with having cat in my house, who brought it?" tayi funfurus dashi ya ƙara ƙulewa, sai kuma yayi ajiyar zuciya lallai yana da aiki a gaban shi, Umaimah ta ɗaga cup ta shanye sauran kununta yana tsaye ta yi gyatsa Ãdil yace "bless you."
Ta ware ido "kai Ãdil wa ya koya maka addu'ar nan? yarhamakillah zaka ce."
Fahad da ran shi ya gama ɓaci ya ɗauke Ãdil, ya fara kuka yana miƙa mata hannu suka shige ɗaki ya buga ƙofar da ƙarfi, yace "will you shut up." ya mishi tsawa, yaushe ma ya saba da ita shi da baya sabo da mutane during weekends yana fita dashi office a yi ta mishi wasa ya ƙi kula kowa, amma ji yadda ya sake da ita.
"Papa take me to Maamah." Maamah ya fara kuka yana kiranta, Fahad ya ji kan shi ya Sara baya magana da yawa amma this small clown ta saka shi ihu, ya kalli Ãdil ya haɗa rai yace "go and lay down." yana shashekar kuka ya hau gadon ya kwanta sai ajiyar zuciya ya ke yi a haka bacci yayi gaba dashi.
Yana ganin yayi bacci ya shiga toilet ya wanke ya fito kenan wayar shi tayi haske kiran Daddy ya gani a screen din wayar.
Tun jiya yake ganin missed calls din Daddy ya kira shi back bata shiga ya san akan wannan lousy girl ɗin ne yasan kawai bacin rai ne bari ya gama aikin shi idan ya gama ya kira ta kar a ɓata mishi mood ya kasa aiki, be gama wannan tunanin ba wayar ta ƙara ringing Daddy ne ya ɗaga suka gaisa.
"Dattijo lafiya baka ganin missed calls dina ne? "No sir I couldnt reach you."
"toh kuna lafiya ina uwata? ina Ibrahim? Yawwa ka na ji ko bata wayar zamu yi magana." babu yadda zai yi Daddy har ya yi switching vedio call ya fita yayi knocking ɗakin shiru, ya kalli Daddy yace "I think she is sleeping. "No ka shiga ɗakin mana, go and check."
kamar baya so ya murɗa ƙofar ɗakin ya shiga ta baza kaya a tsakiyar ɗakin, tana zaune akan gado ta rufe idonta da kyalle hide and seek suke yi da Sasi jin anyi motsi tayi wajen tana lalube taji ta shafa mutum ta bude ido wani mugun kallo yayi mata ya miƙa mata wayar tana ganin Daddy ta saki ihun murna kan shi har ya fara juyawa ya kalli ɗakin ya girgiza kai ya juya ya fita dan har numfashin shi ya fara wani iri ya zauna a falo yana jiranta ta gama ta bashi wayar shi, "yeee Siyama ta fada da ƙarfi sai kuma ta fara kuka." yana ji ana ce mata idan kuka za ki yi zan kashe. ina Uncle isma? Ina Tasiu Baba kace wa Uncle Ismah su yi lissafi da Tasiu, ace Isiyaku ya bawa Uncle Isma breakdown na abunda ya kashe na kayan shagon DIJAH COLLECTION."
"kwantar da hankalin ki za a baki sim zan yi wa Dattijo magana sai mu yi maganar sosai"
"toh Daddy wlh shiru gidan babu daɗi Sasi ce take ɗebe min kewa." "zaki saba ina Dattijon?" Ta fito ta miƙa mishi wayar ya karɓa yayi shigewar shi ɗaki "kai wannnan da baƙin hali yake." ta taɓe baki."
*****
NNPC Housing Estate Pothacourt
Come close my love Sa'ad ya fada wa Amira ta matso yayi mata peck a kumatu yace "thanks for yesterday." ya kashe mata ido ta rufe idonta yayi dariya ya ja hannunta suka fito compound riƙe take da basket ɗin Abincin shi ya shiga mota tana tsaye yace "take care of yourself for me." ya ja motar ta yi mishi waving sai da motar ta fita daga gate ta dawo ciki, Sa'ad is so sweet ta rungume pillow tana blushing ashe da shirme ta yi sai yanzu ta yarda da Umaima akan ɗan Iya gaskiya ne, ko kusa ba za a haɗa Sa'ad da ɗan Iya ba innaah ta girgiza Kai, da ta tuna kunnuwan shi ta girgiza Kai Masha Allah ɗan Iya akwai kunne sai yanzu ta ga munin shi, tace "Allah ya sakawa Iyayen mu da alkhairi." ta gyara kwanciya sosai tana tuno daren jiya tana murmushi har bacci yayi gaba da ita.
