Share this page
ya hadaki da ita, ko gaisuwar kirki na ga kin kuma yi mata sai na wulakantaki sannan na maida ke gidan ubanki, dan ba zai yiwu ba na dauko ki na kawo ki kashe ni kina shiga gindin kishiyata da ba kaunata take yi ba, ke shaida ce a gidan nan dan ta haifi namiji daya kwal ba irin abinda ba'a mana a kanta da danta, to ba zai yiwu ku da kuke nawa ta kwace min ba kin fahimta?" Kai take gyadawa har idannuwanta sun cika da kwala kafin ta saketa ta fita da sauri ta haura sama ita kuwa Hajiar ta ja tsaki tana sake hade fuska domin abin ya bata haushi ainun, sai dai wata hanyar da ta hango ta baraka ta sanyaya mata zuciya, domin ta tabata in dai har abinda ta gani a idannuwan Yumnah kishin wancen yarinyar ne to fa zata bi ta nan ta sa rashin jituwa tsakanin Hajiar da Yumnah, tana ji tana gani sarakuwar ษ—an nata sai dai ta hangota ba dai su yi wata taraya ta zumunci ko fahimtar junna ba! Sosai Khausar ta ji dadin fitar nan, sun je an aunata, daga nan suka je Hajia ta daukar mata takalma masu kyan gaske harda kafa ciki mai dan karamin hls a jikinsa fari kal mai kyan gaske, harfa kayan kwaliya, daga nan suka wuce wajen HAJUA FUSAM, nan fa ta sha kallo ta nemi rikicewa har ta ji wani irin sha'awar son ta ringa gyara jikinta irin na matar da kayan aikin matar, lalle mata sunna gyara, tun daga su dilka, kurkum, kujera, rigar dilka, itacen dilka, turare kai komai da komai dai a wajen matar nan akoy masu kyau da inganci , turatukan da Mama ta daukar mata sai da ta ji kamar ta bude ta yi ta sinsina a hancinta, turaruka masu kanshi , sanyin kanshi da saka nutsuwa a zuciya, daga nan suka wuce gidan aminiyar Maman , nanma sakonta ta amsa sannan suka wuce gidan su KHausar din dan Maman ta yiwa Maman su KHausar din barka da abin arziki, nan ta shaida mata an saka ranar ance nan da wata daya sannan ta ringa godiya dan Khausar ta kasa r8ke murnarta ta sanarwa Maman komai da komai , har maman ta rasa abin fada , sun jima sunna zantawa kafin su tafi gida Da wannan Khausar ta karra kusan sati a gidan su TAUFEEK, a kulun zata je wajen aikinta ta dawo ne, kuma a kulun din shine zai ajiyeta ya je ya daukota, ko fushi fushin da ta so masa na yannayin matarsa sharewa ta yi ta daukarwa kanta alkawarin zata gane me hakan ke nufi dan ta dauki mataki, Yumnah dai ba sa'arta bace ba sa'ar yinta bace, ko tana da wata matsala da itane bata sani ba zata bi a hankali idan ta gane sai ta magance in mai magantuwa ce, in kuwa ba mai magantuwa bace sai ta kama kanta, dan ba zata taba yarda wani abu na rashin da'a ya shiga tsakaninta da ita ba, bata ga dalili ba Ranar da zata koma gida sai da ta ji ba dadi a ranta, Hajia fadi take ta yi zamanta mana, itama ta yi sabo da ita harda na mamaki, dan Khausar akoy dadin zama ga girmama manya ga rashin kiywa, da kyar dai ta iya tafia bayan an cika boot da tsarabe tsarabe da dinkunnanta da kayayakinta tamkar wace ta je wata kasar ta shekare, Mama kuwa ta sakata daki ta mata nasiha mai kama da fada fada, ta yi mata nuni kan yafa dace ta dan gyara, sosai ta hadata da mutanen arzikin da zasu sake gogar da ita a hanya mai kyau ba lalataciya ba, irin tarayar nan da koda baka son gyarawa idan ka yi tsai ka ga yadda mutane ke gyarawar kaima sai ka tsinci kanka a ciki tsamo