne yake tsirtsirfowa Fahad this is the second time kenan haka aka yi mishi na Aysha ma ya girgiza kai yanajin wani irin baƙin ciki na lulluɓe shi.
"Maamah I need more." Ãdil daya gama cinye popcorn ɗin da Umaimah ta bashi ya faɗa yana kan cinyarta, wani murmushin jin daɗi tayi jin ya kirata da Maamah kamar yadda ta faɗa masa ɗazu da suka fita, ta dauke shi suka fita.
Alhamdulillah Daddy ya faɗa "ko akwai mai magana? Fahad yace "sir, I'm sorry but I'm not ready to get marriage."
Daddy ran shi a ɓa ce yace "to idan ni ne ubanka kuma na isa da kai baka da mata sai Umaimah." ya kalli Daddy da sauri ɗazu da aka ce Fatima ya ɗauka Amira ake nufi amma that Noisy girl "no no I can't Sir. ranshi a ɓace yace "I'm sorry excuse me please." ya fita daga palour, Daddy ya kalli Mami da ta fara hawaye yace "ki faɗawa ɗan ki idan be auri uwata ba ya nemi wani uban bani ba." Baba yace "ah ah Yaya Ibrahim ayi komai a sannu dan Allah." Baban ABU yace "Sa'ad kana da abin faɗa? ya ce "ah ah babu komai Baba."
wata ajiyar zuciya Mami tayi, "Allah yayi maka albarka. Amira fah? Baban ABU ya kalle ta, ta kasa magana ta girgiza Kai yace "magana za ki yi." da Ƙyar tace "ah ah."
"ALLAHU AKBAR Allah yayi muku albarka." Daddy ya faɗa yana daukar wayar shi yace "bari na kira Farouk ya zo (Dan Baban ABU ) na bashi auren uwata ai ba shi kaɗai na isa da shi ba."
"Ah ah Yaya abi komai a sannu. cewar Baba Dr, "ba ka ganin yaron nan yaƙi zuwa wajen kowa sai Umaimah ta iya da yara amma shi baya gani." "adai yi haƙuri Yaya." har Farouk ya ɗaga kirsn Baba Dr ya amsa yace mishi ya aiki suka gaisa ya kashe wayar, Daddy yace "ai daka ƙyale ni, yaron nan tun yana ƙarami yake wahalar da ni ashe ni ba komai ba ne a wajen shi." Baba Dr yace "Yaya saboda matsalar shi sai ana hakuri dashi." Umma ma ta ce ayi haƙuri Yaya. Baba yace "duka yaran mu ne mu bi komai a sannu."
Daddy abinda Fahad yayi ya ɓata masa rai sam baiji daɗi ba yace "kuna ganin uwata bata yi jayayya damu ba ƙaramar yarinya sai shi babban banza a haife ya kusa haifar ta." Baban sama yace Sa'ad da Amira su je an sallame su, suna fita ya fito da bundle ɗin 1000note guda 2 ya kalli Baban ABU yace
"Ni Sulaiman Isma'il Bichi ina nemawa ɗana Isma'il Ibrahim Bichi auren jikarku Fatima Tahir Al-arabey wannan kuɗin gaisuwar iyaye ne."
"Masha Allah." Baban ABU ya karɓa yace "mun bayar." wata ajiyar zuciya Daddy yayi yana hamdala da Allah yayi mishi arzikin yan uwa nagari, Baba Dr ya fito da bundle ɗin 1000notes guda 2 shima ya kalli yan'uwansa yace "ni Yusuf Isma'il Bichi ina nemawa ɗana Sa'ad Ibrahim Bichi auren yar uwar shi Fatima Muhammad Bichi. mun bayar gaba-daya suka faɗa banda Baba da yake ta murmushin jin daɗi, Mami da Umma suka rungume juna.
****
💫 UMAYMAH💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 0️⃣8️⃣
Washegari su Baban sama duk suka tafi, yau kwana uku dayin maganar Baba da Daddy na zaune Daddy ya kalli Baba yace
"Muhammad na fahimci duk lokacin dana yi maganar a nemi uban uwata baka so, toh yanzu dai maganar aure ta taso dole yau bayan magariba mu je Ƴankaba wajen Aminin Baban Tahir ɗin shekaru sun shuɗa ya kamata mu ajiye komai." Baba ya nisa yace "babu komai sai muje. "yawwa ko kai fah." Baba ya kira Umaimah a waya yace ta zo part ɗin Daddy yana kiranta ba a fi minti 5 ba sai gata da Iman a hannunta, "hmmm Daddy wasa tare ci ban ban." Ta faɗa tana saka hannu ta ɗauki kilishin da yake ci ta fara ci Baba yace "yar taki sai siɗe baki take yi baki bata ba. "Iman akwai kwaɗayi." cewar Umaima, "ay ke ta gado. Baba ya faɗa, ta tauna kilishin ta bawa Iman a baki.
