Isma'il ya samu aiki da MTN yana office ɗin su na civic centre ya ɗaga kiran ya ce zan kira ki ina attending customer ne. "ok dan Allah ka kira ni." Akwai matsala ne ya tambaya? Matsaloli ma ba matsala ba. "toh ki bari idan na dawo gida ma yi maganar." Tace "toh shikenan u are the best Uncle Ismah." suka yi sallama ita wlh tsoro take ji. ba a yi sati da case din su daya kaita Tahir ya aje ya sata trekking ba, yanzu Allah ne kaɗai ya san abunda zai yi mata ko Daddy zata fadawa, kai kar kuma ta kama kanta tana ta tunani ta ji wayarta ta yi ringing, Huzaifa ne bata dauka ba har sai da yayi mata 12 missed calls to me zata ce mishi, ta fito ta shiga ɗakin Amira daya ke bata da lectures yau ta tarar da ita tana waya sai lumshe ido ta ke yi tasan Ɗan Iya ne masoyin nata ta ja stool ta zauna tana kallon Amira da ta make murya tana wani juya ido, Umaima ta koma daga bakin ƙofa ta ware murya ta kwalwa Amira kira "kizo Umma na kira." ta yi hakan dan tasan dole zai ji taa kawo ƙarshen wayar, Amira ta ɓata fuska ta amsa da toh shikenan later ta ajiye wayar tana harararta "gaskiya ke yar baƙin ciki ce." Tace "ke dalla magana na zo muyi da Uncle Isma yana nan ba za ki ganni ba. "Abokin cin mushen naki toh ki jira ya zo mana, ni kar ki saka ni a matsala Dr ya ce min next week zai turo. Umaimah ta harareta tace "ko ba Dr ba." ta kwashe da dariya "Astagfurullah wannan mutumin zubin kanikawa wlh kamar be san bihim ba amma wai Dr ne." maganar zamu yi ko sai kin gama ci mun mutunci?
"kinsan me....." ta kwashe abunda ya faru ta faɗawa Amira, Dariya sosai Amira ta yi har da hawaye "ba na son wulakanci so nake ki bani shawara, ko hak'uri zan bashi kin ga ba a daɗe da case ɗin can ba." Amira tace "ni me zan ce ki bari Hakimi ya zo sai ki faɗa mishi, ni Huzaifa ne ya bani tausayi ki ɗauki wayar shi idan ya sake kira pls." Abunda za ki faɗa kenan gaskiya ba ki da amfani." ta faɗa tana fita daga dakin.
UK
Papa I want to show you my coloring book. Aadil ya faɗa yana kallon Papan shi, Fahad hankali shi nakan System yace "ok let me have a look." ya tashi a nutse ya shiga ɗaki be daɗe ba ya fito da coloring book a hannun shi ya buɗe yace "Papa I got 9 out of 10, I'm so happy I think you will be proud of me too." ya ƙarbi coloring book din ya kalli Ãdil ya jinjina mishi da hannu yace "that's my boy, that's awesome." Ãdil daɗi ya kama shi, shi dai Papan shi ya zama proud of him, yayi dariya har hakoranshi suka fito reras dasu farare kal irin na yara, wayar shi tayi ringing ya daga da sallama Daddy ne ya amsa sallamar shi suka gaisa tare da tambayar Mami Daddy yace "ta shiga gidan Baban ku, ya ya Dattijo kana lafiya ko?" ya amsa "Fine Sir. Any improvement akan medication ɗin ka? "Alhamdulillah there is improvement sir."
"Masha Allah ina abokina? Daddy ya tambaya, Fahad yace "he is fine sir. Ba ni shi mu gaisa." ya bawa Ãdil wayar yace "Didi grandpa." ya karɓa da murna "good evening Grandpa. "No here is morning." Ãdil yace really grandpa? Yes Ibrahim." Daddy ya kira shi da ainihin sunan shi. "Grandpa where is Grandma she promise to take me to Nigeria? Daddy yayi swiching to vedio call sukayi ta hira da, Fahad ya ci gaba da aikin shi ya kyale su, don sun saba sai su fi one hours suna magana a waya sai ya gaji da surutu ya kwace wayar idan Sa'ad ne kuwa har mantawa yake yi da su sosai suka shaku da Papi kamar yadda yake kiran shi, da yake yana yawan ziyartar su idan ya samu sauƙin aiki.
