Share this page
kwalin ta ɗaura akai kawai dan bazata iya wahala ba, ɗan lip gloss suka shafa suka sa fararen hijabbai zuwa guiwa, they looked so breath taking, fitowa sukayi daga gidan suka rufe ƙofar, Aliyu was waiting for them outside cikin motar sa, Fitowa yay daga motar lokacin da ya hango suna zuwa,kafe su yayi da ido har suka iso wurin shi with a wide smile a fuskokinsu, hugging ɗinsu yayi one by one whispering 'ina ƙaunar ku' to which they replied the same.... Shiga sukayi Aliyu ya jasu, suka tafi,yawo yayi dasu sosai sun nishaɗan tu kafin ya kaisu monalisa Park,ya kaisu ShopRite,suka ci suka sha,their happiness knew no bound But it was short lived,suna tsaka da shan ice cream wayar Aliyu tayi ringing his boss was asking him to return the taxi, Hankalin Aliyu ya tashi miƙewa yayi ya fita daga wurin yana cigaba da amsa kiran,bin bayan shi su Mahmah sukayi,bayan ya ajiye kiran ya kalle su yace '' ku jira Ni yanzu zan dawo'' yayi maganar tare da juyawa zai bar wurin riƙe hannun shi sukayi suna faɗin '' Pa,zamu bika" kyakkyawan murmushi Aliyu yayi, hugging them ɗaya bayan ɗaya one last time ya ƙara faɗin '' Kujirani anan ina zuwa '' badan sun so ba suka barshi ya tafi, bayan ya kusa fita wurin ya juyo yanay musu bye, the rays of the setting sun falling on him, wani irin nauyi ƙirjin su yayi musu, there's a *vague* feeling in there hearts though basu fahimci Meyasa suke jin hakan ba, kamar wuce Aliyu ya dawo. Motar sa ya shiga yayi reverse ya fita daga wurin,ya tsallaka to the other side zooming off Kallon juna sukayi,wuri suka samu a harabar wurin suka zauna,zasu jira Aliyu ya dawo su tafi gida kawai Sunan zaune duk wata motar da ta wuce akan idon su dan dama ShopRite ɗin bakin titi ne, desperately suke jiran Aliyu,amma bai zoba sai wurin ƙarfe biyar da rabi,wani irin farin ciki suka ji ganin dawowarsa, Miƙewa sukayi suka isa bakin gate zasu fita,Aliyu dake ɗaya ɓangaren cikin motar sa yana jiran motoci su wuce kafin yayi crossing over yaji zuciyar sa ta bada Wani duum! Just like that. Shi kaɗai ne a lane ɗin shi, Yar addu'a yayi, shortly after motocin ɗayan side ɗin sunyi clearing Ahankali ya fara tuƙo motar sa, zuciyar sa na tsananin bugawa Su Mahmah dake tsaye ɗayan ɓangaren nan da nan suka tuna incident ɗin Salamatu,wani irin anxiety buildup with in them,suna kallon motar Aliyu da tayi rabin titi tana tunkaro su,when suddenly wata ƙatuwar trailer tayi wurgi da motar Aliyu, rolling motar Aliyu ta fara har ta cimma sauran motacin causing a huge accident,sai petrol ɗin motar ya fashe at the far end kawai sai motocin suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus ''PA NO!!!!" Mahma ta faɗa tana zubewa kan guiwowin ta,Hayaƙi ne ya fara tashi, while sauran motocin sai taka burki suke, kada suma su haɗu da same fate,amma saboda akwai motocin da basu ankara da abinda ke faruwa ba,ko motocin gaba sun taka burki,na bayan su da suka zo at full speed sai su tura su forward making the accident more ugly Mahma ji tayi ta kasa numfashi Suma tayi a wurin, Samha ko kasa motsi tayi, idanun ta akan accident ɗin har yanzu kafin slowly tafara tari, Tana aman jini..... Mutanen da suka taru a wurin suka ankara dasu wani mutum ya kwashe su ya wuce dasu Asibiti. Wurin haɗarin kuwa tsabar hayaƙi the sky looked cloudy,none of the drivers survived harda Aliyu, Fire brigades aka kira suka zo suna ƙoƙarin kashe wutar it felt kamar suna ƙara ma wutar ƙarfi ne instead, mutane especially mata sai kuka suke wasu na video suna azawa a social media.... WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17 Chapter fifty: How they met..... AURA PRIVATE HOSPITAL..... 