fah kin kasa zaman school kin dawo wlh kar fah ki yi spill over."
"In sha Allahu babu spill over mun kusa fara exams shiyasa na dawo."
Umaimah tace"hmmm maimakon ki zauna ki yi karatu sosai sai ki dawo? Ahto wlh ki tsayar da hankalin ki ki ƙarasa ke daɗi miji."
"hmm Allah ba ni da isasshiyar lafiya ne shi yasa."
"me ke damun ki? Amira ta wani lumshe ido "guess."
"idan za ki faɗa ki faɗa kinsan I'm not good at guessing." Amira ta tari numfashin ta da cewa "kin kusa zama aunt."
"what do you mean? are you pregnant?"
"Yes." ta ɗaga mata gira, "Alhamdulillah. ta faɗa ta nata murna harda juyi, Amira a ranta tace bari tayi amfani da wannan damar ta kwaɗaita wa Umaimah ya kamata ta shirya da Fahad lokaci na tafiya.
"Wanne sex ne mace ko Namiji?" Umaima ta katse mata tunani, "haba dai just 3 months is early a gane sex ɗin baby atleast 4 months, kin gani na girme ki da six months I'm your senior." sai ta shafa cikinta tace "and my little angel who knows shekara nawa zai bawa danki ko yarki?" gaba-daya mood ɗin Umaimah sai ya canja ita fah bata san fate ɗin ta ba, kawai gata nan dai, they are house mate kawai babu wani intimacy sai dai tana kama kuɗi musamman yanzu da Komai ya sake buɗewa, sai fah sun zama intimate zata haihu? Yanzu shike nan ita haka zata zauna? Waya sani ko sai Hidaya ta haihu ma ita tana nan sai ta girgiza, Kai to meye mafita? Amira ta kalleta taga ta shiga dogon tunani ta yi murmushi she caught her attention wani abun sai an zungure ta, she is glad she did, tace "hmmm Auntyn Baby bari na barki zan ɗorawa my heart Abinci." mtsw "ko ba heart ba aikin banza." ta katse wayar ta shiga tunani ita kenan Amira is pregnant idan bata ɓata a lissafi ba yanzu suna wata na 5 kenan da aure kai ya Allah ka kawo min mafita.
Aikin da suka yi jiya a office ya ke compiling a gida yana shigar dashi a system team team aka yi grouping ɗin su, shi ne teamlead ɗin group ɗin su collective work ne kowa ya turo nashi shi zai yi final compilation sun turo mishi ta email ɗin shi Mrs Susan da Kevin ne suka turo ya gama aikin ya tura a flash ya goge wanda suka turo mishi wayarshi tayi ƙara ya tashi ya shiga ɗaki, yana tashi Umaima ta fito daga ɗaki da plate a hannun ta ta kalli computer ɗin shi da flash a jiki ta cire flash ɗin ya riƙe tayi dariya ta ji footsteps ɗin shi yana tahowa sai da ya kusa ƙarasowa ta ɗaga mishi flash ɗin tace "do me I do you." ta taka da gudu ɗaki da Zafin nama ya bi bayanta ta faɗa toilet da gudu ta saka a toilet ta danna flushing ya shigo kawai ya ga abunda ta yi ai sai yayi kanta kamar mayunwacin zaki, "how dare you." ya haɗa ta da bango jijiyar kan shi ta tashi, "I said how dare you? Baki da hankali?" ta kalle shi a sama tace "au ashe kana Hausa." ta faɗa numfashita na sama da ƙasa, wata zuciyar tace ba ka ce zaka yi ignoring ɗin ta ba kar fah ka yi kisan kai ya cika ta ya fito idan shi har rufewa yake yi baya ganin gaban shi sosai ya shiga ɗakin shi ya banko kofa.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣1️⃣
Fahad be san irin ɗaɗewar da yayi a kwance ba sai da ya kalli agogo ya ga time ya ja sosai, Astagfullah tun dazu da ya shigo ɗaki yake kwance shi kan shi be san me ya ke damun shi ba kan shi yaji yana mishi mugun ciwo ya rasa ta inda ma zai fara, Wannnan yarinyar ta cuce shi ya yunƙura zai tashi jiri ya kwashe shi ya koma ya kwanta sai ji yayi kamar ana juya shi ga jikin shi kamar temperature ɗin shi ta canja "ya Allah." ya faɗa, wayar shi tayi ringing ba zai iya daga wayar kowa ba a halin da yake ciki bakin shi har wani daci ya ke yi kamar wanda ya tashi daga zazzaɓi, gashi gobe dole zai yi submitting aikin at this point ma yayi regretting shiga harkarta koda yake ba harkar ta ya shiga ba ita take shiga rayuwar shi circumstance ne yasa dole ya kula ta, sun yi akan mage sun yi akan keke, ta tara mishi yara ta yi abubuwan da dole ya tsawatar mata amma zai kyale ta da halinta idan su Daddy sun gaji da zamanta a haka za su raba auren don wannan auren ba shi da wata manufa, ya shafa kan shi ya daure ya miƙe ana bin shi salloli ya shiga toilet ya ɗauro Alwala sallar ma a zaune yayi ta saboda ciwon da kanshi ke masa, yana idarwa ya tashi da sauri yana kakarin amai, aman ya ƙi fitowa ya dawo ya kwanta yana mayar da numfashi.
