Share this page
mahaifiyarsu cewa ta ba KAUSAR ta samu wani abin da ta ga ya dace ta yiwa TAUFEEK kyauta na tayashi murnar aurensa, duda kadan ne ta kamanta , sannan suma zasu yiwa iyayensa daga bangarensu Sosai Mama ta yi farin cikin haka, kuma kwarai ta san hakan ya yi, domin ko rijiya tana son kari kuma ita kula dadi ne da ita , idan har suka kamanta ta tabata za'a ji dadin hakan domin iyayen na TAUFEEK masu karamci ne, sosai ta yiwa mijinta godiya da fatan alkhairi, ita ta san auren namiji mai zuciya ya fi wani mai kudin, domin mijinta Allah ya masa zuciyar nema da kuma sannin ya kamata, mutun mai matukar jajircewa a kan iyalansa, azumin nan aka yi aka gama bai taba fashin yawon kasuwa ba, kuma a kadan yana shigowa da ribar dubu takwas in kasuwa ta yi mugun dadi har sama da haka, in kuwa kasuwa ta cije wani sa'in har kasa da biyar, a haka yake cire yan bukatunsu na su yan fruits haka ko kifi haka sauran kuwa ya juye a asusun da ta tabata yanzu kam ya yi nauyi sosai, kuma a haka ya cire na hidimtawa yaron da yake hidimtawa y'arsa, lalle zata iya cewa ita kam ta dace duniya da kiyama tana fatan ฦดaฦดanta su samu mazaje masu fahimta da fita hakin iyali Bayan ya tafi ta samu su KAUSAR din a daki ta bata kudaden da suka sakata ihun murna da farin ciki, zuciyarta cike da kauna da tausayin mahaifinta, a duniya tana fatan Allah ya bata aikin da zata talafi mahaifinsu da mahaifiyarsu da shi, iyayenta sunne iyaye talakawa masu zuciyar fita hakin ya'yan da bata taba gani ba a duniya, tana sonsu tana tausaya masu tana taya su kula da tarbiyarta kuma ta yi alkawarin in sha Allah ba zata kasance daya daga cikin ya'yan dake jazawa iyayensu azabar ubangiji ta hanyar yada badala a doron kasa ba....nan fa suka shiga tunane tunane da neman abinda ya dace ta ba TAUFEEK matsayin gift, su ce wannan su ce wancen, har dai kansu ya kule suka rasa mafita, sun tsaya a tsakanin biyu, agogo ko Turare....sai dai shima sun fadi ne dan jin dadi dan kuwa ita ta san a turarukan TAUFEEK da wahala in yanada na kasa da dubu talatin , hakama agogon hannayensa bama zata iya kidaya kudinsu ba dan ta tabata masu tsadar gaske ne, maganar suka ajiye kan zasu bincika wajen kawayensu yan gayu su ji sunnayen turaruka sai su zabo na daidai kudin Wannan kennan ___________________________________ Kwana biyu tsakani KAUSAR da A'isha suka shirya suka je gidan aminiyar Aishan, dan ta nacewa yayarta cewa dan Allah ta zo su je dan matar ta iya mak'up tana so su dauki ranar da zata masu domin aure dai yau saura kwana takwas cif, anko dinsu kansu daya ne kawai basu amsa ba Da kyar suka samu gidan, domin ta jima rabonta da ita, sunna dai haduwa a school lokaci zuwa lokaci dan ita Usainar yanzu ta fi ba harkar kwaliyarta karfi babar mai harkar mak'up ce a garin Sun samu tarba ta mutunci, sun kuma taki Sa'a ranar hutunta ce bata kwaliya dan haka suka zauna suka shiga fira KAUSAR kam da hankali du ya dauku a irin sansanyan kanshin da falon matar ke yi na turaran wuta ta gaza hakuri ta ce" Kai Usaina ama dakin nan naki na kanshi mai dadi walahi, haka nake son kanshi mai sanyi da ratsa zuciya" Murmushi Usaina ta yi tana fadin" Lah aunty ki ce kanshin akoyshi har yanzu? Kin kuwa san tun jiya da dare da na turarawa dakin