Volume two
EPISODE 3️⃣6️⃣
UK
Tunda Daddy ya faɗa mishi jibi zasu taho mood ɗin shi ya canja ya rasa a wanne hali yake kamar wanda aka yi wa albishir da Aljanna, kamar yadda ya faɗawa Daddy sabida makarantar Adil yake so su dawo hakan ne kuwa? Ya tambayi kanshi, gaskiya ya fara tuhumar kan shi anya wannnan ba shi ne son ba? Shi be taɓa expericing haka ba, be san soyayya ba, amma feeling ɗin daya fara ji towards her could this be love? kar dai wannnan shi ne so? Amma rabuwa za su yi, yana tunani kanshi ya ɗau zafi ya fahimci zai wahalar da kwakwalwar shi kawai ya bar komai time will tell, let everything Flow naturaĺly, amma is he ready? yayi wani miskilin murmushi ya ɗauki wayarshi yayi ordering sabon carpets da curtains aka yi mishi delivery da kan shi ya cire na dakin Umaimah masu fixing curtains su ka canja dakin yayi kyau sosai ya dade yana tunanin me zai kara sakawa dakin taji daɗi, ji yake zuciyar shi kamar takarda farin ciki yake ji from no where, ya fito daga dakin tunda dawowar yamma ce ya canja bedsheets gibe.
Washegari tunda safe ya saka Mrs Lawrence ta gyara dakin ya bata sabbin bedsheets whites aka shimfida a ɗakin, akwai aiki amma ya dauki one day off he is soo excited har ya ji ma gidan ya canja tun kafin su dawo Amma lokacin da za su shigo dole za su nemi abinci yayi wannan tunanin ya fahimci bata cin Abincin Mrs Lawrence, shi ba abinci ya iya dafawa ba he is not a foodie abinci Sam be dame shi ba, akwai wani restaurant na yan Ghana ya kira Mr charles ya aike shi ya siyo abinci, da ya dawo ya saka Mrs Lawrence ta juye a warmers ta jera a Dinning, ya dubi time in 2 hours time za su iso ya koma dakin shi sai gashi ya fito da airfreshners dinnshi masu kamshi Byredo,Voluspa, Glade ,Vera Wang duk designers ne masu kamshin gaske suna dadewa a waje ya shiga ya fesa har a jikin curtains ya shiga toilet ya fesa sannan ya fito ya rufe mata ƙofa Mrs Lawrence ta yi mishi sallama ta tafi, shima wanka yayi ya ƙara shiryawa ya fito yana kamshi suka kama hanyar airport da Mr charles
Tunda suka shiga jirgi take bacci kamar wacce ta sha maganin bacci tun daga Mallam Aminu Kano International Airport har suka iso Heathrow Airport London (LHR) ita da Aadil suna ta bacci tazarar hours din wajen 7hours ne.
Ana isowa ta mike su ka fara saukowa duk ranta a mugun ɓace yake haka kawai wani ƙunci take ji kamar wacce zata koma kurkuku, Allah ya sani ba don Daddy ne yace yau za su taho ba daa sai ta kara ko sati ɗaya ne tayi abubuwa da yawa zuwan ta yanzu ma akwai plans ɗin Business iri iri, ita kanta tsoron kanta take yi ideas pull her head tana magana a zuciya har suka sauka, suka fito wajen jiran kaya da Adil a kafadarta har yanzu bacci yake, kayanta suka fara gangarowa dake an mata numbering tun da ga Aminu kano from 1 - 8, sai boxes din su an saka mata a trolley tana fitowa ya ganta yace Mr charles ya taimaka mata tana tsayawa ta ga Mr charles "welcome ma'am."
