dole ta haƙura.
Tana gama shiryawa ta sakko wajen su Umma a Falon ƙasa, Umma tace ga abun karyawa nan, ta buɗe ta ɓata fuska tana kallon Umma tace
"fanke kuma da safe Siyama fisabillahi wanne irin fanke?
Shi aka yi da yawa za a kai gidan sadaka. Umma tace acishi kawai ba sai an yi wani abu ba."
"wlh ba zan ci fanke ba."
"Sai ki nemi abunda zaki ci." Umma ta faɗa tana ɗauke kai, "Siyama bakon ka Annabinka, a gida na wlh daɗi nake ci, wlh har na faɗa daga zuwana." Ta shafa wuyanta, "au ke ce baƙuwa? ya Amal na musu dariya tace "Je ki Deborah tana kitchen kamar doya take soyawa ni kuma fanken yayi min dadi."
Ta ja hannun Adil zo mu je, kuma wlh ranar sadakar bakwai za a ɗaurawa Baba aure." Umma ta harare ta.
"idan kika dade zamu Wuce gidan gaisuwar dan su Daddy tun safe suka tafi da mazan gidan Aliyu ne da uncle ismah kawai suka tafi aiki.
****
Yau gaba-daya farin ciki yake yana aiki yana tunanin ko Muhammad Fadoul ya kira ta yasan tana jin kunyar shi, kai he miss her bari ma ya kira ta, ya kira tana ta ringing ba a dauka ba ya gaji ya ajiye wayar, yana wajen har aka yi azahar ya idar da sallah kenan Sa'ad ya kira shi ya tambaye shi ya hanya yace tun ɗazu ya zo yana wajen aikin. "a wanne hotel ka sauka? yace be kama ba tukunna, "okay Hidaya fah tana Maitama ka kai mata ziyara please."
"Oh I will if I can make it." suka yi sallama.
Hidaya tana kitchen wayar ta tayi ringing ta dauka Yaya Fahad gaban ta ya yanke ya fadi ta daga, "send me your addres." ya fada hankali tashe ta tura mishi, bayan kamar 30 mins ya kira yana gate tace ya shigo ya karaso falo suka gaisa ta kawo mishi ruwa da lemo da abinci kadan yaci abincin ya kalle ta yace "do you know what my wife enjoys the most? I mean her favourite things."
Hidaya tayi shiru sai tace "Umaima tana son abinci." ya harare ta tayi dariya, "I'm serious she likes food and money." Ok what else make her happy?
"she loves children." Hidaya ta faɗa tana kallon shi, Shikenan? tace eh. ok ya bata kudi masu yawa yayi mata sallama.
****
SAUDIA
Yau ma yayi kiran duniya wayar ta a kashe kusan kullum sai ya kira bayan awa daya sai ya sake kira babu komai kamar yau ne tunda ya gama abunda ya kawo shi zai kira Yaseer daga US su taho SAUDIA su yi Umara sai su wuce Nigeria akan shi ya koma can, kuma Ummi ta zo tayiwa Allah godiya dan ta samu lafiya sosai ko a waya ka ji muryarta Alhamdulillah, Shahir ya kawo mishi Gahwa, yace shukran. ya karɓa, yayi dialing number Yaseer suka gaisa ya tambayi Ummi yace ta kwanta don sun bar Asibiti suna gidan Dr Huzaifa ya faɗa mishi shawarar daya yanke yace yayi bari ya faɗawa Dr Huzaifa ya saka wayar a speaker Dr Huzaifa yace yayi sai su fara shirin tahowa kawai ya riga ya dauki leave a wajen aiki suka yi sallama.
Wani irin farin ciki Tahir ya ke ji a ran shi yaushe rabon shi da Facebook dole yayi posting farin cikin nan idan be manta ba tun ranar daurin auren Khadijah da safe, yana hawa yaci karo da sakon Hamza yaron Baba Isah, daskarewa yayi a zaune hoton Hamza da suka dauka da Umaimah lokacin da su Daddy suka je ko za a samu labarin shi da wanda suka dauka da Baba Isah tare da message din da Hamza yayi cewa idan ya gani ya kira su, ba a samun wayar shi yana kallon hoton kwalla tana kwarara akan fuskar shi wani na bin wani me zai ce wa Allah sai godiya ya daga hannu yayi addu'a yayi kuka ya dade yana yin ta, mujarrabi ce duk bukatar da kake nema a wajen Ubangiji zai biya maka in sha Allahu.
