ƙarfi, kafin ta fara kalle kalle, uniforms ɗinta ta gani ta kwasa tasa ta fita daga wurin a guje....
Tafiya take tana sambatu kamar wata mai taɓin hankali...
Who suffered the most?
WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter fourty eight: The calamity
#UNEDITED
Tafiya take in the middle of no where ta waiga nan ta waiga can hoping Babu wanda ke Binta, at some point sai ta faɗi ta tashi dan cikin daji be ' I saw it' shine kaɗai abinda take maimaita wa, her lips trembling,jikin ta na ƙyarma, dare yayi sosai irin wurin ƙarfe sha biyu ɗin nan, idan da tana cikin hayyacin ta babu yanda za'ayi take dinga tafiya a wuri irin haka,but ita a gare ta tashin hankali bai wuce abinda ta gani ba just now....
Aliyu ne ke zarya tsakanin gida da police station,gida saboda Samha da bata da lafiya,gashi ta ɗauki damuwar rashin ganin Mahmah ta ɗaura a kai. Police station saboda har yanzu Mahmah bata dawo ba,he wondered ko ina take? Wane hali take cike? Has she eaten? Is she in good hands? Ga baki ɗaya depression da anxiety na ƙoƙarin kama Aliyu,ya'yan sa ɗaya ba lafiya ɗaya is no where to be seeing me yake faruwa?
Zama yayi saman benchin dake gaban police station ɗin yana ji kamar yayi ihu ko raɗaɗin zuciyar sa zai rage '' protect her ya Allah'' Ya faɗa yana kallon sama that was clear ba tauraro ko guda, he was desperate
Miƙewa yayi ya nufi hanyar gida yana tafiya yana ji kamar Iska zai jefar dashi
Tura ƙofar palorn yayi je found Samha lying on the rug ta cure wuri guda, jin an turo ƙofa made her sprang to her feets saura kaɗan ta faɗi
Da sauri Aliyu ya ƙarasa ya riƙota ta faɗo jikin sa breathing rapidly tace '' ka ganta? Is she okay?" She said barely above a whisper,zama Aliyu yayi da Samha sited on his lap, da raunatattar murya yace '' I'm trying '' kwantar da kanta samha tayi a ƙirjin sa her fever 🤒 rising up tace '' pls find her'' hawaye suka fara fita daga idon ta, Aliyu bai san yanda ma zai yi ba,'' ki dena kuka,zamu gano ta uhm?" Jinjina kanta samha tayi, little while later Bacci yayi gaba da ita,ɗaukar ta yayi ya kai ta ɗakin su sannan ya rufa mata ƙofa ya tafi ɗakin su alwala yayi, yayi Sallah yana kwararo adduo'i, Aliyu na zaune wurin har asuba bai runtsa ba. Damuwa bazata bari yayi Bacci ba.
Bayan yayi Sallahr Asuba ya duba Samha,ya tabbatar tayi break fast ya Bata magani before he left to the police station.
Har wurin ƙarfe goma na safe Aliyu da police suna neman Mahmah yet No news, Zama Aliyu yayi ya dafe kanshi wanting to cry when she suddenly appeared kamar an jefo ta,she looked hagard uniforms ɗin abirkice,ga wasu hakukuwa laƙe a gashin ta da yake nan kamar sheƙar tsuntsaye,farar rigar ta tayi datti, ƙafafun ta ba takalmi
'' Mahma '' Aliyu ya kira da ƙarfi,a tsorace Mahmah ta kalli direction ɗin su,Aliyu ya miƙe ya nufe ta da gudu ihu ta tsala kafin Itama ta kwasa a guje she didn't recognize him Dan har yanzu she was in shock
Police ma suka biyo su, sai ihu take tsalawa tana ƙara gudu,cafkota Aliyu yayi '' Mahmah!!! '' tsabar tsoro da shock suna tayi, ganin yanda yarinyar ke gudun Aliyu yaso ya kawo tsaiko,it took Aliyu alot to convince them
A haka ma Saida aka tura su asibitin da jami'in tsaro ɗaya.
