ka siya mata perfumes da kayan make up sai chocolates toh har shekarar nan ta ƙare ka gama burge ta." Sa'ad yayi dariya yace "thankyou."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
VOLUME TWO
EPISODE 1️⃣0️⃣
Laraba (kamu)
Yau ranar Kamu duka su Yaya Surayya sun haɗu da sauran cousins ɗin Amira ana ta raha, an yi decorating compound din da balloons an yi arrangement ɗin wajen yayi kyau barin ma inda Amaren zasu zauna abun sha'awa daga gefe Ten to ten restaurant ne suke jera abincin da za a ci a wajen ga masu rabo da uniform ɗin su, an yi barbacue ɗin raguna, Mami tace Munnirah ta fito da Amaren a fara Dj ya saka wakar Ali jita ta Amarya su ya Surayya suka fito da Amaren sun yi kyau sosai wata maroon gown ce da golden head suka saka sai purse da takalmi golden colour sun yi kyau har sun gaji, sosai Umaima ta yi kyau sai make up ɗin yayi mata kyau Masha Allah, Dada ce ta fesa musu turare Umma daga nesa cikin dabara idan ta kalli Umaimah sai hawaye ta rinka gogewa cikin hikima, aka kira Malama ta buɗe taro da addu'a ta dora da wa'azi hakkin miji akan matar shi, an yi serving abinci da drinks yan uwa suka taso aka fara hotuna Uncle Ismah, Ibrahim da Farouk tare da wasu abokan Sa'ad suka rako shi a ɗauki pictures, Umaimah tace "Uncle Isma dan Allah kawo min abinci wlh tun ɗazu an kulle mu kamar barayi." Yace "kina da matsala." ya tafi sai gashi da abinci a plate ta karɓa ta ja kujera ta hau cin abinta.
Sa'ad ya kasa ɗauke idon shi a kan Amira shi wlh sai Jiya ya kula duk abinda yake nema a mace Amira har ta zarce haka abin ya bashi mamaki, wai tun da shi be kula ba Allah ya sakawa iyayen shi da alkhairi, yadda yake son mace chocolate colour Amira fah tayi masa ta ko'ina dan jiya da kyar ya iya bacci ya matso kusa da it yace "you look takeaway." tayi murmushi tace "thank you ya Sa'ad." ya ɓata fuska har yanzu ba a canja min suna ba? Ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi, Ibrahim ya ɗauke su a hoto yace "let me capture this moment." hoton kuwa yayi kyau sosai, Sa'ad sai kallon Amira yake yi Aliyu yace "ko dai mu tashi ka taho daga baya? Aliyu ya dawo kusa da Umaimah yace a dauke su hoto, su Ibrahim da Uncle Ismah duk sun ɗauka tare da Umaima, suna barin wajen kawayenta su Aishatou daga A&A'S UNIVERSE suka rufe ta da masifa wai Amarya bata cin Abinci a wajen event haka dai suka cigaba da hotona da ƙawayen su har taron ya tashi.
Yau tun safe Amira sai murmushi take yi Sa'ad jiya da daddare yayi mata shopping skincare dinta duk wanda take amfani da su da makeup kit Umma ce ta shigo ɗakin ta riko hannun Umaimah ta zaunar da ita a gefen gado tace "wlh kin ga jama'ar gidan nan yau tafi ta jiya yawa kika kara rashin hankalin jiya wlh sai ranki ya baci wace shashasha ce ke ana ina Amarya kina gani, har da wani yekuwar mai ɗaukan hoto da Amarya ya zo da 1000 a gaban yan Bichi ke so kike a tafi da ke a baki." ta zumɓuro baki tace "shikenan idan aka ce ina Amarya Siyama sai ki amsa." Umma ta kalleta ta girgiza Kai ta fita daga ɗakin Amira ta kyalkyale da dariya, Umaima ta harare ta.
Munnirah ta shigo ɗakin Umma tana yiwa mai make up magana ta yi sauri ta ƙarasa musu kowa ya tafi sai na gida, tace "Masha Allah yarana sun fito
" sai ta juya ta goge hawayen da ya zubo mata yau ranar farin ciki ce ba don kar a maimaita koKe koken ɗazu ba da Khadija ta kira vedio call tana musu Nasiha su bi mazajen su, da yadda suka yi kyan nan ta nuna mata kwalliyar nan amma bari sai ta ɗauko wayarta ta rinƙa daukar su a hoto, Yaya Surayya ta shigo tace "Umma tace su fito a wuce ga Fahad ma yanzu ya ƙarato." "Dan Allah?" Umaima ta faɗa "da Aadil yazo? Yaya Surayya tace "eh gashi can a wajen Baban shi Mami ta ce ya shirya yanzu a wuce gaba ɗaya."