"thankyou." ta faɗa, ya ja trolley ɗin tana bin shi a baya ya fara sakawa a boot "ina yini." ta faɗa, be amsa ba ya gyaɗa mata kai ya mika hannu ya dauki Adil hannun shi ya gogi nata ta yi maza ta janye, ta shiga baya Mr charles ya ja suka tafi, suna isa kawai ta bude motar ta fita ta san Mr charles zai shigo da kayan ta bude dakinta wani cool kamshi mai daɗi ya daki hancin ta, ta ƙara bude hancinta tana shaka tanajin wani farin ciki na saukar mata a zuciya, dakin yayi mata kyau har curtains an canja komai yayi Masha Allah, she wonder wa yayi gyaran nan haka? Saka sabbin curtains tasan kurma ne, tayi murmushi tace "su kurma an yi abin kwarai." ta gode koda yake tasan badan ita yayi ba dama gyaran shi yake yi kafin ta tafi, ta ma fi shi matsuwa su rabu yanzu, ta shiga toilet ta yi wanka ta fito ta rama sallolin da ake bin ta, ta saka kayan bacci ta bi lafiyar gado, dan ta gaji sosai hutawa kawai take son yi har ta fara bacci ta ji kamar a mafarki ana knocking ta tashi ta bude Fahad ta gani a tsaye a bakin kofa, yaɗan zuba mata duka lumsassun idanunshi sannan yace mata "wouldnt you eat something?
Ko a jikin ta tace "a'a Alhamdulillah." ta yi maganar tana lumshe ido ta juya ta koma ɗakin, ya Allah ya faɗa a ran shi yasan akwai gajiya dole ya kyale ta ta huta, haka ya kwashe warmers ɗin ya saka abincin a fridge kar ya lalace Adil ya gyara wa kwanciya shima ya kwanta ya rungumo shi jikin shi, Alhamdulillah he feels comfortable and sound, dawowarsu gidan har ya zama lively ya ƙara rungomo Adil ya yi musu addu'a Bacci ya kwashe shi.
Ta tashi sallar Asuba tana idarwa wani jiri take ji tsabar yunwa bata ci abincin jirgi ba saboda bacci gashi jiya ma haka ta kwanta ta cire hijab din ta fito kayan bacci ne a jikin ta irin three quarter wando da riga mai hannun shimi pink colour ta fito kitchen tana ta dube dube ta bude fridge ko yogurt ta sha taga abinci a cointainer ta fito da su ta yi mamaki jellop rice ce da brown spaghetti da pepperchicken ta saka a Microwave ta yi warming ta fito ta zauna a Dinning kenan Adil ya fito daga dakin Fahad yana ganinta ya nufi inda take "Maamah I'm Hungry."
Tace "go and brush your teeth ka dawo." ya tafi be dade ba ya dawo ta saukar musu da shi ƙasa sam ta manta da warning ɗin shi suna cin abinci ya shigo da sallama daga masallaci yake idon shi a kan su Adil ya tafi da gudu yayi hugging ɗin shi "Papa we are back, I miss you Papa."
I miss u too Didi. ya ja mishi kumatu dan kumatun na shi kamar an hura, "barka da safiya ta faɗa tana juyar da kai gefe, "morning." ya ce ya zauna a kujerar da take facing ɗin su, Adil ya koma suka cigaba da ci tana bashi, kallon hannunta yake yi masha Allah kunshi ja da bakin lalle a bayan hannunta kamar tatoo aka manna, hannun yayi lukwui lukwui ta yi wani fresh idan ya ga zasu hada ido sai yayi maza ya mayar da idon shi kan TV, amma hankalin shi yana kan su, wai gaskiya suna cin Abinci, yaron daya ke fama dashi akan cin abinchi kamar an canja shi yana tunanin yaji tace "oya let's go." ta tashi ya kalli ƙafarta lallen yayi kyau sosai kamar an ɗora shi, ta mike ta yi hanyar kitchen she is careful ba su lalata wajen ba har ta zo zata wuce shi yace "I need a glass of water." kamar ta ji yayi mata magana tace "Ni."
"Yeah."
Ya faɗa, ta tafi ta dauko bottle water da cup ta ɗora a tray ta ajiye a gaban shi, "No no not that, glass cup." ya faɗa, ta ɗauke wanda ta kawo ta koma kitchen, tana mita a zuciyarta ina ruwana ne da kai, ta ajiye mishi glass cup har zata tafi yace "wait." ta dawo ta tsaya a gaban shi tana turo baki irin ka dame ni ɗin nan, tana hararar shi ta kasan ido ya ganta amma ya basar yace "make me a cup of coffee." kawai ya ji bakin shi ya faɗa, he just want her around him.