tsamo A lokacin da ya ajiyeta gida murna wajen yan uwanta ba'a magana Haka su mama ke saka albarka a tarin arzikin da ta dawo da shi, yan anguwa kuwa sunna leke da zunde da bakinsu da mamakin inda ta je har ta jima haka, Ko da Baba ya dawo shima farin ciki kamar me, kasa boyewa ya yi, nan ta nuna zata raraba kayan da yan uwanta Baba kuwa ya nuna aa ko daya summa ai ga sababin kaya nan na aure ta ajiye abinta itama ta ringa sakawa Haka baba ke daga yan jakunkunnan da takalma yana fadin" Ai zaki saka ko khausar din Aba?" Ita kuma tana dariya da fadin" Baba bara ka gani zan saka duka kaffff, kuma harda kwali" Ita dai Mama dariya take yi a ranta tana ayana' Allah ya sa Khausar din ta saka" Kwonci tashi har lokacin auren yan uwanta ya karaso, aka sha biki har biki dan kuwa an yi taro yan uwa da aminan arziki haka yan anguwa sun yi karra sosai an samu tarin gudunmuwa harda na mamaki, dama Aba bai yi sanya ba ya masu abinda ya dace daidai karfinsa haka kuma an ci an sha da anki din atampa daya da suka fitar har dare ya yi aka raka kowace dakinta, ya zamto a gidan a yanzu Khausar ta sake tsintar kanta daga ita sai ita domin Auta namiji ne kuma bama dakinsu daya ba, shi dakin Aba yake kwana Wannan sabon kadaici ya so ya dameta sosai, dan kuwa har sai da Mama ta yi da gaske sannan ta dan saku, ba dan ta warware ta cire komai a rai ba, sai dan irga yan kwanakin da take tunanin itana tana iya wayar gari da sunnan amarya dan kuwa a irgenta kwana duka duka hudu ya rage alkawarin Mujaheed da ya mata cewar za'a kawo sadakinta Sai dai shiru, Aba bai yi mata zancen an tuntubeshi kan maganar ba, ko aiki da take zuwa kuzarinta ragage ne, duda an kusa yayeta dan a yanzu ta haura wata biyu cikin na ukunta take, aiki ta koye shi daidai gwargwado, ama kuzari ya ragu a jikinta saboda tunani da neman mafita a cen kasan zuciyarta Ba sai an fada mata ba, damuwar iyayenta a duniya a yanzun itace Ba sai sun tsangwameta ko sun hannata zaman lafiya ba, ta kalli fuskarsu su kalli tata du safiya ta Allah a matsayinta da shekarunta sun isa su dami kwakwaluwarta da kwonciyar hankalinta Wannan dalilin ya sa koda yaushe wayarta a hannunta take, kunnenta kuwa na sauraro dan son jin sauti daga gare shi, sai dai kwana biyu na ragewa watan ya cika sai ta neme shi dif ta rasa, domin kiran da yake mata na sasafe da darenma idan ba zai zo ba sai ta nema ta rasa Sannu a hankali kwanakin da take irgawa suka shige, nan fa abin ya fara bayana a jikinta domin nan da nan ta fara neman fita a hayacinta, bata fahimtar komai har sai da aka bata kwana biyu a wajen aiki a tunaninsu bata da lafiya ne Wannan damuwa tata ta saka Mama a damuwa har ta tirketa ta ji dalilin rashin cin abincinta da yawan tunaninta Jin abinda yake faruwa ya saka Mama ranta ya baci, a gaskiya abin nan ya fara kona mata rai, ita da kanta a irgenta sau uku kennan Mujaheed yana fadin yau gobe, dan haka ta samu Aba da maganar ta sanar masa Su dukansu basu zaci cewa Fada Aba zai rufesu da shi ba sai da ta fada din, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, cewarsa in har ya yi niya ya shirya to ya fito din in kuwa bai fito ba ba lalle ba dole shi baya neman rabuwa karfi da yaji da yarsa, kuma ya amshi kadararsa ko wace iri ce!, Bacin ran wannan ya saka shi ficewa ya bar masu gidan tunda duku duku ya ki dawowa Sun wuni cikin tashin hankalin nan wani ya sake samunsu, domin kusan karfe hudu na yama aka yi salama cewar ta yi bako ana mata magana a kofar gida............. ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” *DA CIWO A ZUCIYATA* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” _MALLAKIN_ *SAJIDA NIJAR* *FREE BOOK NE* 2๏ธโƒฃ5๏ธโƒฃ LITATAFAN MARUBUCIYAR Duk karyar kada Yar mahaukaciya Neman na kaina Bani da zabi Bak'a ce Kutkale Makauniya ce Mage Duk nisan jifa Idan ka raina inda kake Dutse Alkalamin kadarata Bani da zabi Dakika Biyar Now *Da CIWO A ZUCIYATA* *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicรฉ Lait de nuit Parfums dรฉsodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94 *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ Sunna cikin tashin hankalin wannan su su kadai a gida wani ya same su, domin tana cikin dakinta tana jan carbi wani yaro ya shigo yace ana salama da ita , da ta tambayi waye sai cewa ya yi wani ne wannan dake zuwa koda yaushe wajenta ne Har ga Allah har gagawa take yi wajen mikewa daga saman salayarta ta cenza hijab da dan sauri ta leka ta sanarwa Mama sannan ta fito duda hasken gari ta fito hankali kwonce ta shiga duduba shi Ai kam shi din ne, da farar jalabiya a jikinsa yana tsaye hannu daya goye a bayansa daya a cikin aljihunsa yana ta faman kada kai kamar wanda ransa ke bace Da sasarfa ta gaishe shi bayan ta dan duka, sannan ta mike tsayinta tana kokarin yi masa bismillah kamar yadda suka saba idan ya zo wata mahaukaciyar mota ta nufo ta parker daf da tas har kamar zata gogi tasa Irin tashin hankalin da ta ga ya shiga sai da cikinta ya so murdawa, a hankali ta mayar da hannunta da ta fitar dan yi masa bismillah zuwa cikin gidansu Mata biyu ne suka fito, kamar yaya da kanwa haka Wace ke taunar cingan din ce ta bude cikin motarsa daga gaba ta dauko wayarsa tana ci gaba da tauna cingan din ta danna wayar hannunta ta shiga amsawa kamar haka" Gamu gashi bobo, yanzu fada min yaya zan yi in kashe localisation din" Daga dayan bangaren akai mata bayanin yadda zata kashe ainahin abinda ya basu damar gane inda ya zo daga fitowarsa daga gida bayan ta saka shi a kason kwana uku kennan Tana kashewa ta juya wajen motar tasa ta maka wayar da jikin madubin motar, ji kake tartsatsa karar fashewar madubin motar kafin ta karaso inda yake tsaye mundil a gabanta jikinsa sai rawa yake sai wurna wurnatu yake kai kace in ya sha iska ya dauketa yana iya makata da kasa, domin ita dinma a ginne take koda bata kai Khausar din ba to fa ta kusa kaita ne dan ko a yannayinta ba siririyar mace bace Kare masa kalo take yi tana taunar cingan din nan yana wani kas kas kas sannan ta juyo bangaren Khausar wace ke tsaye, ama kana ganninta ka ga wace ke shirye ta iya aukawa da gudu in ya kama dan kuwa abinda ya dakatar da ita ta yiwu maganar da yake yawan fada mata ne cewa shi din tsayayen namiji ne a gidansa da waje! "Elhaji Mujaheed kennan, wai tsakaninka da Allah a tunaninka shikenan har ka sha bulus ? Kai yanzu a cikin kwakwaluwarka tunaninka nima irin sauran biyun cen ne da ka hade gida daya kake wulakantawa? Ai ina tunanin tun a lokacin da na ki ka hadeni gida daya da matanka ya dace