Daddy yace "zo nan magana zamu yi. ta zauna kusa da shi tana cewa Allah yasa samuwa ce Daddy. "samuwa ce mana." Daddy ya faɗa, yace "bayan magriba ki shirya zamu je unguwa." Visar ta fito ne Daddy?
"Ba wannnan maganar bace, baki da matsalar visa kwantar da hankalin ki." Ta sake cewa "Daddy me yasa ya tafi da Ãdil?"
"shi wa? Baba ya faɗa yana kallonta sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kai, Daddy yayi murmushi yace "Rabu da shi Ãdil ɗin ma ai naki ne za su dawo, sabida makarantar shi da kuma neman shi da aka yi a office shi yasa suka tafi sai ɗaurin aure zai dawo."
Mami da Umma suka yi sallama suka Shigo, shirye shiryen su ke yi sosai na kayan gidan Amira ita a pothacourt zata zauna, Daddy ya kalle su yace "preparation ɗin aure 3 fah za ku yi. Baba yace "tabbas harda Hidaya ita dama kuɗin auren ta ya kusa shekara a hannun Baba, Abokin Daddy Abdulhamid Muhammad ɗan shi Hafiz ne zai aure ta, shima tashin Lagos ne yana karatu a Canada, jin batun auren su Fahad Baban shi yace a haɗa da nasu, in ya so idan ya kammala masters ɗin shi ya dawo sai kawai ayi taron biki ta tare sannan ita ma ta gama karatun ta, "Alhamdulillah." Umma ta faɗa, Allah yasa albarka aka amsa da Amin.
Zuwan yayan Mami ne ya katse su, Yaya Adam shi ne babba a gidansu Mami Daddy da Baba suka miƙe suka bashi wajen zama aka gaisa Umma da Mami suka gaishe shi Umaimah ma ta gaishe shi ta fita, yace "Ibrahim ya hidima? jiya Darsha ta kira tana faɗa min abun da ya faru na zo na ƙara baka haƙuri Fahad be kyauta ba ayi masa afuwa."
Daddy yace babu komai ni abunda ya bani haushi babu wanda ya nuna rashin Amincewa sai shi.
"Ayi haƙuri na kira shi na yi mishi faɗa nace ya sake baka haƙuri." Daddy yace "komai ya wuce ya kira ya bani haƙuri, ɗan yau sai Allah ko sallama be yi mana ba sai tashi muka yi muka ga ya ɗauki ɗan shi sun tafi sai daga baya yayi min text wai an neme shi a wajen aiki, na dai faɗawa ɗan uwan shi ya faɗa mishi lallai lallai ya zo a daura aure dashi ya tafi da matar shi."
Suka ci-gaba da tattauanawa Daddy ya faɗa mishi harda Hidaya za a haɗa.
****
Leeds UK
Tunda Mrs Lawrence ta tashe shi yake ta rigima ya ƙi tashi ta shirya shi, ta gaji da rarrashin shi ta yiwa Fahad knocking ƙofa ya fito ta faɗa mishi Ãdil yaƙi bari ta shirya shi ga shi safiya ce ya kusa tafiya school, Fahad baice komai ba ya bi bayanta zuwa ɗakin Ãdil, yana ganin Nanny ya cigaba da rigima yana faɗin "take me to Maamah."
"go and shower my friend." Fahad ya fada a fusace, sai kawai ya fashe da kuka, "sorry sweetheart. Nanny ta faɗa tana taɓa shi "let go? ya ƙi tafiya Fahad da ran shi ya ɓaci ya kalle shi yace "Didi I don't want to repeat myself go and shower or else, I would never take you to Nigeria never again?" yana jin haka ya miƙe suka shiga toilet, yana tsaye a ɗakin har suka fito aka shirya shi sannan ya bar ɗakin, mtsw yayi tsaki "how on earth zai yi rayuwa da that spoilt brat daga haɗuwa da ita Ãdil komai zancen shi Maamah this Maamah that Maamah duka duka kwana 3 suka yi tare shi ne har suka saba haka." ya girgiza kai Kai zai karɓi auren saboda Daddy amma he will deal with her, "I will deal with you, I will deal with you......." yayi ta maimaita wa sai kuma ya fara arranging neckties ɗin shi a hanger ɗin wardrobe ya gama ya canja bedsheets da wasu farare yana gamawa ya shiga toilet ya fara shirin fita office, yana shiga aka yi horn school bus ta zo ɗaukan Ãdil.
