matuƙar daurewa ji yake kamar ya goya Umaimah don daɗi "yauwa ku shaida wlh idan suka haihu sunana za a saka."
"In sha Allahu kuwa." Baba ya faɗa, "na yi miki wannan Alkawarin." Isma'il ya ji kunya ya tashi, Umaima ta rufa mishi baya Umma da daɗi ya ishe ta tace "mai rawar kai da me karambani Allah dai ya dauwamar da soyayyar nan uba da ya har Aljanna." aka amsa Amin.
......Duban mutane ne suka shaida daurin auren Tahir Fadoul Al-arabey da Khadija Muhammad Bichi akan sadaki 500,000 Lakadan an daura a fadar Hakimi bayan sallar juma'a hawayen murna kawai Tahir yake yi yan uwa aka rinka mishi murna suna musabaha. Dr Huzaifa yace hawaye ya kare, ya rungume shi yace congratulations bro. shi da Yaseer suna ta yi mishi murna sosai yake hawaye yana yiwa Allah godiya. Kafin su baro Bichi sai da yayi nafila raka'a biyu ya kara godewa Allah, sun shiga cikin gida sun gaisa da jama'a an daddauki hotona suka kama hanyar zuwa wajen khadija.
Khadija tunda aka daura take faduwar gaba ta kwanta a daki Munnirah tana ta yi mata mita an yi mata make up farin lace ta saka da adon gold ta sha kun shi ja da baki ta fito a Amarya sak, fuskar nan sai sheki take yi wayar Munnirah Tahir ya kira yace suna falon Baba ta saka Khadija a gaba ta kara fesa mata turare dama kayan an tsuma su a kabbasa da turaruka masu sanyin kamshi.
Suka Shigo da sallama da sauri ya taho ya rungume Khadija ya ji wani abu ya fada mishi daya tokare mishi a makogwaro "Awwwwww." su ka ji Umaima ta faɗa "wlh an burge ni." Munnirah ta yi mata dakuwa suka Shigo aka ɗauki hotuna suka wuce bristol za su yi reception maza kawai.
Mai jego ta yi kyau sosai ita da babyn ta da taci sunan yayar Mami da ta rasu Amina za a kira ta da Amani.
Umaima akwati guda tayi na kayan baby Fahad kuwa shi ya dauki nauyin komai na hidimar da aka yi, kuma ya basu gudunmowar kudi mai nauyi Amira da Khadija.
After two weeks
Tahir ne ya labe a jikin kofa yana jiran ta fito daga toilet, ta fito da towel a jikin ta tana kara daure gashinta da ribbon yayi sama da ita "haba Hayateey baki da tausayi ne ayi ta ja min rai baki san ina kula da ke ba tun jiya kika fara sallah." tayi narai narai da ido "Baban Umaima.....bakin su ya hade data fara magana zata kare kanta ya kashe fitila dakin yanayin mai daɗi ne don ruwa ake yi garin yayi dadi ga kamshin kasa Tahir be saurarawa Khadija ba duk wata kewa da tsohuwar soyayya ta shekara 20 har da doriya ya saukewa Khadija, ta karɓe shi itama acikin sauki ta amshi uban yarta suka farantawa juna rai ya gigita ta da soyayyar shi mai tsayawa a rai "barak Allah feek (God bless you) I can't do without you hayatee, your love means everything to me you are the reason I keep going my Rock, my world." ya fada cikin shauki rungume da ita.
Leeds UK
Zauna yake yana aiki a System Adil yace "Papa when are we going back to Nigeria? I'm bored here I miss my sister." ya kalle shi yace soon Didi.
Company aikin shi ya kammala yanzu sai daukan ma'aikata komai ya tsara abunda ya rage mishi be karasa ginin gidan da zasu zauna ba, amma shi ma ba zai dauke shi nan da wata biyu ba in sha Allah, account din shi yayi girgiza ba kadan ba don wannan babban project ne ya dauko.
Umaima ce take ta ɗinki kai ta gaji ta zo ta tarar da order masu yawa ga yanayin jikinta ba kamar da ba don ma mai ƙoƙari ce ta sauko daga kan keken ta fito ta tarar dashi yana aiki ta nufi kitchen ya bita da kallo ta haɗa musu coffee da samosa ta ajiye musu ta zauna tana sha yana aiki suna hira yana faɗa mata progress din aikin tace "wlh nima na matsu Allah yasa time din an kusa bikin Uncle Ismah kaga shikenan."
