Share this page
directly ita yake kallo,sarƙar hannun ta ta ɗago placing it above his eyes ta fara swinging ɗin sarƙar side by side,idanun Amreesh nabin sarƙar idon shi suka juye 😵‍💫, after a while ta fara '' kai ne silar abinda ya faru a wannan daren..daga yau You won't try to remember abinda ya faru kaji!" Gyaɗa kanshi Amreesh yayi don ba a hayyacin shi yake ba,'' Sleep!! '' ta sake bashi order,Jan blanket ɗin Amreesh yayi ya rufe kanshi ya kwanta,at this point yayi kama da mutum mutumi don controlling ɗinsa take kawai..... The next day Salmah bata ga Amreesh a dining ba hankalin ta ya tashi cuz over the past few days taga yanda ya rame,he had lost the glow on his face ya zama more isolated and lonely more aloof and cold ɗakin shi ta shiga bata ganshi ba ta fito looking so sad, yaushe ne ma? Ba ita tace zata zauna dashi ba in any condition? Me yasa take gudun shi yanzu? Was her love fake? Cikin garden ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita,miƙo mata ruwa yayi daga bayan ta yana faɗin '' Crying isn't the solution...naga yanda kike gudun ZAKEE over the past few days ba daidai bane,ba lallai ya faɗa maki ba but i can see how much he loves you and you suddenly treating him like this isn't fair...kina wahalar dashi knowingly or unknowingly...'' Juyowa tayi tana kallon Dr Ahmad baki buɗe she didn't know what to say..ƙasa tayi da idon ta,ajiye ruwan yayi ya juya yana faɗin '' make it right..don't push him into further isolation..'' daga haka ya fita daga wurin..zama Salmah tayi tana juya maganar Ahmad acikin ranta...what should she do? Abinda aka faɗa mata fa? Should she just... fashewa tayi da kuka tana dafe goshin ta '' ya Allah '' ta furta desperately not knowing what to do,bata tashi daga wurin ba sai da ta yanke hukuncin abinda zatayi next! 01:00am Saye take da kayan bacci a pink nightgown da hular saƙa,her cleavage exposed, miƙewa tayi tasa slippers ta fara tafiya slowly kamar ɓarauniya ta nufi hanya '' leaving without a good bye?" Samha ta faɗa suddenly juyowa Salma tayi their eyes met,ƙasa tayi da nata tace '' i have to...ban kyauta da abinda nayi ma Amreesh ba,I broke my promise...I said...'' da sauri Samha tazo ta rufe bakin Salmah '' i understand Mahma and I'm honestly proud of you da kika ajiye tsoron ki gefe kika fuskanci reality!" Hawaye suka zubo daga gefen ido Samha ta share tace '' Hey don't cry..I got you okay?" Jinjina kanta Salmah tayi kafin ta rungume Samha then she left a ɗar ɗar Samha closed the door behind... Tura ƙofar ɗakin Amreesh tayi ta shiga zuciyar tana ɗarɗar..ganin ɗakin take kamar wurin yan mafiya already her imagination was going wild, hawaye na wanke fuskar ta,ta isa gaban gadon tana leƙa fuskar Amreesh,buɗe idon shi yayi suddenly, zuciyar ta tayi wani uban tsalle kamar zata fito ta baki tayi baya baya ta faɗi, fashewa tayi da kuka Ganin Amreesh ya tashi zaune, pausing Amreesh yayi yana kallon ta with his sick eyes yanda take Matsawa da baya jikin tana matuƙar rawa she looked frightened by him kamar shi dodo ne, Salmah kuwa addu'a kawai take cikin ranta tana matsawa baya ganin Amreesh ya miƙe coming close to her... Sunkuyo wa yayi daidai tsawon ta amma akwai space tsakanin su,ta wani takure heart beating at a wild phase... Bayan kusan minti biyar a haka Amreesh yace '' do you think I'm a monster?" His voice deeper and quieter fiye da kullum, Salmah ta ɗago idonta ta kalleshi,duk da duhun ɗakin suna iya ganin juna saboda hasken dake fitowa daga A'c she could see how pale he looked maganar ma daƙyar yayi ta, sauke idon ta tayi tana ƙara takurewa her lips moving but she couldn't find the words '' I'm not what they told you Mahee... I'm not a monster...you're hurting me by being scared of me..'' ya faɗa tare da stretching