da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Ya dan jima zaune sunna dan tataunawa kafin ya mike gannin har tara ta gota kuma ga ayyukan dake gabansa ya juya yana kokarin tafia Elhaji ya kirayi sunnansa yana kallonsa
Juyowa ya yi dan kiran yana masa ya shiga magana
Da kula ya ce" Shi rike kashi a ciki bashi da wani anfani, Ni kuwa nan da ka ganni bana tunanin in zan iya hakurin jure kallonka a wani yannayi na tsayin lokaci, idan har baka yi kokarin ganin ka samawa kanka mafita ba nine nan zan sama maka ita da yardar Ubangiji, ka ji da rigingimmunma ya isheka ba sai ya hadu da rikicin zuciya ba, mu wuni lafiya"
Tsakani da Allah a yadda ya zubawa abansa ido , ido rufe so yake ya gane inda ya dosa, sai dai sam bai bashi damar haka ba ya sake daure fuska ya cire kai daga dubansa , a dole ya fice yana ta tunanin me magangannun nan ke nufi? Fadanma da ya yi tunanin zai masa bai masa ba sai wasu yare gasunnan dai...., Ajiyar zuciya ya sauke kawai ya ci gaba da HULDODIN gabansa , a dole ranar bai je asibiti ba dan abubuwa sun masa yawa wuni ya yi yana aikin dukiyar mahaifinsa har yama ta yi sannan ya sake yin wanka ya saka sasaukan yadi mai ruwan madara tassss ya fito a nutse ya nufi Masallacin anguwar
Bayan an fito daga sallah ya samu kansa da sake gwada layinta, still dai yana a rufe...., Wani abu mai zafi ya tsaye masa a wuya, dan haka rai bace ya nufi ciki ya karasa bangaren Hajia dake turara turaran jiji a filin gidanta ya dogane da yannayin nan nasa mai kamewa sosai da tsari a lafuzansa ya ce" Dauko hijab dinki ki rakani"
Hajia ta dan zuba masa ido ta shiga duniyar tunani, ina suka nufa to? Sai dai tunawa da ta yi da ai mai kwanoni na gari ta je ta dauko hijabinta dogo irin wanda yake so tana sakawa ta zumbula ta shafa turarenta dan dure sannan ta dauko carbinta da wayarta ta fito ta karasa wajen motarsa ta bude ta shiga tana sakin murmushi ta ce" Ina muka yi magidanci ko gidan zoo?"
Bakin nata da ta ambaci zoo din ya kalla ya cire kai a ransa ya ayana' ai kecema zoo din , da daren nan dan mune aljannu zamu je gidan zoo mu yi me'
A bayane kuwa sai ya girgiza kai bai ce mata komai ba ya ringa tukinsa hankali kwonce har suka karaso anguwar
Baki Hajia ta washe ta kalle shi ta ce" Sai kace wajen Khausara zaka kawo Ni mu yi zumunci, Allah sarki Khausara yarinyar kirki shiru shiru abinta bata cewa komai, Allah ya nunan aurenta na tsumata na tsumumuwata na maka mata magungunan nan na yaran mata ta jiku iya jikuwa ta ringa zubar da........."
"Idan baki yi shiru ba kin san Allah zan sauke ki a tsakiyar titin nan na yi tafiyata, ke wai bakinki baya fadin magana mai dadi sai magangannu irin na gasunnan dai? Ki fa kiyayeni in ba haka ba ina kan bakana sai mun shige cikin samudawan nan na bace maki su dauka su tafi da ke kowama ya huta!" Ya fada a zafafe bayan ya taka birkin motar
Tsitttt Hajia ta yi tana kale kale, idan ba gizo gizo Bama idannuwanta ke maga a gefen cen ai taron samari ne bata gari da karnukansu, yanzu idan ya zubar da ita a nan ai shikenan ya tonawa mai kwanoni asiri, gwara ta yi shiru su je su dawo ita kam yau mai rabata da shi sai Allah
A nutse ya karasa kofar gidan ya tsayar da motar sannan ya sake fuskantar ta
Yanzun a tausashe kadan ya budi bakinsa ya sanar mata ainahin dalilin da ya da ya daukotama ya zo nan din da ita
Kallon da take masa kamar wani wanda ya aikata sabo
Da kyar ta iya budar baki bayan ta tabe ta wani cira kai ta ce" To da bata yi haka Bama sai na san yadda na yi da ita, da kai macuci ne Magidanci? Yanzu Khausararma ka cuta to waye zaka bari? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, dole ya ta gigice ta fita hayacinta, ka ce yanzun ba makiyinta sama da kai kawai?"