09:00am Buɗe idanun ta da sukayi luhu luhu tayi tana kallon ceiling ɗin ɗakin, She felt paralyzed for a moment kafin komai ya shiga dawo mata tiryan tiryan,zabura tayi ta sauka daga kan gadon Gashin ta trailing behind her tayi kama da mahaukaciya at the same time aka buɗe ƙofar Dr ne ya shigo wata nurse biye dashi,Wani irin kallon Mahmah yake from head to toe yana lasar baki, especially yanda rigar ta kamata bringing out her shape Wurin su tayi da gudu,da sauri nurse ɗin ta riƙe ta, sai struggling Mahmah take wanting to break free,'' ki barni in tafi,pa yace mu jira shi zai dawo mutafi gida pls let me go he must be waiting '' Mahma ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga nurse ɗin'' kiyi haƙuri ki zauna pls " inji nurse ɗin helplessly,kuka Mahma ta fashe dashi tana turjewa, zuciyar tana mata wani irin raɗaɗi Perhaps duk abinda ya faru mafalki ne kawai, maybe idan ta koma can wurin zata ga cewa komai wasa ne, komai mafalki ne, maybe zata ga pa smiling at her and he will hug her yet again.... Dr Nan ne ya ƙaraso wurin su ya riƙe Mahma yana ƙoƙarin sata jikin shi,ture shi tayi with tremendous force sai da ya faɗi, waro ido yayi jin yanda ɗuwawan shi suka daki ƙasa,itako nurse ɗinnan sai calming Mahmah take '' rungumeta Mahmah tayi tana Cigaba da risgar kuka cikin kuka tace '' Maam, it's all over yanzu mun zama marayu kenan? Pa yace mu jira shi zai dawo why didn't he return?" Sosai Mahmah ta ba nurse ɗinnan tausayi, ''it's okay '' nurse ɗin ta furta idanun ta na cikowa da hawaye ta tausaya musu sosai. Lokaci guda Mahma ta tuna da Samha,raba jikin su dana nurse ɗin tayi looking around '' Ina ƙanwa ta?"tayi maganar tana zaro idon ta da sukayi jaa,'' Tana I. C.U, kiyi sallah sai kizo in Kai ki!" Jinjina kanta Mahma tayi ta miƙe ta shiga toilet ɗin tayi Alwala tazo ta ɗauki hijabin ta da yayi datti tasa ta tada sallah, although in her mind tana tunanin me Samha keyi a Icu? Drn miƙewa yayi yana dafe ƙugun shi ba karamar buguwa yayi ba,kallon nurse ɗin yayi yana faɗin '' Bring her to my office after wards Nurse habeebah'' '' okay sir'' nurse habeebah ta faɗa. Bayan Mahma tayi sallolin da ake Binta zama tayi wurin tana tuna duk abinda ya faru,kwantawa tayi tana sharɓar kuka kamar ranta zai fita, Nurse habeebah tazo tana yi mata nasiha, zuciyar Mahmah raɗaɗi take mata, ji take ina ma zata iya cire zuciyar ta ajiye a gefe. Bayan ta tsagaita da kukan ta share hawayen ta duk da she didn't think zasu tsaya, '' Ina Samha?" Tashi Itama nurse habeebah tayi ta nufi ƙofa Mahma biye da ita,ICU suka tafi,tun kafin su shiga ta window ta hango Samha kwance saman gado ansa mata oxygen,mutumin da ya kawo sune ya biya kuɗin. Kallon nurse habeebah tayi tana neman ƙarin bayani as they stepped in, nurse habeebah bata ce komai ba,sai fita da