Share this page
sorry Papa. suka fita da Iman, shawarar daya yanke ya san ba za a bashi wani leave ba zai ɗauki leave without pay for 3months su zagaya duniya yana tunanin barin Adil a Kano kawai idan suka dawo su biyo su dauke shi ya buɗe System ya fara typing mail. Allah yasa ayi considering request din shi bari ya je ya samu Mami su yi magana, ya fito ya nufi wajen Mami Deborah ce a palo tana goge goge ya tambaye ta Mami tace tana daki ya hau sama yayi knocking Mami ta amsa ya shigo da sallama tana zaune tana kallon sunna Tv ya zauna. Mami tayi mamakin shigowar shi "yaya dai Dattijo?" ya shafa kai "Mami maganar komawa ta ne nake tunanin barin Adil anan zamu yi tafiya da ita." Ita wa? Mami ta fada tana dariya Alhamdulillah danta yayi baki shima dariyar yayi tace "toh har tsawon yaushe zaku dawo?" 3 months. "hakan yayi kyau indai zai zauna ai shikenan, naga sun shaƙu da Iman yanzu suka fita daga nan wai zashi wajen Maamah, shi ne nake tsoron rigimar shi" Fahad yace Mami sai kuma yayi shiru. menene? Ka faɗa mana. "wlh Mami tuntuni naso kafa company anan kafin na samu aiki yanzu kuma UK din ta ishe ni ina son dawowa nan." "Masha Allah hakan yayi ka fadawa Daddy? A'a ke kadai na faɗawa. toh shikenan zamu yi addu'a. "nagode Mami." har zai fita ta tsayar dashi tace me zai hana ayi enrolling din Adil a makarantar su Iman kafin ku dawo ba zai yi ta zama har 3months babu karatu ba. "yes nayi wannan tunanin." yayi wa Mami sallama ya fita Mami daɗi ya ishe ta. Allah ya kara haɗa kan su abubuwa da dama sun canja a rayuwar Fahad Allah ya cigaba da tsare su Alhamdulillah Sun shigo suna ta guje guje a falon chalet ɗin su hayaniyar su ce ta sa ya fito daga dakin Adil ne da Iman su ke hide and seek yace "Didi come here?" Fahad ya faɗa, "sit I want to talk to you." ya zauna ya nutsu Iman ma ta zauna kusa da shi "I need to discuss something with you Didi Maamah travelled she's not around and I'm thinking of enrolling you in Iman school before she returns I hope you understand me." ya fada yana kallonshi "yeeeee." sai ya ga be damu ba "I will be going to my sisters school yeeeee thankyou Papa." ya matso yayi hugging din shi suka fita suna murna yayi murmushi he is relieved. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 EPISODE 5️⃣7️⃣ Lebanon Beirut-Rafic Hariri International Airport Saukar dare suka yi Yasir ya kira direban shi yazo ya dauke su, sun sauka da gajiya kwarai tare dasu gidan Yaseer yana unguwar Gemmayxah suna shigowa suka tarar gidan cike da yan uwa ana jiran su duk da dare ne amma ko'ina kamar rana saboda fitilu fadar irin kyawun gidan bata baki ne. katon gida ne hawwa uku ma'aikata suna ta kai wa da kawowa motar tana tsayawa aka buɗe musu suka firfito Umaima ta sauko rike da hannun Ummi Hameeda da Khala suka tsaya suna kallon Umaimah na tsananin kama da Ummi da ta ke yi sai da Yaseer yayi musu magana sannnan Khala ta matso ta rungume Umaima "marhaban ya ukti." Yan uwa suka yanyame ta ana ta murna Umaima bakinta yaki rufuwa sai ta ji hawaye yanzu waɗannan duk yan uwanta ne? yau tayi bakin cikin rashin mayar da kai ta koyi larabci da Amminta ta sha bata littattafai na larabci ta jibge ashe saboda irin wannan ranar Amminta ke mata sha'awar ta iya da kyar suka Shigo gidan anyi decorating marhaba bik ya ibnati (welcome our daughter) an yi wa rubutun kwalliya da Gold anyi arrangement din palon yayi kyau sosai an jere Abinci kala