~~~~~
Al-NUZHA SAUDIA
Tahir ne a zaune yana kallon Aljaxeera News yana yiwa Allah godiya iran tana ta samun Nasara akan muguwar ƙasar Isra'ila ( Allah ya cigaba da bawa musulunci rinjaye ) Tun da aka kawo shi Saudiya rai a hannun Allah ya daɗe a Asibitin Saudi-German a kwance yana ganin Dr Mehdi abokin Dr Huzaifa shi ya rinƙa monitoring heart problem ɗin shi, Alhamdulillah ya warware sosai sai dai ciwon daya ke zuciyar shi har abada ba zai taɓa warkewa ba, har yanzu idan ya tuno Khadija tana can tana rayuwa da wani ranar haka zai yini cikin baƙin ciki da damuwa idan ya matsawa kan shi da tunani kuma sai ya sha magani.
Bayan ya samu sauƙi ya buƙaci zama a SAUDIA Ummi bata so ba amma ya nuna ya fi son hakan da taimakon Abokin mahaifin shi wanda Sau'udi ne (ɗan ƙasa) aka yi mishi igamah (shaidar zaman ƙasa), yaso samun matsala da igamar sa wajen siyan gida dan Abokin mahaifin shi Abdul'azeez ibn Talal da asalin sunan Abiy ɗin shi (Fadoul A Muhammad) yayi masa igama da taimakon shi da taimakon Allah ya samu ya siyi gida ya kuma buɗe mall a Suk Al-Alawi Street, da kan shi yake managing wajen kuma sosai Allah ya sawa kasuwancin albarka, Gidan su na Lebanon babu kowa ciki Ummi ta koma gidan Yaseer da zama, saidai tana yawan zuwa ta ganshi.
Tahir sosai ya ke ibadah kullum yana harami ya kan ce shi rayuwar shi sai dai fatan gamawa da duniya lafiya amma maganar Aure babu, sosai Ummi ta damu yayi aure yace mata zai yi idan ya samu matar, kawai faɗa mata yake yi dan hankalin ta ya kwanta amma mace ɗaya yaso a duniya Allah ya ƙaddara rabuwar su, zuwa yanzu kuma ya fauwallawa Allah duk yadda ya tsara mishi dai dai ne.
Wayar shi ce tayi ƙara Akhi Yaseer suka gaisa cikin harshen su na larabci yace ya je family house ɗin su jiya gidan ya lalace yana buƙatar gyara har ya bada iznin a fara gyaran, "ya kamata ka yi ƙoƙari ka dawo haka." Yaseer ya faɗa, ya nisa ya ce "kana ganin zan iya rayuwa a Lebanon yanzu?"
"Meyasa ka ce haka? Idan ina Lebanon ina tunanin abubuwa dayawa related to khadija. Yaseer ya katse shi da cewa "Khadija khadija Khadijah dai ka haƙura haka dan Allah." ai na haƙura amma akhi zama na anan ya fi min kwanciyar hankali." "meyasa zaman Lebanon zai tuna maka khadija?