tayi. Mahma ta ƙarasa kusa da Samha dake kwance rai hannun Allah wani Gwauron numfashi Mahmah tana, suddenly feeling kamar oxygen ɗin wurin wasn't enough, what is happening? Taya rayuwar su turned upside down in a moment? Slowly ta Isa bakin gadon Samha hannu na rawa ta kai ta riƙo na Samha that felt cold, itama Samha tawani irin zama pale kamar bata da jini Ga life supporting machine ɗin da aka laƙa mata, hankalin Mahmah ya tashi '' Meya same ki Samha?" Ta faɗa in a barely audible voice. '' why are you like this? Samha kada ki barni pls,my heart can't bear it, wake up for me Samha '' Mahmah ta faɗa wani kuka na ƙwace mata yet again idanun ta har wani zafi zafi suke mata. Tana nan sai ga wata nurse different from nurse habeebah tazo tayi leading ɗinta zuwa office ɗin likitan ɗazu Izinin shigowa yayi musu kafin bayan wannan nurse ɗin tayi knocking, Shiga Mahmah tayi,wuri ya nuna mata a gaban table ɗin sa yace ya zauna,zama Mahmah tayi tana share Hawaye ɗauke idon shi yayi daga kallon ta yana lasar baki yace '' baku da wani elder family member ?" Girgiza kanta mahma tayi kafin tace '' We have lost our father,Ni da ita kaɗai ne'' gyaɗa kanshi yayi a ran shi yana faɗin ta kwana gidan sauƙi kenan '' I'm sorry for your loss M.s...?Slowly with a cracked voice mahma tace '' Aliyu '' jinjina kanshi Dr yayi yana jin daɗin Muryar ta. '' Me yake damun kan wata?" Ta tambaya without looking at him,shafa gemun sa yayi kafin slowly yace '' Condition ɗinta yayi worse sakamakon hayaƙin da ta shaƙa,da ace ta ƙara mintuna ba tare da ankawo ta asibiti ba she could have lost her life" duk wannan bayanin da yake mahma wasn't getting it,Meya ke damun samha ne? Dama tana da wani ciwo ne? Murya na rawa tace '' Me yake damun tane?" Yana kallon confusion ɗin dake fuskar ta,miƙewa yayi yazo ya tsaya bayan ta ya ɗan ranƙwafo yana faɗin ''Tana da lung cancer final stage, I'm sorry da baki sani ba and it got to this stage,tana buƙatar surgery da gaggawa '' yayi maganar yana ɗaura hannayen sa kan kafaɗar ta ya wani ƙwalalo ido yana lasar baki, just like a typical ɗan iska.... Mahma ko wani jiri taji yana kwasar ta, yaushe? Sheshsheƙar kuka ta fara hakan yasa ya fara bubbuga shoulders ɗinta his hands roaming on her shoulders da wani fake tausayi a fuskar sa '' How did this come to be?" Ya faɗa in a whisper, Gabaki ɗaya hankalin ta baya tare da ita. Tana kuka tace '' Nawa ne kuɗin surgery?" Ƙara tausar kafaɗar ta yayi yana faɗin '' 2 million '' wani irin zabura tayi ta mike daga saman kujerar in the process ta buge masa hanci Da baki da kanta, baya baya yayi yana dafe bakin shi Dammn shit!!! It hurts It's bata ma sani ba,cuz a ruɗe take '' Ina zan samu wannan kuɗin....? WHO will help us...? Ya Allah...'' on and on she went. Ya ɗauki lokaci wurin nayi masa zoge kafin ya sai ta kanshi ya miƙe yana jawo mahma wanting to take advantage of the situation, hannayen ta biyu ya riƙe suna facing juna, Slowly ta zuba almond eyes ɗinta cikin Kananan idanun sa da sukayi ja, and what a very set of ugly eyes he had... Mahma natsuwa tayi tana kallon shi, da wata yar iskar murya yace '' zan iya taimaka miki da kuɗin surgery in kin bani haɗin kai!" Yayi maganar yana lasar baki yana mata kallo