Share this page
ta, ta fara kira bata ji ta fita waje, Khadija ta fara neman ina ma ta saka wayar ta jiya Umaima ta bata ita, lokacin bata wayar take ba ta laluba jakar ta, ta dauko wayar missed call da yawa ta gani Daddy 3 Baba 4 Umma 2 Ibrahim, Sa'ad, Amira Hajiyan Munnirah, Aunty maimuna 1 Yaya Fahad 12 missed calls, ta kira Baba yana dagawa tace Baba Ahmad ya farka amma baya magana. Alhamdulillah muna ta Addu'a kai masha Allah, ya cewa Umma kin ji Ahmad ya farka ta ji yana fadawa Umma ya kyale ta akan waya ta kashe ta kira Daddy ta fada mishi yace "Alhamdulillah ya Rabbi lakalhamdu wash shukr, kin kira Dr? A'a Daddy ta manta dasu zata kira ya hana, "maza a kira Dr." ta katse wayar da hanzari zata fita yace "Khadijah." Muryar shi a karye ta dawo ta tsaya a gaba shi tace "bari na kira Dr ya duba ka." yayi mata alama ta zo da hannu ya miƙo mata hannu ta rike ya tamke hannun ta ya jijjiga fuskar shi ta fara tsartsafo da gumi, bata zare hannun daga cikin nasa ba ta saka gefen hijabin ta da daya hannun ta share mishi zufar. "Nagode Khadija." ya fada da kyar kamar mai koyon magana "Allah yayi miki Albarka ya baki Miji Nagari Khadija." syai girgiza kai ta ke yi, tace "zaka tashi in sha Allah." yayi wata shakuwa. "Laila ha ilallah Muhammadurra sulilllah." Ya faɗa a hankali, sai kuma jikin shi ya saki machine din da aka jona mishi ya hau kara, a rikice Khadija ta zare hannun ta tayi hanyar waje suka haɗu da Gwaggo da Abban su yana shigowa yace "ina zaki? a gigice tace "Dr zan kira." Abba ya karasa dakin machine na kara idon shi a bude yana kallon waje ɗaya, kawai jikin shi ya bashi Ahmad ya tafi yace "inna lillahi wa inna illahirrajiun." yake ta maimaitawa, "menene wai? Gwaggo kamar me sumbatu tace wlh yanzu ya buɗe ido ka gani ma kallona ya ke yi, Dr Vikram ne ya shigo yayi tabe taɓe a jikin machine din yayi shiru ya taɓa pulse ɗin shi ya shafe fuskar shi ya rufe mishi idon shi, ita dai Khadijah tana tsaye a bakin kofa ta kafe Dr da ido ya kalli Abba yace "I'm sorry he is no more." Gwaggo ta share hawaye ta tsaya tana kallon shi aka rufe shi da farin yadi luuuuu Khadija ta ji kanta yana juyawa ta zube a ƙasa a sume. Shigowar shi Asibitin kenan safiya ce direct lab ya nufa ya kira miss Jane ta bashi sakamakon test ɗin jiya tace ya zauna tana zuwa ta bude system kenan kafin tayi printing result ɗin wayar shi tayi kara ya daga Dr Vikram ne yace mishi ya zo room 122 "we lost our patient." hankali tashe Dr Huzaifa ya baro lab miss Jane tana ya tsaya ya karɓa ma be ji ba yana shigowa su Munnirah da Umaima suka rufa mishi baya Gwaggo ta rusa kuka "Dan Allah kar ku yi mishi kuka Allah ya jikanka Amadu ya sada ka da Manzon Rahma." cikin tawakkali da mika wuya tare da sallamawa hukuncin Allah Abba yake yin maganar "ai an sha jinya yayi kankarar zunubi sai dai mu kokawa kanmu." Umaima ta rikice bata taɓa ganin gawa ba sai yau hawaye kawai take yi ta durkushe a kasan dakin "Allah ka jikan ka Uncle Ahmad yayi maka Rahama." Khadija kuwa tunda ta farfado kamar mutum mutumi kamar an dasa ta ta kafe waje daya da ido tana kallo Munnirah ta girgiza ta tace "Khadijah pls ki yi kuka Dan Allah." Abba ya kira Daddy yana dagawa Daddy yace barka da arziki an ce ya farka nan Daddy ya ji mummunan labari aka rude su Umma da Mami kuka