ka san ni ba irinsu bace, ko nace tunda ka san me ka aura ya dace ka taka a hankali, kai yanzu har wani sankon dan daba ne a haka? Kai har dan jagaliya ne? Shine ka tarda babanmu kasuwa yana cinikin hatsinsa ka tayar masa da hankali a cikin jama'a kana masa ikirarin a min magana aure kace zaka yi ba ruwana a cikin maganar kuma gida daya zaka hadani da matar in ba haka ba daular da ake mora sanadinka tsaf tana iya tashi daga sunnanmu? To kai ai baka san da tsohuwar yar iska kake zaune ba sai yanzu, gidan nan da ka bada baka ga sai da aka baka nono ka sha ka kuka damuki abinda ka damuka ba kafin ka yi kyautarsa? Ai kyautar gida da ka yi tun kafin ka aure ni ne , a duniya muka watse ka bada kyauta dan ka yaba kuma sai da saurayina ya tabatar da sunnan gida sunnana ke sama kafin na yarda da kyauta ta zama tawa, kai yanzu kana tunanin dan kana da yan kudaden nan ka fini mutane ne ko wani haukan ke kada maka cewa kana iya kwace gida? Da nake ce maka daga ni ka rufe ka dauki maganar a tatsuniya kennan shine ka nufo wannan zaka kawo min mu jera??????" Ta fadi wannan din tana nuno Khausar wace idannuwanta suka yi waje tsabar tsoro da firgicin abinda yake faruwa, haka kuma kafin kace meye wannan an fara tsalakowa kallonsu, kuma an rasa mai cewa ufan domin fadan kamar mai digi ne da dadin kallo a lokacin har sai da matar nan ta nufota a tsayen da take bata ankara ba ta kama hijabinta ta aniya neman kwashe shi daga jikinta Nan fa hankalinta ya idasa tashi, jikinta haka yake rawa tana rikewa matar na ja Da karfi makociyarsu ta karaso ta aniya shiga tsakani haka yayar matar itama ta shiga Karshe dai da kyar makota uku suka hanna wannan lamari da tuni ya rikita hankalin Khausar ya kuma so ya zauta tunaninta, Tunda take, tunda ta malaki hankalin kanta a anguwar nan bata fito ba fan kwali ba, sai gashi a yai za'a cire mata hijabinta daya da ya fi sutura a jikinta domin a kasan ba wani abin a zo a gani bane dan kuwa zani ne kawai saman yar ficiciyar riga ta shan iska "Au, fadan area zaku mayar da shi ko ku din danginta ne?" Matar ta fada da tarin rashin kunya tana harar makociyar Mama Makociyar Mama da suke abin arziki sosai ta tareta tana fadin" Eh mu iyayenta ne, da komaima, babu abinda zai saka ki cire mata hijab a banza a wofi, mema ta maki ne yarinyar da ba komai take cewa ba? Shekarunta nawa a anguwar nan bata taba yi da kowa ba, haka a makaranta da tana yi da koda sau daya ne an sani, to koma menene ba zaki ci mata zarafi a gaban kartin maza ba, ku kuwa su Isuhu kunna tsaitsaye me kuke jira ku gama gani kafin ku tsawatar ku hanna a zo har anguwa a wulakanta yar gidan mamuda? Ai kam ba adalci a lamarinku dan na tabata da shine walahi sai inda karfinsa ya kare!" Sai da ta yi wannan maganar ne kuma samarin suka shiga hargowar rabiyar fadan da yannayi irin na dabacin nan sunna nuna ko ta bari ko su far mata, tuni aka samu aka sake matsa Khausar hanyar gida, da lalube ta juya tana son bude gidan ta shige ta ga mahaifiyarta ta ja kofar ta fito domin ta kasa hakuri zuciyarta sai harbawa take cike da tsoron menene wannan din kuma Da wani yannayi na yan daba matar nan ta karewa makociyar mama kallo a lokacin da Mamanma ta fito ta ce" Mama, kina jina? Zamu tafi, ama ba hakan na nufin zan kyale