Admitting ɗinta akayi bayan an canja mata kaya zuwa HOSPITAL gown, ganin komai ya daidaita yasa Aliyu komawa gida
Iske Samha yayi a entrance ta dafe fence ɗin ya tsaya cuz she was too weak to stand on her own '' ya Salam Samha '' Aliyu ya faɗa yana isowa wurin da sassarfa, ɗaukar ta yayi suka nufi cikin gidan '' an gano ta?" Ta faɗa faintly, murmushi Aliyu yayi ya ajiye ta saman couch ya jinjina kanshi kafin fuska ɗauke da damuwa yace '' she was running away from me!" Lumshe idanun ta Samha tayi kafin ta sake buɗe su ta ɗan gyara zaman ta a couch ɗin tace '' might she have been traumatized? Ko wani abu?" She said thought fully,dafe goshin sa Aliyu yayi, weakly Samha tace '' it's okay '' gyaɗa kansa kawai Aliyu yayi ya miƙe yana faɗin '' bari inje in ga in ta farfaɗo we will be back soon'' fita yayi bayan haka
Da karfe biyu ta farfaɗo ganin maza biyu akanta yasa ta saki ihu tana matsawa baya,da sauri Aliyu yayi ƙoƙarin matsawa kusa da ita,her screams intensified kafin duk abinda yake within her grasp ta ɗauka tana jifar su '' kada ku matso!!!!, go away!!! I saw it!! I saw it!!" Abinda yake faɗa kenan tana kuka duk ta daburce
Aliyu was dumbfounded kallon likita dake janshi out of the room yayi kafin ya kalli Mahmah da ya zama ƙaramar mahaukaciya. Bayan fitar su Aliyu wata Dr mace ta shigo da nurse biyu mata suma attending to Mahmah
A office ɗin Dr yayi ma Aliyu bayanin finding ɗin su,har wani duhu duhu Aliyu ke gani lokacin da ya fito daga office ɗin
Ɗakin Mahmah ya sake komawa yana kallon yanda take Bacci Saboda Allurar da aka mata, fita yayi daga asibitin ya koma gida samu yayi Samha ta gyara ko ina ta dafa abinci '' bakida lafiya '' Aliyu ya faɗa yana kallon Samha,'' naji sauƙi'' she replied kafin ta ƙara da faɗin '' ina Mahmah?" Numfashi Aliyu ya ja kafin yayi mata bayanin da Dr yayi masa. Sauke idon ta samha tayi,she was right
Miƙewa tayi ta zo kusa da Aliyu holding his hand she led him to his room shidai biye da ita yake kawai, kwantar dashi tayi saman gadon shi ta zauna daga gefen shi tana shafa coily hair ɗinsa tace '' Rest..'' kallon ta kawai Aliyu yake murmushi tayi masa tare da rufe masa ido, lumshe idon sa Aliyu yayi dan dama ya gaji Allowing the darkness to swallow him whole
***********
Bayan sun koma asibiti,Aliyu wasn't allowed into the ward saboda yanda Mahmah ke ihu idan taga namiji kusa da ita koda dr ne, Aliyu was more than depressed yarinyar ta zama kamar wata mental,sai maimaita ' i saw it' kawai take tana kuka she refused to speak to anyone, Dr yayi advising Aliyu ya sata a therapy that might help,ko da yaushe suna tare da Samha.
Sati biyu Mahma tayi aka sallame su daga hospital condition ɗinta yayi improving sosai ta dena sambatu amma har yanzu bata so wani na miji ya raɓe ta har da Aliyu....
A gida ta canja ta zama wata irin quiet ba yawan magana,ba surutu just so quiet..too quiet,dama can tana da saurin kuka,it multiplied,the once cheerful Mahmah turned into a dull Mahmah. They didn't like the new Mahmah,it makes them wonder ko me akayi mata haka?