******
Amama iman ta zo wajenta tana kuka sai ta nuna mata Ƙofar kitchen, da plate ɗin data saka mata soyayyen kwai babu komai a plate ɗin, Umma tace kukan me ta ke yi? Umaima ta daga ta sama tace "na soya miki wani ne baby na kin cinye koh? Umma ta ce anya kuwa ta cinye? nawa kika soya mata?"
"3." Umaima ta faɗa, "haba 3 yayi mata yawa zaki buɗa mata ciki, ina kallo jiya cikinta yayi turtsitsi tana ta nishi ke da yaro yayi kuka sai ki dura mishi abinci ba kowanne kuka ba ne yaro idan yayi yake nufin abinci ya ke so ba." Amama Iman ta ƙara fada tana nuna kitchen sai ga Sasi ta fito daga kitchen ɗin tana lashe baki, "oho wato Sasi ce ta kwace miki kwai ta cinye? sai nuna ta ta ke yi, Umaimah tace "Sasi ta zama bandit, to yi shiru." ta ajiye Iman tace "bari na soya miki wani ta shiga kitchen." Sam bata kula da mutum ba sai ji tayi yace "follow me." Aliyu yayi maganar yana fita sai yanzu abunda ya faru shekaran jiya ya faɗo mata, sun yi maganar da Uncle Ismah yace ta share kawai ba abunda zai faru, hankalin ta ya kwanta ta shiga sabgogin ta, Safiya ce ko wanka bata yi ba riga da wando ne na bacci a jikinta sai hula suka fita ta ƙofar baya, ya nufi kangon Baba da aka saka mishi gate ya buɗe wajen yace "na baki 2 hours ki nome wajen nan failure to do that kinsan sauran." tana shiga ya datse ya kulle da mukulli ba wanda ya kula ya bar wajen.
Iman taji shiru ta fara kuka tana kiran Amama, Umma ta leƙa babu kowa a kitchen, ta tambayi Baba Rabi tace tana wajen wanke wanke bata kula ba Umma ta kira Barira tace ta duba ɗakinta ko zuwa ta yi ta kwanta ta dawo tace bata nan, wasa wasa har La'asar babu Umaimah, Umma tace fita ta yi Malam Idi yace be ga fitar ta ba ga Iman nata kuka Amira ta goya ta sai ajiyar zuciya ta ke yi, Ismael ya shigo Umma ta ce Umaima ce ba a ganta ba yace "an kira wayar ta? "Wlh na sha 'afa. yace "bari na kira wayar tana ringing sai gata wayar a hannun Amira dake shigowa "Ah ah toh ina ta yi?"
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
*Your words and actions will always have consequences. You pay for what you've done to others. If not today, tomorrow. Sadly, with social media we don't realise this. Then we wonder what we're paying for. Go back and search. You will find it.*
EPISODE 0️⃣6️⃣
Umaima tun tana noman da wasa har ta gaji sosai, akwai tabarma a wajen ta yi kwanciyar ta ga yunwa ko breakfast bata yi ba sai dai ta buɗe famfo ta sha ruwa ta kwanta har gari ya fara duhu, Sasi tana ta kukan neman ta, tana zagaye gidan Baba da Daddy hankalin su ya tashi Daddy ya ce "kodai Babangida ne ya fita da ita? Umma tace "ah ah shi da safe ya shigo yayi min sallama za shi Kaduna daurin auren abokin aikin shi, ba su haɗu ba ma lokacin."
