Share this page
yi maka sharri) enjoy your space Dattijo. Yours Bad Girl. Smart. Ya karanta ya ƙara karantawa kan shi ya fara juyawa kawai ya kwanta a kasan carpet din he is lost in thought ya rasa ma tunanin me zai yi wani abu ya zo ya tsaya mishi a makogwaro, ta faɗawa Adil zata dawo in 2 days amma wannan note din ya nuna mishi kawai faɗa mishi tayi kar yayi rigima jikin shi gumi ne kawai yake tsiyaya kamar wanda ya hadiye kunama, baisan Ãdil ya shigo ba sai ji yayi yace "Papa I'm sleepy." ya jawo hannun shi da kyar suka shiga dakin shi yayi mishi wanka ya shirya shi, kawai karfin hali yake yi ya gama ya saka mishi night wears yace ya kwanta,ya fito falo ya rasa uwar uban me zai yi ya dauko ruwa a fridge ya sha ruwan ma babu daɗi, sai juya takardar yake yi a hannu har ta jike ya buɗe ya karanta ya kara ninkewa har ya haddace content ɗin takardar ya dubi time dare yayi sosai, amma Mrs Lawrence tana nan ta tafi? he will confirm tomorrow. Tunda ya kwanta a bangare daya ba bacci yake yi ba anan kasan carpet be motsa ba kamar gunki yadda ya ga dare haka ya ga rana a kunnen shi aka kira sallah ya kasa tashi har sai da aka fito daga masallaci ya tashi hoton ta ya fado daga jikin shi ya ɗauka ya kurawa hoton ido ya ajiye ya shiga toilet dinta yayi Alwala ya fito ya ƙara komawa sai da yayi Alwala sau uku sai ya koma ya kara haka sallar ma yayi ta Rafkanuwa da kyar dai yayi sallah, Ãdil ya shigo ya dan kwarara jikin shi ya yi mishi wanka yace yayi sallah, ya shirya shi sai da suka gama Mrs Lawrence ta zo ya tambaye ta jiya yaushe Umaima ta tafi? Ta yi mishi bayani wajen 01:00 haushi daya ke ji ya sauke mata, "how dare you? Why did'nt you call me, What the fuck you are useless damn it." "Papa why are you yelling?" Fuskar shi babu rahma ko kaɗan yace "you are fired." Mrs Lawrence ta bude baki zata kare kanta yace "I don't want to hear a word from you." Ãdil ya tsaya yana kallon shi. Jikinta a sanyaye ta fito compound dabara ta fado mata tana da number twin bro din shi tunda yana ziyartar su sosai tayi dialing number Sa'ad ya ɗauka ta faɗa mishi komai yace ta tsaya zai kira shi. "sweet waye?" Amira ta tambaya ya faɗa mata, "toh amma jiya mun yi magana da Umma bata ce ta zo gida ba." Sai hankalin ta ya tashi, tace "na shiga uku ina ta tafi?" Kinga relax. ya kira Fahad wayar tana ringing ya ɗauka "guy me ya faru ne? Dama yanzu yake tunanin kiran shi, what happened? He is ashamed of himself ya ma rasa me zai ce, zai faɗa mishi shi yace zasu rabu zasu yi deal zai bata kuɗi ita kuma ta kawo nata conditions ɗin daya yi leading to abunda ya faru ko me? Sai ya ji ya muzanta yarinya ƙarama ta yi mishi wayo, lokacin da ya so su rabu taki tafiya sai lokacin da taso ta tafi ta bar shi lokacin daya faɗa a sonta, yayi murmushi mai ciwo lalle she is Smart, "ka yi shiru." Sa'ad ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, Muryar shi a sanyaye ya faɗawa Sa'ad duk abunda ya faru from A -Z. Sa'ad ran shi ya baci amma ya zai yi da shi dole su nemo bakin zaren ko a haka ma yaji jiki kuma idan Daddy suka ji zancen ran shi saiya ɓaci, shi be ji haushin Umaima ba wannan cin mutunci ne ai duk yadda ake tunani tana da son kuɗi ta bashi mamaki, kuma ta yi mishi dai dai she played him, kudos