"in sha Allah before then ya faɗa. ta tashi ta koma kasa ta mike kafa Adil yazo yana mammatsa mata kafa ya ma sani idan ya ga ta mike kafa abunda take so kenan, mrs Lawrence ta leko ta yi musu sallama ta tafi.
Bayan sallar isha suna kallon documentary channel, Umaima tace "Dattijo."
ya kalle ta wanne "Dattijo kuma? Ba sunan ka ba ne?
"huh I was expecting something a bit romantic name like Darling, sweetheart, honey." Ai mu we are different and unique on our own way mun fita daban da sauran ni kadai ce iri na a duniya I'm unique honey, sugar are outdated i prefer Dattijo.' ta daga mishi gira yayi murmushi "ni fah ko kudin zance irin na masoya baka ba ni ba irin na saurayi da budurwa komai baka sani ba."
"to yanzu ya kike so? Yauwa ka tanadi kudin zuwa zance zan shiga daki na shirya nan da 30mins sai ka aiko ayi kira na.
"wa zan aiko? Come on Dattijo can't you come up with something on your own." yayi murmushi ta mike ta shige daki tana shiga shi ma ya je yayi wanka ya shirya cikin kayan da Sa'ad ya dinka musu lokacin daurin aure ya saka wata Brown shadda yayi kyau harda hula be cika saka manyan kaya ba hasali ma baya dinka su.
"Papa you look great." Adil ya fada, ya zauna ya kalli agogo is almost time ya kira Adil ya zo gaban shi yace "call Maamah for me." har zai tafi ya fada mishi da hausa yace, ya ce ana sallama da Maamah repeat it let me hear you Adil ya maimaita sannnan yace yaje.
Tana zaune a bakin gado ta saka wata atampa straight gown dark green ce da light purple dinkin ya mata kyau cikin ta kamar an dasa shi ya fito sosai ta yafa mayafi light purple ta fesa turarukan daya siyo mata data ke son kamshin su Adil ya shigo da sallama yace ana sallama da Maamah tayi murmushi ta mike ta fito idon shi a kanta ta wuce kitchen Adil har zai koma ya zauna Fahad yace is time for bed. ya ajiye ipad din yace "goodnight Papa, good night Maamah." Umaimah data dauko tray ta amsa shi da goodnight Didi.
Ta ajiye a gaban shi tana gyara lullubin ta "ina yini." ta fada, ya na murmushi yace "lfy ƙalau ya mutanen gidan? suna lfy ga ruwa bismillah.
"toh gimbiyar."
ta zuba ta taso ta miƙa mishi kamar ya rungumeta ta dawo ta zauna "nagode, da farko sunana Ismael Ibrahim Bichi ni ne na uku a gidan mu na karanta architecture a US ina aiki a nan." yayi shiru ya rasa me zai ce "tunda na ganki na fara son ki." sai ta yaye mayafin tace "ka dai fadi gaskiya nida na kusan shan mari."
Yace "ai kin ɓata ni da baki sanni ba. Au haka ne sai. ta gyara lullubin, yace mata "bismillah." Tace "ni sunana Fatima Tahir Al-arabey gidan kakanina na tashi na karanta computer science."
Malama Fatima ki bani dama mu fuskanci juna Fahad ya faɗa "Amma kamar ciki ne a jikin ki? Waya yi miki ciki? Tace "kai ne." sai suka kwashe da dariya ya dauko pounds yana mata spray tana dafewa tana murmushi.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 6️⃣2️⃣
3months later
Abubuwa da yawa sun faru an saka bikin Uncle Ismah nan da wata 2, Ibrahim yana US ƙaro karatu an yi nadin sarauta an nada hakiman Bichi, Rano, Gaya da Karaye zuwa sarakuna ciki har da Babancikin gida, Su Umaimah sun dawo Nigeria an yi bikin buɗe company a Abuja IIB construction company (Isma'il Ibrahim Bichi ) gidan su ya kammala amma basu tare ba shi kaɗai yake Abuja yana interview ɗin daukar ma'aikata cikin Umaima ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe Umma tace a bari ta haihu sai ta tare.
