why not tell Daddy you aren't interested anymore." ya ƙara stressing "ask for divorce from me." Umaima ta ɗaga kai ta harare shi ta ɗauke kai, ya gani yayi kamar be gani ba.
Lallai mutumin nan ya raina ta, Me ya ɗauke ta sakarai? bata san ciwon kanta ba, wato zai zame ita ya bar ta a ciki, he wants to play dirty game with her, hmm an faɗa mishi a banza ake kiran ta da SMART, ta san fah me take yi, wato ita ce mara Abarka kenan duk jajircewar su Daddy tayi rashin kirki kenan, ya ɗauka bata da wayo, "if you're agree with my condition here is an open cheque you can write any amount that you need." ya dawo da ita daga tunanin data tafi, ya ajiye mata a hannun kujera, "I repeat any amount I promise, I will pay you willingly." ya faɗa, yana tsayar da idon shi a kanta sai kuma ya dauke kan shi daga kallonta ya nisa yace "is an AGREEMENT between the 2 of us and promise not to discuss these to any one, if you agree you sign here." ya ajiye mata white paper a kusa da cheque ɗin ta kalle shi ta kalli cheque ɗin da paper AGREEMENT ɗin taga date sunan ta da purpose din AGREEMENT din da wajen signing, jikinta yayi sanyi ta ɗauki cheque ɗin da papper ta ajiye mishi a kusa da shi ko kallon shi bata sake yiba ta juya har ta fara tafiya ta ji yace "I'm giving u 3 days to decide, need to know your stand." bata tsaya ba kawai tayi shigewarta ɗaki ya bita da kallo, wato yarinyar nan baka predicting dinta shi kwana biyu gani yayi ta yi laushi ya dauka easily zai yi convincing dinta ashe da sauran ta, well shi iya gaskiyar shi kenan zaman nasu ba shi da wata manufa, idan lissafin shi daidai ne sun yi 6month kenan da aure, hmm 6month na wahala da ciwon kai ya girgiza Kai ya dauki key ya fita daga gidan.
Tana shiga daki ta zauna a bakin gado tayi tagumi hannu biyu, wannan mutumin so yake yayi playing dirty game da ita ya rufta ta kenan? ya barta wato ita ce bata son zama da shi duk dagewar da su Daddy suka yi akan auren? itama zata so su rabu amma bata da dalilin rabuwar, tana fah da hankali, lallai masu yi mata kallon bata da lissafi ashe suna da yawa, lalle ma yadda ta yiwa Amminta Alkawari yanzu idan wannan hukuncin ta yadda ta yi Ammi zata ce bata ɗauki shawarta ba ita wlh kanta ya kulle, can wata zuciyar tace cheque fah ya baki open cheque ki rubuta duk amount ɗin da kike so za ki iya expanding business ɗin ki, wata zuciyar kuma tace a'a Umaima ko yanzu Alhamdulillah kina samu me kika rasa? Ki bi komai a sannu idan ki ka yadda kin yiwa waɗannan bayin Allah halacci kuwa? Duk kaunarsu gare ki? They always want the best for you bar batun kuɗi mutunchi ya fi kuɗi Umaimah zuciyar ta ke mata sake sake, sai kawai ta fashe da kuka ita kenan haka zata kare rayuwar ta babu future, itama fah tana da masoya bata kula su ne sai Huzaifa shima saboda Sadiq ne take kula shi, haka Abokin Uncle Aliyu Alhassan Turaki ya so ta sosai, ya rinƙa bibiyarta Uncle Aliyu yace yarinya ce saboda lokacin yana da mata da yara biyu ita kuma tana level one, ƙila da babu Ãdil tun farko ba zata yadda ta aure shi ba Ãdil kuwa danta ne halak malak, da mahaifinta yana nan wajen shi zata tafi, tunanin mahaifinta ya sa ta kuka sosai, ta yanke zata fara tashin dare tana addu'a Allah ya bayyana mata shi duk inda yake da zata iya ma azumin litinin da Alhamis zata fara, ta share hawayen ta ta zame ta kwanta a kan gadon bacci ya kwashe ta.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣4️⃣
Umaima na kitchen tana girki Adil yana kan kitchen island ta ɗora shi yana ta yi mata hirar Cindy classmate ɗin shi sun yi faɗa shi ne yace ya daina sharing abincin shi da ita "Maamah she enjoys my food." ta yi murmushi "no Ãdil be a good boy ka ji. ya gyaɗa kai, rowa babu kyau. Be fahimce ta ba ya dai daga kai, "Maamah you're the best cook in the whole world." ta dafe kirjinta, ni? tace ni Umaiman a'a bari na saka maka waigi. tana girki yana ta mata hira har ta kammala, ta ɗauko cooler ta zuba mishi jellop rice da pepperchicken ta haɗa coleslow, tace "bari mu bashi ai be wuce sadaka ba, bari a zuba mishi meye a ciki? Shi yake siyo kayan abincin shi mu bashi sadaka ko Aadil? "what is sadaka?" Ya tambaye ta, tace alms, "what is alms? Ya kara tambaya, wai ni jikar Maryama na zama yar fassara dole mu cigaba da Hausa lesson, alms means charity or donation I hope you understand? we give Papa this food as charity."
