warke "
Aba ya sauke ajiyar zuciya ya fice a dakin, mama kuwa ta yi murmushi tana mamakin KHausar din, koda yake itama cikin KHausar din sai da ta kusa haihuwa cikin ya fara motsi ta fara tsorata tace ai cikinta ana motsa mata, nan ne fa aba ya kaita asibiti aka basu hoton ciki sunna yi aka ga yaro kwonce har ya dauki watanni takwas ba'a sani ba, to kuwa hakan ce ke shirin faruwa da KHausar dan cikin gaba daya a cinyoyinta ya sake badawa da kuma kirjinta , ya yi ham kamar ya yi magana , cikinta kuwa ba zaka gane tana da shi ba, ita kanta mai abin ba ganewa zata yi ba , yan wahalhalun da take sha a wajen miji kuwa ta dauka ne haka yake da wahala ta iya sabawa da yannayinsa, tana iya yinta dan gannin ta saba din tana kuma addu'a
Ko da TAUFEEK ya dawo daukanta a zuwa na uku ta fito Aba ya bata leda shake da hanta mai zafi ya rakata har kusan motar yana ta Adu'ar a sauka lafiya ya dawo ya zauna zuciyarsa da tunanin yar yarsa kafin ya saka Mama a gaba kan sai ta fadawa Maman su TAUFEEK din dan a je asibiti, domin a irin yadda abin nan ya zama yanzu ci gaba ya samu ba'a wasa da harkar asibiti
Da kunya da jin nauyi sosai Maman ta yi kiran numbar maman Taufeek
Bayan sun gaisa cike da jin nauyi Mama ta ce" Mama dama, dama cewa na yi juwar nan ta KHausar ne, a je asibiti "
Mama dake gyaran kayan Baba mai kwanoni ta dakata dan amsa wayar cike da damuwa ta ce" Mamansu juwar ta tashin mata yauma ko? Nima abin nan na damuna, du yadda na yi kuma sai ta nuna wai saboda juwa za'a je asibiti?, Hajiama cewa ta yi wai in bari ba aikin asibiti bane kin ga abubuwan da ta anso take Banka mata ba dare ba rana kuwa? Turare ne wanka ne, ama in sha Allah gobe goben nan za'a je asibiti nice nan zan rakata tunda idan ta kiya masa ban san yaya aka yi baya takurata ba bayan rashin lafiya ce ba abin wasa ba"
Maman su Khausar ta yi dan murmushi tana matse ido dan kunya je dawainiya da ita a hankali ta ce" A'a Mamansu, ai Bama maganar wani ciwo bane in sha Allah, Inaga karuwa ne kawai dan awo ne nace bari in sanar domin ina kyautata zaton itama bata sani ba"
Wani irin tsam mama ta yi, kafin wani irin farin ciki ya shiga mamaye kirjinta tamkar yanzu ne ta ji Taufeek zai iya sama mata jika
Da sauri ta ce" Mamansu kina nufin ciki ne da KHausar?"
Mama ta yi murmushi cike da kunya ta ce" Kai Mamansu Allah ya bamu ALKHAIRI Ni dai na kashe"
Daga nan ta kashe, ita kuma Mama sai ta kasa ci gaba da aikin nata karshema fitowa ta yi ta dauki hijab din ta ta zumbula ta fice da nufin zuwa ta ga ko sun dawo, Duda tunda suka yi kaurar zuwanta daya tak ta saka albarka , sai take ji YANZUN ba zata iya hakura ba sai ta je ta ganta inma da hali a je asibitin nan yanzu, dan in zata irga da kyau KHausar ta jima cikin juwar nan, hakan na nufin ta wuce watannin da ya dace ace ta fara awo fatanta Allah ya sa sun dawo
Tana kokarin karasawa wajen kofar Muryar HAJIA dake rike da leda baka shake da kayan turare turarenta , Hamdiya rike da katon kaskon wutar ta ce" Wace wannan kamar matar mai kwanoni zata je bangaren sirikai"
Tsam ta yi tana zarro ido, sai kuma ta juyo tana murmushi hadi da sosa keya cike da jin kunya ta ce" Lah HAJIA ina yini, dama dama zan leka ne na ga wai ko KHausar din na nan?"