.......Expert Alliance hospital
"Siyama bayana kamar zai balle." to ya kike so nayi? bakin ki baya shiru ki yi addu'a. tun magrib suka taho Asibiti ana ta jiran haihuwa nurse tace da saura tana 4cm "wayyo Allah." Ta kurma ihu, "ki yi salati." tana farawa sai ta kurma ihu Umma ta rufe mata baki "ni zaki tunawa Asiri? Idan mace ta fara haihuwa da iface iface haka zata cigaba da haihuwa daurewa ake yi."
ta yarfa hannu tace "Siyama don baki san yarda nake ji ba ne."
"ina zan sani kin san Khadija ina bacci aka miko min ita." can ta ƙara wani nishi tana cije baki Umma ta fita da sauri kiran nurse, nurse tana zuwa ta karɓi haihuwar.
Umaima ta haifi yaranta twins mata Masha Allah kukan babies ne ya saka Umma shiga da sauri har an goge musu jiki lafiyayyun yara masu kama da mahaifinsu kalarsu kuwa har sun fi Umaima hasken fata ko dan kakan su Balarabe ne sai farin su yayi na Larabawa.
"sannu sannu Umaima." Umma ta faɗa, ta hada su tana kallon su, sun bude ido tar daya har ta fara tsotsar hannu .
......Gidan cike yake da yan uwa ana ta murna Fahad tuni ya zo ya tarar da babbar kyautar da Allah yayi mishi babu kunya tunda ya zo ya kasa ya tsare yana tare da Umaimah Baba da Daddy suka Shigo ganin idon su ya fita.
"A'a nayi sabuwar Amarya Muhammadu na zaɓi wannan." Baba yayi dariya yace "ni Amina ta ishe ni." yar gidan Sa'ad (Amani) gara yar baka bakar waɗannan sai su firgita ni. Hakimi ya shigo yana murmushi, Daddy yace "congratulations kun yi jika." Baba yana tunani a rai ya ce "ta wajen Umaima ƴaƴansu ne ta bangaren Fahad kuma jikoki ne sun ci tudu biyu."
Dada Takanas ta zo ganin babies daga Bichi.
~~~~Haushi ne ya kama Umma makota sun shigo barka Umaimah ta hana a dauki babies, ɗaya ce tayi zazzaɓi don sun je asibiti, kememe ta ce likita ya hana daukan su, Umma kunya ta kama ta Uwargidan Khadi ce neigbour din su tace babu komai ta leka fuskar su tace a haka ma na gan su Allah ya raya.
Umma tayi mata rakiya ta dawo ta balbale ta da fada "wlh sai dai ki koma wajen Mami na gaji da rashin arziki Mijin ki yayi ta min zarya ku koma can ku karata." kullum sai sun yi fada sai ta saka yara a gaba tana kare musu kallo "toh Siyama sai na koma ko na koma ɗakin Uncle Ismah ya taya ni reno meye a ciki." Umma tayi mata banza "Siyama idan na koma Abuja sai na shekara biyu baki sani a ido ba." Umma ta tashi ta bar mata dakin .
.....Khadija ce suka yi sallama tare da Tahir suka Shigo sai buya ta ke yi a bayan shi kamar mara gaskiya, "sannunku da zuwa." Umma da mamaki ya gama kashe ta ta faɗa tana dauke ido akan yar ta, a ranta take jinjina wa ikon Allah Khadija da ciki Allahu qadiran.
Aka rude da murnar zuwan su Baba Rabi ta zo ta rungume ta aka kawo musu Abinci da lemo Munnirah sai dariya ta ke yi, kullum anan take yini tunda aka yi haihuwar ita kaɗai ta san Khadija nada ciki sai yau Umma ta gani, Khadija duk ta daburce su Yaya Hindu duk suna nan gobe za a yi suna yan Bichi ma sun sun sauka a bangaren Mami.
"mun same ku lfy?" Tahir ya durƙusa yana gaishe da Umma, ta amsa da jin nauyi sai ihu suka ji akan su ta rungume Tahir ta dawo wajen Khadija ta rungume ta "Ammina kin yi kyau kin yi kiba." abun dariya Khadija sai ta rufe fuska da mayafi, anata murnar zuwan Khadija sai ga Sallamar su ne Ummi da khala da Hameeda daga Lebanon sun zo suna aka kara hargitsewa da gaishe gaishe.
