Share this page
shirya za'ayi wani drama to entertain the kids Amma ba'asan wa zai yi role ɗin male and the female lead ɗin ba, Salmah ta ce ita da Amreesh za suyi, aiko yaran sun yi farin ciki, Amreesh da Beta ɓa wani acting ba sai gashi a stage da kuma wasu daga cikin ma'aikatan wurin, sosai dramar ta ƙayatar da yaran da kuma masu kallon Duk da Amreesh through out the drama idanun sa na akan Salmah he wasn't focusing mutane sunyi noticing and it makes them wonder ko meye alaƙar su? Bayan an gama Salmah excused her self taje bayi ta fito kenan sai ga wata yarinya riƙe da takar da, murmushi Salmah tayi ma yarinyar ita ma yarinyar sai tayi murmushin har dimples ɗinta na lotsawa, Salmah ta rage tsawon ta to the girls height tace '' meye sunan ki?" Yarinyar da bazata wuce shekara biyar ba tace '' A'isha, amma ana kirana da noor'' bayan tagams faɗin haka ta miƙa ma Salma takardar tace ''wani yace in baki'' karɓar takardar Salmah tayi tace'' waya ce ki bani?" A'ishah tace '' bai faɗamin sunan sa ba'' jinjina kanta Salmah tayi tace ''toh na gode Noor'' yarinyar tayi murmushi kafin tabar wurin,buɗe takar dar Salmah tayi wondering ko daga wane oho, abinda aka rubuta a takardar "𝐴𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠" _𝑇ℎ𝑒 𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡 𝑑𝑜𝑤𝑛 𝑤𝑖𝑙𝑙 𝑠𝑜𝑜𝑛 𝑏𝑒𝑔𝑖𝑛,𝑏𝑒 𝑟𝑒𝑎𝑑𝑦 𝑦𝑜𝑢𝑛 𝑚𝑖𝑠𝑠_😼 𝑌𝑜𝑢𝑟𝑠 𝑠𝑖𝑛𝑐𝑒𝑟𝑒𝑙𝑦: 𝐴𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠😁 Salmah ta juya kalaman cikin kanta,amma ta kasa gane ma'anar su,hakan yasa she concluded ƙila ba ita ake nufi ba, tura paper tayi cikin aljihun wandon ta amma sai paper ta faɗi ba tare da ta sani ba. Tana shigowa hall ɗin Amreesh yazo ya riƙe hannun ta yace '' ina kika tafi?'' murmushi tayi tana jan kumatun shi tace ''cant stay a moment without ur wife huh?" Ganin abinda ke faruwa ya ƙara ba mutane mamaki they really want to know meye alaƙar su, the rest of the day went by quickly ɗaukar photo suke here and there, sai wurin isha'i suka bar gidan marayun yaran nata roƙon su akan su dawo wata rana, Salmah tace ''zamu dawo Insha Allah '' bayan Nan suka rakasu har mota suna musu bye har suka fita daga orphanage ɗin. Salmah sai murmushi take kamar bakin ta zai faɗi tace '' aren't the kids so cute?" Jinjina kansa Amreesh yayi,still driving yace '' lets make kids tonight '' wata irin kunya ta kama Salmah ta ɓoye fuskar ta tana dariya tace '' kai dan Allah '' yace ''did i say anything wrong '' ya faɗa yana kallon ta cuz sun kawo traffic,Bata tanka masa ba.... Ranaku sun ta tafiya har yau yakai tsawon wata guda da Salmah suka tafi gidan marayun, tsakanin ta da Amreesh wata irin shaƙuwa ce, su biyun suke nuna ma juna ƙauna da kuma kula da juna, koda yaushe suna cikin farin ciki, ki manne da juna, at every chance sai Salmah ta ɗauki hoto, ita har tama manta da paper da ta amsa a gidan marayun nan, their lives were perfect and it makes her wonder da gaske rayuwa da kuma soyayya zasu iya kasance wa batare da wani kalubale ba? Wannan idan tayi tunanin zuciyar ta na wani kaɗawa, she feels kamar sai sun jiƙu da so da ƙaunar juna kafin ƙaddara take it's own course to Amma what's in store? No