kallonta ta mike kar ta karya mata zuciya, ta aiko Salama ƙanwar Ahmad tace ta tabbatar Khadija taci abinci, ganin Munnirah me matsa mata taci abincin bata nan, ta haɗa mata tea ta zuba mata doya da sauce a plate tace dan Allah kici Yaya Khadija. haka ta karɓa kamar tana cin madaci slice ɗaya kawai ta ci gabanta yayi wani irin mugun faduwa ta dafe kirji, "sannu Yaya Khadija." Salama ta faɗa, kasa magana tayi ta daga mata kai "Hasbunallahu wa niimal wakil." take ta maimaita wa, irin yanayin ta shiga ana ya gobe Ahmad zai rasu.
A daidai lokacin da Khadijah take faduwar gaba shi Tahir farin ciki ne ya sa ya kasa sukuni ya fito ya tari dan sahu daga hotel din da suka sauka ya tafi Hadejia road gidan da suka rayu da Khadija, ya dade da siyar da gidan kawai ya tako tun daga farkon layin har bakin gate ɗin gidan memories suna dawo mishi ya tuna ranar da suka wuce Khadija a mota da Zaliha ranar daya sake ta, ita ce ranar karshe da suka rabu da Hayateey a hankali yace "I'm so excited zan sake ganin ki." haka ya fito bakin titi ya koma hotel ɗin da suka sauka su uku bristol hotel Ummi a gidan Baba Isah ta sauka.
****
......Yan sanda ne mata guda biyu suka Shigo da sallama Umaima ta nuna Zaliha tace gata nan. A firgice Zaliha ta kalli Umaimah kowa fuskar shi da mamaki Munnirah tayi murmushi lallai ƴar su ta haifu, idan ban da zuciya ta musulunci ko a hanya ba zata kalli Zaliha ba, Daddy yace "ko dai kuskure kuka yi? Babu kuskure sir. Umaimah tace "Daddy nina kira su."
"uwata ayi haƙuri. ya kalle su yace "ku yi hakuri..... sallamar Yaya Surayya da Amira ya katse Daddy suka shigo ana ta gaisawa yace "ku yi haƙuri zamu yi resolving issue din family issue ne." ya debo kudi ya basu suka karɓa suka juya."
Wani irin ihu Umaima ta kurma tana kuka "matar da ta so kashe ni tun ina aciki shi ne ba za a hukunta ta ba? Zaliha ta gigice lallai biri yayi kama da mutum fuskar Tahir take gani yau taga Aya tana kuka tana ki yafe min, rarrashin duniya su Munniran da Yaya Surayya da Amira suka rufu a kanta suna yi ta ki shiru Daddy ran shi duk babu daɗi Baba da Umma sun kasa motsawa Fahad da ran shi ya ɓaci yace "is time for you to leave." ya nuna Zaliha yace "fita anan."
Yaya Surayya ta kalle shi da mamaki, Hakimi ne ya shigo da sallama yace Abbas ya kira ni wai Umaimah tace ya bata yan sanda me ya faru? hankalin shi a tashe Daddy yace zancen da tsaho tana ganin Uncle Isma ta tafi wajen shi da gudu ta rungume shi Fahad ya runtse ido da sauri yana ɗauke kanshi gefe, Isma'il ya jata dakin shi Fahad ya bi su da kallo sai kuma ya tashi ya bi bayan su, ya ɗan dade a tsaye a ƙofar ɗakin Ismael ya fito ya gaishe shi yace ya shiga mana. Baya son tayi mishi wani abu a gaban Ismael shi yasa yaƙi shiga tin farko.