Ranar suna babies suka ci sunan Maryam (Umma) da Khadija, da farko sunan Mami za a saka tace A'a a saka Khadija, Amal da Surayya sun saka sunanta kuma Amani ma yar Sa'ad zabinta ne. Umma anyi takwara haka ma Khadija.
Nonon Umaima ya karbe su sun yi jajir sun yi kiba ana kiran su Nihaad da Nihaal, shanu aka yanka ranar suna Uncle Sa'ad ma yayi bajinta ya dauki nauyin shagalin suna Daddy kyautar wani fili ya bawa Umaima a farm centre, Baba mota ya siya mata su Baban ABU da Baba Dr sai ruwan alert ta rinƙa gani ta samu kyaututtuka Umma ma set din gold na yara ta siya musu. Tahir wani mall daya bude branch a LEBANON ya bawa yan biyu, Fadila ma tazo da laces masu tsada da kayan babies sai ranar sunan aka ganta masha Allah Umma ta yaba da nutsuwar ta, Babangida 500,000 ya bata Uncle Ismah ma 300k ya bata taki karba tace shi da zai yi hidimar biki.
........Kai Khala heater nan babu ruwan zafi sai kin sauka kasa kin dora mana. Umaima ta fada Khala ta mike tace "bari na sauka."
Tuntuni su Ummi sun koma su Khadija ma sun koma Khala musamman ta dauki hutu dan ta kwana biyu wajen Umaimah tare suke rainon tana fita Adil ya shigo yace "Maamah are they sleeping?" ya leka fuskar su "eh bacci su ke yi ina Iman?"
"she's down stairs." suna ta hira da Adil shiru shiru Khala bata dawo ba tace ya je ya kira Aunty Khala ya fita da gudu
Tana shiga kitchen ta dora ruwan zafi a gas Aliyu ya shigo yana neman tea flask zai sha tea ta gaishe shi ya tsaya yana kallonta, kwana biyu dai yana ganinta a gidan amma waɗanda suka zo tare sun tafi.
"Do you need something?' ta dawo dashi daga tunanin daya tafi, "yeah." ya faɗa ya nufi flask din ya daga babu komai tace "let me help you?" ta dauko tukunya ta wanke ta dora mishi ya ja kujera ya zauna.
"what is your name?" ta ji muryar shi a bazata "Khala Yaseer Al-arabey." ta faɗa ya maimaita sunan "nice name, can you tell me more about yourself please?
Tace "I'm Khala Yaseer Al-arabey the eldest daughter of my parents I serve as an asistant lecturer at American university of Beirut I'm 23yrs." muryarta gwanin daɗi ya fada a ran shi, "are you in a relationship?" kawai bakin shi ya fada, har ta hada mishi tea yana sha yana murmushi tace "I'm in a relationship and I'm single." ya zama confused yace "how?" nan ta fada mishi bata son boyfriend din har Adil ya zo ya fita hankalin su baya kan shi.
"I would be honored if you would give me a chance." ya faɗa, "it would have being my pleasure." ta fada tana blushing ta sunkuyar da kai kasa.
Nihaal ce take ta motsu motsu a cire mata pampers Adil yazo yace "Maamah she is not answering me." ta sauka kasa ta shiga kitchen ta tarar dasu Khala sai murmushi take "ke kuma ya haka? Ta faɗa, ta tafi ta kashe gas din don ruwan ya kone.
"abunda aka aiko ki kenan ta fada?" ta sha kunu "oh I'm sorry." duk ta daburce kunya ya saka ta bar kitchen din ya bita da kallo yana murmushi suka hada ido da Umaima data saki baki tana kallon shi ya dauke kai.
Soyayya ce ta kullu tsakanin Khala da Aliyu tun Umaima na zuga Khala har ta gaji Khala ta kwashe duk abunda Umaimah ta fada mata ta faɗa wa Aliyu, da kan shi ya samu Umaima yayi mata magana, no hard feelings yace infact she is his favourite lokacin yarinta ne dole a saka mata ido shi ba tsanar ta yayi ba da kyar ta sauko ya faɗawa Daddy aka nemi Tahir cikin ikon Allah tun zuwan Yaseer jinin su ya hadu da Aliyu ba a dauki lokaci ba aka saka date za a fara daura auren Aliyu a Lebanon suna dawowa ranar Sunday zasu wuce kwara a dauro auren ismael.
.......Fahad ne su ke waya yake tambayar yaran shi "kin san kin kara weeks gobe ana gama biki zamu wuce gaskiya nayi kokari."