yarki bane innhar bata fita daga harkar wancen mutumen ba, da kika ganshi a cen mijina ne, a yanzu dai a gidansa nice ta uku, a cikinmu duka haka kirarmu take dan yana sin manyan mata, Mama nima mun hadu a yawon ta zubar da shi ne ya aureni , ya bamu gida ya bani mota, wannan fa zan iya ce maki zaku samu , sai dai in zaku iya jure hali irin nasa da kuma nawa, dan na rantse maki har saman gadonta yana iya kawo mace ya warwareta sala sala bale idan ya rainata, wulakanci kala kala da gori zata ringa gani a rayuwa dan baya auren yayan masu kudi sai ya nemi yayan talakawa ya wankesu tsaf ya amshi yar ko me ta je ta fada a gida sai dai a bata hakuri a dawo da ita, ga kuma nawa a gefe, dan da kika ganni a nan mama abin kunya ne a cikin kawaye ace wancen ba wada haushin ya karro min wata, babu abinda na rasa shima ya sani, in bama masifa ba shi fa halitar da zai gamsar da matan irinmuma bashi da ita ama haka yake aurowa ya halaka a gida, ai na fada maka ni da kai shege ka fasa Walahi sau dubu zaka hau mace sai na samu jikeken Kato mai sunna kato na kawar da ฦ™ishirwa haka kuma mun riga mun zamewa junna karfen kafa dan ba kari ko uban wa ya yi maka tsaye nice nan na fada, in kuma kun yi gardama ku aura masa ita , ke ki yarda ki aure shi ki zo ki sameni ina nan ina jiranki dan sai na........."......................... ........ Kalaman da kunnayenta suka iya ji kennan ta samu ta karasa dakin Aba da gudu ta zube nan saman kujera ta rufe kanta da hijabinta tana rizgar kuka tamkar kanta zai rabe biyu Wasa wasa Mama ta dauki minti talatin kafin take shigowa, ko tace take shigowa tare da Aba, wanda idannuwansa suka gama kadewa suka yi jajajir har hada hanya yake yi wajen karasawa inda Khausar din ke kwonce Murya a tausashe bayan ya zauna ya ce" Kuka kike yi tun dazu? So kike yi ki hadawa kanki ciwo ne? Tashi mana autana, ya isa hakanan" Tunda ta ji muryarsa a farko kukan ya tsaya , tana jin me ya fada ta fashe da wani kukan mai karfin gaske ta dago fuskarta da ta yi jajajir gashin idonta ya hade ya yi wani irin luhu luhu da shi ta zubawa Baba idon tana girgiza kai a raunane ta sake mayar da kanta ta dukunkune a cikin hijabinta cike da jin kunyar baban da kuma tarin kunyar kalaman da matar nan ta ringa fada a gaban su Mama wa'inda ita dai a kankin kanta tunda Allah ya haliceta babu inda ta tsaya ta ji kalamai mararsa da'a irin wadinnan, sam bata tare da mutane masu gurguwar yare, haka a anguwa bata shige shigen yaren mata masu sakin harshe sunna maganar mazajensu a bayane ba dan raha ba, shi yasa abin ya wani irin daketa ta kasa kallon kowa a dakin Auta ne ya karasa ya zauna yana kama hijabin nata ya ce" Aunty, kin ga kuwa yadda aka musu? Aba fa ya je har gidan da ni yace to kar ya kuma gannin kafar kowa a gidanmu, in fada maki harda shi uncle din Aba yace ya rabaku kar ya kuma ji, kuma sai ki ringa yin kuka? Tunda Mama ta yi kiran Aba muka fito daga kasuwa muka zo fa" A birkice ta dago, ta dubi Aba, har lebenta na rawa rawa ta ce" Aba, kar ya kuma zuwa? To wa zai aureni in bai zo ba Aba?" Mama dake share hawaye a kofar dakin ta shigo kamar an sanyota ta zubawa Khausar ido Muryarta a raunane ta ce" Ke? Kina da hankali kuwa?, Ko tunanin kin gaza samun mijin ya fara taba kwakwaluwarki ne? Kina