Kansa ya mayar ya jingina da kujerar ya lumshe manyan idannuwansa a hankali ya hadiye sawun dake makogwaronsa ya shiga tunanin anya ba ya tafka kuskure da ya zo da matar nan ba kuwa? Yanzun fa ya fada mata yana so ne kawai ta yiwa yarinyar cen fada komai ya wuce, ama ji abinda bakinta ke fada
"Kai, lah, buda ido kalli ikon Allah kamar khausara da kato?" Hajia ta fada tana jimko hannun TAUFEEK
Tsakani da Allah wani irin sarawa da kansa ya yi lokaci daya hadi da wani irin kamewa da kirjinsa ya yi masa bai san lokacin da ya bude idannuwansa ya zuba su a inda Hajia ta nuna masa
Lokaci daya ya sake zuba idannuwan nasa har Hajia ta fice bai sani ba
Yana nan zaune yana kallon dukawar da Khausar ta yi ta gaisar da Hajia da kuma shima wanda suke taren rage tsayinsa da ya yi yana sosa kai da abin ky din hannunsa yana ta sisine kai Hajia kuwa na magana har dai saurayin ya fice ya tafi sannan suka shige ciki ita da Khausar shi dai yana zaune idannuwansa a kafe a dokin kofar gidan
Bai san irin lokacin da Hajiar ta dauka a ciki ba, bai san me da me ta tafka masa ba, yana nan zaune a motar Ac na yi dan motar a kunne take Har Hajia ta fito Mama na biye da ita, KHausar kuwa dauke da kwano rufe ta karaso wajen motar gabanta na faduwa kanta a kasa ta bude bayan motar ta ajiye kwanon saman kujera a hankali ta dago dubanta ta saci kallon gaban, ai kam idannuwansu suka shige cikin junna, nata idannuwan da abin hawaye hawaye, nasa kuwa sun yi wani irin jajajir din da bata taΙa ganninsu a haka ba sannan yana mata wani irin kallon da zata iya fasara shi kamar wanda ke jin haushinta , dan haka a hankali ta sinne kanta ta ja numfashi sannan ta rufe motar ta dawo ta shige gida bayan ta yiwa Hajia salama, Mama kuwa da Hajia a nanma sun dauki sama da minti biyar sunna zantawa kafin Hajia ta karaso ta bude tana kallon TAUFEEK ya gaisar da Mama muryarsa a cakude, maman ta dube shi da kula ta ce" Ashe shiriritar da yarinyar cen ta tafka ko? Ai zata hadu da Ni ne, ana katse zumunci ne dan kawai iya shege? Ka yi hakuri ka ji, in sha Allah zama ta nemeka ne ta baka hakuri!"
Shi dai bakinsa gaba daya ya masa wani irin nauyin da bai san dalili ba
Yana kallon Hajia ta dauko kwanon ta rungume a gabanta ta ce" Ka ga rashin sannin darajar koko, a baya ta dingile shi salon Ya zube na yi asara?, Ja mu je na bada maka maganin mugun ci ka sha ka raga min na sha nima"
Mama kam tana murmushi tana kallo ya tashi motar suka tafi sannan ta koma gidan
Ranta bace ta karasa dakin Khausar ta nemi waje ta zauna ta ce"
............ku taimaka ku yiwa sajidale solidarityππ, ga promotion din, sai na ji kuππππ
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 3οΈβ£3οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicΓ©
Lait de nuit
Parfums dΓ©sodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaΙannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwaraiππ
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuΙi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mataπππππ
Ranta bace ta karasa dakin Khausar din ta dage labulen ta shiga ta zauna lokaci daya Khausar ta dago kanta daga dukewar da ta masa tana kallon Mama lokaci daya mama ta ce" akoy wani abu tsakaninki da TAUFEEK ne bayan zumunci da ya danganci soyaya ko makamancin ta?"
Da sauri Khausar ta kallo Mama tana zarro ido, lokaci daya ta girgiza kai ta ce" Kai , astagfrullah mama da Taufeek kuma?"
Mama ta dubeta da mamakin itama jin astagfarin da ta yi, sai kuma ta tabe baki ta ce" To me kennan? Me Hajia ke fadi haka? Ki karra daure masa fuska sosai ko me?, Bani haske mana na ji?"