Saboda tunaninta ne na yi accident na kwanta asibiti for years, tare da ku muka tafi Nigeria, sai yayi shiru, abunka da farin mutum fuskantar shi har tayi jawur ya fara tari, "I'm sorry for that." Yaseer ya faɗa, suka yi sallama ya buɗe bottle water ya sha ruwa ya canja channel Zuwa saudi Qur'an ya ƙara volume ana ta dawafi ya rufe idon shi yana bin karatun har ya ji yanayin shi ya daidaita.
******
Ammina Umaimah ta ɗaga kiran da sauri, "Ammina ina kwana." ta amsa ta suka gaisa ta yi switching vedio call, Umaimah ta riƙe baki "Ammina ya naga kin rame? Khadija ta yi murmushi tace "ke kuma kin yi kiba." ta yi dariya "ya mai jikin? Ammi kullum sai na kiraki bana samun ki kuma idan na tura miki Vnote ba kya buɗewa." Ta faɗa a sangarce, "toh ayi min afuwa, rashin samu na kinsan mu na Asibiti network ɗin ba shi da karfi da sassafe nake fita Asibiti sai dare na dawo gida, messages kuwa bana buɗewa saboda rashin lokaci,." "toh Ammi ya jikin nashi?
Alhamdulillah an sallame mu ma mun dawo gida. Allah ya ƙara sauƙi.
"Ammi." ki bashi mu gaisa. "yana bacci ya sha magani ne."
"toh dan Allah ki faɗa mishi ina gaishe shi, Ammina ina son faɗa miki wlh ina samun alheri ciniki nake yi sosai ni da wata ce shago zan buɗe a nan turawan nan suna min ciniki sosai, jiya fah na siyar da ruguna 12."
Khadijah tace "masha Allah... Allah ya sawa nema albarka, bani hankalin ki nan magana zamu yi."
"zoh ta gyara zama."
"Fatima! Khadija ta kira ta da sunanta na gaskiya "bana jin daɗin rashin sirrin ki a matsayin ki na matar aure haba Fatima abu ya faru tsakanin ki da mijin ki meye na kawo shi duniya har ki buɗe group ki yi mishi terere?" Ammi me na yi? "Maganar magenki sabida mage ki tara mishi mutane kin kyauta? Duk macen kirki bata kai kara yau ko ke aka zalunta ki yi hakuri zai wuce watarana sai labari na faɗa miki wani abu? Zaɓin iyaye ko baka so ka bi wlh saboda biyayyar nan sai ki ga Allah ya miki wata baiwa ko ta yara masu albarka ko ta shi kan shi mijin bana son ki maimaita kuskuren dana yi a baya, ba zan boye miki ba wannan haɗa shi da iyayen shi da kika yi kin ɗauko hanyar dasa tsanar ki ne a zuciyar shi, Fatima lokacin da na auri mahaifi ki na fi ki karancin shekaru amma na fi ki sanin ciwon kaina abubuwa da dama sun faru wlh babu wanda na faɗawa sai da Munnirah ta dawo daga tafiya kuma har yau ni da su Umma nace an yi kaza da kaza ban taɓa ba shi ciki ba don cin abinchi kawai aka yi shi ba harda ɓoye sirri, kuma kowacce magana akwai Abokin yinta Fatima ga yar uwar ki nan Amira idan kina neman shawara ki neme ta mana zata rufa miki asiri zata baki shawara ni ina tausayin Yaya Dattijon wlh har yanzu ace baki da hankali."
Jikin Umaimah yayi sanyi tace "Ammi wlh nima gasa ni yake yi dan baki san me yake min ba."
"ban sani ba kuma bana son na sani mutum me tsabta an haɗa shi da ke nasan har yanzu kina nan kina taɓa ƙazanta."
"Allah Ammi ina ƙoƙari fah yanzu."