Ya shiga ɗakin tana zaune tana kuka, ranshi duk babu daɗi ya zauna a gaban ta yace "Zarahhhh ta kalle shi wani kuka na sake zuwar mata ya buɗe mata hannu ta faɗa jikin shi ya rungume ta yana ɗan bubbuga bayan ta cike da wata irin kaunar ta dake dukan zuciyar shi yace "I'm sorry for that." Ta sake shigewa jikin shi tana sauke ajiyar zuciya, Isma'il ya shigo da hijabinta a hannun shi zai koma yace masa "no come in." ta sake shi ya bata hijabin ta saka. Fahad ya fito ya dawo falo sai gasu sun fito Isma'il ya riko hannunta suka tarar da Daddy da Baba suna tayi wa Zaliha nasiha sai ajiyar zuciya take yi Ismael yace wa su Daddy zai fita da Umaimah, "hakan yayi PA, an taso ka a wajen aiki." Daddy ya faɗa, wayar munnirah tayi ringing ta daga. Ta gama wayar tacewa Umma zan koma wajen Khadija yanzu ta kira tana jira na, Yaya Surayya tace nima sai muje tare Amira ma tace muje kawai jikinta a sanyaye tunda ta fuskanci kan zancen, Fahad yana kallo su Umaima suka fice su Munnirah suka rufa musu baya.
Toh na tafi Munnirah ta faɗawa Zaliha, suka fita suka bar su Daddy suna mata Nasiha, Daddy ya bata kuɗi masu yawa yace idan an kwana biyu sai tazo ta nemi gafarar Khadija, ba a faɗa da hukuncin Allah tashi kije Allah ya yafe mana gaba ki ɗaya.
"Nagode Nagode Nagode." ta mike tana haɗa hanya ta fita, Daddy ya kalli Baba yace mun yi rana kaina ciwo yake bari nayi Azkar na kwanta. "shikenan Yaya Allah ya sauwaƙe." Mami ta miƙe suka fita tare da Daddy, Umma ma jakarta da hijabi ta dauka ta hau sama sun fasa fita gidan makokin, sai ya zama na daga Baba sai Fahad a falon, tunani yake kar dai yayi rashin hankalin maganar yanzu ganin abunda ya faru, ko dai ya bar maganar, toh idan be faɗa ba haka zata yi ta wahalar da shi hmm. Baba yayi shiru yana kallon shi yace "ya aka yi ne Dattijo?
Gabanshi ya faɗi, gaskiya be kyauta ba shi waya aike sa wannan danyan aikin? ya rasa ta inda zai fara maganar, "Dattijo ka faɗa min mana koma menene da ni da Yaya ai duk ɗaya ne babu banbancin." sai jikin shi ya sake sanyi, a nitse yayi wa Baba bayani be boye masa komai ba.
"Amma ban ji daɗi ba Dattijo kun yi shirme aure ba abun wasa ba ne da za a rinƙa bashi condition, ni da kai ba surukai bane hasali ma ni kaine nawa, daka same ni ka faɗa min baka bukatar zaman nata ni nasan yarda zan faɗawa Yaya ba zai ji zafin kaba."
Baba yayi wani tunani bari ya gwada shi yace "shikenan shi aure rai ne dashi duk lokacin da kaso ya mutu ba zai mutu ba sai lokacin da Allah yayi, yanzu dai tunda baka bukatar ta a rayuwar ka babu matsala nasan yadda zanyi da kowa bame ganin lefin ka kabani takardar ta kawai." da sauri Fahad ya kalli Baba bakin sa har haɗe wa yake yace "A'a Baba wlh inason ta."
A'a Dattijo ba'ayi haka ba kai da har kuɗi zaka bayar saboda ku rabu, yanzu kuwa zaka rubuta takarda babu ko sisinka."
"Wallahi Baba kuskure ne kuma na yi danasanin haka, tuntuni ina son faɗa mata na janye aiki ya min yawa kanna faɗa ta taho."
Baba ya sake gyara zama yana kallon shi kamar gaske yace "A'a Dattijo gara dai a raba auren nan kowa ya ne mi abokin rayuwar shi.