ban turara yau ba, sai da yama nake son turarawa, ai matar nan ta iya hada turare na kasa da kasa, haka na fesawar da kuma humurar akoy wace sai ta yi sati a jikin tufafi kanshin na nan radau, ai baban Abdul baya hanna kudi in dai turaran HAJIA FUSAM za'a siya" Aisha dake murmushin itama tana amsar wanda ta mikowa KAUSAR ta sinsina sai lumshe ido take yi itama ta sinsina ta ce" Kai, ama kawa wannan da tsada ko? Na san wannan in zaka shiga sia ka shirya" Usaina ta sake mikewa ta dauko mata turarukan ta ce" Ke kuw kawata, abu mai kyau ai shi ke siyar da kansa, tsada kuma ai karkon kennan, balema har ga Allah kayanta ba tsada, ga kyautatawa, kw harda gift take sako maka bayan na kudinka fa, kin ga wannan gift din ne , in takarkare maki kin ga dai baban abdul babban mutun ne ko? To walahi turaranta ne yake aiki da shi yanzu, cewa yake yi ko irin wunin office ya kama shi in ya je sake alwallah haka zai ji kanshin na tashi a ruwan, ke abokiyar zamana tun tana jin haushin hakan har ta hakura , nan fa yake amsar turaran wutar wai in zai kwana wajenta ya je da shi, ke dai har abu ya isheta ta nemi Hajia FUSAM itama ta shige, ni yanzu a gidan nan kin ga harta maina a wajenta nake siya da sabulu nawa da na yaranki, kin san kuwa ai kyau ya sa na nace" Itama Aisha yanzun dariya ta yi dole dan yadfa Usaina ta yi, sai take ji a zuciyarta kai dolema ta samu mu'amala da matar ko dan ta dan gyagyara masu harka, ah to magana ta kanshi da gyara wa ya ki? Bale ance da sauki ai kawai zata gwada sa'arta, tana shirin tambaytar numbar natar KAUSAR dake ta faman sinsinar na ruwan dake hannunta ta ce" Usaina kuma a ina take? Ina so, ni kam tunda kin ce harda na maza ina son na mazan" Usaina ta ce" Aunty yar Nijar ce ai, yanzu haka dai tana damagaran kuma ba inda bata aika sako, ga numbartama +227 97 82 44 94 , sunnanta kuwa shine HAJIA FUSAM" Numbar suka kwafa sunna jin farin cikin hakan, dan kuwa irin yadda turaran ke gyare a daure da wata fulawa mai kyau ta tabata a kanti ba zasu samu irinsa ba, dan kuwa hadawa ne take yi da tsararun nagartatun turarukanta su bata kanshi mai ma'ana da sace zuciya...., Sai daga baya nema suka tsayar da lokacin kwaliyar, ita da kanta ta ce su zo karfe goma ta masu kafin dai a dawo daga daurin aure in sha Allah Sun dan jima a gidanta kafin suke yi mata salama, Har sun kusa fita ta biyo su da sako leda baka ta mikawa KAUSAR tana murmushi ta ce" Aunty ga wannan, kin ga yannayin fatarmu kusan daya ce mu ba baki ba mu ba haske bau ba, ki ringa shafawa fuskar kafin ranar kwaliyar, na tabata sai kin siya da kanki a wajen hajia FUSAM" Godiya sukai mata sosai Wannan shine mafarin shirye shiryen auren TAUFEEK Tunda satin auren ya kama kuwa ya zamto babu mai lokacin kansa, duka bangaren biyu cikin shige da ficen shirye shirye suke, harta Kausar ba'a barta a baya ba domin bata zauna ba ta yi nan ta yi nan, ga wani abinda ya faranta mata rai ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” *DA CIWO A ZUCIYATA* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” _MALLAKIN_ *SAJIDA NIJAR* *FREE BOOK NE* 1๏ธโƒฃ1๏ธโƒฃ LITATAFAN MARUBUCIYAR Duk karyar kada Yar mahaukaciya Neman na kaina Bani da zabi Bak'a ce Kutkale Makauniya ce Mage Duk nisan jifa Idan ka raina