hannun sa ya taɓa ta,ta saki kuka me ƙarfi pressing ɗin lips ɗinsa yayi together yana cigaba da kallon ta his heart aching '' zan iya sauwaƙe maki..I can divorce you idan baki so ki cigaba da zama dani..'' Amreesh ya faɗa wani irin ɗaci na mamaye zuciyar sa har zuwa bakin sa...the words were so bitter in his mouth.. Salmah ta wani ɗago da sauri jin abinda ya faɗa miƙewa Amreesh yayi yana tafiya slowly his heart burning and itching... Har ya kwanta saman gadon yaja ya rufa da blanket Salmah tayi shiru kalaman shi na maimaituwa a kunnen ta,if he divorces her...No! Bazata taɓa iya rayuwa ba Amreesh ba! She might be scared of him,but she's unwilling to leave him! Ko da take faɗawa Samha su bar gidan cikin fitar hayyaci ne kawai she can't do that! Miƙewa tayi zuciya cike da tsananin fargaba ta hau gadon ta kwanta bayan Amreesh hugging his waist...jin hannun ta da kuma ɗumin jikinta a nasa yasa ya buɗe idon sa da suke a lumshe kafin slowly ya juyo suna kallon juna runtse idonta Salmah tayi jin ya juyo her body was shaking incessantly Amreesh ya lura da hakan so he kissed her forehead tareda ɗaura hannun shi a waist ɗin ta pulling her closer cikin Muryar rashin lafiya yace '' Bazan taɓa cutar dake ba Mahee...and as long as I live Bazan bari wani ya cutar dake ba!" Slowly ta fara buɗe idon ta kafin ta kalli fuskar shi their gaze met..she saw sincerity a fuskar shi, ya cigaba da faɗin'' You mean the whole world to me,you staying away from me shattered my heart into pieces Mahee...kada ki ƙarayin hakan...Ni ba mugun mutum bane!" Amreesh ya faɗa sounding so vulnerable so sincere,wasu round of tears suka fara bin fuskar ta cuz ta gane cewa she was wrong to have trusted abinda Mariya ta faɗa mata from the beginning batareda tayi bincike ba she was so foolish!" I'm so sorry Reesh!''she voiced out murya na rawa hannun ta gliding on his face tayi nadama, '' I'm happy you're back to me,never leave me again pls'' Amreesh pleaded, jinjina kanta tayi,ya share mata hawaye his hand feeling softer and warmer... Suna kallon juna eyes burning with flame of passion ƙasa tayi da kanta claiming his lips,a passionate kiss was shared between them... ***** The next day Salmah da Amreesh suka yi zaunen su ciki, Samha ce ta kawo masu break fast tana yima Amreesh ya jiki tana hararar shi ta gefen ido...tsuke fuska Amreesh yayi tareda faɗin '' nadai ji sauƙi ehe.. ya san ranki?" Samha ta saki baki tana kallon shi,yanda yake magana kamar dama farin ciki take rashin lafiyar shi ƙwafa tayi kafin ta juya ta fita, Salmah dake zaune tana serving ɗin abincin da Samha ta kawo ta girgiza kanta, Matsowa Amreesh yayi ya rungume ta closing his eyes words can't describe how happy and relieved he felt to have her back.... Karo sukaci da Ahmad lokacin da ta buɗe ƙofar zata fita daga part ɗin,da sauri tayi saurin Matsawa baya ido waje suna kallon juna cikin ido,da sauri tayi ƙasa da idon ta her heart begun marathons her stomach fluttered with butter flies Ahmad ya kafeta da ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa wai yanzu wannan itace ta ceceshi five years ago kuma yake ta neman ta just to find her under his roof! Juyawa Samha tayi da sauri ta wuce ɗakin ta without turning back ciki ya ƙarasa wurin su Amreesh when he was giving the permission to enter yashiga Da rana tareda sauran family members ɗin suka ci abinci, mariya couldn't help but notice sabuwar soyayya da kulawar da Salmah ke ba Amreesh,ba ita kaɗai ba har da sauran mutanen wurin ma suka su da suka san idan tana cin abinci Amreesh comes barin wurin take at 380, maraƙisiyya har takai lomar abinci taji lomar ta laƙe taƙi wucewa saboda tsananin shock itako mariya ko motsi ta kasa wasn't her plan a success? What happened now? Kallon kallo