"wlh Baba ni ne abokin rayuwar ta." sauran kadan Baba yayi dariya ya ɗaure yana mamakin Dattijo daya ware yana tona asirin zuciyar shi, ya gamsu da gaske yayi nadama kuma ya ga soyayyar Umaimah a idon shi ya san Umaimah butsuwa ce sai an yi da gaske kafin a shawo kan ta.
"Allah Baba ba zan iya rayuwa babu ita ba, ta saka rayuwata ta zama mai manufa inason Matata Baba please." Fahad ya faɗa da kalar tausayi, Baba yace naji yanzu da wa ka yi maganar nan?
"Sa'ad ne kawai." To kar a kara maganar da kowa zan same ta mu yi magana zamu warware matsalar in sha Allahu, uwata tana da daɗin zama ku kwantar da hankali ku fahimci juna nasan tana da gazawa a wasu bangarorin a hankali sai ka gyara ta kai ne shugaba rayuwar aure zo mu zauna zo mu saba ne, bama da ita ba ko da waye sai an yi hakuri an kai zuciya nesa, itama zan mata faɗa sosai ka kwantar da hankalin ka, Allah yayi muku albarka."
"nagode Baba Allah ya kara girma." ya tashi ya fita zuciyar shi wasai.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 5️⃣3️⃣
Tunda ya bar wajen Baba ran shi yayi sanyi,
Allah yasa dai ta sauko Amma Hakimi yayi announcing meeting Allah yasa ba zancen ba ne, kai baya jin zancen ne tunda dai su uku ne kawai suka san zancen, data faɗawa Daddy kila da tuni ma ya magantu. Hmmm ko a wanne hali ta ke yanzu?
Yana son ya ji kota ta daina kuka ya kalli Adil daya ke kwance a gefen shi tunda ya shiga part din Daddy ya biyo shi yayi bacci anan bari ya kira Hakimi ya ji ya take ya daga wayar shi ya kira tana ta ringing ba a daga ba.
.........A zoo Road Isma'il ya ajiye ta wajen su Isiyaku, tace idan ya tashi aiki ya biyo su koma gida tare, ranar tayi aiki sosai duk ranta babu dadi ta yi keeping kan ta busy saboda al'amarin Zaliha ya ɓata mata rai babu wanda ya taɓa faɗa mata, Allah sarki Ammi ta sha wahala shiyasa kwanaki ta yi mata faɗa sosai har take cewa an taɓa hana ta abinci? Sai yanzu ta tuna waɗannan abubuwan ne suka yi mata ciwo, shiyasa tafi gane friends Maza akan Mata su Maza basu da bakin ciki da hassadar mu ta mata, indai zaka yi tsabtatacciyar alaƙa da su sun fi daɗin Zama sosai akan mata.
Tana kan keke tana ɗinki gabanta ya faɗi ta dafe kirji tana maimaita innalillahi wa inna illahirrajiun haka ta daure ta cigaba da dinkinta tana shago har 6 Uncle Ismah ya kirata a waya ya zo su wuce gida, ta fito da kumburaren idonta da ta sha kuka ya kalle ta yace "kin gan ki kuwa? fuska a kumbure."
"hmm duk bayanin da na yi maka be isa ya saka dan Adam kuka ba Uncle Isma? to ita Ammi Asiri aka yi mata ni kuma rejecting ɗina aka yi." Ismael yace "kamar yaya? Tace Yauwa dama kai kadai zan faɗawa ta kwashe komai ta faɗa mishi, yayi wani tunani yace "ko shiyasa Daddy yace za a yi meeting?
"anya kuwa kodai akan Ammina ne." Yace "a'a ya kira ni kafin Zaliha ta zo." Na gani ka yi announcing, wannan banzar matar ce ta saka ban yi maka maganar ba.
"Amma Please tunda ya baki haƙuri komai ya wuce. Da mamaki tace "haba Uncle Ismah wulakanci fah yayi min kasan ba a kai ni ƙasa." Isma'il yayi murmushi yace "ni kuwa na sani Smart."
