Share this page
yake yi, Umaimah tayi kamar bata gan shi ba direct dakin ta ya wuce ta tafi raka Aunty Ramla amma hankalin ta yana ɗakin kar dai kekenta zai dauke ta dawo daga rakiyar ta shiga ɗakin bata ga ya dauki komai ba, to tsoron me ma zata ji? Ta dawo falo ta kunna TV bata daɗe da zama ba Adil yazo wajenta yace "Maamah I'm Hungry." Yau she kaci abinci? Tunda yayi zazzaɓi kamar an buɗe mishi ciki sosai yake cin abinci, ta dafa mishi indomie ya zauna yana ci yana mata surutu tana biye shi ya fito daga daki ta maze bata tashi ba ya nemi waje ya zauna. wayarta ta fara ringing Adil ya miƙo mata ta daga kiran Siyawa ce ta kira vedio call. Tace "Siyama wlh nayi mantuwa tun shekaran jiya nake neman ki." "Da aka yi me? Baban Khadija ne zai yi miki magana." Baba ya karɓi wayar yace "tunda kika taho bamu gaisa ba ya kuka zo gida, yaya hanya? ina Dattijo yana lafiya?" ta amsa da lafiya, yace "toh masha Allah nayi ta neman ki ban samu ba. Daddy ya karɓa suka gaisa yace "yau mun tashi da Rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata." Umaima ta zare ido "innalillahi wa inna illahirrajiun Allah ya jikan shi yayi mishi Rahama yasa ya huta." Daddy ya amsa da Amin, "wayyo kuɗi sun kwanta dama Allah ya bashi duniya da lahirar." Muna mishi kyakkyawan zato. "Allah yayi wa iyayen mu Rahama, Siyama kuɗi na manta na karɓi cash a wajen Isiyaka." "har nawa ne kudin? "quater million ne." Umma tace "ni ban gani ba. Acikin drawer na saka zaki biya tunda a ɗakin ki suke. Baba yace "ta biya ki uwata." "Yawwa na kira Dada nayi tunanin wani kasuwanci Baba filin cikin gida tunda babu abunda ake yi dashi kiwo zan yi." Wanne irin kiwo uwata? Fahad dai yana jin su yana mamakin son kuɗi irin nata, "Maamah I'm sleepy." Adil ya faɗa ta nuna mishi ɗaki da hannu ya tafi ya kwanta. "Baba Awaki da tumaki da Raguna zan saka mun yi magana da Dada ana samun masu sauki sallah ce zata zo sai ku siya a wajena ga kwata, million a wajen Siyama." Umma tace baki da hankali kuɗin rago ɗaya kenan. "A'a Siyama ƙanana zan siya nayi kiwo kuma zan turawa Uncle Ismah kuɗi zai siyo wasu sai ya haɗa da kuɗin wajen ki a nemi Akuya mai ciki fah kinsan wata shida suke haihuwa bana san juya." Fahad sai daya kware sabida dariya, Baba yace shikenan zai saka a nome wajen, sai ki biya kudin kiwo. Tace toh sai na biya Baba. Suka yi sallama ta juyo ta harare shi ya taso ta dauka wuce ta zai yi kawai taji ya ɗauke ta tana cilli da kafafuwa ya bude kofar dakin shi ya saka key ya zare ta bude baki zata yi mishi ihu ya haɗe bakinsu kamar ya hadiye ta ya rinƙa bata zazzafan kiss ɗin da dole jikinta yayi lakwas tun tana protest har ta sakankance ta miƙa wuya yayi yadda yake so da ita sai bayan komai ya lafa ta fara mishi kukan shagwaba ya kalle da idanunshi cike da Soyayyar daya kasa yadda da ita yayi mata dariya ya ɗauke ta suka yi toilet. Tun daga ranar ta fahimci key ɗin dakinta ya ɗauke haushi da takaici ya kama ta, tin daga ranar kuma ko suna tare da Adil daya ke mai nauyin bacci ce zai ɗauke shi ya kai shi ɗakin shi yayi yadda yake so da ita, in tayi mishi magana yayi mata banza. Gaskiya ta gaji ai ba haka suka yi ba amma zata yi mishi a rubuce tunda ya manta da agreement ne, ta dauko takarda tayi rubuta kamar haka. *Hello this wasn't part of our initial agreement I will appreciate it if we could stick to the original terms and conditions.