kawai su ke yi. Duka wani signing da cike ciken forms da procedures din asibitin Dr Huzaifa da Baba Dr ne suka yi suna ta processing yarda za a taho da gawa kuɗi ne masu yawa sosai ma'aikatar su ce ta dauki nauyi ana ta kiran Khadijah a waya sai dai Munnirah ta daga, ba za a iya tafiya da gawar Ahmad a ranar ba sai gobe an ci sa'a akwai jirgi, wannan rasuwar ce ta saka Umaima kunna wayarta kamar jira ake tana kunnuwa kiran Uncle Ismah ya shigo ta amsa murya a dashe suka Jajantawa juna yace "ina ya Khadijah? Suna ɗakin da Mamin rijiya kofar dakin ta bude daga inda take tana jin karatun Kur'ani an saka shi low volume Baba Dr ne suka fito tare da Dr Huzaifa yana ta kara mishi godiya ya koma dakin, Dr Huzaifa ya nufo ta "Fatima I'm so sorry for your lost." yana fadan haka kuka ya zo mata kamar me jira yayi ta bata hakuri wanda take gani matsayin uba ya rasu waya sani nata uban ma ko yana raye ko a mace wannan tunanin ya karya mata zuciya sosai da kyar Dr Huzaifa ya saka tayi shiru da wayar ta a hannunta ya kira ta shiga duka ya karɓi numbers ɗinta har ta Nigeria, wayar shi tayi kara miss Jane ce wlh sai yanzu ya tuna ashe fah be karɓi result ɗin ba hankalin shi yayi gaba, ya kalli Umaima yace "gobe zaku koma Nigeria ko? Ta gyada Kai yace mata ta rubuta mishi address ta turo masa zai kawo mata twin din ta Akwai aikin da zai kawo su Nigeria, without second thought ta yi mishi text na kwatancen ta tura masa, "baki da wani layin na Nigeria incase wannan be shiga ba." "sai business line." yace ta bashi ta bashi yayi saving, "to Fatima sai na kawo miki twin din naki." tace I can't wait to see her. In sha Allah. ya fada wayar shi tayi ringing Tahir ne ya ɗaga yace ya zo yayi discharging din shi ko ya nemi shi ya rasa yayi dariya yace gashi nan ya kashe wayar ya kalli Umaima yace "patient ɗina ne ya kira ni bari na je expect us soon na san da wuri zaku wuce ko?" ta amsa da "in sha Allahu." suka yi sallama ya tafi. UK Yau da karsashi ya tashi don ya riga ya haɗa kayan su gobe zasu wuce Najeriya duk da dai yayi ta kiran wayar Khadijah an ce tana hannun Umaima amma bata daga ba yana murna kuma a lokaci guda yana zullumin tafiyar Allah dai ya sa komai ya zo da sauki idan ya sauka Lagos Sa'ad zai zo su haɗu su taho Kano dole yana bukatar back up don Umaima is everyones favourite ya jawo ƙaramin box ya fara haɗa kayan Adil don jiya ya dame shi da tambaya ya fada mishi gobe ne tafiyar sai kuma ya dawo rigimar lalle sai an faɗawa Maamah zai zo Nigeria, yayi mata kiran duniya ba a daga ba ya rufe box din ya dauko frame dinta ya saka a zip din box din shi ya shiga toilet ya wanke hannu ya fito ya fitar da boxes din palo ya kira Mrs Lawrence data kai kayan guga dakin Adil yace ya bata one week off ya debo kuɗi masu yawa ya bata yace idan sun dawo zai kira ta kar ta tafi yanzu zai fita Adil ma yana makaranta har ya shiga mota wayar shi tayi ringing Sa'ad ne ya ɗaga, "when? Ya tambaya, inna lillahi wa inna illahirrajiun may Allah forgive his shortcomings." Suka ajiye wayar ya dade a motar jikin shi yayi sanyi har kamar zai fasa fitar dai kuma ya ja motar ya fita turarukan shi zai je ya siyo. ***** 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣7️⃣ Dr Huzaifa direct office din shi ya je ya kira miss Jane ta kawo mishi result