fallasa mata shi ne tana shigowa yana kallon kofa idon shi a kan ta ta kalli Khala da mamaki a fuskar ta ya mike daga inda yake zaune ya bude mata hannu tana wata tafiya kamar me catwork ta karasa ya rungume ta "oh my Zahra I miss you sweetheart." ya fada yana wata aniyar zuciya itama tayi lub ajikin shi tana shakar kamshin turaren shi har wani lumshe ido take yi ya fara bata kisses.
"I guess I have to leave." Khala ta yi magana Sam ba su ma ji ta ba ta fita ta rufe musu kofa tana murmushi she's lucky ta fada.
........To ba kya daukan waya ta ba dole na taho ba. Fahad ya faɗa yana drying gashinta, tunda suka fito daga wanka ya ɗauko dryer a toilet yake mata drying ya gama kawai wasa yake yi da gashin sai ya nutsa hannunshi a gashin kamar audiga yana wasa da shi kamar susa yake mata sai lumshe ido take yi yayi mata rada a kunne tana dariya tana lumshe ido, zaune take akan stool daure da towel ya shagala kallonta suka hada ido ta mirror kamar an saka musu mayen karfe idon su acikin na juna tsayuwar tana neman gagarar shi ya dauke ta yayi kan gado da ita ya haɗe bakin su suka koma ruwa.
.....Isma'il ne durkushe a gaban Daddy ya sunkuyar da kai "babu yarda zan yi Hakimi duk bayanin da na yiwa Dada bata fahimce ni ba jiya Baban ku takanas ta kira shi Bichi tace ya ja min kunne bata son maganar."
Isma'il gaban shi ya faɗi sai kawai ya ji kamar ana juya shi da za a gwada BP din shi tabbas zai hau.
"kasan iyaye sai an bisu a hankali." maganar Daddy ta dawo da shi "abunda nake so dakai mu bata lokaci dan cikin mu babu wanda be yi Na'am da zancen ba, toh iyaye dole mu lallaɓa su jiya jiya cewa tayi hawan jinin ta ya tashi ka yi hakuri mu cigaba da addua mu ga abinda Allah zai yi, wannan karon ma bata saurari maganar Muhammadu ba tashi ka je Allah yayi maka albarka." jiki a sanyaye yace "Nagode Daddy." ya fita Daddy ya girgiza Kai har ga Allah babu aibu amma dai Allah ya dora su akan Dada.
~~~~Hayatee ki cigaba da yi min yangar daga waya sai na yi ta kiran ki babu response idan kika gani ki share ni shi ke nan Alhamdulillah ko a muryarki na ji jikin da sauki, Hayatee na san fah har yanzu kina iddah ba zan yi abunda ya saba wa shari'a ba. yayi shiru ta ja fasali tace "Baban Umaimah ba haka ba ne."
"toh yaya ne? Ɗazu ka kira ina sallah ne dana idar kuma Umma bata ji dadi ba su Baba na Azumin Litinin na shiga kitchen shirya musu abincin bude baki kayi hakuri." ta fada, wani sanyi ya ji a ran shi Khadija mai nutsuwa ce mai sanyin hali ce yanzu idan tace Baban Umaiman nan sai ya ji kamar ya dauko zuciyar shi ya mika mata.
"ka yi hakuri." ta katse mishi tunani, ya nisa yace "na hakura Hayatee saura 3months 5 days ki fita daga iddah." yana fada ta rufe fuska kamar yana kallon ta yace "kin rufe ido ko? Ya faɗa yana dariya ya san halin Khadijan shi kamar yunwar cikin shi.
.....Da Dubai suka fara yawon shakatawa tun ranar da Fahad ya biyo ta Lebanon ya gama musu shirye shiryen komai washegari tayi ban kwana da su Khala sun shaku sosai harda koken koken su Ummi har da ita a Rakiyar airport ta Ciro warwaron hannun ta na gold guda biyu ta sakawa Umaimah, Tahir ya matso ya rungume ta ya hada hannun su da Fahad yace "safe trip Allah ya kai ku lfy."
Har an fara kiraye kiraye jirgin su zai tashi sai da suka ga sun shige an fara karɓar boarding sannan suka tafi Khala tana ta hawaye, Tahir shima jiran tafiyar Umaima yake yi zai koma SAUDIA. business class suka shiga komai vip treatment ake musu they are very comfortable sanyi yayi mata yawa ya lulluɓa mata sabon bangon da aka basu ya rufa mata sosai ta shige jikinshi.