Munnirah ta riƙe hannun Umaimah, yaya Surayya ta rike hannun Amira "kai kai kai masha Allah." ya Amal ta faɗa "gaskiya Hidaya ta yi missing." Hidaya tana law school duk bidirin da ake yi babu ita.
Suna saukowa Sa'ad yana falon ƙasa yana jira, sun saka peach material da silver head an yi musu riga da bridal skirt sun yi kyau sosai, Sa'ad Ash shadda ya saka da takalmi baki a kafar shi kamshin turaren shi ya cika palon ya kasa haƙuri ya karɓe Amira a hannun yaya Surayya yayi hugging ɗin ta aka ɗauki tafi ana dariya Dada ta dage ta ɗuma mishi dundu a baya aka saka dariya.
Amare suna baya Sa'ad yana gaba Uncle ismah ne zai tuka motar, har za su tafi Mami tace a jira Fahad ya fito, Yaya Surayya tace Mami kar a ɓata lokaci su je kawai ya taho daga baya. Uncle Isma ya ja motar suka tafi, mennah event cente ne grand marcuque anan ake event ɗin, decoration on point da masu rawar Nufawa ne suke yi live, Hamisu breaker ma yana wajen da Djlambo da ya Amal ta ɗauko ta daga Lagos har sun zo shiga Mami ta kira Munnirah tace su jira gasu Fahad nan. ba a ɗauki lokaci ba suka ƙarato wajen, yaran Umaima yan Friday party an musu ankon atampa red and black har maza an musu shirt da wandon jeans suka saka, ƙawayen Amare lace suka yi orange and lemon green, wasu suka saka lemon greeen head, wasu kuma orange sun yi kyau sosai they look soo beautiful, soo calm soo demure, they are just classy, yaran su ne a gaba sai ƙawayen Amare tare suka Shigo sai da Mami ta tsaya a kan Fahad dole ya fito daga mota tare da Ãdil da irin kayan jikin Sa'ad ne a jikin shi Masha Allah yayi kyau, sosai kwarjinin shi ya sake fitowa da yake ba ma'abocin saka manyan kaya bane sai suka yi mishi kyau sosai, Ãdil da gudu ya tafi wajen Umaimah yana kiran "Maamah I miss you." ta buɗe hannu ta rungume shi Fahad ya kalle su ya ɗauke kai, suka shiga cikin hall ɗin a tare Hamisu breaker ya fara wakar Buri abun ya ƙayatar, suna zama mc ya kira best friend ɗin Amira ta fito tayi speechless, Aisha uthman esq daga comment section ita ce best friend ɗinta ta fito kana ganinta kaga classic ƴar gayu da turancin ta na burgewa ta bada biography ɗin Amira aka yi ta mata tafi, Umaima da aka buƙaci best Friend ɗinta ta fito Sadiq wizard ne ya fito ya bada biograhy ɗin Umaimah ak yi ta dariya, haka Friend ɗin Sa'ad shima yayi, Fahad kuwa Farouk ne cousin ɗin shi ya fito yayi nashi, sai aka fara refreshment aka buƙaci Amare da angwaye su fito fili, Fahad ko motsawa be yi ba shi kan shi har ya fara ciwo, Umaima, Amira da Sa'ad suka taso aka rufu a kansu ana ta yi musu liƙi, Dj ta saka wakar johny drille ta my friend Sadiq wizard suka yi ta wa Umaimah liƙi.