"ok nuna min ɗakin ki." ta juya camera ta nuna mata, babu laifi gadon a gyare yake amma pieces ɗin ɗinkin data gama ɗazu duka a kasa bata kwashe ba, Khadija ta shiga tunani tasan tun a gida Umma suna faɗa da ita akan tara panties sai ta saka su kakaf sannan ta jika ta wanke a baza su duka a Toilet su yi ta faɗa da Umma. "Kin gani ko Ammi?" ta katseta daga tunanin da take yi tace "naji nuna min toilet." Umaima da saurinta ta tashi ɗazu data yi wanka ta sake wanke toilet ɗin, ai kuwa sai ga panties kaya guda sun fi 20 ta wanke su ta shanya, hali zanen dutse Khadija ta faɗa a ranta, sai kuma tace "dan Allah idan kin yi wanka tare ake wanke panties, Dan Allah do this for me da safe ki rinka gaishe da mijin ki a rinƙa tsabta, Dan Allah ki kula da Tarbiyyar Ãdil banda shiririta na sanki ki rinƙa dafawa Mijin ki abinci ta nan nasan ba ki da kasala, i know you make the best coppee kila ma ba ki taɓa haɗa mishi ba, da Allah Fatima ki gyara soon you will be a mother."
"Amira ma is pregnant Ammi." ta faɗa da sauri, "to kin gani wata rana kece." ta rufe ido Ammi nima fah baya kyauta min. Khadija tace ya taɓa zagin ki? Ta girgiza Kai, ya taɓa dukan ki? Ta girgiza Kai ya taɓa hana ki Abinci?tace "a'a Ammi."
Idon Khadijah ya tara ruwa da ta tuna yadda Tahir ya kwashe kayan abinci, tuna shi sai da hawaye ya zubo mata, Umaimah jikinta a sanyaye tace Ammi nina saki kuka? zan gyara ki yi haƙuri. Khadija ta yi murmushi ta girgiza Kai ba ke bace Allah yayi miki Albarka sai anjima suka ajiye wayar.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣2️⃣
Jikinta yayi sanyi sosai sai ta ji nadamar abunda ta yi masa ɗazu.
Tana tsaye a falo ya fito ta ji tsoro amma sai ta dake suka haɗa ido ya ɗauke kai be ce mata komai ba jikin ta a sanyaye ta koma ɗaki ga dukkan alamu ma kamar bashi da lafiya to amma ai shi yayi mata mugunta idan ba zai shiga sabgarta ba babu abunda zai haɗa su balle su yi faɗa ta dade sosai a daki har bayan la'asar ta fito Falon ta zauna ta ɗauko wayarta tayi posting kayan sanarta a Instagram wani blogger yayi posting wani labarin abun dariya na Uwar ɗaki da almajirin ta yayi rashin lafiya tace saita yi masa wanka yayi dauɗa da yawa ashe gardi ne jikin shi ne ƙarmi, Umaima ta rinka dariyar labarin, nan ta shiriri ce ta manta da damuwarta ashe tun lokacin data fara dariyar ya fito ya zauna yana jiran colleague ɗin shi Mrs Susan zata zo duba shi ya tsaya yana kallon ta har ta farga ta tashi ta sunkuyar dakai tace "ummm ummm.....dama ina son baka hakuri don Allah ka yi hakuri."
"it's okay." kawai ya ce mata ta tashi ta koma ɗaki tana shiga kira ya shigo wayar ta masu karɓar order ne ba a fi minti 15 ba suka ƙaraso ta fito zata basu kayan suka haɗu da shi suna sallama da Mrs Susan she caught him unaware kawai ta yi hugging ɗin shi idon Umaima a kan su taji wani abu yaɗan tsaya mata a wuya kamar ɓacin rai sai kuma ta ɗauke kanta da sauri a ranta tace wannan mutumin har rungumar mace yake yi lalle ɗan duniya ne ashe ya rinƙa wani basarwa kamar na Allah, fuuu ta wuce shi ta kai saƙo ta dawo ta ga yana kallon ta sum sum ta wuce da kuɗinta a hannu tana murna "kai Allah ya tsinewa talauci da magoya bayan shi." ta faɗa tana juyi.
Washegari
Papa why are you laying down? Ãdil ya tambaye shi, daga kwancen yace "I'm not feeling fine." Oh sorry Papa hard luck. "thank you Didi."
Papa have you eaten? No Didi. But why? Ãdil ya sake tambayar shi, "don't have appetite. You have to eat something. Fahad yayi murmushi wato shi yaro duk abunda ka yi yana kula sak treatment ɗin da yake bashi kenan idan bashi da lafiya, his feeling much better ba ƙaramin burden Mrs Susan ta sauke mishi ba na completing aikin da ta karba zata yi ba, amma be ji daɗin hugging ɗin shi data yi ba yarinyar nan sai ta fassara shi anyway Allah ya gani is not intentional, duk daya dade a Turai sam baya rayuwa irin tasu saɓanin wasu mutanen mu da sai su canja dabi'un su, "Papa you are sweating." Ãdil ya faɗa yana shafa mishi fuska, "why are you sweating? Because I'm feeling much better Didi."