kala falon makeken gaske ne Hameeda ta ja hannun Umaima suka yi sama tace "ibnati you are welcome." thank you Umaima ta mayar mata da murmushi dakin data kai ta mai kyau komai na morewar rayuwa akwai wasu yara suka Shigo kyawawa suna kallon Umaima. "jadda saghirah (small grandmother).". Suka faɗa suna murmushi. Hameeda tana korarsu Umaima tace ta kyale su daya ta zo ta zauna a cinyar Umaimah, Khala ta shigo da sallama Umaima ta kalle ta ta tuno sun haɗu a asibiti, ta matso kusa da Umaima da fara'a tace "you are welcome sister." ta ƙara kallonta tace Khala Yaseer. itama ta tuno da muryar tunda ranar da face mask a fuskar ta tace "you again Fatima?" sai suka rungume juna suna dariya, Khala ta juya harshe tana yi wa Ummi bayani masha Allah tace "hayyah sujood." ta kama hannun yaran sujood da Inaya kannen Khala ne tace "su shirya su fito ana jiran su a kasa. ........ta gaji sosai bayan an gama walimar, su kasashen larabawa da daddare suka fi yin hidimar su yawanci ma duk an tafi Umaimah ta ji dadi sosai ta ga yan uwanta da dama sosai maza da mata, Tahir ne ya shigo yace ibnati kin gaji ko? "wlh nagaji sosai Abbi." ya miƙa mata wayar shi ta karɓa ta saka a kunne. "Zahra ta ji muryar shi har cikin jikinta "you left me behind I'm lonely here." ta yi murmushi ta ce "do you miss me? "Sosai ma Zahra. ya kira sunan ta "hmm I miss everything about you. thank you ta faɗa tana kallon Tahir, yayi murmushi ya fita don ta zama comfortable. Tace "yaushe zaka koma? Ya ja numfashi "where is your phone pls ina ta kira a kashe. ta janyo jakarta ta dauko wayar ta kunna "gata nan. Please ki rinƙa barinta a kunne sai Abba na kira so how was your trip I hope you enjoyed it? Sosai kuwa ka ga yan uwa na mun kusa cika kano. "really? ya fada yana dariya, ba wasa nake ba fah, baka gan su ba kyawawa. "sun kai ki kyau? ta rufe ido "wacce ni? "no you are the most beautiful woman I have ever met?" kawai ta ji bakin ta yace har Aysha?sai da kwakwalwar shi ta yi tunanin sannan ya gane inda zancen ta ya nufa Aysha Maman Adil, ya nisa yace "Aysha is beautiful in her own way she has a very good heart and my parents choose her for me." ta yi shiru tana jin shi "and you are the most precious gift God has given me and I'm grateful for that." Har fah yanzu be taɓa ce mata I love you ba sai ta sha kunu kamar yana kallon ta. "Zarah." ya kira sunan ta "I'm planning a trip for the 2 of us ina kike so mu je? Ta yi shiru kamar bazata yi magana ba, yace are you there Zahra? ta nisa tace "kuma kuɗi za a kashe sosai ko? Yayi dariya yace "ba kya so na kashe kudi? bamu je honeymoon ba ki zaɓi inda zamu je mu huta for 3months." 3months sana'ar tawa fah? Ramla tana ta kira na. yayi dariya yace "nawa ne kudin sai a biya ki? Dan Allah da gaske? Sure. ya fada, shi tana burge shi "toh Adil fah tare zamu je ko? "kin taba gani an je honeymoon da yaro." Sai a fara akan mu. ta fada ita mamakin shi take yi dama yana magana haka "kin yi shiru ina zamu je ke nake saurara zan yi processing visa. tace China da Dubai. "China da Dubai." ya maimaita. "Zahra this is weird na dauka zaki ce Paris, ko maldives ko Taj ma hal a India." "ni ina ruwa na da wata India bana ma kallon su gara na kalli kwallo. Yace na gani ai yar gidan Uncle Ismah, give me reasons me yasa kike son China?" hirar kawai daɗi take mishi shi yasa yake jan magana. China da Dubai accessories din ɗinki na zan siyo biya fah nake Isiyaka