aka shigayi yet no one spoke, Azeezah ce ta hangi yanda Ahmad ke whispering Abu a kunnen Samha dake zaune kusa dashi and she was blushing har fuskar ta tayi ja,wani irin baƙin ciki taji ya soki zuciyar ta,ƙasa tayi da idon ta abincin ya fita daga ranta gaba ɗaya... Har aka ci aka cinye basu dena mamakin sudden change ɗin da aka samu tsakanin Salmah da Amreesh ba... Da daddare bayan Salmah ta dawo da plates ɗin da Amreesh ya ci abinci dasu ta wanke zata fita Mariya ta sha gaban ta looking so furious '' me kike yi da Haryanzu baki bar gidan nan ba? Ke ma kina so ki mutune kamar sauran?" Girgiza kanta Salmah tayi looking so innocent tace '' I figured that...we might not really meet the same fate, kowa da tashi ƙaddara Bazan iya barin mijina ba ko da ace zai ke dinga yanka na yana ci everyday!" Wani irin Banzan kallo Mariya kema Salmah tana ji kamar ta shaƙota, Salmah kuwa murmushi ne a fuskar ta,ta wani ƙwalalo ido tana kallon Mariya...'' ke wai ke mayyace eh? Why can't you just leave? Idan kuɗi kike so...'' '' ba kuɗi nake so ba!" Salmah ta katse ta,'' Toh me kike so eh? Faɗa min!" Mariya ta faɗa a harzuƙe '' Amreesh nake so!" '' faɗi farashin soyayyar ki!" Mariya fired,Yar ƙaramar dariya Salmah tayi kafin ta kalli mariya ido cikin ido tace '' You Can't Buy My Love!" Salmah ta faɗa spelling each word and meaning it...'' kuma na gano some useless elements kawai suke son shiga tsakani na da miji na,i can't risk it..'' Salmah ta cigaba with a wink 😉 in the end, mariya tayi sakake tana kallon Salma wai itace useless elements? Tayo kan Salmah a harzuƙe zata mareta kaucewa Salma tayi sai ga mariya tui aƙasa dariya sosai Salmah tayi kafin ta gudu daga kitchen ɗin tabar mariya zaune a wurin Ɗakin su ta nufa tana Cigaba da dariya but guess what? Khaleel was waiting for her... murmushin gefen baki tayi..she was tired of being the victim.... Approaching ɗinta ya farayi ta tsaya wuri guda...ganin hakan yasa yayi dariya yana jin daɗi don yau yazo da shirin shi,she won't out smart him...wata zalɓeɓiyar bulala ya fito da yana wulwula ta akan Salmah with a smirk on his face idan tayi taurin kai tasha kashi... Salmah kuwa ta cigaba da kallon shi da nutsuwa yana kawo wa Wurin ta ya tsaya yana kallon ta first kafin ya tsuke fuska yana faɗin '' wuce muje..'' kallon hanyar da yake nuna mata tayi kafin slowly ta dawo da idon ta akan fuskar shi '' idan naƙi fa?" Ta tambaya tana ɗage gira, confidence ɗinta ya tsorata shi kawai sai ya shilla bulalar wanting to beat her, kaucewa Salmah tayi,kafin tayi cikin shi giving him a high kick on the jaw ya saki ƙara yana dafe haɓarsa tareda sakin bulalar,sharɓe shi Salmah tayi kanshi ya daki ƙasa,wani ihun ya sake kurma wa,da duk iya ƙarfin ta,ta ishi ishi ta zabga masa bulalar sai ga fitsari shaaa! Yana sakin ihun azaba dariya Salmah tayi crouching down to his height tace '' Too bad...your tricks are just as weak as you...next time kayi ƙoƙarin taɓani or coming in my way...I will break you into pieces inyi packaging and send it to your mom!!" Tayi maganar cike da gargaɗi kafin ta ƙara masa wani round of bulala sai ihu yake yana shille shille saboda zafi salmah na dariya ta bar wurin,jin ihun khaleel yasa mutanen gida zuwa to his rescue Nan suka ganshi kwance cikin fitsari yana risgar kuka every body was confused antamabaye shi me ya faru dashi he refused to say dole suka ɗauke shi suka kai estate clinic... Dariyar dake fuskar Salmah froze lokacin data ga Amreesh kneeling on the ground hannun shi dafe da zuciyar shi yana aman jini his whole body was shaking fararen kayan jikin shi duk sun ɓaci da jini,abinda ya faru shine bayan Salmah ta tafi kitchen ya zauna shikaɗai kalaman Hajiya maleeka echoing in his head forcing him to believe shine yayi abinda