Da safe bayan sun gama breakfast suna zaune ɗakin su, Mahmah tsaye bakin window Samha kuma zaune saman gado tana kallon Mahmah tana sauke ajiyar zuciya can dai ta miƙe ta isa inda take dafa kafaɗar ta tayi '' You didn't tell me،me suka miki? We are worried Mahmah pls '' Cike da damuwa tayi maganar slowly Mahma ta zuba almond eyes ɗinta cikin na Samha,sai ga hawaye kafin ta fashe da kuka tana rufe fuskar ta,Muryar ta da wani azababben ɗaci take faɗa ma Samha abinda ya faru '' I feel humiliated Samha, ji nake kamar zuciya ta zata buga when ever I think about it '' She said, Samha engulfed her in a tight hug tana faɗin '' Na san yanda kike ji Mahmah,but hey... Mu gode Allah da bai basu Sa'a ba,we weren't defiled like other girls uhm?" Jinjina kanta Mahma tayi tana sheshsheƙar kuka,zaunar da ita Samha tayi tana Cigaba da lallashinta
Slowly Aliyu dake tsaye bakin ƙofar ɗakin su ya goge hawayen da suka silalo masa yana yanke shawarar barin China
Wurin aiki ya tafi yayi submitting ɗin resignation letter ɗin sa, Wurin ƙarfe bakwai Aliyu ya shigo gidan da wasu dillalai su dai su Mahmah sai kallo suke as the dillalai entered every corner of the house suna dubawa. Sai wurin ƙarfe takwas da rabi suka tafi
'' We are leaving China'' Aliyu dropped the bombshell lokacin da suke cin abinci da daddare,dukan su suka zuba masa ido suna jiran ƙarin haske, Aliyu ya cigaba da faɗin '' it has taken from us more than it gave us,zamu koma Nigeria cikin dangin mu...'' Aliyu yayi maganar cike da baƙin ciki, kallon juna Samha da Mahmah suka yi kafin suka kalli Aliyu that looked so emotional
Miƙewa su biyu sukayi hugging him from both sides although Mahmah tayi hakan reluctantly, Haryanzu bata gama warkewa ba amma ta ji sauƙi sosai
Wrapping ɗin hannuwansa Aliyu yayi around whispering '' Allah yayi muku Albarka '' ya faɗa.....
Few days later, tsaye suke suna kallon gidan su one last time, this is where they grew up, memories masu daɗi da marasa daɗi na dawowa , kamar kar su tafi but they had to, juyawa sukayi suka kalli neighborhood ɗin su and surprisingly yau akwai mutane tsira ra unlike other days da babu mutane
'' Mu tafi'' Aliyu ya faɗa bayan ya rufe gidan leading them out of the premises
Motar su suka shiga Lang ya kai su airport, bankwana Aliyu yayi da Lang kafin suka shiga airport ɗin bada daɗewa ba jirgin su ya tashi....
Lokacin da suka iso airport ɗin Abuja sai kalle kalle su Samha suke,abun yayi daban... Shi ko Aliyu wani rushe of excitement yaji,at last ya dawo ƙasar shi, mutane sai kallon su ake,hakan yasa Mahma ta shige ma Aliyu jikin ta na rawa slightly especially duk inda ta huta sai taga maza ne saye da matsatstsun kaya offering her ugly smiles, Samha ko tsuke fuska tayi kamar bata San yanda ake murmushi ba
Aliyu da yayi noticing haka da sauri ya tarar musu mota suka shiga suka bar airport ɗin,sun ɗauka hotel za su but to their surprise sai suka ga ankawo su wani haɗaɗɗen gida a asokoro,it turned out years back Aliyu ya sayi gidan dan yana da burin dawowa da zama Nigeria wata rana. Three bedroom me sai ƙaramin parlor gidan ba babba bane dan bai kai gidan su na China girma da haɗuwa ba but it was beautiful and spacious enough to contain them
Kayan su da akayi shipping few days back duk an jera musu komai yanda ya kamata they were relieved
Ɗakin su Aliyu ya kai su kafin ya shige nasa ɗakin,Faɗawa sukayi saman gadon simultaneously suna kallon juna kafin sukayi ma juna murmushi '' it's over daga ƙarshe '' inji Mahma da tunda suka baro China wannan ne karo na farko da tayi magana '' it is '' in ji Samha tana lumshe idanun ta kafin Bacci ya kwashe su
'' Gidan yayi kyau?" Aliyu ya tambaya da daddare bayan sun gama dinner, jinjina kansu sukayi tare,they love the house duk da yaune ranar suna farko, murmushi Aliyu yayi na jin daɗi atleast this wasn't bad for a start...