inda kake Dutse Alkalamin kadarata Bani da zabi Dakika Biyar Now *Da CIWO A ZUCIYATA* *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicรฉ Lait de nuit Parfums dรฉsodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษ“i wannan number 97 82 44 94 *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ Ga wani abinda ya faranta mata rai shine sakon kyautar da zata yiwa Taufeek, gefe guda kuwa Elhaji ya zo kuma ta mayar masa da kudin ama abin mamaki sai ya je ya duka da kansa gaban Mama yace da ita kudin nan ba rokarsa ta yi ba, haka kuma yana iya ba wanima a titi bale wace yake neman aure, da kyar Mama ta amshi kudin, shima dan ya bata kunya sosai irin yadda ya duka din, duda ta san ta girme shi sosai domin dan yanada mata da ya'ya ba wani baba bane, kawai kudi ne suka kwonta ya tara mata abinsa, su kuwa suke gasar haihuwa kamar yadda aka saba Ana gobe auren Mama da makociyarta suka je gidan suka kai gumbar da suka yi da nono da siga a cikin manya kwala shar shar shar da ledar goron HAJIA suka tare a bangaren Hajiar dan kuwa basu je direct wajen Mamansa ba, wajen Hajiar suka sauka makociyar Mama sai mamakin wai dama nan ne gidan su TAUFEEK take yi, domin irin yadda suke ganninsa bajaja a anguwarsu sun zata da kudin ama bai kai haka ba, saima da ta ga abin mamaki kyautar nan da suka zo da ita kamar sun kawo duniya guda, domin HAJIA haka take murna tana farin ciki ta saka yan aiki suka dauka ta ja su Maman suka nufi ciki wajen matan nan wani kallon yacewa makociyar Mama gyara kar ki kifa, ga abin gyare gyare na tarban baki da murnar babar rana, ga yannayin matan kowace da irin nata salo, sai katon falon ya bada kala babu wajen da ba abin kallon talaka ba A haka suka karasa sama wajen Mama suka wuce Hamdiya da bakuwarta ta sha kunshi da kitso kai kace itace amaryar dan a yau dinma dinkin dake jikinta an watsa da zinari ba kannanun kudo bane dan a yagawa kishiyoyi da bakinsu sai yadda hannu take tana karbar baki ta ko'ina dan sun yi gaya sosai ko dan su caji aljihun Elhaji wanda murnar wannan rana ta saka ya bude bakin aljihu fiye da da mikawa yake yi du abinda aka bukata ba kauron hannu Sosai Mama ta yi farin cikin gannin sakon nan, nan take ta saka aka ringa sakawa a frij tana fadin an taimaketa ba sai ta yi ba, ta kuwa manta da maganar dan faro faro mai sanyi na baki, haka take yiwa Mama godiya har sai da ta ji kunya ta lulubeta sannan ta rike su Mama aka shiga hada hada har dai dare ya yi kafin ta sake su tana faman maimaicin fadin" Maman KAUSAR dan Allah fa a zo da wuri goben, kuma ki cewa KAUSAR na ga ta zo yau, koda yake TAUFEEK yace dazu ya leka ya kai mata shadarsu ta diner kuma ya ajiyesu wajen kunshi, ni dai kii fada mata saura gobe ta yi zamanta sai ta ga an hantse na ganta a nan" Mama kam dariya take yi aka saka direba ya dawo da su gida da tarin alkhairi irin na girke girken gidan bikin da ake tata yi ana zubawa baki Bayan tafiyar su Mama, Maman TAUFEEK na cikin hidindimu kira ya sameta daga wajen mijinta Tana shiga ta same shi tsaye a falonsa na farko yannayin fuskarsa a hade tamkar wani abin ya bata masa rai Tun kafin ta zauna ya tareta da yannayi na bacin rai ya ce" Me nake ji haka a wajen yan uwanki ne Umin Boy?, Yaya zaki ki saka su a lamarin