ake tuhumar sa dashi ɗin...but Amreesh ya riga da yasan bai aikata ba so why would he admit daga nan yaji wani ciwon kai ya fara nuƙurƙusar shi,he forced himself to remember, zuciyar sa ta fara ciwo ƙwaƙwalwarsa ta birkice don ya fara ganin abubuwan a buji buji,it wasn't clear,kawai yana ganin pictures ne not clearly..he begun to recall,kaɗan daga cikin abunda ya mantane ya fara tunawa when suddenly ya fara amai..aman jini his head threatening to burst the pressure was too much way too much...idan akayi 😵‍💫 hypnotizing ɗin mutum ya manta Abu any time yayi ƙoƙarin tunawa it will be a bloody fight don zai iya mutuwa ko ya shiga coma ko ya manta komai, Amreesh kept pushing himself yaƙi ya bari, numfashin wahala yake, his eyes utterly red...his teeth clattering jikin shi na rawa jijiyoyin kanshi duk sun miƙe... Salmah was horrified itama jikin ta ya fara rawa '' AMREESHHHH!!!!!!" Faɗuwa Amreesh yayi kwance a wurin looking lifeless... Book 2 na WAYE SHI ?(Behind the mask) paid book ne for 1k, ga duk wanda ke buƙata ya biya Ta wannan account ɗin 9138091955 SALMA ALIYU Monie point Shaidar biya ta wannan number +234 9138091955 WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁 https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt Chapter seventy two: Dark flames.... Sumar wucin gaɗi Salmah tayi kafin ta ƙara ƙwala kiran sunan Amreesh ta ruga da gudu ta jawo shi jikinta ta tana kuka hawayen ma basu fita saboda tsabar tashin hankali, Amreesh wasn't breathing...'' Amreesh!!!!'' ta sake kira tana jijjiga shi tareda tapping fuskar shi that looked pale kamar bashi da jini... Ahmad ne ya shigo ɗakin,yazo duba Amreesh yaji Salmah na Faman kiran sunan shi tana kuka,tana sabbatu da,gaban Dr Ahmad yayi mummunar faɗuwa da sauri ya ƙaraso shima without hesitation ya cicciɓe Amreesh daga jikin Salmah though Amreesh nada nauyi ya fita dashi Salmah without bothering ta jawo wani hijabi saman gado tabi bayan su tana shararar kuka, bayan Ahmad ya ajiye Amreesh a back seat Salmah ta shiga ta zauna hugging his head tana kiran sunan shi.... She couldn't imagine life without him..'' pls...pls wake up plsss!!! '' Sharara gudu kawai Ahmad yake his heart beating in his ears zuciyar sa skipping every now and then, Salmah tsabar kuka her eyes weren't seeing clearly, Bayyana tashin hankalin da Salmah take ciki at this point was impossible, '' you can't leave me like this.... it's not over..'' ta faɗa tana tapping lifeless face of Amreesh her tears wetting his face,hankalin ta ya ƙara tashi ganin Amreesh na zubar da jini ta baki ta hanci ta kunne wani ihu ta kurma da ya gigita Dr Ahmad yasa at the same time ya ƙara gudu akan wanda yake his eyes bloodshot '' Why don't you listen EMRYS!!!?" Dr Ahmad ya faɗa under his breath ba tun yau ba ya faɗa ma Amreesh yadena ƙoƙarin tuna baya but he just doesn't listen...damn!!! ****** Samha da taga lokacin da aka kwashe Amreesh aka fita dashi taji jikin ta ya bala'in yin sanyi...it reminded her lokacin da Mota ta kwashe maman su saman titi and how baban su ya ɗauke ta yasata a ambulance from then on basu sake ganin taba will it be the same with him? Bakin gado ta zauna duk yanda taso kada ta karaya her emotions got the better of her sai gata kwance ƙasa tana kuka sosai Bayan sun isa wani private asibitin da sauri aka karɓi Amreesh directly suka shigar dashi emergency unit likitoci suka rufu akanshi har Salmah zata bisu ta shiga wani Dr ya dakatar da ita '' wait outside ma'am '' Ba musu ta koma baya idonta na cigaba da zubar hawaye Dr Ahmad couldn't even console her don shima dauriya yake kawai Salmah ta shiga tashin hankali especially dataga hours were passing by yet babu Dr ɗaya daya fito daga I c u ɗin,her heart was racing alot of what ifs flooding her mind,there are alot of possibilities game da condition ɗin Amreesh she didn't want to imagine the worst.... Slowly ta dawo ta tsaya gaban ƙofar ta glass opening ɗin take hango Amreesh cikin kayan surgery, yanzu kam bayada mara ba da matacce he wasn't moving kuma kamar fatalwa cuz his skin was super white '' Stay plsssss!!!" Salmah ta faɗa looking hopeless and desperate, Ahmad ne yayi ta maza yazo ya tsaya bayan ta yana lallashinta '' he'll be fine insha Allah,kizo in mayar dake gida ko huta i will stay with him..!" 