*****
Amira ce zaune a tsakiyar gadon ta idon ta yayi jajir suna waya da ɗan Iya da ƙyar ta ke magana tana ba shi haƙuri an yi mata miji, yace babu komai ta bi Iyayen ta, shigowar Umaimah ne yasa ta yi mishi sallama, "me ye idon ki yayi ja? Ko kuka kika yi? Umaimah ta tambaya, Kwalla ta zubo mata sai ta bata tausayi tace "haba Amira ki yi haƙuri mana." ta girgiza mata kai "ba za ki gane ba ke don ba soyayya kika yi ba."
"kamar ya Huzaifa me muka yi idan ba soyayya ba? "Toh ban san zuciyar ki ba." sai ta fashe da kuka "Umaima I love him." ta rungume ta tana buga bayanta, Amira ta sake cewa "I miss yaya Khadija." sai duka suka fara kuka saboda maganar Khadija da Amira tayi.
Jikin Ahmad ya motsa mijinta ba zata samu zuwa ba dan a kwance suke a asibiti Daddy yace bayan bikin su zasu je da su Mami su duba shi.
Haka suka yi kukan su suka more a ɗakin babu wanda ya sani.
Su Mami ke ta lissafin abun da ba a siya ba Munnirah na ƙara duba list ɗin tana rubuta wasu abubuwan kira ya shigo wayar Mami Sa'ad ne, Mami tace yaushe zai shigo yace gobe in sha Allahu, Umaima ta shigo da goyon Iman a bayanta ta kalli Umma tace "su Siyama sai zirga zirga ake yi haka kike so dama kiyita zagaya kasuwanni." Umma ta yi mata banza, Munnirah ta ce "wlh ki fita a ido na ki barmin uwa ta huta. "kai Mamin rijiya me na yi? Mami tace "Ni yau ban saki a idona ba? "ina nan Mami. Munnirah ta ce "yawwa Umma daga gobe zan ɗauke amaren gida na zasu koma."
"toh yayi hakan Allah ya kaimu."
"tunda mun gama bari na je wajen masu event center." Munnirah ta faɗa tana miƙe wa, Umaimah tace "wai wa ya ga Siyama Mc yace kakar Amarya ta fito rawa, sai Siyama ta rinƙa haka." ta fara gwada rawa tana juya hannaye tana cewa "sabada sabada." Munnirah da Mami dariyar su ta tashi Iman, har Munnirah ta mike zata tafi Umma tace "bar min Iman ɗin ku tafi da Umaima dan gara Iman sau dubu idan na goya ta, tayi bacci shikenan." Mami tace "idan ta koshi bata da rigima.
"toh Siyama me kike nufi? "Dan Allah ku je a sauka lafiya ba abunda nake nufi." suna fita Mami ta yi dariya tace "kishiyata ita ce dai dai Dattijo." Umma ta ce "Allah dai ya basu zaman lafiya, idan ba haka nayi ba magana zata saka ni, Allah ya bashi haƙurin zama da Umaimah." Mami ma tace "itama Allah ya bata haƙurin zama da shi." Amin Umma ta amsa.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
*Volume two*
EPISODE 0️⃣9️⃣
Tun a mota Daddy yake yi wa Umaimah bayanin inda zasu da waye Malam Isah Aminin kakanta, tana ta murna kamar an ce Daddyn ta zata gani ta dame su da tambaya Daddy yana bata amsa har suka iso gidan Alhaji Isah, suna parking motar Baba Isah ta shigo Hamza ke jan motar su Daddy suka fito, Alhaji Isah na ganin su ya fito da sauri yana cewa "Alhaji ku ne kuke tafe? mu shiga ciki sannunku da zuwa ikon Allah." Baba yace Umaimah ta fito daga mota suka shiga palour Hamza ya gaishe da su Baba yana ta kallon Umaimah be dai yi magana ba sai da Baba Isah yace "Alhaji Ibrahim wani abu na gani me kama da Hajiya Fatima Al-arabey (Ummi) kwabo da kwabo." Umaimah ta gaishe shi, Daddy yayi murmushi yace ta shiga ciki ta gaisa da mutanen gidan, nan Daddy ya warware mishi komai, Baba ya ɗora da cewa "abune dai an yi shi cikin ɓacin rai sai dai kawai abun daya wuce ya riga ya wuce."