Hajia ta saki murmushi ta ce" Ki ji tsoron mai sama, ba ta zo ta mana Salama ba? Kar ki dauki hali irin nawa kulun ina bangarenku, iyi sirikan zaki sakawa ido? Koda yake gwara in San na bar baya gwara ki fara zuwan kar Na mutu na bar marayan Allah yan uba su ga bayansa, kama ledar mu je in fada maki kowane amfaninsa "
Mama ta ce"
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
*DA CIWO A ZUCIYATA*
๐๐๐๐โคโ๐ฉนโคโ๐ฉน๐๐๐๐
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 6๏ธโฃ3๏ธโฃ
*GARABASA, GARABASA, PROMOTION, PROMOTION DIN LITATAFAN MARUBUCIYAR A KAN FARASHI MAI SAUKI 1K, YAN NIJAR KUWA 1000 FRANCS CEFA*
1: Duk karyar kada
2: Yar mahaukaciya
3: Neman na kaina
4: Bani da zabi
5: Bak'a ce
6: Kutkale
7: Makauniya ce
8: Mage
9: Duk nisan jifa
10: Idan ka raina inda kake
11: Dutse
12: Alkalamin kadarata
13: Bani da zabi
14: Dakika Biyar
15:Wata kokowar
16: Aure yakin mata
17: Ni zan ladabi
18: Daga tafia daukar soja
*Dukansu a kan farashi mai sauki, zaka saka dubu guda ne domin promotion ne nake yi, ka tuntubeni kan layina kamar haka +227 93 81 16 18, Sajida Nijar*
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicรฉ
Lait de nuit
Parfums dรฉsodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*Waษannan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai๐๐
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuษi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata๐๐๐๐๐
Tallah 3
Hajiata, ke kin san rayuwar aure sai da anini, in babu jagab a babar eriya oga ya kama tofa yawu da neman yadda zai yi bawan Allah, idan kuma babar haja a bude ham ai ba labari oga sai dai ya shiga ya fito kamar ya shiga kofar ruwa๐, zo ki ji, a farashi mai rahusa zaki gwangwaje ki rike bakin Elhaji gudun tada yara, ama idan lamari ya yi lamari tsaf zaku karya gadoโน๏ธ๐ซฃ
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI 'DAUKA BA, INA MATA MASU BUK'ATAR 'DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK'ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE AKANSU DAN FARIN CIKIN MA'AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528
kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji
Kad'an daga cikin abubuwan da muke dasu
Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had'u pc +234 703 425 1528
Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k'ara suyi dass abun sha'awar kowane namiji
Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan
Ingantacce Kuma sahihin maganin k'iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar , Rama batayi ba Sam Yar uwa
Sabulun wanka
Kalolin sabulun tsarki
Turaren tsugunno
Turaren al'ajab
Hatsabibin turare
Da sauransu 07034251528
Kalolin gumba
Gumbar Dabino
Gumbar gero
Gumbar madara
Gumbar matsi
Gumbar ukku bala'i
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar sabon budurci
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar aya da kwakwa
Gumbar ridi
Gumbar mazari
Sarauniyar gumba 3in1
Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,
Kalolin gari
Garin mallaka
Garin hutar da malaminki
dakan jaraba
Dakan Amare
Dakan Ni'ima
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Garin sa buzu kuwa
Garin buje.sharkaf
Garin Dan la'asar
Yayan hadiya mai suna dan la'asar
Original Dan goshi
Original Dan goshi (sabon salo)
Original man damo
Original man ayu
Kitsen damo
Sirrin tafin kafa
Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata
Kwallin idonka idona
Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki
Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d'a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had'u pc
Kalolin tsumi
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin madarar ni'ima
Tsumin tabaje
Tsumin Amare
Tsumin sabon budurci
Tsumin nono rakumi
Matan gaske
Ruwan jaraba,
Da sauran kalolin da ban fada ba
Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar
Matsin Dan mannau
Matsin mallaka
Dan la'asar
Sabon budurci
Mak'alemata
Mashahurin matsi
Ukku bala'i
Matsin uban budurwa
Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi
Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,
Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake
*Kyallen al'ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al'ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,
KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen nagari maida kudi gida
07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah
Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528
Maman zarah mabera SOKOTO
Mama ta ce" A'a HAJIA Bara na juya "
HAJIA ta kama hannunta ta saka mata ledar ta yi gaba tana fada da fadin" Aikin banza da na mutu na san da tuni an rabata da mijin tana abu kamar wata wace ta zauna gidan kanwarta , shirme da suka tada rigimar gida in ba dan nace zan dagawa uban kowa nono ba har ta wani ce a bar gidan ita ga wace bata son rigima, Ni ina so kuma du wanda ya dagawa magidanci hankali shi Bama dan balaja'u bane!"