* Ta ji muryar shi a falo ta kira Adil tace ya bawa Papan shi, yana zaune yana shigar da wani aiki a System Ãdil yazo yace "Papa." ya kalle shi paper ce a hannun shi ya miƙa mishi hannu ya karɓa ya karanta content ɗin paper yayi murmushi ya yaga ta into pieces yasa a dustbin, amma tafi shi gaskiya, baya son takura kan shi da tunanin ya cigaba da abunda yake yi. Tana packaging kayanta tana tunanin ai dai ya karanta taji mararta ta murɗa tana shiga toilet taga period ɗin ta ne mamaki ya cika ta, tayi lissafi saura 2 days ma ya zo tayi wanka ta gyara jikinta ranta babu daɗi, haka za a cigaba da zama kenan? wannnan mutumin yayi ta mata mugunta? wlh bari ta same shi ita ta gaji. Yana falo yana ta aikin shi ta zo ta tsaya a gaban shi, ya ɗaga kai ya kalle ta "any problem?" Ya tambaye ta, ya ɗauka ma maganar ɗazu ce ta kawo ta sai cewa tayi "period ɗina ne ya zo." ya tsare ta da ido ta sauke kanta ƙasa yayi mata kwarjini, calmly yace "go on." ya faɗa, kai tsaye tace "wai kodai baka iya ba ne?" kwakwalwar shi ta fassara mishi abinda take son faɗa ya kasa yi mata ciki ke nan? Muryar Ãdil ce ta katse su, yace "Maamah you are covering my view." ta kare mishi cartoon daya ke kallo. Fahad yayi mata pointing Adil yace "and that is your answer." ya kwashe System ɗin shi ya wuce, haushi ya kama ta "toh shake nan abunda zaka ce?" ya yi shigewar shi ɗaki, sai da ya zauna ma abun ya bashi dariya yayi me isar shi, me kuma zai ce mata shi ai kurma ne baya magana sai action, bature kuma yace actions speak louder than voice. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 3️⃣9️⃣ A month later Umaimah ɗakin Adil ta koma da kwana da yake akwai key ajikin ƙofar ta dauke duk inda zata dashi take tafiya, kanya dawo daga aiki ta kulle kanta a daki, wannan dabarar ta fado mata daga baya shima ya manta da key din dakin Adil din sai rannan da ya zo daukar ta ya ga dakin babu kowa haka ya haƙura da kyar ya iya bacci a ranar dan ya riga ya saba kullum tare suke kwana ya rungumeta a jikin shi. Ta ji fitar shi yau da wuri tunda ta yi sallar Asuba take son shiga ɗakinta akwai abunda take son duba wa tana jin tashin motar shi ya fita ta koma dakinta ta dauki PT din data taho dashi tun zuwan ta bikin Hidaya ta siyo da yawa, fitsarin sassafe ake so yafi zama accurate a lissafin ta lokacin period ɗin ta ya wuce da 5 days tana dubawa ta ajiye shi a toilet tank tana jira yayi yan minutes ta duba tana addu'a a ranta Allah yasa hasashen ta yayi daidai, kamar me tsoron wani abu ta leƙa ta ga 2 likes, hannun ta na rawa ta dauka 2 lines radau ta ƙara dubawa haka ne ta fito daga toilet ta yi sujud shukur wani tsalle tayi tana murna "Alhamdulillah Alhamdulillah! ta faɗa kan gado ta yi birgima Masha Allah toh yanzu sai next steps ta shafa mararta, tace "Allah ya inganta mun baby na." Sai ta miƙe ta fara fito da kayan material ɗin mutane da za ta ɗinka, dole ta mayar da hankali ta kammala ta haɗa kan yan kuɗaɗen ta kafin ta tafi. Abun duniya ya dami Fahad yau kusan one week kenan da suke wasan buya da ita, bata yadda ya ganta sai ta fahimci Mrs Lawrence tana nan dan ta san ba ze iya mata wani abu a gaban ta ba sai ya ji kamar ya sallami Mrs Lawrence ɗin ma