yake zuwa kudin jirgi yayi tsada, tunda zaka kai ni ba sai na jefi tsuntsu biyu da dutse daya ba." yayi dariya yace "haka ne you' ve certainly got what you desired for your wish is my command Zahra." Thank you soo much ta faɗa tana murmushi Khala ta shigo ɗakin ta kalle ta tayi murmushi, tace "Ga cousin dina ku gaisa." ta mikawa Khala suka gaisa yace mata ta kula da Umaimah tayi dariya sun dan yi hira har yake tambayar ta me ta karanta ta faɗa mishi, tana ma aiki ta miƙawa Umaima yace "take care of yourself for me and my little one." ta shafa matarta ta yi murmushin jin dadi ta kashe wayar Khala ta miko nata fresh milk a cup tace jadda (Ummi) tace ta sha tunda aka ce tana da ciki tun a Kano ma sai ta saka ta sha fruit sosai ta ke kula da abinda Umaimah zata ci Khala tayi murmushi tace "you are lucky ukti your husband loves you." hmmm yaushe aka fara love ɗin, Umaima tace ita fah bata kira mata boyfriend dinta ba su gaisa nan da nan fuskar ta ta canja har Umaima ta lura ta tambaye ta menene? Tayi mata bayanin Ammar da halayenshi tace ita wlh bata son shi kawai don bata da wani ne amma da ba zata aure shi ba, Umaima ta kalle ta kamar wata uwarta tace "yanzu ma bazaki aure shi ba ana dole ne? "Ya zan yi ukti bani da wani sai shi." ni zan baki wani. ta buɗe wayarta tayi scrolling hoton Isma'il hoton shi ne daya turo mata lokacin da suka je Umara ya dauka a Harami tace "sai dai kice baki ne amma wlh kyakkyawa ne zaki aure shi? Khala tayi dariya ta kalli hoton masha Allah he is handsome nan Umaimah ta rinka fadin kyawawan halayen ismael Khala tana ta dariya. Fahad Tunda suka ajiye wayar yake ta tunanin Umaima tana burge shi shi is industrious tana son sana'a she needs support tunanin dawowar shi ma sai ya ji hankalin shi ya kara karkata ya dawo gida yayi mata setting business yayi dariya dramar su da ba a akan kuɗin kiwo yanzu tace China zasu zai kara, zabar kasashe biyu sai su kara da wanda ta zaba, ya mirgina daya barin yana murmushi kai ta dawo su tafi he will forever be grateful to iyayen shi I love her ya fada a hankali da gaske rayuwar shi tayi manufa yanzu. Ismael ya shigo daki yanzu ya dawo daga aiki ya watsa ruwa ya fito kenan wayar shi tayi ringing kafin ya dauka ta katse Umaimah ce tun ɗazu take ta kira yace yana wajen aiki zai kirata ta kasa haƙuri ta kara kiran shi be gama tunani ba wani kiran ya kara shigowa ya daga "haba Uncle Ismah kace zaka kira ni tun ɗazu na ji shiru? "kiyi hakuri aiki nake yi ɗazu Quality assurance ne suka zo mana supervision I'm busy ne ya aka yi? Tace "Duba WhatsApp dinka na turo maka sako sai mu yi magana." ya amsa da toh bari ya duba, yana dubawa yaga hotuna ne ta turo mishi harda vn hotonan wajen 12, wata kyakkyawar budurwa ce 6 aciki ita kadai ce yawanci Abayoyi ne a jikinta masu tsada sai wanda suka dauka tare da Umaimah sun yi kyau sosai ya bude Vnote din ya ji tace "yauwa Uncle Isma cousin ɗina ce nayi maka mata ka ganta kyakkyawa ce kar ta tsorata ka Allah zamu iya." 