Ita dai Mama sai ta ji kunya gaba daya ta hannata sukuni
Sunna shiga suka tarar da KHausar ta juye hantar nan a plate ta gyara zama saman cafet ta fara ci ta dago tana sakin murmushi da amsa sakamar HAJIA sai kuma ta ga harda mama dan haka sai ta mike gaba daya tana masu sannu ta dauko abinda take dora kaskon HAJIA saboda abin garwashin kar ya zuzube sannan ta je ta dibo masu ruwa ta kawo masu da jus ta zauna tana gaishe su
HAJIA ta mika hannu ta dauko plate din ta dauki daya ta dangwala yaji zata Kai baki TAUFEEK ya sauko daga sama , Allah ya taimake shi da jalabiya a jikinsa ya nufo falon yana jin HAJIA ta ce" Yanzu Khausara abinda zaki ci ki barni Kennan bayan kin ga ba jinnin kirki ne da Ni ba?"
KHausar ta janyo ledar tana fadin" HAJIA kin ga naki nan, biyu na raba dama na daure naki a leda, yinwa ce ta hannani zuwa na kai nace bari na ci sai na kai"
Plate din ya karbe yana sakar mata harara ya ce" An ki ba'a bakin, ke kam gaskiya ki daina zuwar min kina saka min mata a gaba kina hannata ci ta murmuje wannan ai harda daukan alhaki kamar da kudinki aka siyo?"
HAJIA ta kalli Mama ta ce" Ai sai ki amso min ko? Kina kallo d'anki zai min rashin kunya shi algungumi!, Ke Hamadiya je daukon ta ledar , Allah ya taimakeni Khausara na kaunata duk wani wanda baya so sai ya rintse idonsa, yar nan du abinda ta kai bakanta sai ta kai min na kai, har tashina take tana cusan kaza a baki, da babu ita ai da na mutu yanzu, kina gannin tunda Magidanci ya aurota nake Kumari kumatuna sunna dawowa?"
Mama ta sakar masa harara ta ce" Kai, ajiye"
Murmushi ya yi ya karasa daf da HAJIA ya ajiye plate din HAJIA ta zazage sauran hantar ta zauna daf da KHausar suka saka KHausar din a tsakiya ta ce" Saka hannu mu ci, bismilanku ama kar a wuce bibiyu dan Allah, ke Hamadiya karbi nan saka a salatinki maza ki koma wajen uwar rikonki kar ta tsine maki saboda Ni"
Hamdiya ta mike jiki ba karfi ta amsa ta juya ta tafi tana share hawaye, dama ta yi nacin biyo HAJIA ne dan ta san idan har bata ganshi ba yau ta yiwu ita da shi sai a lahira in ana haduwa, Shikenan saboda ta sanarwa mama dan Allah sadakinta da akace za'a kawo gidan iyayenta kar a amsa ita ฦดaฦดansu take so shine ta yi mata dukan Kawo wuka sannan tace zata bar garin a satin nan, ya Allah ita ta san son shi sai ya kasheta
Mama ta rasa ta inda zata bilowa magamar, gashi abin ya tsaye mata a rai sosai ta kasa tashi ta tafi, tana zaune ne HAJIA na cin hantarta da ta kasa tana ta labari , Khausar din na rike da plate din
Ajiyar zuciya Maman ta sauke bayan ta dan yi wani tunani ta ce" KHausar, Ni da kika yi gwajin abinda ke saka ki juwar nan me aka gani?"