Rayuwar su suka cigaba da gudanarwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, Islamiyya Aliyu lokacin da zasu dawo har ya gama komai ya dafa abinci ya kimtsa ko ina da ko ina, sosai suke ƙaunar baban su,time to time yake kai Mahmah taga therapist, wata Rana Aliyu decided to visit his family and make peace kamar yanda Salamatu ta roƙa, shiryawa sukayi su duka suka tafi, Aliyu yayi tsammanin familyn da zasu yafe masa su karɓe sa especially da yazo da ya'yan sa but to his biggest surprise cin mutuncin su akayi akayi musu korar kare his family suna ƙara jaddada basu buƙatar shi da duk wani abu da ya shafe sa including jinin sa, Aliyu was deeply pained almost to a point of depression, it took a lot kafin ya dawo daidai ya rungumi ya'yan sa he needed nothing else...
Rayuwa went on quite smoothly for over a year and half, lokacin Mahma na shekara sha bakwai da watanni, Samha sha huɗu da yan watanni Itama
Another calamity befell them...
Wata rana bayan Aliyu ya ajiye su islamiyya bai dawo gida ba ya shiga neman aiki, kuɗin hannun sa saura kaɗan idan sun ƙare idan baida aiki how will he catter for the needs of his daughters? Da wannan tunanin ya dinga biyar Company zuwa Company Neman aiki amma ko ɗaya bai samu ba... Yana biyar rana har lokacin tashin su daga islamiyya yayi, biyawa yayi ya ɗauke su,ganin su kaɗai ya sanya ya ranshi, tafiya suke suna hira Suna faɗa masa abubuwan da suka faru a makaranta '' Duk ajin mu Ni kaɗai ce ba'a daka ba dan na iya karatu '' Mahmah ta faɗa proudly, dariya Aliyu yayi ganin yanda samha ta ɗaure fuska yace '' ke fa?" Tana huci tace '' wai pa,dama nasan mutumin nan bai ƙauna ta, kuskure guda fa kaɗai nayi shine ya dinga yimin wahayin buloli kamar na aikata wani babban laifi'' ba Aliyu kaɗai ba,har da Mahmah sai da tayi dariya jin abinda Samha ta faɗa. Aliyu zai yi magana idon shi ya faɗa kan gidan su da yake ci da wuta, the flames were flying kamar zasu kama sama, gidajen Biyar dake manne dana Aliyu suma sun babbake,Aliyu was Dumbstruck.....
WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter fourty nine:His last hug
Ji Aliyu yayi komai ya tsaya masa cak, the noise was in back ground tuni ruhin sa yayi tafiya,tafiya mai nisa that perhaps ba zai dawo ba cuz it's too much... Me yasa bala'i ke ta afka masa ɗaya after the other? Ba gidan ne damuwarsa ba, memories ɗin dake gidan,his wife's last momento were turned to ashes tare da sauran abubuwan daya mallaka
'' Ya Allah '' Aliyu ya furta slowly yana yin baya baya kamar zai faɗi
Da sauri su Mahma dake rusar kuka sukayi saurin taro shi, mutanen dake ƙoƙarin kashe wutar wasu daga cikin su suka zo su ka ɗauki Aliyu suka zaunar dashi ƙarƙashin bishiyar that was a little away from their home
Su Mahmah zaune gefen sa,sai abun yayi kama da movie sune yan kallo
Dan zama sukayi suna kallon sauran neighbors ɗinsu da suma gidan su ya ƙone suna birgima suna ihu
Sai kuma gidajen su da suka ƙone ƙurmus,ga fire service sai aikin bada ruwa suke amma a banza, it turned out fuse ɗin ɗaya daga cikin gidajen ne yayi sparking, shine wuta ta kama, kasancewar unguwar masu kuɗi babu mutane da yawa ba'a ankara ba sai da abu yayi nisa,
Aliyu was more than heartbroken,he was shattered ji yake kamar wutar ba'a ginin take ci ba,but on his heart.