from head to toe,Tuni ƙwaƙwalwar ta tafara taro mata abinda ya faru a China, shaking jikin ta ya fara ganin yanda yake ƙara kusanto da fuskar shi dab da Tata,girgiza kanta ta fara yi Hawaye nabin fuskar ta,he wasn't listening '' No'' ta furta in a whisper tana ƙoƙarin ƙwace kanta,ƙara riƙe ta yayi gam, her trauma kicked in her her adrenaline high and survival instincts?"No!!!!!" Ta faɗa da ƙarfi kafin da duk strength ɗinta ya ture shi faɗawa yayi saman table ɗin sa duk abubuwan dake saman table ɗin suka faɗi ƙasa... Rufe kunnuwanta tayi da hannayen ta,tana numfashi kamar zata shiɗe Dr ɗin nan kuwa kasa tashi yayi dama akwai wata Allura saman table ɗin nashi and his butt landed on it..🤣 '' Damn shiiit!!! '' ya faɗa yana sauka daga saman table ɗin,yar ƙara yayi kafin ya miƙa hannu ya cire allurar da ta laƙe masa, it was painful..wurin mahma da ta gama ruɗewa ya ƙaraso a fusace yace '' Ke dan uwar ki matsiya ciyar dan kin samu za'a taima keki shine zaku yi ma mutane hauka ko? To Bari in gaya maki your sister if she doesn't get treated today mutuw...'' kafin ya idasa sentence ɗin da, mahma da ta rufe kunnuwanta ta miƙe idanun ta sunyi wani arnen ja,kamar zakanya tayi tsalle ta cafko wuyan shi, tazaro ido tana faɗin'' Idan ka ƙara faɗin ƙanwata zata mutu,i will cut your tongue and feed it to the dogs I swear'' tayi maganar tana ƙara damƙe masa wuya ta haɗa shi da table ɗin sa,idanun sa waje,har ya fara shinshino mutuwa when suddenly wasu nurses mata biyu suka shigo office ɗin,zubar da Files ɗin hannayen su sukayi suka iso suna ɓanɓare mahma that seemed to be out of her senses,da ƙyar suka cirota daga jikin Dr ɗinnan in the process suka yaga mata hijabi ya rabe gida biyu. Tana sakin shi ya faɗi wurin gasping for air yana matsawa baya, yana tari,ƙwace kanta tayi tafita daga office ɗin looking completely insane Kan doctor sukayi suka tayashi miƙewa,kallon office ɗin sukayi it looked scattered ruwa ɗaya daga cikin nurses ɗin ta bashi ya karɓa gulping it down completely har yanzu bai dawo daidai ba dan ba ƙaramar shaƙa yaji ba. Bayan ta fita daga office ɗin ward ɗin Samha ta koma looking at her for the last time,she can't imagine life without her she had lost more than enough. Share hawayen ta tayi ta nufi kofar baya ta asibitin ta fita, nan ta samu wani baƙin hijabi daya ga ruwa yaga duniya tasa,a little away ta hangi slippers sun ci sun cinye suma tasa sannan ta fita daga asibitin. Tafiya take bata san inda zata ba,ta faɗi nan,ta tashi can, ta zauna nan tayi kuka,ta miƙe can ta cigaba da tafiya she wasn't sure ta ina zata fara neman miliyan biyu in one day ba,idan ta ga masallaci zata tsaya tayi Sallah before she carries on, bayan tayi sallar la'asar unknowingly ta ɗauki hanyar asokoro, tsohon gidan su ta tsaya tana kallo,har yanzu ba'a gina wurin ba,har yanzu the ruins were still there except yan gwan gwan sun kwashe roofs ɗin. Hawaye na Shatata kan fuskarta tabar wurin,inda Aliyu ya zauna ranar taje ta zauna,wani kuka ne ya ƙwace mata remembering how he hugged them ranar,"Papa!! Mama!!" Ta kira da ƙarfi and helplessly,ta daɗe tana kuka awurin kafin ta miƙe ta bar wurin ta cigaba da tafiya without knowing inda take sa ƙafa ba, kallon setting sun