Uncle Ismah idon shi ya kada yayi jah saboda tashin hankali, Daddy ya kira Baban sama ya faɗa mishi har gidan rediyo aka aika Ibrahim ya je ya sanar daya ke weekends ne yana gari, Sasi ce ta hau kan katangar kango ta dirga ta taho wajen Umaimah da sauri da yake an kunna security light wajen yayi haske taje tana yakushin ta bata tashi ba, ta ja hular Umaima ribbon dinta ya cire ta rike a bakinta ta fito ta yi wajen Ismael tana ta binshi be kula ta ba sai da ya kallo ta da ribbon a bakinta tana jan wandon shi ya tashi ya bita suka zo har ƙofar kango tana ta kuka sai ya dawo ya faɗawa su Daddy, Baba yace "a duba ɗakin Babangida mukullin wajen yana wajen shi." Ibrahim yaje ya ɗakko su ka dunguma aka bude wajen saiga Umaimah a kwance a wajen Daddy ne ya ɗauko ta a sume, Baba ran shi ya ɓaci ya kira Aliyu yace kawai amsa ɗaya nake so eh ko ah ah kai ka kulle uwata a kango? shi sai yanzu ya tuna wlh, gaban shi ya faɗi saboda yadda Baba yayi maganar ya ce "ni ne." "ka kyauta." Baba ya kashe wayar shi, jikin shi yayi sanyi sosai ya ƙara gudun motar hankali a tashe don ma motar matsala ta samu a Zaria ba a daɗe da gyara taba, yanzun nan ya cigaba da tafiya kiran Baban ya shigo.
Sun rufa a kanta gaba-dayan su Ibrahim ke bata taimakon gaggawa don an shafa mata ruwa bata farfado ba yayi ta murza tafin kafarta ya danna kirginta ya buɗe bakinta ya hura mata iska ta yi ajiyar zuciya ta buɗe ido dishi -dishi ta ke ganin fuskokin su, sannu suka rinƙa jera mata sai bin su take da ido Daddy yace da Ibrahim "ko asibiti zamu kai ta? Yace
"ba abunda za su yi mata passingout ta yi babu komai zata dawo daidai." Ibrahim ya faɗa, sai lokacin abunda ya faru ya dawo mata ta fara kuka "yi haƙuri." Daddy ya faɗa ya kalli Amira yace "hado mata tea ta sha. Umma tace ba ta karya ba tun safe. Baba ya kalli agogo after 9 lallai ta yi jimirin yunwa bari Babangidan ya zo ya ji me tayi mishi haka. Daddy yace kome tayi masa sai ya kulle ta sabida ta yi mishi me? Kiran Baban sama ya shigo wayar Daddy ya daga yace "an same ta yaya." yana ajiye wayar Dada ta kira tayi musu barka da arziki, Daddy ya faɗa mata aikin Babangida ne, tace "wannan yaro an yi mai baƙar zuciya." Dada ta yi ta faɗa suka yi sallama.
Umaima ta tashi da sauri ta shiga Toilet, tana kwarara amai ta ji yana yin ta ya canja marar ta ta murda period ɗin ta ya zo Umma ta shigo ta ga halin da take ciki ta taimaka mata ta yi wanka ko da suka fito su Daddy har sun fita daga ɗakin.
Aliyu na shigowa gidan suka rufe shi da faɗa babu ƙaƙautawa. A ranshi yace "Abun har ya kai haka dole iyayen shi suna da na gaba da su tunda abun haka ne, yayi musu bayanin abunda idon shi ya gani Umaima saurayi zai yi proporsing da zobe sai ka ce ba musulmai ba sam ba ala 'adar mu bace."
Daddy lokacin da suka titsiye shi yana musu bayani cewa yayi ina ruwan shi, Baba ya rufe ido ya balbale shi da faɗa, Daddy ma ya karɓa yace "ko auren coci zata yi ina ruwanka ka zo ka faɗa mana tukunna ka gani ko ba za mu ɗauki mataki ba haka ake hukunci ka rufe yarinya tun safe da daga suman ta wuce fah? Aliyu ka sassauta wa wannan zuciyar taka kar wata rana ta saka aikin dana sani." Umma ta karɓe zancen da cewa "kamar wata dabba ka kulle mutum ka yi naka waje."
Tundaga ranar ko ya gaishe su da kyar su ke amsa wa, kai yau komai dare sai ya je Bichi, dole Dada ta shiga cikin maganar nan, daga gyara kayanka kakaninta sun tsane shi, Umma a rana ta kira shi sau uku sau hudu barin lokacin dawowar shi ta ji shiru be dawo ba, amma yanzu ko zai kai 11 a waje kafin ya dawo ma ta haye sama ya basu hakuri Umaiman ma yayi mata bayani ba don baya sonta ba ne yake mata hukunci, amma ba komai dole ya ƙyale musu jikar su tinda basa son ana mata magana.