Abun ya ƙayatar sosai Amare sun zauna aka kira kawayen Amare suka fito yan comment section su Aishatou, Aeshertouh ta yi ƙoƙari harda babynta Saheeb ta zo, Umaima sai da tace Aishatou ta kai mata shi, Saadat Baba da Maryama Hamisu suka taso suna yiwa Umaimah liƙi, Ummiai da Mrs Badiatuh suna zaune wai basa rawa can na hango Miss flower Berry tana cashewa Maryam, Hajara Ibrahim, Teddy da Safiyya suna taya ta, Munnirah ta kawo musu souvenir, ta ja Aishatou tace ta ja kunnen Umaima kar ta ci abinci ranta zai baci Amal ta ce su Fattom da MamanRukky su zo su karɓi kudin su na ƙawaye na jiya kuɗin kamu an manta basu karɓa ba, su Hafsat Ibrahim Fatima Abdullahi da Hanan Hamza ƴan gayu sun je wajen Hamisu breaker suka ce wakar jarumar mata zaisa su yi rawa, "Maryam Hamisu zo ki zauna." Umaima ta faɗa, sannu kin yi nauyi Allah ya sauke ki lafiya. har an kusa tashi sai ga Mme janjouna Naseer daga Nijar ta taho tayi latti ta sha ashoben ta tace sai tayi liƙi sefa ta liƙa danma babu lokacin canjin Naira, Uncle Ismah ne ya shigo Dj lambo ta saka wakar who is your Guy aka rude ana bin wakar.
Who is your Guy na only me and you, see as we dey like beans and rice I will never leave your side, I will never leave your side, i dedicate my time to you my Guy.
Uncle Isma yana mimming ya riƙe hannun Umaimah sai kuka dukkan su, ta rungume shi Fahad ya kalle su yayi tsaki "spoilt brat." ya faɗa, babu wanda ya kula ya fita a wajen.
Kusan duk wanda ya san su tare sai da yayi kuka sai da Mami tace ya isa haka aka tashi.
Duka falon Zuri'ar Dada ne iyaye ƴaƴa da jikoki Amira da Umaimah suna tsakiyar falo su Daddy suna zaune kan kujera faɗa ake yi wa Amare da yake abu ne na yan boko bugawa aka yi aka rabawa kowa yaya Surayya ta tashi tana karantawa Nasihohi aka yi musu da su bi mazajen su, su yi haƙuri da juna da dai sauran su, Baba tun jiya da aka daura aure a Bichi yake share hawaye.
Masha Allah....Allah yayi muku albarka yasa ku je a Sa'a yaya Surayya ta gama karantawa, Aliyu ne yace ya kamata yanzu suna airport tunda sai sun je lagos Umaima na jin haka sai kuka ita wlh ta fasa Auran ana ta rarrashinta tace toh a bata Iman su tafi tare, Daddy yace ga Ãdil nan ta tubure zata tafi da Sasi, Daddy yace "Hakim zai miki hikima ki tafi da ita." an fito da Amaren ta ƙofar baya kar Umma ta ga Umaima dan tun safe ta ke kuka kar kuka ya dawo sabo ashe Umma tana kitchen tana ganin su tace "ina zaku kai ta?" sai kuka aka ruɗe da koKe koKe sai da Daddy ya leko yayi faɗa da ƙyar aka saka su a mota suka nufi airport Aliyu da Munnirah da uncle Ismah sai da suka raka Umaimah har Lagos suna reception aka kira jirgin su EMIRATES za su bi, "kin gani na yi miki huda ki riƙe kwallin, kin gani na nade miki kamar gift babu wanda zai gane na bata maganin bacci ba zata yi kuka ba." Uncle Ismah ya faɗa yana miƙa mata kwallin magen.
Munnirah ta rungume ta, tace "Allah ya haɗa mu da alkhairi."
"Uncle Ismah." ta faɗa ta rike shi tana kuka shima kukan ya ke yi, kuka ta ke kamar ranta zai fita Aliyu da ƙyar ya janye ta shima idon shi yayi jajir yayi shaking hannunta yace "be a good girl okay." ta ɗaga mishi kai,
"why are you crying Maamah?" Ãdil ya faɗa kamar zai yi kukan shima, Fahad har yayi gaba ya juyo suka yi sallama da su Munnirah, ya kalle ta yayi tsaki a ranshi, aka kara announcing an fara boarding Munnirah tace "Maza ki bishi kar ya ɓace miki." ta riƙe hannun Ãdil suka shige.
Amira jirgin dare suka bi zuwa pothacourt su ya hindu da Aunty Amal duka tare suka wuce za su yi mata gyare gyare sai dai mu ce Amare da Angwaye Allah ya sauke ku lafiya.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
*Volume two*
EPISODE 1️⃣1️⃣
Shigowar dare suka yi sosai, Mr charles drivern Fahad shi ya zo daukar su a airport, ana zuba kayan Umaima a mota Fahad ya kalli kayan a ranshi yace "koyaushe aka saka waɗannan uban kayayyakin?"