to her irin Fahad Umaima ce dai dai da su. "She make my morning brighter and give me sense of direction Ad I have being living in denial I love her from the bottom of my heart pls I need your help Ad please help me." maganar Fahad ta dawo dashi, jikin shi yayi sanyi jin yadda Fahad ke magana kamar wanda zaiyi kuka yace mishi, "karka damu zamuyi solving issue ɗin okay." US Dr's ne suka rufu akan Ahmad yau wata irin shaƙuwa yake yi hankalin Khadija ya tashi sai kuka take yi Umaima duk ta rude ta rikice tana ta kaiwa da kawowa duk wasu test ita take tsayawa akan shi a dauka Khadija kwata kwata ta rikice bayan an yi mishi wasu gwaje gwaje aka tabbatar musu da hawan jinin ya shiga kwakwalwar shi matakin da ba a so kenan don Dr's sun ce yanzu kusan komai na rayuwar shi ya manta yayi losing memory din shi, tunda Khadija ta ji wannan bayani ta rikice ciwon da tayi na shekarun baya ya motsa mata. Umaima ta rasa ya zata yi da ita. Bayan Dr's sun fito suka ce yanzu sun mishi allurar bacci nan da 4 hours allurar zata sake shi sai a kira Dr din Baindiye ne Dr Vikram Sharma consultant ne sosai ya san aikin shi zai sake duba shi, kuka Khadijah take yi harda shassheka Umaima ta rasa abun yi ta kira Baba tayi mishi bayanin halin da ake ciki tunda ya ji muryar Umaimah a sanyaye ya san akwai matsala Daddy ya karɓe wayar ya kwantar musu da hankali yace sun rasa visa ne, amma iyayen Ahmad da yaran shi suna hanya su Likita ma zasu zo da Munnirah, jin Munnirah zata zo yasa Khadija hankalin ta ya kwanta. "Ammina me zan dafa miki? dan Allah Ammi tun jiya ba ki ci komai ba." idon ta jajir ta girgiza mata kai gashi bata wani bacci kwana take yi tana sallah tana addu'o'i Tahir ya sauka a US ya samu Ummi ba laifi jikin da sauki, Tahir yana zuwa Yaseer ya tafi zai je hotel ya ƙarasa shiryawa gobe zai wuce yana fita Ummi ta bude ido ta ga Tahir da khaala tayi murmushi, khaala ta matso ta yi mata kiss a goshi tace "kayfa haluk jadda?" Da ƙyar Ummi ta motsa lips ɗinnta tace "Alhamdulillah?" Tahir ya riƙe hannun ta yace "Ashshifakillah ya Ummi ( I wish you quick recovery Ummi)." ta ƙanƙame hannun shi da kyar ta kira sunan shi ta mayar da larabci, "bana son na mutu ban ga da ko yar ka a duniya ba." wani abu ya motsa mishi na rashin jin dadi ganin Ummi tana hawaye, yace " please stop crying Ummi." ya faɗa da larabci, shima kamar zai yi kukan Khaala ta shige toilet jiki a sanyaye, kukan take yi ita ma tana tausayin Uncle din ta, da fatan Allah yasa yayi aure, ta dauro Alwala ta fito. Dr Huzaifa da Dr Vikram Sharma sun duba report ɗin Ummi sun yi maganganu sosai sannan Dr Vikram ya tafi ya bar Dr Huzaifa da Tahir suna cigaba da tattaunawa. Tashin hankalin daya shiga na kukan da Ummi ta yi mishi shima ciwon zuciyar shi ya motsa, karshe dai sai da Dr Huzaifa ya bashi gado daya ke asibitin sun yi specialissing a cardiology (zuciya) khaala sai ta zama busy ta je wajen Ummi ta dawo wajen Tahir duk da yake asibitin ɗaya ne amma bangaren su daban daban. Iyayen Ahmad sun zo sun sauka a hotel Baba Dr ma da Munnirah suna tare ganin Munnirah yasa Khadija ta ɗan sake har tana cin abinci Umaima ake bari a gida saboda kawo abinci asibitin, sannan ta koma ta dora na dare ta kai hotel ɗin da iyayen Ahmad suka sauka, sosai itama take kaiwa da kawowa gaba-daya ma ta manta da wani Fahad sai Adil ne yake yawan fado mata sosai take kewar shi, ta san gobe zai yi rigima in yaji shiru bata dawo ba. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣2️⃣ Sa'ad ke waya da Fahad, yace "okay yanzu tukunna ma ka kira ka ji tana ina? Don Amira tace sun yi magana da Umma bata ce mata ta zo ba, kuma let say tana can din dole za a kira ka a ji lafiya." Sa'ad ya faɗa yana saura ranshi, shi wlh kwata kwata ma be yi wannan tunanin ba kuma haka ba tabbas da taje za a kira shi a ji dalilin zuwan nata, tunda bata jima da dawowa daga bikin Hidaya ba, brain ɗin shi kamar bata fuctioning. Sa'ad ya kuma cewa "yanzu ka kira mu ji tana ina kafin mu nemi next steps." "But Ad I'm ashamed of my actions please call and confirm please." yayi maganar muryar shi very low, sai ya bawa Sa'ad tausayi yace mishi "no kai ya kamata ka kira muji idan taje can zamu ji, idan ta faɗi wani abu dole Daddy zai yi maka magana sai mu samu idea na abunda yake faruwa." Fahad ya nisa "ok zan kira Daddy wlh Ad I regret my actions and I'm truly sorry for my mistakes." Sa'ad yace "ni yanzu do as I say ina sauraran ka mu ji yadda zamu kamo bakin zaren, ka kira Daddy din, amma honestly Guy what you did was very wrong." "I know." ya faɗa muryarshi a ciki. "ita mace bata nuna damuwa da rashin amincewa ba why you? And na sha faɗa maka understand each other you took me for granted, Allah yasa abun ya zo da sauki." da sauri ya amsa da Amin. "shikenan ka kira duk yadda kuka yi let me know ok." ya faɗa suka yi sallama har zasu ajiye wayar Sa'ad yace "and again Mrs Lawrence please bata da laifi ta cigaba da aikin ta you are not okay I can hear it from your voice." "ok I will call her." Sa'ad yace tana gidan nace kar ta tafi, "thank you." suka ajiye wayar. Ya mike da kyar ya bude ƙofa tana waje ya ce ta shigo, "thank you Sir." ta faɗa da sauri, sai ya ji ran shi ya sosu mai yake damun shi ne? haushin daya ji zai sauke a kanta me ta yi masa, "I'm sorry for how I reacted." ya faɗa, ya kalli Mrs Lawrence "it's okay sir." ta shigo ta fara aikinta. "Papa fry samosa for me." ya kalle shi be fahimce shi ba yace yaje wajen Mrs Lawrence ta soya mishi, yana zaune sai juya waya yake yi yana tunanin yadda zai kira Daddy, Adil ya dawo da samosa a plate da tea ya zauna yana ci, sai daya ganshi yana cin abinci sannan ya tuno ashe fah ya dade rabon ya saka wani abu a cikin shi, ya shiga toilet yayi wanka ya shirya ya fito toh me ma zai ci? Bari kawai ya haɗa tea ya sha ya kira Mrs Lawrence ta kawo mishi tea Adil ya miƙa mishi plate ɗin samosa, "try it Papa is nice." Kamar wanda aka umarta ya ɗauki ɗaya ya ci ya ƙara ɗaukan ɗaya ya ci, ya daɗe be ci abu mai daɗi kamar samosar nan ba sai daya cinye tas ya tambayi Adil Mrs Lawrence ce tayi masa? Ya ce "No Maamah made it for him." Ya faɗa mishi a fridge ta saka, be ishe shi ba ya kira Mrs Lawrence ta kara soya mishi wani sai daya koshi sannnan ya dauki waya ya kira Daddy. Daddy yana daga wa sai cewa yayi "Allah yayi maka albarka Dattijo." shi dai yayi shiru ya ji me zai biyo bayo baya, Mrs Lawrence ta zo ta fita da Adil school bus ta zo. Daddy yace "ka kyauta ina tausayin Khadija, barin uwata da kayi ta