"but he isnt poor Maamah." ya faɗa, "shhhhh. Ta saka yatsa a lips ɗinta alamar yayi shiru, surutun shi ya fara yawa yanzu ita ta buɗe mishi baki da magana kar ya zama kurma irin uban shi yanzu kuma ya addabe ta da surutun, ta jera abincin Fahad a tray ta bawa Mrs Lawrence nata dan sosai take cin girkin ta, shi kuwa Adil kusan abincin shi ya dawo wuyan ta gaba-daya abincin ta kaɗai yake ci, ta zuba musu suka ci tare sun gama lokacin sallah yayi suka daura Alwala suka yi sallah dayake kofar ɗakin a bude take ta ji shigowar shi dan taji sallamar shi abunda zata shaide shi kenan ko babu kowa a waje yana sallama ta tashi ta kulle musu kofa ta kunna TV ta kai mbc 3 Ãdil ya fara kallon cartoon suna kallo tare hankalin ta ya tafi tunani gobe ne zai ji feedback din ta akan request din shi tana ta addu'a Allah ya kawo mata mafita ta Alkhairi, Allah ya shiga lamarin ta zuciyar ta tana ta saka mata abu toh ko itama ta faɗa mishi nata conditions din gaskiya tana son haihuwa idan suka rabu yanzu bata ci riba ba, amma duk ranar data samu ciki sai ya saketa.
Can ta kara wani tunani toh ai ba haka kawai ake samun ciki ba they have to be intimate kai toh ina mafita? kamar da wani take magana ba zuciyar taba taji zuciyar ta na kimtsa mata wata mafita anya hakan zai yiwu kuwa? idan aka yi hakan zata samu abunda take so? ita kadai ta ke wannan tambayar, idan zai yadda itama da conditions dinta zata yadda su rabu babu ko sisi, amma da sharadi data samu ciki zai bata takardar ta kuma babu sex sai lokacin ovulation kawai that is bayan ta gama period (cikin kwanakin an fi samun ciki) and idan tayi 3cycle (that is 3months) bata samu ciki ba zasu rabun amma shi zai ce ya sake ta alhakin sakin akan shi, idan kuma ta samu ciki zata cewa su Daddy ita ta nemi sakin ta kalli Adil daya zame ya yi bacci ta kai shi kan gado ta rage gudun Ac lokaci ya wuce tana zaune tayi sallar La'asar ta ɗauko paper da biro ta rubuta terms and conditions ɗin ta ta fito ta zauna a falo tana jiran shi, ta duba messages ɗin WhatsApp tana responding ya fito daga daki kamshi shi ya gauraye falon white T shirt ce a jikin shi an rubuta I'm bold and focus I achieve my goal a jikin rigar black jeans ne a jikin shi ga dukkan alamu wanka yayi Umaima na gulmar shi a ranta tace "mutum yayi ta wanka kamar kifi. "are you talking to me? Ya tambaya, ashe a fili tayi maganar ta girgiza Kai "Amm dama ina so muyi magana."