Mutane sai kai komo suke wasu sun taru a gefe suna kallo.
Babu abinda suka tsira dashi dukan su in Banda kayan jikin su. Jin yanda suke ta rera kuka especially Mahmah yasa Aliyu rungume su yana lallashin su duk da shima dai yana buƙatar hakan, daga ƙarshe bayan komai yaci ya cinye sai gani yayi ana kwasar neighbors ɗin nasa especially matan zuwa asibiti,sauke kansa Aliyu yayi, he didn't know what to do.....
Wasu daga cikin mutanen dake tsaye wurin ne suka iso inda Aliyu yake suna bashi haƙuri,Aliyu dai ya kasa cewa komai sai gyaɗa kai yake that's all he could do
'' toh yanzu ina zaka Mallam Aliyu?" Ɗaya daga cikin mutanen ya tambaya,Aliyu ya kalli su Mahma kafin ya kalli mutanen,bai san inda zai je '' Bansa niba nima'' inji Aliyu he's mind wandering,wani can daban yace '' Toh ko kana da gida a wannan unguwar?" Girgiza kansa Aliyu yayi sai kuma Yace '' Nawa ake renting gida a unguwar nan?" Kallon juna mutanen biyu sukayi kafin wanda ya fara magana da farko yace '' duk da ba anan nake da zama ba, aƙalla sai ka tanadi sama da miliyan goma Mallam Aliyu ko ba haka ba Mallam Sani?"
''Hakane Mallam halilu!" Inji Mallam Sani, Share fuskar sa Aliyu yayi, kuɗin dake hannun shi basu kai yawan abinda sukayi mentioning ba,what should he do? Aliyu ya shiga tsananin tashin hankali '' Amma akwai unguwar talakawa daidai idan kana so Mallam Aliyu '' Inji Mallam halilu, da sauri Aliyu ya jinjina kanshi yana zuba musu idanunsa da suka yi uban ja,'' Toh muje a nuna ma, dare na ƙara yi ''Slowly Aliyu ya miƙe,su Samha ma suka miƙe suna biye da mutanen Nan as they led the way, Abin hawa suka hau suka bar anguwar
Bayan tafiya mai ɗan karin nisa suka iso Kado kuchi, unguwar talakawa talak talak kallon ko ina su Mahmah suke they honestly don't like this place, Especially yanda ko ina yake so cramped Babu buɗaɗɗen filin da mutum zaibi ya wuce sai kanayi kana faɗawa gidan mutane wai kuma duk hanya ce.
Shima dai Aliyu unguwar batayi masa ba but yana da wani zaɓi? Sun yi tafiya mai tsawo,suna tafiya Su Mallam halilu na musu bayanin anguwar '' Akwai ɓarayi daya wa da yahoo boys a unguwar nan dole kubi a hankali musamman dakake da wa'yannan kyawawan yaran haka'' Shidai Aliyu jin su yake kawai,sai kuma ya ƙara damƙe hannun Mahmah da Samha cikin nashi jin abinta aka faɗa
Wani one room apartment suka iso luckily wannan gidan ya bambanta da sauran,wannan yana da tsakar gida, sannan zagaye yake da katanga unlike sauran gidajen da suke open spaces,mutum baida wani privacy 🔏
Duba cikin wurin Aliyu yayi, daki guda spacious enough to contain them su uku,duk da ba haka yaso ba, sai akwai wardrobe da gado shike nan, sai tsakar gida akwai toilet da kitchen shikenan
Gidan yayi ma Aliyu hakan yasa yayi payment Wa Mallam halilu dan dama gidan sane, it's a rent gidan kamar sabo
Sallama sukayi ma Aliyu suka tafi.