haka kawai shi da gidan shi ya kasa sakewa, wata zuciyar tace da ba haka kake rayuwar ba, to yanzu kuma ya canja, toh me yasa? Shima bashi da wannnan amsar coffee dinta yake son sha jiya ta haɗa zata sha Allah ya taimake shi ta shiga ɗaki kanta fito ya dauke ya shanye, kai dole ya nemi mafita zai same ta su yi magana wannan agreement ɗin ya gaji it should be over su yi rayuwar aure kamar kowa bari zai yi mata magana idan sun gama conference in 3 days yanzu aiki yayi mishi yawa baya son stressing kan shi da yawa aka yi knocking ya bada izni a shigo Mrs Susan ce tazo ta zauna suka cigaba da aikin tare. Bayan sun fito daga conference daya ke wayar shi a silent take ya ga missed calls din Fadoul Muhammad (Tahir) yayi dialing number back suka gaisa Tahir yace mishi "kwana biyu ina Ibrahim da Fatima yata? "they are fine." "Please ka gaishe su cikin next Month zan kawo muku ziyara UK in sha Allah." Fahad yace "thanks Sir." sun ɗan taɓa hira yace yana Haram yanzu za a yi sallar La'asar suka yi sallama. ***** Lafiya Khadija? Ki yi min bayani menene. kuka ne ya ci ƙarfin ta da ƙyar ta bude baki tana magana muryarta a dashe tace "Baba a sume Ambulance ta tafi da Ahmad yau jikin shi babu daɗi muna asibiti." "innalillahi wa inna illahirrajiun." yi shiru Yana ina? "sun shiga dashi ciki." "Ki kwantar da hankalin ki, ina zuwa zan neme ki." Ya aka yi? Umma da shigowar ta kenan ta tambayi Baba, ya nisa yace "jikin Mijin Khadija ne ya motsa. Umma ta fara hawaye "Allah ka dubi bawanka ka saukaka mishi, ubangiji ya bashi lafiya Allah sarki Yayarsu, Allah yasa ki ci wannan jarabawar." ta faɗa tana share hawaye, Baba ya shiga toilet ya fito ya kalli Umma yace "bari na je wajen Yaya Ibrahim mu yi shawarar yadda za a yi." Umma ta kasa magana ta gyaɗa kai ya fita. Ya shiga bangaren Daddy da sallama ya tarar da Mami da Daddy, suka gaisa nan Baba yayi mishi bayanin komai Mami jikinta yayi sanyi Daddy yace "kai Ahmad yana jin jiki gara a canja mishi asibiti, tuntuni naso yin hakan amma bari muga." ya kira Sa'ad yace ya same shi a falo da yake yazo weekends ne yana gari, ya shigo ya gaishe da Baba Daddy yace "wanne Asibiti ne mai kyau daya ke dealing da matsalar hypertension?" "waye babu lafiya? Daddy ya mishi bayani ya tausaya masa yace "gaskiya dai idan ana son best medication sai US na san su ne best a wannan field ɗin sun ƙware." Daddy yace "okay a ina asibitin yake a US? "A New York ne, Newyork Presbyterian hospital." Daddy ya yi goggling options suka fito da yawa yana cikin asibitoci masu kyau ya cewa Baba bara na kira ta muyi magana, ya kira yayi mata bayani su Ibrahim za su taho a canja mishi asibitin a US aga abunda hali zai yi, ta yi godiya suka yi sallama. Daddy yace "Sa'ad ya dauki leave shi da Ibrahim ko na sati ɗaya ne tunda Ibrahim likita ne zai bada gudunmawa sai su tafi tare . UK Over working kanta take yi sabida tayi ta gama haɗa komai ta bawa masu kaya kayansu jiya ta kira Aunty Ramla tace tafiya zata yi, a jiyan tazo ta karɓi kayanta gaba-daya bata da outstanding orders duk ta haɗa tana tunanin yau ma ragowar waɗanda ba su karɓa ba za su karɓi kayan su duka. "Maamah why are you packing, are we going to Nigeria?" sai jikinta yayi sanyi ta kalle shi ta kawar da kai kar ya karyar mata da zuciya, tace "no I'm