ɗin tayi zuciyar ta na mata wani irin zafi sai kuma ta kalli tall buildings ɗin anguwar there wasn't a single soul waje, cigaba da tafiya tayi.. ashe har ta hau kan titi ita bata sani ba ƙiiiii!! Kake ji saura kaɗan mota ta buge ta,it was Dr Ahmad **""End of flash back""** '' And that's how I met him,who in turn brought me into your life Amreesh " Salmah ta faɗa tana riƙe fuskar Amreesh that had an unreadable expression, duk wannan labarin da ta bashi,she made sure ta cire part ɗin da akayi abusing ɗin su to her it's not something Worth saying,wani irin tausayi yaji ta bashi tausayin da bai taɓa jin shi akan kowa ba, rungumeta yayi sosai ajikin sa, Slowly tace '' I can't lose you Amreesh, losing you will be an even bigger blow to me than all I have been through,kada ka barni ''tayi maganar hawaye wasu na bin wasu,'' I won't Mahee '' Amreesh ya faɗa kissing her hair,shima he had been through a lot but ba kamar su ba. Jin saukar numfashin ta yayi alamun tayi bacci, kwantar da ita yayi,ya rufa mata blanket ya fita daga ɗakin. Dr Ahmad ya gani tsaye a balcony hannun shi riƙe da coffee, Ƙarasowa wurin shi Amreesh yayi, sassanyan iskan brushing against his skin tsayawa yayi kusa da Dr Ahmad ya jingina da railing ɗin wurin '' You okay EMRYS?" Dr Ahmad ya faɗa sipping from his coffee,he rarely calls Amreesh da Emrys sai dai zakee,the two men stood in silence for 5 minutes kafin slowly Amreesh yace ''SEB, kana ganin idan tasan koni WAYE will she stay?" Amreesh ya faɗa with a distanced look a fuskar shi, murmushi Dr Ahmad yayi, mainly saboda Amreesh in za'a kaɗa a raya baya kiran sunan shi, neither Ahmad nor Sebastian sai dai yayi maganar shi kai tsaye yet he just called him Seb today? Yar ƙaramar dariya Dr Ahmad yayi,hakan yasa Amreesh ya juyo ya lalle shi ''Sorry'' ya faɗa yana ɗaga hannu sama in a surrender kind of way can yace '' ka damu ne?" Shiru Amreesh yayi yana ƙoƙarin sanin idan ya damu,after a while yace '' I don't know '' jinjina kanshi Ahmad yayi kafin ya juyo fully suna fuskantar juna yana kallon idon Amreesh yace '' Are You afraid of losing her?" Nan ma Wani shiru ya biyo baya kafin Amreesh yace '' taya zan sani?" '' You love her?" Jinjina kanshi Amreesh yayi, eh yana son ta mana otherwise why would he stay with her?. Bubbuga kafaɗar shi Ahmad yayi with a grin on his face yace '' Kada ka damu Romeo, Juliet bazata Barka ba" '' You think so?" Amreesh ya tambaye duk da zuciyar sa doesn't think so, yacigaba da faɗin '' old man Zakee wants me to bring her na tabbatar can wani zai faɗa mata ina the most horrible way possible '' ''Da gaskiyar ka Zakee and that's why it's important kasamu lokaci ku zauna ka faɗa mata da kanka,komai ya biyo baya then You will handle it uhm?" Nodding Amreesh yayi,amma taya zai fara? Bai saba Magana ba taya zai fara? Zata yarda? '' Go and sleep Zakee '' Dr Ahmad ya faɗa yana tura Amreesh forward, ɗan tsuke fuska Amreesh yayi yace '' stop pushin me Seb'' Dr Ahmad bai ji ba sai da ya kai shi har ƙofar ɗakin shi Sannan yace ''ka wani zo ka tsaya nan,while we are hoping to see babys bouncing,kaje ka rungumi matar ka pls'' '' Ɗan iska '' Amreesh ya faɗa yana shigewa ɗakin shi, dariya Dr Ahmad yayi kafin ya koma ya ɗauki