'Hutu'...salmah ta maimaita acikin ranta, taya zata huta when Amreesh isn't with her? Taya zata huta when Amreesh is in the theater room? Taya zata huta when Amreesh could be in pain? Taya zata huta when Amreesh is on the verge of... girgiza kanta tayi da sauri not wanting to complete the thought '' Amreesh will be fine..'' ta faɗa inaudibly idonta manne da wurin not blinking even for a second '' zan zauna till he wakes up... don..Allah ka koma.. gida, Samha is alone '' tayi ƙoƙarin faɗi, Ahmad ya ƙi yarda at first Amma daga ƙarshe he had to agree... Amma only idan Amreesh was out of danger... Zaman su a asibitin reminded her of lokacin da ta kusa rasa Samha and today...? Why does it feel like her life is moving in circles? Kowane bad experience repeat it self almost exact same way! She lost her mom to a car accident her dad too,she was sexually abused so was her sister and now Amreesh...? Silent tears suka fara bin fuskar ta her heart pounding her body weak...idan Amreesh ya mutu she won't survive Da ƙarfe ɗaya da minti 30 operation room ɗin ya buɗe, Salmah kamar zata wuntsila ta faɗi '' ya..y..ya jikin shi?" Ta tambaya, shima Dr Ahmad tuni ya ƙaraso, ajiyar zuciya likitan ya sauke tareda faɗin '' he's out of danger now!'' Murmushi Salmah da Ahmad sukayi for the first time '' likitan ya cigaba da faɗin za'a maida shi I C U yanzu'' da sauri Salmah tace '' zan iya zama dashi?" Likitan yace a'a saidai su dawo gobe it's the rule of their hospital ba'a zama da mara lafiya and besides he needed to be alone,suna nan tsaye aka fito da Amreesh daga theater room ɗin,rufe bakinta Salmah tayi jin kuka na ƙoƙarin ƙwace mata '' Amreesh '' she whispered tana kallon kyakkyawar fuskar shi data ƙara kyau duk da rashin lafiyar but he looked pale.... '' come with me to my office...'' ya faɗa after a while, gaba yayi suka bi bayan shi, Salmah felt so light weighted kamar zata faɗi, Ahmad felt miserable kuma har yanzu zuciyar sa cike take da tsoro Bayan sun shiga office ɗin Dr yayi musu bayanin condition ɗin Amreesh '' he tried to force his brain to remember certain events,this mounted pressure on his brain and body shine dalilin dayasa ya suma, idan da har an ƙara koda minti ɗaya ne ba tareda an kawo shi asibiti ba he could have lost his life, sannan next time idan ya sake yin irin hakan he could die ko kuma ya shiga coma for life time ko ya rasa ransa!" Salmah ta rufe baki jin bayanin likita ashe sun auna arziki, she felt so weak,so pained just WAYE SHI? Waye Amreesh? What's the mystery surrounding his life? So much pain... Godiya Ahmad dayaji zuciyar sa na neman fashewa yayi ma likita kafin suka fita daga office ɗin,sai da Salmah ta sake zuwa inda Amreesh,it was a VIP suit...ta tsaya daga waje tana kallon shi '' So much pain...who are you?" Ta furta barely above a whisper before they left Through out the drive home Babu wanda yayi magana except Salmah dake ta tsiyayar hawaye,she wants to be apart of Amreesh tana so ta zama matar sa fully and to know what's happening to him...suna shigowa gidan suka ga mutanen gidan kowa tsaye cirko cirko cikin kayan bacci, Pah ne kamar zai faɗi yazo wurin Ahmad body trembling yace '' Ahamadu ina Muhammadu?" Yayi maganar yana leƙa bayan