*Rabbi mujibul muddari izah da 'an, inni muddar wa Qad da'autuka fa 'aljibni ( suratul naml Verse 62)*
Ya duba lokaci karfe 9 na dare Nigeria banbancin mu 2 hours ne da SAUDIA dare be yi nisa ba ya fara kiran Hamza ta gama ringing ba a dauka ba, a na biyu ya daga da sallama, suka gaisa "Tahir." Hamza ya kira shi da karfi, ina ka shiga? Iyayen Khadijah sun zo kaga sakona?"
"na gani."
Nan ya faɗa mishi layin da suka san shi da shi ya samu matsala kuma dai Allah ya yanke ganawa, Hamza yace bari ya gani ko Baba idon shi biyu.
Ba'ajima ba yaji yana cewa "Baba Tahir ne." Hamza ya faɗa a background ɗin.
"Tahir Baba Isah ya faɗa da mamaki ya karɓi wayar, Baba Isah yayi mishi faɗa sosai, Tahir dai yana ta bada haƙuri yace suna hanya acikin wani satin. "ya kamata don an yi Rasuwa mijin ita Khadijah ne ya rasu har na je musu gaisuwa." suka yi sallama da wayar Tahir yayi bacci be san lokacin da bacci ya dauke shi ba yana kallon hoton Umaimah.
*******
Kullum daga Bichi sai an kai abinci sadaka gidan mutuwar haka daga Sultan Road Baban sama kullum da shi ake yini su Baban ABU ne da Baba Dr suka koma ya tafi da Iman ma ganin Munniran tana fama da Khadijah tun washegari suka tafi zasu dawo sadakar bakwai, Umaima da ita ake yini tana tare da su Khadijah. Abun tausayi mutuwar ta daki Khadija ta rame ta fita daga hayyacinta ga rashin bacci sai da Baba Dr ya rubuta magani yace a siyo mata, saida tasha jiya ta samu bacci, yau aka yi sadakar uku mutane jimgin a gidan su Umaima suna tare da su Mami daki guda aka ware musu, wayar ta ta yi ringing ta ga an saka *Mi todo ( my everything)*
Mamaki ya kama ta to waye haka? ta fita ta daga wayar.
"Zarahhhh!" ta ji saukar muryar shi a kunnen ta, ta cire wayar ta kalli number sai kuma ta mayar kunnen ta da ƙunkuni tace "hi waya baka number ta?" Yayi wani murmushin da saida taji sautin shi a kunnen ta, haushi ya sake kamata kawai ta kashe wayar ta zo mayar da wayar jaka taga ATM card ɗin shi, yau za ta bawa Sa'ad wato ga mayyar kuɗi.
3days later
Sa'ad ya kira Fahad suka gaisa yace mishi ya aiki yace "I'm almost done." Guy dasu Adil ya kawo min ATM card dinka in ji daughter wai kace a bani." Fahad yayi ajiyar zuciya yace "ok she wants to make things difficult for me." nan ya faɗa mishi bata yayi ko zata buƙaci wani abu shi ne ta dawo da shi, "it's fine ka ajiye a wajen ka." sai ya bawa Sa'ad tausayi yace "ni kaina guduna take yi yanzu idont want to force her."
"ka kyale ta ko ni na kira bata ɗauka, daga baya she blocked me maybe dan bana samun ta."
Sa'ad yace "this is serious, but duk laifin ka ne."
"I know Ad and I truly regret my actions, mun yi magana da Daddy gobe zan taho zan samu sadakar 7 tunda jibi ne zan nemi Baba mu yi maganar yarinyar nan zata bani ciwon kai."
"Its okay hakan yayi." Sa'ad ya faɗa, wayar a speaker ya saka ta Daddy ya zo kiran shi zai aiki shi ya ji duk conversation ɗin su ya juya ya fita ran shi yayi mugun baci, ina ma ana dawo da hannun agogo baya daya bawa Dattijo mamaki ya faɗa a ran shi.