ɗin ya dan jira kamar 15mins ta shigo da result din a brown envelope an yi sealling dinta ya karɓa, shi kan shi fargabar buɗewa yake yi Allah yasa hasashen shi yayi daidai har ya dauko zai buɗe wayar shi tayi ƙara Tahir ne ya jawo drawer ya saka ya fito ya ƙarasa wajen shi yana shiga ya ganshi a tsaye, yayi dariya yace "ina zaka? "Tun ɗazu ka zaunar dani, mu je wajen Ummi." suka hau lifter fourth floor, suka ƙarasa dakin, Ummi na zaune Yaseer na mammatsa mata ƙafa suka shigo ya karasa kusa da ita suka gaisa da Dr Huzaifa. "kayfa haluk ya Ummi?" Tahir ya faɗa, ya rike mata hannu yayi mata kiss a goshi, "Kayfah haluk akhi Yaseer? ya faɗa yana kallon Tahir. "Alhamdulillah" Ummi ta jawo hannun Tahir tayi mishi nuni daya zauna kusa da ita, tace "ibni inna ni uridu minka an tazawaj (my son I want u 2 get married)." dukan su suka kalli Ummi. "lay down and rest Ummi." Yaseer ya kwantar da ita ta rufe ido kamar me bacci cikin larabci taci gaba da cewa "har ga Allah bana jin daɗin ganinka haka Tahir zan so kayi aure naga iyalinka kafin Allah ya dauki rayuwa ta zan so naga Zuri'ar ka, Tahir shi ne kaɗai burin da nake da shi a duniya wannan shi ne zai sa nayi kwanciya cikin salama." Tana daga kwancen take magana Tahir ya rintse ido, idonsa ya kada, in sha Allah zai cikawa Ummi burinta zai yi auren da yace ba zai ƙara aure ba, amma zai daure kamar tasan ita yake kallo ta bude ido ta kalle shi yace "Ummi in sha Allah zan yi aure daganan mu wuce Lebanon ko acikin yan uwa ki samar min mata, nayi miki alkawari zan aura in dai hakan zai saki farinciki." Zumbur Ummi ta mike ta rungume shi cikin jin daɗin maganar shi tace "ni na warke." ta kalli Dr Huzaifa, Yaseer yayi dariya yace haba Ummi daga jin zancen aure sai ki warke? Rashin auren shi yake tayar min da ciwo shekarar shi nawa yanzu? Shekaru sun ja. Tahir ya yi dariya yace "Ummi ga babban tuzuru nan har gara ni na taɓa aure." ya nuna Dr Huzaifa Ummi ta dawo kan shi tace "wlh idan kana so sai na nema maka." yayi murmushi yace kyale Tahir Ummi na kusa aure. "Allah yasa, Dr ku sallamemu mu tafi gida na warke." A'a da sauri Ummi? ya gwada jinin ta yace da sauki sosai nan da jibi za a iya sallamar ki, amma ki gama shan waɗannan magungunan. Ya tafi wajen magani ya nunawa Tahir wanda take sha sau uku "yanzu ya dawo sau 2, Amma wannan na sau daya ne da daddare ta cigaba da shan shi. Allah yayi maka albarka Ummi ta faɗa, yayi musu sallama ya fito. Washegari Da sauri ya isa office ɗin shi yau kamar ya makara jiya bayan ya bar wajen Tahir gida ya tafi sai daga baya ya tuno da result din kamar ya dawo dai ya hakura ya zauna ya bude drawer ya Ciro result din zuciyar shi tana bugawa kamar me duba sakamakon jarabawwa shi DNA 100% correct ne duk result din daya bayar ya bude ya yi kamar 5min yana dubawa ya mike zumbur daga kan kujera ya kai gwauro ya kai mari ya rasa ma wanne tunanin zai yi. HUKUMULLAH (Allah's will) ya zauna a seat ya tashi ya buɗe kofa har zai fita ya dawo kan shi ya kulle shi yanzu ta ina zai fara? wannnan abunda yayi is a crime yayi ba tare da sanin su ba is against their profession, toh ai taimakon Dan uwan shi yayi, amma meyasa iyayen Khadija suka kasa faɗa mishi tana da ciki? Ai bayan rayuwar su ya auri ƙawarta don Fatima zata yi 20 to 21yrs lallai laifin da