Khausar ta sake lumshe idannuwanta wasu hawayen suka biyo su, a raunane ta ce" Mama, wai du tsakanina da TAUFEEK ace yana boye min wasu sirikansa? Yaya yake so na dubi alakarmu kennan? Ni na zata zumunci muke yi na gaskiya wanda ba karya a ciki, sai kawai na kama shi da wannan baban abin? Mama ya zamo min kamar wani bako, kar ki so ki ga yadda ake girmamashi a wajen aikin nan, baba da yaro, ashe shi din baban likita ne muke zaune ya rufeni? Mama ki duba ki gani menene bai sani ba nawa? Ni me nake boye masa ne?, Ni kam ba zan iya ci gaba da wani zumuncin da shi ba, dan na gama dauka cewar kallon shashasha yake min wace ban san ciwon kaina ba, in ba wannan ba a shekarun nan ai da ya kamanta sanar min wanene shi, Mama asibitin lafiya fa shine mai ita, baban likita ne har muΖamin inspector gareshi, me kennan? Mutumen da nake tunanin na fi kowa sanninsa sai na ga nice ban san waye shi ba? Me kuma ya rage?, Ai ya gama bankadar min da komai ko Mama?"
Ta karashe tana jin ciwon abin nan har cikin ranta,
Mama ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da tunanin da ya darsu a ranta ta zauna da kyau tana fuskantarta ta ce" shine zaki yi fushi har haka?, Aikinsa ne fa ya zo masa a haka, bayan wannan din akoy wani abin da kike gannin bai kyauta maki ba da ya taba aikata maki?, Khausar sai nake gannin kin dauki abin nan da zafi, ke da kanki kin san a duniya yana mutuntaki ko? KHAUSAR a tunanina abin alfaharine, kina kallo ba dangin iya ba na Aba yake zumunci da ke, ke kadarama dan ya gane mutanen da basa maida hankali a makarantarku ne din ai ina ganin a kan dalili mai kyau yake tsaye ko?, Ke dinma kina da ladan hakan ko menene?, Khausar ki duba ki gani kina gama karatu kin shige babbar asibiti kin koyi aiki cikin jin dadi dan ke ake koyawa kuma ake ba albashi, kina gamawa gaki yau kece likita a asibitin nan wace da muna firar da wata bakuwar maman biyu sai da ta sake kallona tace lalle mun yi Sa'a, tana son numbarki dan in zata je ta ringa kiranki wai ai asibitin ka samu shigama sai ka dace da Sa'a? Haba Khausar, ke da zaki yi murna ki yi farin ciki ki taya shi da addu'a? TAUFEEK ne fa, yau kuma har ake jin kanku? Ai saima ya ga bakya farin ciki da kasantuwarsa haka ko? Ko kin fi ya kasance maki dai wannan mai shiriritar abokin naki da bai samu gama makaranta ba?, Haba yar gidan Aba ke da kanki??????"
Khausar ta sake sinne kanta ta gaza ba Mahaifiyarta amsa, zuciyyarta na tsintsinkewa tana jin kamar bata kyauta ba, tana kuma jin ai shine bai kyauta mata ba tunda yana tunanin ba zata iya rike sirinsa ba
haka Mama ta bata lokaci tana mata nasiha kan lamarin, har ta umarceta kan ta je ta bashi hakuri goben ta mayar da komai ba komai ba, su ci gaba da zumuncinsu har a ga yadda Allah ya yi, sannan suka tatauna kan bakon nan nata na yau, bako daga zuwa da maganar aure? Eh lalle an sanshi shi din mai sauki ne kan halayan yan gidansu, sai dai ai ba shi zai aurar da kansa na, harda cewa a yau sai ya hadu da Aba ya gaishe shi ya nuna masa yana so? Lalle ko bai zo da wasa ba da gasken yana so din, ko kuwa wani kasurgumin dan rainin hankali ne, wai tafiya zai yi yana so kafin ya tafi a daura masu aure sai ya tafi ya dawo? A nufinsa tafiyar ba zai jima ba zai yi ta?, Lalle yana tare da baban lamari, ta yiwu kuma ADU'ARSU ce Allah ya amsa tashi daya ya kawo mijin ashe a kusa ma yake, kuma gashi ba za'a bata lokaci ba? Kai kuwa da sun ji dadinsu su kam, dan haka yanzunma aduar ta yi a kan lamarin sannan ta fice tana jiran Aban Khausar din
Sosai ta KWONTA da abin a ranta, abubuwa biyun nan, damuwar TAUFEEK sai kuma maganar bakonta, eh lalle bashi da laifi kuma kai tsaye da Mama ya zanta, a maganar nasihar mama kuwa kwarai ta shige ta, ama har yanzu tana jin haushin abin bata san dalili ba sai dai abu daya ta san zata iya aikatawa shine bin umarnin na Mama, zata je ta bashi hakurin ne , ama a cen kasan zuciyarta bata ji in har zata iya dawo da zumuncinsu irin na da ba
A bangarensa kuwa, a wannan dare Yumnah ta amshi maza iya maza, har sai da ta fara sarewa duniya domin bata taba tunanin bayan azabar da ta sha ta first night karatun na jiranta ba, dan kamar wanda wani ya kunno shi, ko shi din kansa cikin Sannin kansa yake? Abinda ya sani zuwa biyu rak da ya mata ba asalin shine abinda ya sa ya amayar da damuwarsa ba, dan ji yake yi kamar ya dan shafa bayan kwarya ne, sai dai gannin irin jigatar da ta yi sai ya daga mata kafa ya bata lafiya, ama ina tsabar ta wahala jikinta ya ki amsa tun karfe bakwai na safe ya gama kimtsawa sannan ya taimaka mata ya shigar da ita mota hankali kwonce ya nufi asibiti da ita, baya wani Dari dari, hasalima yana so ya ga ita din idan ta san waye shi me zata yi dan kuwa a kasan zuciyarsa ya gama yarda cewa a nan zai nunawa mata yana da zuciya shima a jikinsa!