Tunda suka iso take bacci ya barta a hotel ya fita yayi musu shopping kanana kananan abubuwan amfani, tafiyar tsutsa yake mata a kafa ta bude ido "Zarahhhh wannan baccin ya isa haka ki tashi ki yi wanka za ki ji daɗi." ta turo baki "kai baka gajiya da wanka dai wanka dai kamar kifi." yayi dariya ya fara mata cakulkuli tana dariya ya ɗauke ta kamar baby yayi toilet da ita.
Ta fito sun shirya yace zasu fara shiga gari yau sun fara da Burj khalifa world Tallest building, sun fita musamman aka hada su da driver da zai rinka zirga zirga da su sun je palm jumeirah wajen ya hadu sosai beach ne sun dauki hotona har da wanda ta dauka a kan doki, Fahad yayi mata pictures kamar babu gobe tunda ta sauko ta fara jin jiri jiri kamar zata faɗi ya tare ta "menene? Tace "Kaina ke juyawa." sai ta fara Amai hankalin Fahad ya tashi yace da direban ya kai su nearest hospital, sun je yayi komai aka basu damar ganin Dr likitan tayi mata tambayoyi tace ta kwanta tayi mata scanning cikin ya kusa 4months ita a lissafin ta 3months, Dr tace ba wani abu bane cikin ne ya saka ta a yanayin da take ciki ta rubuta mata magunguna folic acids, Vitamin D, omega 3 fatty acids suka fito daga office din daga nan suka koma hotel, Ranar Umaima ta lafke mishi tayi sai yayi mata tausa sai ta ce bayanta ya kwantar da ita ajikinshi yana ta matsa mata jiki duk ta rikita shi sai wash take yi yana binta da sannu sannu! dai an fada tafi cikin carbi da kyar ya lallaɓa ta taci abinci tana bori tana komai suka yi wanka ya kasa daga mata kafa ya lallaɓa ta ta bashi hadin kai.
Washegari suka dora daga inda suka tsaya sun je Burj al Arab Dubai mesium Dubai miracle garden yayi mata siyayyah kamar babu gobe duk abunda ya siya idan ta ga price tag tayi ta mita gaskiya yayi tsada, wata jaka ya siya mata ta yi converting kuɗin to Nigerian currency duba da yarda kudin mu darajar shi ta fadi ta ji kuɗin yayi yawa ta hau fushi ita wlh daya bata ta kara jari yana ta lallaɓa ta daga nan suka wuce Dubai gold souk Allah ya taimake shi tace ta gaji shi kadai ya shiga ya fito da leda a hannun shi.
sun gaji yayi musu order abinci, duk cin abincin ta ya lura bata ci kamar da, da kanshi ya rinƙa bata a baki ita ta fara shiga wanka ta fito ya dauki ledar ya fito da sarka tana zaune a gaban mirror ya saka mata, tace "daga gani nasan an ci kudi kuma nasan da tsada ka siya." ta faɗa, yayi murmushi tace "thank you soo much." sai ya ji zuciyar shi na melting yayi murna tana son ta yace "you are my heaven on earth and I don't know how to thank you enough this is just a small expression of my gratitute." wani irin yanayi ta shiga sai murmushi take yi ta mike ta rungume shi .
.....Maldives suka wuce daga Dubai!
Kwanan su 5 yau a Maldives Umaima cikin ta ya fito kana ganin ta ka ga mai ciki ta yi haske sosai fatar ta tayi kyau masha Allah, shima Fahad ya murje kana ganin shi kasan hankalin shi a kwance yake yau veligandu suka je beach ne suka dauki pictures a bakin ruwa daga nan suka wuce Banana Reef sun je sunset cruises ko view ɗin wajen kawai zai saka nishadi da kwanciyar hankali, Grand friday mosque anan suka yi sallah suka koma hotel.
Vedio call suke yi da su Daddy yace uwata me kike ci haka? tace Daddy komai ma ci nake, Daddy bana samun Uncle Isma a waya December ce fah saboda yan Christmas na saka Akuyoyi kar fah nayi asara." Fahad daya ke jinta yayi dariya, Daddy yace "Manager fah sai a hankali."
"me ya same shi?
Nan Daddy ya mayar mata komai tayi sallama da Daddy sai jikinta yayi sanyi bata kyauta ba Uncle Ismah ne fah ya sha tare mata fadan Babangida, Fahad ya fahimci ta damu ya tambaye ta kamar zata yi kuka tace "ban kyauta ba." tayi mishi bayani.