yayi musu mai girma ne, ya tattara komai ya mayar cikin drawer, zancen ya same Tahir wajen Ummi ma be taso ba bari ya kira shi kawai yazo ya same shi, ya ɗauki wayar shi yayi dialing number Tahir. ****** UK Mr charles ne ya kawo su airport Ãdil sai murna yake zasu wajen Maamah, sun yi boarding suna cikin jirgin Fahad ya kira Sa'ad ya faɗa mishi sun taso zasu haɗu a Lagos, yace shi yana pothacourt amma nan da 2hours zai isa Lagos sai ya jira wajen 4 hours akwai wanda zai gani a Lagos ɗin, amma zai yi kokari ya gama kafin su ƙaraso, suka yi sallama aka sanar a saka belt ya ɗaurawa Adil ya kunna mishi cartoon, ba'a fi 30mins da tashi ba Adil ya haushi da tambaya tun yana bashi amsa har ya gaji, can kuma bacci ya ɗauke shi ya gyara mishi kwanciya yarda zai ji dadi ya saka wayar shi a flight mode ya bude account ɗin Umaima na instagram yaga tayi posting rasuwar Ahmad yayi scrolling ya dade yana kallon wasu pictures dinta ita da Amira da wasu da ita da Baba, da wasu ita da su Daddy da Baban sama, lokacin auren Ahmad ne data dauke su a palo Rasuwar ce kila yasa ta saka hotunan dan ya haddace komai na instagram account ɗin ta, sun kusa sauka, abu biyu ne a ranshi yana murnar za su haɗu da zullumin da zai shiga idan iyaye suka ji zancen nan, shi ne mai laifi Allah ya kawo komai da sauƙi, Allah ya shiga lamarin ya runtse ido. Gabadaya Ahalin gidan sun haɗu ana ta jajanta mutuwar Ahmad dan su Dada da wuri suka taho da Babancikin gida suna ta waya da Baba Dr akwai takardar da zasu karɓa a asibiti idan ba haka ba baza a karɓi gawa ba a airport, ita ta dan tsayar da su, amma yanzu sun karɓa sun wuce airport karfe 10 jirgin su zai tashi, Daddy yace Allah ya kawo su lafiya, Baban sama yace indai sun kusa sauka sai mu tafi airport ɗin mu jira su. Hakan yayi mu matan sai mu wuce galadanci mu jira ku acan, baza mu biku yawon filin jirgi ba." Umma ta faɗa, Baba yace hakan yayi. Dada tace "kamo min Zainab a waya Azumi." Umma tace wayar tana sama bari ta dauko, ta tashi Dada tace "wlh ku shaida idan Zainab bata zo gaisuwar nan ba babu ni babu ita, ba zan ce Likita ya sake ta ba, amma zata ji babu daɗi, haba akan ta aka fara kishiya duk abunda ya shafi Azumi ko yaranta ta daina zuwa Kowacce hidima ta tsame kanta." "ayi hakuri Dada. Baba yace mutuwa ta kori komai dole zata zo. Allah ya bata sa'a. ****** Wayar Tahir tayi ringing suna ta hira da Ummi tinda ya amsa mata zai yi aure ta saki ranta, ya ɗaga kiran Dr Huzaifa yace "ok gani nan zuwa." suka ajiye wayar yace wa Ummi Dr Huzaifa ne yake kira na. Ummi tace a dawo lafiya, Yaseer yace idan "zaka dawo ka taho da fruits." ya amsa da toh ya fita. Yana buɗe office din ya tarar da shi a tsaye da waya a hannunshi tun ɗazu yake gwada number Fatima taƙi shiga, Tahir yana shigowa wayar ta shiga ta ɗauka suka gaisa yace "Fatima kina nan ko kun wuce? A'a mun dan samu delay ne amma gamu acikin jirgi. Yace "shikenan sai mun zo gani ga wani mai kama da ke." Tahir ya kalle shi wanne shiriri tane kuma haka da mace yake magana, shi ne mai kama da mace? Yana zancen zuci suka yi sallama idon shi a kan Dr Huzaifa. Dr Huzaifa yace "tea or coffee? No bani ruwa kawai. ya nufi fridge ya ɗauko mishi ruwa da cup ya ajiye a gaban shi duk jikin shi yayi sanyi ya rasa ta inda zai fara yi mishi bayani, Tahir