Dawowa cikin gidan Aliyu yayi ya same su tsaye jigum jigum, Suna ganin shi suka yo wurin shi da sauri,riƙe hannuwansu yayi leading them to seat on the bed
'' Kuyi haƙuri,abinda zan iya yi kenan we have to navigate I know it will be hard Amma insha Allah komai zai daidai ta,idan na samu kuɗi masu yawa zan ƙara gina muna babban gida'' said Aliyu,duk yanda yake ƙoƙarin kada hawaye su zubar masa sai da suka zubo,share masa hawayen sukayi hugging him ,They were all so miserable 😖
****"""
It took a while kafin suka saba da sabuwar rayuwar su,oh they learned to cope, cikin sauran kuɗin da suka rage ma Aliyu ya siya musu kayan sawa,dana abinci dana shafawa sannan yasa su islamiyya he can't play with that...
Daƙyar da suɗin goshi yasamu aka bashi hayar taxi so he became a taxi driver,sai yayi buga buga yake samun costumers
Aliyu ya canja ya zama wani abin tausayi kamar ba shi ba. Bala'in tausayi yake basu, amma alhamdulillah duk da bai samun da yawa they were at peace and contented ga shaƙuwa tsakanin su cuz Aliyu was very much taking care of them yana kaunar su baya son abinda zai taɓa su, suma kuma suna matuƙar ƙaunar baban nasu
Trouble Came knocking lokacin da Samha ta fara yan ciwuka,yau lafiya gobe ba lafiya ciwon ciki ciwon kai,da farko Aliyu ya ɗauka saboda sabon environment ne,cuz akwai sauro So maybe malaria ke damun ta hakan yasa yake siyo mata magani daga chemist, and it suppresses the illness na ɗan wani lokaci sai dai idan rashin lafiyar ya tashi dawo wa it comes back with ful swing,ganin Abu yaƙi ci yaƙi cinye wa gashi idan tayi tari sai ya dinga zuwa da jini yasa Aliyu ya kai ta wani private hospital Dan yasan government hospital ba dole su ɗauki abin serious ba,kuɗin test were very expensive a private hospital ɗin amma haka Aliyu ya biya, Test na farko aka gano tana da lung cancer final stage
Ji Aliyu yayi duniyar tana wani juya masa, lung cancer final stage? How ? Kuma babu wani symptoms daya nuna hakan in Banda tarin da tayi mai jini was it possible?
Dafe kanshi Aliyu yayi '' Hasbun Allah wani'imal wakeel'' Ina zai samu wa'yannan maƙodan kuɗin?
'' likita za'a iya suppressing ɗin rashin lafiyar further na ɗan wani lokaci har insamu kuɗin da za'a yi mata aiki?"Aliyu yayi tambayar his voice breaking,Jinjina kanshi likitan yayi yana kallon Aliyu da ya rame ya ƙanjame cike da tausayi sannan yace '' za'a iya amma it's very risky,sai dai idan tana shan maganin da za'a bata Insha Allah if she sticks to it hakan zai yi suppressing ɗin rashin lafiyar '' share hawayen shi Aliyu yayi yace '' nawane kuɗin maganin?" Kallon Aliyu Dr yayi kafin yace '' i will give it to you for free Dan gaskiya maganin akwai tsada, dubu ɗari biyar ne magungunan'' gumin da yaketoma Aliyu ya share ya zube akan guiwowin shi yana yima Dr godiya miƙar dashi Dr yayi leading him out of the office suka tafi ward ɗin Samha, she looked pale idon ta biyu tana kallon ceiling, tsayawa bakin window Aliyu yayi yana kallon ta, he felt weak '' kayi haƙuri' inji likitan,gyaɗa kanshi Aliyu yayi,in this life they have suffered enough. Barin shi wurin Dr yayi yaje ya kawo masa magungunan Samha yayi masa bayanin yanda zata sha.yana faɗin '' remember na ɗan wani lokaci ne kawai,kuma ko na rana guda kada ta tsallake maganin uhm?"