"Allahu kadiran ala manya sha'u jini ba karya ba." cewar Baba Isah, "haka Allah ya tsara Alhaji Muhammad wlh rasa gidan ka dana yi da rashin samun ka a waya duk shi ya jawo wannan saɓanin, yayi musu bayanin sau biyu Tahir yana zuwa neman Khadijah, ya ƙara da cewa "na ƙarshen ma ya je har Bichi ya tarar da ɗaurin auren Khadijah. har ciwon da ya ji na Tahir ɗin a bakin ɗan shi Hamza ya kwashe labari ya faɗawa su Daddy, falon yayi tsit Baba jikin shi yayi sanyi, Baba Isah ya ɗora da cewa "mun je mu Lebanon ɗin dan mu duba shi amma mun yi rashin sa'a an ce mana basa nan kusan 4 years kenan rabon su da gidan, haka Allah ya tsara ba kokarin da ban yi ba kar auren nan ya zo ƙarshe amma bawa baya wuce ƙaddar shi."
"babu komai Allah ya rufa asiri yanzu ma maganar aurenta ce ta taso idan da hanyar da zai san da yar shi toh a sanar da shi ko dan gaba." Daddy ya faɗa, Baba Isah yace "harda mahaifiyar shi sun zo wlh Allah be yi za a gana ba ne, kuma duka wayoyin su basa tafiya har ta ɗan uwan shi Yaseer haka muka sha wahala da muka je Lebanon, naso ganin shi kansu tafi saidai bai yiwu ba dan a sume aka tafi dashi asibiti."
innalillahi wa inna ilaihirraju'un kawai su Daddy su ke maimaita wa, Daddy yace "shikenan idan an samu labarin shi a sanar mana." Daddy ya miƙa mishi IV na ɗaurin aure "wannan juma'ar ne ma." ya faɗa, in sha Allahu Hamza zai kawo ni, bari na kira shi mu ji ko akwai wata mafitar. Hamza ya shigo tare da Umaima Baba Isah ya tambaye shi ko da yadda za a samu Tahir? Yace "wayoyin shi basa tafiya amma bari mu gani." sai ya buɗe Facebook ɗin shi, rabon da ya hau shekara 5 tun ranar daurin auren Khadijah da yayi posting kamar haka
*I am excited to meet Hayatee after so many years*
be kara hawa ba, Hamza suka yi selfie da Umaimah yace zai turawa Tahir duk lokacin daya gani yasan zai neme shi, Umaimah jikin ta yayi sanyi suka ɗauki pictures harda Baba Isah duka Hamza ya turawa Tahir suka yi addu'ar Allah yasa ya gani, haka dai suka yi sallama bayan sun yi exchange number waya sai kuma ɗaurin aure idan sun haɗu
*****
Mami ke magana da Fahad a waya akan shirin zuwan Umaimah m, "Dattijo ɗakin Ãdil ya fi space pls make sure an kwashe kayan ɗakin a mayar da shi ɗaya ƙaramin, a bawa Umaimah babban an make sure an ƙara gyare gyare Amarya za a kawo." Fahad yayi shiru Mami ta sake cewa "pls don't argue do the needful pls, brothern ka baya ba mu ciwon kai ya turo kuɗin lefe da duka expenses duk da Daddyn ku yace shi zai yi amma kai kullum mu yi ta draging da kai kullum sai na kira na ja maka kunne haba Dattijo Dan Allah idan ka zo kar ka bani ciwon kai, duk abunda ka yi kaina yake dawowa, pls ka bar ni na huta haka, are you there?"
"Yes Mami." ya amsa da ƙyar ran shi a ɓace shi duk wannan damun shi da ake yi na meye? "and ka taho da wuri Sa'ad tun jiya ya zo hope I am clear?"
"ok Mami."
"Allah yayi muku albarka sai anjima." suka ajiye wayar, yana office yana duba wani sketch ɗin wani company daya zana, yana ƙara crosschecking Mami ta kira, zane is his hobby amma kwanan nan ko zanen ma daurewa kawai yake yi duk an rikita shi da maganar that small clown, ya kashe system ya dafe kai, ya manta yaushe rabon da yaci Abinci sai dai tea cikin shi ya murɗa, da gaske yunwa yake ji amma Sam ba shi da appetite duk sanda aka yi mishi maganar yarinyar nan sai mood ɗin shi ya canja haka jiya da daddare Sa'ad ya kira wai ya kai musu ɗinkin ɗaurin aure ƙarshe da faɗa suka rabu, ya harhaɗa kayan shi ya fita dan ya gaji he needs to find something to ear.