je wajen mahaifiyar ta abu ne mai kyau yana jin jiki, kasan Sa'ad ne da Ibrahim suka canja musu asibitin, an ce sun kware sosai." sai yanzu ya fahimci zancen dan lokacin da Sa'ad yana can sun yi magana, ok US ta tafi kenan, kenan bata faɗawa iyayensu abinda ya faru ba, yayi ajiyar zuciya yana ɗan jin relief, Fahad yace ya kira ne su gaisa suka yi sallama, suna ajiye wayar ya kira Sa'ad ya faɗa mishi inda take, Sa'ad yace shikenan zai yi tunanin next steps. US 2days later Ahmad jikin shi ya kara tsanani don ya shiga coma Khadijah sosai ta kara hargitse wa ta fita hayyacinta duk rarrashin da ban bakin da Munnirah take yi a banza gwaggon Ahmad mahaifiyar shi tace Munnirah yau ta zauna a gida tare da Khadija itama ba lafiya ce da ita ba ta rame ta fita hayyacin ta wayoyin ta ma suna hannun Umaima, ita Umaimah tunda ta bar UK ta kashe wayoyin ta da wayar Amminta take amfani, da ƙyar aka shawo kanta ta yarda zata huta kwana biyu a gida, dan da gaske idan aka bata gadon Asibiti kwanciya zata yi Gwaggo suka tafi tare da Umaimah, su ke kai wa da kawo wa akan Ahmad musanman Umaimah da yaran shi. Umaima na zaune a ƙasan carpet gwaggo na kan kujera Dr's suka Shigo tare da Baban Ahmad sai yaran shi, aka kara examing din shi aka rubuta wasu allurai da za a yi mishi, an mishi allurar suka ce after 6 hours akwai wata da za a ƙara mishi Dr yace zai dawo after 6 hour ɗin suka fita. **** UK Tunda suka yanke shawara da Sa'ad akan ya zo Nigeria su riga Umaima shawo kan iyayen su ya karɓi number Umaimah kullum cikin kiran ta yake a kashe, kullum yana cikin zullumi ga Adil tunda ya kirga 2 days bata dawo ba kullum cikin rigima yake mishi da kananan koke koke, aiki ma tun jiya daya je ya ka sa aikin komai sai dawowa yayi daga karshe ya rubuta 2 weeks leave da kyar GM yayi approving yana zaune a palo ya kai tashar SAUDIA yana sauraren karatun Alqur'ani aka yi sallama, Ramla ce ta shigo ta gan shi a zaune surprisedly taji yace "welcome." suman tsaye tayi tana kallon shi ya kula da mamaki kwance a fuskar ta, kamar a tsorace take ya kira Mrs Lawrence ta kawo mata lemo da ruwa, "have a seat pls." ta zauna a darare tace "hmm dama number Umaimah ce bata tafiya har layin nata na Nigeria ko whatapp da instagram bata hawa shine nace bari nazo na ji lafiya ko instagram bata posting." be san lokacin daya ce muga instagram page ɗin nata ba, Dressesbyumayma ya gani dama neman hanyar da zai yi communicating da ita yake tunda kullum baya samunta a waya atleast ya samu abunda zai debe mishi kewa. yace mata tana Nigeria tana da mara lafiya ne, "Allah ya sauwake Please a faɗa mata na zo." tayi mishi sallama jikinta a sanyaye ta fita, Adil ya shigo "Papa im back." ya daga mishi kai "welcome Didi." "is Maamah back? ya tambaya, bece mishi komai ba ya tsare shi da ido, kawai sai ya fashe mishi da kuka. Shima da zai iya kukan zai yi ko zaiji sauƙin zuciyar shi, yayi rarrashin duniya Adil da ko uniform be cire ba yaƙi yin shiru ya rinƙa birgima yana kiran Maamah, "No Adil don't provoke me I will beat you I'm not joking." Ranshi a ɓace yake maganar amma inna Aadil be saurare shi ba kuka yake yi yana kiran Maamah, ran shi ya ƙara ɓaci idon shi ya kada yayi jawur shima da yana da wanda zai yiwa kukan dayi zai