one knows the future right? Ganin tunanin bazai haifar mata da ɗa mai ido ba yasa ta ture sa gefe ta fuskanci rayuwar su..... A ɓangaren Dr Ahmad kuma kullum sai sunyi waya da Samha sannan ga wani irin sonta da begen ta da yake, Dr Haleema da Dr Ameenah sun dage shooting their shots Amma har yanzu basu yi nasara ba, not that Dr Ameenah tana tai makon Dr Haleema ne dan Allah sai dai dan wata manufar tata. Samha kuma ta zama wata irin star a ELITE ACADEMY kowa yasan Samha especially idan akace sam the rule breaker, kusan ko da yaushe sai an tura Samha detention for breaking one rule or the other Amma bata zuwa,sai taita raɓe raɓe kada su haɗu da mr kanya da take kira da mr giant, Sulale wa take, tayi ta zagaya makarantar,idan ta gaji ta koma hostel tai ta laftar Bacci, Amma duk da haka Samha na da ƙoƙari kusan kowane teacher yasan ta and they like her alot, Bata copying note,tun lokacin da suka zama abokai da Adrian shike mata note, shi har cikin zuciyarsa son Samha yake, and idan yan ajin su suna zagin ta behind her back he always stood up for her hakan yasa, Samha Akwai farin jini Akwai maƙiya kwando kwando, Dark flames sun wani kwanta kwana biyu yanzu sun koma ga sauran daliban,badan sun ajiye ƙudirin su game da Samha ba, rather sun canja taku,yanzu main target ɗin su Ra'esah da fateemah saboda sun ga yanda samha take son su, their friendship has blossom into something beautiful sun zama kamar yan uku,ako da yaushe suna tare, idan zaka ga Samha to zakaga Ra'esah da fateemah. Zeenah da Lucy suma suna nan suna shirya nasu tuggu, ita zeenah dan Ahmad Lucy dan Adrian su kuma sauran biyar ɗin wato ƙawayen su dan baƙar mugun ta da hasada kawai. 04:30 Samha ce ke tafiya cikin hostel ɗin su tana murmushi,yanzu suka gama magana da Ahmad and she just discovered Ahmad da Amreesh ashe cousins ne and his full name is DR AHMAD ALIYU ZAKEE, maman Ahmad da Amreesh twins ne,sai kuma baban su wa da ƙane ne, wannan discovery Saboda wata Sunday Samha na zagaya makarantar da yamma suka haɗu da Adrian he was wearing a white t shirt and a pair black trouser '' Hi'' ya faɗa nervously juyowa Samha tayi da murmushi tace '' oh mai kan taliya, how are you?" Ya ɗan ɓata fuska yace ta dena kiran shi mai kan taliya yasan abinda hakan ke nufi tace '' toh ai idan na kalli blonde hair ɗin ka taliya nake tunawa ''duk wannan maganar suna yi suna tafiya ne,Saida suka ɗanyi nisa sun kawo ƙarƙashin wani Cherry blossom 🌸 🌼 Adrian yace su zauna wurin,zama sukayi kuwa the weather was so nice iskan dake kaɗawa? It was almost December,tun da suka zauna Adrian ke ta mutsu mutsu alamun yana so yace wani abu but he didn't know how, noticing ɗin hakan yasa Samha tace '' You've got something to tell me?" Jinjina kansa yayi yana shafa ƙeyarsa, nervously his green eyes slightly wide, ya sauko saman guiwar sa ya fito da rose daga cikin aljihun wandon sa yace'' I don't know when it begun,but I think I like you! Ina taso in faɗa maki Amma bansan Taya ba,i finally gathered the courage today Samha, I love u so much '' tun da ya fara magana Samha ke kallon sa she felt bad for him, shiko Adrian he was dying to hear her answer,bugun