Kano
Umma jikin ta yayi sanyi Baba ne yake waya ta fuskanci da Khadija ne yana ta bata baki "cuta ba mutuwa ba ce ki kwantar da hankalin ki muma muna hanya in sha Allah zamu zo duba sa, ko jiya mun yi maganar zuwan, ga Umman taku ku gaisa." Umma ta karɓi wayar muryar Khadijan a dishe irin mutum ya sha kuka, tace "ki yi hak'uri Yayarsu ke dana ke cewa kin fi kowa dauriya Allah ya bashi lafiya yi hak'uri kin ji kar kisa damuwa a ran ki Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗun shi muna hanya in sha Allah." suka ajiye wayar Umma ta kalli Baba da jikin shi yayi sanyi tace "Baban su ya kamata a shirya tafiyar nan kwanan nan. "za a yi in sha Allahu, kwangilar mu ce ta fito ta Abuja sai dai Alhaji shamsu yayi handling kafin na dawo wani uzurin ya danne wani bari za mu ƙara magana da Yaya Ibrahim, kawo min furar ko ba a dama ba?" "Ah ah anyi tana fridge." Umma ta miƙe ta fita.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣3️⃣
Duka wani shirye shiryen tafiya duba Mijin Khadija ya kammala tafiyar ta su nan da kwana biyu ne Baba da Daddy Umma da Mami su huɗu sun yi magana da Khadijah an yi admitting din shi a India, Umma ke waya da khadija take sake kwantar mata da hankali Munnirah ta shigo, Umma ta aje wayar tana mata maraba, ta gaishe da Umma, tace "wlh gudowa nayi daga aiki na gaji." "A'a Munnirah a rinƙa kamantawa dai. "wlh Umma tun sassafe muke ta abu ɗaya har wani jiri jiri nake ji na ɗauki excuse na taho nan."
"To Allah ya taimaka ki je kitchen masa muka yi nasan kina so." "wlh kuwa na zo a dai dai, ƴa ta ta kira ni jiya ta yi layi ashe? "hmmm wannan shashashar ƴar taku tunda ta yi layi bata la'akari da banbancin lokaci tsakar dare take kiran mu, dana gane yanzu idan zamu kwanta kashe wayoyin nake yi gaba ɗaya Hakimi ne yanzu bata barin shi yayi bacci, can su karata." Munnirah tana daria ta miƙe ta fita.
UK
Yauwa Isyaka ka saka mun ribar a dollar account ɗina a cire kuɗin accessories da za a siyo ka tambayi nawa ne kuɗin ticket da visa na Dubai ɗin gara mu fara siyowa da kan mu, mu zama International kawai, kuma akwai varieties acan nawa ne balance ɗin daya ke account?" Umaima ta tambaya, tayi shiru tana sauraren shi, "yawwa a riƙe Amana kasan ƙanin mahaifiya ta manager ne a bakin ƙwandala aka cire yana turo min details ɗin komai, bana wasa da dukiya a kula yawwa suka yi sallama." Kwanciya ta yi tana mirgima a gado tana murna ta haɗa first million ɗinta kai masha Allah ta zama milloner ta zama Hajiya sai ta tashi ai kuwa akwai atamfofin da materials ɗin da ta saka Barira tayi mata packing tace zata fara ready to wears anan, lokacin nemo cousin ɗin wizard da ke aure anan UK yayi tunda ta san mutane, ta fara binciken Ghana must go ta fito da su, amma akwai matsala babu keke kai ita fah dole ta nemi abun yi ta gaji da zama haka can ana haɗa mata kan dukiya nan kuma tana kama pounds ɗin ta don ma Isiyaku akwai Amana babu wani Babangida da yake duba mata komai kawai barazana ce.