Sauran one month su gama hutun su daga nan India suka je suka yi 1 week sun je Taj ma hal daganan suka wuce China Umaima ta ruɗe ya kaita wajen kayan accessories ɗin ɗinki ta sayi komai a farashin sari kamar me bude shago, satin su 2 a China, suka fara haramar dawowa gida basu gama hutun ba saura sati daya tariyar Khadija a wannan satin shi yasa suka dawo.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 6️⃣0️⃣
Suna sauka a mallam Aminu Kano International airport kiran Sa'ad ya shigo wayar Fahad ya daga yace "kun sauka ko?
"Yea yanzun nan." ya faɗa musu inda yayi parking yana kallon su ta mirror yarda ya riko hannunta, Sa'ad ya fito yana dariya "welcome back. ya kalli Umaima da idonta yayi luhu luhu saboda bacci yace "daughter sannu da zuwa." suka karasa mota yace "Guess what? Yana kallon su "I'm the latest Papa in town."
Dan Allah Amira ta haihu? Me ta haifa? har ta wartsake tana kallon Sa'ad yace "saura ke." Masha Allah congratulations. Fahad ya miƙa mishi hannu, Umaimah tace "tana ina ko tana asibiti?
"tana gida an sallame su." Yaushe ta haihu wlh anci Amanata yanzu Amira ta haihu a kasa kira na? Surprise mu ke son baku. "wannnan ba surprise bane Alhamdulillah it's a double celebration." yeah Fahad ya faɗa yana murmushi "wlh kamar motar bata tafiya." Sa'ad yayi dariya yace don kina sauri ne.
Hankalin ta duk yayi gida, "wai me ta haifa ne? Baby girl. "kai I'm so happy."
Suna isa ta fito da hanzari kamar zata kwasa da gudu Fahad yayi sauri ya rike ta "easy kinsan ba ke kadai bace." ta daure dai ya rike hannun ta suka yi bangaren Mami anan Amira take Sa'ad ya rufe motar ya saka Malam Habu ya kwashe musu boxes ɗin su ya kai ciki.
"Assalam alaykum." ta faɗa da karfi, su Mami Khadija, Munnirah, da Umma suna kasa Amira tana ɗakin kasa anan take jego, suka shigo rike da hannun juna Umaima ta kwace hannunta dukkan su kallonta su ke yi tayi kyau sosai cikinta ya fito ta gaishe su, Umma sai kallonta take yi, Khadija cikin hikima ta sulale ta fita ta baya saboda kunya irin ta ta.
"kishiya ta sannunku da zuwa." Mami tace ɗazu nake cewa zan turo miki hoton baby na manta." "gaskiya Mami ba a kyauta min ba."
Su Daddy suka Shigo Umaima ta gaishe su tana mitar ba a faɗa mata ba "wai ina baby? Kamar ta ji tambayar da aka yi sai ta fara kuka Umaima ta mike da sauri ta nufi ɗakin da ta ji kukan babyn, Baba Rabi ce take mata wanka "A'a uwarɗakina lale maraba an dawo? "Mun dawo." Umaima ta tsira mata ido Babyn kuwa katuwa masha Allah tayi kama da Sa'ad amma chocolate colour ce kalar Amira kyakkyawa ce masha Allah, Baba Rabi ta gama shirya ta ta saka ta a showel ta miƙawa Umaima ta fito da ita wajen su Daddy tana cewa.
"Daddy ka taɓa ganin kyakkyawar halitta irin wannan?
"Wa a kai kasuwa ina da Darsha matata fara me zan yi da wannan." Fahad ya zo ganin baby tace sai dai ya ganta a hannun ta Umma tace "me yasa kike haka ne?" kafin tayi magana Amira ta fito Fahad yayi mata ya jiki ta kalli Umaima ta harare "ta wlh zan rama."
Sai ta kalli su Daddy tace "Daddy wlh ka ceci Amira." duk suka zuba mata ido ba a gane zancen ba, "da aka yi me?"
"Da Daddy ya taimaka ya bata Uncle Sa'ad mana da Ɗan Iya ta aura wallahi yar nan bazata ganu ba, Ɗan mitsitsin kai dashi ga kunnuwa wai falaki idon shi ciki ciki ga ƙaramin jiki kamar ragowar Aski." Sa'ad dariya har da hawaye, Amira ranta ya baci Daddy daya dage kar yayi dariya yace "rabu da ita Auta." Auxubillahi Allah babu kyau raina halittar Allah cewar Umma, "nima ba rainawa nayi ba fasalta muku shi na yi, ai haka yake ko Amira?"