yace "sai kallo na kake yi ka kira ni." Ai na rasa ta inda zan fara ne? Ka fara ta ko'ina mana. Dr huzaifa yayi gyaran murya yace "kai musulmi ne haka ne? ya gyaɗa kai, "kasan yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau yana cikin shika shikan imani a matsayin ka na musulmi haka ne? yace haka ne, "bana son ka rike abun a zuciyar ka Tahir, duk abunda ya faru da bawa haka Allah ya tsara bamu ba wayo ko dabara haka ne? Tahir yace ka faɗa min mana menene zuciyata ta lalace menene na boye boye." "Subhanallah ba haka bane ai zuciyar ka yanzu ta warke garau tunda zata samu abunda take so." Tahir ya girgiza kai yace abunda zuciyar shi take so tayi mishi nisa yayi murmushi mai ciwo, ka fada min wlh zan tafi ya miƙe. Dr huzaifa ya sha gaban shi yace "yanzu misali ace Khadija ta haifa maka ƴa bata faɗa maka ba how will you react? Tahir yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "zan ji babu daɗi amma duk abinda Khadija tayi nasan zafin abunda nayi mata ne Hayateey mai biyayya ce sai dai iyayenta su hana na sani, wai meye ma kwanan nan ka dame ni da maganar Khadija me nayi maka? Why do you want to hurt my feeling? Ka tambayi tun rabuwar mu bamu sake haduwa ba na faɗa maka menene?" Dr huzaifa yace "I just spoke with your daughter." ya kafe shi da ido "daughter how? Who? When?" Tahir ya jero masa tambayoyi yin kai tsaye, Kwata kwata be dauki zancen da mahimmanci ba. .........Dr Huzaifa ya fara bashi labarin patient ɗin su da Fatima mai kama da Ummi, Tahir yayi dariya yace "shi kenan kaga mai kama da Ummi shikenan saita zama yar Khadija? "no Tahir bangama bayani ba." "ok go on." "A hankali na fara tambayar ta Mamanta da farko wata ta nuna min mahaifiyar patient ɗin mu idan baka manta ba jiya na tambayeka ka fasalta min Khadija sak yarda ka fasalta min haka Maman Fatima take." Ai sai Tahir ya miƙe yana kallon Dr Huzaifa "no no that isn't enough I need more evidence." "relax.' ya mayar dashi ya zaunar ya kafe shi da ido, yace "duk information din dana ke son samu akan Fatima daga baya ta faɗa min gaskiya the only issue da zan samu tabbas shi ne DNA and is against our profession is a crime when caught I will loose my career my job and every thing so pls calm down and understand me." Tahir da jikin shi ya fara sanyi ya kafa mishi ido ko kiftawa baya yi. Dr Huzaifa yace "Allurar dana yi maka jiya nayi ne dan nayi prolonging discharging dinka na dauki samples." Tahir ya kara mikewa ya buɗe baki ya rufe ya kasa magana, Dr Huzaifa yayi shiru yana kallon shi kirjin shi yana sama da kasa, karfa ya sume mishi, Tahir yayi mishi alama ya cigaba da hannu ya cigaba da magana. "na yi mata ita ma Allah ya kawo sanadi da tayi collapsing nayi amfani da wannan damar na dauki samples and the result came out FATIMA is your daughter 100% accurate." Kawai Tahir sai ya ji kunnen shi ya toshe kamar ya daina jin larabci kamar be gane ba ( duk maganar da larabci suke yi ) yana dai zaune Dr Huzaifa yayi scrolling ya nuna mishi hoton su da Umaima, wata irin faduwar gaba yayi sai ya mike ya rike wayar da ita kadai ce a hoton zai ce hoton Ummi ne na shekarun baya aka yi editing ko dai playing din shi yake yi, Dr Huzaifa ya dauko result ya mika mishi ya bude hannu na rawa ya karanta result din ya kalli hoton luuuuu ya tafi