Ghana must go ce manya wajen guda 5 da set din boxes ɗinta aka loda su a boot ɗin motar, Ãdil tuni yayi bacci yana kafadar shi, "welcome sir." Driver ya faɗa, ."thank you Mr charles."
Ya juya wajen Umaimah yace "ma'am you are welcome." ta ɗaga mishi kai kawai ya buɗe mata bayan motar ta shiga Ãdil da Fahad suka zauna a gaba, jikinta yayi tsami sosai ta gaji ga kukan da tayi kanta azabar ciwo yake yi mata, Mr charles ya ja motar suka tafi Umaima sai kallon manyan gine gine take yi da manyan tituna ko'ina haske kamar rana suna ta ratsa wurare abun sha'awa sun yi tafiya kamar ta 30min suka tsaya a gaban wani katon gini ta ɗaga kai ta karanta HAREWOOD HOUSE estate ne mai kyau aka yi scanning motar su ka shiga, kowane gida a jere Street Street da ƙaramar katanga ta zagaye kowane gida, estate ɗin gwanin burgewa ga haske kamar rana ga shuke shuken flowers kowane Kofar gate akwai drum na shara a gefe, suka tsaya a No 101 gate ɗin ya buɗe Mr charles ya shiga da motar yana yin parking ya fito da kayan Umaima, Fahad trolley 1 ce nasa, ya fito da card kamar ATM yayi scanning jikin ƙofar ta buɗe aka shigar musu da kayan, straight Fahad ɗakin shi yayi da Ãdil ya kwantar dashi sannan ya fito yayi waje, ta ji dai yana magana da direban ya dawo ya rufe ƙofa tana tsaye ya kalle ta ya ɗauke kai sai kuma yayi mata pointing daki da yatsa "here is your room." be ko tsaya yaji mai zata ce ba kawai yayi shigewar shi ɗakin shi ya rufe ƙofa, ta kaici ya kama Umaimah taji wasu hawaye sun zubo mata ta goge hawayen ta kalli uban kayan a tsakiyar falo wato ita zata kwashe wannan kayan ke nan, a ranta tace ai kuwa zai ga tsiya."
Ɗakin daya nuna mata ta shiga wow! gaskiya komai na ɗakin ya burge ta, direct toilet ta shige ta yi fitsari da ƙyar ta watsa ruwa tabi lafiyar gado gajiyar da ke tattare da ita ta rufeta sai bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
****
Ke Amira tashi maza ki je mijin ki sai zarya yake mana a ɗaki. yaya Surayya ta faɗa, gyaran kitchen ne ya rage musu sai kayanta da suka jera mata a wardrobe aikin da wuri su ka gama, Surayya ta sake cewa "kin yi shiru shigowar da yake yi an faɗa miki don mu ne har da wani ko a kawo mana room heater? Ko a ina sanyin da za a saka wata heater."
"wlh kun zama yayun banza, ba ku da girma sai na jiki.
"shike nan Yaya Hindu ai ma yi mata faɗan ta gyara ko, kinsan mijinta wayayye ne babu duhun kai a tare dashi ba kamar ɗan uwan shi ba."
Yaya Surayya tayi dariya tace "taɓ lallai Amal waye mai duhun kan? Fahad ɗin ne mai duhun kai hmmmm irin wannan suka samu mace saita Allah."
Ita dai Amira ta yi shiru duk ta takura, sai jin knocking suka yi ya Amal ta yi dariya tace "Bidiri." ta buɗe kofar ta tsaya a bakin ƙofar tace "ya aka yi? Menene ya aka yi kuma?" Ta tambaya, "zan wuce ne." ta matsa mishi ya shigo Amira tana bakin gado da hijabi a jikinta ya shigo yace musu babu hand wash a toilet ɗin ɗakin nan ya miƙa musu abu a leda, hand washed ne da freshener dasu toothpaste, Yaya Surayya tace "toh mungode."
"Abincin ya ishe ku? Ya ishe mu. Ya sake cewa "babu wata matsala ko? "ya Ilahi mun ce babu babu dan Allah mungaji kwanciya zamu yi." Amal ta faɗa tana kunshe dariya, ya kalli Amira kamar kwai ya fashe mishi a ciki ya fita.