Cikin sakalci da shagwaɓa tace "ni gaskiya ni gaskiya." ta bubbuga ƙafa a gaban shi, ya Allah ya faɗa a ran shi, ta juya kamar da gan gan take juya mazauna ta ta dan dade kadan ta dawo da ƙaramin tray da mug a kai tana ajiyewa ta zura da gudu ɗaki kar ma ya yace tamai wani abu, sai abun ya bashi dariya, kawai hannunta ne da kafafunta yake kallo amma shi yaushe zai ci abunta, ya dauki tray ɗin da ta dora mug din coffee din yana ta tiriri kamar wanda aka umarta wata zuciyar tace dan sha ka ji mana, wata zuciyar tace kai wannan me ta iya? sai kamshi yake yi haka kawai zuciyar shi ta aminta da ya ɗan sha kaɗan mana ka ji idan da daɗi, ya rintse ido yayi sipping ya ƙara, "is it real? Ya ƙara sha anya kuwa? Wannnan coffee ɗin a prufrock kawai yake shan irin shi, daya ke yana zuwa ya sha yana daga mug ɗin ya shanye ko dai wani yayi mata, toh amma su kaɗai ne a gidan, ko Mrs Lawrence once in a while yana sata ta haɗa mishi amma ba haka take yi ba.
Gaskiya be ishe shi ba ya tayar mishi da son ya ƙara sha ya tashi yayi knocking ɗakin, "Adil ka je ka saka uniform tunda mun gama wankan." ta fada tana daga kwance be jira an bashi izni ba kawai ya shigo ta tashi zaune dan bata yi tsammani ganin shi ba "who made that coffee?" ya tambaya ji wani rainin hankali ta faɗa a ranta . Ya kara maimaita tambayar, sai cewa ta yi "kai ne ka yi." ta juya mishi baya, yayi murmushin gefen baki ya daɗe a tsaye yana kallon ta, wato magana ta faɗa mishi ta dauka ya fita ta dago suka haɗa ido ya kawar da kai ya juya ya fita.
Saboda kifadi irin nashi ya kasa cewa ta yi mishi wani.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 3️⃣7️⃣
Fahad ne ke tunanin yau kwanan su biyu da dawowa amma yarinyar nan ta share agreement ɗin su, toh me take nufi? tana nufin shi zai je ya neme ta kenan? haka last month tunda aka yi sau ɗaya sai da dabara ya sake, haka ake agreement? Meyasa tayi creating abinda ba za ta cika ba? Mtws she is not serious tana nufin shi zai kai kan shi kenan? ya ga kamar harkokinta take yi, yayi murmushi daya tuno jiya ya shigo ya tarar tana juyi da kuɗi a hannu tana murmushi, she likes money.
"Sir we are done." muryar Mrs Susan ta dawo dashi daga duniyar tunani, ta miƙa mishi files ɗin ya duba ya kalleta "thankyou, I will get back to you."
"OK sir."
ta nufi kofa ta fita, ya cigaba da crosschecking files ɗin aikin har ya dauke lokaci mai tsawo, ya gaji sosai yunwa ya ke ji dama abincin shi coffee ne sai biscuits idan yana sha'awar solid food yana zuwa Ledbury restaurant yayi ciye ciyen shi shima bana kirki ba, ya kira secretary ta haɗa mishi coffee bata dade ba ta kawo shi yana turiri yana aiki ya kai baki yayi sipping kwata kwata be yi mishi daɗi ba salam yawun bakin shi ma yafi wannan coffee ɗin daɗi, ya ajiye kawai, coffee din ta kawai yake so tunda ya sha shekaran jiya yayi mishi daɗi sosai, ya so tayi mishi jiya amma kwata kwata be ga fitowarta ba sai ta murnar kuɗi suna haɗa ido ta gudu ɗaki ya dai ji karar kekenta.
Ya gama duba files ya rufe kawai ya haɗa System ɗin shi ya dauki phones din shi da key ya fita.