Amira data cika ta yi fam ko kallonta bata yi ba.
.......Wlh abun yana damuna Umma ke yiwa Umaimah bayanin halin da Ismael yake ciki "kwata kwata yanzu fah bashi da walwala, bari ki ganshi. ta kalli agogo "ai ya kusa dawowa kwanaki sai da yayi kwana biyu a asibiti, ba komai ba ne nasan zancen yarinyar nan ne Baban Khadijah yayi ta ƙoƙari akan Dada amma babu nasara." idon Umaima ya kawo ruwa jikinta yayi sanyi tace "wannan wacce irin tsohuwa ce mai kafiyar bala'i saboda Allah. Umma ta yi mata dakuwa, "toh Siyama ba ke kika kira ni ba? Na kira ki ina tunanin abunda ya shafi Hakimi kai tsaye ya shafe ki, ita kanta maganar ta dame ta kawai ta nunawa Umma babu komai amma abin be yi mata daɗi ba ta tausaya mishi "Siyama wannan ba wani abun damuwa ba ne ba shi da mata sai Nabila." Umma tace Fadila dai."
"Ah su Siyama an rike sunan suruka." Umma tayi tsaki ta fita "sai ana maganar Arziki da ke ki kawo shirme."
Bayan fitar Umma ta dade tana tunanin mafita bata samu ba tayi kwanciyar ta bacci ya dauke ta, ta farka bayan La'asar wata yunwa ce ta taso ta tayi sallah da kyar ta sauko kasa Khadija ce da Umma tare da Munnirah da Baba Rabi sai Barira, Khadijah tana gefe da hisnul Muslim a hannunta su Umma kayan souvenir suke packing saura kwana 4 a daura Aure, ba wani abu za a yi ba bayan an daura aure a Bichi Umma zata yi walima a gida anan Kano washegari zasu wuce SAUDIA.
Umma ta kalle ta tace "Yanzu haka kika sauko? Wani burgujejen gajeren wando ne a jikinta sai T shirt "kinsan gidan nan baya rabuwa da maza." Siyama mazan ai muharramai na ne. ta wuce kitchen Khadija sai ta kalleta ta ɗauke kai tana mamakin hali irin na Umaima, ta dawo kusa da Khadijah ta zauna tana cin abinci taci kaɗan tace "wlh Awara nake son ci da yaji dakan ballagaza." Umma tace "Barira ta siyo miki." Umma ta bata 1000 "yajin dai shi ne matsala." Sai na daka babu matsala, Ammina ya shirye shirye?" ta faɗa tana dariya Khadija ta harare ta Munnirah tace "ba wani shiri mu ke ba. Ai kuwa zan ɗan zubar da rabin galoon na kwaso shoki. Khadija tsam ta tashi ta hau sama Baba Rabi tayi dariya tace "uwarɗakina kenan kowa abokin wasa ne." Umma tace ai ta bar ta da halinta tunda ita ba hankali ne ya wa dace taba. har zata yi magana Ismael yayi sallama ya shigo "sannunku da gida." ya faɗa suka amsa be tsaya kallon su waye ba a falon ya wuce, Umaima da sauri ta bi bayan shi har zai saka key ta shiga ɗakin gaba-daya ya canja kamar ba Uncle Ismah ba sai ta ji hawaye zai zubo mata.
"Uncle Ismah lfy? Yayi shiru ya zauna bakin gado yana cire takalma da socks "saboda Fadila ne ka rame haka?
Be bi takan maganar taba yace "yaushe kika dawo? Ɗazu da safe ta faɗa, "ka ganka kuwa? Toh yaya zan yi I taught you will support me ni kadai nake abina sai na kira ki kiƙi daga waya, atleast if I share my pain with you zan samu sauki amma kin share ni yaya zan yi Umaimah." sai hawaye, tace "ka yi haƙuri Uncle Ismah na yi maka laifi amma in sha Allahu baka da mata sai Fadila." ta faɗa da yakini, kawai ya tsaya yana kallon ta tace "in kawo maka abinci pls Uncle Ismah wannnan ba Uncle Ismah na ba ne I want my Uncle Ismah back." ya yi murmushi yace kawo min ta fita daga ɗakin.