Yana tashi daga wajen aiki direct ya tafi Bichi.
Aliyu na gama yiwa Dada bayanin abinda ya faru tahau salati "Ashe haka abun yake to ni rufa ta suka yi ance kawai ka rufe ta ka yi naka waje, ai kuwa da sake babu mai watsa min zuri'a, idan ma ubanta za su nemo su bashi yar shi can su karata amma ba a nan ba auren zobe ina." ta girgiza Kai, Aliyu yace "Dada ba fa auren zobe ba ne Alkawari ne na masoya zasu kulla akan zai aure ta haka ake yi." "haka ake yi a ina? Ta tari numfashin shi kar ka bata min rai Alkawarin da wa? Oho ita uwar kanta kenan shikenan ba mu da mutunci, su ma masu ɗaure mata kugu a banza take ganin su tunda zata yi Alkawarin aure ba su sani ba." Dada kamar ta rufe shi da duka kamar shi ne Umaimah a gabanta, tace "kai dai Allah yayi maka Abarka ka ma fi iyayenka kokari bar ni da su za su sha mamaki kuwa."
"Dada ni zan wuce 10 har ta gota. Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi tace "Ah ah Ali ka bari gobe da sassafe sai ka wuce aikin daga nan." haka ya haƙura yayi kwanciyar shi babu wanda ya kirashi kila ma babu wanda ya kula ya kwana ko be kwana a gidan ba.
Daddy da Baba suna dawowa daga sallar Asuba gari yayi haske don basa dawowa da wuri, mamaki ya kama su da suka ga Motar gidan Hakimi da Sarkin mota a harabar gidan Daddy yace "Muhammadu Allah ya sa lafiya." suka gaisa da Sarkin mota yace "Hajiya Dada na kawo." Tun daga bakin ƙofa suka fahimci abunda ya kawo ta Dada faɗa take yi kamar ta ari baki suka shigo da sallama, tace "yawwa ku nake jira." su na gaishe ta da kyar ta amsa, Umma tana ta bata haƙuri tace "Dakata Maryama ke ai yarinyar nan kin gama ɓata ta to ku saurare ni ku buɗa kunne ku ji da kyau umarni ne ba shawara ba ko dai ku nemo ubanta ku bashi yar shi ko kuma shi wanda zasu yi auren zoben idan da gaske yake ya fito ku aura masa ita kafin ku ji sun gudu." Daddy ya tari numfashita da cewa "ba fa auren zobe ba ne proporsing ne yarinta ce kawai. Dada tayo kan Daddy da faɗa "Ibrahima!Ibrahima!! Ibrahima!!! Sau nawa na kira ka? Daddy yace 3, "Toh ka fita a ido na." "ayi haƙuri Dada. Daddy da Baba suka hada baki, ta nisa ta jah fasali ta kalli Baba ta ce "Magaji ina muka kwana a maganar mu? Maganar auren Sa'adu in dai ba tsohuwar banza aka mayar da ni ba dole ya fito da mata, kai ka ce a bari ya nutsu toh kuwa dole ya fito da mata yanzu sun doshi Arba'in ga Abashiya nan yar gidan Malam liman ta gama sakandare me ake jira? kunsan Allah jikar Maryama dole ku aurar da ita." Dada tana wannan maganar Daddy ya tafi wani tunani sai ya ji kamar an saka shi a Aljanna ko wanne saurayi Umaima zata aura dole sai iyayen shi sun nemi sanin ubanta, sun yi kuskure tun kwanaki har ga Allah yayi maganar za su nemi ubanta abunda ake gudu gashi yana shirin faruwa......ina fatan kun gane muryar Dada ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi ya nisa ya kalli Dada da Baba Umma harta tashi yace "dawo ki zauna Maryama, Dada nayi wani tunani yanzun nan inaga me zai hana mu hada Dattijo da uwata shi kuma Sa'ad ya auri yar uwarshi Amira shikenan ko ba haka ba?" ALLAHU AKBAR Dada ta yi kabbara shi kenan bakin mu alekum, Baba bakin shi ya kasa rufuwa yace "amma haɗin yayi me yasa tuntuni ba mu yi wannnan tunanin ba? lokacin ne be yi ba cewar Dada, Umma daɗi ya cikata sai kuma tace "anya yaran nan za su bamu haɗin