"okay." ya zauna a kujerar dake facing ɗinta, "carry on." ya faɗa yana kallon wayar hannun shi tace "na yarda zamu rabu." ya dago kan shi ya kalle ta yace "that is nice." "amma. ya tsaya ya ji me zata faɗa ta miƙo mishi takarda ta koma ta zauna ya buɗe takardar ya karanta yayi kamar minti 5 yana maimaita karanta wa ya ɗago suka haɗa ido ya kasa cewa komai sai juya takardar yake yi a hannun shi ta katse shi da cewa "you can give it a second thought, ka yi tunani duk abunda ka zartar is okay with me." tana gama fadin haka ta miƙe ta shiga kitchen ya bi ta da kallo, tray ɗin data saka mishi abinci ko tabawa be yi ba bata ji haushi ba ta saba da hakan umarnin Ammi take cikawa ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa ta zo ta wuce ɗaki yana zaune a wajen da paper a hannu.
Jiya wlh be yi baccin kirki ba yayi mamaki yana ganinta kamar mara wayo ashe tasan me take yi har ta iya rubuta nata conditions din aiki yake yi a system amma kwata kwata baya sauri saboda tunanin da yake yi, ya nisa "is it worth it ya kawo wani yaro ko yarinya rayuwar shi? Ãdil ma be shirya ba Allah ya yi ikon shi ba zai yi karya ba Ãdil is the best thing that happen to him a rayuwar shi ya sani rayuwar shi is boring daga ibada sai aiki shikenan Adil ne yake saka shi farinciki and Alhamdulillah a wajen aiki ma an kara mishi matsayi shi a san ran shi ya gama aure ko haihuwa, amma Adil zai so ace yana da ɗan uwa ya ji kamar ya yarda da offer ɗinta, kai is he doing the right thing? zai yi Istikara na 3days can kuma tunanin zuwa umara ya faɗo mishi dama ya yi niyyar zuwa da azumi amma bari kawai zai rubuta one week off a wajen aiki ya je umara ya dawo ya jawo wayar shi ya buɗe Qatar app ya fara ƙoƙarin buɗe app ɗin.
*****
Uncle Ismah ka tambayi agent? Umaima ta faɗa, "masha Allah duka package ɗin har kuɗin transport ɗin ziyara da komai da komai shikenan zan turo yanzu in sha Allah."
"lalle kin zama Hajiya." Ismael ya faɗa "ƙwarai kuwa, da wasa nake yi? ina fah samun alkhairi." Uncle Isma yace "naga kudin yayi yawa ko dai a cire ni sai a biya nasun idan yaso ni ba sai da azumi ba ko maulidi sai naje." A'a wallahi sai dai Siyama ta haƙura daga baya taje." Daga ɗaya bangaren Ismael yace "baki da kirki uwar tawa?Masha Allah Masha Allah Sun shigo." ya faɗa yana dariya, Allah ya biya ki. "kaga azumi 19 zaku tafi ku dawo ana gobe sallah, kuna dawowa zaku tarar dani a gida." Saboda me? Ka manta bayan sallah da sati daya bikin Hidaya."
"haka ne fah, Allah ya nuna mana." ta amsa da Amin, Uncle Ismah yana ta godiya yace "zaki hana iyayen mu bacci, ba zan faɗa musu ba sai na gama komai zuwa gobe sai na faɗa musu yanzu daga nan ma can wajen agent din zani mu gama."
"Uncle Ismah ka taya ni Addu'ar Allah ya bayyana min mahaifina, da wata buƙata ta Allah ya biya min, sai business ɗina, pls idan kun je."
"baki da matsala in sha Allah." suka yi sallama.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣5️⃣
Umma ce a kan Amira tana ta fama da ita taci abinci tun shekara jiya ta taho gida bayan sun gama jarabawar ƙarshe sai service, sosai ta ke yin laulayi, "wash wash Umma wlh bakina daci." baki fa dole yayi daci me kika Ci? Jikin ki har yanzu da zazzaɓi bari Ibrahim ya ƙara duba ki ko ruwa ne ya daura miki, jikin naki babu kwari. Umma ta haɗa tea ta miƙa mata "daure ki sha." ta karɓa ta shanye ta ajiye cup kenan ta tashi ta shiga toilet da gudu, "ikon Allah." Umma ta faɗa, ta bi bayanta ta taimaka mata tas ta Amaryar da shi suka fito tana ta mayar da numfashi, "sannu" Umma take ta jera mata ta koma kan gado ta kwanta, Umma ta buɗe mata window ta samu fresh air, tana zaune har bacci ya ɗauke ta sannan ta fito ta rufe mata ƙofa ta sauko ƙasa ta taradda su Daddy dukkan su a ƙasa suna kallon Aljaxeera tace"a kawo tea ko coppee?"