Kamar wata mara galihu, gani mayyar kuɗi an faɗa mishi son shi nake yi? Allah yanzu dai yayi nadama. Isma'il ya faɗa, "ni wlh ya sake ni makaranta ma zan koma na tafi Lebanon neman Babana tunda babu wanda ya damu, shima dan babu uba na ne yake min gani gani."
Da sauri Uncle Ismah yace "kedai kika fassara haka."
Har suka iso gida sunata tattaunawa, da sallama suka Shigo tayi wa su Baba sannu da gida ta haye sama, Daddy yace uwata fah mun yi mata laifi. Baba yace shirmenta dai mace tazo neman gafara ki dauko mata yan sanda mun zama ɗaya kenan.
Ranta a ɓaci tayi bacci, tana cikin baccin Amira ta ɗaka mata duka ta tashi, Amira tace "ban son wulaƙancin na zo kin share ni ko ba kya murnar gani na? babynki yana murna zai zo wajen Aunty Umaima."
Amira ta bata haushi amma faɗar hakan da ta yi sai ta shafa mararta, oh dan Amana ita kwata kwata cikin nan baya bata wahala hasali ma babu wanda yasan da shi ta zauna ta kalli Amira tace "wai wata nawa cikinki naga girma yake yi."
7month fah. Dan Allah ki saka Umaima in kin haihu. Amira ta harare ta tace "ki taso kici Abinci in ji Umma."
Hmmm wlh bani da appetite. Amira ta rike baki "wai yau wacce rana Umaima da kin Alda'am." Mtws tayi tsaki tace kya ji dashi.
Suna haka Baba yayi sallama ya shigo ya kalli Amira yace "auta bamu waje zan yi magana da uwata." Umaima ta marairaice fuska Baba yace "fishin ne har yanzu? Baba kuka bar Azzalumar matar nan taci bulus. yace Allah yana son masu afuwa uwata, ta zalince ta yanzu waye da riba? Fada min da kanki, kina ganinta sa'ar Khadija ce amma kalli kamar ta haife ta, hakki kawai ya ishe ta, wannan ya isa darasi ga masu hali irin nata. Sai kuma yayi shiru yace "Fatima."
Umaima ta dago da sauri ta kalli Baba, yace "magana zamu yi Dattijo yayi min bayanin komai dukan ku kun yi wauta." tace "Baba cewa fah yayi baya buƙata ta zai bani kuɗi mu rabu na fita daga rayuwar shi." Baba ya katseta "duk na ji bayanin shi kuma yayi nadamar abunda yayi kema baki kyauta ba kin yi laifi, me yasa kika taho babu iznin shi? mun dauka da yardarshi kika tafi wajen Khadijah aure ba abun wasa ba ne daga yanzu idan kun samu matsala ku zauna ku tattauna ko rayuwar Khadija ta zame miki darasi mana, komai dan haƙuri ne wani abun ba mu sani ba sai ɗazu da kanta ta faɗa mana." Umaima tace "hmmm ai Baba bazan iya irin na Ammi na ba." Na sani dan ba halin ku ɗaya ba, cikin yara na Khadija bata dana biyu kuma kowa nasan halin shi, yanzu dai tunda babu wanda ya ji zancen nan sai ki rufa muku asiri a cigaba da haƙuri ina ta murna tunda aka yi auren bamu ji matsala ba kar ki ba mu kunya uwata.
A sangarce tace "toh Baba be taɓa cewa yana so na ba." Baba yayi dariya yace "ni ya faɗa min idan wannan ne matsalar, bana son kowa ya ji zancen nan."
"toh naji amma ka dan yi wani abu ka bani cin hanci dan da Siyama zan faɗawa kuma magana ta je kunnen Siyama kowa sai ya ji." ta faɗa tana dariya, Baba yace "shikenan me kike so?" Dayi dariyar ta mai kyau tace "Ba mai ji Baba amma mu ɗan huta gaskiya kar mu koma yanzu."