zuciyar sa ya ƙaru,tsoro slowly settling in it. Tace '' tashi'' miƙewa yayi, itama ta tashi, ta ɗan tsaya kusa dashi,he was taller than her ahankali tace '' I appreciate ur love Eddie,Amma kayi haƙuri inada wanda nake so, I can't accept your love'' jin hakan yasa sanyin yamma ya bugi Adrian hard, it was chillier than usual, zuciyar sa kamar zata faɗo, maƙogaron shi sai kai kawo yake, ahankali yayi dropping ɗin hannunsa dake riƙe da rose ɗin yace ''Oh,i was lately tace '' I'm sorry '' ''it's not your fault '' ya faɗi hakan kanshi na kallon ƙasa, Samha felt bad for him. Bayan wani lokaci yace ''who is this lucky person?"da murmushi a fuskar ta Tace '' Dr, sunan sa Dr Ahmad '' jinjina kansa Adrian yayi'' and his last name ?" Samha tace '' I don't know '' ya sake faɗin ''baki sanshi da kyau ba, ki ƙara sanin shi before getting into a relationship '' jinjina kanta Samha tayi tana faɗin ''thank you'' after a while Matso wa yayi ya laƙa mata rose 🌹 ɗin a gefen kunnen ta,ƙamshin ta na shiga hancinsa kamar yanda nasa ke shiga nata '' keep the rose,it suits you '' yayi whispering a kunnen ta kafin ya juya ya bar wurin Tabi bayan sa da kallo. Abinda ya faɗa mata na yawo akan ta, hakan yasa yau ta kira Dr Ahmad tana ta suburbuɗo masa tambayoyi har ta kai ga sanin alaƙar su da Amreesh,da ta ɗauka friends NE su. Tayi nisa sosai da hostel ɗin su, taga Lucy, zeenah, Kathy, Amarachi, Hauwa,Maryam da Ameerah tsaye gaban ta da sharɓa sharɓan buloli wanda idan aka yiwa mutum guda sai buzun shi, she wondered ko ina suka samo waɗannan bulolin? Bata da amsar wannan tambaya, But one thing is for sure, those whips were meant for her...... WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17 Chapter twenty one: the punishment Idanun Samha sun wani ƙara girma kallon tsakanin bulalen da kuma waɗan da ke riƙe dasu, damn!! Gara tayi ta kanta yanzu ba lokacin zama heroine bane, da'ace babu waɗannan sheɗanun abubuwan a hannunsu, perhaps da ta tsaya sun kece raini, amma yanzu..... Ganin sun kusa cimma ta yasa samha tattare doguwar rigar ta, ta kwasa da gudu suma ganin haka yasa sun fara Binta a 380 Ita Samha abun gabaki ɗaya dariya ma yake bata,wai itace zaratan yan mata guda bakwai ke bi da bulala da zummar zasu zane ta, Sun ƙara yin nisa sosai da hostel har sun fara gajiya, itama Samha ta gaji it has been long since she ran like that, ƙarƙashin wani bishiya ta tsaya tana haki,suma iske ta sukayi suna Faman haki Zee ta miƙe tana nuna Samha da bulalar ta, tace '' dan ubanki yau zaki yi bayani,shegiya mayya'' Lucy ma tace '' wato harda su sa Adrian yayi confessing yana sonki ko? Zaki gane kuren ki'' Maryam da su Ameerah ma sai tofa albarkacin bakinsu suke suna zagin Samha tare da threatening ɗin ta akan yau sai da wata ba ita ba. Samha ko sai kallon su take tana ƙoƙarin ɓoye murmushinta,just now tayi diverting ɗin sune daga inda mutane suke,saboda idan ta fara basu tarbiyya (kashi) kada arabasu. Bayan sun gama jawabin su,they expected that Samha would look scared but to their dismay sai suka ga Samha ta ƙyalƙyace da dariya Sai da tagama sannan tace '' toh ku Yanzu Saboda jakanci shine zaku wani biyo NI