arranging them." ta faɗa sai kuma tayi wani tunani ta juyo ta kalle shi "i will be away for 2 days please be a good boy Didi okay?" Maamah carry me along. "No I will be back soon ok." ya ɗaga kai ta ja hannun shi suka shiga kitchen yana mata surutu tana aiki, tayi aiki da yawa, ta yi masa samosa meatier, spring rolls, tayi stew da yawa ta soya nama, tayi pepper chicken ta kwaɓa cin cin ta je tayi sallah ta dawo ta soya tana yi Adil yana ci ta saka a cointainer ta saka a fridge, ta faɗawa Adil nashi ne idan zai ci Mrs Lawrence ta soya mishi ta nuna mishi inda ta ajiye masa cin cin harda stew ta saka a fridge idan zai ci rice ko spaghetti. Yace "I hope you will be back soon Maamah?" Yes Didi. taki haɗa ido dashi dan karya bata tausayi suka koma ɗaki. Washegari Passport ɗinta tunda suka dawo yana wajenta ta riga ta siyi ticket, jirgin ƙarfe 2 zatabi zuwa US, can zata wuce sun yi waya da Ammi kusan sati kenan tace mata tana Asibiti ta duba wayarta ta turo mata address ɗin gidan da Daddy ya kama mata By 1pm agogon England tayiwa Ãdil sallama ta kira uber ya kaita airport tana isa tayi boarding pass ta wuce USA. Lokacin da ta isa sunyi waya da Khadija tana asibiti, dan haka direct ta wuce ƙaramin gidan da Daddy ya kamawa Amminta 2 bedroom ne, ta shiga ɗaya ta ajiye kayan ta ba tare da Khadija ta gani ba, sannan ta fito ta tafi Asibitin. Ta tadda Khadija ita kaɗai abun tausayi tace "Ammina ke kaɗai ce babu wanda ya zo?" Khadijah ta nisa idon ta yayi jah saboda tashin hankali tace "jiya su Ibrahim suka koma daya ke babu zaman jinya." "me yasa kika taho? Khadijah ta tambaye ta, tayi shiru ba tace komai ba, Khadija bata kawo komai ba kuma hankalinta ba a kwance yake ba sai kawai ta bar maganar. LEBANON Yaseer kewa Tahir bayanin ciwon Ummi wannan lokacin ya matsa mata sosai zasu koma asibiti, har sun ajiye waya ya kira Dr Huzaifa tunda a US yake yana son ya nema mishi best hospital na hypertension, Dr Huzaifa yace ai asibitin su yayi specialissing a kan cardiology and hypertension sun yi making arrangement akan yadda abubuwan zasu kasance Tahir yace su fara processing tafiyar shi ma yana hanya in sha Allahu, Allah dai ya bata Lafiya. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 *Volume two* EPISODE 4️⃣0️⃣ Ya duba agogon hannun shi karfe 11:15 fitowarsu daga conference din da suka yi na 3 days kenan farinciki yake yi yau zai je su yi magana sosai ta fahimtar juna wannan agreement din yau zai zo ƙarshe zai faɗa mata gaskiya kawai, wata zuciyar tace mishi ka fasa rabuwa da ita kenan? Of course yes na fasa. ya bawa zuciyar shi amsa "we will live as a family." yayi murmushi yana tuna conversation ɗin su da yaji akan kiwon Awaki wai kar a siyo mata juya yayi dariya silly girl ya ƙara kwanciya a kan kujerar office ɗin shi yana jujjuyawa, she is a drama queen da gaske Daddy yace she deserve him sosai yanzu ya fahimci da gaske yana son ta tuntuni he is in denial, amma yanzu kam yayi admitting rai da ruhin shi nata ne ita kaɗai, she is fun to be with, zaman da yayi na ɗan lokaci da ita ya fahimce ta duk da ba wani magana suke yi ba tana da nata flaws ɗin amma ba komai zai gyara ta, bama matsala ba ne bata son gyara waje shi sai ya gyara, yanzu kullum sai yayi wa Daddy addu'a sosai yanzu rayuwar shi tayi manufa akan