"oh yanzu hankalin ka ya dawo jikinka." Hmmm! kinsan na aikatu ina can ina nema muku kudi.
After 2 weeks
Yau su Daddy suka dawo an daura auren Khala a Lebanon tare suka taho da ita sun dawo ranar Saturday ta sauka a part din Mami sun huta yau Sunday suka tafi kwara daurin auren Hakimi su Daddy da suka nema mishi aure zuwan su na farko basu gamu da mahaifin Fadila ba Uncle dinta suka gani a wajen daurin auren Daddy ya kalli fuskar mahaifin Fadila yace "A'a Abdulwasiyu."
Shima yace "Mai yaji." ya kira Daddy aka kara gaisawa "kar dai Fadila yar kace?
Nan aka tuno da tsohuwar abota Baban Fadila ajin su ɗaya da Daddy a Barewa college, shi Baba Ajin su daban, sunan Mai yaji da ya kira Daddy dashi awaken shi ake samun yaji mai daɗi lokacin suna makaranta Dada take daka musu yaji mai daɗi.
An daura aure suka taho Amaryatun Alhamis suke hidimar bikin su a haka ma mahaifin Fadee ya hana wasi bidioin.
Dinner
An yi dinner a green desert Fadila da Khala white gown suka saka mai mayafi Aliyu da Ismael suit suka saka dinner ta kayatar kowa mamakin yarda Aliyu ya ware yana rawarshi yake, yan banki sun yi mishi kara, suma collugue din Uncle Ismah sun yi bajinta, Umaima uwarbiki ta kasa zama daɗi ya ishe ta Uncle Ismah yana aure an zo yanka cake Aliyu ya bata a baki har da yi wa Khala kiss kafin ma mc ya bashi dama aka rude da ihu an ci an sha Umaimah ta yi rawa sai da Fahad ya janye ta, sun ɗauki pictures da Amare da Angwaye an tashi lafiya sun dawo ana mayar da yarda aka yi Umaimah tana ta bawa su Baba labarin Aliyu ana ta dariya ta kalli Umma tace "Siyama ya muka ji da murmushi su Uncle Babangida yau kamar an mishi gorin murmushi." ana ta dariya ya shigo da sallama rike da hannun Khala.
Uncle Ismah Lagos aka tura shi daga wajen aiki. Fadee ta yi resigning ta bishi ta fara business ɗin laces, Aliyu ya tare a gidan shi na sardauna crescent Umaimah ma ta koma Abuja babu dadewa Fahad ya buɗe mata Umaima fashion House.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 6️⃣3️⃣
After 7years
Rayuwa tana tafiya cikin kwanciyar hankali da godiyar ubangiji abubuwa da dama sun faru a wannan zuri'a mai albarka masu daɗi da akasin haka ciki kuwa har da mutuwar Babancikin gida mutuwar data gigita ahalin shi an kadu da wannan babban Rashi, Baban sama aka naɗa a sarkin Bichi bayan yayi retire lokacin yana matsayin Cp (Commisioner of Police) ya dawo cikin masarauta da iyalan shi wannan ya saka Dada samun nutsuwa, Hajiya Dada tsufa ya cimma ta kullum tana cikin ciwon kafa duk sati sai an kai ta Dala othpedic ƙarshe madai a wheelchair ake dora ta (Allah ya sa mu cika da imani idan babu mutuwa akwai tsufa ). Zuri'a sun kara samun haife haife don Amira ta kara yara biyu Nihlah da Aseem sunan Daddy da Umma Ibrahim da Maryam. Hidaya haihuwar kwanika take yi ta kara haihuwa uku bayan Amani ta haifi Amna, Ayman da Abid. Ibrahim ya auri wata abokiyar karatun shi a US yar Malaysia ce sun samu aiki acan yaran su 2 Isma'il dai dai lokacin rasuwar babancikingida aka haife shi suke kiran shi da Amir. Aliyu da Khala sun haifi yara biyu duka Maza Tahir aka yiwa Takwara sai mai sunan Daddy Tahir ana kiran junior sai mai sunan Daddy ana kiran shi da Daddy.
Uncle Ismah da Fadila yaran su 2 mata Fatima Umaima da Fatima (little) yace ko yara nawa zai haifa mata sunan su Fatima sai dai a canja nick name. Khadijah ce mai guda ɗaya sa'an su Nihaad sun bashi wata 6 sunan Baban su Tahir yaci ake kiran shi da Khalifa.