har nan wai zaku buge Ni Ko?" Sai da tayi maganar suka fara noticing Ashe sun yi nesa da makaranta. Sun kusa shiga daji, kallon kallo sukayi ma juna sai kuma Maryam tace '' perfect yanzu zamu ci ubanki la'ada waje'' wani kallo Samha tayi ma Maryam kafin ta kalli sauran They all looked angry kamar zasu haɗiye ta,jin jina kanta tayi tace '' zee, kinsan na taɓa faɗa maki,ki faɗa ma ƙawayen ki su dena shiga what's in between me and you idan ba haka ba i will break their bones and their will be no evidence to support cewa nice na karya su ko?'' Samha tayi maganar da murmushi a fuskar ta, idanun ta har wani ƙyalli suke Zee da su Lucy suka kalli juna obviously maganar ta ta basu tsoro amma suka dake after all Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi, Samha taci gaba da faɗin '' yau ne ranar'' Amarachi tace ''baki da hankali,ki kalli yawan mu ki kalle ki ke kaɗai and you're still making mouth '' Zeenah tace '' ku ci ubanta '' tana faɗar haka dukan su,suka yo gaba, da sauri Samha tayi tsalle ta riƙe wani reshe (branch) daga bishiyar da suke ƙarƙashi, Ta ɗaga ƙafafun ta, ta halbe Ameerah dake gaba a fuska, Ameerah ta saki ihu tana dafe fuskar ta Ga baki ɗayan su they were momentarily stunned Hakan yasa Samha ta diro,sannan ta jawo Zee ganin hakan yasa sauran fara shaulo bulolin su, Samha tayi amfani da zee' a matsayin shield Maimakon bulalar ta samu Samha sai ta dinga samun xee, Zee sai ihu take tana faɗin '' kutsa ya, wayyo Allah na'' bulalar ta kai mata karo wallahi, fuskar ta tayi ja, Tura ta Samha tayi,zee tayi gaba ta faɗa ma sauran dake bayan ta,dukan su, su bakwai sai gasu a ƙasa Samha tayi amfani da wannan damar ta ɗauki bulolin da suka zo dasu, kafin su iya miƙewa, Samha ta fara basu tarbiyya Sai ihu suke ƙwalawa azo a taimake su, but they were far from the school Samha tace '' Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi,true ,but In this case Sarkin ƙarfi yafi Sarkin yawa'' Samha tana magana tana bugun su ta ko'ina duk sunyi jage jage da hawaye Wayar ta, ta ciro ta ɗauke su hoto making sure fuskokinsu sun fito tayi captioning ''#school belles beating to a pulp by the unknown " sannan tayi posting a school blog anonymously Ta gama bugun su ta tsaya tana kallon su one by one sannan ta tuntsire da dariya tace '' next time ku sake biyoni,ku baku san da cewa Ni ɗin nan i love fighting so much, Saboda daga karshe nice a sama,kunga yan......'' kalamanta sun katse lokacin da ta hango mr giant (Mr kanya) yana doso inda suke,waro ido tayi tace mr giant na tafe fa,hankalin su Zee ya matuƙar tashi, he has punished them once yanzu kuma basu marmarin ya sake hukunta su.... Ƙoƙarin tashi suke su bar wurin Samha tace '' ai bazai yiwu ba'' tana gama faɗin haka,ta ɗauki bulolin ta ƙara masu atleast biyar biyar,sai ihu suke,ganin mr kanya ya kusa ƙarasowa Ta maza ta sama kowa bulalar sa a hannun sa, idan kagan yanda tayi musu zaka ɗauka faɗa sukayi da juna. Kafin mr kanya ya iso wurin,samha ta shige cikin dajin ta yanki hanyar da zai maida ita makaranta directly. Su xee ko ba abinda zuciyoyin su suke in ba tafasa ba. The girl is a devil's incarnate,sun yi nadamar biyo