Munnirah ta fito yau da sassafe zata je bankin stanbic ibtc na bank road tana sauri tayi wani transaction ne tun kwana 3 da suka wuce ta turawa Hajiya kudi be shiga ba kuma an yi debiting din ta shi ne ta taho da kanta, ta zo parking motarta wata mai shara irin na titin nan da gwabnati ta dauka da uniform dinta maroon riga da suke daurewa akan kayansu tayi blocking wajen Munnirah tayi mata horn sosai sannan ta matsa "ikon Allah me ta ke tunani haka? Ta fito tana kokarin rufe mota ta ji an ce Munnirah ta juya suka hada ido da matar me shara bata gane ta ba sai tayi tunanin kunnen ta ne har zata yi gaba ta ji an sake kiranta ta tsaya ta waiwayo har matar ta matso suka hada ido da ita, idon ta yayi zuru zuru a rame take tubarakallah daga ganinta a gajiye take, "Munnirah baki gane ni ba ko? Zazzzzaliha ce." ta faɗa kamar mai in ina.
"Zaliha." Munnirah ta maimaita sunan da mamaki "baki da lafiya ne Zaliha? Ina kika shiga a Saudiya? Mun hadu da Mama tana neman ki?" idanta ya kada ta fashe da kuka "Mama tace kun hadu takardar kwatancen da kuka bata ce ta ɓata, ku yi min aikin gafara Munnirah." sai ta durƙusa tana gunjin kuka mutane har sun fara tsayawa kallo Munnirah tace "jira ni na shiga banki na fito ina zuwa."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 5️⃣1️⃣
Munnirah ta gama abunda zata yi ta fito daga banki ta tarar da Zaliha a tsaye a jikin mota ta ƙarasa wajen ta sai da tayi magana sannnan tayi firgigit ta ɗago tana kuka ta kalli Munnirah ko suturar jikinta ta san ta kai wani matsayi, Zaliha ta koma gefe ta ba ta hanya tace "yawwa Zaliha ina sauraren ki?" sai ta durƙusa tace "ki yi min aikin gafara ki kai ni wajen Khadija?"
"gaskia a yanzu ba za ki samu ganinta ba?" da sauri ta tari numfashita "saboda me? "Khadijah an yi mata rashi mijin ta ne ya rasu."
Zaliha a ranta tace Allah kenan wato Khadija har tayi aure bayan Tahir kila ma sun hayayyafa, mugunta fitsarin fako ita gata nan tun wannan auren cin Amanar bata sake aure ba sai wahala.
"yanzu kina wace unguwa? Munnirah ta tambaye ta, "hmm ina birget, Allah ya jikan mijin Khadija yayi mishi Rahama, dan Allah ki kai ni na yi mata gaisuwa."
"A'a Zaliha gaskiya yanzu tana gidan iyayen Mijin sai dai idan ta dawo gida gobe." To ki kai ni nayi wa su Umma gaisuwa na roƙi gafarar su, Munniran Allah ne ya karbi Addu'a ta ya haɗa ni da ke."
Munnirah ta kalli agogon hannunta takwas saura ta bude mata gaban mota tace "shiga muje." sai rarraba ido ta ke yi ta shiga.
"yaushe kika dawo daga saudia? Munnirah ta faɗa tana kallon titi, Zaliha tace "shekera daya kenan Munnirah yaran ki nawa?" tace "ɗaya."
Sai hawaye ya zubo mata ita gata nan babu auren babu yara duk jikinta a sanyaye tace "Munnirah ni mai laifi ce dan Allah ku yafe min na cutar da Khadija ban yi halacci ba." Ba ni zaki nemi gafara ba Zaliha wacce kika zalunta zaki nema. Wani takaici ne ya tukewa Munnirah zuciya ta tuno da halin da Khadija ta shiga, in banda zuciyar musulunci ma ta kula Zaliha? Sam babu wani karsashi na ka haɗu da wanda ka daɗe baka gani ba ta mayar da hankalin ta kan tuƙi bata ƙara cewa komai ba har suka iso gidan su Khadijah.