hidimar auren nan bayan sunna nan sunna kaf kaf da ransu sunna fatan birgeki? Me yasa komai sai dai ki tare ko dan ke kika haifi Elhaji karami ne?" Da mamaki ta kafe shi da ido, sai kuma ta sauke dubanta a kan matansa, sun sha kwaliya tamkar zasu je gasar kyau, kowace sai walwali take yi haka kuma fuskarsu a sake ainun da suka yi ifo hudu A hankali ta ja numfashi muryarta a raunane ta ce" Ka yi hakuri, ba za'a sake ba, in bandama abin iyayen Elhaji karami har sai an saka su abu nasu? Ni a sama nake ina fama da bakin da suka zo daga gida ai gidan baki daya a hannunsu yake, inace harta masu dafa abincin maza da aka dauko kannin hajia ne ko menene?" Wani irin makuku ya zo ya tokare wuyan Hajiar, har ga Allah ta tsani in ana kwatance a ringa nuna kanninta dan tuwo tuwo ne dan a habaicin da suke mata har nunawa ake yi kamar dan daudu, wani takaici ya kamata su da suka zo dan su saka yau ranar da ta fi kowace rana mahinmanci a duniyarta mijinta ya fatataketa ta yadda har a daura auren ba zata fahimci komai ba dan bacin rai su ga ta tsiya sai gashi dan bakin munafurci irin nata ta wani bashi hakuri tana sinne kai bakar munafuka Elhaji kuwa sai ya cire kai daga yannayinta ya ce" To a kiyaye, taron nan shine na farko a gidana kuma shine mafi daraja da zan gabatar dan auren yarona ne baba kuma namiji daya kwal, babu wace zan saurarawa idan ta dagan hankali ciki harda ke mahaifiyarsa, ku je ku bani waje dan baki ne da ni kuka kirayeni na zata wani abin ne mai mahimmanci, in sha Allah gobe daurin auren safe zamu yi ina son gama abinda ke gabana na zo na dan huta" Wannan shine bata lokaci bukata bata biya ba, a haka suka bar wajen nasa baki dayansu kowace ta nufi inda ta fi wayo, Mama kuwa ta ki nuna fushinta ta ci gaba fa hidindimunta sama da kasa domin su dakunnansu suka wuce , hakan ya sa ta rungumi abinta hankali kwonce ta ci gaba da hada hadarta da fatan du wani abu da suke nufi da ita ya kare masu dan ba zata biyewa fitintinnunsu a irin wannan babar ranar ba A lokacin da su Maman KAUSAR suka dawo gida nan suka baje ana ta raraba abincin ana mikawa makota sunna ta maida kirki da datako na wannan ahali, lalle abin ya ba makociyar Mama mamaki kuma irin yadda ta ringa maganar cewa take yi ai komaima sai a yiwa bayin Allan nan sun san darajar dan Adam........ Su Kausar kam kowace na nata uzurin ama kuma sunna jin firarakin su Maman har dare ya yi sosai ta mike ta shafa sabulun nan na wajen FUSAM ta barshi ya dan huta a fuskarta sannan ta wanke tana shafa fuskar ita da kanta cike da mamakin irin santsin da fatar nata ke yi, wannan dan fari farin na fatarta du ya fita yanzun sai wani sheki da fatar take yi ko bata shafa mai ba bata mata futu futun nan A nutse ta kwonta a wajenta zuciyarta cike da farin ciki da fatan gannin babar ranar amini, dan uwa, aboki, yaya a wajenta, lalle wannan rana tana daga daga cikin ranakun da take fatan gani a duniya na alkhairi, Murmushi ta yi tana dafe kitson da kai mata na hannu kora baya kannanu rass tana tunanin wai atach irin na kitson nan suka siyo rauda rauda za'a saka masu a keya, ita kam bata san ko zata iya yarda da wannan bidi'ar ba, sai kuma ta sake sakin murmushi a hankali ta furta" Gobe dai in sha Allah zan raka ka dakinka