Ãdil why are you bored?tunda ya dawo daga makaranta ta kula he is moody abinci ma kaɗan ya ci yace mata ya ƙoshi, ta kunna wayar ta ta saka musu waka, tace "oya tashi mu yi rawa." ta saka wakar baby shark saboda Iman ta saka wakar a wayarta ta riƙe hannun shi tana jujjuya shi tun daga entrance yake jin wakar ya shigo da sallama ya gan su suna rawa ya girgiza kai ko sallamar da yayi ba su ji ba tana wani juyi suka haɗa ido da sauri ta kashe wayarta "sannu da zuwa?" ta faɗa, ya tsaya yana kallonta sai da suka haɗa ido ta tuna da kayan dake jikinta croptop ce iya cibiya da boomshot a jikinta, da sauri ta ja hannun Ãdil suka shige ɗaki ya daɗe a tsaye a wajen sannan ya wuce ɗaki yana cewa "silly girl, ita haka ake welcoming miji."
"miji." zuciyar shi ta ƙara tuna mishi, kai da rabuwa ma za ku yi, haka ne fah rabuwa za su yi, she needs to do the needful ko sa yi su rabun ma yau dai zai yi mata magana day 3 kenan of her ovulation day.
Suna shiga ɗaki ta jawo Ãdil jikin shi ta ji zafi ram hankalin ta ya tashi, ashe baya jin daɗi shi yasa ya zama moody sai tattaba jikin shi take yi "sannu Didi, sannu kaji." ta kwantar da shi ta saka Abaya ta fita tayi mishi knocking ɗaki kamar jira yaje yi ya buɗe, "hmmm Adil baya jin daɗi." ta faɗa a rude, "what happened?" ya tambaya "he is moody tun ɗazu yanzu kuma jikin shi da zafi." tana faɗa ta koma wajen shi ta dauko shi ta dawo falo ta zauna tana jiran shi, be dade ba ya fito ta dauke shi suka fita ya bude mota ta zauna a baya tare da Adil, ya so ce mata ta dawo gaba amma dai ya rabu da ita.
Direct Nuffield heath leeds hospital sukaje Dr zai yi examing ɗin shi tunda file ɗin su a nan yake, suna shiga office ɗin Dr nurse ta zo daukan blood sample yana cinyar Umaimah har yanzu, ta rike hannun nurse ta kankame Adil tace "wlh da zafi." ta runtse ido, nurse tayi dariya tace "it wont hurt I promise." ta ki bari Dr yace "is just blood sample relax pls." shi dai kallon su yake yana gulmarta a ran shi tafi me ciwon tashin hankali ya ga dai zata ɓata musu lokaci ya matsa kusa da ita ya ce "calm down it wont hurt ok." ta gyaɗa kai tana hawaye ta kankame hannun shi, da kyar aka ɗauka jinin, nurse ta fita tayi kamar 15min results ya fito malaria ce dama yayi tunanin haka tunda idan tare suka yi tafiya Nigeria yana taking precautions, an rubuta musu magani da allura da za a yi mishi an zo yin allura Sam Umaima tace sai dai ya sha magani aka yi ta fama da ita "I want to ease myself Maamah." Adil ya faɗa, Fahad ya ɗauke shi daga hannunta ya fita nurse ta rufa musu baya ya kai shi fitsarin nurse tayi mishi allura, kukan shi ta ji ta fito da sauri ta nufe shi "menene? Menene?duk ta rikice shi dariya ma ta bashi "relax he will be fine." ya fada Adil yana hannun shi ya rinƙa miƙa mata hannu ta karɓe shi suka tafi gida.
Suna zuwa gida tayi mishi wanka da dabara take bashi abinci yana Dinning yana kallon su yadda take lallaɓa shi abincin ma a cinya ta ɗora shi take bashi "yauwa Didina ɗan ƙara, ƙara ka ji ɗan Maamah." ya bude baki, tace "yawwa zaka sha juice? ya ɗaga kai ta tashi suka wuce shi ta zuba mishi a cup ya sha tace "toh ya isa." dama magungunan shi a wajenta suke ta rinƙa bashi daya bayan daya yana sha har suka gama tana ta shafa shi sai ya fara ƙananan kukan rigima a ruɗe tace "ina yake maka ciwo? Sannu kaji." yana kuka tana hawaye "yi hakuri ka ji?"