ta.instead of beating her to a pulp they got beaten up Mr kanya ya ƙara so wurin yana kallon su sternly yace'' what's going on here?" Da sauri suka miƙe daga jikin juna dan har yanzu suna yanda Samha ta barsu ga wani azababben ciwon jiki da suke ji. Zee ce tayi masa bayanin abinda ya faru, Wani irin kallo yayi mata from head to toe sannan da Muryar ban tsoro yace ''You're very stupid,do you think I'm a fool? Duk yawan kun nan riɗa riɗa da ku,kuce wai wata karamar yarinya ta duke ku har haka? Toh ina yarinyar?" Maryam tace '' wallahi...'' ''shut up ur dirty mouth '' mr kanya ya daka mata tsawa,dukan su saida suka tsorata Yace '' wato iskancin ku ya kai ku bar makaranta Ku zo nan kuna faɗa ko? Lafiya tayi muku yawa'' dukan su a tsorace suke, yanzu gudun su Yace zai basu punishment duk sunyi tsuru tsuru da ido, Kathy, Lucy da zeenah jikin su da fuskokinsu sunyi jaa ga shatin buloli, that because su farare ne. Mr kanya ya gama ƙare masu kallo kafin yace '' your punishment is,zaku cika drum ɗin nan dake back yard for a whole week '' zaro idanu sukayi suna kallon juna, akwai nisa daga tap zuwa drum ɗin and it's huge Kathy tace '' Sir please don't.....'' yace '' your punishment is multiplied '' a gasp escaped their lips suka kalli Kathy with accusing eyes Tayi ƙasa da kanta. Mr kanya yace '' zan rufe idanuna idan na buɗe su nagan ku anan, You will serve for a month straight '' yana gama faɗar hakan ya rufe idanunsa da sauri suka fara gudu, every part of them itch.... Bayan ya buɗe idanun sa mr kanya yabi bayan su da kallo, apart of him believing what they said..... But no evidence *********************** Koda Samha ta koma ɗakin su it was 7 30 Ashe hanyar da ta bi nada nisa, Ra'esah da fateemah suna kallon ta sukace daga ina rule breaker? Dariya sukayi su dukan su kafin Samha tace '' wani aiki ne ya tsayar dani amma yanzu an gama '' tana gama faɗar hakan ya shige toilet Na'ema dake kwance saman gadon ta,tabi Samha da wani tsinannen kallo she really hates the girl, Ina ma zata samu ko da one opportunity ne..... Bada daɗe wa ba Samha ta fito, alwala tayi yazo tayi sallah tana nan zaune har aka kira sallar isha'i suka yi Sallah banda Na'ema. Bayan Samha ta tambayi meyasa bata yi Sallah ba tace '' mind ur business '' Jan bakin ta Samha tayi shiru Fateemah ganin tense atmosphere ɗin hostel ɗin tace '' muje cafeteria'' miƙewa sukayi da hijabban da suka yi Sallah suka nufi cafeteria Suna tafe suna wasa not minding dare ne, sanyi har ya sauko ga taurarin da suka ƙawata sama, the view was amazing Ra'esah ta nuna wani tauraro mai haske tace ''Samha kinga wancan tauraron?" Samha da Ra'esah suka kalli inda take nunawa suka ce su basu ga komai ba saida ta ta nuna musu sannan suka ce sun gani, Ra'esah ta dafe ƙirji tare da sauke ajiyar zuciya ta ce '' thank God '' Dariya suka sa su duka kafin tace '' ako da yaushe ina ganin kine kamar tauraron da yake haskawa yake kuma haskaka wanda ke tare dashi Samha,i never liked anyone the way I like you " Ra'esah ta ƙare maganar tana riƙe hannun Samha,itama Fateemah tace '' Yes samha,you're a shield that protect us from the storm, , U give us courage Sam, Muna