"A'a kawo mana green tea coppee ɗin nan akwai caffeine shekaru sun ja sai kana kula." gaskiya ne Daddy ya fada, kafin Umma ta tashi Mami ta shigo da sallama hannunta riƙe da basket ta zauna suka gaisa da Umma Daddy yace "me muka samu? Amira na yi wa farfesu. "oh su Darsha masu surika, bari na kira uwata na faɗa mata abinda ake a gidan nan nasan ita zata ji dani." Daddy yayi maganar da tsokana, "ni bana suruka da su Amira ita da Umaima ai ba surukai na bane ƴaƴana ne." Umma ta taya ta da cewa "barin ma Umaima da bata san wani abu suruka ba." aka yi dariya, "ya jikin nata? Mami ta tambaya, "jiki da sauki ta samu bacci ne na fito amma idan ta farka Ibrahim zai sake duba jikin nata tinda yana gari." Oh me gida yana gari ashe? eh ya shigo jiya da daddare yanzu haka yana can yana baccin nashi sai Azahar zaki ga ya shigo. maigidana yana ƙoƙari dole akwai gajiya jiki da jini.
Mami na rufe baki Ismael yayi sallama suka amsa ya shigo ya gaishe su, ya kalli Umma yace "Umma goron albishir zaki bani."
Da aka yi me? Alheri ya samu. Umma tace "dalla tafi can kai ma so kake ka zama yar taka mara lissafi." Ismael yayi dariya yace shike nan Umma, Mami keki bani tunda Umma bata so." ba musu ta miƙa mishi wayarta "Hakimi ai bana yar haka da kai." Ta faɗa tana murmushi, "A'a Mami wasa na ke miki." Baba yace wasa sai ka tafi Bichi ku yi da Dada. Baba har da kai a albishir ɗin ya fito da ticket ya miƙawa kowa nashi da sauran biyu a hannun shi yace "gashi inji jikar ku."
"masha Allah, Alhamdulillah Allah yayi mata albarka." Baba sai juya ticket din yake da mamaki ashe da gaske yarinyar nan take? Daddy yace na faɗa muku gaba uwata zata riƙe mu Allah yayi mata albarka.
ƴaƴansu sun ɗauke musu komai Alhamdulillah suna da rufin asiri amma yadda suka rinka murna kamar basu taba zuwa umara ba, sun je aikin Hajji da Umara sau babu adadi, amma wannan kyautar sai ta zame musu kamar wannan shi ne zuwan su na farko, Umma ta share hawaye tace "ashe tana da hankali Allah yayi mata albarka ya ƙara buɗi." Amin suka amsa, suna ta murna Ibrahim da Aliyu suka Shigo suka ji abunda ya faru, suka taya iyayen su murna "toh ai ba a gama ba." Ismail ya miƙawa Baba "wannan na Baban Sama ne ga nawa kuma." Daddy yayi kabbara yana laluben wayar shi a aljihu "ba shakka dole PA ya je Umara. kwarai kuwa Umma. Ya fada yana dariya, Ibrahim yace "bari na kira ƴata naji ni me na yi mata ba a biya min ba. Aliyu dai be tanka ba ya mayar da hankali kan tv.
Baban Sama Daddy ya kira ya saka shi a speaker "Assalamu alaikum." Baban sama yayi Sallama Daddy ya amsa ya tafi kai tsaye "Yaya jikar ka ta biya maka Umara." Wace jikar tawa? Uwata mana. "Ibrahim yau kuma ni ake yi wa tsokana ni fah ka kira ba Likita ba." Daddy yayi mishi bayani yace gashi nan zuwa Kanon yanzu zancen ya fi ƙarfin waya.