*****
Sun fito waiting lounge suna jira,Tahir ne ya fara hango Hamza yace dasu Yaseer gashi can su ƙarasa, suna taho wa Hamza ya gan su ya karaso da fara'ar shi ya durƙusa gaban Ummi ya gaishe ta suka gaisa dasu Tahir yana tsokanar shi "gaskiya ka zo ka ba ni addu'a nima akwai wata budurwa ta da iyayen ta suka hana ni nima dai ayi dani." su Yaseer da ba jin Hausa suke ba suka yi murmushi, sun isa gidan Baba Isah da ke Ƴankaba Mummy uwargidan Baba Isah kamar yarda yara suke kiranta tayi musu kyakkyawar tarba ta sauke Ummi a dakinta tayi sallah ta huta, Mummy ta zo kiranta suka shiga palour Baba Isah inda aka tanadar musu Abinci bayan an kammala Baba Isah ya kalli Ummi ya juya harshe dan alakar su da maigidan ta mai ƙarfi ce yace "Alhamdulillah Hajja Fatima nayi murna na yi farin ciki da zuwan ku abunda ban ji daɗi ba daTahir ya tafi babu waiwaye duk wayoyin da aka san shi dasu basa shiga." Ummi tace ayi hakuri an yi kuskure ciwon mahaifiya ta da jinyarta har tazo ta rasu shi yasa hankali ba a kwace yake ba ga shi ita ma ba lafiya ce ta ishe ta ba. Baba Isah yayi mata ta'aziya ya dora da cewa "iyayen Khadija sun zo neman Tahir da yar shi Fatima." yayi mata bayanin komai har rashin kyautawar da Tahir yayi na neman alfarma da iyayen Khadija suka yi saida ya sake mata bayani, mun yi musu laifi mai girma tunda babu laifin komai ya sakar musu ya suma kuma sun yi kuskure duk da daga baya sun nemi su haɗa shi da yar shi don lokacin da suka zo ma maganar aurenta ake yi."
Tahir ya ɗago da sauri ya kalli Baba Isah, har an yi mata aure wata kila ma ta haihu yana da jika ya Allah! ya rasa a wanne yanayi yake ciki, Tahir yace "Baba na sani ni mai laifi ne amma Rabuwar auren mu kaddara ce da tuggun mace, sam baya son tuno abinda Zaliha ta yi mishi."
Allah ya kyauta ina tunanin gobe ne sadakar 7 bari na kira waliyin Khadijan sai muji, ina so ya bamu lokaci goben sai mu je in sha Allahu. suka amsa da Amin.
*****
Kasancewar jirgin safe ya biyo da wuri ya sauka ya duba agogon hannun shi ƙarfe 8am ya fito uber ne ya kawo shi gida babu wanda ya san ya dawo, so yake su yi magana da Baba duk ya kasa samun sukuni straight chalet ɗin su ya wuce na bangaren Daddy ya shiga dakin shi ya daɗe yana tunani kafin ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya canja kaya ya nufi part ɗin Daddy yana shiga Mami kaɗai ya tarar a falon ya gaishe ta, tace "a'a Dattijo yanzu kake tafe? ya amsa da "eh."
Tace OK bari a kawo maka breakfast. Yace no Mami I'm OK bari na je wajen Baba. yana fita Daddy ya sauko Mami tace "yanzu Dattijo ya zo ya tafi wajen Baban su."
"toh madallah." Daddy ya faɗa, Darsha bani maganin Basur ɗin nan na jiya naji daɗin shi."
OK bari na tafasa. Mami ta tashi Daddy ya kira Ismael ya daga yace "ka tafi wajen aiki ko? yace eh.
"ina group din da uwata ta buɗe ina so ka sanar gobe akwai meeting karfe goma na safe, yau ma su Surayya suna hanya kowa zai zo."
Uncle Ismah yace "to Daddy."
Suka yi sallama yana ajiyewa kiran Baba Isah ya shigo suka gaisa ya kara yi mishi gaisuwa yace "Alhaji Ibrahim ina son zuwa gobe idan baka da uzuri." har Daddy yace babu sai ya tuno da meeting yace family meeting ne kawai karfe 10 , amma wajen 12 goben za ka iya zuwa Allah dai yasa lafiya? A'a wlh lafiya ƙalau Alhaji Ibrahim sai dai goben in sha Allah.
******
Baba suna zaune a falo da Umma bayan ta kwashe kayan break fast da suka gama ci kenan Munnirah tayi sallama da Zaliha biye da ita, Umma a ranta tace to ina Munnirah ta samo wannan firgitacciyar matar. Munnirah ta durƙusa a gaban Baba da Umma ta gaishe su, sai waige waige Zaliha take yi tana ƙarewa falon kallo, ikon Allah arziki yaci uban na da kaiconta hassada bata yi ba, lalli ta yarda an ce hassada ga mai rabo taki ce.
Muryar Munnirah ce ta dawo da ita daga dogon tunanin data tafi, tace "Zaliha ce Umma ta zo ta baku haƙuri." Umma ta maimaita Zaliha? Baba sai ya manta wacece ma Zaliha sai da Umma tace "ta zo tayi mana me? Ta ƙarasa kashe Khadija wacce dalilin ta ta haɗu da hawan jini da depression ko me? Munnirah me yasa kika kawo ta?"