Washegari da safe
Mrs Lawrence ta shigo shirya Ãdil ya tafi makaranta yanzu baya kwana a ɗakin shi sai na Umaima tana ta knocking Ƙofar ta ji shiru.
Shi bature idan ba a bashi izini ba baya shiga waje, ta koma dakin Fahad ta yi knocking ya buɗe ta yi mishi bayanin ta yi knocking shiru ya buɗe ɗakin ya shiga ga sababbin kayan data fito dasu jiya nan a zube kamar me siyar da materials da Atamfofi suna kwance a tsakiyar gadon ƙafar Ãdil a kan cikinta hannunta ta dora a wuyan shi, wasu gajerun kayan bacci ne a jikin ta wandon da kaɗan ya wuce pant tsayi, gashin ta ya barbaje ribos ɗin yayi nasa waje wuyarta a karkace, Fahad ya tsaya yana kallon su haushi ya kama shi ya ɗauki Ãdil har ya juya zai fita sai kuma ya dawo ya gyara mata wuyan ta daya karkace, ya sake ƙarewa ɗakin kallo yayi tsaki ya fita ya miƙawa Mrs Lawrence shi ya koma ɗakin shi ya ƙarasa shiryawa.
"No not this I want beans cake and kinew." Ãdil ya faɗa yana kallon Mrs Lawrence data gama shirya shi ta haɗa mishi lunchbox ɗin shi, "what Didi?" oat aka dama mishi da plaintain, ya sakawa Mrs Lawrence kuka shi beans cake and kinew (kunu), tace "I don't get you Didi you are almost late."
Ya tafi ya buɗe ɗakin Umaimah "Maamah wake up wakeup Maamah I want beans cake." yayi ta girgiza ta, Mrs Lawrence ta taso tana mishi magana yayi banza da ita, Fahad ya fito ya haɗa copee yana sha ya ji muryar Ãdil a ɗakin Umaimah ya bi shi, "come here." ya faɗa, "Papa I want beans cake and kinew Maamah promise me pls Papa." ya ja hannun shi ya zaunar dashi yace "eat." ya faɗa mishi, ya ɓata fuska zaiyi kuka ya kalle shi yarinyar nan ta ɓata mishi yaro Ãdil mai jin magana ne yaron shi baya surutu barkatai amma jiya daya sashi a gaba da magana sai da ya kunna mishi cartoon ya kyale shi da surutu yanzu kuma wata rigimar ya koya, "I don't want this Papa, I want kinew." sai yanzu ya gane kunu yake nufi ya kalle shi yace "I want to tell you something, I want you to be a good boy, I don't want that girl to distract your studies stay away from her okay." ya gyada kai aka yi horn Mrs Lawrence ta fita da shi.
Yana dawowa daga school yayi kan Umaimah dake kwance a falo da gudu ta rungume shi tana faɗin "Oyoyo My boy."
"Maamah I'm mot happy with you." "da a ka yi me? ta faɗa, ya kalle ta be gane ba, tace "oh dole fah ka iya Hausa, what happened?"
Ya faɗa mata dalili, tace "sorry I will make it up next time."
"thank you Maamah."
Mrs Lawrence tayi tayi dashi ya taso tayi mishi wanka yaƙi, Umaimah ta cire masa uniform ɗin ta barshi da gajeran wando da white singlet suka baje a falon sunata sha'anin su.
Fahad yana office aiki ya mishi sauƙi ya haɗa tea yayi connecting CCTV ya san Ãdil ya dawo Allah ya sa ya ji abunda ya faɗa mishi, ya duba falo babu kowa, ya koma kitchen Mrs Lawrence ce ke wanke wanke ya koma ɗakin Ãdil nan ma babu kowa ɗakin Ãdil na da ya koma can ya gan su suna cin abinci yayi zooming Ɗanwake suke ci.
"hmmm Maamah is yummy." Ãdil ya faɗa ya ɓata bakin shi da manja, "Maamah Ãdil ya kirata, Fahad ya ƙara volume "Maamah I want to tell you a secret." Tace "ok I'm all ears."
"Papa said I should stay away from you." Au haka yace wannan mutumin sarkin faɗin rai da kafiɗiri.
"what was that?" Ãdil ya tambaya, duk yayi staining jikin shi da maiko, baƙin ciki ya kama Fahad yayi switching system ɗin "this is bullshit."