******
Ãdil na ɗakin Fahad yana kallon Cartoon a System ɗin shi, shi kuma yana gyaran shelves ɗin shi daya jere littatafai yana ƙara arranging ɗin su ya gama ya dawo kusa da shi yace Didi "yes Papa." Fahad ya danna pause a Cartoon ɗin yace "I will be away for a week pls behave yourself while I'm not around." "Papa where are you going? "Umara." ya faɗa, ya sani yanzu ba zai damu ba kuma shima hankalin shi a kwance yake yasan yarinyar can zata kula dashi, sau da dama yana monitoring ɗin su, best part ma yadda take koya mishi karatu abun yana mishi daɗi, ba zai yi karya ba yana jin daɗi sosai shiyasa yanzu duk ma abunda zata yi lallaɓa ta zai yi su rabu lafiya, and dole zai sameta yace mata zaiyi tafiya, yana ta sake saken, request ɗin ta zai je yayi addu'a akai Allah ya bashi mafita.
Saturday ce yau babu makaranta Ãdil yana tare da Umaima sun gama breakfast kenan tana koya mishi funwork sun gama ya tattara ya shiga ɗakin shi ya ajiye tana zaune Fahad ya fito da tab a hannun shi ya na scrolling ya samu waje ya zauna ganin ya zauna be saka ta tashi ba wayar ta tayi ringing vedio call ne Uncle Ismah ya kirata ta ɗaga gaba-dayan su ne a Falon Baba Uncle Ismah yace su Baba ne za su miki godiya, "Daddy Umaima ta kira sunan shi." Cikin barkwanci yace "sai uwata yar albarka." ya faɗa yana dariya "mungode sosai Allah yayi miki albarka." Fahad sai ya zama confused sai ya ji Baban sama ma yace "kin taso ni daga Bichi wannan abun arziki haka.
"babu komai Baban sama neman dama dan ku nake yi so nake ku ji daɗi." Daddy yace "wlh mun ji kuma muna alfahari da ke kin kashe kuɗi fah mu 6 kika biyawa Umara Allah ya saka da alkhairi." Fahad da mamaki yasa ya kame a zaune kusan duk bayan sati 2 yake tura musu kuɗi na hidimar gida da sauran su amma be taba jin Daddy yayi murna haka ba, shi be taɓa tunanin biya musu Umrah ba, ashe dai tana da hankali, "Mami ta leƙo tace Allah yayi albarka." Umaima tace "lalalala haka kika biyewa Siyama kika hanƙara ƙiba haka?dama Siyama ta zama madiga diga ita kaɗai ga ɗakuna birjik ta shiga wannan ta fita wannan toh da sake." Umma tayi mata daƙuwa tace "ba a abun arziki da ke Allah yayi albarka." Amin ta faɗa "amma Baba idan kaje Umarar nan ka taho da balarabiya ƴar shawalwala." Daddy dariya harda ƙwarewa yace "ni fah? "na yarje maka na tsaya muku aure zan muku tunda narka ƙiba su ke yi." Fahad dariya yake son yi ya ɗaure shi be iya wannan wasan jika da kakar ba ko Dada tana yi shiru yake yi, Umma tace bar maganar wasa mun kai ɗinki shagon ki na biki dana sallah. "kuma nawa kuka bashi deposit? Sai mun bayar? Umma ta faɗa "wllh sai kun bayar haba Siyama ai sai ku karya ni." Toh hannu be san na gida ba?"
"be sani ba Siyama, bari ma na kira Isiyakun." Daddy yace su biya ki kuɗin ki duk ƴaƴansu kuɗi gare su. "Yawwa Daddy wlh su zan kira na caje su."
"Ina Dattijon?" Daddy ya tambayr ta, tace "oh sweetheart zaka ce ba Dattijo ba." ta faɗa, ta maze kamar bata san yana falon ba, be san lokacin da dariya tazo mishi ba yayi mai isar shi, "mutum ɗaya sai ya biya muku kuɗin ɗinkin, ina Uncle Aliyu mutanen banki ai da kuɗina a hannun shi." network ya fara fluctuating ya ɗauke ma gaba-daya ta tashi ta koma ɗaki, Fahad be ji daɗin tashin ta ba he enjoys her company.