~~~~Tahir ne yake ta shirye shiryen tahowa Nigeria sun yi tsare tsaren su da Yaseer na yan uwansu mutum 10 da za su zo ɗaurin aure daga Lebanon, shi ba wani biki zai yi ba Ummi ce ma ta ce su taho Lebanon ayi biki saboda yan uwa ya dai lallaɓa Ummi tayi haƙuri idan sun huta kwana biyu a SAUDIA zai kawo ta Lebanon ɗin sai ayi walimar welcoming din ta da ƙyar ta yarda, sai kuma tayi tunani sun hadu da jarabawa iri iri suna bukatar kasancewa tare da juna.
Dr Huzaifa ma zai taho daga US suna waya ma da Ibrahim sun tsara idan yazo daurin aure tare zasu koma US komai na harkar tafiyar shi ya kammala wani abun ma Dr Huzaifa ya turawa har gidan da zai zauna Dr Huzaifa ne ya kama mishi.
Yan uwaa sun hallara gobe ɗaurin auren Khadijah kuma yayi dai dai da sunan Amira sai aka ce a haɗa gaba-daya tunda dai duk Mutane ɗaya za a gayyata su Yaya Surayya da yaya Hindu Aunty Amal duk sun zo da yaran su Falon ya cika Umaima ta sauko da hijabi ta gaishe su tayi hanyar fita "ina zaki.? Umma ta tambaya, tace "Wani waje zani."
wajen bashi da suna? Baba ya faɗa, kin dai tambayi Mijin ki? Tace munyi waya tun jiya. "shikenan." cewar Baba, dayake Fahad tunda suka dawo ya tafi Abuja sosai ya mayar da hankali akan ginin companyn shi da zai dawo Abuja yana da gida a Abuja amma uncompleted building ne sosai ya zama occupied wayar ma yawanci sai da daddare suke yinta, aiki kawai yake da engineers, so yake ya ci karfin aikin sosai kafin su koma.
"Maamah zan je." Adil ya faɗa, tace "No Adil ina Iman ka je ku yi wasa." ta fita already ta yi wa Mallam Sadi magana zasu Bichi ta shiga mota suka kama hanya ba a fi minti 10 ba bacci ya kwashe ta.
"Ranki ya dade mun iso." maganar Malam Sadi ta tashe ta, tayi hamma ta bude ido tayi hamdala "sannu Mallam Sadi bacci ne ya kwashe ni."
"na gani Hajiya."
Yayi parking ta fito ta dauki wayar ta ta kira Sadiq wizard ya daga "yauwa na zo pls zan kira ka kar fa a samu matsala."
"baki da matsala smart." ya faɗa, Mallam Sadi fito min da Kayan. ya fito da gurasa da kilishi da dambun kaza da kanta tayi wa Dada dambun ta shiga da sallama Dada ce a falo tana kallon sunna TV Malam Daurawa yana wa'azi Umaima ta yi murmushi komai zai yi daidai kenan abun ya zo akan gaba, da carbi a hannun Dada tana ja Mallam Sadi ya shigo suka gaisa da Dada ya fita.
"wacece nake gani kamar jikar Maryama?" "ni ce Dada." ta faɗa tana gaishe ta "Sai yau kika ga damar zuwa? "haba Dada gurasa na bayar ayi miki ba a gama da wuri ba."
Dada tace "eh to na ga zuwan ki."
Umaima ta gyara zama tace "Allah dai ya kara nisan kwana mai albarka, Allah ya tsare ki ya bar ki da Babancikin gida."
Dada tayi murmushi tace "ni dai bani da dabbobin baki."
"ni da nake da uwar kudi na Dada." Umaima ta faɗa,
"Ahto."
"Dama mallam ɗaurawa ne ya aiko ni yace na gaishe da Dadan Bichi dattijuwar arziki."
"Mallam Daurawan?" Dada ta faɗa tana dafe kirji.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 6️⃣1️⃣
Bana son karya. Dada duk ta rikice a duk Malaman Addini Dada tana son Malam Daurawa, "kin yi shiru?" "To Dada Baban wani abokin karatu na ne." Allah jikar Maryama? ƙwarai kuwa Dada.
"shi ne baki taɓa fada min ba?
Ai Dada kullum idan mun haɗu sai nace Kakar Ammita masoyiyar shi ce. kwyarai kuwa wannan haka yake.