Suna gamawa Umaima ta hau neman Sasi suna ta neman ta Ãdil yana taya ta, ta tambayi Mrs Lawrence tace bata ganta ba.
Yau be dawo da wuri ba ya shigo gidan a gajiye be nemi Ãdil ba ya san yana wajen Umaimah, Mrs Lawrence da take mopping a falo ta yi mishi sannu da zuwa ya amsa ya wuce ɗaki wanka ya ke so yayi danya gaji yana bude ɗakin wani irin wari ya daki hancin shi, ɗakin da ɗan duhu ya kunna fitila me zai gani Sasi ce tayi kashi a tsakiyar gadon shi ta koma gefe tana bacci, "to ya aka yi ta shigo mishi daki." Ya tambayi kanshi, ko ta shigo ya rufe ta a ciki be sani ba? Idon shi yayi jawur, jijiyar kan shi ta daga da sauri yayi toilet yana amai jikin shi sai gumi ke tsirtsirfowa.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣4️⃣
Yana fitowa daga toilet ɗin yayi waje ya kira Mrs Lawrence a kitchen yace mata "follow me." ta biyo shi bata taɓa shigar mishi ɗaki ba sai yau ya bata hanya ta wuce Sasi idonta a rufe sai jijjiga ta ke yi irin na mage, yace "I need you to take the cat out of my room ASAP, consider her as a gift." da murna ta ɗauke Sasi ta cure bedsheet ɗin yace ta saka shi a trash don babu maganar wanki, tana ta murna bature da son pet tayi mishi godiya ta ƙanƙame Sasi tana Meow Meow suka fita daga gidan dan ta gama aikinta na yau sai gobe kuma, Umaimah na ɗaki suna bacci da Ãdil bata san wainar da ake toyawa ba.
Ya zauna a falo ya dafe kai yayi ordering sabuwar katifa a company ba a fi 30mins ba aka yi mishi delivery, suka fita da tsohuwar aka saka sabuwa yayi wa ɗakin gyara na musamman har curtains ya canja ya gyara gadon ya wanke toilet aikin ya ja shi lokaci ya shiga yayi wanka, bayan ya fito ya shirya ya dauko turaren shi prada L Homme ya fesa ya dauki Gucci pour Homme ya fesa a singlets da boxes ɗin shi, turarukan shi duka designers ne bayan ya shirya ya ɗauko fresheners a toilet Airwick freshmatic da oil diffuser ya fesa a ɗakin ya ƙure Ac sannan hankalin shi ya kwanta, ya daidaita sallaya ya tayar da sallah yana idarwa ya ji an buɗe ƙofar a hankali Ãdil ne ya shigo.
"Papa I'm glad you are back I have been staying away from Maamah just as you told me."
Fahad ran shi ya ɓaci kawai ya tsaya yana kallon shi wato har ya iya ƙarya, Sam Ãdil baya ƙarya me ke nan? ya kalle shi singlet da wando ne a jikin shi duk yayi staining ga dukkan alamu bacci yayi singlet ɗin duk tayi squeezing, "Papa I stay away from her trust me." ganin Fahad ya ƙura mishi ido yana kallon shi, har zai ƙara magana yace "shut up you lier." ya faɗa da tsawa, yaro zai raina mishi hankali yaushe aka haife shi? idon shi ya ciko da hawaye yace "I'm sorry Papa."
"now tell me why did you lie to me."
"but papa I like her." sai hawaye ya ziraro mishi, sai kuma tausayin yaron ya kama shi dole yana buƙatar motherly love "its okay." har zai yi hugging ɗin shi ya ga he is dirty ya riƙe hannun shi suka shiga toilet.
Washegari Umaimah ta zame jiki ta tashi ta gyrawa Ãdil kwanciya, ta kalli gadon gaba ɗaya sun wargaza shi da wasan da sukayi kan suyi bacci duk sun jeho da pillows ɗin ƙasa.