KHausar ta kalli Mama tana sauke numfashi ta ce" Ba'a ga komai ba Mama, hatta bugun zuciyata daidai ne"
HAJIA ta ce" Me kuwa za'a gani Allah na tuba , na fada maki a ringa kula da magauta bakya ji, in sha Allah sai na maidawa mai neman Khausara da balaki aniyarsa, da Dije ake zance!"
TAUFEEK ya karbe hantar da ta dauko cikin kason KHausar ya mayarwa KHausar din ya karbe plate din yana sakar mata harara ya ce" Mama, Ni abin nan zan aunata da kaina gobe in sha Allah, ina kyautata zaton bata wani je wajen docter ba dan ba son allura take yi ba"
Mama dake kauda kai ta ce" Ok, Allah ya nuna mana, ama ka yi mata harda pregnancy test "
Da sauri ya juyo daga barin HAJIA dake son karbe hantar ya zubawa Mama ido, itama KHausar sai ta samu kanta da zubama Mama ido jin abinda Maman ta ce, ita kuma Mama sai ta mike tana alamun tafiya zata yi
HAJIA ta mike ta karbi plate din tana fadin" Yau ga bakin ciki, sai na ci, ke minene shi prcy taste din?"
Mama ta yi turus , ta juyo ta zubawa HAJIA ido, gannin itama amsa take so sai ta dan sosa goshinta ta ce" Dama, Mamansu KHausar ce ta yi kirana dazu tace juwar nan ta KHausar a duba ta yiwu wata kama ce"
"Ki rantse da huwa rahamanu, Kina nufin Juwar da y'ar nan ke yi ko sati bata cika a gidan nan a matsayin matar MAGIDANCI juwar ciki ce? La'ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi sallalahu alaihi Wasallam, wayo Ni Dije Allah na gode maka , ke ama tsaya yo wani irin ciki kuma? A irgena ai ta yi wata bakwai a gidan nan ga ciki shafe kamar nawa ? Ke dan mike dan mutun ai ya fi karfin kwonciya a mara ko? Dan mike in gani , kar dai yar nan irin matan nan ne da ciki ke shigewa nono da duwawu, tashi in gani sun karu ne ko mene? Yau na ga ikon Allah Ni Dije, yanzu ciki ne da ke?" HAJIA ke fada tana salalami, Mama ta yi saurin ficewa ya zamto sai TAUFEEK din da KHausar da HAJIA, sunna bin hajiar da kallo tamkar bakuwar halitta
TAUFEEK ya lumshe idannuwansa da kyar, a hankali ya ce" HAJIA barta dan Allah kar ki dagata da karfi mana kin ce a cinya in fa kika daki kan dan ko yar a cinyar nata?"
HAJIA ta saki KHausar ta dan matsa daf da shi ta ce" Kuma fa hakane, to ama kai likita ita likita karatun jabo ne kuka karanta da zaka dirkawa yar mutane ciki ana ce min juwa take? Wannan ai wulakanci ne, Magidanci ka yiwa Allah ka tashi mu je a tabbatar min da cikin nan ko na iya rintsawa, wayo Allah mai alheri ashe ashe abin a kusa yake, kai ana iya shege kace na maka auren dole?"