"Dakata Maryama." Baba ya faɗa, Umma ta yi shiru har idon ta yayi ja tuno irin wahalar da Khadija ta sha a baya, jikin Munnirah yayi sanyi tunda Umma ta fara fada Zaliha take kuka, Baba ya kalli Munnirah yace "ina kika samo ta? Kafin ta basa amsa Umaima ta biyo Adil da gudu da wayarta a hannun shi yana dariya ganin da bakuwa a falon ta ɗan tsaya Adil ya fita bangaren Daddy da gudu, Umma ta harare ta, tace "Siyama kuka kike yi?" Zaliha ta firgita da ganin Umaima ko ba a faɗa mata ba tana wannan koma wacece jinin Tahir ce saboda kamar tasu ta ɓaci, sai ta saki baki tana kallon ta sai da ta ji Munnirah tace "a banki muka haɗu da ita, tace na taimaka na kaita wajen Khadija ta nemi afuwar ta nace babu hali yanzu ta dage sai na kawo ta wajen ku ta nemi gafara." Umaimah tana jin abunda Munnirah ta faɗa ta nemi waje ta zauna, Baba ya kalli Zaliha kafin yayi magana Daddy da Mami suka Shigo, "Muhammadu na jika shiru?" Baba yace "Yaya Munnirah ce tazo da baƙuwa shi yasa." Umaima ta ce "Daddy jarida aka kawo zauna mu ji." Allah uwata? Daddy ya faɗa yana neman waje ya zauna, Mami tace "ga ɗanki can ya hana Amal bacci." Umaimah tayi murmushi tace "gara ta tashi Mami."
"Bismillah Baba ya kalli Zaliha, ta buɗe baki da ƙyar tace "Dan Allah ku yafe min ku yi min aikin gafara nasan na zalunci Khadija Baba nasan ban kyauta ba, Umma dan Allah ku yi haƙuri nayi nadama hassada da baƙin ciki da son zuciya ne ya kai ni ya baro ni." kuka take yi kamar zata shide, Daddy yace "wai menene? Baba yace "ƙawar Khadija ce data auri mijinta." Umaima ta ƙura mata ido ta ƙara gyara Zama.
"na cutar da Khadija nina yiwa Tahir asiri ya rabu da ita." Umma ta rufe fuska Munnirah ta jijjiga kai, Daddy yace "saboda me kika yi mata asiri?" tana wani irin nishi tace "son zuciya son zuciya ya kai ni da rashin godiyar Allah, Baba shi ne kudin hayar mu shi ne kayan abincin mu, Umma ita ce sutura ta kullum a wajen Khadija nake yini sharrin zuciya yasa na fara mata hassada saboda Khadija mai ƙoƙari ce sai ya jawo mata farin jinin malamai da dalibai ta dalilina ta haɗu da Tahir sai naga ta yaya zata auri Balarabe."
Sallamar Fahad tasa tayi shiru tana mayar da numfashi, ya gaishe da Baba da Umma Munnirah suka gaisa hankalin shi na kan Umaimah daya kasa gane yanayin ta har zai fita Baba yace ya zauna. "go on."
Daddy ya faɗa, "na haɗa ta da malami ya ce na karɓo suturar ta da abincin gidanta kuɗin hannunta duk wannan abubuwan na karɓa nakai masa, dasu yayi amfani yasa Tahir ya janye yi mata hidima har abinci ya hana ta, sannan ya tsane ta kuma an yi hakan tabbas." Umma ta girgiza kai don taso ta fahimci haka a lokacin, "hakan be yi min ba Suwaiba ta haɗa ni da wani sabon Bokan ta yace na bada hoton Khadija zai yi aiki bayan ya gama aikin yace na bawa Tahir umarni ya sake ta, na same shi a wajen aiki nace ya sake ta." sai tayi shiru ta kalli Umaima da ta kafe ta da ido ta cigaba da cewa "tana Amarya na rinka bata pills dan kar ta dauki ciki......kawai Zaliha sai ganin Umaima ta yi a gabanta ta kwashe ta da mari, "da kyau Umma ta faɗa, "tashi ki fita."
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 5️⃣2️⃣
Munnirah da kyar ta riƙe Umaimah ta koma ta zauna tana mayar da numfashi, Fahad ran shi ya ɓaci, Baba jikin shi yayi sanyi ashe sihiri ne ya ɗauki zafi da Tahir sosai, Umma har ta tashi Daddy yace "Maryama koma ki zauna." Daddy yace wa Zaliha cigaba muna jinki.