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 5️⃣8️⃣ Ya girgiza kai wannan yar tashi tana da rigima sai ya tuno da Fadee maganar da ta yi mishi ɗazu. Fadila Abdulwasiyu bayarbiya ce da suke aiki tare Allah ya haɗa jinin su, sosai su ke mutunta juna farko babu wata maganar soyayya a tsakanin su sai da ta yi wata tafiya gida Mamanta bata da lfy nan abun nasu ya canja salo don Isma'il a wannan lokacin sai ya damu kullum suna waya yana tambayar Mama dayake layin waya a tsakanin staff free ne ana basu staff line da kadan da kadan kamar wasa soyayya ta kullu. Fadila yar asalin kabilar Yarabawa ce Yarabawan kwara su ne fulanin yarbawa kuma suna da riko da Addini acikin Yarabawa sun fita daban da sauran Yarabawa al 'adun su suna kamanceceniya da Hausawa harda Kwara a daga tutar Usmanu danfodiyo suna cikin daular Usmaniyya har yarda Hausawa su ke tsarin tsangaya na karatun allo mutane ne masu son Addini sosai kuma kaso mafi rinjaye a Kwara duk Musulmai ne Fadee kamar yarda ake kiranta a gida ta fito daga gidan malamai mahaifinta babban malami ne mai bada ilimi yana da makarantar islamiyya Abdulwasiyu islamic School, malami ne kuma grand khadi ne a kotun jihar Kwara yana da yara maza da mata sun yi karatun boko mai zurfi sosai dana Addini dan yaran shi akwai hafizan Al qur'ani, Fadee tana cikin yara mafi soyuwa a wajen mahaifin ta dan sosai da zata taho Kano aikin MTN ya so ya hana ta sai da Mamanta ta saka baki akan zata zauna a wajen kanwarta da take aure a Kano Aunty Mansura kanwar Mamanta ce uwa ɗaya uba ɗaya tana zaune a kabuga don Isma'il ya sha zuwa hira wajenta a kabuga. Baban su Fadee yana basu damar su yi degree matan kafin su yi aure ita kadai ce har ta fara aiki bata yi aure ba Fadee kyakkyawar gaske ce chocolate colour tana da kira mai kyau pull package ce ga ilimin Addini wannnan zuwan data je gida Alfa kamar yarda suke kiran Baban su yayi mata maganar aure yace ya bata nan da karshen shekara idan bata fito da miji ba zai hada ta da dan uwan ta Zikirullah. Zikirullah dan dan uwan shi ne daya rike shi tun yana yaro ya hada shi da yayan Fadee Abdulkarim tare suka tashi idan kuma tana da wanda take so ta fada mishi ya turo ranar da Fadee ta faɗa mishi ko baccin kirki kasawa yayi yana ta so ya kira Umaima ya fada mata kuma ta turo mishi da wannan. ........Hayatee Tahir ya kira ta da tattausar murya "wai har yanzu ba ki warware ba ne muryar ki can kasa nake jinta ki kwantar da hankalin ki nima ba wani abu zan fada ba, ya saukin jiki?" Alhamdulillah ta fada "Hayateey haka Mamana take neman kuɗi? I'm impressed ta yi min bayanin business dinta Alhamdulillah na kusa hutawa kenan." "shirmenta dai." Khadija ta faɗa yace "Nooo wannan ya wuce shirme she amaze me she is doing great things." khadija tace "asalin shagon nawa ne Daddy ya bani tayi hijacking daga machines har tailors ɗin duka, duk da dai ta kara wasu daga baya har ma'aikatan ma ta kara, ka yi mata fada babu kyau mutum yayi wa kudi mugun so haka." "No hakan yana da kyau she should be independent ta tsaya da kafarta sosai I like that." dama tasan neman kuɗin su iri ɗaya ne da mahaifinta barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba ta faɗa a ranta, tace "Nagode Allah ya saka da alkhairi. Yace "da aka yi me? Raguna da ka siya haka da yawa har Bichi ka aika fah mungode. "no don't mention abunda ya kamata kenan tsakanin mu babu godiya kin tuna min ma bari na tura mata kuɗin ta, yau saura 3months ki gama iddah. bata ce komai ba ya san ba zata yi maganar ba suka yi sallama ya ajiye wayar. 