Besty, ina farin cikin hakan, Allah ya nuna mana ya da matarka ce har aljanna".... A'isha ta yi murmushi itama tana jin Adu'ar yayar tata, a hankali ta lumshe idannuwanta tana tunanin gobe, watau gobe idan da rai da lafia sai sun kafawa yayarsu tarihin da bata shirya ba, domin sai sun yi mata kwaliyar da bata taba yi a fuskarta ba, har fata take yi safia ta yi a yi ta ga yaya fuskar zata dawo, har aunawa take yi a zuciyarta shin yaya kwaliyar zata amshi yayarsu? Ta tabata wanda baya kwaliya idan ya yi yana yin kyau, to ama ita yayar tasu zata amince ne?.....haka dai kowa da irin zumudin dake zuciyarsa suka yi barcinsu sunna dan tsinkayo firar mahaifinsu dake ta murnar an yi murnar kyautarsu duda ba wani taka kara ta yi ta karya ba.............. Da safe kusan karfe tara Aba ya fice a gidan da nufin wucewa wajen daurin auren direct, Mama kuwa ta gama kimtsawa ama jira take yan matanta su gama hada kayansu su fita tare ita zata je da yan anguwa ne su kuwa zasu wuce wajen kwaliya ne Karfe tara da minti arba'in da yan kai suka sauka a gidan Usaina da akwatin kayansu madaidaiciya mai dauke da suturun da zasu cenza suka ajiye kayan sunna kallon yadda dakin kwaliyar nata ya kawatu masha Allah kamar ba a kasar hausa ba, har sai da KAUSAR ta ji tana sha'awar malakar dakin kwaliya Rukaya ce aka fara dandasawa kwaliyar, KAUSAR na kallo tana jin anya zata iya kuwa wannan hoda haka? Ana tsaka da yin kwaliyar ta lalubo wayarta gannin karfe goma ta gota sosai ta shiga gwada neman layin TAUFEEK tana tunanin zuwa yanzu ai ta yiwu har sun dawo gida dan karfe tara ne daurin auren Kiran farko ba'a daga ba, sai a na biyu ne aka daga Muryarsa a hankali, cike da kamala ya furta" Asalamu alaiki wa rahamatullah" Cike da murmushi ta furta" Wa iyaka, Sanar min abin farin ciki Ango....." A hankali ya yi dan murmushi yana dan tare hularsa da abokinsa amininsa kuma bakonsa ke son ja dan tsokana , ya ce" KAUSAR...." KAUSAR ta yi dan tsai jin muryar nasa wata iri, a hankali ta ce" Lafiyarka kuwa? Ko kukan angwaye ka yi da aka daura?" Murmushi ne ya subuce masa jin abinda ta fada, sai kuma muryar abokin nasa na fadin" Bani ita, KAUSAR yaya aka yi kika yi wannan rashin kirkin kika ki zuwa ki rakamu wajen daurin auren bestynki? Bestyn kennan? Gayanan yana ta kuka muna rike shi wai ango ne shi" Yar dariya ce ta subuce mata tana zarro ido ta ce" Lah, ka zo? Na shiga ukuna yau da tsokana, ai ganinan na fi so in ya dawo na wuni inai masa nasiha sannan da ni za'a rakashi dakinsa danma kar ku cutar min shi" Kasancewar sun saba dama, idan sun hadu ko a waya ne sai sun yi ta tsokanar junna sunaiwa junna neman rigima mai ban dariya shi yace shine bestyn TAUFEEK, ita tace yaushema ai shima ya sani ya kauce ya bata waje bata son rigima dai da sauransu , hakan ce yanzunma , tana ta murmushi ta ce" Gaskiya ni ka bashi wayar sai nake jinsa kamar a takure, me ka masa ne dan bana nan?" TAUFEEK dake kallon titi direba na tuka su shi da Alhhusain ya yi murmurshi ya sake zubawa hanyar ido har suka karaso yana jin rikicin amininsa da aminiyarsa ya amshe wayar a tausashe ya ce" Ki tabata na ganki in ba haka ba ina iya yin fushi KAUSAR" Zata bashi amsa ya katse kiran yana kallon kiran YUMNAH dake shigowa Murmushi ya yi ya