A raunane ya sake duban HAJIA a fizge ya ce" Tashi ki je bangarenki kin ji kakata?"
HAJIA ta sakar masa harara ta dauke kai ta ce" Aikin birit in ji tusa ai ko tsohon mutun yau ba zai rabani da KHausara ba, kin ga cinye hantar kin ji? Baiwar Allah ashe yan kwadayin da na fara tsorata na ALKHAIRI ne?, In me ta sameni ina ci yar nan sai ta ci shi har na fara tsorata ashe ashe ashe asusun Magidanci ke habaka? Ka tashi mu je!" Ta idasa fada da dan karfi tana wartar kaskon wutar nan ta ce" Bari in kai raushin in zo, dauko mata sutura mu je!"
HAJIA na fita ya samu ya kamo hannayenta yana sake tsatsareta da ido
A hankali ya ce," Dan Allah fada min haka ne? Are you pregnant?, KHausar tunda muka zama abu daya da kwana uku kika fara juwar nan, tl me please Akoy babyna a nan?"
Cike da kunya KHausar ta sada kanta tana janye hannunta , gaba daya ta shiga a halin rudu
Taufeek ya sake janyota jikinsa sosai yana dage rigarta a tausashe ya ce" Kar ki sako kunyar nan yanzu, na fi so na gane eh ne ko a'a? Ina son ganewa"
Ajiyar zuciya ta sauke, ta rasa ita amsar da zata bashi, abinda ta sani shine kwarai lokuta da dama idan mahaifiyarta ta tsananta juwa kwanaki ฦalilan tsakani zata tashi da nakuda ne, ama shin itama irinta ne ko yayane?, Ita dai bata sani ba, kuma shima ta tabbata ya shiga rudani ne na tunanin maganar nan, ko dan shi din likitan kwakwaluwa ne ba na mata ba? Ama koda likitan kwakwaluwa ne yanada wasu sani a fanin matan, shine zai fada mata ai ba ita ba,
A sanyaye bayan ta kama hannun nasa itama ta ce" TAUFEEK ban sani ba, ban sani ba, Ni dai na san ina juwa, ina cin abinci fiye da da, wani lokacin kuma nakan ji gajiya sosai ama da zarar na yi barci Shikenan sai ka ga komai ya wuce"
Zai kuma yin magana wayarsa ta ringa ringing sosai a dole ya dauko ya daga bayan ya ga mamansa ne
Da wata Muryar da maman bata cika amfani da ita ba ta ce" TAUFEEK dama Yumnah nakuda take yi tunda yama ban sani ba?"
A hankali ya samu kansa da lumshe ido, a Nutse ya ce" Nakuda?, Ban je part dinta ba , tana wajenku ne?"
Mama ta furzar da hucin bacin rai , ta cire hijab dinta ta ce" Ni na isa na san abinda take ciki ko na kai matsayin sani? TAUFEEK ace ina cikin gidan nan da raina da lafiyata ka auro macen da zata raina Ni? Tun ban yarda na furta ba har ta kaini makura? Ni makiyiyarta ce ko bata san girman mahaifiyarta ba da zata raina Ni?, Ace ina cikin gidan nan jikinta ya motsa na abin dake cikinta wanda nake cikin zumudin zuwansa duniya nake siye siye dominsa nake addu'a ba dare ba rana kan Allah ya nuna min, sai yanzu HAJIA nawarah ta shigo ta fada min cewa wai tunda yama sunna tare da mahaifiyar Yumnah a bangarenta tana kan gwuiwa YANZUN dai jikin ya motsa sosai ta yiwu haihuwar ce in sanar maka zasu tafi asibiti? Na nuna a kan me ba'a sanar min ba tace wai Yumnar ce bata so KHausar ta san tana nakuda sai dai ta ganta da abinda ta haifa? Wannan wace irin masifafiyar nataciyar gaba ce yarinyar nan ke fama da ita a ranta tana tare da yan zuga?, To bari ka ji, ina fatan matarka ta sauka lafiya, ama ka sani na kai makura , tunda har Ni Khadija ban isa da ita ba ba laifi Allah ya raya , ama Nima babu ruwana da dukkan abinda ya shafeta , ciki harda abinda zata haifa!"