3days later Yana zaune a seat din shi ya rinƙa ganin kiranta yana shigowa ya kyale ta yana attending customer yana mishi sim swap ya daɗe yana attending mutane wasu complain ne na kwashe kudi ko an saka su a tsarin da basa so sai wajen Azahar ya samu kan shi ya fito zai je masallaci "babe where are you going? Fadila ta faɗa, yace mata sallah ta duba agogo tayi murmushi ya daga mata gira ya fita, bayan yayi sallah ya kira Umaima ta daga "haba Uncle Ismah yau kwana nawa na jika shiru? Gata ku gaisa yana ta tsaya ko sauraren shi bata yi ba yama rasa me zai ce mata sai hello yake yi tana salam alaykum, yayi ta hello kamar matsalar network kawai ya kashe wayar shi, ya zai yi da Umaima? wayar tana ta ringing yayi mata text babu network ne. Dama fita zasu yi da Khala Umaima ta takura sai sun yi waya da Uncle Ismah ita dai khala kawai jin Umaima take yi tana ganin ba shi yace yana sonta ba kamar abun yayi wani iri amma bata son nunawa Umaima bata so kawai tana bin ta a haka text ɗin Ismael ya shigo na rashin network Umaima tayi tsaki tace babu komai ma gwada gobe sun shirya sun yi kyau sosai suka sauka kasa Ummi ta buɗe musu hannu ta rungume su tayi musu kiss a goshi "Tubarakallah masha Allah kun fito? Khala zata dan yawata da Umaimah wurare a Lebanon driver ya dauke su suka fita. Sun sha yawo sosai sun je Qadisha valley, Raouche Rock, Mount lebanon, Beirut national museum sun yi dauke dauken hoto a museum daga karshe suka wuce Beirut souk sun shiga shops sun yi siyayyah sosai Tahir ya basu kudi sun shiga restaurant suka ci abinci sai yamma suka dawo gida, sun dawo suka tarar da Ammar da Tahir da Ummi suna hira suna shigowa Khala tana ganin Ammar ta sha kunu "ibnati." Tahir ya kira Umaima "ki duba wayarki na tura miki sako." da sauri ta bude Ummi na mata magana ma bata ji ba alert ne mai nauyi tace "nagode Abbi." ta rungume shi tana dariya Ummi ce take yiwa Ammar bayanin Umaima bata jime Ummi take fada ba amma ta gane ya kalle ta yana wani jijjiga kai Tahir yayi musu sallama ya fita Khala har zata hau sama yace "hey come here." Tab lallai wannan mutumin, Khala ta dawo Umaima sai hararta take yi me yasa zata dawo "find me something to eat" Ummi da hankalin ta yana kan waya da Dr Huzaifa yayi mata bayanin wani magani da zata fara sha wayar Umaimah ta yi ringing ta tashi ta hau sama har Khala ta shiga kitchen Umaimah ta kira ta a waya ta hau saman ta sameta tana shiga ta saka key a kofar dakin tace "you are not going any where sai dai ya mutu da yunwa haka Ammar din yake Allah ba zaki aure shi ba." ........Yaso sun kara magana da Umaima tun jiya yake kiranta baya samunta bari kawai yayi mata Vnote idan ta gani yasan zata neme shi shi ya zai yi? Umaima ce suke shawarar komai na rayuwar su hatta aiki ma ya samu offer a Nepa at the same time aka kira shi interview MTN tace Allah ya sauwake me zai yi da nepa daukan tsani zai yi ita ta ce ya karbi MTN, Fadee yau ma sai da ta kara yi mishi magana gaskiya yana son ta har ga Allah yanzu yana tsaka mai wuya amma dai yau zai yiwa Daddy maganar yasan Umaima sai tayi fushi har ga Allah ya fara son Fadee kafin ma tayi mishi zancen cousin din ta yana zaune yana kallon kwallo a palo Baba ya shigo ya gaishe shi ya hau sama ya mike bari ya je ya samu Daddy yasan yanzu shi kaɗai ne ......Daddy ya gama sauraren shi yayi shiru jikin shi yayi sanyi Daddy yace "toh masha Allah ina kace iyayen ta su ke? A kwara ya fada, "a hannun wa take anan?" ya fada mishi kanwar mamanta "toh ai babu wani abu hasali ma abu ne mai kyau tunda dai musulmai ne Addini shi ne abu na farko da zamu duba kuma kace malamin addini ne. ya sunkuyar da kai tashi ka je zan nemi yan uwa na mu yi magana ismael ya fito yana