Materials da atamfofin ta tattara babu wani arranging ta watsa su a sif ta rufe, toilet ta shige tayi wanka tana fitowa ta tsaya a gaban mirror tana kallon yadda skin ɗin ta ke wani glowing ta sake yin fresh kodan babu inda take zuwa yanzu saidai taci ta kwanta, babu ranar BUK, mai taɗan shafa sama-sama tasa kwalli ta sa powder kaɗan tasa white lipstick, Sif ta buɗe ta ɗakko wata coffee ɗin doguwar riga mai roba tasa, rigar bata kai mata ƙasa ba amma ta wuce gwiwa ta zauna a jikin ta tayi mata masifar kyau, kashinta ta sake tajewa tayi parking ta fito daga ɗakin tayi kitchen. Suka gaisa da Mrs Lawrence ta shiga store Allah ya taimake ta ta samu indomie ko buɗe ta ba'ayi ba ta fasa kwalin ta ɗauko guda biyu ta fito, Mrs Lawrence na tsaye tana kallon yadda take aikin sosai ta burgeta, a zaman su da A'isha bata fiya shiga kitchen ba in ka ganta a kitchen to wani abun zata ɗauka, amma wannan fine lady ɗin is different tinda tazo gidan ko ruwa bata taɓa cewa ta kawo mata ba, komai ita take abinta sai dai inta gama ta barta da wanke wanke da gyara kitchen.
Umaimah na girkin tana tunanin inda Sasi ta shige,wata zuciyar tace ki tambayi me gidan tsaf zai ɗauke miki ita, tana gama dafa hadaddiyar indomien data cika gidan da ƙamshi ta zuba a plate ta buɗe fridge da dau ruwan sanyi ta fito, ɗaki ta koma har yanzu Ãdil bai tashi ba ta ɗauko wayar ta ta dawo falo ta zauna tana cin indomie tana chatting dasu Sadiq wizard a group ɗin su, tana gama cin indomien ta miƙe akan carpet plate da robar ruwan na gefan ta.
Tana kwance Fahad ya shigo ya ɗan tsaya yana kallon plate da robar ruwan ransa a bace ya ƙaraso kanta yace "hi didn't I old you bana son kina cimin abinci anan?"
Umaimah ta daga kai ta kalle shi ya wani haɗa rai kawai saita maida kanta ta ci gaba da chatting ɗin ta, "kut me yarinyar nan take nufi ne?"
Kamar ya sake mata magana kuma saiya fasa ya kira Mrs Lawrence yace ta kwashe plate da robar ruwan.
Yana ƙoƙarin barin falon wani tunani ya faɗo wa Umaimah da sauri ta miƙe tayi wajen shi kawai sai ganin ta yayi a gaban shi yaɗan matsa baya kaɗan, tace "dan Allah ka bani Mage na?"
Fahad kawai ya tsaya yana kallon ta "how dare her? Har tana da got din tambayar sa Magen ta, yanzu ya gama yi mata magana tayi masa banza shine saboda rashin kunya zata tsare shi tana tambayar shi Magen ta. Ya zagaye ta zai shige ɗaki, wata zuciyar ta cewa Umaimah kinga wannan mai mugun halin in baki lallaɓa shiba Sasi tasha ruwa ke nan, yo a banza ma kika yi daɗin baki bare akan Sasi, kai tsaye Umaimah tabi shawarar zuciyar ta yana ƙoƙarin shigewa ɗaki kawai ta riƙe mishi hannu da sauri, Fahad mamaki ne ya ƙamar dashi a inda yake, ta zagayo gaban shi ta wani kwantar da murya tace "please Uncle Papa mai kirki dan Allah ka bani Sasi na kaga ita kaɗai ce ƙawata please."
Tayi maganar idanunta a cikin nashi, ganin ko motsi baiyi ba ta sake matsawa kusa da shi, ɗan gab ɗin dake tsakanin su baifi yatsa ɗaya ba ta riƙo ɗaya hannun shi freely tace "please Papa mana"? Ta faɗa tana jijjiga hannun shi sai kuma tace "tom na daina cin abincin a falo shi ke nan? Dan Allah Papa ka bani Sasina."
Ta ƙarasa maganar tana bata fuska cike da shagwaɓa ta fara buga ƙafar ta a ƙasa, Fahad mutuwar tsaye yayi yana kallon yadda take buga ƙafa tana girgiza hannun shi, tunani yake wannan dukan ta zaiyi ko ture ta zai yi ya huce, kawai sai yaji iskar wajen tayi masa kaɗan numfashin shi na toshe wa da sauri ya janye ta gefe ya shige ɗakin shi ya turo ƙofa, wata zufa ce ta rufe shi ya ƙaro ƙarfin AC amma ji yake kamar bata aiki toilet ya faɗa ya sakar wa kanshi ruwa.