'' insha Allah '' Aliyu ya faɗa yana ƙara yima Dr godiya, shiga wurin Aliyu da Dr suka yi,kallon ƙofar Samha tayi ganin Aliyu ta miƙe zaune da ɗan ƙaramin murmushi a fuskar ta,her hair scattered over,tace '' mu tafi gida Pa, ban son wannan wurin it stinks'' Dariya Aliyu yayi dan baison taga hawayen shi ya zauna kusa da ita holding her close yace '' idan kina cewa asibitin Dr na wari zai maki Allura '' Turo baki Samha tayi ta kalli Dr da yake murmushi,yar hararar shi tayi tace '' Toh ai gaskiya ne ''ƙarasowa ciki de yayi da murmushi a fuskar shi,the girl is just so cute, batareda yace komai ba yayi examining ɗin ta,ya tambaye ta how she was feeling '' naji sauƙi pa, mutafi gida Mahmah na jira fa!" Tayi maganar tana sauka daga saman gadon,tayi inda hijabin ta,ta ɗauka tasa, Aliyu yabi ta da kallon tausayi, dawowa tayi ta riƙe hannun Aliyu trying to stand him up miƙewa Aliyu yayi,ya kalli Dr tare da faɗin '' a gafarce mu Dr '' jinjina kanshi Dr yayi fuskar shi ɗauke da murmushi Haryanzu yana cigaba da kallon Samha dake jan Aliyu har suka fita daga ward ɗin
Taji sauƙi sosai saboda Allurar da akayi mata when they arrived.
'' Pa,me yake damun Samha?" Mahma ta tambaya bayan sun gama cin abincin rana,ɗan pausing Aliyu yayi cuz he couldn't tell them what was wrong could he? Ya ƙirƙiri murmushin ƙarya yace '' malaria da typhoid'' tunani Mahmah ta shiga yi, is it possible to cough blood saboda mutum na da typhoid? Ko dai...
Aliyu ya katse tunanin ta ta hanyar faɗin '' zan tafi aikin sai na dawo "
''Allah ya kiyaye ya bada Sa'a,kazo mana da agwaluma" inji su biyun, involuntarily murmushi ya suɓuce ma Aliyu,a genuine one,fita yayi yana dariya...
Bayan tafiyar Aliyu gyara ko ina sukayi suka kwanta suna hira tsakanin su,ko tv basu da balle suyi kallo, kuma Aliyu ya hana su zuwa gidan maƙwabta. Kuma baza su je islamiyya ba cuz Samha bata da lafiya she needs a breathing space
*******
Rayuwar su ta cigaba da tafiya da daɗi da babu, Samha na cigaba da shan magungunan ta,duk in tayi tare sai hankalin Aliyu ya tashi,ga ko rabin kuɗin surgery ɗinta Bai samu ba,farin cikin shi ragagge ne due to this ga hawan jini da depression da yake battling silently. Allah ya taimakisa yana ɗan samun cinikin taxi ɗinsa
Their last moment together shine ranar da birthday ɗin su ya zagayo, Samha ta cika shekaru sha biyar,Mahma kuma sha takwas dan dama birthday ɗinsu ɗaya, Aliyu yana da kuɗi da yawa hakan yasa he decided to take them out suyi celebrating shima kuma ya samu ya ɗan declutter his mind.
Shiryawa sukayi cikin wasu dogayen riguna na Atamfa fitted,Mahma tayi packing gashin ta into a low pony tail,ita Samha ɗan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 52