"yanzu ma cewa yayi idan na zo na kira shi a hada shi da ke."
"ke Dan Allah?" Dada ta fada da sauri. ƙwarai kuwa." Dada ta mike tace "bari na dauro Alwala sai ki kira shi." toh Dada a fito lafiya. Umaima tana zaune tana dariya cikin ruwan sanyi hakarta zata cimma ruwa, bata fi 5min ba ta dawo har hijabi ta canja ta zauna "yauwa kira mu gaisa yarinyar kirki."
Umaima ta daidaita yanayinta kar ta yi dariya, wizard shuuumi ne tun suna makaranta Allah yayi mishi baiwar kwaikwayar muryoyin mutane jiya bata yi bacci ba sai da ta lalubo karshen matsalar, ta dannawa Sadiq kira ya daga tace
"yauwa magajin Malam dama ina Bichi ne Malam ɗin yana kusa."
Sadiq yace "eh bari na duba ɗazu dai yayi baki." Toh duba yau dai ga Hajiya Dada. Umaima ta faɗa, Dada tace "Allahu Akbar jini ba karya ba sai na ji kamar muryar Mallam ɗin ma."
Yauwa ga shi nan Sadiq yayi gyaran murya "Assalamu alaikum."
Dada sai ta sauko ta durƙusa a kasa, Umaima ta juyar da kai Dada ta amsa sallamar.
"Hajiya Dada Allah ya ja kwana mai Albarka." Amin Mallam.
"kullum ina jin sakon gaisuwa nace dai a haɗa ni da Dada yau mu gaisa." "Tabbas wannan gaskiya ne Mallam."
"Hajiya Dada."
Na'am Mallam.
"wani hanzari ba gudu ba jikarki ta bawa yaron wajena labarin jikan ki zai auri wata baiwar Allah a Illori Kwara."
"haka ne Mallam amma nace ya nemi wata."
"Hajiya Dada ina roka miki gafarar ubangiji hakan ba dai dai ba ne Ahlul kitabi ma an bawa musulmi dama su aura Mace ce ba a bata wannan damar ba saboda raunin su kar Miji ya ringaye ta balle banbancin yare wannan kuskure ne ba dai dai ba ne ki tubarwa Allah idan Allah yayi matar shi ce sai ya dauki ran ki ayi ba kya nan."
Dada tace "In sha Allahu da ni za a yi Malam." Yauwa Hajiya Dada daga hannu mu yi addu'a." Sadiq ya rinka kwararo addu'a suka shafa, "yauwa Allah ya ja kwana."
"Amin Allah yayi maka albarka ya kara hasken makaranta nagode kwarai zan aiko da kudin sadaka."
kit sadiq ya kashe waya Dada ta kalli Umaima tace "jikar Maryama Allah yayi miki Albarka kin gani zance cikin Hikima da kwanciyar hankali, amma su Ibrahima karfa karfa suke min,
Dan Allah bayani be fito ba filla filla ba gwanin shaawa?" Umaima tace "Ya fito Dada." Umaima ta faɗa, "Yawwa kamo min ɗan kanzagin nan." "wake nan?" Umaimah ta tambaya, Dada tace "Ibrahima mana ranar Asabar idan an daura auren Hadiza ranar Lahadi su wuce Illori baki alekum su je neman auren."
"hakan yayi Dada." Umaima ta kira Daddy ta saka a speaker tace "Daddy ga Dada."
Au Bichi kika taho?
"eh tana nan waje na yar kirki ta haɗa ni da Mallam
Daurawa."
Daddy sai ya saka wayar a speaker suka ji muryar Dada tana ta bayani an mata wa'azi mai shiga jiki Hakimi bashi da mata sai Fadila, kana ji na? "Ina ji Dada"
"ranar Lahadi sai ku wuce ku nema masa Auran." dariya ake ta yi a falon, sun gane shirin Umaima ne, "ya nake jin dariya?
"A'a yara ne suke wasa."
Oho ta faɗa suka yi sallama.
Umaima tun tana hanya ake kiranta, Daddy ya kira yana ta saka mata albarka har ta iso gida ana ta murna Baba yace "wai me kika faɗa mata ne? ta buɗe jaka ta fito da yan 500 tace "wannan na Mallam Daurawa ne. aka yi dariya, "gashi nan cikin ruwan sanyi ta yarda kuma na raba ta da yan canji ladan zaman motar data saka ni."
Ismael yayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 27