*****
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣6️⃣
SAUDIA
Yau Juma'a ce Fahad ya fito daga masaukin shi yana ta sauri dan ya kusa makara dan ma Allah yasa masaukin shi kusa da Harami ne har an gama khuɗuba za a tayar da sallah Allah ya taimake shi dai ya samu sallar juma'a cikakkiya, yana zaune yana addu'a Askar su na gyaran hanya su na ta tashin mutane ya tashi ya shiga wajen ɗawafi rana ake sosai ga zafi, ya buɗe jakar goyon shi ya fito da bottle water ya sha ya cigaba da ɗawafi yana zagayen ƙarshe bayan yayi sallah raka'a biyu ya dawo ya shiga Hijir Isma'il yayi sallah ya ɗaga hannu yana addu'a akan ƙudirin Umaima idan akwai alkhairi Allah ya tabbatar yayi istihara kuma Alhamdulillah abun ya kwanta a ran shi zai so Adil ya samu ɗan uwa Allah yasa Daddy kar su yi fushi da abinda suka yanke, yayi wa kan shi da iyayen shi addu'a sosai yayi wa Adil da fatan gamawa da duniya lafiya, har zai shafa be san lokacin da bakin shi ya furta itama (Umaimah) Allah ka biya mata bukatar ta ba, wajen akwai turmutsutsu yana ƙoƙarin fitowa wani bawan Allah ya faɗo mishi gaba-daya Fahad da ƙyar ya ɗaga shi daga kafaɗar shi abun ya bashi tsoro ganin numfashin shi yana sama yana ƙasa da ƙarfi ya rungumo shi suka fita daga wajen, can daga waje akwai carpet nan ya kwantar da shi ya bude jakar shi ya fito da ruwa ya tallafa kanshi ya sha ruwan, ya shafe mishi fuska da ruwa, ga dukkan alamu zafin rana ne ya gigita shi kuma ya lura numfashin shi da kyar yake fitowa ya jinginar dashi ya rinƙa daga alm din shi yana bubbuga gabobinshi, a hankali ya fara bubbuga gefen zuciyar shi ganin ya dage wajen ya lura kamar ciwon zuciya mutumin yake dashi, shi da ba likita ba ne amma ya san ƙananan abubuwan da ake wa masu heart problem, ya cigaba da bugun gefen heart ɗin shi kar blood clot ya tsaya a heart ɗin shi ana bukatar blood circulation.
hmm, hmmm hmmm!!! ya ja numfashi, da jaka a zagaye a kugun shi, yayi wa Fahad nuni da ya buɗe, Fahad ya Ciro ya bashi ya buɗe ya Ciro magani ya taimaka mishi ya sha ya cire mayafin Hiramin shi yana mishi fifita be fi kamar 5min ba ya buɗe idon shi sosai akan Fahad har shi ma Fahad ɗin yayi mishi kallon tsanaki, A'a yaya haka? ya ga fuskar Umaimah a tare da mutumin, to ko mahaifin ta ne? amma ya ji an ce shi ɗan Lebanon ne, koda yake zai iya zuwa umara amma zai yi confirming.
"ibni (my son)." muryar Tahir ta katse shi, ya kalli sardeden matashin daya taimake shi alokacin da yake buƙatar taimakon "what is your name? Tahir ya faɗa, haka kawai Fahad ya ji yana tausayin mutumin yace "Isma'il." "may Allah azzawajal bless you Ismael, are you from Sudan? No I'm from Nigeria.
"Nigeria." ya maimaita ya buɗe baki zai yi magana wayar shi ta yi ƙara yana kokarin fito da wayar ID card ɗin shi ya faɗi be kula ba, ya dauki wayar ya juya harshe, Fahad daya kula da ID card ɗin ya ɗauka ya ga sunan shi Fadoul Muhammad, "toh kama ce kawai ke nan, ba Baban ta bane, shi Baban ta kamar ya ji Tahir sunan shi, dama an ce kowa da me kama dashi a duniya, sannan wannan bawan Allah
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 27