Son yara dabiar ta ce tana bubbuga shi har yayi bacci dama rigimar bacci ce, ta ajiye shi ta harhaɗa maganin ta dawo ta ɗauke shi, ta shige daki, Fahad ya bita da kallo, yace "No wallahi bata isa ba." ya harhada kayan shi ya shiga dakinshi, ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya a wasu Ralph Lauren night wears ya fesa turare ya tayar da sallah ya idar ya fito daga dakin ya nufi dakin ta yana buɗewa ƙofar ta bude bata saka key ba yayi switching light tana kan gado wata peach rigar bacci ce a jikinta mai santsi ta rungume Adil kamar zata mayar shi ciki ya dade yana kallon su wani farin ciki ya kama shi har kasan zuciyar shi, ya sunkuya cikin dabara zai dauke shi ta kara kankame shi ya dan tsaya ta cigaba da bacci da hikima ya dauke Ãdil ya kai shi dakin shi ya rage mishi Ac ya rufe mishi kofa ya fito ya nufi dakin ta ya kashe wutar ya matso kusa da ita ya rungume ta acikin jikin shi, kamar a mafarki ta bude ido ta fara shafa fuskar shi "Adil."
ta kira, ta kara shafa fuskar shi ta ji kamar ba shi ba ne ta ƙara kiran shi a rikice zata tashi yayi mata faɗa a kunne "you took Adil away from me, I need my own baby."
Ta bude baki zata yi magana ya haɗe bakin su da sauri yana sauke wata ajiyar zuciyar a bakin ta.
Umaima tunda Munnirah ta bata kayan gyara ta saka a gaba ta rinka ci harda dambun kaza da su gumba sai ta mayar shi abun kwaɗayi.
Subhanallah yau kam Fahad ya manta home training jijiyar kan shi ta mike wani irin yanayi ya shiga daya manta a wace Nahiyar yake ne a cikin duniya, Sarrafa ta kawai yake yi babu kakkautawa, mazantakar shi ta motsa, wani irin feeling da be taɓa expericing ba a rayuwar shi ya bijiro mishi Umaima tun tana ɗaure wa har ta fara kuka muryarta ta dashe, gabadaya notikan kan shi sun kunce wasu irin surutai yake yi kamar shirme, "Zahraah! Zahrah ta ce ke?"
Ya faɗa yana jijjjiga ta kuka take yi shima kukan ya ke yi da gaske, surutai yake yi harda su thank you Daddy, Nagode Baba, ya kankame ta kamar zai mayar da ita cikin jikin shi, sai kuma jikin shi ya saki, surutai yake yi ni kaina me dauko muku rahoto abun ya bani kunya na rufe musu ƙofa nayi nawa waje.
Kiran Assalatu ne ya tayar da shi a cikin sauran hasken ɗakin yake kallon fuskarta gaba ɗaya a cikin jikin shi take ta wani cure baki taɗan turo shi gaba, a hankali ya miƙe ya zauna ya kunna side lamp ya kurawa dakin ido duk dunyi pieces din ɗankin sun watsar da bedsheets da blanket a ƙasa sai ya ji kunyar abinda ya faru ta kama shi, ya kalle ta zuciyar shi na budewa ya ƙara kura mata ido ya kai lips ɗin shi zai yi mata kiss ta buɗe ido ya maze, yace "wake up its subh." A sakalci ta murguɗa miki baki ta juya baya, yayi murmushi ya fita daga ɗakin ya leka Adil ya ga har yanzu be tashi ba ya tafi dakin shi ya shiga toilet oilet.
Yana fita ta sauko da kyar jikinta ko'ina ciwo yake mata, wlh mugu ne mutumin nan, ta fita da ƙyar ta iya daukan Adil yana bacci ta dawo dashi wajen ta, ta shiga toilet ta yi kwanka, tana fitowa tayi sallah, tana idarwa ta nufi kitchen tayi toasting bread ta haɗa komai a tray ta shiga ɗaki ta saka key, yinwa take ji kamar an yi mata sata sai da taci ta koshi ta ji ana knocking.