"should I on the Ac? Yes Didi.
Surutun shi ya dame shi amma baya son korar shi kar ya ji babu daɗi, ya dauko remote ya danna ya ja blanket ya rufa mishi yace "I'm coming Papa." ya fita.
Shigowar Ãdil ne yasa Umaima ta yiwa Sadiq sallama Sun dade suna magana tana mishi godiyar karamcin cousin din shi Ramla, ta buɗe hannayenta ya zo tayi hugging ɗin shi "Maamah Papa baya fine."
Tayi murmushin maganar shi "good job, bashi da lafiya zaka ce." yana ƙoƙarin yin magana da Hausa, "toh muje mu daura mishi abinci.
Ta debo potatoes ta fere ta ɗauko liver a fridge tayi potatoes porriage sai maganar Ammi ta faɗo mata akwai coffee maker ta haɗa mishi hmm Ãdil ya shaƙi kamshin girki "zan ci Maamah." ya faɗa, ta dora shi a kitchen island ta zuba mishi ta haɗa tray ɗin Fahad suka fito tana riƙe da tray ɗin ya buɗe ƙofar ta shiga ta ajiye mishi "nagode." ya faɗa, ta yi murmushi gara dai ta tsaya a lane ɗin ta wannan mutumin kuli kuli ne bashi da gaba amma duk abunda Ammi ta faɗa mata zata gyara in sha Allah.
Papa get up and eat Maamah made it for you with love. Fahad ya kalli shi wannan yaro wayon shi yayi yawa ga maganar tsiya kamar Sa'ad ne ya haife shi, ya tuna sau da dama idan bashi da lafiya duk abinda ya kawo mishi yana cewa he made it with love shi ne shima yake faɗa mishi, yayi mishi wayo yace ya sha magani ne ba zai ci abinci yanzu ba sai nan da 6hours ya san time ɗin yayi bacci. "okay Papa." ya faɗa, sai kuma ya tashi ya fita ba a daɗe ba ya dawo da story books a hannu shi, yace "choose one Papa? I wanna read it for you."
"any one Didi."
"okay" ya ɗauko the tale of peter Rabbit ya fara once upon a time .........ya gyara mishi kwanciya a jikin shi tuni bacci ya ɗauke shi littafin ya faɗi ƙasa, ya tashi ya fitar da abincin data kawo mishi ko buɗewa be yi ba, shi yaushe zai ci abincin ta ya shiga toilet yayi wanka ya fito yayi shafa'i da wuti ya kwanta.
Tunda Amminta ta yi mata faɗa ta gyara sosai da safe zata fito su gaisa zai dai ce mata fine shikenan zata yi breakfast ta ɗora a Dinning lunch ne bata yi dashi don baya gida sai dinner ta kan ce sadaƙa take bashi be taɓa ci ba kuma bata damu ba sai daga baya ya faɗawa Adil ya faɗa mata ta daina girki da shi, shike nan tin daga lokacin ta daina, ta daina zaman falo iyaka cinta kitchen data gama tayi shigewar ta daki, kasuwancin ta shi yake debe mata kewa sosai ta ke haɗa kan yan canjinta shi ya ɗauke mata hankali, amma tana tunanin ita kenan ba zata samu ciki ba kenan? Wannan ya saka har tashin dare take tana rokon Allah ya kawo mata mafita, abunda bata damu dashi ba ke nan, a gida sai Umma tayi mata gorin bata ganin Amira tana kiyamullaili bata da bukata ne a wajen Allah?sai dai ta yaye baki tayi ta bacci su yi ta faɗa ashe lokacin zai zo da zatayi da kanta.
Shi kadai ya ke tunani a office yarinyar nan ya ga kwana biyu ta yi sanyi ya ga changes sosai kar dai ya matsa mata ne shi baya son mutum a takure kullum tana ɗaki kar wani abun ya same ta, mtsw yayi tsaki haka kawai yana zaman shi lafiya an haɗa shi da wani aure kai dole zai neme ta zai bata offer su rabu kwai Allah ya sa ta bashi haɗin kai.