A'a uwata shi da ya bar aiki. "shikenan saboda kai zan koma Baba, gobe meeting din me za a yi? Baba yace "Yaya Ibrahim ne ya kira bani da masaniya, to ko maganar za a yi?
"anya kuwa? Babu wanda yasan zancen sai Sa'ad." ta faɗa, "eh gaskiya bana ji zai faɗi maganar.
Ta dafe kirji, Baba yace menene? Wlh Baba gabana faɗuwa yake. Subhanallah ki yi ta innalillahi wa inna illahirrajiun babu abinda zai faru in sha Allah, mu je ki ci abinci." suka sauko tare.
~~~~~Washegari
Tun karfe 7 aka yi sadakar bakwai Dada bata samu zuwa ba saboda Babancikin gida baya jin daɗi amma an aiko da masa mai yawa daga Bichi, suna zaune ana ta karbar gaisuwa Ismael ya kira Umaima Daddy yace su fito matan a tafi.
Nan su gwaggo aka hau koke koken sallama da Khadijah itama kukan take yi mutuwar sai ta dawo musu sabuwa har mota suka rakata kowa jiki a sanyaye.
Baban sama anan su Daddy suka tarar dashi Baba Dr ma yana gari tun jiya dashi aka yi sadakar aka shisshiga mota aka nufi gida Daddy yace Muhammadu kira Yaya Abubakar (Baban ABU) mu ji ko ya kusa ƙarasowa. Baba ya ɗaga waya ya kira shi.
Suna isa gida da yake fitar sassafe ce yanzu ake karyawa, kuma ranar ta fado a Sunday kowa yana gida.
........Munnirah ke lallaɓa Khadija ta samu taci wani abu, Umaima tun tashin ta da safe gabanta yake ta faduwa, Munnirah tace "wacce irin sangarta ce wannan kin saka ta a gaba kina mata kuka Umaima, ki barta da abunda yake damunta mana kina kara mata damuwa." Umaima sai ta kara gyara kwanciya a cinyar Khadija tana tsiyayar da hawaye tace "wlh Mamin Rijiya gabana keta faɗuwa tun jiya." Munnirah ta kalli Khadija dan tun jiya tace mata gaban ta yana faɗuwa sai Khadija ta fara kukan itama, tana tunanin to waya sani ko wani mummunan abu ne zai same ta? Tana kuka ta fara karanta *"Wa ufauwidu amri illallah innallaha basirun bil ibad (and I entrust my affair to Allah, indeed Allah is all seeing of his servant ) surah Ghafir,Verse 44*
Itama Umaimah sai ta kama tana yi a haka ya Amal ta shigo tace Daddy yace su sauko su ake jira.
Khadija ta goge hawayenta haka suka yi ta kuka suka haɗu suna ta rarrashin su, Allah ya jikan Ahmad cewar Aunty Amal sai hak'uri da ƙyar Khadija ta lallaɓa suka sauko .
Bayan kowa ya hallara Baban sama yace 'Sallu alannabiyul kareem." aka yi wa Annabi salati ya kara yiwa Khadijah gaisuwa aka kara yiwa Ahmad addu'a sosai aka shafa ya kalli Daddy yace "Bismillah Ibrahim."
Daddy yayi sallama ya kalli agogo ba su fara da wuri ba sun ci lokaci har 11 ta yi ya nisa yace "Alhamdulillah mu iyaye ne duk abunda muka zartar akan yaran mu muna ganin mun isa ne haka ne? aka amsa haka ne, yace "madallah." kafin ya cigaba Baban ABU ya shigo aka gaggaisa.