"ke Amira tashi ki bi mijin ki wlh." ya Hindu ta faɗa, kawai sai Amira ta fara kuka.
"kinsan Allah tashi." ta ja hannunta ta buɗe ƙofar tana rike da ita har ƙofar ɗakin Sa'ad tayi knocking, kamar a bakin kofar yake ya buɗe da sauri yaya Hindu ta juya ta tafi, yace "Allah ya ƙara girma da nisan kwana mai albarka Yaya." ya ɗaga Amira cak ya shige ɗakin da ita da ƙafa ya tura ƙofar dakin jikake Gam, "duk wayon Amarya dai sai an sha romonta." Ya faɗa yana juyi da ita a ɗakin.
Ni kuwa na sake ware Ido na dakko muku rahoto Kofar ɗakin ta rufe gaba ɗaya.
KANO
Haba Maryama mace ce fah duk daren ɗaɗewa gidan wani zata ke da zaki yi farin ciki mun rabu da su lafiya Gaba-dayan mu a wajen daurin aure babu wanda be zubar da hawaye ba, uwata akwai shiga rai yadda kika haƙura da Khadija ta tafi wata uwa duniya haka itama za ki saba, duk kin ɗaga wa Muhammad hankali jiya yace ma baki yi bacci ba, Maryama idan ban ga chanji ba zan faɗawa Dada, so nake su huta kanya siya mata layin can sabida arinƙa jin lafiyar ta, bari ma na kira Dattijon ya siya mata sabon layi ba sai mun dame shi yana wajen aiki ba."
Daddy ya ƙarasa maganar yana yin dialing wayar Fahad a kashe, Baba yace "ka ƙyale shi ya gaji, an sha gajiyar biki ga gajiyar tafiya abinda nake ta faɗa mata kenan." Daddy yace "kin dai ji abunda na faɗa miki koh?" da kyar Umma ta amsa da dasashiyar murya, tace "nagode Yaya."
"Bafulatana fah kike Maryama." Umma tayi murmushi tace "ay jika ce Yaya." Baba hankalin shi ya kwanta ganin ta saki ranta.
UK
Ya fito ya ji kai kawo a kitchen yasan Mrs Lawrence ce yau weekends ne babu aiki tunda yayi sallah ya koma sai yanzu ya tashi, Ãdil ma har yanzu bacci yake yi shima grocery shopping za shi, ya ƙare wa Falon kallo abun mamaki kayan jiya an yi parking ɗin su waje guda, me take nufi? Shi zai shigar mata da kayan?
Mrs Lawrence ya kira yace ta buɗe ɗakin ta shigar mata da kayan zai fita ya dawo.
Buɗe ɗakin da Mrs Lawrence tayi shi ya tasheta ta buɗe ido rana gatse gatse, tace "kai Siyama shi ne baki tashe ni ba." sai ganin motsattsiyar tsohuwar baturiya ta yi tace mata "good morning ma'am." ta tashi zaune "morning." ta amsa mata, Mrs Lawrence ta rinƙa shigo mata da kaya ɗaya bayan ɗaya har ta gama, ta shiga toilet Alwala ta daura ta fito tayi searching qiblah ta tayar da sallar tana idar wa cikinta yayi ƙara, tace kai wlh yunwa nake ji." ta fito ta shiga kitchen "is breakfast ready? Ta tambayi Mrs Lawrence tana tunanin ƙila ita ce mai aikin.
"yes ma'am, let me arrange the dinning." Umaimah tace "eh gaskiya don yunwa nake ji." bata fahimci me Umaima ta faɗa ba sai kawai tayi mata murmushi.