yi don ya samu sauki, ya rasa abunda yake mishi daɗi, a hankali yace "please Didi wipe your tears." ya miƙa mishi tissue "please." ya ƙara faɗa calmly, ya fara rage kukan "I will take you to her I promise." Da sauri Adil ya tashi ya share hawayen shi "ok Papa." ya ƙarbi tissue ya goge hawayen shi yana ajiyar zuciya sai ya bashi tausayi, "now tell me what do you want to eat? "no Papa Maamah made stew for me I will ask Mrs Lawrence to cook rice for me." "ok." ya riƙe hannun shi ya cire mishi uniform yayi mishi wanka suka fito ya kira Mrs Lawrence yace ta dafa mishi rice ya kunna mishi cartoon suna kallo, hankalin shi ya tafi tunani Mrs Lawrence ta yi serving Adil abinci, tunda ta ajiye a dinning kamshin stew ɗin ya dami hancin shi tun samosan jiya shi ne har yanzu a cikin shi saboda tashin hankali mantawa yake yi da abinci, ya kalli Ãdil ga wani pepper chicken a gefe, "come and join me Papa?" Ãdil ya faɗa, yaci spoon ɗaya ya miƙawa Fahad ya karɓa yaci haka suka rinƙa kama kama kan ka ce me sun cinye abinci ba zai yi ƙarya ba ya daɗe be ci solid food me daɗin wannan ba, so all this while this is what he have being missing? ***** Khalaf ce ta fito da sauri zata je office ɗin Dr Huzaifa, Umaima ta taho da hanzari suka bangaji juna ledar hannun Umaima ta magani ta faɗi ƙasa khala ta sunkuya ta ɗauka ta miƙa mata "sorry sister." khaala ta faɗa da murmushi a fuskarta, "Umaima da face mask ne a fuskar ta itama tace mata "never mind." tana kallon khala ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, "are you here to visit someone? Khala ta tambaye ta, "my uncle is admitted here." Khala tace " Am sorry for that, and my grandma is also here." Umaima tace "wish her quick recovery." Khala tace "thank you, where are you from?" "Nigeria." Umaimah ta faɗa, "my Uncle know much about your country." Really? Umaima ta tambaya, khala tace "yeah nice to meet you my name is khaala Yaseer from Lebanon." ta mikawa Umaima hannu, Umaimah ta bata tana hannun tace "my name is Fatima and my father is from Lebanon too." Da sauri khaala tace "really? Where is your Father?" Umaimah ta buɗe baki zata yi magana Dr Vikram Sharma daya aike ta karɓar magani ya hango ta, ta yi maza da sauri ta karasa wajen shi, ita fa ake jira, kafin Khaala ta kula har tayi mata nisa ta biyo bayanta rooms dayawa ta rasa wanne room ta shiga down floor ne su Ahmad, su Khaala kuma suna fourth floor. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣3️⃣ Ganin ta kure raw na dakunan wajen bata gane inda ta shiga ba ta juya ta tafi office din Dr Huzaifa tana tunani a rai taso ta ji ina su ke zaune a Lebanon dan farat daya taji tayi mata bata ga fuskar ta sosai ba saboda da face mask ɗin fuskarta, amma daga ganin ta ba za su wuce sa'anni ba daga dukkan alamu, ta daɗe tana knocking kofar office ɗin ta ji shiru ta bude babu kowa a ciki ga wayoyin shi a zube a kan table, Abbun tane ya kirata yace yana son magana dashi ya kira Dr Huzaifa be dauka ba yana son jin lafiyar Tahir tunda ya ji bashi da lafiya hankalin shi be kwanta ba, yana hanya gobe tunda Allah ya taimake shi abunda ya je yi ya kammala, ta fito daga office ɗin ta tafi taso sun ƙara haɗuwa da Fatima dan gobe zata koma Lebanon idan Abbu ya dawo, don har an