zai faɗi Dr Huzaifa ya tare shi numfashin shi yana sama da kasa ya kwantar dashi a doguwar kujera ya kunna fanka ya dauki ruwa ya shafa mishi a fuska ya cire mishi riga ya buɗe bakin shi ya hura mishi iska. Tahir yayi ajiyar zuciya hmmm!!!!......ya buɗe idon shi ya kada yayi jawur, abun tausayi yace "pls Huzaifa I hope I'm not dreaming? is Fatima my biological daughter?do I have a daughter Fatima? Am I Fatima's father? could you tell me how I'm related to Fatima as her Father?" Dr Huzaifa ya lura da sumbatu yake yi kawai ya hada allura yayi mishi bacci ya kwashe shi ya rufe shi a office din ya fita ya san nan da 3hours allurar zata sake shi. After 3hour Ya bude office din ya gan shi a zaune ya shiga da sallama "ka tashi? Ya mike jikin shi babu kwari ya nufi Dr Huzaifa yace "Me yasa baka faɗa min ba sai yanzu? Tahir ya rufe ido yana faɗa, Dr Huzaifa ya tsura mishi ido yace "dole sai an yi bincike tukun." Me yasa daka bincika ba ka faɗa min? Toh sai yau na duba result ɗin saboda rasuwar patient din mu ba fault ɗina zaka tsaya nema ba ni fah taimakon ka nayi" kamar Yaro Tahir yace "kuma fah haka ne." sai ya tafi ya rungume Dr Huzaifa ya fashe da kuka "I will forever be indebted to you Dr." 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣8️⃣ Yanzu ɗazu da daughter na ka yi magana Dr? "Eh ita ce." sai ya miƙe yana cewa "Ummi ta zo mu tafi Nigeria kawai." Dr Huzaifa yayi murmushi "relax mana calm down." da kyar Dr Huzaifa ya lallaɓa shi ya zauna yace "ka tsaya a yi komai a hankali, kai ta Fatima kake yi yanzu ita kuma Khadijah mijinta ne ya rasu dole suna cikin tashin hankali yanzu haka ne?" Gaba ɗaya baya tunani straight kan shi ya kulle ya manta ina ne ma gabas ya tambayi Dr Huzaifa ya nuna mishi ya daɗe a sujada yana godiya ga Allah, in sha Allah Khadijah zata dawo rayuwar shi a karo na biyu, har sai da Dr Huzaifa ya leƙa shi ya ga hawaye kawai yake zubar wa fuskar shi tayi jawur, ya ɗago ya ƙara rungume Dr Huzaifa, yace "you are more than a friend to me Dr." yayi murmushi yace "congratulations Angon Khadijah." Tahir yayi wani blushing "oh my God kar ka karasa kashe min zuciyata Dr." ya dafe kirjin shi "yanzu dai ayi discharging ɗin Ummi mu tafi." "A'a ka yi haƙuri yau suka tafi wajen jibi sai mu tafi har da ni zamu wuce." Dr ba zan iya jira ba I want to see Hayateey and my daughter. lallai Khadijah yar halak ce ta cika burinshi na saka sunan Ummin shi, ya yafe mata rashin faɗa mishi yana da daughter da batayi ba, yayi scrolling picture ɗin Umaimah ya ƙara kalla ya mike yace. "bari naje wajen Ummi." Suka fito da Dr Huzaifa sai sauri yake kamar ya tashi sama, Dr Huzaifa ya tsaya a reception ya faɗi file number Ahmad aka bashi yana son ganin information ɗin, dan he wants to confirm something. Tahir yana gani ya mika hannu ya karɓi file din wani aiki da akayi mishi Khadija ta saka hannu ya kalli sunanta in pull Khadija Muhammad Bichi da signing ɗinta, ko daga bacci ya tashi ya san rubutun Khadijah, Dr Huzaifa ya karɓa ya mayar musu, duk Tahir ya rikice tuni ya kwashe numbers ɗin ta ya zuba a wayar shi har wata iska ya ji tana shigar shi, Dr Huzaifa ya zaunar dashi a reception yace mishi "abunda nake so kayi haƙuri kar kayi gaggawa yanzu idan sun tafi ana alhinin mutuwa ba za a saurare

Chapter 19 of 27