Umaima ta koma ɗakinta ta yi wanka ta buɗe boxes ɗinta ta fara neman kayan sawa, ta ɗauko wata rigar material brown mai tattara a sama rigar mai karamin hannu tasa tayi mata kyau sosai bata ɗaura ɗankwali ba, ta jawo kwalin da ta sa Sasi aciki ta buɗe ta fito da gudu tuni ta farka ta ɗauke ta suka fito ta zauna a dinning Mrs Lawrence ta ajiye mata tray a gabanta custard ne a mug sai toast bread guda 2 da wani munafukin biscuit kwalli 2 Umaimah ta kalli tray ɗin ta kalli tsohuwar baturiyar tace "bantan uban nan wannan ne abincin?" Mrs Lawrence ta bita da ido irin ban gane me kika ceba.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 1️⃣2️⃣
Leeds UK
Meow Meow Sasi sai kuka take yi, Umaimah ta kalle ta ta kalli abincin da aka ajiye mata tasan yunwa ce, ta miƙe tabi Mrs Lawrence kitchen, Mrs Lawrence tana shirya cutleries sai ganin ta tayi, tace "Please I need milk?" ta buɗe wata cupbord ta bata Madarar ta karɓa ta fito daga kitchen ɗin, cointainer ta ɗauko a cikin kwalin da aka sa Sasi ta kaɗa mata Madarar ta bata, sai kuma ta fara binciken Ghana must go tana buɗewa taga kananan botikikan su gyaɗa nikakkiya, manja, busasshen kifi, dambun nama, kilishi, cin cin, harda barjanjen wake zai yi kwano 5, garin kunu, kuka, kubewa, garin Ɗanwake, harda yajin daddawa duk abunda zata buƙata an saka mata tana buɗe kayan sai ta ji hawaye tace "Allah sarki Siyama tasan aikin ta ne."
Ta kira Mrs Lawrence ta taya ta suka jera kayan a store, ta ɗebi wake ta yi blending ta haɗa ƙullun ƙosan ta mai rai da lafiya, ta dama kunun gyaɗa ta na aikin Ãdil ya farka ya fito falo yana cewa "is there anyone?
"I'm here Didi." Mrs Lawrence ta faɗa tana nufo falon, ɗakin shi ta jashi ta yi mishi wanka, suna fitowa a shirye Umaimah tana gamawa har ta fara jerawa a Dinning, Ãdil na ganin ta yayi wajen ta da sauri yana kiran Maamah.
"Maamah you will be living with us?
"Yes."
Ta amsa mishi yayi wani tsallen murna, "yes"
Kayan abincin ta sauke musu ƙasa a tsakiyar falo ta zubawa Ãdil, Meow Sasi ta ji kamshin ƙosai ta fito daga ɗaki "Maamah what is this? Ãdil ya tambayeta, tace "kunu mana, baka san kunu ba?" sai ya zama lost saboda be fahimci abinda tace ba, ta gane be fahimce ta ba, ke nan baya jin hausa kwata kwata a ranta tace taɓ aiki ja, "ai fa dole ka ko yi Hausa yaro sai kace jikan Elizabeth to bazan yi turanci ba." Sai kuma ta kalle shi tace "try it is nice." ya riƙe kofin kamar me tsoro ya sha kaɗan "hmm is nice Maamah." Ya faɗa yana kaɗa kai, ta bashi ƙosai, yace "and what is this? "Kai ya ilahi beans cake." ta faɗa mishi, ya gutsira har da rufe ido "is yummy."
Tayi masa murmushi, tana ci tana gutsirawa Sasi, Ãdil ya ci ƙosai sosai, tayi mamaki kunun yana shanye wa yace mata "I need more." ta ƙara mishi suna haka ta ji maganar Fahad a kitchen da Mrs Lawrence sai ta ji foootsteps ɗin shi kamar yana tahowa, yana ƙarasowa cikin falon yaji muryar Ãdil yana cewa "Maamah will you make this for me to school."
"why not My Son." ta faɗa, da yake ya ƙoshi ya daƙumi Sasi, wata tsawa suka ji Ãdil ya tsorata ya faɗo kanta Sasi ma sai ta tsorata tayi ɗaki da gudu, Umaimah kawai ta tsaya tana kallon shi, tace "wallahi babu kyau tsoratar da musulmi haramun ne."
"what the heck." ya faɗa a fusace, ya kalleta ta yi baje baje a tsakiyar falon, kujerun farare ne idan anan zasu ci abinci dole a yi staining cushion ɗin, ya kalle ta ran shi ya sake ɓaci da tayi kamar babu kowa a wajen, yace "next time eat at the dinning not here, don't mess here." Ta ɗaga kai ta kalle shi galala ta zuba idanunta a cikin nashi, ya kalli Ãdil daya ƙanƙame ta yace "let's go."
Meow Sasi ta taho tana kada mishi jela ya ƙara kulewa, "I'm not sure I'm comfortable
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 27