Daga haka Mama ta katse kiranta ta jefar da wayar ta yi zaune a bakin gadonta tana dafe kanta wasu hawaye Masu zafi suka balo mata
Shin yaushe ne zata samu sasaucin zama da abokanan zamanta? Ko dai har ta koma ga Ubangijinta ba ranar samun sauki? Tun bata saba wahalaliyar raayuwar nan ba har ta gane in fa ba kanta ta rike ba komai na iya faruwa ciki harda sakwantar mata da cilon danta, sai ta basu lafiya take rayuwarta a gefe itama
Ama abu kulun cikin tugu da shari kala kala ake yi mata?
Tun tana da jan sawunta har yanzu da jinni ya dauke mata take kokowa da su da lamarinsu, shin yaushe zasu bata lafiya? Ace matar TAUFEEK, TAUFEEK nata , sai dai ta hangota da su? Me take tunani ne ita Yumnar?, Ba damuwa ko TAUFEEK suka kwace zata yi addu'a ta bishi da addu'a bale wata Yumnar banza da wofi, Allah ya taimaketa ga KHausar, wace ta mayar da ita tamkar uwar da ta haifeta, tunda ya auri KHausar take rayuwa da yanci itama a cikin gidan, take da abokiyar fira, mai yi mata girki ta kawo mata, mai zuwa ta yi mata fira, mai share mata kaso tamanin a damuwarta, kuma ga kyautar Allah ya bata itama, in sha Allah zata kaita asibiti da kanta gobe da safe a duba mata ita, su dawo ta raini cikin nan dan ba zata yarda ta koma aiki ba sai ta haihu da izinin ubangiji
A kalla ta dauki minti ashirin a zaunen nan tana share hawaye ta ringa jiyo hayaniya sama kamar za'a tsaga falon nasu
Sai da ta Saurara sannan ta ji gabanta ya fadi, ba dan komai ba sai dan tunawa da ta yi waye danta da tsinkayo muryarsa da ta yi sama da ta kowa, da Muryar kakarsa na dafe masa baya sai uwa uba Muryar mahaifinsa
A dole ta saka hijab dinta ta fito sanan ta nufi kasan tana kallon taron ba laifi harda maman Yumnah da yayarta da kuma Yumnar dake murkususu ko yaya aka yi aka nufo nan da ita kuma?
Mai kwanoni ne ya sauke ajiyar zuciya dan ya san yanzu rigimar ta lafa tunda wace ake rikicin kanta ta sauko, ya kuma san ita din mai hakuri da sanyaya fitina ce da KOWAMA bale in ta ga abin ya shafe shi, sai ya sauke ajiyar zuciya a karro na ba adadi ya ce" Maman Magidanci, ai gwara da kika sauko, shin ko me ya bata masa rai ai yana iya yin hakuri har wannan taa samu lafiya , haihuwa ai ba wasa ba maman Magidanci , sun fito zasu shiga Mota su nufi asibiti wai ya tarda su yace idan aka fita da ita a bakin aurenta sai kace ba likita ba? Kuma na yi tsawar kin ga HAJIA a gefe kin san dai ba barina zata yi in Hanna ba, dan Allah a yi hakuri a yayafawa matsalar ruwan sanyi, komai ya yi zafi maganinsa Allah, kuma hakuri shine ja gaban komai a rayuwa kin ji maman mai kwanoni?" (Wato ashe da baya kiran sunnanta dan fa ci sunan HAJIA ne?)
Mama ta kai dubanta kan KHausar wace mahaifiyarta ke sake talabarta dan ko tsayawa ta kasa yi, da gaske haihuwa ta zo mata dan kiris ya rage dan du ta fita hayacinta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 47