Daddy ya cigaba da magana "duk hukuncin da muka zartar bana tunanin akwai cutar wa ga yaran mu. Fahad da hankalin shi yana kan Umaima jikin shi yayi sanyi hankalin shi ya kai kololiwar tashi suka haɗa ido da Sa'ad ya girgiza masa kai.
"Abunda yasa na tara ku tun farko ina ganin haɗin dana yi na Dattijo da uwata kamar za a samu fahimtar juna ganin yadda yake ita uwata kuma mai raha ce da daɗin zama mai karsashi ce a hankali zasu fahimci juna, ashe ba haka ba ne." Fahad yayi mutuwar zaune kwakkwaran motsi ya kasa falon yayi tsit, Baba da mamaki yake kallon Daddy yana son sun haɗa ido da shi yaƙi kallon shi ya dauke kai. "shi dan uwan shi tun farko ya karbi zaɓi na Amma shi Dattijo sai da aka kai ruwa rana toh yanzu ba sai anjima ma Dattijo ya sakar min uwata wlh." Baban sama yace "subhanallah me ya faru? Me yayi zafi Ibrahim?" Baba Dr yace "Yaya abun be kai haka ba. "ya kai Likita."
Innalillahi wa inna illahirrajiun Umma take maimaitawa, Mami har ta fara kuka, Umaimah ita hankalin ta yana kan Amminta da ta zama absentminded kamar bata wajen tare suke a zaune a waje ɗaya jikinta ma yayi zafi tana jin hucin zafin jikinta kamar wuta.
"Yaya ayi hakuri sun fahimci juna."
"dakata Muhammad ka kyale dan yau da kaina na ji yana faɗawa dan uwan shi a waya wai har kuɗi ya bata cheque ta rubuta ko nawa ne dan su rabu."
Aliyu ya daga kai ya kalli Fahad ya sunkuyar da kai ran shi a ɓace ya ƙara tamke fuska.
"Ita kuma daya ke ta haifu taƙi yarda, babu abunda ban ji ba." nan Daddy ya warware musu komai, Mami kuka take yi su Yaya Surayya jikin su yayi sanyi.
"wlh Daddy yayi nadama cewar Sa'ad."
Fahad ya taso a hankali ya nufi Daddy ya durƙusa a gaban shi yace "Daddy ayi min Afuwa wlh nayi nadama nayi kuskure." idon shi yayi jawur saboda tashin hankal.
"zancen ku ke so." cewar Daddy, Baban sama zai yi magana isowar Baba Isah dasu Tahir ta katse abunda zai fada.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 5️⃣4️⃣
Baba ne ya tashi da sauri yana kallon ƙofa yace "wa nake gani kamar Tahir?"
Tahir da yayi shigar Hausawa farar shadda ce a jikin shi da hula baƙa yayi kyau Yaseer, Dr Huzaifa da Ummi na biye dashi a baya.
Daddy ya miƙe yana musu maraba.
"sannun ku da zuwa." Umma da jikinta yayi sanyi ta faɗa tana miƙe wa ta bawa Ummi wajen zama.
Kowa a falon Ummi yake kallo da mamakin kamanin ta da Umaimah, tunda Baba ya ambaci Tahir Umaimah take kallon su ɗaya bayan ɗaya, kamar fah Tahir taji ance.
Khadija da take kusa da ita ta daga kai gabanta na wani irin mugun faɗuwa ta kalli Tahir tabbas Habibinta ne ko acikin dubban maza zata tsamo shi take taji kanta ya fara juyawa.
Shi kuma a ɗarare ya shigo kan shi a ƙasa yana auna girman laifin da yayi wa waɗannan bayin Allah kuma surukai a wajen shi. Daddy ya basu waje suka zauna, "a kawo ruwa da lemo." Baban sama ya faɗa, Isma'il ya tashi ya tafi ya kawo.