Karfe goma Khausar ta nufi hawa matatakalar office dinsa kanta tsaye
Eh lalle ta ringa jin wani abu mai kama da shayi a zuciyyarta bale idan tana karra kusanta kanta da office din tana sake gannin girmansa a bayyane , sai dai wani gefe na zuciyyarta ke fada mata *TAUFEEK NE, BESTY DINTA* ko me ya zama shi dinta ne dai, da izinin ubangiji ta san zasu sasanta a wuce wajen fushin
Da nutsuwa ta kama abin budewar ta bude bayan ta dan buga , bakinta dauke da salama kasa kasa tana wara dubanta dan son hango shi
A hankali idannuwansu suka shige cikin na junna, Yumnah dake kwonce saman doguwar kujera idannuwanta lumshe tana aukin tunanin abinda ya tsaye mata a zuciya ta rasa mai bata amsa tun zuwansu asibitin nan da mijinta da irin gaisuwar da ake masa ana sir sir, da office din nan da suka shigo, yana shirye shiryen duba lafiyarta wanda hakan ya matukar bata mamaki duba da ai bai gama karatunsa ba, sai baban mamakin ya risketa wani likita ya shigo da wani file suka duba tare cikin dan gaggawa TAUFEEK nata ya shige cikin dakin cen, jim kadan sai gashi ya fito cikin shiga irin ta likita, likitanma baban Likita a gaban rigar da siririn rubutu an rubuta DOCTER TAUFEEK, wanda hakan ya kusan sumar da ita, har ya tabbatar mata yana zuwa zai je tiyatar gaggawa ya dawo ne, yanzu abin ya same shi, ya fice kusan awa biyu da rabi kennan tana kwoncen nan zuciyyarta ta gama cicira mata lisafi sai yi take ta rasa me zata fahimta dan abin nan ya zo mata a ba zata, tarin tambayoyin dake kwakwaluwarta kuwa tamkar zasu fasa mata kai ne, sai ta matar da ta jima bata gani ba , wato mayar mijinta ta shigo da shigar itama irin na likitocin, harma shigarta ta so tsoratata domin sket da riga ne na atampa masu ruwan blu a ciki sai riga fara dake saman su sai dan karamin mayafi sosai da ta dan yane kanta da shi , hannunta daya da agogo dayan ba komai , wuyanta da abin awo irin na likitoci, kaffafuwanta sanye da takalmi plate mai masifar kyau dan ya dauki yan kaffafuwanta da basu da girma, idannuwanta da kwali radau lebenta kuwa da dan jan baki madaidaici uwa uba kanshin da ta shigo da shi kanshi ne mai sanyi du irin kanshin da office din ke yi kuwa ana jin nata kanshi ne mai sanyin gaske da kuma nacin waje, sai kawai Yumnah ta zama mutun mutumi ta zubawa Khausar din ido ta kasa amsa koda gaisuwarta dan sai ta fara tsoron ko ba a duniyar mutane take ba yau? Domin wannan da take gani mace ce mai cikakken classs da kanshi bayan wace ta sani tamkar guzumar mace idan tana tafe take?