Yana shige wa tabi bayan shi da kallo tana ƙwafa "Allah saika bani Mage na." Tana juyowa suka haɗa ido da Mrs Lawrence data shigo da kayan Ãdil da aka kawo yanzu daga laundry, ita Mrs Lawrence mamaki ne ya ishe ta to abu ne da bata taɓa gani ba, tsawan zaman ta dasu bata taɓa ganin randa A'isha ta tsaya dashi irin haka ba.
Umaimah ta ɗauki wayar ta ta hau online ta fara duba Amira taga bata online tana duba Sa'ad taga yana kai ta danna masa video call.
Yana fitowa daga wankan ya saka three³ wando da singlet ya fesa turare ya fito shi kanshi bai san me ya sake fitowa dashi yanzu ba saidai yana buƙatar fresh air iskar ɗakin shi jinta yake tayi masa kaɗan.
Yazo zai fita Sa'ad na daga kiran Umaimah, ya ɗan kalli inda take kwance kanta yana kasa ta ɗora ƙafafun ta akan jujera hankalin ta kwance ya fita daga gidan, ta fara yiwa Sa'ad magana.
"Uncle Sa'ad wlh ɗa uwanka ya ɗauke min Sasi kayi masa magana ya bani Mage na." Sa'ad yayi dariya yace "baby Sasi din yaushe?
Jiya har Mrs Lawrence na tambaya tace bata ganta ba, saboda Allah ita take debe min kewa idan Ãdil baya nan ita ce abokiyar hirata, pls ka kira shi wlh shi ya ɗauka."
Amira tayi slicing kankana a plate ta taho wajen Sa'ad boomshot ne a jikinta da crop top pink colour tayi parking gashinta Sa'ad ya miƙo mata hannu ta zauna a cinyar shi, Umaimah ta ware ido tace "inye meye haka Amira kin samu waje sai iya shege ki ke yi."
Amira tayi wani far da ido ta kai kunnenta bakin Sa'ad ta yi mishi raɗa, "ba fa na son wulaƙanci meye haka? Umaimah ta faɗa, "me aka yi?" inji Amira, Sa'ad ya fara loosing control yayi gyaran murya, yace
"yawwa daughter next week sweetheart zata koma makaranta." wacce haka? Umaima ta faɗa, yayi dariya "zamu kawo ɗinki." tana jin ɗinki ta hau dariya tace "kayan kala nawa ne? zan yi magana da Isiyaku." kala goma ne Amira ta faɗa, "kuɗin ki 250k."
"kin ma isa, idan naje zamu yi magana da su." wlh Amira irin ku ne masu karya mutum kinsan irin accessories ɗin da za a saka?" Amira tace Ina laifin 100k."
Umaimah tace "Kai wacce kalar wiwi kike sha? toh gaskiya kar ki kai mu yanzu bespoke muke ɗinka wa, mun zama International dan Dubai zai je siyo kaya." "akwai shagon irinku birjik a kano."
"Har na 1500 zaki samu."
Sa'ad dai dariya kawai yake yi yace "za a biya daughter."
"yawwa Uncle Sa'ad ya za a yi na samu keke?" ya ce "keke kuma? Me za ki yi da shi." Uncle Sa'ad nifa ba cima zaune ba ce irin matarka ɗan Adam da buri, nafi ƙarfin yar murya irin matarka, Yawwa albishirinka." yace "goro."
"na yi first million ɗina shekaran jiya."
Yayi mata jinjina tana da passion ɗin sana'a kawai support take nema she is industrious irin su Umaimah Asset ne, yace "babu komai za a yi miki delivery." ta yaya? Ta tambaya, yace "kin manta shekara ta nawa a US, ke dai kar ki damu." toh wlh sai ki rage mana kuɗin ɗinkin. ta harari Amira, "nagode." ta saki ihu "wlh Amira ki canja hali." har Amira za ta yi magana Sa'ad ya haɗe bakin su,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 27