💫 UMAYMAH 💫
✍️A&A PEN
Follow our Whatsapp group via this link https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3
https://wa.me/+2348039352724
Volume two
EPISODE 2️⃣3️⃣
Jikin ta a sanyaye tayi wanka tana fitowa tasa Purple ɗin riga da wando na Pakistan mai white veil bata bi takan mayafin ba, ta fito falo ta zauna ta zabga uban tagumi, gaba ɗaya bata jin daɗin yanayin ta tin jiya da Amira ta kirata tana mata tsiyar tana da ciki ga faɗan da Amminta tayi mata gaba ɗaya komai ya tsaya mata, komai ma yanzu sai taji baya mata daɗi. She have been thinking about her life, shi ke nan ita rayuwar ta haka zata ƙare she don't have any plans or future. Babu wani ci gaba daga gida zuwa gidan Miji, she loves child, she wants to be a real mother. But how? Ta tambayi kanta, ta duba wayarta taga date ɗin Auran su yanzu is almost 6 months but nothing change.The way Amira suke rayuwa da Sa'ad suke treating juna sincerely speaking suna burgeta, "but how could she achieve all this things? You are a married woman and your husband is around you." Wata zuciyar ta bata amsa, "husband." Ta maimaita ƙasa ƙasa ta gyara zama, taci gaba da tunani.
Tana cikin tunanin suka dawo daga fitar da su kayi tin safe, Ãdil ya taho wajen ta da gudu yana kiran "Maamah I'm back home and i bought something sweet for you." Yayi maganar yana ciro abu daga leda, sai lokacin ta kula dasu sam bata ji shigowar suba. Mood ɗin ta very low tayiwa Ãdil smiling, ya bata chocolate ɗin daya siyo mata ta karɓa tayi hugging nashi muryar ta very calm kamar ba Umaimah ba tace "thank you my darling."
"Maamah hope you like it?" Wani murmushin jin daɗi tayi tana kallon shi tace "yes my love." Yayi ihun murna yace "Papa i told you she will like it, i love you Maamah." Umaimah taja hancinshi tace "I love you too Didi."
Fahad dake tsaye yana kallon su haka kawai sai yaji wani abu kamar tausayin ta ya ɗan taɓa shi, the way she talks to him kasan naturally tana son yara, but he don't knows what happened to her kwana biyun nan tayi silent da yawa babu karaɗi babu neman magana, "is he the reason of her moods?" Ya tambayi kanshi.
Tunanin ya ajiye ya cewa Ãdil "Let go and shower is time for your siesta." Ya kama hannun shi yana waving Umaimah suka shige ciki, yana yi masa wanka yana tunanin shawarar daya yanke kawai zai sameta suyi magana.
Tana nan a zaune ya sake fitowa ya shiga kitchen ya haɗa coffee ya dawo falon bata sani ba tayi nisa a cikin tunani, ya kalleta da kyau, "kome ke damunta you are responsible for it." Mindset ɗin shi ya faɗa mishi haka, har ya zauna a kujerar dafe facing ɗin ta bata kula ba.
"Hi."
Yayi mata magana, firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi, ya sake kallon ta da kyau yayi sipping coffee ɗin shi, without his permission yaji bakin shi na furta "are you okay?"
Umaimah ta juya cikin falon tana kalle kalle kamar me neman wani abu sai kuma ta dawo da hankalin ta kanshi ta nuna kanta tace "Are You talking to me?"
Yadda tayi maganar with full of surprise yaso sashi smiling sai kuma ya maze with full of class yace "yeah, what's your problem, ahm i mean what happened to you?"
"Hmmm nothing am perfectly fine Alhamdulillah."
"Okay, Please let's talk."
"Hmmmm."
Ta gyara zama akan jujerar ta wani juya masa baya, ya kalle ta ya girgiza kai, very calm and matured yace" Well I think we need to discuss some issues. sai ya gyara zama ya kalle ta ya ɗauke kai, wayar shi ta yi ringing ya tashi "excuse me." ya faɗa, ya shiga ɗaki ba a ɗauki lokaci ba ya dawo da cheque a hannun shi ya zauna ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yace "yes as I was saying, staying together as couples doesn't make any sense so
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 27