matuƙar ƙaunar ki" Jawo su Samha tayi, and engulfed the three of them in a hug cike da ƙaunar juna kafin Samha tace '' nima ina ƙaunar ku sosai, I can't stand if something were to happen to you'' Sun daɗe a haka kafin suka rabu, Fateemah tace '' aga wa zai riga kaiwa'' aiko suka kwasa da gudu suna rige rige. Banko ƙofar cafeteria ɗin sukayi dukan su, suka zube ƙasa suna dariya, kowa ya zuba musu ido giving them weird looks especially saboda hijaban su,no one wears that... Su dai su Samha ba abinda ya dame su, miƙewa sukayi Ra'esah tace '' na riga'' ''wai ma na riga'' haka sukai ta gardama har suka samu wuri suka zauna, Samha taje counter ta karɓo musu abinci. Kowa ya maida hankali yana cin abinci some are busy chatting Samha ta karɓo abincin kenan ta kawo daidai wurin table ɗin wasu, ɗaya daga cikin yaran dake zaune a table ɗin ta saita ma Samha ƙafa ji kake' gwain gwain,tim!!" Duk abinda Samha ta karɓo ya kife ita ma Samha ta faɗi Wurin ya ɗauki shiru,all eyes on Samha da kuma yarinyar da ta taɗe ta, sai wani ciccin magani take Da sauri su Fateemah suka zo suka miƙar da Samha suna kakkaɓe ta '' kin ji ciwo?" Fateemah ta tambaya idanun ta na cikowa da hawaye, Ra'esah looked worried, girgiza kanta samha tayi sannan Samha ta kalli yarinyar Calmly tace '' baki ga kin ture Ni ba?" Yarinyar ta miƙe ta hayayya ƙo ma Samha da faɗa tana zagin ta sannan tace'' wallahi dan kinga kina ma mutane su ƙyale ki Ni in kin min cimaki uba zanyi'' sakaka Samha tayi tana kallon yarin yar, suma su Ra'esah sun yi mamakin jin yanda yarinyar ta wani bi tana zagin Samha ta zubda habaici... Over all mutanen cafeteria suma sunyi mamaki ,abinda ya fi basu mamaki the fact that Samha batace komai ba, dan sun san ba'a mata ta ƙyale.sai murmuring ake, a tunanin su ko Samha ta tsorata ne saboda yarinyar da ta taɗetan tana da tsawo ga ƙiba,in fact Samha ta bata suna 'giant number 2' dama tasan yarinyar Ra'esah da fateemah suka ja Samha suka bar wurin ita kuma yarinyar ta ɗauka tsoron ta suke sai cigaba da tujara take. Wani Abincin Fateemah ta karɓar musu, suka zauna suna ci suna hira kamar babu abinda ya faru, itako yarinyar har lokacin taƙi yin shiru ƙawayen ta sai zuga ta suke Soon sai ga dark flames sun shigo, sanye suke da wasu orange ɗin riguna da jeans dukan su, wurin yayi shiru kamar ba kowa wurin. Kusa da table ɗin su samha suka tafi suka zauna, Ra'esah da fateemah became tensed banda Samha. Bayan sun shigo sai gasu Lucy da zeenah su bakwai suma sun shigo, the atmosphere in the cafeteria became even more tensed Saboda yanda suke kallon Samha kamar zasu cinye ta ɗanya, itako yi tayi kamar bata San da ko ɗaya daga cikin groups ɗin a wurin ba. Table ɗin dark flames su zeenah suka zauna so their were eleven of them in total '' hi guys '' matan suka gaida mazan,da wani jin kai su kuma suka amsa abinci aka kawo masu,suna ci suna hira tsakanin su time to time suna kallon table ɗin su Samha Hauwa a fakaice tace '' the fight is not over '' Samha tasan da ita suke,she smirked she likes it, she doesn't want the fight to be over not yet Fateemah da Ra'esah tuni suka yi shiru suka cigaba da cin abincin su duk