Bakinta ta dan dantse a hankali cike da takaicin sabon rashin mutuncin nan na Yumnah, tana kallonta ta yi salama ai ko salamar ce ta amsa ama sai ta wani kafeta da duba irin na rainin nan ba zata yi mata magana ba?
Cire kanta ta yi daga kanta ita dinma, dan kuwa ba zata yarda karamar yarinya ta nemi raina mata wayo ba, a tunaninta rukayama ta girmi Yumnah bale A'isha har a gangaro kanta, idanma wani abu na mata hayaki a kai ta nemi sa'anta ta yi da shi ba wai ita KHausar ba
Gannin kamar baya office din ta juyo a Nutsenta zata bar office din, nan Yumnah ta zubawa bayanta ido, domin Ζarara rigar likitocin ta dage saboda uban Bombon din dake bayanta wanda ya yi wani irin yanayi na heart ya yi dasss a jikinta yake kuma juyawa dan radin kansa ba tare da an saka son juyashi a rai ba , domin da aka so juya shi dan neman fitina da lalle an barawa mata abin duba na gani na fada a idannuwansu!
Handle din ta kama ta bude dan tafiyarta, a hankali idannuwanta suka sauka a saman fafadan kirjinsa wanda ke cikin riga mai dogon hannu baka sidik mai botura a gabanta hannun rigar daya a tatare har cen saman dantsensa hakan ya bayanar da girman hannun da yannayin karfi ya nuna kansa da irin jijiyoyin nan na kakarfan maza sai byro dake cikin hannun , dayan hannun kuwa rike da wani file ga dukkan alamu magana yake yi ta katse a lokacin da suka yi ido hudu da Khausar din
A hankali ya dauke dubansa daga saman fuskarta, itama a hankali ta ja baya ta basu hanya suka shigo domin bayanshi akoy docter biyu, dayar na rike da rigarsa ne , dayan kuwa baya rike da komai sunna ta zantawa ta yiwu kan aikin da suka gama yanzun ne
Kanta sade da girmamawa ta gaishe su a jimlace a matsayinsu na iyayen gidanta sannan ta juya a hankali da nufin barin office din , dan ta ga aiki ne suke yi gashima ya nuna kamar bai wani santa ba????
"Nurse...,......." Muryarsa ta katse mata hanzari, wata murya daban da wace ta sani, murya mai cike da isa da iza da kamala, murya mai cike da aji da hobasa
A hankali ta dakata, sannan ta juyo garesu, dan a wajen nan dai karamin kwarin idan tana da kwakwaluwa itace, dan haka ta dawo a Nutse ta dakata da ladabi ta ce" Yes Sir"
Bai bi ta kanta ba, saman kujerar nan ya karasa ya zauna yana dan wara hannayensa kadan , ya kai dubansa wajen doctor dake gaishe da Yumnah, ita kuwa ta wani gyara zama ta kile abinta tana amsawa cike da aji, dan zuwa yanzu tana daf da gane mijin nan nata fa kamar mataimakin oga ne a wajen nan ko yana kusa da mataimakin ogan
Sai da ya gama shan kanshinsa a jimlace ya miko mata katinsa, katin dake iya bata damar zuwa du inda take so a cikin asibitin kanta tsaye idan ta nuna , take kuma da hop din taba du abinda take so kanta tsaye, cike da basarwa ya ce" ki je cafetariat ki sama mana abinci"
Katin ta amsa, a hankali ta dan sake zuba masa ido, sai ta ga gaba daya duba ko na second daya TAUFEEK bai yi mata ba
A hankali ta juya jiki ba karfi zata tafi ta ji Muryar docter nan macen tana fadin" Sir sai na je na samo abincin mana, kawo katin , Nurse wacece sunnan ki?"
KHausar ta dakata ta juyo yanzunma jikin ba wani kwari ta ce" KHAUSAR "
Likitar ta karaso da nufin amsar katin, dan a ganninta wannan nurse din ta jiya jiyan nan bakuwa ina ita ina samun darajar zuwa aikensa uwa uba harda katinsa? Ina ba zai yiwu ba, sai dai bai bata damar hakan ba da wannan bakon yannayin nasa ya tare mata hanzari ya ce" A'a, ki barta ta je" ya ci gaba da duba takardunsu hankali kwonce ya yi watsi da su su dukansu! Watsi da su mana, daga maganar nan TAUFEEK bai sake cewa da su uffan ba har Khausar ta juya ta fice tamkar an zare mata laka
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
*DA CIWO A ZUCIYATA*
ππππβ€βπ©Ήβ€βπ©Ήππππ
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 3οΈβ£4οΈβ£
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 47