.....Tahir ke yiwa Khalifa faɗa yana ta iface iface kar ya tashi Khadija da ke bacci yace yayi karatun shi dan akwai shi da wasa ya je ya dauko qur'ani Tahir yace haddda zai karɓa ya buɗe yayi bismillah ya fara daga sama suka fara yayi aya 50 suratul bakara yace ya tsaya.
ya ce barakallah feek ya shafa kan shi Khalifa akwai kiriniya kokarin shi ne yasa yake daga mishi kafa. Khadijah ke ganin an shagwaba shi, ta fito ta tarar dasu ta zauna kusa da Tahir ya cewa Khalifa ya je yayi kallon cartoon zai neme shi anjima.
"Hayatee." ya kira ta kin tashi? Kai da daga "kun tashe ni tun ɗazu." oh ayi mana hak'uri. ya jawo ta jikin shi yayi mata kiss a goshi "wannan baccin da kike anya? Ta bude ido ban "gane ba? yayi dariya yace "Allah yasa ciki ne ."
tayi shiru Allah yasa ba ciki ba ne haba ta barwa Umaima. zo ki ji yayi mata rada a kunne.
~~~~~Umayma ta tarar da Nihaal kwance a falo ta fito daga Dakin Fahad ana kiran Asssalatu ta tashe ta "meyasa kike kwance a falo?" ta murza ido tace "Maamah Nihaad ta cika dakin da warin tusa tun dare take tusa I need seperate room Pla Maamah." kai waɗannan yara Allah ya shirya "me yasa baki je ɗakin Arif ba? "Maamah I don't want disturbance Arif snores."
Nihaal ke nan sarkin iyayi komai na Fahad ta kwashe babu abunda ta rage, "say something Maamah." Umaima tace "tashi ki je ki yi sallah and wake your sister." ta shiga dakin Arif ya bude ido tace koma baccin ka uba na. ya rufe ido ta shiga ɗakin ta tayi wanka ta yi sallah tana zaune tana Azkar ta fara jin hayaniyar su dayake an yi hutun 3rd term suna gida ta leƙa dakin lafiyar ku? Wanne rashin hankali ne da sassafe zaku fara?
"Maamah kayana ta saka. Nihaad sai muzurai ta ke yi, Maamah nawa ne. Nihaal har ta fara hawaye ta dauko na Nihad duk ta yaga su tace "Maamah ga nata." Umaima ta kalli kayan ta girgiza Kai bata gama Azkar ba zasu hadu anjima
Suna Dinning zasu yi breakfast Adil ya fito daga ɗakin shi ya gaishe da iyayen shi.
"Ina kwana Yaya." suka gaishe shi ya amsa Fahad ya kalli Nihaad data yi wata shiga kamar yar bori yace Mamana wacce irin shiga ce wannan? wandon jeans rigar atampa hular sanyi ga wata jaka a rataye a wuyanta kafin tayi magana Umaimah da fushi tace "kyale ta nayi amma jikinta zai faɗa mata, ga wata shegiyar jaka kamar yar wanzan ko bacci da ita take yi a rataye a wuya ko uban me ye aciki, wlh da ina da iko dake boarding zan kai ki." Fahad ya kalli Umaima ya kunshe dariya don yasan halin Umaimah ne haka kullum Umma take fada, hand me over that bag Fahad ya miƙa hannu Adil yayi dariya yace "she's too rough." ta turo baki ta mika da kyar yana budewa yan 50 Naira,100, 20 har da 10 Naira. Umaima tayi salati "kuɗina kike dauka?" don basa basu kudi tace "wlh Maamah ba kudin ki ba ne."
Ina kika samu? ki bude baki ki yi min magana Umaima ta faɗa kamar zata dake ta Nihaal har zata yi magana Nihaad tace "ina ruwanki amebo." Fahad ya tsura mata ido, Umaima na harararta ta sunkuyar da kai tace
"abincin break nake siyarwa." abincin da ake bata na lunch bag dinta, Fahad yace ba kya cin abincin ne?
Wai rabi take siyarwa taci rabi.
"wlh sai kin tafi boarding. Umaima ta faɗa, Fahad yace su tashi su tafi tunda sun gama cin abinci.
"Yaya let's
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 27