a takure kamar sauran ɗalibai Samha tace'' naga nawar in koma gida wallahi '' Ra'esah tace '' ai an kusa fara jarabawa '' Fateemah tace '' za mu yi kewar ki Sam '' Samha tace '' xamuyi exchanging ɗin address, ya Ahmad zai kawoni mu gaisa '' da gangan Samha ta kira Ahmad dan taba zee haushi and she succeeded Maganganun su,suka ci-gaba da yi while dark flames low key low key suke studying ɗin Ra'esah da fateemah, suma yaran suna da kyau Lashe bakin su sukayi exchanging knowing glances,idan Samha taƙi samuwa there are other alternatives.... WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17 Chapter twenty two: the fall out The next day bayan an tashi break, Ra'esah ne da su Samha suka shigo cafeteria, unlike the usual atmosphere inda ko ina yake shiru, yau ko ina sai surutu ake, mutane suna duba wayoyinsu suna stealing glances on Zeenah and her co's Dark flames na zaune a seats ɗin su, ga wasu mata kusan su huɗu zaune a cinyoyinsu doing all sorts of things cikin mutane ba kunya ba tsoron rabbi, su zeenah da Lucy on the same seat, fuskokinsu sun yi baƙi ƙirin, it turned out photos ɗinnan da Samha ta ɗaura a school blog anonymously have gone viral, mutane sai mocking ɗin su suke SAMHA na shigowa all eyes turned to her, ana ƙus ƙus,duk da babu wanda yasan waya ɗaura hotunan,they were ninety nine percent sure Samha ce. Ita ko samha as usual she confidently stepped in walking side by side with her sisters as they chat happily Ra'esah CE a matuƙar ba zata suka haɗa ido da Emmanuel ya wani kashe mata ido yana shafa lips ɗinsa and biting it at the same time, wani irin faɗuwa gaban ta yayi Na'ema ko tunda suka shigo kallo guda tayi musu ta ɗauke kai,cike da baƙin cikin kusancin su. Wani table kusa da table ɗin su zeenah wata yar yarinya duma duma cike da ɗaga murya tace '' Ashe ma duk wannan ɗage ɗagen,da jiji da kan na banza ne tunda har ba'a da ƙarfi,aikin banza....'' Tana faɗar wannan maganan mutane suka ɗauka akayi musu chaa,the silent mockeries became loud wani irin kunya ne ya rufe su Suka fara mayar da martani ga waɗ ke zagin su Amma to No vail Hakan ya zafafe su, Lucy ta miƙe cike da zafin zuciya ta jawo Samha ta fara duka, Samha was stunned Sauran ma suka taso suna taya ta,ganin za'ayi wa Samha taron danandagi yasa su Ra'esah shiga don su taya ƙawar su. The girls were busy beating each other black and blue, sun yi buɗun buɗun saboda sai da suka kai ƙasa suna faɗa. Sai banke tables suke suna jan gashin juna suna yagawa juna uniforms Mutanen cafeteria were cheering them on, Na'ema abun ya ƙara bata haushi ganin duk tsawon lokacin da suka kwashe tare da su Ra'esah they never made any attempt to help her when in trouble... Amma Samha da basu daɗe da sani ba? They are ready to sacrifice their lives for her. Wani irin tsanan Samha taji ya shige ta,Yes! She hates the girl kuma idan da zata samu dama she will ruin her. Suko mutane sai shewa suke ganin skirt buɗe a banza, the guys were hitting the table the cafeteria became absolutely chaotic Sai naushi suke exchanging, Samha was having the best time of her life, acikin wurin Babu wanda yayi ƙoƙarin raba faɗan,

Chapter 14 of 52