nufin in akace ya zo ya aureki zaki iya yarda bayan duka kaf abinda kika gani kika kuma ji? Yau ba dan Allah ya sa ana mutunci da makota ba ai da sai sun gama wulakantaki tsaf sai dai ki mutu in mutuwa zaki yi dan kuwa da y'ar bariki ta hado ki fa Khausar!, Ke wai shekarunkima nawa ne? Ko hamsin ne da ke sai aka yi me? Ko mun mutu mun barki ke daya a gidan nan sai aka yi me? A kanmu farau ne? Ke ba yar bariki bace, ke ba mai wulakanta mazan bace, kadararki ce fa ta zo a haka kuma shikenan sai ki dauki ciwo mai tsanani ki sakawa zuciyarki? Khausar ina sane da halin da kike ciki na ki baki dama ne kar abin ya zama shirme ki kasa rike kanki a cikin gida, ama tunda haka ne ya isa haka, ya isa hakanan khausar, miji idan ya samu to in bai samu ba babu yadda zamu yi, abinda na sani daya ne tak shine idan kika wulakanta kanki ta hanyar bin maza kin cucemu kuma kin cuci kanki, ki ci gaba da kula da mutuncin kanki da namu har yadda Allah ya yi!" Daga haka Maman ta yi gaba ta barsu da binta da Kallo, Baba ne ya tausasa muryarsa ya yi mata nasiha sosai , kafin shima ya tashi ya fice masalaci Da raunin zuciya da komai ta karasa wajen salaya ta samu ta yi sallah sannan ta kwonta a nan har dare ya fara yi Kiran da wayarta ke yi ya sakata laluba ido har yana rufe mata dan abinda ke ranta ta daga bayan ta ga sunnan mai kiran ta yi masa salama a sanyayen da yannayinta yake Kasancewarsa mutun daya kwalin kwal dake saurin cenkar yannayinta, hakan ce ta kasance yanzunma, harma kamar ya mike ya fice daga cikin mutane ne ko menene muryarsa a tausashe ya ce" Me yake damunki? Dazu ance baki je aiki ba baki da lafiya, wht hpn?" Ya karashe hapn din yana gagawar dakatar da nurse din da ta shigo da nufin yin magana kan list din wani magani da aka rubuta za'a ba wani patient a asibitin, domin du a rikice suke tunda ya masu dirar ba zata sai guje guje suke dan kar ya kama su da wani laifin domin ya samu abinda ba daidai ba yana cikin fadan ne ya ce da su ohk tunda haka ne da shi suke maganar, kuma sun san me hakan ke nufi shine fa du suka rikice yana office din docter Ibrahim sunna maganar abinda yake faruwa a asibitin ne ya danna mata kira Rabewa Nurse din ta yi kanta a kasa , shi kuwa ya saurara yana son jin amsa daga Khausar A hankali ya furta" Khausar? Ko kin yi barci ne?" Khausar ta lumshe idannuwanta, a hankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin gurbin idannuwanta, muryarta a shake ta ce" Aa, ban yi ba" "Kuka kike yi ne? " Ya fada a sanyayen da ya saka nurse din nan da mahaukacin mamaki satar kallonsa, domin tunda take bata taba jin dai ya yi doguwar fira da su ba in ba shafar aiki ya yi ba, ama kuma in ya kamaka da laifi a kan marar lafiya yadda ka san zai cinyeka danye haka yake damkarka, a ranta ta ayana' ta yiwu da Hajia yake' watau Mama, dan kuwa du duniya ita kadai ce suka san ko asibitin ta zo idan zai mata magana to fa a sanyaye muryarsa take, dan kuwa hajia kakarsa su caku be tace ba'a yi yace sai an yi, matarsa kuwa basu taba ganninta ba, basu san yaya mu'amalarsu take ba "Rashin lafiyar ne yau ake yiwa kuka? Yayama aka yi baki da lafiya ama baki sanar min ba? Kin sha magani ne????" Ya sake fada a hankali sosai a kuma sanyaye sai dai kuma abin auna zafin

Chapter 18 of 47