murna. ......Kwarai Ibrahima da kyau wato kai ne zakakori duk wani kulla auren wahala da masifa ka kware yaushe muka fito daga bala'in auren Hadiza da Ɗahiru? yanzu ka kinkimo Yarabawa babu mata a Kanon ne? Idan babu mu nan akwai yammata ga Rumasa'u nan har kwaleji ta yi da iliminta. "Dada ba haka ba ne abu ne mai kyau babu haramci kuma Addini be hana ba Almuhim musulmai ne mun tattauna da Babancikin gida da sauran yan uwa na kowa yayi Na'am da zancen Dada ayi hakuri amincewar ki kawai ake jira." "Ibrahima bude kunnenka da kyau ka ji babu zuri'a ta babu Yarabawa ba musulmai ba ko yar limami ce kar fa a kaini bango, yan uwan shi ma suna zaune ba su yi ba sai shi isasshe." Daddy yayi shiru har ta gama ya fara bata hakuri tace "ka turo min Magaji." ta fada ta kashe wayarta duk maganar da suka yi Baba yana ji don wayar a speaker ta ke. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 5️⃣9️⃣ Ismael yana ta murna ya shiga daki ya kira Umaima dole yayi mata bayani yasan yar gidan shi zata iya kullatar shi tana daga wa tace "ubana na kaina." ta fada daga daya bangaren. kwana biyu network ya hana mu magana. duk sai ya daburce ya rasa abunda zai faɗa mata, "ya naji kayi shiru? "hmm kina jina? "ina jin ka." "yauwa kin ga ne dama - dama wlh. sai kame kame yake yi, dama me wai? "Wlh kin sani ko....da ƙyar yayi mata bayani yana ta inda inda. Tace "Au Uncle Ismah watsa min kasa a ido zaka yi? me yasa tuntuni baka faɗa min ba fisabillahi, ka yi breaking ɗin heart ɗin yar uwa ta." shi mamaki ma ta ba shi wanne irin breaking heart shi da ko sau daya basu yi magana ba. "haka ma kace toh yanzu tsakani da Allah ka kyauta min? Ki fahimce ni kar mu yi haka da ke. "na nawa kuma yanzu cewa zata yi yaudarar ta nayi ka mayar dani mutuniyar banza nagode bayarbiya ta fi ni." kawai ta kashe waya hankalin Ismael yayi mugun tashi yayi kiran duniya taki daukan wayar ta tura mishi text. "babu komai nagode." kawai abunda ta rubuta kenan shi dama ya san za a yi haka tama kasa tsaya wa ta saurare shi ya bude WhatsApp ya tura mata sako yayi mata bayani wlh ya ri ga yayi committing kan shi ta yi hakuri ya gani ta karanta amma bata yi magana ba. 2 weeks latter Safiyar Asabar ce bayan sallar Asuba ta koma bacci kenan bata dade da komawa ba Khala ta shigo dakin ta tashe ta ta bude ido "lfy? Ta tambaye ta, Tace ta shirya ta fito ana jiran ta a kasa "kai dan Allah Khala ke ma kin iya mugunta irin ta Amira mutum yana bacci a tashe shi babu kyau tashin mai ciki ko dan ba lafiya kika karanta ba." "yi hak'uri Khala ta fada tana dariya (da turanci suke magana ) "jiran ki nake yau kwalliya zan miki. Kwalliyar me? Kedai shiga ki fito. Ta yunƙura ta shiga toilet ta ɗan dade ta fito Khala ta dauko makeup kit tana jiran fiowarta, ta fito ta gama shafe shafen mayuka Khala ta zaunar da ita tana mita tana komai "wai ina zamu ne? A'a ina zaki dai. bangane ba? "Pls ki yi shiru mu gama." ta tsantsara mata kwalliya ta dauko wata Abaya da suka siyo mai stones coffee brown tayi mata rolling ta yi kyau kamar ka sace ta ka gudu ta riko hannun ta suka sauko kasa babu kowa tace "ina bakin? "Kar ki damu." Suka fito suka shiga wani part a kusa da wannan ta taɓa tambayar Khala na waye tace part din Uncle ne (Tahir) idan ya zo daga SAUDIA yake sauka anan yayi kwana biyu kafin ya koma main House din su na unguwar Hamra acan yake zama. Suka bude kofa suka shiga kamshin turaren shi ne ya

Chapter 24 of 27