coffee ɗin sa ya shige nasa ɗakin. Hawa saman gadon Amreesh yayi ya ja blanket ya rufa pulling Mahma close, kallon fuskar ta yayi for seconds kafin slowly yayi pecking ɗin lips ɗinta,in a whisper yace '' I don't know if you will stay with me if you find out Mahee, but I don't want to let go..." WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17 Chapter fifty one: The game 𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘)𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17 https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt 𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝑓𝑖𝑓𝑡𝑦 𝑜𝑛𝑒:𝑇ℎ𝑒 𝑔𝑎𝑚𝑒..... The next day.... 11:00am News room Amreesh zaune gaban yan jarida cikin shigar baƙaƙen kaya from head to toe,ƙafa ɗaya saman ɗaya, Baƙin gashin sa ya sauko har kafaɗar sa slightly covering his left eye,hakan yasa ya ƙara zama kamar wani villain daga movie...ga ƙamshin turaren sa da ya cika ko ina, it's hard to breathe, fuskar shi ba rahama ko kaɗan sai ma tsuken da take fiye da koda yaushe, Ga wani irin dangerous aura that oozes out from him.... Gabaki ɗaya News room ɗin wani irin tensed atmosphere ne,duk da Ac'n dake kunne gumi suke, tun ɗazu Suka dinga rantafo tambayoyin su,yet Amreesh yayi shiru yaƙi tankasu rather sai binsu yake da cold eyes ɗinsa dake piercing right through their souls,kowane ɗan jarida tsoro ne bayyane a fuskar sa kada ace yayi offending ɗin big short,idan hakan ya kasance then...ba ɗan jaridan kaɗai ba,har da gidan jaridar su abun zai shafa, lokaci ya cigaba da tafiya yan jarida sai kallon juna suke suna kallon Amreesh that looked like a devil from hell, A matuƙar bazata suka jishi yana faɗin cikin sexy voice ɗinsa '' Who gave you the audacity to print those pictures...'' Abinda ya faɗa kenan ba tare da ya kalli kowa cikin su ba. Wani irin gumi ne ya fara tsatstsafo musu dukan su,they were confused basu ya kamata su yi tambaya a basu amsa ba? Why are they getting questioned in return? Amreesh ya cigaba da kallon su da icy cold eyes ɗinsa ganin yanda tsoro ya bayyana a fuskokinsu,wani ɗan jarida cike da ƙarfin hali yace '' Yallaɓai Zakee, wannan tambayar taka don ka kauda hankalin Mutane ne daga tuhumar da ake maka ne ko akwai wata manufa?" Wannan tambayar da ɗan jaridar yayi yasa sauran yan uwansa sauke ajiyar zuciya, maybe yanzu pressure will be shifted back to Amreesh,kafe ɗan jaridan da ido Amreesh yayi,hakan yasa ɗan jaridar yaji hanjin cikin sa kaɗawa, The atmosphere was intense '' dame ake tuhuma ta?" Amreesh ya faɗa da wani irin devilish voice da kuma Hausar da basu yi tsammanin ya iya ba, yana watsa musu wani shegen kallo,kusan sumar zaune sukayi, wata yar jaridar da tasa wasu shegun matsatstsun kaya,duk surar da Allah yayi mata a waje tana wani ƙwarƙwasa tana juya ido in a seductive voice take faɗin '' yallaɓai Zakee ana tuhumar ka da lalata da ƙananun yara because you're influencial,kuma iyayen yaran basuda yanda zasuyi cuz at last you're a powerful person mai zaka ce game da hakan?" Completely yanda take maganan da body language ɗinta zai nuna maka abinda ke ranta,she was advertising her self,tana manta da aiki suke anan,well who wouldn't? The mighty Amreesh Zakee ga kyau kamar shi