baya daga aiki sai aiki Adil ne kawai farin cikin shi amma yanzu, sai yayi murmushi ya shafa kan shi, yace "her presence brightens up my day and fills me with purpose." shi kaɗai yana ta murmushi har Mrs Susan ta buga mishi table, tace "share the good News with me Mr Bichi." ya kalle ta ya basar ta ce ta turo mishi mail ya duba yayi treating is urgent ta fita ya shiga duba report din. US Prebyterian Hospital Newyork. Ahmad ne a kwance a gadon Asibiti an saka mishi Nasogastric Tube a hanci saboda ta nan yake cin abinchi an saka mishi oxygen Khadija ce a kan kujera tun tana gyangyaɗi har bacci ya kwashe ta Umaima tana zaune a ƙasan ƙaramin centre carpet tana karatun novel a waya Amira ce ta turo mata littafin take karantawa bata da lokacin karatu da saboda harkokin ta amma yanzu zaman shiru ya saka ta fara karantawa kuma ta ji dadin littafin mai suna Hafsatu Sa'idah wanda A&A PEN Suka yishi, sosai labarin ya ja hankalin ta yayi mata daɗi ta tsinewa Samira da Umma Sa'a yafi cikin kwando dubu, aka yi knocking Ƙofar ta ajiye wayar, Dr ne ya shigo tare da nurse ya duba report din patient din Umaima ta matso suka gaisa ya rubuta magunguna da za a siya yace idan ya tashi a kira shi suka fita tana zaune wayar Amminta dake kusa da ita tayi ƙara tayi maza ta dauka Daddy ne yace "a'a yana ji uwata? Ni ce Daddy." "Masha Allah yaushe kika zo? "Ɗazu da yamma." Daddy yace "kai amma Dattijo ya kyauta Allah yayi mishi albarka, da muna tunanin Azumi ta taho tunda ma kina nan shikenan." ita dai ta yi shiru, "ya jikin Ahmad din? Tace "Daddy an saka mishi oxygen wlh yana jin jiki." "Subhanallahi ina Khadijan? Bacci take yi, ko na tashe ta? "A'a gajiya ce ƙyale ta muna yi mishi sannu." suka yi sallama. Yaseer ne yake tare da Ummi yau Tahir zai taho suma kwanan su biyu kenan a Asibitin Ummi ta samu bacci Dr Huzaifa ne ya shigo da sallama Yaseer ya tashi ya rungume shi suka juya harshe ya Duba Dr's report ɗin ya gyaɗa Kai, in sha Allah akwai improvement hawan jinin nata wannan lokacin yayi high sosai ba a so ya harba mata kwakwalwa sai a samu matsala shi yasa ake kokarin controlling. wannan bayanin Dr Huzaifa yake yi wa Yaseer kira ya shigo wayar shi Hameedah ce matar shi ta tambayi jikin Ummi yace mata da sauki ta duba WhatsApp ya tura mata saƙo khaala ta taho ya siya mata ticket da komai na tahowa shi zai dawo LEBANON saboda anyi mishi waya an kama mutum biyu da Almundahanar kudade masu yawa a companyn su, sun ɗan yi hira akan jikin Ummi suka yi sallama. UK Ya tashi daga aiki yana tunanin me zai siya mata wanda zata ji daɗi kai be san me take so ba me zai siya ne? To ko Sa'ad zai tambaya, amma shima ba lalle ya san wannan ba, to ko zai tambayar mishi matar shi? It will look some how, wannan yarinyar kuma (Hidayan) baya son ma kiranta sai raini ya shiga tsakani. Zuciyar shi ta kimtsa mishi ya siyo flowers ya shiga mota ya tafi interflora ya siyo ya tsaya ya siyo mata chocolates masu tsada sai abunda ya fi so wato turare nan ya rinƙa dibar mata designers perfumes sai da ya cika carts ɗin da turare aka yi mishi packaging ya fito yana murmushi. Yana shigowa gida Mrs Lawrence ta yi mishi sallama ta tafi dama ta fahimci Madam bata nan dole ba zata bar Adil shi kadai ba, "Papa welcome back." Ãdil ya faɗa, ya daga mishi kai yace "thank you Didi." shi kaɗai ne a falon yana game ya ajiye kayan hannun shi a Dinning ya nufi ɗaki ya watsa ruwa be ganta ba ya san tana ɗakin ta ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin wata riga turtle neck fara mai sharashara ya taje gashin kan shi daya kwanta gwanin sha'awa ya fesa turare kamar an yi barin su a jikin shi, shi kan shi ya burge kan shi komai yayi dai dai ya duba agogo lokacin sallah yayi bari ya je sallah ya dawo ya fito ya tarar da Adil inda ya bar shi ya so yayi magana, is on like her bata barin Adil shi kaɗai, ya je yayi sallah. Sai da ya yi isha'i sannan ya dawo. Ãdil baya Falo yanzu direct ɗakin ta ya wuce ya tura kofar a hankali kamshin humrar ta ya kama dakin har sai da ya lumshe ido, komai a ɗakin neat a gyare ba kamar yadda ya saba shigowa ya gani ba, ya samu waje ya zauna may be tana toilet, yayi kamar 15min shiru ya miƙe dan be ji karar ruwa ba anya tana toilet, ya bude babu kowa, shima a gyare. to ko suna dakin Adil ya fito ya tarar da Aadil a Dinning yana cin spaghetti da juice a cup, yaɗan sauke ajiyar zuciya saida ya ɗan nutsu sannan ya wuce shi yana tunanin tana kitchen, ya shiga bata nan ya buɗe store babu kowa sai ya zama confused, bari ya duba dakin Adil ya fito ya wuce shi har ya kusa gama cin abincin, ya shiga ɗakin Adil nan ma bata nan ya buɗe toilet babu kowa sai ya rude to tana ina? Ya fito ya koma dakin shi ya sake fitowa a firgice ya cewa Adil "where is Maamah?" Directly yace masa "Maamah is not around Papa, she travelled to Nigeria." Ai kawai sai ya sulale ya zauna jagwab a ƙasa take kan shi ya sara ya kurawa Adil ido yaga ko a jikin shi, something is fishy me ta faɗa mishi da be damu ba? "come here DIDI?" ya tambaye shi yau she ta tafi, ya faɗa mishi tayi tafiya ɗazu zata dawo in 2 days. Hankalin shi yayi mugun tashi toh meyasa ta tafi? Daya sani data ce mishi tana period last month daya zaunar da ita sun yi maganar kawai. Innalillahi wa inna illahirrajiun, Allah ne kaɗai ya san me zata faɗawa iyayen su, jijiyar kan shi ta mike gaba ɗaya ya burkice. "Papa are you okay?muryar Aadil ta dawo da shi daidai, yayi mishi yake ya miƙe da ƙyar jiri yana ɗaukan shi da kyar ya kai kan shi ɗakinta ya zauna bakin gado ya tashi ya buɗe wardrobe ta kwashe komai nata empty, gaban shi ya faɗi, idon shi yayi ja ya dawo ya zauna a kujera yana wani irin numfashi kamar me asthma ya ɗaga kai ya kalli hoton ta a bedside ya saka hannu ya ɗauki hoton a tsaye take kanta babu ɗankwali tayi parking gashin ta a gefe kamar baby tayi murmushi, sosai tayi kyau a hoton, zuciyar shi yaji tana wani irin gudu a girjin shi, har zai mayar da hoton wata farar takarda a ninke a wajen ta fado, frame din ne ya danne ta daman purposely aka ajiye ta a wajen kenan? ba manta hoton ta yi ba ke nan? da sauri ya warware takardar data ta rubuta sako kamar haka. 💫 UMAYMAH 💫 ✍️A&A PEN Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3 https://wa.me/+2348039352724 Volume two EPISODE 4️⃣1️⃣ Hello I hope this message finds you well, I take great offence to being asked to leave your life, I am well aware of my worth and have always known that you never truly accepted me from start, Now I have decided its time for me to leave and I need my divorce paper or else (wallahi na

Chapter 16 of 27