"har bibiyarta nake ina siyo mata pills idan ya kare saboda bana so ta haihu kafin na shigo gidan, Kafin su rabu mun riga mun shaku da Tahir hasali ma a waje na yake cin abinci, suna rabuwa aka daura mana aure bada son ran Mamana ba dan saida nasa aka rufe mata baki sannan ta yarda akayi aurena da Tahir, auren be jima ba Suwaiba ta fara nuna tana son shi tunda na lura naja baya da ita, kuma kamar Asirin ya fara sakin shi ya fara maganar Khadija hankalina ya tashi ba yarda zan yi dole na kara komawa wajen Suwaiba. Wata ranar Alhamis muna magana da Suwaiba na saka wayar a speaker muna magana da ita akan ta taimaka min kamar aikin ya fara karye wa ta ji haushi ta fara yi min gore goren abubuwan da tayi mun har naci nasara, Ashe Tahir yana ɗaki ya dawo ni kuma ina falo kofar a buɗe take a ranar yayi min saki uku." ta dunkule hannu ta matso gaban Baba da Umma "dan Allah ku yi haƙuri Alhakin Khadijah ke bibiyata naje SAUDIA ta hannun Suwaiba ta jawo ni jiki ganin na rasa Tahir ashe tuggu ta shirya min an kama ni da ƙwaya a SAUDIA, nayi shekaru 9 a sijin, dukiyar dana tara an sace na dawo bani da komai." Umma jikinta yayi sanyi ta share hawaye tace "mun dauke ki ƴa me muka yi miki?
"Maryama ya isa haka ayi ta maimaita zance?"
She's mean Fahad ya faɗa a ran shi.
"dan Allah baba ku yafe min ko na samu saukin matsaloli na yanzu sharar titi na ke yi da aikin mu ke ci da sha Mama bata da mataimaki sai ni ƙani na mace ta janye hankalin shi." Baba yace "Zaliha alkhairi yana zama sharri? duka ku uku yayana na ɗauke ku na ji zafi lokacin da Tahir ya rabu da Khadija ashe ba laifin shi ba ne." ganin yarda Baba yake magana da tausasawa kawai karshen zancen ace an yafe mata ita bata taɓa jin wannan labarin ba Ammin ta jaruma ce sai kawai Umaima ta tashi ta shiga dakin Isma'il bata fi15 min ba ta fito.
Baba yaci gaba da cewa "kin san sai da aka yi admitting dinta a psychtric? har depression ya kama ta. Zaliha kuka take tana girgiza Kai kamar zata tada iska "ku yi min aikin gafara nayi nadama." Daddy yace "ni ban san ma wannan zancen ba Muhammad." ya kalli Zaliha yace "baiwar Allah..Allah yaso ki da rahama ba ki mutu da hakkin Khadija ba Allah kana mishi laifi ya yafe maka amna laifin wani ubangiji baya yafewa. tabbas Mami ta faɗa, "wannan zuciyar idan ka biye mata da ƙawa na rayuwar duniya zata kai ka ta baro, mu nan sai dai ki nemi gafarar su Muhammad dan kin ɓata musu amma mafi cutuwa Khadija ce kuma bata nan sai dai ki dawo wani lokaci."
"Baba Umma ku yafe min." ta riƙe kafar Umma da jikin ta yayi sanyi itama kukan take yi tace "na yafe."
Muhammad baka ce komai ba? yace na yafe mata Yaya, ta nemi gafarar Khadija." Nagode Nagode, Munnirah nasan na bata miki ke ce ƙawar Khadija ta hakika ki yafe min. wayar Umaima ta yi ringing ta daga tace ku shigo.
........Munnirah tun ɗazu data fita da safe har yanzu bata dawo ba ta kalli agogon wayarta, kusan sha daya mutane ana ta shigowa gaisuwa ana tafiya galibi ba masu zama ba ne da an yi gaisuwa ake tafiya Gwaggo ta shigo dakin ta kira Khadija ta zo za a yi mata gaisuwa da ƙyar ta taso Abokan Ahmad ne suka yi mata ta'aziya ta koma ɗaki, Gwaggo ta shigo da kayan break fast tace daure ki ci dan Allah wannan rashin cin abincin naki zai saka miki ulcer, ko ba kya so haka zaki daure ki ci, toh ya za a yi haka Allah ya hukunta mungode mishi. Khadija idonta ya tara ruwa, Gwaggo tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 27