yayi kansa ga izza ga mulki? Ga wani irin charming Aura he's the perfect definition of every girls' dream Kallo ɗaya Amreesh yayi mata ya ɗauke kai,while yan uwanta yan jarida ta basu mugun mamaki,sun santa she was professional yanzu kuma what's with the attitude? Dawo da kallon kan Amreesh sukayi yanzu ba lokacin damuwa da abinda tayi bane, lokacin ɗaukar labari ne... Jinginar da bayan sa Amreesh yayi a kujerar da yake zaune yana yi musu kallon ƙasan ido,for a heart beat sun riƙe numfashin su, why the hell is he like this!!!? '' Duk wanda yake tuhuma ta da lalata da yarsa anan ko a wani wurin daban can step forward '' Suka ji deep voice ɗinsa,he said it so casually kamar ba wani abu bane... Amreesh kuwa wani irin yanayi ya tsinci kansa, he's heart was raging. .in a way it never did. Yan jaridar suka fara kallon kallo,Toh su dan rabbi Ina zasu san dawa dawa yayi ma hakan? '' Yarinyar da aka kama ku can testify '' wani ya sake faɗa a tsorace,kallon shi Amreesh yayi kafin slowly yace '' Where is the girl?" Yawu ɗan jaridar ya haɗiye, perhaps Amreesh yayi threatening ɗin ta ba lallai ta iya magana ba,or perhaps karuwar sace? Tsit sukayi a wurin, The tense doubling up, Gyara zaman shi Amreesh yayi a matuƙar kausashe yace '' ku dukan ku have invaded my personal privacy, Kuka tozartani nida mata ta ta hanyar yaɗa hotunan ƙarya" Kalaman sa sun sauka cikin kunnuwansu kamar Bombshell, idanu waje suke kallon Amreesh matar sa? Yaushe yayi aure?so suke suyi muhawara a tsakanin su yet Amreeshs' Aura was oppressive...so damn oppressive!! Secretary Ayman dake tsaye a bayan fage ya waro ido shima,damn! Bai san da cewa matar ogansa bace yarinyar nan, gaske Amreesh yayi magana maimakon yanda suka saba sai dai shi yayi attending ko insun zo tare sai dai shi ya amsa yan jaridan amma yau Amreesh yayi magana da kanshi what position must she have hold on his heart? tunanin shi ya katse lokacin da yaga Amreesh ya miƙe yana faɗin '' I have the right to sue you all for personal privacy invasion,zaku haɗu da lauyoyina....'' daga haka Amreesh ya sauka daga stage ɗin yana tafiya ɗaya bayan ɗaya mike he owned the place.... Yan jaridar yanzu kam They were dripping with sweats, Kai idan ma akwai abinda yafi zufa yanzu shi suke,wasu har sun fara kuka,they knew it, Amreesh was ruthless sun sani Amma to this extent? Damn shiiit! Susa suka zo ɗaukar labari how did things turn out this way? Sai gudu suke suna bin Amreesh amma tuni Amreesh yayi gaba Secretary Ayman bayan shi, Yana wani murmushin mugunta,yasan boss ɗinsa rarely reacts idan an masa Abu amma when he does? Kashin mutum ya gama bushewa.... And in real sense bawai yan jaridan yake nufin su biya ba,Gidan tv'n su zasu biya. Amma ai ta shafe su ko? Albashin su zai koka aiko? Shigewa motar da aka buɗe masa Amreesh yayi yana kunnen uwar shegu da magiyar yan jaridar, They have crossed the line they shouldn't have involved his personal life..... Jinginar da kansa yayi on the head rest ya lumshe idanu,his cologne along with his aura ya wani cika motar. Ayman da driver suka kalli juna, basu san inda zaya ba,and suma da kansu suna tsoron yimasa magana kada ta shafe su. Secretary Ayman be yayi shahadar faɗin

Chapter 33 of 52