ki dagawa saboda sun karaso gida ne ana ta busa ana hayaniya kala kala idan yace zai daga ba zata ji shi ba sai ya soke wayar a aljihun rigarsa ta ciki a nutse ya ringa shiga jama'a murmushi kwonce a saman fuskarsa yana cikin shiga irin ta danyan yadi mai laushin gaske, wanda laushinsa ne zai nuna maka karkonsa da kudinsa a ido, mai dan duhun haske ama ya dauki zubi madaidaici a babar rigar, sai hula nutsatsiya mai yannayi da suturar jikinsa Daria take yi bayan ta kashe ta yi ido hudu da Aisha Haba ta dafe ta ce" Wannan abin na idannuwanki bakya ji ya maki rumf A'isha? Innalilahi wannan ni a titi ai ba zan shedaki ba, uw awara jarumar indian film dai wannan hanci an sake janshi haka?" Aisha ta saki murmushi itama ta ce" Aunty saura ke taso ki ga a maki mu tafi kar a cinye miyar kari fa" Kausar ta mike tana cire katon hijabinta ta karasa tana sake kallon kitson yadda aka boye shi a bayan daurin dan kwalin kamar ba kari ba, sai dai yadda ya malalu ai mai hankali dai ya san ba gashin bahaushe bane Tana kallon Usaina dake hada kalolin hoda dan ta fitar da kalar fuskarta ta ce" Ama Usaina ni ba zaki saka min abin karin ba ko? Ni dai gaskiya kin ga wannan katon ribom din nake so nawa yake shi? Ni karin gashin nan sam bana so" Usaina ta yi murmushi ta ce" Aunty, tsaya mu gama sai mu ga in ribom din zaki fi jin dadi a jikinki sai a saka shi, shima ai yanada girma sosai kuma kasa kasaa muke saka shi sai dauri ya hau kansa ya zauna, ama shi daurin da ake masa simple ne irin na zahrah buhari dai haka" Ita dai sarautar Allah ta zubawa ido aka ringa juya fuskarta nan a juyo nan, ama ta ki a saka mata abin saman ido mai kalolin nan, sai dai sun ci karfimta gashin ido sai da suka saka mata madaidaici daidai da yannayin fuskarta, haka kuma jan bakin Nude ne aka saka mata ba mai karfi bane kuma ba'a yi mata barbada kumatu ba, kwaliyarta dai simple ce, kwalin nema ya so tsayar da su domin da kyar idon ya daina hawaye aka diga mata abin wanke cikin ido idon ya yi haske sosai sannan ta mike ta dauki nata lesh din itama ta zagaya baya dan sakawa domin sai ta saka za'a daura mata dan kwali Hankali tashe ta yaye labulen dake karewa ta ce" ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” *DA CIWO A ZUCIYATA* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”โคโ€๐Ÿฉนโคโ€๐Ÿฉน๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’” _MALLAKIN_ *SAJIDA NIJAR* *FREE BOOK NE* 1๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ LITATAFAN MARUBUCIYAR Duk karyar kada Yar mahaukaciya Neman na kaina Bani da zabi Bak'a ce Kutkale Makauniya ce Mage Duk nisan jifa Idan ka raina inda kake Dutse Alkalamin kadarata Bani da zabi Dakika Biyar Now *Da CIWO A ZUCIYATA* *Tallah, tallah, tallah* *SECRET DE LA FEMME DU MANGA* _Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_ Farar Humura Bakar Humura Humura special, humura de bain Humura epicรฉ Lait de nuit Parfums dรฉsodorisant Parfums rideau et dras Lait de nuit Alkam Kulakcam *Waษ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa* Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes *Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:* mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ Hajiya Fusam na zaune a

Chapter 8 of 47