*****
Su Umaimah na gidan Munnirah ita ce take yi musu duk wani gyare gyare na Amare Musamman Hajiyarta ta ɗauko Gajiram daga Maiduguri don Hajiyan Munnirah yar Maiduguri ce, ta sauka gidan Munnirah, suna shan Dukkhan da halawa, an tsuma su sosai, Umaima sosai take tsayawa ana mata komai su gumba da tsumi idan an bata ci take yi babu bata lokaci, sosai Munnirah ta ji dadi bata wahalar da ita ba, zabo, kaza, haƙƙin daka sha da madara ko nono Umaima da kanta ma ɗauka take ta ci, Amira ce dai da ƙyar take ci sai Munnirah ta tsaya a kanta wani lokaci ta faki ido ta zubar, zancen a faɗi yadda suka yi kyau ma ɓata baki ne, fatar su tayi fresh tayi kyau sai glowing suke musamman Umaimah tayi wani smooth, an musu gyara ciki da waje, gobe za a fara biki laraba kamu Alhamis mothers eve sai jumma'a a ɗaurin aure a Bichi, Asabar kuma su Umaimah zasu wuce, Amira ma Asabar za su wuce pothacourt amma su da yamma, Gajiram ta gama turara su da turaruka kenan wayar Umaima tayi ringing Uncle Ismah ne yace su fito yazo ɗaukan su da ke yau zasu koma gidan Umma, kuma mai lalle ta zo tana jiran su, tace "gamu nan fitowa Uncle Ismah." ta faɗawa Amira Uncle Ismah ya zo, Munnirah tana gidan Umma saboda shirye shiryen biki tare ta ke tafiya da Iman kar ta dame su har ta kai ƙofa zata fita Amira tace "wa kika bar wa kayan naki duk kin watsar kin yi gaba." "haba sisto haɗa mana pls ina jiranki." Amira ta yi ƙwafa ta fara haɗa musu kaya "gaskiya ina tausayin ya Fahad. Umaimah tace "kya ji dashi. Au haka zaki ce bari na bar miki kayanki. "sorry yi hakuri tawan. ta fita.
"Uncle Isma ya kaga ni." Tayi maganar tana juyi yace "ah lalle Amarya kin fito fa." ta wani saki murmushi, "yawwa Uncle Isma ay zaka cigaba da kula da DIJAH COLLECTION dan shekarar nan na zuba dukiyata a ciki dan Allah kar wajen ya mutu, gullisuwar ma Tasiu zai yi handling, zan ma cigaba a UK."
"a ina? ya tari numfashita, "acan mana ai akwai Hausawa ni har an haɗa ni da mutane." kawai ya tsaya yana kallon ta.
Yar Chadi ta tsantsara musu lalle da yake Umaima fara ce kamar dora mata shi aka yi yayi bala'in yi mata kyau kamar fararen Sudan dinnan, Amira ma tayi kyau kwarai chocolate colour ɗinta ta kara fitowa sosai, wayar Amira tayi kara yan North West ne ƙawayen ya da zasu zo gobe ta kara jaddada musu su zo da wuri, ita Umaima friends dinta kadan ne wanda ta gayyata yan BUK dan ashoben su ma ita ta ɗinka musu.
Sa'ad ya shigo ɗakin Uncle Ismah inda suke, dan dakunan sama cike yake da yan uwa har part ɗin Daddy jama'a ne yan Bichi yau kwanan su uku a gidan, "Uncle Sa'ad sannu da zuwa." Umaima ta faɗa, Amira ta daga kai ta kalle shi tace "ina yini ya Sa'ad." ya kalle ta yayi ajiyar zuciya har ya kusa zama lost saboda kyan da tayi mishi da kyar yace "lfy ƙalau Aunty Amira." ta sunkuyar da kai tana murmushi, "na gan ki mana daughter." ya fita Umaimah ta bi bayan shi, suka tsaya a corridor ya tambaye ta ko akwai abunda su ke bukata? Tace babu komai ya mika mata brown envelope "gashi ko zaku buƙaci wani abu." da murnar tace mungode har zata tafi yace mata "daughter me Amira tafi so ayi mata kyauta."
"ai wannan burge ta babu wuya kawai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 27