kai kuwa?ina jin Dattijo wancan ma haka yace baya so." toh da aka yi ai sun zauna ga shi harda yaro a tsakani Maryama mu muka haife su fah ba su ne suka haife mu ba." Daddy ya faɗa, "haka ne Yaya kasan ɗan yau." mu ma iyayen yau ne, Dada kawai a yanke mana lokaci duk a kira su su zo hakan yayi?" Dada ta gyaɗa Kai, Daddy ya sake cewa "amma dole zamu je wajen Aminin kakanta Alhaji Isah gaskiya yakamata su san da zaman ta abu ne ya faru na bacin rai tunda wannan zancen ya taso sai a nemo su, kirawo Darsha ta zo Maryama ayi maganar nan a gaban ta hakkinta ne ta san me ake ciki." Umma ta mike ta cewa Dada na kawo miki abun karyawar yanzu? Dada tace "Eh kam yanzu na karya na yi fitowar safe don wlh jiya ban rintsa ba, Allah dai ya yiwa Ali albarka ga shi an samu maslaha." suka amsa da Amin.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
*The quest for Love changes us.There is no seeker among those who search for Love who has not matured on the way. The moment you start lookingfor Love, you start to change within and without.”*
EPISODE 0️⃣7️⃣
Bayan kwana biyu da maganar Daddy ya kira Fahad.
"Good morning sir, Fahad ya faɗa da girmama wa, Daddy ya amsa da "morning Dattijo ku na lafiya, ya Aboki na?" fine Sir. Daddy yace "Masha Allah, ka na ji Dattijo ka yi ƙoƙari ka zo gida infact hutu nake so ma ku ɗauka kai da ɗan uwan ka is very urgent nake neman ku, shima na kira shi jiya ina tunanin gobe ko jibi zai zo, tun jiya naso kiran ka kaima sai kuma na shiga sabgogi, mun je Bichi da Babanku, are you there Dattijo?" Daddy ya tambaya jin yayi shiru, muryar sa very low yace "Yes Sir, but let's discuss the issue now please, is anything alright? hope no problem?"
"No no no not at all Dattijo, maganar mai mahimmanci ce ta baki da baki not on phone, meye duration ɗin leave ɗin ku?" Fahad yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "30days a year was planning to go for Umara during Ramadan." Daddy yace "yayi kyau ka yi applying leave kawai." Fahad kamar yasa kuka yace "But Sir Ãdil is currently in school and I don't want to distract him." Daddy ya tari numfashin shi da cewa "is not a problem do as I say."
"ok Sir."
Yauwa Daddy yace sai na ji ka ya ajiye wayar.
Fahad ya riƙe wayar, ya rintse ido yana tunanin me zai yi a gida kuma yanzu aiki yayi mishi yawa, hutu a tsakiyar shekara.
"Papa are you okay?" Maganar Ãdil ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi ya zuba mishi ido yana kallon plate ɗin da ke gaban shi, boiled egg ne aka yanka mishi into pieces sai slice bread and tea, ya sha tea ɗin half cup bread ɗin be ci ba, yace "why are you not eating?"
"I'm full Papa."
"add a little Didi." Fahad ya faɗa, da ƙyar Ãdil ya ƙara cin rabin slice bread ɗin, ya kalle shi ya ce "we are going to Nigeria." Ãdil cikin murna ya ce "really Papa? Ya gyaɗa mishi kai, ya dira daga dinning yayi tsale yana cewa "i am excited Papa pretty cool. ya matso ya miƙe a kujerar Dinning yayi mishi peck a kumatu yace "thank you Papa." Fahad ganin Ãdil na burnar tafiyar sai ya ji tafiyar bata dame shi ba.
*****
After 3 days
Umaima da Amira ke ta aiki a kitchen Barira da Baba Rabi suna taya su yau gidan a cike yake da manyan baƙi su Baban sama ne suka zo suna palour Baba tun safe suke ciki ga dukkan alamu magana ce mai mahimmanci su ke yi a tsakanin su.