Mrs Lawrence ce zata shirya Adil ya tafi makaranta tace ba zai je ba bashi da lafiya. Bayan ta gama cin abincin tana shiryawa ya zo yayi ta knocking ta yi mishi banza ta gane shi ne ta ji foootsteps ɗin shi dan haushin shi take ji yayi mata mugunta saura kaɗan ta yi mishi Allah ya isa, haka ya gaji da knocking ya tafi office, yau jinshi yake sakayau ga wani farin ciki dake mintsinin zuciyar shi, kwakwalwar shi kamar an wanke ta da soso da sabulu wani irin karkashin aiki yake ji, wani karfi yake ji daya rasa daga ina yake zuwa haka yayi ta aiki kamar workaholic sai dai idan ya tuno wani abun daya faru jiya sai yayi murmushi wani farin ciki yake ji har karkashin ran shi, shi kan shi ya bawa kanshi mamaki dama yana da irin wannan urge ɗin? sex be dame shi ba amma shi yanzu kamar wani sabon mutum haka yake jin kan shi, "anya shi ne kuwa ya tambayi kanshi?"
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 3️⃣8️⃣
Tun daga ranar kuma Umaima ta fara wasan buya dashi bata sake bari sun hadu ba, har ya tafi aiki ba zata buɗe kofa ba kafin ya dawo kuma ta gama duk abinda zata yi tayi shigewarta ɗaki ta kulle, sosai ta mayar da hankali a sana'ar ta don sosai take samun order tana karɓar kudinta, amma yau kam tunda kwanakin ovulation period ɗin ta ya wuce zata fito ai agreement ne ita ma ta gaji da zaman ɗaki, dan haka ta shirya ta fito da wani material ta yanka kiran Aunty Ramla ya shigo wayar ta suka gaisa, Ramla tace "zan yi kokari na shigo yau akwai dinkin da neigbour dina ta bani na kawo miki, akwai masu son Alawar madara ma."
"Toh Aunty Ramla sai kin shigo." suka yi sallama tana murna ta mayar da hankali akan yanka da take yi, dan yan diaspora ne suka kawo ashoben biki kuma cikin satin nan ne taci ƙarfin aikin ta yi yafi rabi kawai idan yana gida ne bata yin dinki kamar yadda ta yiwa Uncle Sa'ad alkawari.
"kai wannan iko Allah yasa dai an dace. Ko tayi tafiyar ta ta cigaba da harkokinta wannan takura har ina.
"Aunty Ramla wai tun yanzu zaki tafi?
"wlh na bar yara kinsan tare muke da sister na, toh ta je Katsina yaran su kaɗai ne a gida tin da mun gama gara na tafi, idan da wani abu zamu yi waya.
*****
Ya dawo aiki yana ɗaki wasu files yake dubawa ya ajiye, hmm yarinyar nan ta raina shi kwata kwata basa haɗuwa yau kusan 3 days kenan be saka ta a ido ba ya shafa kan shi, "tayi polluting min shi Adil idan yace ya kirawo ta sai yace tayi bacci." baya son matsawa yaron da tambaya idan shi yayi knocking bata buɗewa amma idan Adil ne tana buɗe mishi zata mayar da kofa ta rufe, amma ba komai zai yi maganin ta a haka zata samu cikin? Ya shafa kan shi yayi murmushi ba zai yi ƙarya ba he miss it and he is yearning for more, wannan tunanin kaɗai yasa tsigar jikin shi ta tashi, ya haɗa files ɗin gefe ya shiga toilet ya sakarwa kan shi ruwan sanyi dole ya ɗauki mataki akan ta ta raina shi, amma zai nuna mata a gaba yake da ita, to me yasa ka damu da ita? wata zuciyar ta tambaye shi.
"ita ta kawo condition kuma dole ta cika.
"ai ovulation period ya wuce."
Yayi tsaki ko ya wuce dole ya karɓi haƙƙin shi, haƙƙin ka? Ba rabuwa zaku yi ba? Ya kasa cigaba da tunanin ya daura towel ya fito.
Suna sallama da Ramla ya fito daga dakin shi sai kamshi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 27