"Tahir Babana ko? Babana ake nufi." Umaima ta faɗa a hankali tana tahowa inda suke, babu wanda ya kula ana ta gaishe gaishe har ta zo kusa da su tace
"Kaine Babana?" muryar Khadija Tahir ya ji a kanshi ya ɗago da sauri idon su ya faɗa cikin na juna, gaban shi ya faɗi da sauri ta ƙarasa wajen shi ya miƙe ya buɗa mata hannu ta rungume shi tana fasa kuka.
"Alhamdulillah Babana ne ashe zanga Babana kanna mutu? Ina ka tafi ka barni na yi missing ɗinka."
Tahir kuka ya ke yi hawaye wani na bin wani, tausayin su ya kama su Baba, Umma da Mami sai share hawaye suke, sosai Umaima ta basu tausayi.
Ummi ta taso daga inda take zaune ta riƙe Umaimah, ta ɗago suka haɗa ido da Ummi gabanta ya faɗi sai ta rungumeta, tasan koma wacece wannnan jinin ta ce, da wani irin farin ciki ta kalli su Baba tace "laaa ku kalli twin ɗina jama'a." ta fada tana dariya da hawaye sai yanzu ta kula da Dr Huzaifa yayi mata murmushi tace "Dr my twins." yayi murmushi ya ɗaga mata kai
"your grandmother." ta kara rike ta ta fara waige waige "Ammina."
Khadija ta kafe waje daya da ido (absent-minded) kamar mutum mutumi, Ummi ta ja hannunta suka zauna, Tahir sai dan kalle kalle yake yana neman Khadija, idon shi ya faɗa kanta ta kafe inda suke zaune da ido, amma kamar ba nan hankalinta yake ba. "Hayateey."
ya kirata da wata irin murya mai cike da kewa, a hankali sakon shi ya je gareta ta kalle shi suka haɗa ido babu ko kiftawa.
Maganar daddy ce ta katse shi daga kallon ta, hankalin shi ya koma wajen Daddy.
Fahad har yanzu yana gaban Daddy a tsugunne bai ɗago kanshi ba, farin ciki ne ya mamaye ran shi ya taya Umaimah murna, tabbas yau ranar farin ciki ce a bangare ɗaya kuma be ji daɗi ba ace ranar da zai haɗu da surukinsa a ranar aka haɗa meeting akan shi, Baba Dr ya miƙawa Dr Huzaifa hannu su ka ƙara musabaha yayi wa su Daddy bayanin ya taimaka musu sosai a US aka yi ta mishi godiya.
Umma godiya ta keta yiwa Allah sai Tasbihi take a zuciya tana kallon Umaimah da Ummi, Su Aliyu, Ibrahim, Sa'ad da Isma'il suka gaishe dasu Tahir, kowa bakin shi da fara'a.
"my granddaughter." Ummi sai ta kalli Umaima ta kalli Tahir, Umaima ta lafe a jikinta kamar zata koma cikinta, Masha Allah Daddy yace kowa ya koma wajen shi ya zauna ya fara godiya ga Allah yayi musu sannu da zuwa ya kalli Tahir yace
"kafin dai komai Tahir mun yi maka laifi matsayin ka na uban Umaima, ba komai ya saka ba a faɗa maka ba alokacin sai halin da Khadija ta shiga Hasali ma ba ta yar ake yi ba alokacin ta halin da Khadija take ciki shi ya daga mana hankali. Daddy suka ya yi mishi bayani har zuwan da suka yi neman shi wajen Aminin mahaifin shi "muna kara baka hakuri kuma har ga Allah muna da niyyar zuwa Lebanon neman ka." Baba Isah ya karɓi zancen "kwarai kuwa an yi haka duk nayi mishi bayanin komai haka Allah ya tsara kuma ya hukunta, Alhamdulillah Tahir me zaka ce?"
Yayi Sallama yayi gyaran murya Umaima murmushi kawai take yi a lokaci daya kuma tana hawaye yace "ni mai laifi ne nima ina buƙatar yafiya a wajen ku duk abun daya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 27