Ahmad kamar Ahmad ya ɓoye Amreesh behind him, sauran mutane came closer hearing what he'll say '' he was in a coma...'' Ahmad ya faɗa simply,baya baya Pah yayi zai faɗi Ahmad yayi saurin taro shi,his eyes filled with tears, maraƙisiyya da Saudat suka wani saki ihu suna murje murje while parlon ya ɗauko salati Salmah unable to stand all this yasa ta wuce sama da sauri tana rufe bakin ta cuz she so badly wanna cry... Tana shiga ta iske Samha, Itama ido sunyi luhu luhu Rungume juna sukayi suka ɗaura daga inda suka tsaya '' i can't live without Amreesh Sam....Bazan iya ba!" Salmah ta faɗa cikin kuka..'' You won't..'' Samha tayi reply tana goge ma salmah hawayen ta,sun daɗe a wurin kafin suka tafi ɗakin Samha anan suka kwanta..... The next morning wurin ƙarfe tara suka isa asibitin, Salmah Samha da Ahmad suma sauran mutanen gida zasu zo... fitowa sukayi suka nufi suit ɗin Amreesh, Salmah taji ƙafafunta were heavy her chest tightened lokacin da taga Amreesh kwance... he wasn't moving, he wasn't saying a thing,she so badly wants to hear him call her ' Mahee ' '' Ka buɗe idon ka Amreesh...your Mahee is waiting to see you...to hear your voice pls ..'' Salmah ta faɗa tana riƙe hannun shi da ba'a sama drip ba tana kuka, Ahmad ya ɗauke kanshi gefe his eyes very red, Samha ta miƙe ta fita daga suit ɗin her heart beating wildly, tafiya take batasan inda take sa ƙafarta Bama Ji tayi ta ci karo da mutum, slowly ta ɗago reddish foxy eyes ɗinta ta kalle shi...it was Andrew...Andrew of dark flames..suka wani tsare juna da ido...kallon ta yake his eyes holding something.... something she couldn't name Samha ta matsa baya wanting to change way, Gaban ta Andrew yasha yana faɗin '' well look who's here!" Yayi maganar with a scoff sai ga sauran members of dark flames saye suke dukan su cikin jajayen kaya riga da wando their mowhawk hair style dyed with red color sun wani ƙara girma '' Oh... it's MS feisty!" Su duka suka faɗa suna kallon Samha from head to toe suna tuna yanda Ahmad yayi torturing ɗinsu.... Littafin WAYE SHI?(Behind the mask) Book 2 paid book ne for 1k ga duk wanda ke buƙata ya biya ta wannan account ɗin 9138091955 SALMA ALIYU Monie point shaidar biya ta wannan number+234 9138091955 WAYE SHI?( Behind the mask) By Autumn 17 🍁🍁 https://chat.whatsapp.com/ITRS0D9vLpo1uGMEvTahfs?mode=wwt Chapter seventy three: Ra'esah..... Ƙwafa sukayi closing in on Samha, Mathew yace'' What? Suprised to see us? Kinyi tunanin wannan ɗan ƙaramin azaban da brother ɗinki ya bamu will be enough to scare us?" Samha ta ƙyafta ido confused wane brother kuma? '' we're enemies for life!" Gefe ta sake bi zata wuce Emmanuel ya sake Shan gaban ta cike da zafin rai Samha ta wanke fuskar sa da mari '' incase if you have forgotten let me remind you...I was...I still am...and will always be Samha! Don't try to double cross me!" Emmanuel was shocked suma sauran haka the shock could not be hidden on their faces Andrew yayi composing kanshi clicking his tongue ya dawo ya tsaya gefen Samha ya ɗaura hannun sa kan kafaɗar ta kamar su abokai ne with a smile yace '' Feisty as always....'' Samha ta ture hannun sa tareda naɗe hannun ta akan ƙirjinta Chibuke ya wani shafa kanshi da dariyar shaƙiyanci ya dawo ya tsaya ɗayan gefen Samha suka sata a tsakiya '' You look prettier I have to admit....'' Samha ta juyo gefen sa with a smug smile tace ' because you're ugly... doesn't mean everyone has to follow suit right?" Fuskokin dark flames yayi baƙi, Chibuke har wani huci yake his face looking reddish '' I swear...I wish to cut out your tongue...ganin ki Ako da yaushe kina tafiya lafiya lau makes me feel like murdering you and then incinerate your body into the river!!" Emmanuel ya faɗa a harzuƙe kamar zai

Chapter 45 of 52