"Alhamdulillah mun ma gama." Umaima ta faɗa tana buɗe pot ɗin gaban ta, brown rice, peppersoup, pepperchicken, samosa, sai salad da suka haɗa da zoɓo da kunun aya, Sasi ta zo tana jan skirt ɗin Umaimah, ta ɗauki nama ta bata ita ma ta hau cin kaza, Amira dake ƙarasa kintsa kitchen ɗin tace "Allah ya sauwaƙe miki Umaimah, dan Allah ki daina yi mana tsamen nama sai da ƙuma kike yi da hannu sai yayi tsami. "Dan ma dai ni nayi girkin, matsala ta ɗaya da ke sa ido ina ruwanki? Amira tace "Da ruwa na mana. "toh sannu Siyama." Baba Rabi tace "a dai yi haƙuri autar Umma. sallamar Sa'ad ce ta katse su da murna Umaima tace "oyoyo Uncle Sa'ad yaushe kazo ba muji ba muna nan." ya amsa yana dariya kamar yadda yanayin sa yake, Amira ta gaishe shi ya amsa da lafiya ƙalau Autar Umma su Barira da Baba Rabi duk suka yi mishi ya hanya ya amsa, ya shaƙi kamshin girki yace "kai kai kai wanne delicious ake yi mana? Yayi maganar yana kallon Umaimah, tace "Kayan daɗi." ta fada tana buɗe mishi warmer ya shafa cikin shi "har kin sa na fara jin yunwa wannnan Kayan daɗi haka? Uncle Sa'ad ka ganka kuwa? Ka yi kyau ka yi fresh." Yana murmushi yace "Allah daughter? Ta juya wajen Amira tana cewa "Ko ba haka ba Amira?" Amira ta ɗaga kai bata yi magana ba, Sa'ad ya kamo hannun Umaimah yana cewa
"yawwa daughter wai meeting ɗin nan su Daddy basu faɗa miki akan me aka taso muba? Muna tsakiyar aiki." kai da wa? Umaima ta tambaya, yace "Ni da Fahad yana hanya ma." ya kalli agogon hannun shi yana cewa "any moment from now jirgin su zai sauka." "hmmm Uncle Sa'ad kwanan nan su Daddy idan suna magana dana zo sai su yi shiru, wlh tsofaffin nan akwai abunda su ke ƙullawa, jiya Siyama na shiga ɗakinta tana waya bata kula dani ba saida ta gama wai tun yaushe na shigo? Bata ga shigowa ta ba? Me na ji duk ta gigice, kumafa da Dada su ke wayar sai da nace ni hankali na baya kan wayar ta sannan ta kyale ni, ni yanzu bana ma kula su tunda munafuka suka ɗauke ni." wayar Sa'ad ta yi ƙara ya daga kiran yace "Guy welcome back home, ok gani nan." ya kashe kiran yana cewa Amira, "Amirori any idea? Ta yi wani far far da ido, Amira yar gayu ce akwai iyayi da gwalli magana ma in zata yi saita karya harshe saɓanin Umaimah da komai nata naturally take yinsa, "not really I have no idea." Amira ta faɗa, Umaima ta saki baki tana kallon ta, shima Sa'ad kallonta ya tsaya yi, sai kuma yayi murmushi ya fita.
Fahad da Baturen ɗan sa Ãdil sun iso gidan ana ta murna da maraba. Da dare bayan an kammala cin Abinci kowa ya hallara an zauna Mami da Umma suna zaune a two sitter Sa'ad da Fahad suna kusa da juna, Sa'ad ba yadda be yi Ãdil ya zo wajen shi ba ya ƙi yau ya guji Papi sai wajen Daddy da tinda suka zo ya maƙale masa ana ta yi wa Sa'ad dariya, Amira da Umaimah na zaune a ƙasan carpet Aliyu, Ibrahim da Uncle Ismah basa nan, Aliyu ya je Lagos, Ibrahim be samu damar zuwa weekends ba, Uncle Ismah kuma ya fita.
Baban sama ya gyara zama yana kallon su yace "Toh Masha Allah." muryar sa ta dawo da hankalin kowa kan shi, ya buɗe taro da addu'a aka shafa, Ãdil da ke kan cinyar Daddy yace I want to pee. Umaima najin haka ta miƙe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 27