fara neman ta a wajen aiki, tana shiga Ummi bacci take yi kwana biyun nan alluran da ake mata suna saka ta bacci sai ta dade tana yi wayarta tayi ƙara ta ɗauka Abbu ne ya tambaye ta Dr Huzaifa tace daga office ɗin shi ta ke baya nan yayi mata tambayoyin jikin Ummi ta faɗa mishi da sauki ya bukaci ta bashi Ummin a waya tace bacci take yi, ya tambaye ta jikin Tahir tace ya ji sauki sosai kawai Dr Huzaifa ne yace yana buƙatar hutu sosai shiyasa be yi discharging ɗin shi ba suka yi sallama. Saurin da tayi na kawo wa likita maganin numfashin ta yake sama da kasa ta cire face mask ta shigo ɗakin Dr Vikram yace "you stayed for too long." "I'm sorry." ta faɗa, Dr Huzaifa daya ke rubutu ya dago ya kalli wacce ta bata musu lokaci ya dubi agogon hannun shi yana son zuwa wajen Tahir har ya dauke ido akan ta ya kara mayar da ido kanta kamar wuta ta ja shi wani irin shock ya shiga da ganin fuskar ta, Gwaggo tace "sannu, ai tana ma ƙoƙari." Umaimah tace "wata ce ta tsayar da ni a hanya." Babu komai wannan zirga zirgar da kike yi ai da wahala Allah yayi albarka." "let me see the other test?" muryar Dr Vikram ta dawo da Huzaifa daga Duniya tunanin daya tafi ya miƙa mishi takardar test ɗin da aka saka ta a bayan gadon da Ahmad yake kwance, Amma Dr Vikram be ga kammanin patient ɗin su da wannnan yarinyar ba? Ko shi kadai ya gani ko daya ke ba lalle shi ya kula ba, shi ya dade da su Ummi shekaru masu yawa tun kwanciyar Tahir asibiti suka zama aminai sun wuce abokai ko SAUDIA da ya kwanta akan matsalar zuciyar shi tare suka tafi yayi jinyar shi da yake lokacin yana hutu. "i think we are done." muryar Dr Vikram ta dawo dashi kamar mutum mutumi ya gyaɗa kai. Umaimah ta harare shi a ranta tayi tsaki tace "Wannan mutum akwai shegen kallon kurilla, ka ci kan ka idan maye ne." ta ƙara dagowa suka haɗa ido ta harare shi, aikin banza ya ɗauke kai yayi murmushi, "yaya aka yi ne Umaima." gwaggo tayi maganar, tace "babu komai gwaggo." ta ja mayafi ta rufe fuskar ta, Dr Huzaifa ya shafa aljihun shi be ɗauko wayoyin shi ba dole ya dawo ɗakin nan dabara ta fado mishi file ɗin Tahir daya ke tare da shi kawai ya ajiye shi as ya manta zai zama dalilin dawowar shi a zuwan ya manta tunda an gamawa Ahmad komai na yau Nurse kawai zata zo bayar da magani suka fita da Dr Vikram. "kaai na tsani kallo wlh." gwaggo tace "nima na gani kinsan fararen nan akwai su da son mata." gwaggo tayi murmushi tace "ko ya ɗauka budurwa ce." sai da ta faɗi haka ma Umaima ta shafa mararta ita wlh mantawa take yi da wani Fahad da Auran shi Adil ne kawai a ran ta tasan zai yi rigimar nemanta, wayar Khadijah dake tare da ita tayi kara ta daga Sa'ad ne, da dabara ta fita waje ta daga yace "haba daughter meyasa tunda ake abunnan baki faɗa min ba bana samun ki a waya WhatsApp intangram duka ba kya hawa sai Umma na kira tace a wannan layin zan same ki." Tana jin muryar Sa'ad bata son yin maganar nan da kowa sai Uncle Ismah bari tayi idan suka koma Nigeria ya zo da kan shi ya tonawa kan shi asiri, amma ita ba za ta yi maganar da Sa'ad ba ta make murya a ciki ta gaishe shi, yace "yaya lafiya dai ko? "hmm bana jin dadi ne." Ayya wlh naso mun yi magana amma I don't want to stress you pls have enough rest, ya mai jikin?

Chapter 17 of 27